Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu indai tayi tafiya ko yaya take sai ƙafafun ta su kama ciwo, sannu Ammy tayi haɗi da cewa "anya ummy baza muje asibiti ba saboda ciwan ƙafafun nan"
"a'a ba sai munje asibiti ba,  yaushe ango na zai dawo?  "
"yanzu nayi waya da shi da gobe zai dawo, amma yanzu sai ranar lahadi saboda meeting da za suyi na family "
"to Allah ya kaimu, su Ahmad ɗin sun sanar da shi kiran da suke mashin ne"
"a'a basu faɗa mashi ba har yanzu, ya dai ce man dawowar shi zai yi ko ba su faɗa mashi ba wai ya gaji da zama fa aiki ya bari, na daice yayi haƙurin su faɗa mashi "
"eh gaskiya ya ka mata  ya tsaya yaji kiran mi suke mashi "
"kin san halin shi ummy wani lokacin da baƙar zuciya "
"ai kuwa dole ya rage ta, tun da komi ma su kayi mashi shi ya jawo ma kansa "
"haka ne, ummy yaushe su mamy su kace zasu dawo?" ammy ta faɗa
"ta ce man wani watan idan Allah ya kaimu "
"Allah ya kaimu, ina son idan za su koma na bi su na kwana biyu banje Morocco ba "
"gaskiya ya kamata kije har da yarannan "
"da su nake son zuwa musamman shazim da bai son shiga mutane "
Ummy tace "ai lamarin angon nawa ne sai adu'a " firar su suke har sai da bacci ya fara ɗaukar su, sannan ummy ta tashi ta tafi ɗakin malam.....
Episode 32_33

......... Washe gari ta kasan ce friday, sun tashi da shirye shiryen tar bar baƙi, uncle Ahmad ne yace ma  Kairiyya ta samu  Feenah da su Fatima su gyara part ɗin da ke kusa da na innah.
A part ɗin innah ta same ta kwance kan gadon innah da a'lama ma a nan ta kwana, ko da Kairiyya tayi mata magana cewa tayi   "mizai hana a sa masu aiki su yi gyaran"
Kairiyya tace "wannan kuma abbah zaki faɗa ma haka bani ba, tun da bani nace ayi gyaran ba " innah na zaune kan carpet tana jin su amma bata ce komi ba
"To gaskiya ni  bazan   iya ba,gara ma tun wuri kije ki samu masu aiki kuyi gyaran tare,  amma ni bazan iya ba" abun yayi matuƙar ba   Kairiyya  mamaki duk da daman tasan Feenah, ba kasa fai ake sata aiki tayi ba, in dai batayi niyya ba to fa bazata  yi ba, amma ba ta yi tunanin cewa Abbah zai iya sata abu tace bazata yi ba,
"yanzu dai mi kike nufi "
" bana jin daɗi, bazan iya ba "ta bata amsa kai tsaye, Kairiyya tayi tuna nin Innah zata sa baki jin abun Feenah tace amma sai taga innah tayi kamar ba bata san da zaman su a ɗakin ba , kallon Innah tayi tace "Innah kina jin mi tace ko " Innah tace
"dan Allah ni karki dame ni, tun da tace bata jin daɗi, to sai ki ƙyale ta, ai sai  da lafiya ake komai " jinjina kai Kairiyya tayi haɗin da cewa "haka ne kam, gaskiya ne " tana gama faɗa ta tashi ta fice daga ɗakin, innah tace
"yau ga fitinanniyar yarin ya"da harara Feenah ta rakata tana faɗin "sai kace an ce mata nima yar wahala ce irin ta " ta faɗa haɗi da jan tsaki, juya kwanciyar ta tayi tana kallon Innah tace "Amma dai Innah su gwaggo uwani na zuwa yau za a yi meeting ɗinnan ko "
"sannu uwar yan gaggawa, saboda cin rabo ne abun kawai daga zuwa sai a kama meeting, ai a bari su huta "
"shikenan da ƙarfe nawa tace zasu baro kurfi"
"wannan ne kuma ban sani ba ".

