Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"mu da yake bamu da galihu ko "
"ni ba haka nake nufi ba" hannun noraiz ya ja "wuce mu tafi" ficewa su kayi su fatima su ka bi bayan su zuwa part ɗin uncle Ahmad,suna shiga part ɗin mansoor su ka nufa, nocking su kayi, izinin shiga aka basu, tura ƙofar su kayi suka shiga zaune su ka samu Abdallah da mansoor shazim na kwance kan three seater idanuwan shi a rufe da a lama bacci yake, sallam su kayi, amsa masu sallamar su kayi "ina wuni ya dr " fatima tace,  gaishe da shi sa'ada tayi, amsa masu yayi cikin kulawa, sai sannan suka gaishe da mansoor ƙin amsawa yayi sai ma hararar su da yayi "ok sai yanzu kuka san da zamana ko " haɗa baki su kayi wurin faɗin
"a'a yaya "
"ba wani nan, ai na san zaman da nake da ku "
"a'a yaya "
"shikenan dai, mi aka dafa mana, naji tun da kuka shigo nake jin ƙamshi " fatima tace "abun daɗi, kuma na ya dr ne " zaro ido mansoor yayi "ai haka, abun ƴar wariyar launin fatace kenan dai " dariya fatima tayi
"wasa fa nake yaya, kaima kasan na ku ne" fatima sun shantake sai surutu su ke ganin boss na bacci,firar su kawai su ke, abun da basi sani ba idon shi biyu yana jin su banza kawai yayi da su, sai da yaji da gaske ba fita zasu yi ba sun samu wurin zama yasa shi buɗe ido yana faɗin "ke tashi ku ba mutane wuri " simi simi suka tashi su ka fice, mansoor ne yace "miye haka zaka wani kore su "
"an kore su ɗin " banza kawai mansoor yayi da shi bai sake cewa komi ba, tsaki Abdallah yaja yana faɗin "sai kace wani kafi rashin san surutu, zaka wani kore su " ta shi yayi ya nufi bedroom ɗin mansoor batare da yace masu ƙala ba, suma fita lamarin shi su kayi, mansoor ne yayi serving ɗin su basu jira fitowar shazim ba su ka kama cin abincin su, lokacin da zai fito har sun kusa kammalawa, zama yayi yana cema mansoor  "nima sai ka zuba man ko"
"in dai ni zan zuba maka sai dai kar kaci ɗan rainin hankali " ɗaukar plate shazim yayi yana zuba abinci ba tare da ya sake ce ma mansoor ɗin komi ba.
mansoor zamu sa ƙafar wando ɗaya da kai kai da Abdallah kun fa damu shazim tam 😏
fira mansoor da Abdallah su ke shazim kuma na cin abinci, da ya kammala fatima ya kira ta kwashe dishes ɗin,

sai da yamma liƙis Abdallah ya koma gidan uncle ahmad , fatima kamar tayi kuka, sai da yace mata zai dawo tukunnan ta haƙura, tare su ka tafi da shazim da mansoor a motar Abdallah, Abdallah ke driving mansoor na kusa da shi yayin da shazim ke baya, fira suke shazim na baya yana jin su amma bai sa masu baki ba har suka iso gidan uncle ahmad.......
Episode 30_31

............  Horn Abdallah yayi a bakin gate ɗin gidan, ta ƙaramar ƙofa mai gadin gidan ya leƙo ganin motar Abdallah yasa ya koma da sauri ya buɗe mashi gate, ciki ya shiga da motar ya nufi parking lot yayi parking.

