Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dole  sai a hospital ba  " shazim ya faɗa

Majeed yace "to shikenan , Allah ya bata lafiya "
"Ameen ya Allah " shazim ya amsa, babu wanda ya ƙara cewa komai cikin su har suka ƙara so  gida, horn su kayi da sauri mai gadi ya buɗe masu, ciki su ka shiga, a compound drivern yayi parking da Ambulance ɗin, jin jiniyar Ambulance ne yasa Ammy dake parlor zaune fitowa da sauri gaban ta na faɗuwa, tana fitowa su shazim na fito da fatima, da sauri ta ƙara so kusa da su dan taga waye kuma ba lafiya, ai ko da tayi arba da fatima kwance kamar matacciya,wani mummunan faɗuwa gaban ta yayi, jiri ne ya fara kwasarta  ta tafi luuu zata faɗi  babu wanda yalura da ita sai noraiz,da wani masifafen gudu  ya ƙaraso wurin ta yana kiran sunan ta cikin ƙaraji  ya ganin ta tafi luuu zata faɗi,ririƙeta yayi,ƙasa suka nufa shi da ita dan tuni har ta sume,  gaba ɗaya hankalin su shazim ya dawo kanta, shazim a tamanin ya ƙaraso wurin su  saura kaɗan ya faɗi......

_Episode  _44_45_

_..........Gaba ɗaya hankalin su shazim ya dawo kanta, shazim a tamanin ya ƙara so wurin su  saura kaɗan ya faɗi, tallabo kanta yayi  yana kiran sunan ta

"Ammy!  Ammy!!  pls ki tashi dan Allah " sai ro ƙwan ta yake da ta tashi duk ya bi ya firgice sai jijjiga ta yake, noraiz ban da kuka babu abun da yake, ilya ne ya shiga ciki da sauri, ruwa ga ɗauko a kitchen da sauri ya fito ya dawo wurin su, Abdallah ne ya amsa ya nufi ammy da ke kwance a jikin shazim, da sauri ya kwance marfin robar ruwan ya shiga  yayyafa mata sai da ya yayyafa mata kusan sau ukku sannan ta ja wani dogon numfashi, Alhmdllh su ka shiga furtawa, hawaye ne suka taru idanuwan ta
" mi ya faru da fatima??, kar ka saki kace man ta mutu  " tana faɗa hawayen da suka taru a idanuwan ta na zuba, abun tausayi su Abdallah ma sai da zuciyoyun su suka karaya ganin yanda Ammy ke zubar da ƙwalla
"ki kwantar da hankalin ki Ammy, ba wani abu bane ya same ta lafiyar ta lau "
"taya zaka ce man tana lafiya bayan na ganta a haka "

