Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙira mata ido ji yake kamar ya mayar da ciwan a jikin shi tsabar yan da yake jinta a cikin jikin shi
"zaki sha ruwa ne " shazim ya faɗa ganin tana miƙa hannu alamar wani abun zata ɗauka, girgiza mashi kai tayi
" Eh ya shazim "  hannun yasa ya ɗauko ruwan da ke kan table ɗin da magungunan ta ke kai cire marfin jirkar yayi da kanshi ya bata a baki, bata wani sha sosai ba ta kauda kai, ajiye jikar shazim yayi yana cemata " ki koma ki kwanta " da to ta amsa haɗi da komawa ta kwanta drip ɗin da ke jikin ta ya cire mata
  "zaki sha tea ko " ya tambaye ta, ɗaga mashi kai tayi alamar eh
"Ok bari na kawo maki sai kisha maganin ki daga nan " ya faɗa haɗi da tashi ya bar gaban gadon kallon Abdallah dake tsaye ya zuba ma fatima ido kamar ya cinye ta yayi " lafiya dai ko?" ya tambayi Abdallah haɗi da tsare shi da idanu, kawat kawata hankalin Abdallah na kan fatima bai ma san shazim na mashi magana ba, har sai da shazim ya ɗan taɓa shi tukun ya dawo cikin hankalin shi, zuba mashi ido yayi yana kallon shi
"malam lafiya ka wani tsare ni da idanu " Abdallah ya faɗa yana wani shana mur
"kai zan tamabaya ai wannan " shazim ya faɗa yana zuba mashi harara, jin muryar  Abdallah ne yasa fatima jutuwa da sauri ta kalli inda suke tsaye shi da shazim
"Ya dr " fatima ta kira sunan shi cikin kasalelliyar murya ta marasa lafiya, matsawa yayi kusa da ita yana faɗin " "na'am fatima, ya jikin ki" hawaye ne su ka taru a  idanuwan ta tace " ya dr, yaushe kazo "
"tare muka zo da ke, ya jikin " ya faɗa haɗi da neman wuri bakin gadon ya zauna, fita shazim yayi zuwa part ɗin shi .