Kai masha Allah gidan ya haɗu ba'a cewa  komi,  part biyu ne gidan,ɗaya yafi ɗaya girma,ba laifi gidan yana da girma,
fitowa su kayi suka nufi ƙaramin part ɗin,   ciki su ka shiga bakin su ɗauke da sallama, wata yar matashiyar budurwa su ka samu a parlor kwance kan sofa ta juya ma ƙofa baya, sallamar da suka yi ce ta sata tashi zaune haɗi da amsa masu  sallamar,kyakyawace fatar jikin ta  chocolate color,baza ta wuce shekara 19 zuwa 20 a duniya, jikin ta sanye da  english wear's riga da skirt,  cikin parlorn suka shiga, haɗi da samun wuri kan sofa suka zauna, gaishe da su wannan budurwar tayi, sannan tace ma   Abdallah " yaya jiya mu kai ta jiran ka ka dawo baka dawo ba "
"yanzu ai gashi na dawo ko "
"amma sai da yamma, wai ma ina kaje"
"to uwar masu iya surutu, ban sani ba wuce ki kira mana ummah"
"yaya nice ma mai surutun ko "
"zaki wuce ko sai ranki ya ɓaci " barin wurin tayi tana turo baki, wata ƙofa ta nufa, ba nocking kawai ta buɗe ƙofar ta shige bayan kamar minti biyu sai ga wata kyakyawar mace ta fito daga ɗakin jikin ta sanye da gown ta material, a ƙallah zata yi kimanin shekara 40 a duniya, ba fara bace amma bazaka kira ta da baƙa ba chocolate ce kamar ɗiyar ta, ƙara sowa tayi cikin parlorn tana faɗin "Abdallah daga bari naje na dawo sai kwana " murmushi Abdallah yayi ba tare da yace komi ba, gaishe da ita su shazim su kayi,fuska ɗauke da fara'a ta amsa tana faɗin " daga ziyara sai ku riƙe mana shi harda kwana "
mansoor ne yace " ai gashi nan mun dawo da shi "
"ai duk da haka " fira suke da matar cikin nishaɗin amma ban da shazim, dan shi yama ƙosa su tashi, tashi tayi tana faɗin "sai fira muke ba'a kawo maku abinci da ruwa ba " mansoor ne yace "a'a ba komi yanzu zamu wuce "
"a'a gaskiya sai kunci ko da snacks ne, bari na sa Ameera ta kawo maku " tana faɗa ta koma ɗakin da ta fito ɗazu,shazim yace "ba sai ta kawo ba A hashim tafiya zamu yi " rai a ɓace
Abdallah yace"wallahi baku isa ba kuna nan har sai uncle ya dawo " ganin ranshi ya ɓaci ne yasa mansoor cewa su jira ɗin, fasa tafiyar su kayi, Ameera ce ta shigo parlorn hannunta ɗauke da tray ruwa ne da lume, ajiye wa tayi a gaban su shazim, inda ta fito inda nake kyautata zatun kitchen ne chanta koma, sai gata ta fito hannunta ɗauke da snacks wata na biye da ita da bowl ɗin kayan marmari, a gaban su shazim ta sake ajiyewa, wacce suka fito tare ce ta gashe da su shazim, barin parlorn su kayi suka koma inda su ka fito, sai da Abdallah yayi da gaske sannan shazim yaci wani abu daga cikin abun sa aka kawo ma su, sun jima a gidan har sai da uncle Ahmad ya dawo suka gaisa, uncle ahmad yana matuƙar kama da abie sai dai abie ya fishi hasken fata,sun jima suna fira dashi, yanda ya sake masu kamar abokin su,da zasu tafi shida Abdallah su kayi nasu rakiya har parking lot.
lokacin da su ka koma estate  lokacin kusan ƙarfe goma da rabi na dare, kowa ma kwancin shi ya nufa, alawala yayi ya kabbara sallah,daya gama adu'a kwai yayi ya kwanta. 

