Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

safwan kuma ya amshi na hannun Aairah yana ce mata " sannu da ƙoƙari "
Yawwa tace tana ya mutse fuska
"to fa ni da yake bani da galihu shiyyasa ba'a amshi na hannu na ba " Ameerah ta faɗa, dungure mata kai Abdallah yayi yana faɗin "bani nan uwar yan ƙorafi " turo baki tayi tana faɗin " yo ai dole nayi magana ya Abdallah an amshi na hannun su amma ni ban da ni "
"to naji Abdallah ya faɗa yana ajiye bowl ɗin da ya amsa a hannunta kan table ɗin da ya ajiye saura kusa da su abie.

"to oya a koma ciki" Abdallah ya faɗa, juyawa su kayi su ka nufi cikin gidan
wurin su abie ya koma,zama yayi kan kujerar da ya taso ɗazu yana faɗin

" abie babu wata matsala za su iya zama a can "

" amma Abdallah baka ganin za'a takura su, ni dai da ka bari kawai na nemar masu wata a nan"

" abie babu wani takura, amma idan baka son zaman su a can to dan Allah ka bari su zauna hostel babu abun da zai faru da su inash Allah, Amma na san Ammy bazata ji daɗi ba ace tana garin au zauna a hostel "

"A'a gaskiya ba za su zauna a hostel ba "
" to shikenan ka bari kawai nayi ma Ammyn magana "

_Duk wannan dagewar da Abdallah yayi yana yi ne dan shima ya samu dalilin zuwa lagos ɗin a kai a kai shiyyasa duk yabi ya dage_

" to shikenan, kira ta ni sai nayi mata baya ni da kaina"

to Abdallah yace yayin da yake zaro wayar shi dake cikin aljihu yayi dialing number Ammy, tana picking ya miƙa ma Abie tana faɗin gashi abie, amsa yayi haɗi da kara wayar a kunne, muryar Ammy yaji tana sallama haɗi da faɗin " Abdallah "
"bashi bane abie ɗin sa ne, an wuni lafiya "
" lafiya lau Alhmdllh, ya aiki"
" Alhmdllh, ina su shazim "
" suna nan kafiya, ya su hajiya kubrah da ƴa ƴa na, har yau dai sunƙi zuwa ko daya ke ba'a kawo man su ba zance ?"
" suna nan lafiya saboda su ne ma yasa na kira "
" to, Allah yasa lafiya?"
"lafiya lau, maganar makaranta ne mun nema masu makaranta ne a abuja to da suka basu addimisson sai suka tura su branch ɗin su dake nan lagos, bana son su zauna a hostel ne saboda yara yanzu suna gaban ka ma sai a hankali bare ace basa gaban ka shine nace nake son su zauna nan sai su dunga zuwa suna dawowa "
" Amma gaskiya banji daɗi ba,yanzu akan su Aairah har sai ka ka kira da kanka, haba dan Allah "
" ba wani abu bane, faɗin ai yana da daɗi "
"duk da haka dai banji daɗi ba "
" to ayi haƙuri "
"shikenan ya zanyi tunda anriga an gama, yanzu yaushe za su fara lectures?"
" nan da sati uku ne "
"to Allah ya nuna mana, nan ai gida ne ko da ka ma barsu a hostel naji labari bazan bar su ba "
"to shikenan nagode "
"wane irin godiya kuma"
"to shikenan sai sun zo ɗin "
" to Allah ya kawo su lafiya "
"Ameen ya Allah " abie ya faɗa  sallama su kayi ammy na faɗin tana gaishe da mom, miƙa ma Abdallah wayar  abie yayi , amma bai san yana yi ba saboda hankalin shi ba anan yake,
_har wani ajiyar zuciya  ya saki daya ji ammy tace ko da sun zauna a hostel zata dawo da su ne gida, yanzu ko ba komi ya samu kafar da zai riƙa zuwa lagos ba tare da wani yayi tunanin wani abu ba_

