Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗakin ta "
"bata can " noraiz yace " kila tana part ɗin uncle Ibrahim "
"mi take a can kuma?" shazim ya tambaya "nima ban sani ba "
"to kaje ka kira ta " da to noraiz ya amsa haɗi da juyawa ya nufi part ɗin uncle Ibrahim shi da mahmud,da sallama su ka shiga part tsit main parlorn babu kowa, bedroom ɗin sa'ada suka a bakin ƙofar ɗakin suka tsaya mahmud ne yayi nocking, zaune take bakin bed tana kuka taji ana nocking, tashi tayi ta nufi ƙofar ta buɗe mahmud ne yace " sa'ada kice ma fatima ta fito su tafi "
cikin muryar kuka sa'ada tace "ai bata nan, ina tunanin tana ɗakin ga " noraiz yace "bata can " maimaita maganar sa'ada tayi "bata can yaya, to ina ta tafi?"
"shine ba mu sani ba, mun ma yi tunanin kuna tare "
"ai tun da ta fita a parlor na biyo bayan ta ban san ina ta shiga ba da na zo ɗaki banganta ba  sai nayi tunanin ko tana ɗakin ta , to ko dai tana tare da Aunty kairiyya " sa'ada ta faɗa, fita su kayi zuwa part ɗin uncle Ahmad mahmud da sa'ada ne suka shiga part noraiz wurin shazim ya nufa, yana isowa shazim yace "wai ina fatimar ne kasan ƙarfe nawa yanzu "
"yaya gata nan zuwa, bata tare da sa'ada ne " ok kawai yace, gaba kusa da driver noraiz ya buɗe ya shiga, mahmud ne ya fito shi da sa'ada wurin su suka nufo tun kafin su ƙara so noraiz yace "tana ina "
sa'ada ce tace "can ma bata nan " shazim yace "bata nan" ɗaga mashi kai sa'ada tayi alamar eh, wayar shi ya ciro ya shiga dialing number ta tana ringing amma ba'a ɗauka ba, tsaki shazim yaja yana faɗin "amma sai na ci mutuncin yarinyar nan" sai da yayi mata kusan 5 missed call bata ɗauka ba, ganin dai da gaske fatima ba ɗaga wayar zata yi ba ne yasa shazim cewa "noraiz ku shiga ciki ku duba ta ko tana ɗakin ammy, ko ina dai ku duba ta " da to suka amsa noraiz ya fito su ka nufi part ɗin su, ba inda basu duba har bedroom ɗin shazim dana noraiz ɗin amma ba fatima ba dalilin ta,ne man fatima har part ɗin innah da na su Aunty zainab,su da zasu bi jirgin ƙarfe biyar na yamma sune har aka yi sallar magrib ba su tafi ba suna ne man fatima,abun da ya ɗaga masu hankali ganin wayar ta da suke ta faman kira a main parlorn part  ɗin uncle Ibrahim kan sofa  sa'ada har ta fara kuka, hankalin shazim yayi ƙololuwar tashi, ina fatima taje.
duk wannan bidir da suke na ne manta babu wanda su ka faɗa ma suna ne manta, zaune suka yi a main parlorn part ɗin su shazim kowa yayi ta gumi tunanin kawai suke ina fatima ta shiga, sa'ada kuwa sai kuka take mahmud na lallashin ta,har aka yi sallar isha basu san in da ta shiga ba, tashi sukayi su ka nufi masallaci, sa'ada kuwa part ɗin su ta nufa wurin momy , ko da ta shiga samun momy tayi zaune bakin gado tayi tagumi, damuwa ce ƙarara a fuskar ta,  da gudu fatima ta faɗa saman jikin ta tana kuka, ɗago da ita momy tayi tana faɗin "lafiya ke kuma daga ina haka, mi kike ma kuka kuma " cikin shashekar kuka tace "momy ba'aga fatima ba " da sauri momy ta ɗago da fuskar ta tana faɗin "ban gane ba, ina ta je "
"momy tun ɗazu muke nemanta ni da su ya shazim ba mu gan ta ba, muna ta kiran wayar ta ashe tana a nan parlor ta barta "  dafe kai momy tayi tana faɗin "ya salam, ina taje , kun du ba har part ɗin su innah da na su Auntyn ku?"
