Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

parlor suna breakfast, ga naku nan kai ma mun kawo maku kai da ya Abdallah " murmushi yayi a zuciyar shi yace " Ameerah ba dai surutu ba,  Aaimah ce tayi gyaran murya tana faɗin
" to ni dai a bani wuri na wuce dan na gaji da tsuyuwa" girgiza kai safwan yayi da murmushi a fuskar shi yace
" Aairah uwayen ƙorafi, zo ki wuce kar ki faɗin ƙasa " ya faɗa haɗi da matsa mata hanya, ciki ta shige tana faɗin " wai dan Allah mi yasa ya safwan kake ce man Aairah ne, ba fa ita bace wannan Aaimah ce " ta faɗa yayin da take ajiye tray ɗin kan carpet, Ameerah ma bayan ta ta bi ita ma ta ajiye wanda yake hannun ta
"to naji ina ita Aairah take na ganku ku ka ɗai, ita bata zuwa a gaisa ba" 
"tana parlor wurin su mom " Aaimah ta faɗa yayin da take nufar ƙofa
"to ki kira man ita " da to Aaimah ta amsa haɗi da nufar ƙofar fita su ka fice,  tana zuwa wurin su mom tace " Aairah kije ya safwan yana kira " ɗagowa Aairah tayi tana faɗin ni kuma
"A'a ba ke ba ni " Aaimah ta faɗa yayin da take jan kujera ta zauna

"dallah daga tambaya zaki wani mai da man da baƙar magana "

"an mai da maki, dallah malam idan zaki tashi kije ki tashi idan kuma bazaki tashi ba kiyi ta zama ƴar rainin wayau wai ni A'a ni " Aaimah ta faɗa tana kwai kwayon yanda Aairah tayi magana,

Aairah tace " mom kina jinta ko daga maganar ariziƙi sai ta tsiya "

dafe kai mom tayi tana faɗin
" ya Allah, ke Aaimah kar na sake jin bakin ki ke kuma Aairah tashi kije kira da yake maki " 

tashi Aairah tayi tana hararar Aaimah, taɓe baki Aaimah tayi tana faɗin
" inga sun zazzago ƙasa  sannan zan san kina harara"tsaki Aairah taja haɗi da wuce wa ta nufi  part ɗin Abdallah, girgiza kai ka wai mom tayi ba tare da tace ma su komai ba.

Nocking tayi, izinin shiga aka bata, tura ƙofar tayi ta shiga, zaune yake kan sofa  kamar yanda su Aaimah su ka barshi hannun shi ruƙe da cup ɗin tea sai turiri yake,yayin da Abdallah ke zaune kan carpet yana haɗa breakfast fitowar shi kenan daga bedroom ya samu an kawo masu breakfast, safwan  ɗago da fuskar shi yayi ya zuba mata ido haɗi da amsa mata sallamar da tayi, gaishe da su tayi tana faɗin " ya safwan gani Aaimah tace wai kana kira na " amasa mata gaisuwar yayi yana faɗin
" dama ba wani abu bane kawai naga baki zo bane shine na ce su kira man ke mu gaisa tunda ke baki zo ba "
" zan zo ya safwan breakfast nake ne shiyyasa "
" ok yayi kyau, kin tashi lafiya "
" lafiya lau "
" masha Allah "
" ina iya tafiya " ta faɗa dan duk ta gaji da tsayuwa da kuma kallon da yake mata
" eh kina iya tafiya dama kiran kenan "
"to sai anjima " ta faɗa haɗi da ju yawa zata wuce Abdallah ne yace " ki dawo anjima ki kwashe wannan kayan " ya faɗa yana nuna mata kayan breakfast ɗin da ke gaban sa, da to ta amsa haɗi da kama hanyar ficewa, idanu safwan zuba mata har sai da ta ɓace ma ganin sa tukun ya janye idon sa, karb su ka haɗa ido da Abdallah, hararar shi yayi yana faɗin
" lafiya da wannan kallon malam " taɓe baki Abdallah yayi yana faɗin
" aiki ya zo ga ma iya "
" ƴan sa ido ba " safwan ya faɗa
" mi zan sa ma ido a nan, Allah ya kiyaye " Abdallah ya faɗa yana mai da kanshi kan breakfast ɗin da yake yi
"Ohon maka kuma  wannan " safwan ya faɗa shima yana kai cup ɗin tea dake hannun shi baki, babu wanda ya sake cewa komai cikin su.