Kairiyya ko da ta fita daga part ɗin Innah part ɗin uncle Ibrahim ta nufa,  sumun Fatima da Sa'ada tayi, tace su zo su tai maka mata su gyara part ɗin da ke kusa da na Innah, ba musu su ka taso suka bi bayan ta, lokacin da suka isa part ɗin   a buɗe su ka same shi, duk a tunanin Kairiyya  Abba ne ya buɗe shi, sai da suka shiga ciki su ka samu laure mai aikin mama da saude mai aiki momy suna ka kaɓe ƙura, cewa tayi "ai da kun barshi " laure tace "A'a aikin zai yi maku yawa
Ashe  laure ce ta amshi key wurin mama ta buɗe part ɗin ta kira saude ta taya ta su graya pary ɗin, a ganinta ga su a estate ɗin mi zai sa su Kairiyya su yi akin, Kairiyya ta ce"ai da kun barshi, tun da gani ga fatima da  sa'ada  "      laure tace "A'a aikin zai yi maku yawa, ki bari kawai muyi "
Kairiyya tace "Allah kuwa da kun barshi za mu iya"
"A'a duk da haka dai " ganin sun nace ne yasa Kairiyya cewa sai dai suyi aikin tare,a haka su ka cigaba da aikin suna fira sun ɗauki tsawan lokaci kafin su gama,sai wurin sha biyu da minti arba'in da wani abu su ka kammala, part ɗin uncle Ibrahim su Fatima su ka nufa, wanka su kayi da sallah kowace ta nemi wurin kwanciya ba tare da sun nemi abinci ba  duk da suna jin yunwa.

  ✨SHAZIM✨

Kwance yake kan gado a rigingi ne kanshi yana kallon sama, idanun shi a rufe da a lama bacci ya ke, wayar shi dake kan bed side ce ta fara ringing, har kiran ya katse bai motsa ba,wani kiran ne ya sake shigowa, mutsu mutsun  buɗe idanuwan shi ya shiga yi ,  bu ɗe su yayi yana kallon saman ceiling, ya ɗauki kusan five seconds yana kallon,  kiran na shirin katsewa ya zura hannu ya jawo ta, picking yayi ba tare da ya du ba mai kiran na shi ba, muryar majeed ce ta daki dodon kunnen shi yana sallama, sallamar ya amsa cikin kasa lelliyar murya ta masu bacci yake  faɗin"majeed kai ne "
"eh nine, kamar ma bacci kake?"
majeed ya tambaye shi amsa  ya ba shi da "kai dai bari, ya aiki"
"Alhmdllh, dama na kira ka ne saboda kayan nan da ke store, masu su fa sun fara bibiyar kayan "
"mi ya faru kace haka? "
"jiyan bayan tashi na security ya kira ni yake ce man wa su mutane sun zo bayan tafiya ta, wai sun zo da shigar jami'ain kiwan lafiya,  an turo su ne dan su yi bin cike a abnoor a kan ana ba da magani ba bisa ƙa'ida ba , sun nemi da su  buɗe masu store"
"store kuma, su yi mi kenan a ciki "
"shima tambayar su yayi mi za su yi a store shine su ka ce wai suna son su bincka magungunan da muke da su, bai dai buɗe ma su store ɗin ba dan cewa yayi ba shi ke da makullin store ba,da ya faɗa masu haka sai tambayar shi su kayi wai hospital ɗin na waye, so ya dai ceman bai faɗa masu saboda bai yadda da su ba, in dai har da gaske turo su a kayi yasan baza su zo a wannan time ɗin ba, sun dai ce zasu dawo"
"ok yaushe su ka ce zasu dawo "
"ba su faɗa mashi ba, sun dai ce kawai za su dawo "
"ok to shikenan, nima ranar sunday zan dawo, idan na dawo za mu san yan da zamu bullo ma al'amarin insha Allah, buri na dama su fara bibiyar kayan"
"Allah ya kaimu ranar sunday ɗin"