"eh momy babu inda bamu duba ba amma bata nan"
"har ɗakin feenah kin duba "
"a'a momy ban duba ba "
"to ta shi muje mu duba " ta shi su kayi zuwa ɗakin feenah babu in da basu duba har cikin toilet sai da su ka duba babu almun ta,ɗaya bayan ɗaya duk wani ɗaki da ke part ɗin sai da suka duba amma bata ba alamar ta, date kai momy tayi kamar mai tunanin girgiza kai ta shiga yi tana faɗin " ba gaskiya bane , hakan ma bazata taɓa faruwa ba, idan ko haka ne na shiga uku ni turai "
"momy miya faru, miye kuma ba gaskiya ba?" sa'ada ta jefa mata tambayar haɗi da tsare ta da idanu
"bakomi sa'ada,kije part ɗin su Kairiyya ku sake duba ta " momy ta faɗa tana nufar  part ɗin dady,fita tayi zuwa part ɗin su shazim yan da ta bar su ɗazu zazzaune kan sofa yanzu ma haka ta same su amma ban da shazim
"ya noraiz an ganta " girgiza mata kai kawai yayi, fashewa tayi da kuka sai kace ƙaramar yarinya, mahmud ne yace" dan Allah sa'ada kiyi mana shiru, ba ɓacewa tayi ba za'a ganta"
ficewa tayi daga part ɗin.

Su Asma'u ne zaune a main parlorn part ɗin uncle Ahmad, fira su ke duk a kan meeting ɗin ɗazu da abun da shazim yayi, kowace na tofa albarkacin bakin sa, kairiyya ce ta saukko daga sama part ɗin mansoor  hannun ta ɗauke da tray da alama dinner ta kai masa ta shigowa parlor sa'ada na banko ƙofa kamar zata ɓallata ta shigo fuskarta jage jage da hawaye,da sauri su ka juyo suna binta da idanu gaban su sai faɗuwa yake jira kawai suke su ji tace ga wanda ya rasu dan duk a tunanin su mutuwa akayi , sai kuka take ta kasa cewa komi,magana su ka shiga yi mata "ke wai mi akayi ne kike kuka, wani ne ya rasu " sai jefa mata tambayoyi suke amma ta ƙice masu ga abun da take ma kuka, karshe ma part ɗin mansoor ta nufa da gudu, ta shi su kayi suna binta da idanu har ta haye sama, kallon kallo su ka shiga yi ma juna, fitowar shi kenan daga bedroom ɗin shi  yaji an banko ƙofar parlor  ɗin shi kamar za'a ballata har sai da ya ɗan tsorata da ganin sa'ada idanunta sunyi luhu luhu "ke lafiya daga ina haka " bata bashi amsar tambayar da yayi mata ba sai ma ƙara sautin kukan da tayi,  har sai da mansoor ya kwatsa mata tsawa yana faɗin "ke lafiya kike wannan kukan mi a kayi maki " cikin shashekar kuka tace "fatima ce..... " bata ƙarasa ba mansoor ya katse da "fatima ce tayi mi, kiyi magana mi ya samu fatimar " fashewa tayi da kuka tana faɗin
"tun ɗazu muke nemanta ba mu ganta ba" tsaki mansoor ya ja yana faɗin "ina fatimar zata je, ki je dai ki sake du bata "
"wallahi yaya ba inda ba mu  duba ta ba amma ba mu  ganta ba ni da su ya shazim  " ya salam mansoor ya furta yana faɗin "an kira wayar ta kuwa "
"tun ɗazu ya shazim ke  kira amma tana ringing ba'a ɗauka "  ok bari na zo mansoor ya faɗa haɗi da nufar bedroom ɗin shi  da sauri ya tura ƙofar ya shiga, wayar shi da ke kan sofa ya nufa ɗauka yayi ya shiga dialing number fatima tana ringing amma ba'a ɗauka ba kamar yan da sa'ada ta faɗa mashi kusan 5 missed call, ɗan dafe kanshi yayi yana furta "ya Allah " fita yayi daga bedroom ɗin in da ya bar  sa'ada a nan ya same ta ƙofar fita parlorn ya nufa bin bayan shi sa'ada tayi, su Asma'u har yanzu suna nan tsaye hankalin su duk a tashe, ganin ya mansoor da sa'ada da sauri kairiyya ta nu fi mansoor tana faɗin "yaya wai mike faruwa ne " ficewa yayi batare da ya bata amsa tambayar da tayi mashi ba ganin haka ne yasa ta jawo hannun  sa'ada tana faɗin " sa'ada wai mike faruwa ne "