Haka kwana ki su kai ta tafiya har
shazim sunyi tsawan sati ɗaya da kwana biyar  da zuwa abuja,a cikin kwana kin nan kunsan kullum sai Abdallah yazo wurin su ko su suje, fatima ma da sa'ada zuwan su gidan uncle Ahmad biyu, har lokacin su uncle ahmad basu sanar da shi kiran da suke mashi ba, shi kuma bai tambayi kowa ba ya dai zuba masu ido idan  har basu sanar da shiba, yayi alƙawarin bazai tambaye su ba zai haɗa kayan ahi ne kawai ya koma logas, ya gaji da zaman abuja, aikin shi ne kawai ke damun shi, shi da yazo da niyyar kwana biyar, ya kai wannan lokacin ne saboda Ammy, amma da ba dan haka ba da tuni ya daɗe da komawa,har ammy ya kira yace shi dai zai dawo, amma sai ta hana shi tace ta zauna har sai in sun sanar da shi kiran da suke mashi, ba dan yaso ba ya haƙura.  
kullum idan  mansoor zai tafi aiki tare suke tafiya.

kwance yake kan bed ringing ɗin wayar shi ne ya tashe shi,lalubo wayar, a hashim ne ke kira ,  picking call ɗin yayi  haɗi da yin sallama sannan ya ɗaura da cewa"lafiya kira da sassafe haka? " banajin mai a hashim ke cewa, na dai ga shazim yayi murmushi da alama a hashim ya bashi amsar da ta dace da maganar da yayi,sannan ya ce "kar ka damu very soon"  sun ɗan jima suna waya sannan suka yi sallama, tashi yayi ya nufi toilet, bayan kamar minti 5 sai gashi ya fito ƙugun shi ɗaure  da farin  towel,clothes set ɗin shi ya nufa cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin wani yadi fari da baƙi mai taushi da ɗaukar hankali,  gaban dressing mirror ya nufa  kwalbar turare ya ɗauka ya feshe jikin shi,wayar shi dake kan bed ya ɗauka sannan ya fice ya nufi hanyar fita tana zuba ƙamshi, part ɗin uncle ahmad ya nufa a bakin ƙofa yaci karo da mansoor, mansoor na ganin shi yace" dama wurin ka zani, naga har kusan 11 baka fito ba kana can kwance "ɗan ya tsine fuska yayi yana faɗin " wallahi kuwa abun da ban taɓa  yi ba  kenan, amma yau ban san ya akai ba "hannun shi mansoor ya ja yana faɗin "mushiga ciki kayi breakfast may be gajiyan jiya ne "ciki suka shiga mama da kairiyya suka samu a parlor gaishe da mama yayi kairiyya ta gaishe da shi mama na faɗin "ga breakfast ɗin ku chan kan dinning " tashi sukayi suka nufi dining ɗin, kairiyya  tayi saving ɗin su tana kammalawa ta dawo kan sofa, mahmud ne yashigo shi da noraiz, wurin su shazim suka nufa suka gaishe da su, suma suka zauna domin yin breakfast ɗin.
suna kammalawa shazim da mansoor suka fice daga part suka nufi na uncle Ibrahim.
zaune take kan sofa ta juya ma ƙofa baya sallamar su ce tasa ta juyowa, fuskar ta da fara'a ta nufe tana gaishe da su, mansoor ne ya amsa amma shazim ɗaure fuska yayi kamar an aiko masa da saƙon  mutuwa
"bro ana gaishe da kai "
"naji" shine kawai abun da yace,kuka ne ya ciyo feenah ta rasa mi tayi ma shazim yake wulaƙanta ta, ace ko gaisuwar ta baya iya am sawa,  juyawa tayi da sauri ta nufi bedroom ɗin ta kukan na neman kufce mata
"gaskiya baka kyautawa, narasa miya sa ka tsani feenah kwata kwata baka son ta, in ta gaishe ka baka son amsawa wai miye duk hakan "
"ka gama"fuska da alamun ɓacin rai mansoor yace