hannun ta Abdallah ya kamo  yana faɗin  "fatima ina tambayar jikin ki kinyi shiru "
"ya dr da sauƙi "
"Allah ya ƙara sauƙi "
"Ameen" shazim ne ya shigo hannun shi ɗauke da cup ɗin tea sai turiri yake,kusa da gadon ya matso, amsar cup ɗin Abdallah yayi yana faɗin
"tashi ki zauna kisha tea ɗin " yunƙurin tashi tayi, aje cup  ɗin yayi  kan table domin ya tai maka mata ta tashi  tun kafin ya ajiye shazim ya kamata ya tayar da ita zaune,
" thanks" Abdallah yace, harara shazim ya zuba mashi murmushi kawai Abdallah yayi   da kanshi ya shiga bata tea shazim kuma na duba mata magungunan da ya kamata ta sha, da ta kammala sha amsar magungunan Abdallah yayi ya miƙa mata da kanshi tasha, matsowa shazim yayi da allura a hannun shi yana faɗin " to malam matsa " juyowa Abdallah yayi yana kallon shazim dake tsaye hannun shi riƙe da allura,
"ka matsa nace bawai ka kallan ba "
matsawa Abdallah yayi yana faɗin
"ka dai yi a hankali dan nasan halinka, ban da mugunta"
"ka san Allah zanyi maka ita idan baka yiman shiru ba ɗan rainin wayau kawai " shazim ya faɗa yana nuna ma Abdallah allurar da ke hannun sa
" zaka iya  " Abdallah ya faɗa haɗi da nufar kan sofa ya zauna, fatima dai sai binsu take da idanu abun ba ƙaramin burgeta yake ba,  matsowa shazim yayi kusa da ita yana faɗin "miƙo man hannun ki " hannun rigar da ke jikin ta taja haɗi da miƙa mashi hannun, a damtsen hannun ta yayi mata alurar yana tsirawa  ta rintse  ido da sauri Abdallah yace "wai Allah, dan Allah kayi mata a sannu "
" ka takura man fah, ai da zuwa kayi ka amsa kayi mata da kanka  " shazim ya faɗa
" bana iya yi mata allura ai " tsaki shazim yaja " aikin banza da na wofi "
" kai kaga aikin banza " fatima sai murmushi take dan ba kaɗan su ke sata nisha ɗi ba, lura da hakan ne ma yasa shazim biye ma Abdallah har sai da wani baccin ya sake ɗaukar ta tukun su ka bar ɗakin dan lokacin sallar asuba yayi, alwala su kayi a part ɗin shazim su ka nufi masallaci tare da noraiz su ka tafi, lokacin da su ka dawo Ammy da sa'ada  su ka samu a medical room ɗin tare da fatima da ta sake farkawa, gaishe da Ammy su kayi haɗi da zama kan sofar da ke ɗakin har sai da gari yayi haske tukun su ka tashi su ka bar Ammy da sa'ada Innah Asabe ma ta shigo ta duba jikin fatima,da ta tashi tafiya kitchen bin ta sa'ada tayi ta shirya ma fatima lafiyayyen breakfast, duk da bakin nata ba daɗi haka Ammy da sa'adar su ka tasa  ta gaba sai taci, ganin sun damu taci ne yasa ta  daure badan tana jin da ɗin shi ba taci   sosai sa'ada  taji daɗin ganin taci, fatimar ma daɗi taji ganin yanda kowa ke nan nan da ita ta kuma ji daɗin ganin  ƴan uwan ta a tare da ita, ko da Ammy ta kira malam ta sanar da shi farkawar  fatima hamdala yayi ma ubangiji kuma da safen ya sa driven shi ya kawo  su shi da ummy, da shazim bari yayi sai anjima yaje ya ɗauko su da kanshi sannan ya sanar da su farkawar fatimar, amma sai  Ammy ta riga shi kiran  malam  sai dai kawai ya gansu sun zo, majeed ma ya zo shi da mamar shi sun daɗe gidan sosai  sannan su  ka tafi,shazim da har ya shirya zai je Abnoor sai ga kabir ya zo duba jikin fatima,  tun jiya ya kira wayar shazim bai ɗauka ba shine ya kira noraiz, shine noraiz ɗin ya sanar da shi ai sun dawo da rashin lafiyar fatima, shine daya fito daga gida zai je eko ya fara zuwa nan dan ya duba jikin ta,da kabir ɗin zai wuce ne ya shirya su ka tafi tare ba yanda bai yi da Abdallah ba akan ya bishi su tafi amma yace zai tsaya idan lokacin shan maganin fatima yayi zai bata har  ce mashi shazim yayi ai Ammy na nan amma ƙiri ƙiri ya ƙi binsu, tafiya shazim yayi ya bar sa shima  bai wani jima ba ya wuce Abnoor can ma ana yi sallar asr ya dawo, Abdallah da ya zauna gida kulawa sosai ya ba fatima da tace kaza jiki na rawa zai yi mata shi tun yana ba Ammy mamaki har ya dai bata mamaki, dan sosai ya cire duk wata kunya daya ke ji ta Ammy,su malam kuwa ba ƙaramin daɗi yaji ba ganin yanda Abdallahn yake kula da fatima a gaban su, har kiran Abie da mom yayi ya ba Ammy da malam har da ummy su ka gaisa su ka kuma yi ma su ya mai jiki,  sai da daddare su malam suka tafi akan gobe ma zasu dawo su sake duba jikin ta.
haka fatima ta cigaba da samun kulawa daga wurin kowa a cikin su har ta ɗan samu sauƙi ta ma koma ɗakin ta da  zama yanzu ba'a mata allura magunguna kawai take sha, kwanan Abdallah huɗu ta wuce katsina dan tun tuni uncle ahmad ya tafi, ya tafi ne akan zai dawo ya sake duba jikinta shi da su Abie, kamar tayi kuka da zai tafi taso ace ya ɗan yi kwana ki da yawa cematan da yayi zai dawo ne yasa ta haƙura.
Shazim kullum kafin ya tafi aiki sai ya tabbatar da taci abinci kuma tasha maganinta, noraiz ma ya fara aiki
kulawa kowa yake bata hakan yasa ta ƙara jin daɗi kuma jikin ta Alhmdllh masha Allah dan ba inda bata zuwa, kuma taji daɗin da sa'ada ta biyo ta.

Satin su ɗaya da dawowa lagos su uncle Ahmad su ka zo da uncle Ibrahim, kairiyya, feenah, gwaggo Halima , luqman har da momy da mama, mansoor bai samu zuwa ba saboda aiki amma yace insha Allah yana nan zai zo idan ya kammala, ba yanda ba su yi da innah da gwaggo Uwani su zo ba amma tace wallahi ita ba zata zo ba ta so ma ta hana su uncle Ahmad ɗin ma zuwa amma su kace su sai sunzo sun gaishe da fatima.