"da gaske nake Ammy, ki kwantar da hankalin ki " ya faɗa haɗi da kallon su majeed yace " majeed ku shiga ciki da ita " da to majeed ya amsa, shi da Abdallah su ka shiga da fatima, da sauri Ammy ta tashi ta bi bayan su, bin bayan ta noraiz yayi ya na  share hawaye , shazim kallon sa'ada da ke gefe rakuɓe gefe sai hawaye take  yayi yace " shiga ciki mana " da to ta amsa haɗi da bin bayan su noraiz ta shiga ciki,komawa yayi cikin Ambulance ɗin ledar magungunan fatima ya ɗauka sannan yayi ma drivern sallama, bai  shiga ciki ba   waya ya ciro daga aljihun wandon shi, dialing ɗin wata number yayi,wanda ya kira na ɗagawa bai ko amsa mashi sallamar da yake yi ba yace " kayi sauri ka  kawo man na dawo " yana gama faɗa yayi rejecting kiran, ciki ya nufa, bai same su a main parlor ba hakan yasa shi nufar medical room ɗin su dake kusa da part ɗin shi, tura ƙofar yayi ya shiga ciki, tsai tsaye ya same su fatima kuma na kwance kan gadon marasa lafiya gaban gadon ya ƙarasa haɗi da ajiye ledar da ke hannun shi kan ɗan table ɗin dake gefan gadon wani drip ya sake fiddowa daga cikin ledar haɗa shi yayi duk su Ammy na nan sun zuba mashi ido harya gama haɗa shi ya sama fatima, sai da ya gama dai data komai sannan ya kalle su yace " mu fita mu bata wuri "
ficewa su kayi zuwa waje, ban da Ammy matsawa ma tayi kusa da gadon ta zauna kan wata kujer ta roba  dake gefan gadon
"Ammy mu fita bata son kowa kusa da ita yanzu " shazim ya faɗa
"babu inda zani, ina nan har sai ta farfaɗo ta faɗa man abun da ya same ta " lallashin ta ya shiga yi akan ta tashi su fita amma ƙiri ƙiri tace bata fita, saima tsare shi tayi akan dole saiya faɗa mata abun da ke damun fatima shiru yayi yana kallon Ammy ba tare da yace mata komai ba
"magana nake maka shazim mike damun fatima ka wani tsare ni da idanuwa kana kallo na" Ammy ta faɗa da damuwa a fuskar ta, duk ta damu da son jin miya samu ɗiyarta
"kiyi haƙuri Ammy kamar yan da nace maki ciwanta ne ya tashi "
" haba shazim sai kace dai ban san yan da ciwan nata yake ba, kuma yaushe rabon da ya tashi ina tuna nin tun tana ƙarama kuma  kai da kanka kace man ta samu sauƙi idan ba abu yayi tsanani ba ba lallai bane ciwan ya tashi"
"haka ne Ammy, amma ai bai zama dole sai abun yayi tsanani ba"
"shazim!  shazim! !  shazim!!!,  sau nawa na kira sunan ka "
"sau uku Ammy "
"to ka faɗa man mike damun ɗiyata mi ya haddasa mata wannan ciwan tun kafin ranka ya ɓaci, idan ma laifi tayi maka ka dake ta ka faɗa man dan na fara zargin laifinka ne ciwan ta  "
"Ammy kema kin sani bazan taɓa sa  sannu na daki fatima ba ko kau mi tayi man "
"to naji faɗa man mi yasa same ta " baya son ya faɗa mata ne dan kar ta tashi hankalin ta sosai,
"kayi shiru?"
"zan faɗa maki Ammy, amma yan zu ina so na ɗan watsa ruwa, zan zo part ɗin ki na same ki "
"na lura dai faɗaman ne baka son yi "
"ba haka bane Ammy zan faɗa maki amma yanzu ki bari na watsa ruwan, ko fa breakfast ba muyi ba mu ka taho" jin yace ko breakfast basu yi bane yasa tace " to shikenan na ji zan koma part ɗina, amma kar ka shanya ni, zan sa Innah Asabe ta shirya maku breakfast a dinning "
"insha Allah da na shirya zan shigo "
"to shikenan "
fita su kayi daga ɗakin, bin bayan Ammy noraiz  da sa'ada su ka yi , a parlornta ta zauna kan sofa,  kusa da ita noraiz yazo ya  zauna, sa'ada kuma kan sofa ta zauna tana faɗin " ina kwana Ammy " kwata kwata Ammy bata san da sa'ada aka zo ba sai yanzu da ta gaishe da ita sannan ta san da ita su ka zo " lafiya lau sa'ada  tare ku ke kenan "
" eh Ammy, ya gida "
" Alhmdllh, ya su momyn ku "
"suna lafiya "
"Masha Allah "Ammy ta faɗa
Innah Asabe ce ta shigo parlorn, gaishe da ita noraiz da sa'ada su kayi, cikin kulawa ta amsa tana tambayar ya mutanen abuja.

_*✨SHAZIM✨*_

A bakin part ɗin shi ya sami su Abdallah sun yi  tsaye, kowa da abun da ke damun shi majeed gaba ɗaya hankalin shi a tashe yake burin shi ɗaya su keɓe da shazim yaji miye ke damun ta yayin da Abdallah ke gefe guda sai cika yake yana batsewa duk dan saboda majeed dan duk ya lura da take taken shi, da kallon shazim ya bi su,  murmushin gefen baki yayi
  yana faɗin "lafiya dai dakarun yaƙi, duk kun wani yi ma mutane cirko cirko sai kace wasu body guard "
majeed ne yace " dan Allah ka ajiye  wannan wasan a gefe,  ka ƙi ka faɗa man mi ke damun fatima dan na daɗe ban ganta aciki irin wannan halin ba " 
  Abdallah ne yayi saurin cewa
"wai kai dan Allah wannan damuwar ta micece ne, duk ka wani bi ka damu mutune da mike da munta sai kace in an faɗa maka ɗauke mata ciwan zaka yi " wani ɗan iskan kallo majeed ya bi Abdallah da shi can kuma sai yace
"in abun da ya dame ka ne wai da tambayar da nake tun da ba kai nai mawa ba, wai ma miye naka a ciki ne  ina ruwan ka da ni ne ma"
"wannan kuma matsalar kace" Abdallah ya faɗa haɗi da jan tsaki ya shige part ɗin shazim, shazim dai na tsaye yana bin su da idanuwa  dariya ce ke cin sa amma sai ya ɗaure fuska bai yi ba amma a zuciyar shi dariya kawai yake mas.