"ya kairiyya fatima ce ake nema ba'a ganta ba " dafe ƙirji kairiyya tayi tana faɗin "ba'a ganta ba "
"Eh, tun ɗazu muke nemanta ni da su ya mahmud amma bamu ganta ba, ko ɗazu da na shigo nan ita muke ne ma"
Asma'u da Amina har haɗa baki su ke wurin jan tsaki da faɗin "aikin banza kawai saboda kawai ba'a ganta ba zaki wani shigo ma mutane kamar wacce wani nata ya rasu " mutsww su ka sake jan tsaki, kairiyya ce tace " amma nayi mamakin abun da ya fito daga bakin ku wallahi, haba Aunty Asma'u cewa tayi fa tun ɗazu ake nemanta ba'a ganta ba "
Amina ce tace "ke kairiyya ki kam kan ki, ko cewa tayi ta mutu ina ruwan mu "
kairiyya tace "wallahi ku dai canza dan wannan ba rayuwa ba ce "
hayayyaƙo mata su kayi da masifa Fiddausi tace "gaskiya fa ta faɗa ko da ace ba ƴar uwar ku ba ai ita muslma ce bare jinin ku ɗaya da ita, gaskiya ku gyara "
kallon juna su kayi suna faɗin "yau ga ƴan isakan yara wa'azi za ku yi mana " kairiyya tace " ba wa'azi za muyi maku ba gaskiya ce muke faɗa maku "
"to ba mu so " a cewar Amina, jan hannun sa'ada kairiyya tayi su ka bar part ɗin zuwa part ɗin innah wurin gwaggo Halima, ita ka ɗai suka samu a  part ɗin gwaggo Uwani da innah ba su nan, suna asibiti wurin feenah data yanke jiki ta suma lokacin da uncle Ibrahim ya fitar da ita daga parlorn da suka yi meeting ɗazu,   abun dake faruwa su ka faɗa mata,sosai hankalin ta ya tashi, wayar ta ta ɗauka ta shiga dialing number uncle Ahmad da yake shima bai nan yana tare da su innah , korma uncle Ahmad bayani tayi akan abun da yake faruwa, sosai ya nuna tashin hankalin shi, tamabayar gwaggo Halima yayi "ina su shazim ɗin su ke "
"ina jin suna part ɗin su, nima su kairiyya ne suke faɗa man abun da ke faruwa "
"ok gani nan zuwa " ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran.
"ga Abban ku nan zuwa,  amma da mamaki abun ina zata nufa, ku tashi muje, ke sa'ada je kikira man usman kice ya same ni a nan part ɗin  " da to ta amsa haɗi da tashi ta fita.

Lokacin da mansoor ya fita part ɗin su shazim ya nufa, noraiz ya samu a parlor mahmud ya fita, tambayar shi yayi "ina shazim ɗin" amsa noraiz ya bashi da "ya shiga ciki yanzu " ok kawai mansoor yace haɗi da nufar sama part ɗin shazim,ba nocking ba komai ya tura ƙofar da ƙarfi ya shiga
ɗago da idu shazim yayi jin yanda mansoor ya shigo kamar an jeho shi da idanu  shazim ke binshi, magana ya fara "yanzu dan wulaƙanci shazim ace kun nemi fatima baku ganta ba amma ka kasa faɗa man sai da sa'ada ta faɗa man, wai wannan haushin nawa da kake ji na minene"
"dan Allah ka barni naji da abun da yake damu na"
"ok abun da ke damun ka ko "
"haba dan Allah kaine da wata magana, yanzu fa nake shirin kiran ka sai gaka ka shigo "
"uhmm" kawai mansoor yace sannan yace "to ina ta tafi "
"nima ban sani ba, bawani wuri ta sani ba bare nayi tunanin ko tana can" dan jinjina kai mansoor yayi yana faɗin " haka ne gaskiya" can kuma ya matso kusa da shi  ya zauna yana faɗin "ɗan kira number a hashim kaji ko fatima taje gidan su" wani kallo shazim yayi mashi "  ban gane ba, mi zai kai fatima gidan a wannan lokacin "
"dan Allah dai ka kira shi "
"ni bazan kira shi ba, kai mi zai hana ka kira shi " mansoor yace 
" kai matsalata da kai kenan,  to bani wayar ka na kira shi tun da baza ka kira shi" ɗaukar wayar yayi  ya shiga kiran number A Hashim, bugu biyu yayi picking ko sallamar da yake mashi bai amsa ba yace "Fatima na tare da kai?"
