Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gani ai"
"ba abun da zaka gani sai alkairi, dan Allah muma bar wannan zancen"
"za'a yi shine wata rana "
"naji koma yaushe za'ayi shi" kai kawai mansoor ya girgiza yana murmushi ba tare da yace komi ba, sun ɗan jima suna fira daga bisani mansoor yayi mashi sallam ya fice.
tashi shima yayi ya nufi bedroom ɗin sa, toilet ya shiga ya ɗauro alwala
yayi shafa'i da wutiri yana gamawa ya nufi bed ɗin sa bayan ya kashe bulbs ɗin ɗakin hada bedside lamp, wayar shi da ya ajiye kan bedside drawer ce ta fara ringing , hannu yasa ya jawo wayar yana duba mai kiran shi unknown number ce, tsaki yaja haɗi da rejecting,yana rejecting wani kiran ya sake shigowa "wai waye wannan zai ta kura man ne "ya faɗa haɗi da sake rejecting kiran, sai ga message ya shigo buɗe message ɗin yayi yana karanta wa, yana kammala karantawa , tsaki ya sake ja, kashe wayar yayi baki ɗaya, blanket yaja ya rufe jikinshi baki ɗaya har kai

washe gari weekend

Momy ce da su sa'ada a kitchen suna haɗa breakfast feenah ta shigo jikinta sanye da pajamas masu santsi white color, sun bi shape ɗin jinkata kanta sanye da black ɗin hula, hugging ɗin momy tayi ta baya "inakwan momy "
"lafiya lau, kin tashi kenan? "
fatima tace
"ina kwna aunty feenah "
banza tayi da fatima har sai da momy tace baki ji ana gaishe da ke ne
"naji "
"ok amsawar ce baki iyawa "
kallon fatima feenah tayi tana faɗin
"lafiya " tsaki momy ta ja haɗi da mai da kanta kan abun da take, fatima ma nunawa tayi ko ajikinta abun da feenah tayi mata, abu yayi matuƙar ɓata ran sa'ada kasa daurewa tayi har sai da tace "gaskiya aunty feenah abun da kike baki kyautawa "
"ni kike gaya ma haka"
momy tace "ai gskiya ta faɗi" jan hannun fatima sa'ada tayi sai hura hanci take tace " zu mu fita parlor "
"a'a bari mugama aikin "
"kizo kawai mu tafi " da hararar feenah ta raka sa'ada "zan kamaki ne yarin ya, zaki san wa kike hura ma hanci"
kallon momy tayi tana faɗin
"mi kike dafawa ne momy?"
"to acici bansani ba "
"momy dan Allah ki dai na ceman acici"
"bazan dai na ba " bubbuga ƙafa ta shiga yi cike da shagwaɓa, luqman shigowar shi kenan kitchen ɗi yaga feenah na momy shagwaɓa , daga shi sai boxer black color, mangare mata kai yayi yan faɗin"sakaryara banza ji kayan dake jikin ki, ko kunya ba kiji, ko  aliyu bazai yi  abun da kike ba "
"ina ruwan ka dani da zaka dake ni mugu kawai, kai bakaga kayan dake jikin ka ba sai ni azzalumi "
"ke dan ubanki ni kike faɗama haka"
"eh an faɗa maka "
duka yazo kai mata da gudu ta ɓoye bayan momy, ture ta momy tayi tana faɗin" matsa ki bani wuri mara kunyar banza, kai kuma fice ka bani wuri "
"haba momy yaza kice haka, rashin kunya take man fa kuma ji kayan dake jikinta "
"fice nace ka bani wuri kai bakaga kayan dake jikin na ka bane, ko kunya baka ji da ƙannan ka kake irin wannan shigar kana yawo cikin gida" gwalo feenah tayi mashi
"wallahi zan kama ki ne "yana faɗa ya wuce kamar zai tashi sama, kallon feenah momy tayi tana faɗin "kema wuce kije ki canza waɗannan kayan tun kafin ranki ya yi mummunan ɓaci"
"haba momy, miye aibun wannan kayan dan Allah "
"ki fice nace "
"dan Allah momy kiyi haƙuri "banza momy tayi da ita, kama ma momy tayi suka kammala breakfast ɗin,mai aikin momy ce ta shigo ta kwashe flaks ta kai dinning, dawo wa tayi tana faɗin"momy ina na yallabai shazim yake "
"gashinan " momy ta faɗa haɗi da miƙama mai aikin, charab feenah ta amshe flaks ɗin daga hannun momy tana faɗin "jeki kawai zan kai masa"
"A'a hajiya da kin kawo na kai masa"
"nace kije zan kai masa"da to mai aikin ta amsa haɗi da ficewa ta bar kitchen ɗin, fita itama feenah tayi tana faɗin "momy bari na kai masa na dawo" bata jira mi momy zatace ba kawai ta fice.