Majeed ne yace " ni wallahi abun a hashim ma mamki yake bani, dan na tambayi abun da ke damun ta laifi nayi ne zai wani dage shi a dole kar a tambayi mike damun ta sai kace wani mugun abu "

Shazim ne yace " kar ka damu ranshi ne kawai a ɓace ba wani abu ba "
"dan ranshi na a ɓace shine zai ta wannan ƙarfin halin"
" ya isa dai yanzu kayi haƙuri, komai ya wuce  "
hmmm kawai majeed yace dan ba ƙaramin ɓaci ranshi yayi ba da abun da Abdallah yayi mashi,
"kayi tsaye mu shiga ciki " shazim ya faɗa, ok kawai majeed yace haɗi da bin bayan shazim su ka shiga ciki, zaune su ka samu Abdallah kan sofa ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya jin alamar shigowar su ne yasa shi zaro wayar shi da ke cikin aljihun shi yayi dialing number Abie, yana picking ya tashi ya fita zuwa waje, a bakin ƙofar part ɗin ya tsaya amsa sallamar da abie yayi yayi sannan yace " ina kwana abie, ya su mom "
"lafiya lau, ya su shazim ɗin ya kuma jikin ƙanwar tasa "
" lafiya lau abie, jikin ta da sauƙi "
" to Allah ya ƙara sauƙi, shazim ɗin na kusa "
" eh bari na bashi "
" to " abie ya faɗa, ƙofar ɗakin ya tura ya shiga ciki, zaune majeed yake yayin da shazim ke tsaye bakin fridge, ƙara sawa Abdallah yayi kusa da shi miƙa mashi wayar yayi yana faɗin  " abie ne ke magana" ok shazim yace haɗi da amsar wayar ya kara akunnen shi " ina kwana abie "
"lafiya lau shazim, ya kwana biyu, ka yada mu ko " murmushi yayi yana cewa " ba haka bane abie, ya mom "
"haka ne mana shazim,ban taɓa ganin ƙafar ka a katsina ba  idan ba abuja kaje ba nima  ina nan ai ban taɓa ganin ka ba "
"Insha Allah abie ina nan zuwa , zan maka zuwan baza ta "
"to Allah yasa, ya jikin fatima "
"da sauƙi abie "
"to Allah ya ƙara sauƙi, ga mom ɗin ku nan za ku gaisa " abie ya faɗa, to shazim yace , muryar mom yaji tana cewa "shazim ya gida "
"lafiya lau mom,ina kwana "
"lafiya lau, ya su ammyn ku "
"lafiya lau su ke "
"Ashe fatima ba lafiya,to Allah ya bata lafiya "
"Ameen ya Allah "
"Ammyn ku na kusa "
"A'a tana part ɗin ta "
"to shikenan ka gaishe man da ita   dan Allah "
"insha Allah zata ji "
"yawwa to nagode sai anjima " mom ta faɗa haɗi da yin rejecting,cire wayar yayi daga kunnan shi haɗi da miƙa ma Abdallah , amsa Abdallah yayi.
bedroom shazim ya shiga, kamar yanda yace ma Ammy wanka yayi jallabiya ya sa ya fice zuwa part Ammyn zaune take kamar ɗazu, sai dai yanzu ita kaɗai ce noraiz na part ɗin shi sa'ada kuma na ɗakin fatima,  zama yayi kan aofar da kusa da wacce Ammy ke zaune
"Ammy " ya kira sunan ta  a hankali , juyowa tayi tana kallon shi, magana ya soma cikin natsuwa
"Ammy kiyi haƙuri da abun da zan faɗa maki "
"ina sauraron ka shazim, haƙuri kuma ya zama dole tun da bazan guge abun da ya riga ya faru ba " ajiyar zuciya ya ɗan sauke, duk abun da ya faru a Abuja sai da ya sanar da ita har da irin matakin da ya ɗauka a kan luqman sai da ya faɗa mata, Ammy taci kuka kuma taji haushin hukuncin da su uncle Ahmad su ka yanke ma shazim dan kwata kwata bata son feenah , saboda rashin tarbiyar ta da rashin kamun kanta taso ace da kairiyya suka haɗa shi bawai da feenah ba, sannan ranta yayi matuƙar baci da luqman ta so ace shazim yayi mashi hukunci fiye da wanda yayi mashi, ta san duk abun da ya faru a kwai sa hannun innah da gwaggo Uwani
"na sara miyasa innah bata ƙaunata da su shazim wai mi nayi mata ne a rayuwa, duk abun sadiq yayi mata amma da wannan zata saka mashi, ya Allah ka kawo man ƙarahen wannan al'amarin " Ammy ta faɗa a zuciyar ta
kallon shazim tayi tace " yan zu yaushe su ka ce sun tsai da ranar bikin "
"ni ban san yaushe za su tsai da ba, bana ma so na san lokacin "
"shi luqman da yace yana son fatimar sun amsa cewa zasu bashi "
"a lokacin basu amsa ba, amma na san zasu amsa ne,amma ki kwantar da hankalin ki Ammy babu mai ma fatima auren dole da wannan yaron in dai ina raye "
"shazim bana son ka nuna ba su isa da kai ba ko dan yan Ibrahim ya kula da rayuwar ku "
"Ammy ni bazan nuna masu basu isa da ni  ba, amma bazan bari su zalinci fatima ba"
"shikenan, amma auren naka da feenah fa, na so ace da kairiyya su ka haɗa ka  ba wai feenah "
"dan Allah ma Ammy ki bar wannan zancen, ni bazan auri wannan yarinyar ba ko kuwa mi zasu yi"
"shikenan, fatima yan zu miye yake damun ta "
"jikin ta da suƙi kawai dai alurar da nake mata ce ke sata bacci saboda firgitar da take yi ne, amma insha Allah nan da zuwa anjima ma zata iya farkawa "
"Allah ya bata lafiya, amma gaskiya luqman bai kayuta man ba, mi yasa zai yi man haka a rayuwa"
"Ammy kar ki damu da batun luqman yanzu abun da yaso ya aikata Allah bai bashi sa'a ba ta dalilin ciwan fatimar daya tashi sai yaji tsoro bai mata komai ba,  dan haka ki kwantar da hankalin ki kawai "