"Fatima kuma?" a hasale shazim yace "taya ina tambayar ka kana tambayata"
"ba dole na tambaye ka ba, ni yau she rabon da naga Fatima,in ba ma rainin wayau ba a wannan lokacin zaka tambaye ni fatima  " har ya ɓuɗe baki zai yi magana mansoor ya fisge wayar dan ya san abun na iya koma masu faɗa, kara wayar yayi a kunne yana faɗin "sorry Abdallah,  ka gane neman ta muke ne, an kira wayar ta bata yi picking ba  tun ɗazu mu ke neman ta , shine sai nayi tunanin ko tazo gidan uncle ne wurin Ameera"
hankalin A Hashim yayi matuƙar tashi  jin ya ce ba'aga Fatima ba, cikin tsantsan  tashin hankali yace "amma ina taje mansoor "
"wallahi shine ba mu sani ba"  Abdallah yace "ya ilahi" haka kawai ya ce haɗi da yin rejecting ɗin kiran, ta shi mansoor yayi ya fita daga parlorn ya nufi main parlor, yan da ya bar Noraiz haka ya same shi har da mahmud da ya shigo yanz, gwaggo Halima ce ta shigo ita da kairiyya da sa'ada sai usman ,  har time ɗin kuka sa'ada keyi, kairiyya na lallashin ta, kusa da su mansoor ya matsa, haƙuri ya shiga ba ta akan insha Allah za'a ganta, fitowa shazim yayi bedroom ɗin shima ya nufo main parlor wuri ya samu kusa da noraiz ya zauna, ya usman ne yace " shazim  tun yaushe ne kuka duba baku ganta ba "
"tun fitar da tayi ɗazu da ana meeting, nayi tunanin ko tana nan ɗakin ta ko wurin sa'ada "
"ya salam" ya usman ya furta haɗi da cewa "amma ba inda kake tunanin zata "
"ina zata je yaya bayan ba wanda ta sani abuja " kallon sa'ada ya usman yayi "ke sa'ada kin kira ƙawayen ki ko taje wurin wata daga cikin su "
"yaya ai ni bana da ƙawaye,kuma ma tun da tazo gidan su momy kaɗai muka je sai gidan uncle ɗin ya Abdallah "
"waye kuma Abdallah "ya usman ya tambaya, mansoor ne yace "wani course mate ɗin shazim ne kuma ma mun kira shi bata can "  shiru sukayi ba wanda yasake cewa komai, kowa na tunanin inda ta shiga, shazim kuwa alƙawari ya ɗauka  duk abun ya same ta wallahi bazai ƙyale kowa dake cikin estate ɗin ba tunda ai sune silar   shigarta wannan halin har tasa ƙafa ta bar estate ɗin, damuwarshi yanzu shine ina taje awane hali take dan yasan duk in da take zai yi wuya ace ciwanta bai tashi ba, ya usman ya tashi yana faɗin "ina zuwa wannan zaman bazai mana maganin komi ba " tashi ita ma gwaggo Halima tayi "haka ne usman bazama ya kamat muyi ba " tashi su kayi duk suka fita aka bar mansoor da shazim
mansoor yace "ina mamakin inda taje, to wai mi zai sa ta bar estate ɗin nan" shazim yace " wallahi muddin wani abu ya sameta ran kowa sai ya ɓaci " shiru kawai mansoor yayi baice komi ba, can kuma sai yace "yo wai ma an tambayi security ko sunga fitar ta " sai da mansoor yayi maganar sannan hankalin shazim ya kai ga nan "hakane kuma mansoor wallahi ni duk banyi wannan tunanin ba "
"idan tafita dole zasu ganta ko da ta ƙaramin gate ta fita, tashi mu tafi  " mansoor ya faɗa haɗi da ɗaukar wayar shi su ka fita zuwa main gate da ya usman suka ci karo shima main gate  ɗin ya nufa, a tare suka ƙara sa, securityn na zaune kan benchi da suke zama,su ƙara so inda su ke, gaishe da su security su kayi a taƙaicw suka amsa masu mansoor na faɗin " tambayar ku muke son yi"
babban cikin su ne yace "Allah yasa mun sani yallabai "
a hassale shazim yace " kunga ficewar fatima "
"gaskiya yallabai ba muga fitar ta ba, motar Alhaji ce kawai ta fita shi da su innah in ba dai atare da su ta fita ba "
Mansoor yace "kun tabbata baku ga ficewar ta ba, kuma bawani driver da ya fita da mota "
"gaskiya babu, bayan Alhaji Ahmad ba wanda ya fita da mota " wuce wa shazim yayi batare da ya jira su mansoor ɗin ba, juyo suka yi suma zasu bi bayan shi sai ga mota ta nufo main gate daga waje, tsayawa su kayi dan suga waye, ɗaya daga cikin security ne ya nufi motar ba kowa bane face ya Abdallah ya kasa zama hankalin shi ya ƙi kwanciya tun da aka ce ba'aga fatima ba, izinin shiga ciki security ya bashi, ciki ya shigo ganin su mansoor ne yasa shi tsayawa wurin su sai da yayi parking sannan mansoor ya gane shi, mansoor ce mashi yayi" ya shiga ciki kawai shazim ma yanzu ya wuce" ciki ya shiga yayi parking a parking lot, part ɗin kawai ya nufa , tsaye ya samu shazim a parlor, gaba ɗaya hankalin Abdallah a tshe yake tsare shazim yayi da tambayar ina taje ne Fatimar, amsa kawai shazim ya bashi da bai saniba, gashi malam da Ammy sai kiran shi su ke yace zasu dawo yau gashi har dare yayi babu su babu labarin su. 

