Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lafiya ya dawo dasu lafiya..

suna fita daga gidan direct gidan malam suka wuce dan suyi mashi ban kwana, sosai malam yayi masu nasiha da  fatan isa lafiya, suna fita ilya ya kama hanyar airport, koda ya kaisu sai da ya jira har jirgin su ya tashi sannan ya dawo gida.....

✨Abuja✨

Airport, passengers ne suka fara fitowa ta ƙofar da aka rubuta exist wacce aka tana da domin passenger, su shazim ne suka ɓullo ta wannan ƙofar yana gaba fatima da noraiz na biye da shi abaya da trollys ɗinsu a hannu, wata kyakyawa matashiya ce wacce zasu yi sa'anni da fatima fara ce sai dai bata kai fatima haske ba,   ta nufo fatima da gudu tayi hugging ɗin ta tana faɗin "oyoyo sister" fatima da fara'a a fuskar ta tace "ya kike sa'ada" wacce aka kira da sa'ada, tayi murmushi tana faɗin "lafiya lau ya hanya" sannan ta juyo tana cewa" ya Shazim ina wuni" amsa mata yayi da "lafiya lau" sannan ta juya tana gaishe da noraiz, da fara'a a fuskar shi yace "ai nayi tunani fatima kaɗai kika gani " da murmushi a fuskar ta tace "a'a ya noraiz kuma ai na gan ku " suna nan tsaye wasu ƴan mata  kyawawa su biyu suka  iso farare ne sai dai ɗaya tafi ɗaya haske, mai hasken sosai tana kama da  sa'ada sai dai ita daka ganta zaka san tana ƙara wa dana kanti,  jikinsu sanye da ɓakar jallabiya sunyi rolling da gyelen jallabiyar,  wurin su suka  nufo,  mai kama da sa'ada  cike da yanga take  faɗin "hi ya shazim "haɗi da nufar Shazim da nufin tayi hugging ɗin shi, kasa ƙarasawa tayi ganin wani mumunnan kallo daya bita dashi fuskar shi a ɗaure kamar bai taɓa dariya ba, kwal kwal tayi da ido kwalla na taruwa ciki tace " haba ya shazim miyasa kake haka , daga na  nuna farin cikin ganinka " banza yayi mata kamar ma ba da shi take ba,gaishe da shi ɗayar tayi, cikin sakin fuska ya amsa yana faɗin "ya kika kairiyya "
"lafiya lau, ya hanya?"da alhmdllh ya amsa mata,hugging ɗinta fatima tayi tana faɗin "nayi kewar ki aunty kairiyya" da fara'a a fuskar ta tace "nima nayi kewar ki",   wasu maza   ne suka ƙaraso wurin su su biyu sanye da uniform, suna ƙarasowa suka ce  "barkan ku  da zuwa ranka ya
daɗe " kallon su shazim yayi yana cewa "barkan ku dai aminu ya kwana biyu"
"alhmdllh ranka ya daɗe" wanda aka kira da aminu ya ce, ɗayan ne ya ce "yallabai ya lagos " shazim na kallon shi ya ce "alhmdllh kamal, ya aiki"
"lafiya lau ranka ya daɗe"sannan suka gaishe da noraiz fuska ɗauke da fara'a ya amsa, sannan fatima ta gaishe da su, amsa mata suka yi  cikin kulawa fuskar su  da fara'a, suka  amshi trollys  ɗin noraiz  da na shazim  dake hannun noraiz aminu na  cewa "mutafi koh ran ka yade "ok kawai shazim yace ya kama hanya,   su  aminu na  gaba  da trollys ɗinsu, sa'ada ce ta amshi na fatima, wannan budurwar wuce su tayi fuuu kamar zata tashi sama, fatima ce tace "aunty feenah abun ba magana "juyowa tayi ta kalli fatima sama da ƙasa fuska a haɗe tace "sannu" ta juya tayi gaba, da idanu kwai fatima ta bita, taɓe baki noraiz yayi, fuskar sa'ada da ɗan damuwa ta kama hannun fatima tana faɗin "sorry sister " ɗan yaƙe fatima tayi tana faɗin "bakomai" tsaki kairiyya ta ja a zuciyar ta tana faɗin "ko yaushe feenah zata dai wannan banzar ɗabi'ar "