Ameen ya amsa, sallama su kayi, mai da wayar yayi kan bed side, tunanin ya shiga"wai su waye masu wannan kayan ne?" tambayoyi yayi ta jefa ma kanshi bashi da mai bashi amsar su, ya jima a kwance shi bai koma bacci ba shi bai tashi ba, sai da aka fara kiran sallar asr, sannan ya sauka daga kan gado ya shi toilet, wanka ya sake da al'wala, shiryawa  yayi cikin wani yadi mai taushi brown color ya sa hula milk color, feshe jikin shi yayi da turare mai ƙamshi, masha kamar ka sace shi ka gudu, shoe rag ɗin sa ya nufa ta kalmi ya ɗauko brown color ya sa , wayar shi ya ɗauka da key ɗin mota ya fice zuwa parking lot, wata farar mota da bai taɓa hawa ba tun da su ka zo ya nufa, shiga yayi cikin ta yayi reverse ya nufi main gate, ya na nufar main gate wasu motoci  guda shidda su ka shigo cikin estate ɗin,ko mawa yayi yana tafiya slowly time ɗin da  ya iso bakin gate ɗin har  sun gama shi gowa, ficewa yayi ya bar estate ɗin,part ɗin innah motocin su ka nufa, parking  su ka yi, na cikin motocin ne su ka fara fitowa,wata kyakyawar mata ce ta fara  fitowa fara ce amma ba sosai ba  a ƙallah zata yi kimanin shekara 51 zuwa da biyu Aunty uwani kenan,  part ɗin innah ta nufa, ɗaya bayan su ke fitowa daga motacin, harda wata mata mai matuƙar kama da wacce ta shiga part ɗin innah sai dai tafi waccen haske nesa ba kusa ba,a ƙallah za tayi kimanin shekara 49 Aunty sadiya sunan ta ƙanwar Aunty uwani ce  , su uku suka fito daga bayan motar ita da wasu matasan  mata ɗaya da yaro a hannun ta ɗayar kuma da goyo, mai yaron  bazata gaza shekara 32  ba a duniya, sunan ta Aunty Zainab ɗiyar gwaggo Halima   ce ita ce babbar ɗiyar ta, ɗayar kuma bata wuce shekara 30,ita kuma sunan ta maryam ɗiyar gwaggo  Uwani ce,  motar da ke bayan su wasu ƴan mata ne su ka fito su hudu uku daga baya ɗaya kuma daga gaba ta fito, wacce ta fito daga gaba a ƙallah zata yi ki manin shekara 23 sunanta farida ɗiyar gwaggo Halima ce ita ma  sai  ƴan mata guda uku biyun  zasu yi sa'annin baza su wuce shekara 27  ba Asma'u da Amina kenan,dukkan su suna da aure sai dai ba wacce ta haihu Amina Anwar take aure ɗan gwaggo Halima , ɗayar kuma bata wuce shekara 25,  sai motar da ke bayan su yar matashi yar buduwar wa ce ta fito baza wuce sa'annin su kairiyya ba, sai maza su uku, motar da bayan su kuma duka maza ne manya su huɗu,du kan su part ɗin innah su ka nufa da sallama a bakin su, innah na zaune kan sofa ita matar da ta fara shigowa , tashi innah tayi tana faɗin " lale marhabun , sannun ku da zuwa" wurin zama ko wannan su ya samu, wa su kan sofa wasu kan carpet,   feenah ce ta shigo  da gudu daga ita sai vest da da wando gyelen da ta ɗaure kan ta da shi a hannu ta shigo da shi ta nufi wannan  matashiyar wacce za su yi sa'annin, hugging ɗin ta tayi "oyoyo sister yau she rabon da na ganki "
"ai baki son zumunci ne feenah "
"kaji sai kace kema zumunci kike so"
"wallahi kin san gara ni da ke "
"ba wani nan, yau she rabun ki da abuja, zaki wani ce gara ke "
babban da ke cikin su ne ya daka ma feenah tsawa yana faɗin " ke baki da hankali , baki ganin  mutane zaki wani shigo da gudu ko sallama babu, ji kayan da ke jikin ki " faɗuwa gaban ta yayi dan shaf ta manta da wane kaya ne jikin ta, ta kuma manta cewa harda ya usman za'a zo, dan bala'in shakkar sa take
"iskanci ki na nan ko,ki shiga hankalin ki da ni, kina son kafin na bar garinnan jikin ki yayi tsami, sa karya kawai " innah tace "A'a usman da kata daga shigowar ka baza ka ta kura ma yarinya ba, kai shikenan bazata nuna murnar ganin ƴar uwar ta ba "
wannan matar ce wacce ta shigo daga baya  gwaggo Halima tace "dama mama  har yanzu baki daina goyan bayan  feenah ba, ki duba fa yan da ta shigo ko sallama babu, ji kayan da ke jikinta  "