_*✨LAGOS✨*_

Zaune yake a office ɗin shi yana aiki, files ne gaban shi na patient yana duba wa, wayar shi ce ta fara ringing, hannu ya sa ya ɗauko ta, du ba mai kiran shi yayi, privet number shine abun da ya gani, tsaki ya ja haɗi da yin rejecting kiran ya cigaba da abun da ke gaban shi, wani kiran ne ya sake shigowa, ko kallon inda wayar take bai yi ba haka taita ruri har ta gaji tayi shiru alamar mai kiran ya gaji
sai ga message ya  shigo, ɗaukar wayar yayi dan ganin wanene ya turo mashi message, baƙuwar number ce ya gani kuma da alama bata nigeria ba ce, buɗe message ɗin yayi ya fara karan tawa kamar haka

_DR ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN,manya yan aji bakwai ba'a ɗaukar baƙuwar number ganinka  kuma sai an cika form,wow i like your style  keep it up  na san nan gaba zai yi maka amfani, ba komai bane ya sa nake neman ka ba face ina so na sanar da kai illar dake cikin yaƙin da kake son  jefa kanka aciki,manyanka ma sunyi ba suci riba bare kai ƙaramin alhaki ko da yake hausawa na cewa barewa baza tai gudu ɗan ta yayi rarrafe ba malam Abdulƙadir o afuwan dr Abdulƙadir kar kace na mai da kai malamin makaranta 😊, ya ta kwaranka kuma kakan ka mun kwana biyu ba mu gaisa ba amma da alama yanzu na lura  kana so mu dawo da zumunci dake tsakanin mu , fatan yana lafiya shi da hajiya zainab ina nufin ummy????, 
Abdulƙadir ina mai baka shawara idan har kana son zamanka lafiya a duniyar nan to ka tsame hannuka daga abun da kake shirin aikatawa gudun aikata abun da zai jefa ka cikin matsala kai da iyalanka, fatan zaka ɗauki shawarata duk da na san kai mai taurin kai ne amma ina mai baka shawara._

Wani wawan tsaki shazim ya ja lokacin da ya kawo ƙarshen message ɗin yana faɗin " aikin banza matsora cin banza da wofi kawai, mu zuba mu gani ni da kai da duk wani mai hali irinka shege ka fasa " ya faɗa yana
maida kanshi yayi kan abun da yake, wani tsakin ya sake ja yana sake faɗin " aikin banza matsoracin banza da wofi kawai "

Ƙofar office ɗin yaji an turo an shigo, majeed ne ya shigo a uzirce kamar wanda aka jeho, wurin shazim ɗin ya matsa yana faɗin " amshi shazim ka gani " ya faɗa yana miƙa ma shazim wayar shi, amsar wayar shazim yayi yana duba abun da majeed ɗin ke nuna mashi, text message ne shima aka turo mashi da irin number da aka turo ma shazim yanzu, karanta message ɗin shazim ya shiga yi

_ABDULMAJEED MA'ARUF WAKILI,na san za kayi mamakin wanene ni da kuma sunan ka da na ambata, kar kayi mamaki yanyi ne yasa haka.
a taƙaice dai abun da ke tafe da ni,  ba wani abu bane face ina so na ja maka kunne kai da  abokinka, ku rufa ma kanku asiri ku fitar da kanku acikin yaƙin da  iyayen ku su ka kasa,idan kuma ba haka ba zaku sa kan ku cikin bala'in da ba kuyi tsammani ba ku da iyalanku, shawara ce idan kun  ɗauka  ku zata yima amfani idan kuma kun ƙi to duk abun da ya biyo baya  kuyi kuka da kanku._

Tsaki shazim yaja yana miƙa ma majeed wayar shi, amsa majeed yayi yana faɗin
" ni dai shazim a ganina mu fitar da kan mu a wannan matsalar ko dan su Ammy "

" tsoro kaji ne wai majeed?"