"ok ni kake cema nagama ko yayi kyau"
riƙo hannun shi yayi yana faɗin"sorry bro kai." bai ƙarasa maganar ba saboda fisge hannun shi da mansoor yayi yana faɗin "ra bu dani bana son jin komi daga gare ka" yana gama faɗa ya juya ya bi bayan feenah, ɗaga kafaɗa shazim yayi irin abun bai dame shi ba,sama ya nufa wurin uncle Ibrahim,yazo shiga kenan yaji yayi karo da mutum har sai da ya ɗan ja baya ,ɗagowa da kanshi yayi yana kallon luqman dake gaban shi tsaye  yana liliya goshin shi da alama yaji zafin karon da sukayi, kallon shazim yayi yana faɗin  "kayi hauka ne" tun kafin ya ƙarasa shazim ya ɗauke shi da wani mummunan mari har sai dai ya kusa faɗuwa, cikin azabar zafi ya ɗago yana faɗin "wannan wane irin zalunci ne azzalumi kawai mugu"sake wanka mashi mari shazim yayi har sai da ya duƙe kasa, amma duk da haka bai fasa ce mashi  azzalumi ba,shaƙo wiyan rigar shi shazim yayi haɗi da kai mashi duka a baki, wahalalliyar ƙara luqman ya saki dan ba ƙaramin zafi yaji na har bakin shi ya fashe,uncle Ibrahim ne da ya fito sai ga mansoor da feenah har da momy sun nufo sama  ta dalilin ƙarar da luqman ya saki,ganin yanda ya shaƙe mashi wuya ne yasa uncle Ibrahim cewa "shazim miye haka kashe shi zaka yi ne, wai ma miya haɗa ku ne, kake mashi wannan dukan"
cikin kukan wahala luqman yace" ba abun da  nayi mashi ya hau duka na, da yake azzalumi ne shi "wani sabon naushin  ya sake kai ma luqman a baki, cikin sauri uncle Ibrahim ya ƙaraso kusa da su dan tun da ya fito yana tsaye ne a bakin ƙofa, hannun shazim ya fize daga riƙwan da yayi ma luqman yana faɗin "shazim baka da hankali ne illata shi kake son yi ne?" ran shazim ne ya ɓaci da maganar uncle Ibrahim,  yasan cewa luqman bai da kunya kwata kwata kuma ya raina shi ya san dole sai da dalili zai mashi wannan dukan,amma da alama laifin shi yake gani,  ce mashi yayi"eh, tun da shi bashi da hankali, bai san ina ke mashi ciwo ba"
"shazim ni kake faɗa ma haka?"     banza yayi da uncle Ibrahim sai ma kama hanyar fita yayi,  riƙo shi mansoor yayi yana  faɗin "bakaji ana maka magana zaka fice "cikin ɓacin rai shazim ya ce "sakar man hannu na mansoor" ƙin sakar mashi hannu mansoor yayi,  ganin bazai sakar mai hannu bane yasa shi fizge hannun shi ya fice daga part ɗin bin bayan shi mansoor yayi yana ƙwala mashi kira ,da kallo uncle Ibrahim ya bi su har suka bar part ɗin ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli luqman yana faɗin"maganin ka kenan luqman, tun yaushe nake maka faɗa akan ka daina shiga harkar shi amma baka ji, yanzu da bama kusa Allah ka ɗai yasan irin illar dazai yi maka "cikin kuka luqman yace"yanzu dady goyan bayan shi kake, duk irin wannan dukan da ya yi man"
"dole na goyi bayan shi dan na san halinka da rashin kunya, kuma haka nan bazai rufe ka da duka ba batare da kayi mashi komi ba "cikin ɓacin rai luqman yace "tun da haka ne dady, wallahi sai na rama bazai dake ni a banza ba wallahi"juyawa yayi zai bar wurin da sauri uncle Ibrahim ya jawo hannun shi yayi yana faɗin "ashe baka da hankali ban sani ba,dallah wuce ciki sakarai kawai " ya faɗa haɗi da janshi suka shiga parlorn shi aka bar momy da feenah tsaye, feenah ce tace "wai miyasa ya shazim ya tsane mu ne, ji dukan da yayi ma ya luqman dan Allah" ɗan nisawa momy tayi sannan tace "idan har da laifin shazim to na innah yafi yawa dan ita ta haddasa komi, ita tasa luqman bai ganin shazim da mutunci"