"dan Allah ya isa haka sadiya, daga zuwan ku za ku ta kurama yarin ya, sai ɗoki take ku zo amma kun zo za ku fara tasa ta gaba da masifa "
"to shikenan , nayi shiru "
Usman yace "zaki fice kije ki canza kayannan ko sai na ɓaɓɓalaki wa wuya kawai"
jan hannun matashiyar budurwar feenah tayi su ka fice, su Fatima ne su ka shigo su  da momy  bakin su ɗauke da  sallama, amsa masu sallamar su kayi cikin parlorn su ka shiga, gaisawa momy ta shiga yi da su gwaggo uwani, su fatima gaishe da  su su kayi,gwaggo Halima ce kawai ta amsa gaisuwar da fatima tayi masu , amma gwaggo uwani yi tayi kamar ma bata san da fatima ba a parlorn sai ma tashi da tayi ta nufi ɗakin innah,da idanu kawai fatima ta bi ta idanun ta na kawo ƙwalla, gwaggo Halima ce ta lura da halin da fatima ta shiga, dafa kafaɗar tayi "Fatima ya Ammyn ku, ina su noraiz da shazim " tayi mata tambayar ne dan ta kau da mata hankali daga abun da gwaggo uwani tayi mata,
"ya noor na tare da ya mahmud, ya shazim ne dai ban san inda yake ba amma ina tunanin yana tare da ya mansoor "
"masha Allah, ya su malam"
"lafiya lau su ke " janta da fira tai tayi har sai da ta saki ranta
"Fatima mu baki ganmu ba ne " wata kyakyawar budurwa ce zaune kusa da sa'ada
"Allah sarki Aunty farida so nake mu gama gaisawa da gwaggo, ina wuni, ya hanya?"
"lafiya lau fatima, ya lagos, ina Ammy"
"Ammy na lagos "
ɗaya bayan ɗaya fatima ta bisu tana gaishe da su, wasu su amsa wasu yi banza da ita,har da masu sarka mata habaici,  da ta gaji da ganin abun da suke mata tashi tayi ta bar part ɗin ta nufi na su, hawayen da take ɓoyewa ne su ka shiga gangaro mata, tarasa miyasa gwaggo uwani bata ƙaunar su ita da ƴaƴen ta, ta ci kuka kamar mi ita ka ɗai a part ɗin har bacci ya ɗauke ta kan sofa.
A can part ɗin Innah kuwa, gwaggo Halima ce ta kalli su Aunty maryam da su Aunty Amina tace "yanzu ku da hankali ku da wayan ku kuke abu kamar wasu ƙananan yara, musamman ke maryam da girman ki zaki biye ma su Asma'u "
Aunty maryam tace "mi nayi kuma mama "
"ina kallon ku ke da su Asma'u  Fatima ta gaishe ku Zainab ce da Fiddausi kawai su ka amsa mata, miyasa kuke haka da hankalin ku"
"mun fa amsa baki lura bane "
tsaki ya usman ya jaya " wallahi har mamaki ki ke bani maryam ko yaro ƙaramin bazai yi abun da kike yi ba , ku kuma ku shiga hankalin ku" ya faɗa haɗi da nuna su da yatsa, mama ce ta shigo su ka gaisa da gwaggo Halima, bata wani jima ba ta koma part ɗin ta, mai aikin momy da mama ne suka shigo da manyan tray ɗauke da ruwa da lemu, bayan sun ajiye masu gaishe da su suka yi, sannan su ka fice suka kawo masu abinci da snacks .
Mansoor ne ya shigo parlorn, wuri ya samu kan sofa yana gaishe da su gwaggo uwani wacce   fito war ta kenan  daga bedroom ɗin Innah, hannu ya miƙa ma usman su ka gaisa "ya usman kwana da yawa, ka shige jos ba'ajin ɗuriyar ka"
"ba wani na shige jos, ai kai da shazim ba mutunci ne da ku ba, musamman shazim sai ya shigo jos sau ba a dadi amma ban taɓa ganin ƙeyar shi ba"
"Ka san shi da aiki ya Usman, may be shi ke hana shi zuwa in da kake"
"ba wani aiki kawai dai ba ya son zumunci ne"
gwaggo Halima ce tace"mansoor yana  ina ne   abokin naka "
"wai shazim?"
"Eh shi "
"Ina tunanin yana part ɗin su,na kira maki shine?"