parking lot ɗin airport  ɗin suka ƙara so time ɗin har shazim ya shiga bayan mota ya zauna, aminu na saka kayan su cikin booth, amsar trolly ɗin dake hannun sa'ada kamal yayi ya saka a booth,   buɗe ma su  baya yayi, noraiz ya shiga sa'ada ta ce " kamal mu zamu tafi a motar aunty kairiyya  "
"to shikenan hajiya " kama hannun fatima tayi suka nufi inda motar kairiyya  ta ke, tsaye suka same ta bakin mota,
sa'ada tace
"lafiya dai aunty kairiyya"
"babu komi, ku nake jira ne "
sa'ada tace "aunty feenah tafiya tayi?" eh kawai kairiyya tace haɗi da buɗe motar ta shi, suma shiga sukayi fatima na gaba kusa da kairiyya sa'ada na baya,   key tai ma mortar haɗi da yin  reverse   tabi bayan motocin da su shazim ke ciki, suna tafiya kamal na tambayar noraiz  ya lagos da ammy, da alhmdllh noraiz ya amsa mashi sosai suke fira da shi har suka kawo wata danƙareriyar anguwa ta ji da faɗa, gidajen dake anguwar ka ɗai sun isa su sa ka fahimci cewa anguwa ce ta manyan mutane, gidaje ne naji da faɗa, road road ne gasunan kala kala kowane road kalar tsarin ginin   gidajen ta da ban, karya kwana animu yayi ya shiga wani road bin bayan shi su kamal suka yi shi da kairiyya , masha Allah wani haɗeɗen  estate ne naji da faɗa,  aƙalla gidajen dake cikin estate ɗin zasu kai 20 duk da akwai wainɗan da anyi foundation ba'afara gina su ba,   tsarin gidajen dake cikin estate ɗin yafi na sauran gidajen dake sauran road ɗin  haɗuwa da tsari,komai na gidajen iri ɗaya ne,  tafiya suka yi mai ɗan tsayi, sannan suka kawo bakin main gate ɗin estate ɗin   ,securitys ne zaune kan bench a bakin gate ɗin estate ɗin,   ɗaya daga cikin su ne ya taso ya nufo motar,  sauke glass ɗin motar aminu yayi,  gaisawa yayi da security ɗin, tambayar shi securityn yayi daga ina, amsa aminu ya bashi "daga airport muke, yallabai shazim ne ya zo " liƙawa security yayi yana cema shazim "ranka ya daɗe barka da zuwa, ya hanya "da alhmdllh shazim ya amsa masu, sauran security ɗin ma ta sowa su kayi suna gaishe da shazim sannan suka nufi motar dasu noraiz ke ciki suna gaishe su,  cikin sakin fuska suka amsa masu,   buɗe masu gate security yayi ,ciki aminu ya danna kan hancin motar kamal na biye da shi, sai da suka ɗanyi nisa da tafi sannan suka iso bakin wasu gidaje biyar  dake jere duk da akwai yar tazara tsaka nin su  , huɗu girman su ɗaya, ɗayan kuma yafi su girma sosai,  mai girman dake tsakiyar su aminu ya nufa ,  parking aminu yayi bakin wannan ƙaton gidan wanda yafi sauran gidajen girma da haɗuwa parking lot ɗin  gidan ya nufa yayi parking, motoci ne da a ƙalla zasu kai biyar an rufe su, fitowa aminu yayi ya buɗe ma shazim ƙofa amma sai shazim yace kawai ya ɗauki kayan ya wuce, hakan yasa shi  nufar  booth ɗin motar ya fito  da trollys ɗinsu, ya nufi entrance ɗin shiga  gidan ya tsaya,  kamal ma ya nufo nan yayi parking a parking lot   fitowa noraiz yayi, su fatima kuma wani part kairiyya ta nufa da su tayi parking, fitowa   sa'ada da fatima  suka yi, sa'ada ta  buɗe booth ta fito ma fatima da trolly ɗin ta, fatima leƙa ta window tana faɗin "aunty kairiyya sai mun shigo " da to kairiyya ta amsa, reverse tayi ta nufi wani part tayi parking, ficewa tayi ta nufi cikin part ɗin.