Sa'ada lokacin da suka fita daga part su shazim part ɗin su ta nufa, ta shiga bedroom ɗin momy ta shiga bata same ta ba tunawa da tayi ɗazu momy part dady ta nufa ne yasa fita ta nufi part ɗin dady, tunkafin tashiga ta fara jin muryar momy tana faɗin "amma ban taɓa tunanin baka da hankali ba luqman sai yau, dama ashe shashasha ne kai ban sani" muryar dady taji yana faɗin "dan Allah ki daina ɗaga murya turai "
"ok in daina ɗaga murya ko.... " bata ƙarasa ba saboda tura ƙofar da sa'ada tayi ta shiga tsaye ta samu momy da dady sai luqman da ke zaune kan sofa jikin shi sai rawa yake  kamar wanda zazzaɓi yayi ma mugun kamu,jin anturo kofa ne yasa shi tashi da gudu ya nifi bedroom dady,ganin sa'ada ce yasa shi tsayawa yana haki kamar wanda yayi wasan tsere, dady ne yace "ke kuma daga ina haka "
"dady fatima fa ake nema ba'a ganta ba "
"to naji fita ki bamu wuri"
" dady amm..... " bata ƙarasa ba ta dalilin tsawar da dady ya daka mata yana faɗin
"nace fita ko so kike sai ranki ya ɓacin"
ba shiri ta fita, amma sai ta ƙi tafiya ta tsaya tana sauraron mi suke cewa, bana ji mi take ji naga dai taja baya da sauri tana kallon ƙofar can kuma ta fita dagu.........
_Episode 40_41_

............ba shiri ta fita, amma sai ta ƙi tafiya ta tsaya tana sauraron mi suke cewa, bana ji mi take ji naga dai taja baya da sauri tana kallon ƙofar can kuma ta fita dagu tana kuka, bedroom ɗinta ta nufa tana shiga ta faɗa kan bed fashewa tayi da wani matsanancin kuka, kuka take kamar ranta zai fita sai birgima take kan bed ɗin tana faɗin "wayyo Allah nah, Allah kasa abun da kunnuwana suka jiman ba gaskiya bane, idan har haka ta kasance bazan taɓa yafe maka ya luqman " sai kuka take tana ta roƙwan Allah yasa ba gaskiya bane tashiga tashin hankali da jin abun da su dady ke tattaunawa sai ta baka tausayi yan da ta dage tana rokwan Allah yasa ba gaskiya bane,can kamar an tsikareta ta tashi ta fita daga bedroom ɗin da gudu ta nufi sama part ɗin dady har tasa hannu zata buɗe ƙofar part sai aka turo ƙofar dady ne sai momy dake bayan shi da kaganta kasan tana cikin damuwa idanun ta duk sun kumbura ba ƙaramin kuka tasha ba,tsaye su kayi suna kallonta sai kuka take dady ne yace "wai wannan kukan da kike na minene, miya dawo da ke nan ba nace ki wuce ba " ƙara sautin kukan tayi ba'a ma jin mi takecewa sosai " dady ƴar uwata "
"dan Allah kiyi haƙuri sa'ada za'a ganta yanzu ma wurin su shazim ɗin zan tafi, kiyi shiru kinji" ya faɗa cikin sigar lallashi
"to dady, amma maganar wa naji kunayi, wacce ya luqman....... "
bata ƙarasa ba dady ya katseta ta hanyar daka mata tsawa" wai ke wace irin yarinya ce sa'ada, nace maki za'a ganta kuma maganar da kike cewa munayi ba'a kanta bane, ki kwantar da hankalin ki " ya ƙarasa maganar yana lallashin ta
" amma dady dan Allah ka bari naga ko wacece pls "
"miyasa baki jin magana ne sa'ada, wuce ki tafi bedroom ɗin ki ki kwanta kar ki haddasa ma kanki ciwan kai kinji za'aga fatima "