"a'a ƙyale shi na san zai shigo " tsaki gwaggo uwani ta ja tana ce ma mansoor "kai je ka kira shi, tun da shi ya fi ƙarfin ya shigo gaishe da mutane"
"da kin  ƙyale shi yaya, na san zai shigo zuwa anjima kuma ma duka mintin mu nawa da shigowa, ra bu da shu Mansoor ba sai ka kira shi ba  "
"haka ku ke dama ke da su yaya, yaro yaita abun da yaga dama  amma ku baku gani, da ance kaza za ku kare shi"
"ba haka bane, idan har kika ga munyi goyi bayan shi to fah yana da gaskiya, haka nan baya abu batare da dalili ba"
" haka ku kaci rani, in dai shazim ne za mu gani "
banza gwaggo Halima tayi da ita kamar ma ba da ita  take maganar ba,
Mansoor yana nan zaune  noraiz da mahmud su ka shigo, wuri suma suka samu kusa mansoor su ka zauna, gwaggo uwani ce tace " ai nayi tunanin kai ma kafi ƙarfin gaishe da mutane kamar ɗan uwan ka " bai amsa mata tambayar ta ba sai ma gaishe ta da yayi, haushi abun ya bata , ta so ya bata amsa amma sai yayi kamar ma ba da shi take ba, da lafiya ta amsa mashi
suna gama  gaishe da su , su kayi  fice war su, su noraiz basu jima da fita ba  ba mazan ma su ka  tashi har da mansoor suka fice, shi da anwar part ɗin su shazim suka nufa sauran kuma suka nufi part ɗin da aka tana da domin su, a can su saude su ka kai ma su abinci.
bedroom ɗin sa suka nufa, mansoor yayi nocking har ya gaji, wayar shi ya ciro daga aljihu ta lalubo number shazim ya kira, har ta tsinke bai yi picking ba sai da ya sake kira sannan yayi picking, yana ɗauka mansoor yace "kai wai kana lafiya ake ta nocking " kwance yake kan bed ɗin Abdallah a gidan uncle Ahmad, ɗan ya tsina fuska yayi yana faɗin "bafa na nan, na fita tun ɗazu"
"ok kana ina ne?"
"ina wurin Abdallah "
"yaushe zaka dawo,su Anwar fa sun zo kuma gwaggo  Halima na neman ka"
"may be  sai dare ko gobe" amsar wayar Anwar yayi yana faɗin "muna gidan zaka ce wai sai gobe, wasa dai kake ko"
"Anwar ya hanya "
"Alhmdllh, ina nan ina jiran shigowar ka"
"to shikenan sai na shigo "
"ok ina zama jira "yana gama faɗa yayi rejecting kiran, barin part ɗin su kayi zuwa part  ɗin mansoor.

Sai da yamma liƙis su  Abbah  suka dawo daga wurin aiki  nan part ɗin innah su ka yada zango a parlor, suna firar yaushe gamo da ƴan uwan su,
Auny uwani ce tace" yaya ba naji kamar kace shazim da noraiz suna garinnan ba da muka yi waya da kai "
Uncle Ahmad yace "eh suna nan, basu shigo kun gaisa ba ne "
"banga ƙeyar ko ɗaya daga cikin su ba, dama noraiz me ɗan iya gaishe da mutane inya gansu, shi ko wannan uban marasa kunyar yafi ƙarfin gaishe da kowa"
Uncle Ahmad yace "haba uwani, wai miyasa a kowane lokaci kike ma shazim musammanar fahimta ne,yanzu haka baya nan ne , shi yasa baizo ya gaishe da ku ba "
"dama nasan haka zaka ce yaya, da anyi magana kan shi sai ku   goyi bayan shi "
gwaggo Halima tace"bawai an goyi bayan shi bane, kece dai baki fahimci shi ba, kuma ai noraiz ya shigo nan kun gaisa da shi "
"to naji, ai naga ke yazo ya gaishe ki ke da kika fahimci shi" girgiza kai kawai gwaggo Halima tayi ba tare da tace komi ba,
Uncle Ahmad yace
"ya isa haka, idan ya dawo zai shigo ku gaisa "
"Allah yasa "a cewar gwaggo uwani
sunjima a part innah suna fira, sai da aka fara kiraye kirayen sallar magrib su ka bar prt ɗin zuwa masallaci, su ma gwaggo Halima ta shi su kayi su ka shiga ɗakin Innah domin gabatar da ta su sallar, har sai da su kayi isha sannan su ka dawo parlor , sai bayan sallar isha kairiyya ma ta shigo gai she da su, su Aunty maryam kamar su cinye ta dan bata zo tun ɗazu ba, haƙuri ta ba su akan bata jin daɗin ne shiyyasa ba shigo ba, bata wani jima ba ita ma ta koma part ɗin su.