Fatima gaba ɗaya hankalinta tashi yayi da ta ga luqman dan ta tsorata da shi,bawan Allah duk ya sha jinin jikin shi ganin yanda take ɗari ɗari da shi, ga wani kallon tsana da shazim ke binshi ga Ammy kwata kwata ta ƙi bashi fuska ko da ya gaishe da ita kadarn kadaham ta amsa mashi  ƙarshe ma tashi yayi ya bar parlorn ya nufi parking lot ya zauna a mota , haɗa kan shi yayi da siti yarin mota duk ji yayi ya tsani kan shi yayi kuma daya sanin abun da yayi mata, ganin duk ya damu ne ya kuma ware kanshi ne yasa Ammy ta ɗan saukko tanuna ba komai komai yawuce har ta sa noraiz ya kira mata shi, ko da yazo haƙuri ya bata akan abun da yayi fatima, ta kuma ce ta yafe mashi amma a zuciyar ta ɗauki alƙawarin ba zata bari ya auri fatima ba
Fatimar ma ba yanda ba'ayi da ita ba akan ko magana tayi ma luqman ɗin ko da bazata yafe mashi ba amma taƙi.

Fennah sai ƙoƙari take taga shazim ya kula ta amma ya ɗure fuska ko kallon banza bata ishe shi ba,da su uncle su ka tashi tafiya ƙin binsu feenah tayi dole ita a nan zata zauna, ganin ta dage ne yasa Ammy cewa a barta idan mansoor yazo sai su koma tare harda kairiyya ma, sa'ada daman ba mai maganar ta dan cewa tayi tun da fatima baza tai karatu abuja ba to ita zata yi lagos , ko da tace haka dady bai yi musu ba ya amince mata.
da zasu wuce sai da suka je gidan malam,su ka kuma roƙi afuwar shi akan abun da luqman ɗin yayi, ya kuma haƙura yayi masu Allah ya kiyaye hanya.

Shazim fa har su ka tafi ban da gaisuwa babu abun da ya haɗa shi da su har su ka bar garin.

Abdallah kamar yan da yace kwanan shi biyar da tafiya, ya dawo shi da uncle Ahmad mom da ummh, abie bai samu zuwa ba saboda wani uziri daya tsare shi, hakan yasa su ka zo su ka ɗai ban da shi, Ammy taji ɗadi sosai ta kuma yi masu godiya, fatima kamar tayi dan bata taɓ gaini mom ba a zahiri sai dai photo da waya sai ga shi yau taga mom ido da ido.
wani abu da na lura da shi kallon da mom ke ma ammy da wanda ammyn ke ma mom kamar sun taɓa ganin juna ko, duk da sun kasa tuna inda su ka taɓ ganin juna.
A ranar su mom su ka koma katsina Abdallah kuma sai da yayi kwan biyu tukun ya koma.


_* to masu karatu kar ku manta an tafi an bar Feenah da kairiyya akan idan mansoor ya zo za su tafi tare da shi , yanzu wasan zai fara amma kafin nan ina so na sanar da ku waye shazim*_


_*WANENE  DR ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN ( SHAZIM) *_

Dr shazim ya ka sance ɗane daga zuriar alhaji nuraddeen ahmad sharani.
Alhaji nuraddeen sharani, mutum ne mai rufin asiri, ya ka sance ɗan kasuwa ne mai sayar da kayan masarufi, alhaji nuraddeen yana zaune ne a garin kurfi dake jahar katsina, anan cikin garin yake gudanar da harkar kasuwancin shi da ƙauyakun da ke kusa da garin kurfi.