kwance yake a bedroom ɗin sa , cikin bacci yaji ana nocking ƙofar bedroom ɗin sa, farkawa yayi batare da ya motsa ba ya dai buɗe idon shi, sake nocking ɗin kofar aka yi, ta shi yayi ya nufi ƙofar ya buɗe, feenah ce tsaye , kallon sama da ƙasa ya sahiga binta da shi, ganin kallon da yake mata ne ya sata duƙar da kai "inakwan ya shazim "bai amsa mata gaisuwar ba sai cewa yayi"mi ya kawo ki part ɗi na?"
"yaya dama momyce tace na kawo maka breakfast " juyawa yayi yana faɗin
"ok kina iya ajiyewa kan dinning "
"haba ya shazim, dan Allah wai mi nayi maka a rayuwa ne kake wulaƙan ta ni, ko gaisuwa ta baka amsawa"
shigewa yayi cikin bedroom ɗin batare da ya bata amsa tambayar da tayi mashi ba, kamar ta fashe da kuka saboda tsabar baƙinci, tarasa mi tayi ma shazim ya tsane ta a duniyar nan kwata kwata baya ƙaunar ta ya tsane ta, parlor ta koma kan dinning ta ajiye mashi haɗi da ficewa tana sharar ƙwalla, tana shiga part ɗin su ɗakinta ta nufa, kan bed ta faɗa, sai a lokacin ta fashe da kuka.