fashe tayi da kuka "ni dai dady ka bari naga ko wacece "  tsawa ya daka mata "ina wasa da ke ne, ko ki bar wurinnan ko ranki ya ɓaci shashasha"
hawayen da momy ki ɓoye wa ne suka zubu "wallahi Alhaji in jiye maku abun da zai biyo baya  da luqm"
dady yace "dan Allah turai kiyi man shiru, kija ta ku bar nan wurin "
"dole na faɗi haka Alhaji,  an cuc..... " bata  ƙarasa ba dady ya dakatar da ita ta hanyar cewa
"wai miyasa kike da taurin kai ne turai, nace ki jata ku bar nan "
jan hannun sa'ada tayi tana faɗin "zo nan kinji kiyi haƙuri ki daina kuka, kinji jikin ki harya ɗauki zafi " momy ta faɗa haɗi da jan hannunta, fisgewa sa'ada tayi ta nufi ƙofar zata buɗe, da sauri dady ya fisgota ɗauke ta yayi da wani mumunnan mari har sau biyu, tangal tangal tafara zata faɗi ƙasa, fa sauri momy ta taro ta zuwa jikinta ta rugume ta tana kuka " kijata ku bar nan"
"ba inda zan kai tai, ku faɗa ma yara in da ƴar uwar su take, ko wallahi naje na kira su duk abun da zai biyo baya ya daɗe bai biyo baya ba "
"turai haka kika ce, kin kuwa san mi kike faɗa kuwa, kina cikin hankalin ki kuwa"
"cikin hankali na nake, nasan mi nake, wannan ai zalunci ne " tana gama faɗa ta ɗago da kan sa'ada tana faɗin "sa'ada tashi ki kira man mansoor ko shazim " shiru sa'ada bata amsa ba bakuma ta motsa ba, ashe tun marin da dady yayi mata momy ta tare ta suma tayi batare da sun sani ba, da sauri momy ta ɗago ta kalli dady tana faɗin " ta suma Alhaji, Innalillahi" ta faɗa tana bubuga ta tana faɗin "tashi kinji, dan Allah ki tashi " momy gaba ɗaya hankalin ta ya tashi, key dady yasa ma part ɗin shi ya rufe ya yafita ya bar momy da sa'ada durƙushe a ƙasa momy sai kuka take,daƙyar ta samu ta ɗauki sa'ada ta nufi ɗakinta da ita, kwantar da ita tayi kan bed sannan ta nufi dressing mirror ɗakin ta ɗauki jirkar ruwan da take ajiye wa duk dare, a hannu ta tarfa ruwan ta nufi fuskar sa'ada ta yayyafa mata sai da ta sake yayyafa mata sannnan ta ja wani dogon numfashi,Alhmdllh momy ta furta hadi da kiran sunan sa'ada, jin muryar momy ne yasa ta tashi   zambur kamar wacce aka zungura " momy ina fatima, ina ƴar uwata take, momy dan Allah ki faɗa man in da take " ta ƙarashe maganar tana kuka
"kiyi haƙuri sa'ada ƴar uwar ki bata ɓata ba kiyi shiru kijin, kar ki ja ma kanki ciwo "
"amma wacece a part ɗin dady naji kuna faɗin ya luqman yayi raping" da ta faɗi haka har sai da gaban momy ya faɗi " momy kinyi shiru,idan har ba ƴar uwata bace pls momy wacece " hawaye ne suka taru a fuskar momy, girgiza mata kai tayi " sa'ada nima ban san wacece ba, dadyn ku yaƙi bari naga ko wacece "
"momy amma a ɗakin na same ki pls momy ki faɗa man " shiru momy tayi batace mata ƙala ba, tana son kowa ya san halin da ake ciki amma ta tsoron wane irin hukunci luqman zai fuskanta take, ganin tayi shirune yasa sa'ada faɗin "momy ki faɗa man, ko naje na kira ya

Please Login or Register in order to submit comment