"haba momy yaza kice haka,ba ruwan innah, dama chan ba son mu yake ba"
"nace hakan,duk ba ita ta haddasa komi ba tasa kuka tsane su kuke mashi rashin kunya,ke ma duka yaushe kika dai na raina shi,  dalla wuce ki bani wuri" wucewa feenah tayi tana turo baki ta nufi ƙofar fita zuwa part ɗin innah, a bedroom ta same ta mai aikin ta na shirya mata kaya a wardrobe, kallon mai aikin feenah tayi tana faɗin "ke tashi ki bamu wuri"ta shi talatu tayi ta fice, kallon feenah innah tayi tana faɗin "ke kuma lafiya kika korar man mai aiki? " zama tayi bakin bed ɗin tana cewa "tacika sa ido ne da gulmar tsiya"
"to aikuwa ke zaki ƙara sa man tun da har kika kore ta "ɗan ya tsine fuska feenah tayi tana faɗin "ai yanzu zan tashi sai ta zo ta ida maki"sannan ta ɗaura da cewa "innah kin san mi ya faru kuwa?"gyara zama innah tayi tana faɗin "a'a sai kin faɗa,mi ya faru"
"uhmm ya shazim ne yayi ma ya luqman dukan tsiya har da fasa mashi baki"zaro ido innah tayi haɗi da rike haɓa tana faɗin "wallahi bazai yiwu ba, shikuma sai luqman ɗin ya tsaya kamar wani sakarai har ya zubar mashi da jini"
"to kema innah in ban da abunki ina ya shazim ina ya  luqman "miƙewa innah tayi tana cewa "to wallahi bai daki banza, ka gaman azzalumi yaro"ficewa tayi daga bedroom ɗin tana masifa ta nufi part ɗin uncle Ibrahim, momy da ke zaune kan sofa tun daga waje ta fara jiyo masifar innah, sai gata ta shigo, tana ganin momy tace "ina Ibrahim ɗin yake? " sama momy ta nuna mata da hannu, fuuuu innah ta wuce zuwa sama tana ta zazzaga masifa,tana shiga parlorn ta samu uncle Ibrahim shi da mansoor dake kwance kan sofa, ko sallama babu ta faɗo tana faɗin "wallahi bazata saɓuba bindiga a ruwa,ina luqman ɗin yake"miƙewa luqman yayi ya nufe ta "dan mi zaka tsaya wannan yaron mara mutuncin  yayi maka duka irin haka sai kace jaki" uncle Ibrahim ne yace
"haba innah yaza kice haka,bayan kin san halin luqman da rashin kunya dole yana da laifi"
"hakama zaki ce yaron yayi mashi irin wannan dukan, amma kace shine mai gaskiya"
"ba wai na goyi bayan shi bane,  a'a nasan halin luqman ne da rashin kunya shine kawai , kuma kema nasan kinsan halin shi sosai" tsaki innah taja tana faɗin "shima ai ba kunyar bace da shi, kuma wallahi bai daki banza ba, idan da ya dake shi nayi shiru lokacin da yake yaro yanzu bazan yarda ba ace da girman shi ya dake shi ba in zuba ido ina kallo   idan kai bazaka ɗauki mataki ba ni zan ɗauka da kaina"
"yawwa innah shiyyasa nake ƙara sonki kin fi dady sona "
"karka damu zanyi maganin shi, fita ka bamu wuri zamuyi magana "da
to innah ya amsa sannan ya kama hanyar ficewa daga parlorn,  kallon uncle Ibrahim tayi sannan tace "kai kuma zauna "zama yayi kan sofa dake kallon wacce innah ke zaune..
  