kallon motar feenah dake parking lot ɗin sa'ada tayi, aranta tace kenan gida aunty feenah ta dawo ,  trolly ɗin fatima   ta ja suka nufi entrance ɗin gidan ,kamal na parking noraiz ya fito ya nufi aminu dake tsaye   yana jiran fitowar shazim ya kai masu trolly ɗin cikin gidan  amma bai fito ba  noraiz na isowa ya tambayi aminu lafiya, amsa aminu ya bashi da shazim ya ke jira ya fito   noraiz ya ce " ok muje  kawai" da to aminu ya amsa yana gaba noraiz  na baya,    buɗe ƙofar aminu yayi  suka shiga har time ɗin shazim bai fito ba yana zaune cikin mota, haɗeɗen parlor ne mai kyan gaske dan inka shiga sai kayi tuna nin ba acikin estate ɗin  kake ba, babu motsin kowa aciki sai ƙarar ac dake aiki ita kaɗai,kota ina ƙamshi ne ke tashi cikin parlorn, up stairs aminu ya nufa , ɗakuna ne saman sosai, wata yar hanya aminu ya bi nanma wani parlorn ne wanda yafi na ƙasa haɗuwa  da tsari, wani stairs ɗin suka ƙara nufa nanma parlor ne shima ya haɗu ga tsari mai kyau,sannan suka nufi wani ɗan corridor , bedrooms ne kusan guda huɗu anan aminu ya tsaya yana ajiye trollys ɗin yayi ma noraiz sai anjima, godiya noraiz yayi mashi sannan ya ja trolly ɗin shazim ya shiga ƙofar dake kusa da shi, ɗan ƙaramin parlor ne mai kyan gaske kusan tsarin shi ɗaya da parlorn shazim dake lagos, nan kamshi yake mai daɗin gaske ga sanyin ac, bedroom ya nufa nan ma ya haɗu shima kamar na lagos ne sai dai yafi na lagos girma da wasu abubuwan, har cikin wardrobe noraiz ya saka ma shazim trollys ɗin shi sannan ya fice daga ɗakin yanufi nashi, shima nashi ya haɗu sosai banbancin shi dana shazim bawain mai yawa bane bedroom ya nufa ya rage kayan jikin shi ya nufi toilet domin ya watsa ruwa ..

✨Shazim✨

wayar shi dake cikin aljihu ya fiddo, number ammy yayi dialing saida ta kusa tsinkewa sannan ammy tayi picking bakin ta ɗauke da Sallama, amsa sallamar shazim yayi yana faɗin ammy ya gida, da lafiya lau ta amsa tana tambayar shi ya gajiyar hanya da kuma mutanen abuja "gajiyar tafiya akwaita ammy  alhmdllh" murmushi ammy tayi mai ɗan sauti tana cewa "gajiya sai kace wanda yaje a mota ko a ƙafa" kwantar da kanshi yayi jikin saet ɗin motar yana shafa kanshi ya ɗan lumshe ido yana faɗin "da gaske nake ammy " ammy tace
"to yayi, ya mutanen gidan? "
"wallahi ban saniba dan ban shiga ba"
"to saboda mi, ina fatima da mai babban suna? "
"fatima na part ɗin uncle Ibrahim, noraiz kuma na part ɗin mu "
"to kai kana ina? "
"ina cikin mota, yanzu muka iso ne ammy, na tsaya in kira ki ne "
"ok miyasa ku baza ku sauka part ɗin ibrahim ba kona yaya ahmad "
"bakomai ammy, shi da kanshi uncle Ibrahim ɗin yasa aka gyara mana nan"
"duk da haka shazim da kuna zauna part ɗin shi, nasan shima dan ya san halinka ne ba zaka  zauna part ɗin shi ba yasa aka gyara maku nan "
"ammy ba haka bane"
"to yaya ne in ba haka ba? "
"kawai ya san zamufi sakewa ne apart ɗin mu shine kawai"
"shikenan shazim, amma da mun gama wayar nan  ku shiga part ɗin innah ku gaishe ta dan Allah "
"to" kawai yace dan wallahi kwata kwata bai son ganin tsohuwar,
"to sai anjima, in ka shiga kace ina gaishe dasu dan Allah "