zaungurin shi safwan yayi cikin magana raɗa raɗa ya ce
" hankalin ka yanzu ya kwanta ko"
"sosai ma kuwa " Abdallah ya faɗa a hankali yanda su abie baza su ji ba "
"Amshi wayar ka na ce " abie ya faɗa yana sake miƙo mashi wayar, amsa yayi yana faɗi
"ka gani ko Abie, na san ma bazata ji daɗi ba "
"duk da haka dai tunda an faɗa mata ai shikenan nan "
murmushi uncle ahmad  yayi yana faɗin "yanzu sai da ka samar ma su idan ka fi yarda sannan hankalin ka ya kwanta yaya"
"bazan ɓoye maka ba gaskiya sai yanzu naji zan iya bari suyi ne sa da ni "
"to ai shikenan tun da ka amince "

Cikin gida su Abdallah su ka nufa shi da safwan, suna shiga main parlor da hayaniyar su Aairah su ka fara cin karo suna ma Ameerah dariya  tana kuka saboda ba su samu addimisson a abuja ba, ta so suyi makaranta tare amma Allah bai nufa ba shine suka tasa ta gaba suna mata dariya.

"ku har gobe baza kuyi hankali ba, ai gara ma da abie yace anan za kuyi karatu saboda baku da hankali "
Tsi su kayi, Ameerah kuma bata bar kukan da take ba tsawa Abdallah ya daka mata yana faɗin " billahil'azim ko kiyi man shiru ko ranki ya ɓaci " shiru tayi amma hawaye basu daina zuba ba, tsaki yayi ya nufi part ɗin mom, safwan kuma zama yayi kan sofa Aaimah tace "dan Allah ya safwan da gaske abie bai amince ba " ɗaga mata kai yayi alamar eh,ɓata fuska Aaimah tayi tana faɗin
" Amma miyasa abie zai ƙi amincewa "   dariya Ameerah ta kwashe da ita " wallahi Allah ya ƙara naji daɗi da abie ya ƙi amincewa "
"yar baƙin ciki insha Allah zai amince"
"bazai amince ba insha Allah" 

tashi safwan yayi yana faɗin
"Aairah ki kawo man tea please " turo baki tayi tana faɗin to, dama tun da ya zauna wurin bata sake cewa ƙala ba, haka nan ita fa shishige matan da yake yi ba burgeta yake ba,tashi tayi ta nufi kitchen ɗin shaf shaf ta haɗa mashi tea ta nufi part ɗin Abdallah, nocking tayi, da kanshi yazo ya buɗe mata ƙofar matsawa yayi gefe yana faɗin ki shigo ciki
" mom ke kirana " ta faɗa so kawai take ya amsa ta gudu, amsa yayi yana faɗin" to muje can main parlor sai na sha a can idan kin dawo daga wurin mom sai kizo " to tace haɗi da yin gaba yana binta a baya har main parlor, kan table ta ajiye mashi ta nufi ɗakin mom  da Abdallah ta ci karo zai fito,  yana ganin ta yace
"harkun biyo ni kenan"
"yaya ba kai na biyo ba wurin mom na zo "
" ba wani " ya faɗa haɗi da ficewa, ciki ta ƙarasa tana faɗin
" mom kinji dai ko abie bai amince ba"
"to ya za kuyi sai haƙuri "
" ya muka iya tunda bai amince ba " ta faɗa kamar zatayi kuka bed ɗin mom ta nufa ta kwanta, murmushi mom tayi " yanzu fa kina iya kuka "
" A'a mom ba kuka zanyi ba"
" ai nayi tunanin shi za kiyi, to wasa yake abie ɗin ku ya amince "
" dan Allah mom da gaske "
" A'a da ƙarya "
" sorry mom, farin ciki ne yasa nace haka, amma naji daɗi da abie ya amince " tana gama faɗa ta fice ta nufi parlor wurin su Aaimah, dariya ta fara yima Ameerah kafin ta sanar da su abie ya amince,ƙululun baƙin ciki kamar ya kashe Ameerah, saboda dariyar da Aairah ke yi mata.

Aaimah kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha da Aairah ta sanar da ita abie ya amince, haushi da takaici kuwa wurin Ameerah ba'a magana.