wanka yayi sannan ya fice ba tare da ya zuwa part ɗin uncle ahmad,sai da ya gaishe da mama sannan ya wuce sama wurin uncle ahmad,gaisawa suka gaisa ya nufi bedroom ɗin mansoor,tura ƙofar yayi bakin shi ɗauke da sallama, zaune yake yana aiki cikin laptop , ɗago da kan shi yana kallon shi "ai nayi tunanin sai na zo tuk zaka tashi? "
"ai da kazo ɗin "
"kunyi waya da a hashim kuwa? "girgiza mashi kai shazim yayi alamar a'a "ya kirani ɗazu yake ce man ya kira ka bai samu ba"
"na kashe wayata ne da zanyi bacci may be ya kira ya ji akashe"
"to ba mamki, sai ka kira shi"
ok kawai yace, wayar shi ya jawo yayi dialing number kairiyya, tana picking yace "ki kawo man breakfast part ɗin mansoor "yana gama faɗa yayi rejecting ba tare da ya tsaya yaji mi kairiyya zata ce ba, kallon shi mansoor yayi yana faɗin "ɗazu fa da su fatima suka shigo mama tace su zo su kaimaka breakfast suka ce sun baro feenah zata kai maka, bata kai maka ba? "
"ta kai"
"to mi yasa ba ka ci ba?"
"saboda bana jin yunwa lokacin "
"ba ka jin yunwa ko ko dai bazaka ci ba saboda ita ta kawo, wai mi yasa kake haka ne shazim "
"dan Allah ka rabu dani, bana ji yunwa ne lokacin, yanzu kuma ina ji shine kawai"
girgiza kai kawai mansoor yayi ba tare da yace komi ba ya mai da kan shi kan aikin da yake, nocking ɗin kofar aka yi, ba da izinin shiga mansoor yayi, kairiyya ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama hannun ta riƙe da tray, amsa mata sallama suka yi, ƙasa ta ajiye tray ta jawo center table ta ajiye gaban shazim tana faɗin "ina kwana ya shazim " da lafiya lau ya amsa mata, tray ta ɗaura kan table ɗin tayi serving ɗin shi,thanks yace haɗi da ɗaukar spoon ya fara cin abincin, ficewa tayi daga ɗakin, a hankali yake cin soyayen arish kamar baya son ci,sai da yaja time kafin ya kammala, wayar shi dake gefan shi ce ta fara ringing, ɗaukar wayar yayi yana duba mai kiran, ammy ce, picking yayi haɗi da sallama yace,om the other hand ammy ta amsa mashi sallamar tana faɗin "mutanen abuja "
shafa sumar kanshi yayi yana faɗin "ina kwana ammy"
"lafiya lau, ya  uncles ɗinka da innah "
"suna nan lafiya "
"ina gaishe da su, ina auta ta na kira  wayar ta bata ɗauka ba "
"yanzu haka ta jefata wani wuri "
"to idan ka ganta kace ta kirani"da to ya amsa yana faɗin "ammy ga mansoor zaku gaisa "ya faɗa haɗi da miƙama mansoor ɗin wayar, amsa yayi yan kara wayar a kunnen shi, gaisawa su kayi ammy na faɗin "mansoor kayi mana hijira koh "
"a'a ammy aikine ke riƙe ni"
"dama ku ai baku da wani excuse sai na aiki, yaushe rabon ka da zuwa lagod"
"insha Allah ina nan zuwa "
"to Allah ya yarda, ka gaishe man da su baban ka"
"za su ji insha Allah "
"to nagode "ammy ta faɗa haɗi da yin rejecting, miƙama shazim wayar yayi, amsa yayi yan dialing number, malam   ringing ɗaya biyu malam yayi picking, gaishe da shi shazim yayi, cikin kulawa ya amsa mashi yana tambayar ya abuja, sun ɗan jima suna magana daga bisani suka yi sallama, majeed ya kira amma tana ringing ba'a ɗauka ba, mai da akalar kiran yayi kan a hashim, shima tana ringing ba ai picking ba, ajiye wayar yayi kusa da shi, fira suke shiga yi shi  da mansoor jefi jefi, har lokacin sallar zuhur yayi, ta shi suka yi suka ɗauro alwala suka  fice a main parlor suka ci karo da kairiyya ta fito daga kitchen mansoor ne yace ta shiga part ɗin shi ta kwaso kayan breakfast ɗin da takai ma shazim da to ta amsa haɗi da nufar part ɗin sa, ficewa suka yi zuwa masallaci, da aka gama sallah mansoor yace su shiga part ɗin innah, da sallama suka shiga part ɗin bakowa sai mai akin innah da ta fito daga kitchen jjn ana sallama, amsa masu sallamar tayi tana gaishe su haɗi da cewa, innahr ta shiga sallah yanzu, ok mansoor yace wuri suka samu kam sofa suka zauna, shazim wayar shi da ke cikin aljihu ya ciro yana ɗan daddana ta, fitowa innah tayi hannun ta riƙe da ɗan kwalinta kanta duk furfura an mata kitson zane guda shidda da gake tana da suma ba laifi, kallon su tayi tan riƙe haɓa "ku kuma daga ina da wannan ranar" mansoor yace "ina wuni innah " lafiya lau ta amsa, kallon shazim dake ta aiki dan gwala waya innah tayi tana cewa "shi kuma wanccan ya fi ƙarfin ya gaishe ni ne ko mi"ɗan taɓa shi mansoor yayi "ana magana"
ɗago da kanshi yayi yan kallon mansoor yace "ni wai "wani kallon raini wayau mansoor yayi mashi jin tambayar da hake mashi bayan yasan tun da innah ta shigo ya san da shigowar ta, innah ce tace "a'a ba kai ba mu ɗan rainin hankali " murmushi shazim yayi haɗi dacewa "anwuni lafiya, ai ban san kin fito ba ranki ya daɗe "tsaki innah ta ja tana faɗin "da ban wuni ba zaka ganni haka ne "
d murmushi a fuskar shi yace"ai ban sani ba "
"ai kin banza "shine kawai abun da innah tace, basu wani jima ba suka fice daga part ɗin, da harara innah ta raka su harsuka fice, parking lot suka nufa, motar Shazim suka shiga, estate ɗin suka bari