_Abun da ya faru, lokacin da fatima ta fice daga parlorn da suke taro,luqman  shi kuma haushin ta nuna bata son shi ne yasa shi fita ya bi bayanta ya tare ta yana mata masifa ita harta isa tace bata son shi daga zai taimaka mata shine zatace bata son, angaya mata shima son ta yake, kawai dan an haɗa shi da Allah ne akan yace yana son ta ne yasa yace yana son ta,maganar daya faɗa ce ta wai an haɗa shi da Allah yace yana son tace ta ɓata mata rai ta kai ga zazzaga mashi masifa son ranta hartana ce mashi ɗan shaye shaye, shikuma haushin rashin kunyar da tayi mashi ne yasa cewa yau sai ya nuna mata cewa shi cikaken ɗan iska ne,  shine fa ya saɓeta kan kafaɗa, tana kuka ta kai mashi duka a baya har cizon shi tayi amma ya ƙi sauke ta har sai da ya isa ɗakin shi sannan yayi wurigi da ita kan gadon shi haɗi da maida ƙofa ya rufe ba tausayi ya afaka mata,kuka ta shiga yi tana roƙwanshi daya ƙyale ta amma sam sam bai saurare ta ba,dan ma kar ta sa wani ya jisu ne yasa shi rufe mata baki da nashi,sumbatar ta ya shiga yi ba arziƙi tun tana kuka har ta kai ga fara kai mashi duka ta ko ina har da cizo da ya kushi, wani ya kushi  ne da takai mashi a gadon bayan shi ne yasa shi haɗa ta da bango har kanta ya fashe ta kifa ƙasa azabar zafin da taji ne yasa ta fasa ƙara wanda hakan ya jawo hankalin dady daya shigo part ɗaukar key ɗin mota saboda suma da feenah tayi zai kaita asibiti, da yake ɗakin luqman ɗin yana kusa da na shi shiyyasa yaji ihun da fatima ta tayi, har ya shiga ɗakin ya same ta ya she a ƙasa shikuma luqman tsaye yana zare ido duk ya tsorata, anan sai da dady ya wanke shi da mari kafin yasa shi su ka kama fatimar suka shiga part ɗin shi da ita duk yayi hakan ne dan kar shazim ya san abun da ya faru yayi tunanin suma kawai tayi na tsoro bai san lalurar ta ce ta tashi ba, sai da suka ya yayyafa mata ruwa ta ƙi tashi sannan hankalin dady da na luqman ɗin kanshi ya ƙara tashi
momy kuma motsin su ne yasa nufar part ɗin dadyn amma sai ya hanata ganin fatimar ba irin tambayar da bata yi mashi ba dan taji ihun fatima amma dady yace ba komai, da sa'ada ta faɗa mata ba'aga fatima bane yasa ta zargin ko dai fatima ce_