"to insha Allah zasuji "daga haka yayi rejecting ɗin kiran,number malam ya lalubo bugu ɗaya malam ya ɗauka da Sallama, gaishe da shi noraiz yayi, cikin kulawa malam ya amsa da tambayar shi hanya da su fatima, sunjima sosai suna waya da malam sannan suka yi Sallama, cikin aljihu wando ya maida wayar, sannan ya buɗe motar ya fice, ya nufi part ɗin su  ko da ya shiga bedroom ɗin shi ya nufa yayi wanka ya kwanta kan bed, nocking ya ji anayi daga parlor, shiru yayi kamar yana bacci dan ya san bazai wuce noraiz bane, kuma ya san  ya zo ne dan su tafi parts ɗin uncles ɗin su, shiyyasa yayi shiru dan bai shirya zuwa wurin kowa ba yanzu, jin shiru yasa noraiz tuna nin koh yayan nashi barci ya ke, barin bakin ƙofar yi  ya fice daga gidan, gidan dake kusa da wanda kamal ya aje fatima da sa'ada noraiz ya shiga da Sallama, parlo ne mai girma ya ji furnitures masu kyan gaske,   tsit yake ba kowa a ciki, wani ɗan corridor ya nufa ya shiga wata yar ƙofa,nan ma wani ɗan ƙara min parlor ne,  shiga ciki yayi da sallama, kyakyawar  tsohuwa ce   zaune kan carpet jikinta sanye da atamfa ɗinkin riga da zani  sai feenah da ke kan sofa kusa da ita fuskar ta duk hawaye jin sallamar norai ne ya sa feenah goge  hawayen da ke fuskar ta,zuba ma noraiz ido tsohuwar tayi har ya ƙara so  cikin parlorn  ya  neman wuri ya zauna kan sofa yana faɗin "inawuni innah " amsa mashi tayi da "lafiya, ai nayi tuna nin kaima kafi ƙarfin kazo ka gaishe da ni kamar ɗan uwan ka mara kunya, dan nasan idan ba Ibrahim ya kira shi ba bazai ta ɓa shigowa nan ba saboda aisha ta riga da tasa ya gama raina ni baya ganin mutunci na "
"kiyi haƙuri innah yana nan shigowa bacci ya kwanta saboda jiya bai samu yayi bacci sosai ba "
"kai da Allah yi man shiru, wane haline kuma na abdulƙadir wanda ban sani ba, itama fatima tafi ƙarfin tazo ta gaishe ni koh"
"A'a innah tana tare da sa'ada nasan zasu shigo ne "ta ɓe baki innah tayi tana faɗin "Allah sa"
da ammen noraiz ya amsa  haɗi da miƙewa yana faɗin" innah zanje part ɗin  uncle Ibrahim"
bai jira mai zata ce ba ya fice abun shi, da harara feenah ta bishi yana fita tace "kingani koh innah shima noraiz wulaƙanta ni ya ke, dan tunda suka zo ko kallon banza bai yi min ba, da ya shazim ya dizgani a airport dariya yayi shida fatima "
"rabu da yan banza, zanyi maganin su ne daga su har uwar ta su,  kuma shi wannan mara mutuncin nasan miye maganin sa, bari dai kawunnan nashi su dawo"
"yawwa innah shiyyasa nake sonki wallahi "
"ai karkiji komai,su dai dawo, zai san dani yake magana, sai dai kuma abun da nake so a wurin ki shine ki kama kanki  ki daina son taɓa jikin shi dan nasan halinki da ɗabi'ar banza "
"Insha Allah innah na bari bazan sake ba "
"Allah ya sa " da ameen feenah ta amsa,  suna nan  zaune suna fera sa'ada suka shigo ita da fatima ko da fatima ta gaishe da innah cewa tayi" sai yanzu kika ga damar zuwa, ai da kinyi zaman ki baki shigo ba "haƙuri kawai fatima ta bata, ko kallonta bata yiba suka cigaba da fira ita da feenah, ganin haka ne yasa fatima cema sa'ada ta tashi suje part ɗin su aunty kairiyya, tashi sa'ada tayi suka fice zuwa part ɗin uncle ahmad, anan suka samu noraiz shida mahmud,gaishe da mahmud fatima tayi, sannan suka shiga bedroom ɗin mama ( asiya mahaifiyar su mansoor )  suka gaisa tana tambayar fatima ya su ammy, sun ɗan jima suna fira da ita sannan suka tashi suka nufi bedroom ɗin kairiyya.