✨KATSINA ✨

zaune suke kan sofa part ɗin abie,jinkin sanye da riga da skirt na material  Aairah tace
"abie wai yaushe  zamu tafi ne"
"yayan ku zaku tambaya"
"yaya fa abie "
"eh,  shi zai kaiku  "
"amma dai baza mu wuce gobe ba ko,  tunjiya mun gama shirya kayan mu "
"to wannan ne ban sani ba, idan   ya dawo sai ku tunbaye  shi "
"to abie "
wayar abie ce ta fara ringing, miƙa masa Aaimah tayi tana faɗin uncle mustafa ne, amsa abie yayi yana picking, ficewa su kayi zuwa bedroom ɗin a kan bed suka ya da zango, Aaimah tace "Allah ya sa ya ce gobe zamu  tafi "
"ammen Aaimah , wallahi na gaji da zaman gidan,  ko ba komi zaka ga wurare kala da ban da ban "
"Allah dai yasa yace goben "
Aairah tace
"to ameen,harna ƙosa na ganni a can nasan zamu sha ya wo da Ameera, bari na kirata ma"
Aaimah tace
"eh ki kira ta "
wayar ta ta ɗauko tayi dialing number Ameera, ringing ɗaya ta ɗauka tana faɗin sister wai yaushe zaku zo, abba yace yau amma gashi har dare baku zo ba"
Aaimah tace"ke ko sallama babu "
"bazaki gane bane na ƙosa na ganku ne, yaushe rabon da na ganku"
"sai ya abdallah ya dawo shi zai kawo mu ne"
"aikuwa kiran shi zanyi ince dan Allah ya kawo ku gobe"
nan sukai ta labari kan school, har time ɗin sallar asr yayi, alawala suka yi suka gabatar da sallar suna nan zaune kan carpet mom ta shigo jikinta sanye da gown ta shadda white color anmata kwalli da black ɗin net, hannun ta riƙe da hijab da jaka da alama fita zata yi, gaishe da ita suka yi Aairah na faɗin"mom jar kin shirya"
"eh na shirya, ku tashi kuje  kitchen baaba larai na can tana aiki ku kama mata "
"to mom yau she zaki dawo "
"sai dare gaskiya, dan daga gidan granny zan shiga gidan safiya, sai dai dare"
Aairah tace "da na san zaki can da tun ɗazo muka shirya muka bi ki "
"A'a ko da ku shirya bazan je ko ina da ku ba"
"saboda mi mom "
"koma saboda mi ku bari wani lokacin kun tafi "hanyar fita mom ta kama tana faɗin "ku taso kuje ku kama mata aikin "da to suka amsa suna tashi suka bi bayan ta, har compound suka rakata abie suka samu tsaye jikin mota yana jiran mom, tare zasu fita zai ajiye ta gidan granny shi kuma zai wuce gidan dadi,  a dawo lafiya suka yi masu sannan suka koma ciki, kitchen suka nufa wurin baaba larai, kama mata aikin suka yi suna ɗan fira, sun ɗan jima suna aiki sai gaba da magrib suka kammala, cema baaba larai su kai ta tafi kawai zasu gyara kitchen ɗin da jera abinci kan dinning, da to baaba larai ta amsa haɗi da ficewa ta nufi ɗakin t, Aairah ta kaima su bala na su dinner ɗin Aaimah kuma ta jera kan dinning, sai da suka tabbatar sun kammala duk wani abu da ya dace sannan suka nufi ɗakin su domin yin sallah, bayan sun gama sallah parlor suka dawo zama suka yi suna kallo,har akayi sallar isha, ɗaki suka koma domin gabatar da sallar, sai bayan sallar isha mom da abie suka dawo, dinner su kayi, bayan sun kammala su Aairah suka nufi ɗaki domin bacci .......