"shikenan shazim, amma taya zan yarda bai keta man haddin yarinya ba"
"nasa matar uncle ɗin Abdallah tayi mata awo kuma sakamakon ya nuna cewa ba abun da ya same ta "
"to shikenan Allah ya bata lafiya,  kaga ma ko gaisawa ba muyi da Abdallah ba nagama kamar har da Abdulmajeed ku ka shi go "
"Eh tare muke da shi "
"to bari nasa sa'ada ta kawo maku breakfast naji kace bakuyi break ba kuka taho "
"Eh Ammy " shazim ya faɗa haɗi da tashi ya nufi part ɗin shi wurin su Abdallah.

Ɗakin fatima Ammy ta nufa, zaune ta samu sa'ada bakin gado ta zuba uban tagumi
Sallama Ammy tayi sa'ada bata amsa ba ganin kamar hankalin ta baya tare da jikin ta ne yasa shiga ciki  kusa da sa'ada ta ƙarasa, dafa kafaɗar ta tayi tace " sa'ada lafiya kika zuba uban tagumi ina sallama bakya ji "
" ba komai Ammy "
"ya za kice ba komai bayan na ganki cikin damuwa haka, ko dai duk a kan fatima ne " ɗaga mata kai sa'ada tayi alamar eh
"ki kwantar da hankalin ki za ta samu sauƙi insha Allah "
" to Ammy "
"yawwa, zo ki je part ɗin shazim ki kai masu breakfast,ke ma kizo kiyi "
"to Ammy ta faɗa haɗi da miƙewa su ka fita zuwa dinning, jera mata kayan breakfast ɗin Ammy tayi a tray, trayn ɗin bai ɗauke kayan duka ba hakan yasa Ammy cewa taje ta dawo sai ta kai masu sauran da to ta amsa har ta kama hanya zata nufi sama sai ga noraiz ya sauko amsar trayn yayi yace taje ta ɗauko sauran dan yaji lokacin da Ammy ke cewa taje ta dawo ta ɗauki sairan, " to ya noraiz " ta faɗa haɗi da komawa ta ɗauko sauran ta bi bayan shi, a bakin ƙofar part ɗin suka tsaya.

Sa'ada tayi nocking, shazim ne yazo ya buɗe masu, amsar trayn da ke hannun sa'ada yayi noraiz kuma ya shiga da wanda ke hannun sa, juyawa sa'ada tayi ta koma parlorn Ammy
"yawwa har kun kai masu "
"Eh "
"to kema jeki kiyi naki breakfast ɗin" da to ta amsa haɗi da nufar dinning ta zauna ,noraiz ma da ya shigo parlorn  dinning ɗin ya nufa  samun wuri yayi ya zauna , sa'ada tayi serving ɗin shi
Ammy kuma ɗakin ta ta nufa ta kira malam da ummy ta sanar da su da wowar su shazim da kuma rashin lafiyar fatima, malam ranshi yayi matuƙar ɓaci ya kuma ce wallahi babu wanda zai Aura ma  fatima luqman, idan da yayi shiru innah na abun da ta gadama akan su yanzu bazai yi shiru ba sai dai duk abun da zai faru ya faru.
"insha Allah ina nan zuwa anjima na duba jikin fatimar "
"ai baba da kun barshi, jikin nata da sauƙi "
"A'a, sai na zo "
"to shikenan Allah ya kawo ku lafiya " da Ameen malam ya amsa,  rejecting kiran yayi.

wanda shazim ya kira a waya ne yazo, magungunan ne ya kawo mashi wanda zai cigaba da ba fatima.

sai bayan sallar asr majeed ya tafi gida, akan zai dawo da daddare ya sake duba jikin fatimar,Abdallah kuwa kamar ya shaƙe majeed haka yake ji, shima majeed ɗin haushin Abdallah yake ji dan gani yake duk wannan abun da yake yana yi ne saboda kishi, ya lura son fatimar yake
ko wannan su kishi ne ke ɗawai niya da shi.