wani matashin saurayi ne ya shigo  parlorn da sallama  hannun shi riƙe da briefcase,  da sauri noraiz  ya nufe  matashin yana cewa "oyoyo ya mansoor,nayi kewar ka sosai"rungume shi mansoor yayi yana cewa " lil bro saukar yaushe? "
" tun ɗazu, ina ta zuba idon ganin ka, ya aiki" shafa kanshi mansoor yayi yana faɗin "alhmdllh,ya su ammy da auta? " muryar fatima sukaji fitowar ta kenan daga ɗakin kairiyya  tana cewa "gani anan yaya "juyawa mansoor yayi yana cewa "autar ammy, yan graduation kice tafiyar harda ke"ɓata fuska fatima tayi tana faɗin "ai ni fushi nake da ku kai da ya dr, ko ɗan text message na happy graduation" matsowa kusa da ita mansoor yayi yana faɗin "sorry lvly sis bahaka bane munso muzo har lagos ɗin Allah ne dai bai nufa ba, amma kiyi haƙuri gift ɗinki na nan na ajiye maki"washe baki fatima tayi tana faɗin "tnxs big bro"
"to shikenan autar ammy ni zan shiga ciki na watsa ruwa " mansoor ya faɗa haɗi da nufar up stairs,"to sai ka fito "fatima ta faɗa, tashi   noraiz da mahmud su kayi suka fice su fatima kuma suka zauna kan sofa suna fira ita da sa'ada.

shazim daga wannan kwanciyar  bacci yayi awan gaba da shi ba shi bane ya tashi ba sai gab da magrib, yana tashi ya nufi toilet yayi wanka haɗi da alwala,sannan ya shirya ya fito  daga bedroom ɗin ya nufi dinning, abinci yaci kafin ya fice daga  part ɗin,ya nufi   masallacin dake cikin estate ɗin ,ana gama sallah ya fito ya nufi part ɗin uncle ahmad,kairiyya da su fatima  ya samu a parlor , gai she dashi kairiyya ta sake yi tana cewa" ya gajiyar tafiya  ya  shazim " amsa mata yayi da Alhmdllh sannan yace" uncle fah? " yana sama ta bashi amsa, tashi yayi ya nufi up stairs ya shiga wani ɗan ƙaramin parlor, zaune uncle ahmad yake kan carpet, mama na kusa da shi,sallama yayi ya shiga ciki, amsa mashi sallamar sukayi, wuri ya samu kan carpet ya zauna yana gaishe da su amsa mashi sukayi cikin kulawa uncle ahmad na tambayar su malam da ammy,"suna lafiya" uncle ahmad ya ce "masha Allah, kaje wurin Ibrahim?" shazim yace" a'a yanzu dai zan tafi " uncle ahmad yace
"to shikenan, bari sai ka ci dinner tukunnan sai ka tafi "
"bana jin yunwa uncle yan zu na ci abinci" uncle ahmad yace "to shikenan tashi kaje wurin Ibrahim ɗin "
da to shazim ya amsa haɗi da miƙewa ya fice,yana fita bedroom ɗin mansoor ya nufa, zaune ya same shi yana waya, harara ya watsa ma shazim, murmushi yayi haɗi da samun wuri kusa da shi ya zauna  yana faɗin"my lover bro  wannan hararar ta mi cece" katse wayar mansoor yayi yana faɗin"amma wallahi ka rainani shazim ni nema lover ɗin koh "
"eh mana, yaya  "
"ni nama manta nayi maka magana fushi nake da kai "
"kaina bisa wuya minayi kuma lover bro "duka mansoor ya kai mashi ya kyauce "Allah zanyi maganin ka idan har baka daina ce man lover bro ɗinnan ba"
" sorry na dai na"
"da dai ya fiye maka, kuma ka tashi ni ka bani wuri "