Episode 26_27

'''''''''''''''Wayar Aairah ce ta fara ringing, Aaimah cewa tayi "to ni sai da safe, dan nasan indai ya mus'af ne to ke kam ba yanzu ba,  duba mai kiran tayi, mus'af ne picking tayi fuskarta ɗauke da murmushi  tace "hubby barka da dare "
"barkan ki dai my love, ya gida "
"lafiya lau "cikin sauƙin soyayya suke wayar, anan mus'af yake sanar da ita next week  zai wuce uk (  can  ya kuma da  karatun ) , Aairah kamar tayi kuka dan taso ace suna ƙasa guda da shi,  bata son yayi mata nisa, ta dai yi mashi fatan alkairi sun ɗan jima suna waya daga bisani suka yi sallama.

✨SHAZIM✨

tsaye ya ke bakin window ya riƙe curtain  (labule)   yana waya da a hashim, fuskar shi  a sake suke fira, a hashim na cewa "saboda mansoor ne kawai zan shigo gobe amma da dan kai ne bazan zo ba "
"to ko yanzun ma kakar ka shigo tun da ina nan"
"kai dai kawai saboda mansoor "
"ai da kayi zaman ka "
sun ɗan ɗauki tsawan lokaci suna fira sannan su kayi sallama,ya juya kenan zai bar bakin window  ya hangi wasu manyan truck's guda ukku suna shigowa  cikin estate ɗin da alama  ta ƙaramin gate suka shigo,mamaki ne ya kama shi,waɗannan  truck's daga ina kuma minene suka ɗauko,  ya jima tsaye yana kallon truck's ɗin har suka yi parking a bakin  babban store ɗin estate ɗin, mutum uku uku ne su ka fito daga cikin kowace truck, bayan truck ɗin da ke gaba suka nufa, mutum biyu ne suka buɗe truck ɗin suka shiga miƙoma sauran wasu manyan kwalaye suna shiga da shi cikin store ɗin,  barin bakin window yayi       ya nufi toilet ya ɗauro alwala, sallah ya gabatar ko da ya gama sallah ya jima zaune kan carpet  bai ta shi ba, tunani ya shiga yi game da kwalayen da yaga masu truck ɗin na shiga da su cikin store,shin kwalin minene kuma na waye,  ya jima a zaune  har sai da ya fara jin  bacci sannan ya ta shi ya kashe light ɗin ɗakin ya  nufi bed  ya kwanta, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awan gaba da shi.
washe gari kamar jiya feenah ta kawo ma shazim breakfast kamar yan da ya tsallake jiya baici ba haka ma yau baici ba ya nufi part ɗin uncle Ahmad a can yayi breakfast tare da mansoor,fita su kayi shi da mansoor.

✨KATSINA✨

......... zaune su ke kan dinning suna breakfast, kallon abie Aaimah tayi tana faɗin "abie dan Allah idan zaka je gidan dadi ka tafi da mu"
"safiya ce yanzu ku bari sai da yamma sai kuje "
Aairah tace
"dan Allah abie, muna so ne muyi mata wuni "girgiza kai mom tayi tana faɗin "ku shikenan tun aka ce ba school daga nan ƙafa fuwan ku suka dai na zama wuri ɗaya "
"ba haka bane mom mun jima ba muje gidan ba ne "
"ba ma kunjima baku je ba, ina tunanin ko ranar friday kuje gidan" Aaimah tace "dan Allah dai mom "abie ne yace
"kuyi sauri ku shirya "
haɗa baki sukayi wurin cewa "yawwa abie  mungode "da sauri suka bar dinning area suka nufi bedroom ɗin su.