feenah tun korar da usman yayi mata bata sake shigowa part ɗin ba sai yanzu ta shigo ita da ilham, a nan parlor suka zauna suna fira da su Aunty maryam.

Wuraren ƙarfe 9 ya motar shi ta shigo estate ɗin, a hankali yake driving  kamar baya son yi, part ɗin su ya nufa yayi parking, ya jima zaune a mota yana  waya, sai da ya kammala wayar shi tukunnan ya fito ya nufi cikin part ɗin tsit babu motsin kowa kamar ko wane lokaci, bedroom ɗin shi ya nufa, kayan jikin shi ya shiga ragewa bayan ya ajiye wayar shi da key ɗin motar da ya fita, toilet ya shiga, bayan kamar   10 minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe, bakin window yaje ya tsaya yana kallon   cikin estate ta baya  kamar mai tunanin  wani abu , ya jima a tsaye a wurin,daga baya ya saki curtain ya bar jikin window ya nufi clothes set ɗin shi, pajamas ya ɗauko riga da wando, wandon iya kar shi gwiwa sai riga mai garen hannun,cire bathrobe ɗin jikin shi yayi daga shi sai short, pajamas ɗin ya ɗauka ya sa, bayan ya gama sawa,cap ya ɗauko irin ta sanyi black color ya sa,fehe jikin shi yayi da turaren shi mai ƙamshi,  wayar sa da ya ajiye kan bed ya ɗauka ya zura ta cikin pocket ɗin wando, flip flops ya zura a ƙafar shi, fita yayi daga bedroom ɗin main parlor ya nufa fita yayi daga part ɗin zuwa part ɗin mansoor,yana shiga main parlor su Amina,  Asma'u da farida ya samu zaune kan sofa suna fira sai  kairiyya  da ke kwance kan sofa,ɗauke kai yayi daga kansu,  amsa mashi sallamar da yayi su kayi, gaishe da shi su ka shiga yi, ba tare da ya tsaya ba ko ya kalli inda su ke ba yace lafiya, iya abun da yace kenan ya haura sama wurin mansoor, tura ƙofar parlorn yayi ya shiga, samun mansoor yayi zaune kan doguwar sofa shi da Fiddausi suna fira ( ɗiyar gwaggo Halima ce,  ita ce budurwar shi da suke waya )  a bakin ƙofa ya tsaya yana kallon su, daga baya kuma ya shigo cikin parlorn, mansoor yace "ok ashe zaka dawo " ba tare da ya amsa mashi tambayar da yayi mashi ba, fuska a ɗaure ya kalli Fiddausi yace "ke tashi ki ba mutane wuri

Episode 34_35

............. Wani ɗan iskan kallo shazim ke bin mansoor da shi
"kasan Allah ko ma wane irin kallo zaka man sai dai kayi amma ba in da zata, tun da ba kai ka kawo ta ba "
"ok haka kace "
"Kwarai kuwa haka nace, kayi duk abun da ka ga dama " Fiddausi dai na bayan mansoor tana zare idanu ƙes take jira ta watsa a guje, kallon ta shazim yayi yana faɗin "ke zaki zo ki wuce ko sai ranki yayi mumunnan ɓaci "
fitowa tayi daga bayan mansoor zata fice, jawo hannun ta mansoor yayi yana faɗin "in wasa da ke ne " hawaye suka fara sauka daga fuskar ta, girgiza mashai kai tayi alamar a'a, "to koma kan sofa ki zauna " ƙin komawa tayi saima sake ɓoyewa da tayi bayan mansoor ɗin, nufo su shazim yayi gadan gadan, ai ba shiri ta watsa da gudan, dan bata san mi zai yi mata idan har ya kamta,sai da ta kusa shiga parlor sannan ta tsaya kan stairs case tana mai da nufashi,  kallon ta su Asma'u su kayi, Amina tace "ke lafiya daga ina haka, sai kace wacce wani abun tsoron ya biyo " bata bata amsar tambayar da tayi mata ba sai ma binsu da take yi da idanu, sai da ta ɗan dawo cikin hankalin ta sannan ta ƙaraso cikin parlorn ta nemi wuri kan sofa ta zauna,sake tambayar ta Amina tayi "yo yana wuce ya shazim ne ya koro to" acewar Asma'u,
Amina tace "wai baza ki yi magana bane"
Sai a lokacin ta samu damar cewa "ya shazim ne ya koro ni ya mansoor yace ba inda zani, ganin yace ba idan za

Please Login or Register in order to submit comment