Alhaji nuraddeen yana da mata ɗaya tilo mai suna habiba ana kiran ta da ruma,  ita ma yar cikin garin kurfi ce, barumiya ce kyakyawar gaske, shekarar su goma cif da aure Allah bai basu haihuwa ba, ruma kullum cikin tashin hankali take saboda tsangwamar da iyah ( mahaifiyar nuraddeen )  ke mata ita da ƴaƴen ta, har ta kai ko hidima suke ruma bata zuwa saboda kyara da tsangwama da suke mata, ganin yanda hankalin ruma yake atashe yasa nuraddeen ya shiga kwantar mata da hankali yana nunamata cewa Allah yana sane dasu kuma zai basu haihuwa karta damu da duk abunda ƴan uwan shi ke cewa, sosai yayi mata nasiha akan su cigaba da adu'a kawai, kwantar da hankalin ta tayi ganin mijinta bai damu da rashin haihuwar ta ba, mahaifiyar nuraddeen ta takura ma shi akan dole fah sai ya ƙara aure tunda matar shi bata haihuwa, nuna mata yayi baya buƙatar ƙara aure, indai haihuwa ce Allah zai ba ruma, sosai ran iyah  ya ɓaci jin abunda ya ce ta kuma ɗauki fushi da shi akan ƙinbin umarnin ta da yayi, har gida taje ta samu ruma tayi mata cin mutunci, duk a tunanin ta ita ta hana nuraddeen ƙara aure saboda ta shanye shi, sosai tsanar da yan uwan nuraddeen kema ruma ta ƙaru saboda ƙin ƙara aure da yayi, ruma ba ƙaramar wahala take sha ba awurin iyah , dan kusan kullum sai ta zo har gida ta ci mata mutunci, hakan yasa tayi ta roƙwan mijin nata akan ya bi umarnin mahaifiyar shi  da nuna mashi mahimmanci bin umarnin nata, da farko ƙin amincewa yayi sai da ruma ta rinƙa tasa shi gaba tana yi mashi kuka akan ya ƙara auren, haka nan  ba dan ya so ba ya amince da ƙarin auren, iyah da kanta ta nema mashi auren ɗiyar aminiyarta, ba a ɗau wani lokaci ba aka ɗaura auren nuraddeen da amayar shi hauwa'u ana kiran ta da maijidda, ranar da aka kai hauwa'u gidan shi ya haɗa su ita da ruma yayi masu nasiha akan suyi haƙuri su zauna lafiya, hakan ce ta faru dan sosai ruma da maijidda ke zaman lafiya, ruma ta ɗauki maijidda kamar ƙanwarta uwa ɗaya uba ɗaya........ 


_Episode  48_49_

........... Watan maijidda ɗaya da satittika a gidan nuraddeen Allah ya albarka ce ta da samun ciki , zo kaga murna wurin nuraddeen da ruma, da iyah  taji labarin cikin maijidda har gida ta zo tayi ta sakar ma ruma habaici tana ce mata juya, ita kuwa ruma babu abun da ya dame ta tasan Allah da ya bama maijidda yana sane da ita, sosai take kula da maijidda, cikin na kaiwa wata biyar ta hana maijidda aikin komai a gidan daga sallah sai bacci da cin abinci take yi,da  cikin ya isa haihuwa iyah  ta mai da  maijidda gidan ta, a cewar ta a gaban ta zata haihu, watan cikin  maijidda tara da kwana goma ta haifi ɗa namiji kyakyawa  mai matuƙar  kama da nuraddeen, zo kaga murna wurin angon jego da iya,  ruma ma ba'a barta a baya ba tayi murna da farin ciki sosai, da ranar suna ta zagayo yaro ya ci sunan mahaifin nuraddeen Ahmad  ana kiran shi da magaji, sai da maijidda tayi arba'in ta koma ɗakin mijinta,ruma ta cigaba da kula da ita da yaron ta har yayi ƙwari, shekarar magaji biyu maijidda ta samu wani cikin ta haifi ɗiyarta mace wacce taci sunan iyah watau maryam suna ce mata uwani haka maijidda tayi ta haihuwa amma ruma shiru bayan uwani maijidda tayi halimatu daga kan halimatu ne ta ɗan dakata bata ƙara haihuwa ba, yaranta sun taso cikin soyayyar mahaifin su da abokiyar zaman ta, sosai ruma ke son yaran kusan kullum suna tare da ita dan halimatu ma awurin ruma ta taso, haka rayuwa ta cigaba da tafiya,iyah ta tasa nuraddeen gaba akan dole sai ya saki  ruma dan bataga amfanin ta ba tunda bata haihuwa, hankalin nuraddeen da ruma sosai ya tashi, amma bai saki rumar ba, ganin ba shi da niyyar sakin ruma ya sa ta sa aka kira mata shi har gida, tayi mashi faɗa sosai akan ya ƙi bin abun da ta ce har ikirari tayi mashi akan ko dai ya saki ruma ko kuma ta tsine mashi , ba shida wani zaɓi a lokacin bayan ya ai watar da abun da mahaifiyar shi ta ce, haka ya samu ruma yace taje gida sai ya nemeta, hankalin ruma ya kai ƙuloluwar tashi da jin abun da  nuraddeen ya faɗa, haƙuri ta shiga bashi ita da maijidda, nuna masu yayi bashi da wani zaɓi ne, kuma ai ba sakin ruma yayi ba, cewa kawai yayi ta tafi gida insha Allah zata dawo idan komai ya daidai ta tsakanin shi da iya, dole ruma ba dan ta so ba ta haɗa kayanta ta tafi gidan iyayen ta, sun sha kuka ita da maijidda san da zata tafi, haka ta tafi gida rai babu daɗi, koda ta tafi gida nan ta samu yayarta bilkisu  da ke aure cikin garin katsina ta zo, ran mahaifiyar ruma da na ƴar uwarta ba ƙaramin ɓace yayi ba akan abun da nuraddeen yayi, ko da bilkisu ta tashi tafiya tasa ruma tayi a gaba akan ta haɗa kayan ta su tafi katsina da farko ruma ƙin amincewa tayi akan zata tsaya har sai komai ya dai daita tsakanin ta da nuraddeen, hakan yasa mahaifiyarta ta yi mata faɗa sosai ba dan ta so ba ta bi bilkisu  zuwa katsina, bayan tafiyar ruma katsina nuraddeen ya zo gida wurin mahaifiyar ta ya bata haƙuri akan abun da ya faru ya kuma nuna mata bashi da yanda zai yi ne umarni ne daga mahaifiyar shi, mahaifiyar ruma ta fahimci shi ta kuma yi mashi uziri, sannan ta ce yayi ma mahaifiyar shi biyayya ka wai ya saki ruma,hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba jin tace wai ya saki ruma, ƙin amincewa yayi, sai ma haƙuri da ya ba mahaifiyar ruma. 