Kamar yanda malam yace da daddare su ka zo shi da ummy,  majeed  ya dawo shi da mamar shi daya faɗa mata fatimar bata da lafiya shi ne tace zata zo ta gaishe da ita, sun daɗe a gidan daga baya su ka tafi, su malam kuma shazim cewa yayi dan Allah su kwana nan,
"A'a aboki gida zan koma, ai nace sai ranar da ka zama babban mutum tuk zan dawo gidan nan "
"dan Allah dai malam  iya yau fa "
"ahab sai dai kayi kuma, komai dare sai na tafi gida fatimar dai ta farka  " ba yanda bai yi da malam ba amma yace a'a bazai kwana ba ba dan ya so ba ya haƙura, tun suna sa rana farkawar fatima har suka fara fdda rai malam ma har ya ce ummy ta zo su koma gida, Ammy ma ta so ace sun kwana Amma yace A'a gobe dai zasu dawo idan ta farka, rakiya su kayi masu har parking lot idan drivern malam yake sai da suka ga tafiyar su tukun suka koma ciki.
kowa shirin kwanciya yayi ya nufi ɗakin shi, Ammy ta so ta kwana medical room ɗin wurin fatima gudun kar ta farka cikin dare amma shazim yace ta bari shi zai kwana ɗaki ita ta tafi ta kwanta kawai, tafiya tayi amma gaba ɗaya hankalin ta na kan fatima ko da ta tafi ɗakin ta bata kwanta ba alwala tayi ta shiga nafilfilo tana roƙwan Allah ya fatima lafiya, sa'ada kuma a ɗakin fatima ta kwana.
Shazim bedroom ɗin shi ya shiga yayi wanka ya canza kayan da ke jikin shi zuwa na bacci parlor ya dawo wurin Abdallah dake zaune yana latsa wayar shi shima sanye yake da pajamas, kallon shi shazim yayi yace " ka shiga ka kwanta ni zan kwana wurin fatima dan ina kyautata zaton zata iya farkawa a kowane lokaci "
"bana jin bacci, kai idan kana ji zaka iya kwanciya ni sai na zauna na jira ta farka " murmushi shazim yayi dama ya san in dai yace zai haka to Abdallah bazai kwanta ba
"ko ina jin bacci dole na haƙura"
"kai kana ma ji ke nan "
"na san kai ma kana ji sai dai ka ƙi kwanciya "
"to ina ji bazan kwanta ba"
"to ai shikenan " shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya ɗauki laptop ɗin shi, tashi Abdallah yayi ya bi bayan shi, medical room ɗin su ka nufa kan sofa suka zauna, shazim na aiki a laptop yayin da Abdallah ke aikin latsar waya......



_Episode  46_47_

..........Medical room ɗin su ka nufa kan sofa suka zauna, shazim na aiki a laptop yayin da Abdallah ke aikin latsar wayar shi,suna ɗan taɓa fira jefi jefi, har shazim ya gama abun da yake a laptop fatima bata farka ba, wajen Asuba ta fara mutsu mutsun farkawa, da sauri su ka ƙara sa wurin ta, sai kiran sunan Ammy take da shazim,sai ƙoƙarin tashe take mai da ta yayi ya kwantar "ya shazim ina Ammy " fatima ta faɗa
" Ammy tana ɗaki bacci take, ya jikin naki "
"ya shazim ina nake "
"kina gida ya jikin "
"ya shazim ina ta kiran ka amma baka zo ba "
"yanzu ai  gani a kusa da ke "
"ya noor ma da Ammy duk na kira su amma basu amsa man ba, ya luqman so yayi ya kashe ni ya shazim " ta faɗa hawaye na bin idanuwan ta, sosai ran Abdallah  ya ƙara ɓaci da abun da fatima ta faɗa
"kiyi haƙuri kinji, bazan sake bari wani abu ya faru dake ba insha Allah, ki kwantar da hankalin ki "
"dan Allah ya shazim kar ka bari su Aura man shi wallahi bana son shi "
"bazan taɓa bari su aura maki shi ba karki damu "
"ya ina son ganin Ammy "
"Ammy bacci ta ke fatima, dare ne yanzu ki bari sai da safe zata zo kinji "
Abdallah na gefe ya

Please Login or Register in order to submit comment