"afuwan ya mansoor " juya mashi baya mansoor yayi yana faɗin
"ka tashi nace ka bani wuri" hannu shazim ya sa ya riƙe kunnuwan shi alamar ban haƙuri yana cewa"haba ya mansoor dan Allah fa"kallon shi mansoor yayi yace
"Uhmm , ya hanya, ya su ammy da malam"
"suna nan lafiya "
"masha Allah"
dafa kafaɗar shazim mansoor yayi sannan ya ce "bro wai miya farune ake ta kiran ka amma baka ɗaga waya wani time ɗin ma akashe, kasan ka ɓata ma su abbah rai sosai " kallon mansoor shazim yayi "yaya su abbah sun ta kura dole sai nayi aure ni kuma yanzu bana da ra'ayin yi"
"ƙanina kasan mi? " girgiza mashi kai shazim yayi,alamar a'a,  ɗan nisawa mansoor yayi sannan yace "miyasa baka son yi aure yanzu, duk wani rufin asiri na duniya Allah ya baka shi, to miyasa bazaka godema ni'imar da yayi maka ba " kwantar da kanshi yayi saman  kafaɗar mansoor sannan yace " yaya bawai bana son auran bane kwata kwata' a'a nafiso su ƙara man lokaci  har nasamu wacce take sona nake son ta, amma yaya kowa yaƙi fahimta ta  "
shafa kanshi mansoor yayi yana faɗin "karka damu bro ni na fahimce ka insha Allah suma su abbah zasu fahimce ka "
"Allah yasa yaya"
"Ameen "( a kwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin shazim da mansoor, mansoor ya girmi shazim bawai sosai ba, tare suka taso har makaranta tare suka yi )
"tashi muje part ɗin uncle Ibrahim dan nasan ba inda kaje tun da kazo "
"nayi baccine shiyyasa "
"ok tashi muje "tashi sukayi suka fice direct part ɗin uncle Ibrahim suka nufa, bakin su ɗauke da  sallama suka shiga,momy suka samu zaune kan sofa ita da aliyu, da gudu aliyu ya taso yayi hugging ɗin shazim yana faɗin "oyoyo yaya "ɗaga shi sama shazim yayi yana faɗin "haidar ykk,ya school"
"lafiya qlu yaya" masha Allah shazim ya faɗa haɗi da sauke shi ƙasa yana faɗin "momy anwuni lafiya "
"lafiya lau alhmdllh, ya hanya, yasu ammy da malam "
"lafiya qlu Alhmdllh "mansoor yace "momy ina wuni " 
"lafiya qlu Alhmdllh, ya aiki "
"alhmdllh momy, uncle na ciki "
"eh yana part ɗin shi"
"ok  bari mushiga momy " to momy tace sukuma suka nufi corridor dake kallon parlorn ,wani ɗan ƙaramin parlor suka shiga, shiru parlorn yake bakowa sai ƙarar tv da ta ac, mansoor ne yace su zauna may be uncle ɗin na ciki, zama sukayi kan sofa,  muryar uncle Ibrahim su kaji  daga bedroom ɗinshi cikin  faɗa yana cewa "wannan ai maganar banza ce maganar wofi, amma kabani mamaki, to bari kaji tun wuri kasan yan da za'ayi " muryar wani matashi sukaji daga bedroom ɗin yana ba shi haƙuri "dan Allah dady kayi haƙuri, wlh mistake aka samu amma insha za'a dawo dasu, ko yanzu nayi magana da c.p dake chan yace suna nan suna bin ciken idan suka shige da sun samu zasu sanar da ni "
"da dai yafi, dan bazan yi asarar million dollars ba a bazan, in ma ban da shashan ci irin na yaran yanzu ina ake samun matsala irin haka ai tun chan ya kamata ka duba bawai sai kun zo nan ba "