abie ne a parlor tsaye yana  jiran su Aairah , mom ce ke sau kowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya black color, wurin abie ta nufo tana faɗin "ba su fito ba ko "
"eh kinsan su da shiririta, duk ta ƙare tafiya zanyi idan ya so daga baya mudi ya kai su"
"afuwan abie ga mu nan" cikin sauri suke taka stairs case ɗin, sanye su ke da hijab har ƙasa onion color ,ƙara so wa su kayi, kallon mom abie yayi yace "sai mun dawo "a dawo lafiya tayi masu haɗi da juyawa ta nufi kitchen, fita su kayi abie na gaba suna bin shi a baya har compound, motar su ka shiga, Aaimah na gaba kusa da abie yayin da Aairah take baya,  fira suke cikin kwanciyar hankali har suka iso gidan dadi,horn abie yayi a bakin gate mai gadi ne ya leƙo ganin motar abie yasa shi komawa ciki da sauri,ya  buɗe mashi gate, ya shiga ciki parking lot ya nufa, sai da ya gama dai daita parking ya kashe motar Aairah ce ta fara fitowa sannan sai Aaimah, jiran abie su ka yi har ya fito su ka shiga cikin gidan tare,cikin parlor su ka shiga suna sallama tsit parlorn yake  babu kowa,wuri abie ya samu kan sofa ya zauna har zasu nufi ɗakin  Aunty Rabi sai gata ta fito tana amsa masu sallamar da su kayi, gaishe da ita su Aairah su kayi da fara'a a fuskar ta amsa masu sannan ta nufi wurin abie "yaya ina kwana "
"lafiya lau, ya gidan "
"Alhmdllh"
"mama na ciki ne?" abie ya tambaya
"eh tana ciki "
"bari na shiga mu gaisa "da to Aunty Rabi ta amsa, ta shi abie yayi ya nufi bedroom ɗin dadi, zaune take kan sallaya ta gama sallar walha  tana adu'a, zama abie yayi gefan gadont har sai da ta gama adu'a, waigowa tayi tana kallon abie ta ce "Muhammad kai ne tafe "
"eh mama, ina kwana "
"lafiya lau, ya su kubra "
"suna nan lafiya, tana gaishe ki "
"ina amsawa"su Aairah ne su ka shigo da gudu su ka nufi dadi suna faɗin "dadi munyi kewar ki" basu ƙarasa ba abie ya dakatar da su da  faɗin "lafiyar ku lau kuwa,za ku wani nufe ta da gudu hak, salan ku danne mata ƙafafu fa bayan kun san fama take dasu,   Allah yasa in ƙara ganin irin haka " ya faɗa cikin faɗa, tsaya wa su kayi suna kallon dadi kamar za su yi kuka
dadi tace "a'a da ka barsu ƙafafu ai sunyi  lafiya  ba abun da zasu man"
"kar kice  haka mama,ji fa yanda suka nufe ki da gudu,  waɗannan yaran wani lokacin jinsu su ke kamar wasu ƙananun yara"
"duk da haka dai da ka barsu, ku zo nan"dadi ta faɗa tana miƙa masu hannu, matsawa su kayi kusa da ita su ka zauna "inakwna dadi "
"lafiya lau, ya gida "
"lafiya lau"
"masha Allah" fira su ka shiga yi da dadi, abie dai na zaune yana jin su, tashi yayi yana faɗin "mama ni zan wuce "
"zauna ina son magana da kai" komawa abie yayi ya zauna yana faɗin "to Allah ya sa lafiya"
"lafiya lau" ta faɗa tana kallon su Aairah ta ce ku ɗan  bamu wuri " da to suka amsa haɗi da ta shi suka fice,  dadi tace " dama magana ne akan ɗana, tun ranar da nayi maku magana kai da mustafa ban sake jin wani ya ce komi ba dangane da maganar " ɗan nisawa abie yayi sannan ya ce