Sosai rayuwar ruma ta chanza a gidan ƴar uwar ta, soyayya da kulawa ta ke samu daga wurin ƴar uwar ta da mijin ƴar uwar ta, hakan ya sa ta saki jikinta sosai a gidan ga kuma yaran ƴar uwarta  da take kallo kamar ƴaƴen da ta haifa da cikin ta, ko wane lokaci tana tare da su, suma da sun dawo makaranta zaka same su manne da ita, watan ta ɗaya a gidan ta ƙara fresh tayi kyau  hasken fatar ta ya ƙara fitowa har yar ƙiba tayi,zazzabin dare ne ya taso ta gaba,sai ta wuni lafiya amma da dare yayi sai zazzaɓi ya rufe ta, ko da bilkisu ta fahimci haka sai ta ce mata ta shirya su tafi asibiti amma ruma ta ƙi, wata rana suna zaune kan dinning  zasu ci abinci daga  buɗe warmer ƙamshin abincin ya daki hancinta   tashi tayi  da gudu ta nufi   toilet,  amai tashiga ƙwarawa kamar zata amayar da ƴan hanjin cikin ta  , biyo bayan ta bilkisu tayi tana mata sannu da faɗin "nace muje asibiti amm kin ƙi saboda taurin kai, yanzu ai dole ki shirya mu tafi"
da ƙyar ruma ta buɗe baki tace " ba sai munje ba yanzu da nayi aman na samu sauƙi " ƙin sauraran ta bilkisu tayi sai ma ficewa da tayi ta nufi ɗakin ta tana faɗin " ki shirya kawai mu tafi bana son taurin kai"
tasa ta gaba bilkisu tayi  ta shirya suka je asibiti, koda suka je aka yima ruma aune aune anan likita ya shaida mata cewa  ruma na ɗauke da ciki tsawan wata uku da sati biyu, zo kaga murna wurin ruma da bilkisu, Allah sarki abun da suka da ɗe suna nema har ake mata gori  ake kiranta da juya yau gashi  Allah ya ba ta ,  koda labari ya isa kurfi sunyi murna da jin wannan labari, har gida mahaifiyar ruma ta sa aka kira mata nuraddeen ta sanar da shi, bawan Allah harda kukan shi saboda tsabar farin ciki, yana koma wa gida ya sanar da maijidda, ita ma tayi farin ciki kamar mi, koda iyah ta ji labari ita ma harda kukan ta musamman da  ta tuna cin kashin da suka yi ma ruma ita da ƴaƴan ta har suke kiran ta da juya, har gida ta je ta bama mahaifiyar ruma haƙuri akan ruma ta dawo ta haihu ɗaki mijin ta, da farko ƙin amincewa mahaifiyar ruma tayi sai da iya tai ta bata haƙuri tukun ta haƙura kuma tayi mata alƙawari akan rumar zata dawo, iyah taji daɗi kuma tayi ma mahaifiyar ruma godiya, hakan ce ta faru, bilkisu da kanta  ta shirya  ruma ta dawo da ita gidan mijinta, soyayya da kulawa iyah ta shiga bama ruma tana tattalin ta kusan kullum tana gidan nuraddeen kamar wannane jika na fari da za'a haifar mata, haka shima nuraddeen kamar ba'a taɓa yi mashi haihuwa ba ,  wani ikwan Allah maijidda sai ta fara jin haushin kulawar da iyah da nuraddeen  ke yima ruma, tana ganin kamar  sun fi son ruma akanta , ƙi ƙiri ta fara nuna hassadar ta a fili, iyah kuwa da nuraddeen basu ma san tana yi ba, da cikin ruma  ya kai watannin haihuwa  kamar yanda iyah tayi ma maijidda haka tayi ma ruma ta mai