_Wannan kenan_

Lokacin da Ammy  su ka gama waya da abie,parlor ta fito wurin su fatima take sanar da fatima zuwan Aairah, fatima kamar tayi hauka dan daɗi da ma ta jima tana son ganin su har cewa take idan su ka samu hutu sai taje katsina ko dan taga waɗannan yan biyun na su ya dr, yau gashi burin ta na ganin su zai ciki har ma za su zauna tsawan wa su shekaru,taji daɗi sosai da wannan labari da Ammy ta sanar da ita Ammy na barin wurin ta ɗauki wayar ta ta kira Abdallah dan sake ji daga bakin shi, ƙara tabbatar mata yayi da sunan zuwa nan da three weeks.
"ya dr dan Allah su zo next week, wallahi na ƙosa na gan su "
"one week da three weeks ai duk ɗaya fatima, in dai da rai da lafiya za ki gansu har ma sai kin gaji "
"duk da haka dai ya dr"
"to ni dai babu ruwana hukuncin abie ne wannan "
"shikenan Allah ya kaimu, ka basu wayar to mu gaisa "
"sai dai na tura maki number Aairah ko ta Aaimah"
"kai ya dr, to naji ka tura man duka "
"to shikenan zan tura maki "
"yawwa ya dr nagode bye "
"Wait naga sai wani rawar ƙafa kike, karfa su zo ni ki share ni kuma dan saboda ke nasa abie ya amince za su zo dan nima na samu damar ganinki" ya faɗa yana ɗan murmushi, rufe ido fatima tayi ita a dole kunyar zancen shi taji
"kinyi shiru idan haka ne gara tun wuri na sani "
"haba ya dr dan Allah ka daina faɗar haka, kaima ka san babu abun da zan samu da zai ɗuke man hankali har na share ka "
"na sani, nima wasa nake maki, naga dai kina ta rawar ƙafa ne "
"na ƙosa na gansu ne"
"very soon zaki gan su "
"to shikenan, katuro man number"  to ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran, bayan kamar minti ɗaya sai ga number ya turo mata duk da ta Aairah da Aaimah,ko kiran shi tace taga number bata yi ba saboda zumuɗi, number Aairah tayi dialing, da sallama Aairah a bakinta tayi picking kiran, a hanzar ce fatima ta amsa mata sallamar tana faɗin
"sister ya kike, ya gida "
"lafiya lau, pls wake magana " Aairah ta faɗa, murmushi fatima tayi sannan tace " na san bazaki gane ni ba, fatima ƙanwar ya shazim abokin ya Abdallah"
"ooo Allah sarki, ya kike ya su Ammy "
"lafiya lau su ke, yanzu take faɗa man zaku zo lagos ke da Aaimah"
"Eh"
"dan Allah kuce ma abie ya barku ku zo next week ba dole sai nan da sati ukku ba pls "
abun mamaki ma ya ba Aairah ganin yarda fatima ke zumuɗin zuwan su duk da ba su san juna ba a zahiri, hakanan taji fatima ta kwanta mata arai ita ma taji ta ƙagu da taganta
" shikenan insh Allah zan roƙe shi ni da Aaimah "
"yawwa nagode sosai, ina Aaimah take?"
" tana wurin mom "
" ok dan Allah ki bata mugaisa harda mom ɗin "
" to shikenan, kashe idan naje wurin su sai na kiraki "
" to " fatima ta faɗa haɗi da kashe wayar.