Da yamma innah ta aiki feenah  kiran uncle ahmad, tana zuwa part ɗin ta samu su noraiz a parlor, yi tayi kamar bata san da su a parlorn ba ta nufi sama,faisal ne yace "lallai ma wannan yarin yar uncle ahmad na zaune a parlorn shi, mama na zuba mashi fura a cup ta shigo da sallama,amsa mata suka yi uncle ahmad na cewa"mamana zo ki zauna "ya faɗa haɗi da nuna mata kusa da shi, zuwa tayi kusa da shi ta zauna,"daga ina mamana? "
" daga wurin innah na ke , tace na kira mata kai "
"to, kice mata gani nan zuwa" da to feenah ta amsa haɗi da ficewa ta bar part ɗin ta koma na innah.

lokacin da suka fita daga part ɗin uncle Ibrahim part ɗin su ya nufa ya shiga bedroom ɗin shi,da ƙafa ya tura ƙofa da ƙarfi  har yaso da tsema mansoor hannun dake bayan shin, ja da baya mansoor yayi yana kallon ƙofar kamar shazim ɗin a wurin,tura ƙofar yayi ya shiga zaune ya gan shi bakin bed, ƙarasawa cikin yayi ya zauna kusa da shi yana faɗin "shazim miyasa ka dake shi, mi yayi maka"banza shazim yayi da shi har saida ya ƙara tambayar shi, still banza yayi da shi ran mansoor ne ya ɓaci, cikin masifa yake ce ma shazim "wai bakaji ina maka maganane, ko nima shashasha ka ɗauke ni ban sani ba"
ɗan nisawa shazim yayi, sannan yace"dole nayi banza da kai mana"
"ok haka kace koh "
"eh" abun yayi matuƙar ɗaure ma mansoor kai, cikin lallashi ya ce"kayi haƙuri nasan kana ganin kamar na goyi bayan luqman ne"shiru shazim yayi kamar ba da shi mansoor yake ba
"haba shazim na san kana jina"
"ina jinka mana" haƙuri mansoor ya shiga ba sai da ƙyar ya sa mu ya shawo kansa har ya dai na fushin da ya ke.

innah da feenah ne zaune a parlor, feenah ta kwanta tana daddan wayar ta, innah kuma na zaune ta ƙurama tv ido, sallama su  uncle ahmad su ka  yi haɗi da  shigowa, amsa ma su  sallamar innah tayi, wuri suka samu su ka zauna, uncle ahmad yace "innah gani feena tace kina kira na, Allah dai yasa lafiya "
"lafiya lau " innah ta faɗa haɗi da kallon feenah tace "takwara tashi ki bamu wuri " da to feenah ta amsa haɗi da miƙewa ta fita,
laɓewa tayi a  bayan ƙofar part ɗin innah, maganar da su innah ke yi take saurare  sai sakin  murmushi take, alamar buɗe ƙofa taji  za'a fito taji, hakan ya sa da gudu tabar bakin ƙofar ta ɓoye bayan part ɗin, uncle ahmad ne da uncle Ibrahim su ka fito daga part, tsayawa tayi har sai da taga shun nufi part ɗin uncle Ahmad sannan ta nufi part ɗin innah da sauri, a bedroom ta samu innah da waya kare a kunnen ta, zama tayi tsakiyyar bed ɗin innah tana faɗin "dan Allah innah kiyi sauri ki gama wayar nan pls"
da ƙuwa innah tayi mata, dariya feenah, ganin wayar innah ba mai ƙarewa ba ce yasa ta kwanciya kan bed ɗin sai sakin murmushi take kamar wacce aka yima albishir da gidan aljanna, innah ta ɗan ɗauki lokaci tana waya,lokacin da ta kammala, zama tayi ita ma kan bed ɗin "ke kuma lafiya kika zo zaki ta kura man " ta shi feenah tayi tana ɗan ya tsine fuska tace " dama nazo ne naji ya kukayi da su dady "
riƙe haɓ innah tayi tana faɗin "sannu uwata, to ban sani ba" murmushi feenah tayi tana faɗin "ai naji komi kuka ce " ɗan zaro ido innah tayi tace "dana ce ki fita  kenan laɓewa ki kayi kina sauraron mi muka ce "
"a'a ai ba duka naji abun da kuke cewa ba "
"ƙarya kike kinji komi"
"Allah a'a, yau she uncle ahmad yace su Aunty uwani zasu zo "
"ban sani ba, tashi ki bani wuri "
"dan Allah innah ki faɗa man " innah tace "naƙi in faɗa" roƙonta feenah ta shigayi akan ta faɗa mata yau she zasu zo, amma ƙiri ƙiri innah ta ƙi faɗa mata.