" dole naji tsoro shazim, barazana fa yake mana, ni abun da nake ganin zai fi shi ne kawai kayan nan mu miƙa ma hukuma su "
" to dan yana mana barazana sai mi, ya isa yayi mana abun da Allah bai nufa ba ne, sannan kaya da kake cewa mu miƙa ma hukuma su tamkar munji tsoron ne kuma Allah zai kama mu da laifi duk wanda ya cutu a kan kayan "
" bai  isa ba shazim,kuma Allah bazai kama mu da lafin wani ba tunda hukuma muka ba kayan kuma muna kyautata zaton tayi adalci ne"
"majeed ina so ka fahimci wani abu a lamarin ƙasar nan cin hanci yayi yawa muna ba da kayan nan zai ba da cin hanci ne a bashi batare da tausayin bayain Allah ba da aka ɓata ma rayuwa ba, yau da ace ƴaƴansu zasu ba da bazan da mu amma inaji ina gani bazan bari a cuci al'ummah ba "

"haka ne shazim, amma duk da haka mu miƙama hukuma ko dan su Ammy dan  gaskiya ina jin tsoron abun da zai biyo baya idan muka cigaba da riƙe waɗannan kayan "
" to idan kana jin tsoro ka kira shi kace kai ba ruwanka, Amma ni ba gudu ba ja da baya " shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi wata ƙofa dake kallon in da yake zaune, tashi majeed yayi yana faɗin " miyasa zaka ce haka shazim, ko da naji tsoro ai bazan iya tsame hannu na ba na barka "
Shigewa ciki yayi ba tare da yace mashi komai ba, bin bayan shi majeed ɗin yayi, tura ƙofar ɗakin yayi ya shiga, ma daidai ci ɗaki ne mai kayan gaske harda ɗan madaidaici family bed a cikin sa da sofa masu kyau guda, tsaye ya hango shazim bakin wani ɗan ƙaramin fridge ya na ɗauko robar ruwa, sofa dake ɗakin ya nufa haɗi da samun wuri ya zauna, shima zama majeed yayi yana faɗin " Please shazim ina so ka fahimce ni ne, bana so mujefa wani daga cikin ahalin mu acikin matsala ne shiyyasa na ce haka" ajiye robar ruwan shazim yayi yana faɗin " majeed akwai wani ɗan adam daya isa yayi ma bawa abun da Allah bai ƙaddara ba "
"A'a shazim "
"to inaso ka fitar da wannan tsoron a ranka ka fuskanci gaskiya, duk wani barazana da zai yi mana yana yi ne dan muji tsoro "
"to shikenan, yanzu ya zamuyi "
"karka damu zanyi shawara komai na yanke zan sanar da kai "
"to shikenan bari na koma office na barshi ba kowa "
"to shikenan, ka ja man ƙofar idan ka fita" shazim ya faɗa, tashi majeed yayi ta fita haɗi da rufe mashi ƙofar kamar yan da yace.
Zamewa yayi ya kwanta kan sofar, idanuwan shi ya rufe  kamar mai bacci.

Duk  yinin ranar a wannan ɗakin yayi shi ko sallah a nan yayi ta, sai da yamma bayan sallar asr ya tashi ya koma cikin office ɗin kayan da ke kan table ɗinshi ya tattara ya zuba cikin locker sannan ya ɗauki briefcase ɗin shi da wayar shi ya fice zuwa parking lot in da ya ajiye motar shi, briefcase ɗin ya fara ajiye wa sannan ya zagaya ma zaunin driver ya zauna, key yayi motar haɗi da reverse ya nufi gate, da katar da shi mai gadi yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu, parking yayi a bakin gate ɗin yana ce ma maigadin " lafiya dai ko?"
"lafiya lau ranka ya daɗe, dama wasu mutanen suka zo neman ka ɗazu"
"Suna ina?"
"ban barsu sun shigo ba yallaɓai sun tafi "
"saboda mi mudi, nan fa asibiti ce dan mi zaka hana su shigowa idan suna tare da patient ne fa "
"yallaɓai abun da yasa na hana su shigowa shine basuyi kama da marasa lafiya ba yallabai wallahi da ƴan dambe su kayi kama duk sun wani sha baƙaƙen kaya kamar sheɗanu "
"mi suka ce maka da suka zo?"
"wai maigindan su ne ya aiko su wurinka,daga ganin ba su da gaskiya shiyyasa ni da su isya muka hana su shigowa "
"koma dai minene, daga yau idan su ka sake zuwa ka kirani ka faɗa man kaji ko "
"eh naji ranka ya daɗe, insha Allah su ka sake zuwa zan kiraka na sanar da kai "
"to shikenan, buɗe man gate na wuce"
"to yallaɓai " mudi ya faɗa haɗi da nufar gate  ya buɗe mashi, ficewa  yayi ya daga Asibitin ya hau kan titin da zai sada shi da  gida.