"haka ne mama, naje har garin na ku, amma ban samu wanda yace ya san inda ya koma ba, an dai ce man a kwai  wani  abokin baban sa  da suke  kasuwanci tare, amma yanzu baya garin, lokacin da  bai da lafiya babban ɗansa yazo ya tafi da shi, sun dai faɗa man ɗanna sa yana kaduna da zama"hannu dadi ta ɗaga sama tana faɗin
" ya Allah, Allah ka bayyanar da shi, hankalina ta shi yake duk lokacin da nayi mafarkin habiba,ban riƙe amana ba "  ta faɗa hawaye na  sauka a fukar ta,lallashin ta abie ya shiga yi,    hannu yasa ya  share mata hawaye yana faɗin
"ki dai na  kuka mama, insha Allah za'a gan shi, ki daina cewa ba ki riƙe amana ba Allah yaga niyyar ki"
"Muhammad dole na ce haka, amanar yaron nan ta bar man , da ace da ubansa ya nuna bazai bar man shi ba na cigaba da kula da shi ina ziyartar shi, amma  sai  na fita batun shi, kaga kuwa ban kyauta ba "
"kiyi haƙuri komai zai wuce da izinin ubangiji, za muyi iya bakin ƙoƙarin mu ganin mun samu inda yake "
"to Allah ya yarda "
"Ameen " abie ya ce
"Muhammad wai ya jikin abokin ka, kwana biyu ba muyi waya da safwan ba da mahaifiyar shi  , ban kuma tambaye ka  ba "
"jiya munyi waya da safwan, ya sanar min an ma kusa sallamar shi , ya nemi alfarmar a bar shi can wurin su"
"ai gara yayi zaman shi can, ko dan saboda azzaluman mutanen nan "
"gaskiya a gani na gara ya dawo nan, har Allah yasa memoryn shi ya dawo"
"to Allah ya ƙara sauki , amma kana ganin idan ya dawo ƙasar nan  mutanen nan zasu barshi, baza su cigaba da bibiyar  rayuwar shi ba "
"haka ne muddin suka san yana raye baza su ƙyale shi ba,ko da nace ya dawo nan bawai zai koma can bane, a nan zai zauna tare da mu har memoryn shi ya dawo ya tuna da iyalan shi,ta hakan ne za mu iya samun  sa'a akan su, amma idan yana can ba lallai ne ya iya tuna baya ba "
"gaskiya hakan shi ya fi, dan ya ji jiki da da ƙarar kwana da tuni sun kashe shi, kuma yan da ya manta da abun da ya faru za su iya ƙara cutar da shi muddin ya koma " ɗan nisawa abie yayi yace
"haka ne, shi da yake mahaifin safwan kwanan shi sun ƙare shiyyasa suka samu galaba a kan shi har su ka  kashe shi"
"insha Allah  , Allah zai toni asirin su"
"Ameen, burina kwai ya dawo cikin hayyacin shi, ya tuna da baya "
" ameen, Allah ya bashi lafiya " da ameen abie ya amsa, sun ɗan jima suna tattaunawa akan abokin abie, daga baya yayi ma dadi sallama, parlor dadi ta nufa wurin su Aairah da Aunty Rabi.

✨Abuja✨

Zaune ya ke kan carpet  a parlor yana aiki a laptop, sanye yake da  short black color iya gwiwar sa,  sai t_shirt ita ma black color, wayar sa da kan hannun sofa ce ta fara ringing , jawo ta yayi haɗi da du ba mai kiran, murmushi yayi ganin A  hashim, picking yayi tun kafin yace wani abu A hashim yace " hey man  gani a bakin gate ɗin estate, kasan halin

Please Login or Register in order to submit comment