✨SHAZIM✨

Kayan shi ya hau haɗawa dan yayi alƙawarin sai ya bar abuja gobe da izinin ubangiji, ya gaji da zaman jiran jin kiran da su ke mashi, shiyyasa kawai ya yanke shawarar tafi gobe  ko da shi kaɗai ne ban da su fatima, inyaso daga baya sun dawo, yana cikin haɗa kayan mansoor ya shigo bedroom ɗin, turus ya tsaya yana kallon shazim dake ta faman haɗa kaya, yi yayi kamar ma bai ga shigowar mansoor ba yaci gaba da abun da yake matsowa mansoor yayi kusa da haɗi da dafa kafaɗar shi yace "wai shazim kana nufin har yanzu baka haƙura ba" ba tare da ya kalli mansoor ba yace
"wa yace maka fushi nake  "
"to idan ba fushi kake ba, miye na wani haɗa kaya, dan nasan halinka kana iya cewa lagos zaka koma"
"faɗi kake ana jinka "
"haba shazim miye abun fushi a nan"
"wai dan Allah wa yace maka fushi nake, kawai ina son na koma ne saboda aiki na da baro,  luqman har ya kai matsayin da zai ɓata man rai ne na koma lagos "  ɗan ajiyar zuciya mansoor ya sauke "to shikenan, amma ka bari su abbah su ce ka tafi ko"
"mansoor baza ka gane bane, aikina fa na baro tsawan sati ɗaya da wani abu haba "
"haka ne shazim, amma duk da haka ya kamata ka jira kaji mi zasu ce "
"ai ba tafiya zan yi ba batare da na sanar da su ba, zan faɗa masu in son in tafi gobe "
"to shikenan "mansoor yace, kama mashi yayi ya haɗa duk wani kayan shi da ya zo da su, bayan sun gama masallaci su ka nufa su kayi sallar magrib har da isha daga nan  part ɗin uncle Ahmad su kaje, dinner su kayi bayan sun kammala ne shazim ya samu uncle ahmad har part ɗin shi ya sanar da shi yana so zai koma lagos gobe, ko da ya faɗa mashi cewa yayi ya bari sai nan da ranar lahadi, saboda family meeting da za su yi ranar asabar, ba dan ya so ba ya haƙura, part ɗin su ya koma kwata kwata baiji daɗin hana shi tafiya da uncle Ahmad yayi ba kuma, ammy ya kira ya sanar da ita, ce mashi tayi yayi haƙuri ya jira, ko ba komi zaiga ƴan uwanshi da ya daɗe bai gani ba dama waɗan da bai san su ba, dan bashi da yanda zai yi ne yasa ya haƙura, baya farin ciki da wannan family meeting ɗi.

✨Ammy ✨

kwance take kan gadon ummy, gama wayar su kenan da shazim ta kwanta, tunda su shazim suka tafi abuja kullum tana gidan malam, wata ranar ma a nan take kwana, yau ma anan zata kwana, ummy ce ta shigo ɗaki da sallama, amsa mata sallamar ammy tayi, bakin bed ummy ta zauna tana wash,

Please Login or Register in order to submit comment