"sorry dady insha Allah  zasu dawo "
"Allah ya sa, ina so yanzu daka fita kasake kiran c.p ɗin kaji a wane mataki suke "
"to" fitowa saurayin yayi da wani kallon yabi su shazim dake zaune kan sofa  sannan ya kama hanyar fita daga parlorn, mansoor ne ya daka mashi tsawa yana faɗin "kayi hauka ne luqman, sa'annin wasan ka ne mu daza kallemu ka wuce kafi ƙarfin ka gaishe da mune "
wanda aka kira da luqman ne yace "sorry yaya ban lura da kai bane "
"idan baka lura dani ba, baka ga  shazim bane ko kafi ƙarfin ka gaishe da shi ne "
"a'a"
"oya koma ka gaishe shi kafin ranka ya ɓaci " juyawa luqman yayi ya koma cikin parlorn, sai da yaje har gaban shazim sannan ya ce "ina wuni ya hanya " idan har bango na magana to shazim ya amsa mashi gaisuwar, dan yi yayi kamar ma bai san da wata  hallita ba wai luqman a parlorn, duk abun da ke faruwa uncle Ibrahim na tsaye bakin ƙofar badroom ɗin shi yana kallon su, sake gaishe da shi luqman yayi still bai amsa ba,gyaran murya uncle Ibrahim yayi, hakan yasa gaba ɗaya suka mai da hankali su kan shi ƙara sowa yayi cikin parlorn yana faɗin "shazim baka ji ana gaishe da kai? " maimakon shazim ya bashi amsar tambayar da yayi mashi sai ma cewa yayi "uncle anwuni lafiya" ganin ya waske ne yasa uncle Ibrahim amsa mashi gaisuwar yanama luqman alama ya tafi da ido , ficewa luqman yayi daga parlorn ( luqman ɗan uncle Ibrahim ne, shine babban ɗan shi sai feenah daga feenah sai sa'ada da aliyu, uncle ahmad kuma mansoor ne babba sai faisal daga faisal sai mahmud sai kairiyya sai salma ) 
Episode 22_23

Kallon shazim uncle Ibrahim yayi yana cewa "shazim ya su ammyn ku da malam?"
"lafiya qalau suke "
"to masha Allah,  ya gajiyar  hanaya "
"alhmdllh "
"ka shiga wurin innah kuwa? "
"a'a, daga part ɗin uncle ahmad nake, amma daga nan chan zan tafi "
"haba shazim ai tun da kuka zo chan ya kamata kufara shiga, bawai sai yanzu ba "
"haka ne uncle, na ɗan gajine to shine sai na ɗan kwanta "
"ah to gaskiya tashi ku tafi,inya so sai ku dawo "da to suka amsa haɗi da miƙewa suka nufi ƙofa, suna fita uncle Ibrahim ya ciro wayar shi daga aljihu dake ringing, picking yayi yanufi bedroom ɗin shi.

A bakin part ɗin innah suka tsaya shazim na faɗin " muna shiga da masifa zata tare ni nasani " murmushi mansoor yayi yana cewa "lamarin ka kai da innah ai sai Allah "
"ai big bro innar ce ta cika matsala "
"kai kuma baka ganin zarau sai ka tsinka "
"innar ce ai sai da irin haka "
"haka dai kace,  wuce mu shiga karka ƙara bata lokaci tace da ka bari sai gobe " dariya suka kwashe da ita yayin da suke shiga part ɗin bakin su ɗauke da Sallama,  feenah suka samu kan sofa tana charting a wayarta, tashi tayi zaune tana amsa masu sallamar da sukayi, zama su kayi kana sofa, sai kallon shazim take, shi kuwa tun da suka shigo ya ɗauke kai kamar bai ganta ba,  mansoor ne yace" ina innah take? "

Please Login or Register in order to submit comment