Wayar shi dake ciki briefcase ɗin shi ce ta fara ringing, banza yayi da wayar dan ya san bazai wuce wannan shashashan mutumin ba ne, wani kiran ne ya sake shigowa, tsaki yaja yana faɗin
"sai kuma kayi ta yi"
Kira ne yai ta shigowa ba ƙaƙautawa amma ko kallon briefcase ɗin bai yi ba bare ya ɗauki wayar har ya iso gida, horn yayi a bakin gate mai gadi ya buɗe mashi, ciki ya shiga yayi parking a parking lot ya jima a motar bai fito ba wayar shi ya ciro cikin briefcase ɗin dan ganin wane mahaluƙin ne yayi tayi mashi wannan kiran duk da yana da ya ƙinin waɗannan mutanen ne sai dai kuma da ya duba mai kiran nashi number mansoor ya gani da ta Ammy sai noraiz da fatima, faɗuwa gaban shi yayi yana faɗin
"Ya Allah,  mike damun su Ammy su ke man wannan kiran" a hanzar ce ya buɗe motar ya fita ko briefcase ɗin shi bai ɗauka ba ya fice zuwa cikin gida yana shigowa main parlor tsaitsaye ya samu su Ammy har da mansoor wanda zuwan shi kenan, sallama yayi ya nufi Ammy yana faɗin "Ammy lafiya mike faruwa ne ??"

"Feenah ce ta fita tun ɗazu da safe tace man zata je gidan su ummy to shine tun ɗazu bata dawo ba da muka yi waya da  ummy nake ce mata feenah wai yaushe zata dawo naga yamma tayi ko nan zata kwana shine take ceman wai wace feenah ita duk yau bata ganta ba,  na kira wayarta ni da su fatima yafi a ƙirga amma a kashe kuma ka san bata da lafiya  "
A jiyar zuciya  shazim ya sauke  yana faɗin " wallahi Ammy ba kuji yan da kuka tayar man da hankali ba, yanzu duk dan wannan yarinyar ta fita ne kukai ta man wannan kiran kuma kuka tashi hankalin ku"
"shazim ba asan inda taje ba fa nace maka kuma an kira wayarta a kashe  amma kake faɗin haka "
"Ammy ina wannan yarinyar zataje da  har zata ɓata, kawai dai taje yawan banzan ta da ta saba amma kina nan zata dawo da ƙafar data fita "

ran mansoor ne ya ɓaci jin abun da shazim ke faɗi ya rasa miyasa shazim bai ƙaunar feenah , amma sai yayi shiru baice komai ba

"haba shazim ya za kace haka, feenah fa yarinya ce ina zata je a garinnan da bata sani ba dama a abuja ne sai nace taje gidan su mahaifiyar ta ko gidan ƙawayen ta "
"Ammy ki kwantar da hankalin ki in dai akan wannan yarinyar ne ba in da zata shige a garin nan ta ɓata,  tana yawan da ta saba ne amma ba ɓata tayi ba  "
" wai shazim minene tsakanin ka da feenah duk kabi ka tsani yarinya kawai dan ta nace tana sonka shine zaka riƙa jifar ta da waɗannan kalaman " a slowly shazim ya juya yana kallon mansoor dake tsaye bayan shi  fuskar shi a murtuke tsan tsar ɓacin rai ne a idanuwan shi, side smile shazim ya saki yana faɗin " kai kuma saukar yaushe?"
" ban sani ba " mansoor ya faɗa
" to fa daga tambaya "
"ka riƙe tambayar ka bana so " murmushi shazim yayi wanda har ya bayyana kyawawan haƙuran shi
"wai wannan fushin duk na minene ƙarya na faɗa bata yawan ne " shazim ya faɗa yana ɗaga mashi gira
"kanka ake ji kuma " mansoor ya faɗa
"dan Allah ya isa haka, ya muna cikin wani hali ku kuma daga haɗuwar ku zaku kama yi ma mutane jaraba " Ammy ta faɗa
mai da kallon shi yayi ga Ammy yana faɗin " kar kia damu fa Ammy zata dawo ne dan kanta " yana gama faɗar haka ya nufi sama zuwa part ɗin shi da kallo kawai su ka bishi, sun rasa wace irin tsana ce shazim ke yima feenah da har bai damu da ɓatan ta ba kuma ya san bata da lafiya.

Zaune su kai a parlor ko wa yayi shiru suna jiran tsammani har akayi sallar magrib ba feenah ba labarin ta, wasa wasa dai har tara na dare feenah bata dawo ba kuma duk in da suke zargin za su ganta sun je amma ba labarin ta, fidda rai su kayi da zata dawo, mansoor ne yace su tashi kowa yaje kwanta idan bata dawo ba gobe za  su je police su  shigar da ƙara kawai, kowa ya aminta da maganar mansoor haka ne yasa su ka tashi kowa ya nufi ɗakin baccin shi.
Ammya na shiga ɗaki wayarta na fara ringing, abun yayi matuƙar bata mamaki ganin number feenah bayan yanzu ta gama kira a kashe, picking call ɗin tayi da ko sallamar da feenah keyi bata amasa ba tace " feenah ina kika shige duk kin bi kin tayar mana da hankali " daga cikin wayar fashewa da kuka feenah tayi tana faɗin " Ammy ni bana son na koma abuja "
" haba feenah idan baki son komawa sai ki faɗa man amma ba wai ki bar gida, yanzu kina ina?"
"ina gidan su wata class mate ɗina , dan Allah karki bari ya mansoor ya tafi da ni "
" shikenan bazan bari ya tafi da ke ba amma kar ki ƙara irin wannan shashancin kinji na faɗa maki"
" to Ammy bazan sake ba insha Allah "
" to shikenan, gobe ki dawo da safe "
" to Ammy "
" yawwa sai da safe " ammy ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran, fita tayi zuwa part ɗin shazim,nocking tayi mansoor ne ya  zo ya buɗe mata, a bakin ƙofa ta tsaya, mansoor yace" ki shigo mana Ammy "
" A'a ba sai na shigo ba, feenah ce ta kirani yanzu "
da sauri mansoor yace " ta na ina Ammy?"
"tana gidan wata ƙawar ta" 
Shazim dake zaune kan sofa taɓe baki yayi a zuciyar shi yana faɗin " ni ai na sani "
" amma feenah bata da hankali shine bazata faɗi ba zata tayar ma mutane da hankali dan sakarci"
" kai dai ka bari kawai mansoor, wai abuja ne bata son komawa shine tayi tafiyar ta "
" lallai ma yarinyar nan, zata dawo ai ta samu mutane " a zuciyar shi kuma yace  " na san ba kowa zai sata ba sai Innah "
" abun da nake mansoor idan zaka tafi  ita ka barta nan ɗin tun da tana son zama"
"Amma Ammy gata ga sa'ada abun zai yi yawa. "
"haba mansoor wane irin yawa ana zaman lafiya, idan ita ma Kairiyya bazata bika ba ka ƙyaleta lokacin da su ke san komawa sai su koma "

_ita sa'ada a nan zatayi school tare da fatima shazim ya nema ma su addimisson_

" shikenan Ammy" mansoor ya faɗa
" yawwa, sai da safen ku " Ammy ta faɗa haɗi da ja masu ƙofar, sai da safe su yayi mata, bedroom ɗin shazim ya nufa dan shi har ya shige.

_SAURA PEG ƊAYA YA RAGE A SEASON ONE_

_ZAN ƊAN JE HUTU KAFIN NA FARA SEASON TOW_

_GA MAI SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN DOCTOR SHAZIM 300 NE BA YAWA_

_3169482544 MUKHTAR HADIZA FIRST BANK_

_SAI A TURA SHAIDAR BIYA TANA WANNA NUMBER 09132289761 KO 08133650574_



_Episode  66_67

........... Kamar yanda Ammy tace ma Feenah  tun da safe ta dawo, sosai mansoor yayi mata faɗa kamar ya daketa,arziƙin Ammy kawai taci ya rabu da ita, washe gari da zai tafi ma faɗa yayi mata sosai akan ta kama kanta, in dai ta bari yaji ta aikata wani to zai zo ne da kanshi ya tafi da ita komai kuwa zatayi, ce mashi tayi inasha Allah ta bari  bazata yi wani abu ba, noraiz da fatima da sa'ada su ka raka su airport shi da kairiyya dan shazim tun faɗan da su kayi ba su wani shirya ba shiyyasa bai raka shi ba.