da ta gidan ta da zama, yan da iyah ke son ruma ta ke bata kulawa kamar ta ɗauke mata nauyin cikin haka ta ke ji, saboda cikin ba ƙaramin wahalar da ruma ya ke ba, kullum nuraddeen ya nan manne da ita sai dare yake koma wa gida, sosai ran maijidda ya ƙara ɓaci saboda dawowar da nuraddeen ya ke yi da daddare da kuma wunin daya ke yi wurin ruma, gani take kamar saboda cikin ruma ya banzatar da ita da yaran ta,sosai tsanar ruma ta ƙaru a zuciyar ta  duk ta manta rawar ƙafar da nuraddeen yayi lokacin da tana da cikin magaji, cikin ruma sai da ya kai wata goma da satittika bata haihu ba, hankalin nuraddeen ya tashi sosai ganin har tsawan wannan lokacin bata haihu ba, kwantar mashi da hankali iyah ta shiga yi akan ya kwantar ta hankalin shi ana samun irin haka, amma fir ya ƙi amincewa har sai da ya ɗauki ruma zuwa asibiti, ko da likita ya duba ruma anan ya gano cewa bazata iya haihuwa da kanta ba sai anyi mata cs, lokacin da bilkisu ta zo asibitin duk wani abu da ya kamata a yi na cs ɗin nuraddeen yayi har an  shiga da ita theater room, bakin theater room ɗin suka tsaya shi da bilkisu suna jiran tsammani, har kusan awa huɗu ta shuɗe amma likitocin ba su fito ba lokacin ana ta kiran sallar asr, masallaci nuraddeen ya tafi ya bar bilkisu, har ya je ya dawo ba'a fito da ruma ba likitocin ma ba wanda ya fito, hankalin nuraddeen ya kai ƙololuwar tashi, sai da wasu awannin suka shuɗe sannan wata nurse ta fito daga ɗakin hannun ta riƙe da jariri cikin towel, da sauri nuraddeen da bilkisu suka nufo nurse ɗin suna tambayar ta jikin ruma,miƙa ma bilkisu jaririn tayi tana faɗin "ana gyarata ne,idan an maida ta ɗakin hutu sai ku ganta" da to su ka amsa mata , amsar jaririn bilkisu  tayi tana kallon shi kyakyawan gaske a cikin  kamannin ruma babu abun da ya baro kamar tayi kaki, idonun shi rufe da a lama bacci ya ke, barin wurin su nurse ɗin tayi, hankalin nuraddeen duk a tashe so kawai ya ke yayi ido biyu da ruma,  sake buɗe ƙofar theater room ɗin aka yi dr ne ya fito yana cire safar hannun shi, da sauri nuraddeen ya ƙarasa wurin shi yana tambayar shi wane hali matar shi ke ciki,  "  Allah ya bamu ikwan cetan jaririn amma mahaifiyar shi ta sha wahala sosai,  yanzu dai munyi mata allurar bacci tana ɗakin hutu,ko da  za ku  ganta sai  zuwa anjima"
"to shikenan dr, nagode "ya faɗa haɗi da miƙa ma mashi hannu su kayi musaba ha, dr yace "babu komi, Allah ya bata lafiya"da ameen nuraddeen ya amsa, wuce wa dr yayi zuwa office ɗin shi,nuraddeen  ko ma wa yayi idan da  bilkisu take ya amshi jaririn yana kallon shi, ji yake  kamar ya mai da shi ciki tsabar yanda ya ke son shi, ruma bata farka ba sai wajen ƙarfe 9, nurse ce tazo ta sanar da su farkawar ruma, ta shi su kayi suka bi bayan

Please Login or Register in order to submit comment