Wani wawan tsaki feenah taja, dama tun da taji Ammy ta faɗin zuwan su Aairah taji ranta ya ɓaci hakanan taji ta tsane su duk da bata san su ba amma taji  bata ƙaunar su zo
" haba ya feenah miye abun tsaki kuma?"
" dole nayi tsaki, saboda ke shashasha ce baki san mutane ba amma dagaji za su zo sai wani zumuɗi kike "
" bangane bata san su ba, ke dai idan baki san su ba to kiyi shiru amma ita ta san su ko nima nan da kike gani na san su " sa'ada ta faɗa tana hararar feenah
"ƙannan uwarki ne su da zaki ce kin san su,kuma wallahi na kama ki zaki san ni kike harara"
" ba ƙannan uwata ba ne, amma ai su muslmai ne kuma muslmi ɗan uwan muslmi ne, to wai ma ina ruwanki idan sun zo ke dai ba a kanki za su zauna ba kuma ai dai inji nan ba gidan dady bane bare har sai kin zaɓi wanda zaizo kema kara ki akayi " sa'ada ta faɗa tana miƙewa tsaye dan ta san abun da zai biyo baya tsakanin ta da feenah ba mai kyauba ne, tashi feenah ita ma tayi ai tana gani haka ta kwasa da gudu sai ɗakin Ammy tana faɗin " Allah yasa idan su ka zo su koya maki hankali, tunda ta ƙamarki yi ma mutane wulaƙanci sai kace ma nan ɗin gidan ku ne "
"ai da kin tsaya inji uban da kike faɗa ma wannan maganganun " gwalo sa'ada tayi mata tana faɗin
"da karyeyyen hanun " ta faɗa tana langabar da hannun ta irin ciwannan taji  tana faɗin " wayyo Ammy wurgi ya shazim yayi da ni "
A harzuƙe feenah ta bi bayan ta, da gudu sa'ada ta shige ɗakin Ammy jikake garam ta banko ƙofa ta rufe da key, bubbuga ƙofar feenah ta shiga yi tana faɗin
"wallahi sai na ci ubanki na kamaki "
daga cikin ɗakin sa'ada tace
" ki kashe ni idan kin tashi "
" zaki san da ni kike magana feenah ta faɗa haɗi da barin bakin ƙofar, ta koma cikin parlor, samun fatima tayi tana   waya da mom da Aaimah, haushi kamar ya kashe feenah, ta shima tayi ta nufi bedroom ɗin ta da take kwana, wayarta ta ɗauka tayi dialing number Innah, tana picking ko sallama bata ti ba ta zayyane mata komai dan gane da zuwan su Aairah har da ƙari

_aikin banza sai kace Innar wani abu zata iya😏_

Baƙin ciki da takaici ne ya cika Innah ƙala bata ce ba ta kashe wayar, haushi kamar ya kashe feenah jin innah bata ce komai ba.

Shazim da ya dawo gida Ammy ke sanar da shi zuwan na su, Allah ya kawo su shine kawai abunda yace.

_dafta ban san wulaƙanci fah ehe_

A kwana a tashi babu wuya wurin ubangiji yau ya rage saura kwana biyu su Aairah su zo lagos, duk wani shiri da za suyi sun kammala, ranar da zasu tafi kawai su ke jira, Abdallah ne zai kai su, sai ya gama su komai a school sannan zai dawo.

Ameera sun koma Abuja tun last week, ta sha  kuka kamar mi bata yanda zata yi dole ta haƙura, taci ƙurin suyi school tare amma bai nufa ba.

Washe gari ranar da za su tafi har gida su ka je su ka yi ma dadi sallama, sannan su ka je gidan granny da gidan Aunty safiya, najma ma kamar ta haɗiye zuciya dan baƙin ciki za su tafi su barta, saboda ita dadyn ta a nan ya samar mata da school, sai da daddare sannan su ka koma gida..........

_WASHE GARI_

_SEASON TOW KENAN, MU HAƊU A SEASON TOW DAN JIN YARDA ZATA KAYA ZAMAM SU AAIRAH A LAGOS, GA FEENAH YAR BAƘIN CIKI_

_SHIN WANENE SU SHAZIM SUKA RIƘE MA KAYA YAKE MA SU BARA ZANA, YA MAGANAR AURAN SHAZIM DA FEENAH DUKA WANNAN AMSAR TANA CIKIN SEASON TOW_

_ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN DOCTOR SHAZIM SEASON ONE_

_ZAN ƊAN JE HUTU KAFIN NA FARA SEASON TOW_

_GA MAI SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN DOCTOR SHAZIM 300 NE BA YAWA_

_3169482544  MUKHTAR HADIZA FIRST BANK_

_SAI A TURA SHAIDAR BIYA TANA WANNA NUMBER 09132289761 KO 08133650574_

Masu cewa ban sa Account number to ga shinan na sa.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment