Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yan uwan shi, maijidda kuwa ita da su uwani da yaran su suna part ɗin hajiya zainab , ranar juma'a aka ɗaura auren Abubakar Nuraddeen Ahamad Sharani da amaryar shi Aisha  Abdulƙadir  murna wurin ango da amarya ba'a cewa komai da yamma Alhaji abdulƙadir da nuraddeen suka haɗa aisha da sadiq su kayi masu nasiha,sannan suka je wurin hajiya zainab,nasiha sosai tayi masu da fatan alkairi,  aisha na kuka ƙannan hajiya zainab suka yi mata rakiya gidan mijinta, ranar lahadi yan uwa da abokan arziƙi suka fara tafiya , ƴan kurfi kuma washe gari zasu tafi litinin kenan , da yamma maijidda tasa  aka kira mata sadiq ta sake mashi maganar Ibrahim, cemata sadiq yayi "innah baba ya hana, ina kuma tsoron abun da zai biyo baya idan nace dole sai Ibrahim ya tsaya"bal bale shi da masifa maijidda tayi,  wai bai son zumunci dan yaga Allah ya ɗaukaka shi shine zai fara ƙyamar ɗan uwan shi,abun yayi mugun bama sadiq mamaki, bai taɓa tuna nin maijidda zata ce mashi haka ba arayuwa, haƙuri kawai ya bata, washe gari da safe sadiq yaje gidan alhaji abdulƙadir domin gaisawa da su ya kuma  yima su nuraddeen rakiya saboda da safen zasu tafi, koda ya gaishe da nuraddeen bai san miya faru kawai nuraddeen ya rufe shi da faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba yana cewa "kenan ni ban isa na hana ka abu ka hanu ba ko "
haƙuri sadiq ya shiga bashi batare da yasan miya aikata ma mahaifin nashi ba, sai da zasu tafi halimatu ke bashi haƙuri haɗi da faɗa mashi abun da ya faru, wai ashe lokacin da ya bar ɗakin da maijidda ta sauka, fita tayi daga ɗakin taje har ɗakin hajiya zainab ta roƙe ta akan dan Allah tunda sadiq da aisha basu gidan yanzu za su ji duk ba daɗi mizai hana Ibrahim ya dawo gidan da zama, to shine hajiya zainab ta sami alhaji abdulƙadir da maganar shiku ya samu nuraddeen akan dan Allah ya bar mashi Ibrahim ɗin, to shine nuraddeen yayi tuna nin sadiq ne ya faɗama abdulƙadir ɗin shine ya rufe shi da faɗa, koda halimatu tagama faɗama sadiq bai ji daɗin abunda maijidda tayi ba yaso ace ta bari ya lallaɓa baban nasu harya amince, amma ta ɓata mashi komai gashi baban yayi fushi da shi, kafin su wuce sai da  sadiq ya sake bama nuraddeen haƙuri,ya haƙura amma akan da Ibrahim zasu tafi daga baya sai ya dawo amma ina abdulƙadir yaƙi amincewa , ba yanda nuraddeen ya iya dole ya bar Ibrahim, maijidda daɗi kamar ya kashe ta,  nuraddeen na lure da ita bai dai ce komai ba,sai da suka isa kurfi yayi mata tatas dan ya san ita zata sa sadiq duk shirin ta ne, nunawa tayi ko a jikin ta burinta dama Ibrahim  ya zauna a lagos to burinta ya cika komi zai ce bawai zai dame ta bane, watan  sadiq da aisha ɗaya  dayin aure suka wuce abuja aka bar Ibrahim a lagos saboda makaranta da ya ke zuwa, cikin ƙan ƙanin lokaci Ibrahim ya goge ya zama ɗan gayu,saboda ba ƙarmin kulawa yake samu daga wurin su hajiya zainab ba,sadiq watan su bakwai a abuja  ya nema aisha  admission ta fara zuwa makaranta, idan zai tafi aiki tare suke fita ya ajiyeta a makaranta ranar da take da lectures ɗin yamma kuma ya ɗauko ta, mota ya siya mata ranar da take ra'ayin driving da kanta sai taje da kanta ta dawo da kanta , akwana a tashi aisha har ta kai aji uku a jami'a matar magaji ta haihu ta haifi ɗa namiji  kyakyawan gaske sunan yaron mansoor lokacin Aisha tana ɗuke da ciki na tsawan wata biyar,  sosai take samun kulawa daga mijin ta da cikin ya isa haihuwa lokacin suna hutu zasu shiga aji huɗu, hakan ya sa sadiq ya ɗauki hutu wurin aiki suka tafi lagos dan ta haihu a chan, cikin yardar ubangiji da komawar su ba da jimawa ba Allah ya sauketa ta samu ɗa namiji kyakyawan gaske mai matuƙar kama da ita, murna wurin sadiq ba'a cewa komai, hakama iyayen aisha da ƴan kurfi sunyi matuƙar farin ciki, da sati ya zagayo, yaro ya ci sunan Alhaji Abdulƙadir   suna kiran shi da {shazim} malam yayi matuƙar farin ciki da wannan ta kwara da sadiq yayi mashi,haka ma aisha taji daɗi sosai,kulawa sosai take samu wurin ummy, da tayi arba'in suka tafi kurfi ita da sadiq,Ibrahim ya so su tafi tare da shi amma makaranta ta hana saboda yana shekarar ƙarshe a jami'a,  sun samu tarba ta musamman daga wurin maijidda haka ma magaji da nuraddeen   hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma sadiq ba, matar magaji kuwa komawa su kayi tamkar ƙawaye ita da aisha, yaron ta mansoor shekarar shi ɗaya da rabi a duniya, kafin su koma lagos Aisha  sai da ta zaga gidajen ƴan uwan sadiq, ta kuma je gidan uwani da halimatu, suna komawa lagos basu jima ba suka wuce abuja , haka rayuwa ta cigaba da tafiya Ibrahim ya gama makaranta, sadiq yace ya dawo abuja yayi masters,  shazim ya taso cikin kulawa da soyayyar iyayen shi da dangin shi musamman Ibrahim duk abunda ya siya zai ce na Shazim ne, haka ya taso cikin kulawa da gata,da shazim ya isa yaye lagos suka kai shi wurin ummy, har sai da yayi shekara ɗaya a lagos lokacin yayi wayau sosai, ya iya tafiya ga surutu, haka zaka same shi ya tasa hajiya zainab gaba da surutu abu kaɗan yace ummy { da yake shima haka yake kiran ta saboda yaji ammyn shi na kiran ta da haka}

*_WANNAN  KENAN_*


 ....  Ibrahim ya fara zuwa makaranta Aisha  kuma na shekarar ƙarshe, shazim nada shekara uku a duniya sadiq ya ajiye aiki ya kama kasuwanci gadan gadan riba sosai yake samu, cikin ƙanƙanin lokaci ya zama attajirin gaske ya buɗe  katafaren  company da yake sarrafa kayan masarufi musamman shinka fa, kasuwancin shi na ta haɓaka ,  ɗaura  Ibrahim yayi kan wasu harkokin kasuwancin yana kula mashi da su, gida ya gina mai girman gaske ya kuma biya ma baba, innah,  malam,  ummy makka , sai shi da aisha, farin ciki wurin su ba'a cewa komai ya sha adu'a wurin su, kafin ya tafi ya tare a sabon gidan da ya gina, da zasu tafi ya ce ma magaji ya dawo Abuja  da zama shida matar shi da  ƴaƴan shi ,   da ma gidan da ya gina yayi shine saboda su, magaji yayi godiya sosai ya kuma tattara komai nashi dake kurfi sun dawo abuja shi da  matar shi asiya, sunje sun sauke farali,  a abuja su ka sauka da ma ta nan suka tafi, sai da malam su kayi  sati shi da ummy sannan suka wuce lagos, baba kuwa da innah nan zasu zauna part ɗin su da ban, har da ibrahim da baiyi aure ba part ɗinsa da ban , innah sai nan nan take da sadiq ta ɗauki son duniya ta ɗaura mashi tun bai sakin jiki da kulawar da take nuna mashi har ya fara sakin jiki,  abun ba ƙaramin ba nuraddeen mamaki yake ba, yan da ta sauya. 

Shekarar shazim 5  sadiq ya sa shi makaranta shi da mansoor  aisha ta sake haihuwar ɗa namijin mai matuƙar kama da sadiq, sosai sadiq ya yi murna haɗi da gode ma Allah, ranar suna yaro yaci sunan baba watau nuraddeen suna kiran shi da { noraiz}  baba yaji daɗi,satin noraiz uku da haihuwa asiya ta haihu ita ma ɗa namiji sunan shi mahmud,  Ibrahim ya samu mata yayi aure sunan matar turai, yar kano ce amma iyayen ta anan abuja suke da zama, shekarar ta ɗaya ta haifi ɗa namiji mai suna luqman lokacin noraiz da mahmund nada shekara ɗaya da kusan rabi,  shazim shidda mansoor  bakwai faisala ukku ƙanin mansoor, wani abun mamaki tun da matar Ibrahim ta haihu innah ta ɗauki karan tsana ta ɗaurawa aisha da asiya  kamar sunyi mata wani laifi, duk da wannan chanji da take nuna masu hakan bai hana su kyautata mata ba, kuma kan su haɗe yake dan matar Ibrahim ba ruwanta hakama yaran su kansu haɗe yake ko wane lokaci suna tare da juna musamman shazim da mansoor dan ko school tare zaka gansu da ƙanin su faisal da yake ansa shi makaranta shi ma , noraiz ne dai da luqman sai mahmud  ba'a kai da sa su ba , sai daga baya aka sa noraiz , luqman da mahmud   makaranta, shazim da mansoor kullum sun part ɗin baba kakansu wani lokacin har da su noraiz kullum haka suke in basu part ɗin baba suna part ɗin papah { sadiq} ko hutu shazim zai je lagos tare suke zuwa shida su mansoor luqman ne dai bai taɓa zuwa ba.

_*WANNAN KENAN*_. 

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau daɗi gobe akasin haka
sadiq ganin duk aboka nan shi na siyasa ne ya shi samu baba da batun yana so ya shiga shiyasa ƙin amincewa baba yayi hakan yasa abokan sadiq su kayi zuga suka zo wurin baba dan su roƙe shi akan ya bar sadiq, ai kuwa faɗa sosai baba yayi ma sadiq ya ce kenan dama su suka hure mashi kunne ya ke son  shiga shiyasa,dole ta sa sadiq haƙura ganin baba yayi fushi sosai, lagos yaje ya sanar da malam abun da ke faruwa, hakan ya sa malam wanke ƙafa yazo har abuja wurin nuraddeen, tattaunawa suka yi malam kuma ya roƙe shi akan ya bar sadiq ɗin, ba dan hakan ya kwanta ma baba arai ba ya amince,sosai sadiq yaji daɗi, da  matakin ɗan majalissa ya fara ,cikin ikwan Allah ya samu,shekarar su uku da fara mulki ya ida ginin estate ɗin daya fara  opposite da gidan shi, suna gab da sauka daga mulki  da jam'iyar su zata tsai da  ɗan takara suka tsai da shi, ƙin amincewa yayi dan shi baya da burin yin muƙami mai girma irin wanna,matsa mashi suka yi ba dan ya so ba yace "to shikenan,  amma sai yayi shawara da iyayen shi, duk abun da suka ce da shi zaiyi amfani ", ko da ya samu malam da baba da maganar  cewa suka yi yayi haƙuri ya yi, ai abu ne mai kyau  insha Allah zasu taya shi da adu'a, yaji daɗin hakan da suka ce ya kuma samu ƙwarin gwiwa, cikin ikwan Allah ana zaɓe sadiq ya samu,daya ci zaɓe sai Ibrahim da magaji suka koma estate da zama,sadiq ya so  malam ya dawo abuja da zama lokacin daya zo yi mashi fatan alkairi daya ci zaɓe amma ƙiri ƙiri malam ya ƙi amincewa, baba ma da farko cewa yayi sadiq ya bar shi anan gidan shi amma sadiq ya ce a'a ya fi so ya zauna tare da shi yanda zai riƙa bashi shawara, sadiq ya fara mulkin shi cikin adalci mutane na jin daɗin mulkin shi,aiki ya ne ma ma Ibrahim da magaji dan tun dawowar shi abuja sadiq ya ne ma mashi admission ya jona karatu sai dai iya kar shi degree  saɓanin Ibrahim da ke da master's  ,business ɗin shi kuwa ya ɗaura wani aminin shi  daya ke da amana,  lokacin daya kusa gama zagayen farko na mulkin shi , Allah yayi ma nuraddeen rasuwa mutuwar da ta girgiza ahalin ga ba ɗaya musamman sadiq ya fi kowa fita hayyacin shi, sun shiga alhinin mutawar nuraddeen kamar mi, malam yaji mutawar aminin shi kamar mi, lokacin da aka yi  adu'ar bakwai maijidda tace zata koma estate da zama wurin su magaji bayan da sadiq bai yi da ita ba amma ta ƙi zama ko da takaba ta gama amma ina  ba dan ya so ba ya sa aka kaita, time ɗin da akayi arba'in ɗin nuraddeen matar Ibrahim ta sake  haihuwa ta samu ɗiya mace kyakyawa mai suna hawa'u innah kenan suna kiranta da feenah,innah taji daɗi da Ibrahim yayi mata ta kwara ai kuwa ta ɗauki son duniya ta ɗaurawa feenah,bayan haihuwar feenah da sati biyu asiya ma ta haihu, ita ma ɗiya mace ta haifa  mai suna kairiyya,   watan nuraddeen tara da rasuwa za'a sake  sabon zaɓe sadiq ya bar gidan gomnati  ya koma gidan shi inda ya fara zama, awannan zaman ana saura sati ɗaya zaɓe Allah yayi mashi rasuwa, ta dalilin haɗarin mota, sunje wani ƙyauye ne a hanyar su ta dawowa su kayi haɗari wasu a nan take suka mutu sadiq kuma sai da yayi jinyar kwana biyu sannan Allah yayi mashi rasuwa ,mutawar sadiq ta girgiza dan gin shi kamar mi, aisha ta shiga tashin hankali mara misltowa da rasuwar sadiq hakama ƴaƴan ta sunci kuka kamar ransu zai fita duk da bawani wayaune da su ba sosai har dama dama shazim, kusan zaucewa aisha tayi, malam ma ya shiga  alhini wanda ya fi na lokacin mutuwar nuraddeen , ummy taci kuka kamar mi dan ba ƙaramin son sadiq take ba tana mashi kallon babban ɗanta.

_*ALLAH SARKI NIMA NAJI MUTUWAR KA KAMAR NAI HAUKA ABBA ALLAH YA JIƘAN KA DA RAHAMA AMEEN*_.

A estate akayi zaman makokin shi har aka yi kwana bakwai,  laulayin ciki Aisha ta fara na tsawan wata biyu sai bayan rasuwar sadiq  cikin ya bayyana , ta sha kuka kamar ranta zai fita, tana tausa yin abun da zata hai fa zai taso batare da ya san waye mahaifin shi ba, ko da maijidda taji labarin cikin aisha baƙin ciki kamar ya kashe ta,  ta fara nuna ma aisha tsana da tsangwa ma, hakan ne ya sa aisha ta ce zata koma lagos da zama, amma si malam da ummy suka ce ta bari ta gama takaba sannan, haka ta haƙura har ta kammala ta kaba, amma da zata tafi sai Ibrahim da magaji suka roƙeta akan dan Allah ta zauna har sai ta haihu sannan   saita koma lagos ɗin, hakanan ta haƙura ta zauna ba dan ta so ba dan kwata kwata yanzu bata jin daɗin zama da innah, ta ware ta  su asiya kawai take  so su da ƴaƴan su ta ɗauki karan tsana ta ɗaurama su Shazim ba hali su shiga cikin ƴan uwan su ko su je part ɗin ta ta fara kyarar su kenan da hantarar su, ta kuma sa su mansoor tsanar su babu hali su raɓu da juna, tun abun bai damun Aisha  har ya koma yana damun ta, har ta kai da samun innah dan ta bata haƙuri ko tayi mata laifi ne batare da sanin ta ba , amma sai innah ta rufe ta da masifa wai tayi mata rashin kunya, haƙuri kawai aisha ta bata, lokaci ya shuɗe har cikin aisha ya shiga watan haihuwa, a lokacin ma ta so ta koma lagos ta haihu a chan amma ƙiri ƙiri innah ta ce bata isa ba sai dai ta tsaya ta haihu a nan in ya so daga baya bayan ta yaye abun da ta haifa sai ta tafi tabar masu ƴaƴan su, maganar innah ta girgiza Aisha  ba kaɗan ba tun tana boye ma malam da ummy irin zaman da suke yi ita da innah har ta kasa haƙuri ta kira ummy tana kuka ta zayyane mata duk abun da ke faruwa tun daga mutur sadiq har yan zu, abun yayi matuƙar ba ma ummy mamaki dan ita bata san halin innah ba kallon mutuniyar kirki take mata ashe ba haka take ba, ko da ta sanar da malam shima abun ya bashi mamaki dan bai taɓa tuna nin haka daga wurin ta ba, haƙuri suka bata akan tabi komi a sannu in sha Allah komi zai wuce kuma baza su bari a rabata da ƴaƴan ta ba, Ibrahim yana bata kulawa sosai , hakan ya sa ta kwantar da hankalin ta taciga da kula da ƴaƴan ta , shazim tun da ya lura  da innah bata son shi da mahaifiyar shi kuma su mansoor ma basa son su yanzu   sai kawai ya yanke shawarar fita harkar kowa da ke cikim estate ɗin , ko part ɗin su ya dai na zuwa, da tare su ke  tafiya makaranta dasu mansoor amma ganin yan da suke takura ma shi shi da  noraiz ya sa ya dai na tafiya tare da su, yasa ammy ta ba ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan makullin motar ta yana kai su, abun yayi matuƙar bata ran  innah, ta tasa aisha bala'i tana son raba zumunci, ta kuma amshe makullin motar daga hannun drivern,  ran shazim ya ɓaci da abun da innah tayi,  ai kuwa  har part ɗin ta yaje ya ɗauke key ɗin motar lokacin tana cikin toilet wanka su mansoor kuma na parlorn zaune  dama cikin drawer ta sa shi,innah na fitowa feenah ta faɗa mata shazim ya shigo mata ɗaki kuma ya ɗauki key,mamaki abun ya ba innah ba shiri ta fice sai part ɗin Aisha  tun daga bakin ƙofa ta fara masifa tana zage zage aisha na zaune kan kujera ita da mai aikin ta tana matsa mata ƙafafun ta dake ciwo  ta ji haya niyar innah, ta na shirin tashi innah ta shigo ta hau bala'i tana zagin ammy, haƙuri ammy ta shiga bata dan bata san mi tayi mata ba, suna nan sai ga shazim ya shigo innah na ganin shi ta shaƙo wuyan rigar shi tana faɗin

" ɓarawon banza ɓarawon wofi,bani key ɗin da ka ɗauko ɗaki na munafuki"

gaban ammy ne ya faɗin jin abun da innah tace, shazim kuwa cike da masifa ya ce

"wallahi ni ba ɓarawo bane, kuma key bazan ba da  ba tun da ba naki bane "

suman tsaye ammy tayi jin rashin kunyar da shazim ke ma innah, mamaki da tsoro ne ya kama innah jin abun da shazim ya ce mata, yaron da ko yatsa kasa mashi a baki bazai tauna ba amma shine yau yake faɗa mata magana cike da rashin kunya, katse mata tunani yayi ta hanyar figewa daga riƙwan da tayi mashi ya nufi up stairs ya haye, bin shi kawai tayi da kallo har ya ɓace ma ganin ta, ammy tace
"dan Allah kiyi haƙuri innah zan amshi key ɗin in maido maki"

fashe wa da kuka innah tayi tana faɗin

"munafuka nasan ke zaki zuga shi yayi man rashin kunya, kuma wallahi ki sani dani kike magana"

tana gama faɗar haka ta fice daga part ɗin.......... 🖊  

_Episode  52_53_

............ Innah na fita ammy ta wuce bedroom ɗin ta, noraiz ne ya shigo yana kuka, har zai nufi ɗakin ammy sai ya fasa saboda maganar shazim daya ji yana ce mashi"lafiya kai kuma kake kuka,  waya dake ka ?  " cikin muryar kuka noraiz ya ce "su  ya mansoor ne da luqman " balbale shi da masifa shazim yayi dan mi zai tsaya luqman ya dake shi bayan ƙanin shi ne, shiru noraiz yayi, tsaki shazim ya ja haɗi da cewa "suna ina? " noraiz ya bashi amsa da "part ɗin uncle Ibrahim  "    shazim bai ce komi ba ya kama hanyar fita daga part ɗin ya fice, yana fita part ɗin uncle Ibrahim ɗin ya nufa, luqman da feenah ka ɗai ya samu zaune a parlor suna kallo, bai yi wata wata ba ya haushi da duka sai da yayi mashi jina jina sannan ya kyale shi yana kuka,  feenah ce ta miƙe tana faɗin "ya shazim dan mi zaka dake shi" buge mata baki shazim yayi yana faɗin "rufe man baki koke ma na haɗa da ke " kuka ta kama yi tana faɗin Allah ya isa ban yafe ba kuma sai na faɗa ma dady da innah"

kwata kwata feenah bata da kunya koko alama, kuma hakan ya samo asali daga wurin innah saboda mugun son feenah take kamar mi, ita ta shagwaɓa ta kuma ta zuga ta akan dun wanda ya dake ta tace bata yafe ba idan bazata iya ramawa ba, hakan ya sa ta taso a sangarce ga rashin kunya iri iri feenah ta iya ta , abu ƙaɗan tace innah ko faɗa dadyn ta yayi mata tana kuku zata faɗa ma innah, ita kuma tai ta bala'i,saɓanin kairiyya da ba ruwanta, kuma tana son su noraiz dan kusan kullum tana part ɗin ammy,ita ba ruwan ta shiru shiru ce,   mari shazim ya   kaimata ta ruga da gudu tana kuka ta shige bedroom ɗin momyn ta,yazo fita yaci karo da mansoor da faisal zasu shigo part ɗin, cakumo wuyan rigar mansoor yayi, faɗa sosai ya kyaure tsakanin su har sai da momy {turai}  ta fito ta raba su,  mansoor na kuka saboda ciwan da shazim ya ji mashi, wuce wa shazim yayi zuwa part ɗin su, yana tura ƙofa yaci karo da ammy tsaye , "daga inah kake? " shine abun da ammy tace, shiru yayi bai bata amsa ba,jin yayi shiru ne yasa ta sake mashi tambayar,  shiru ya sake yi ,  saukar mari kawai yaji a kumatun shi, abun da ammy bata taɓayi mashi  ba, rufe shi tayi da faɗa sosai,tana gamawa ta juya,   yana dafe da kumatu yace "dan Allah ammy kiyi haƙuri " wuce wa tayi batare da ta kalli inda yake tsaye ba, bin ta yayi har ɗaki yana bata haƙuri sai da ƙyar tace taya fe mashi kuma ya ɗauko key ɗin daya ɗauko ɗakin innah ya kawo mata,  da to ya amsa haɗi da ficewa ya bar ɗakin, key ɗin ya ɗauko ya bata, ƙarar buɗe main  ƙofa sukaji da ƙarfi, sai kuma haya niya fita ammy tayi zuwa parlor, innah suka gani ruƙe da hannun feenah  su luqman na bayan ta tana ta zazzaga masifa,  uncle Ibrahim ne ke bata haƙuri yana faɗin

" dan Allah innah kiyi haƙuri"

"wlh ba zan haƙura ba, yan da ya dake su wlh sai na rama masu "

ammy ce tace "mike faruwa ne? "

tun kafin ya bata amsa innah tayi saurin cewa " munafuka annamimiya, kina iya cewa baki san mi wannan fitsararen ɗan naki yayi ba, bayan ke kika sa shi munafuka kawai "

muryar shazim suka ji yana cewa "gaskiya innah ki dai na ce ma ammy na munafuka dan ba munafuncin da tayi maki, dukan noraiz su kayi ni kuma na rama mashi, kuma wlh suka ƙara dukan shi sai nayi masu mafiyin haka tun da ba jakin su bane "

tsawa uncle Ibrahim ya daka mashi yana cewa " kai baka da hankali ne shazim, innar kake faɗa ma wannan kala man, kar na sake jin bakin ka "

innah tace "ai da ka barshi yayi man abun da uwar shi ta koya mashi, na san nan gaba har duka na tana iya sa shi tun da ba sona take ba"

uncle Ibrahim yace "kar Allah ya nuna mana hakan, dan Allah kiyi haƙuri ki koma part ɗin ki"

tasa ƙeyar su feenah tayi zuwa part ɗin ta tana tafiya tana zagin shazim,Aisha  tayi tsaye ta kasa ko motsi,

uncle Ibrahim ne yace "dan kiyi haƙuri da halin innah, karki sa abun a zuciyar ki kinga dai halin da kike ciki,ce mashi ta bakomi nagode haɗi da nufar part ɗin ta, faɗa tayi ma shazim har da duka, tana faɗin saboda zuwa makaranta yayi abokai marasa kunya shine zai zo gida yana ma manya rashin kunya, ta kuma gargaɗe shi kar ta sake jin yayi faɗa da wani cikin estate ɗin,
cemata yayi to, bawai dan ya dena ba, ya zame ma yaran gidan abun tsoro dan ko kallon da bai yi mashi  ba kayi mashi to zai hauka da duka ne ba ruwan shi, tun ammy na mashi faɗa har dai ta zuba mashi ido tana adu'a Allah ya shirya shi, dan komawa yayi mar kunyar ƙarfi da yaji har jira yake wani ya tsokane shi ko noraiz, dole tasa yaran tsoron shi.

Wata  rana wasu mutane suka zo da ga  hukumar efcc, har part ɗin ammy wai ana zargin marigayi Abubakar, da satar kuɗin gomnati,dan haka ammy ta tattaro duk wani takardun dukiyar sadiq ta basu tun daga kan filaye har zuwa na company,  abun yayi matuƙar bama ammy mamaki haka ma su uncle Ibrahim,ai kuwa kaca kaca ammy tayi masu ta kuma ce "babu wan da ya isa yasa ta bada koda allura ce daga cikin dukiyar   sadiq, mutumin da yake hukunta duk wan da

Please Login or Register in order to submit comment