_*✨KATSINA✨*_

Addimisson ɗin su Aairah abokin uncle Ahmad ya amso,  sai dai kuma ba anan branch ɗin su dake abuja ba su ka basu Addimisson, branch ɗin su dake lagos su ka tura su,ko da uncle Ahmad ya sanar da abie cewa abie yayi baza su tafi lagos ba sai dai ya nema masu wata school ɗin anan katsina amma baza su lagos ba saboda shi baya son su zauna a hostel, mom ma da taji cewa tayi gaskiya sai dai suyi a nan amma bata bada goyan bayan suje lagos ba,su kuma suna so ba yanda ba suyi da abie ba akan ya amince yace A'a, sai ma kiran wani abokin shi yayi da ɗiyar shi ke school of nursing yace idan ba su gama bada addimisson ba yana so zai sama ma su Aairah.
" gaskiya ina tunanin sun gama ɗaukar ɗalibai amma zan bincika naji"
" to shikenan, komai kenan sai ka kirani ka sanar dani "
" to insha Allah " abie ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran
" haba yaya miyasa zaka ce haka, tunda dai suna son makarantar yaya ai banga aibu ba, kabi su da adu'a kawai insha Allah babu abun da zai faru da su har su gama " uncle Ahmad ya faɗa
" Ahmad ni bazan bar yarannan ba su zauna a hostel ko da ace a cikin garinnan ne bare ba nan ba can wata uwa duniya,  gaskiya bazan iya ba "
"yaya wai mi kake tsoro ne aciki, tarbiyya dai daidai gwargwado suna da ita nasan baza suyi abun da za muyi da mun sani ba, dan Allah ka bar yarannan suyi karatun su inda su ke so, ka bi su da adu'a kawai "
"dan Allah abie ka bar su, insha Allah wani abu bazai faru da su ba sai alkairi " Abdallah ya faɗa wanda zuwan su kenan shida safwan yaji uncle Ahmad nama abie magana akan makarantar
"Ai kai daman bakin ku ɗaya da su "
"ba haka bane abie, tunda suna so kuma kai kan ka ka yarda da nagartar makarantar ka barsu kawai dan Allah"
"yaya idan kana tsoron rayuwar da za suyi ne, ni ina da wani aboki dake cikin makarantar a nan yake zaune da iyalin shi sai kawai su zauna a gidan shi amma dan Allah karka hana su "
"Yanzu dai sai Alhaji umar ya kirani na ji, idan an samu nan ɗin to nan kawai za su yi idan ba'a samu bane to"
"dan Allah dai ka bar su kawai suyi karatun su a inda su ke so "
"Kaga wanda kake magana abokinka ne kar mu takura mashi "
"Idan kana ganin haka yaya to su zauna a hostel ɗin shi sai ya riƙa lura da duk wani shigi da ficen su "
"abie wallahi ina mamakin yanda kake ko kwanto akan su Aaimah"
"dole nayi kokwanto Abdallah, yara ne yanzu ka haife su ne baka haifi halin su ba "
"haka ne abie, abun da nake gani kawai mizai hana su zauna a gidan su shazim kawai dama fatima a can shazim ya nema mata addimisson kaga kawai sai su riƙa zuwa tare suna dawowa tare, hankalin ka ma sai ya fi kwanciya "

"to zan dai fi yarda da hakan, amma kana ganin baza'a ta kura su ba "
Uncle sadiq dai na gefe yana sauraron su kamar yana fahimtar mi suke faɗa, safwan ma sauraron na su yake amma baice ƙala ba

"haba abie wane irin takura kuma shazim fa nace maka ba wani ba,yanzu idan yaji kace haka ai bazai ji daɗi ba"

"duk da haka Abdallah, ka san halin su Aairah ba jin magana su ke ba kana gani a nan idan iya shegen su ya motsa yanda ake fama da su"

"wannan abie duk rashin aikin yi ne ke damun su, Amma da sun fara zuwa makaranta za su daina wasu abubuwan "

Fitowa su kayi daga cikin gidan
Aairah na ɗauke da tray wanda snacks ne a ciki, Aaimah kuma ruwa ne acikin trayn dake hannun ta yayin da Ameerah  bowl ne babba a hannun ta  yanka kun kayan marmari ne a ciki, wurin su abie su ka nufa dake zaune  a garden, ƙarasawa wurin su su ka yi,ya Abdallah ne ya nufe su trayn dake hannun Aaimah ya amsa

Please Login or Register in order to submit comment