Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


"yanzu ta shiga ciki "
"ok ce mata gamu nan "
ta miƙe kenan sukaji muryar innah tana faɗin "dama kunyi tafiyar ku dan bana da lokacin ku yanzu nima"murmushi shazim yayi a zuciyar shi yana faɗin "sarki,baki taɓa shanye raɗa" kamar daga sama yaji muryar innah na faɗin
"kayi murmushi mana tun daga mahaukaciya sabon kamu na magana"
kallonta shazim yayi batare da yace komai ba, hakan dayayi ne ya harzuƙa ta daman a harzuƙe take
"kai ni daina kallona da waɗannan idanun ka, karka cinye ni "
da buɗar bakin shazim sai cewa yayi "dagama kin samu ina maki kallon love "riƙe haɓa innah tayi tana faɗin
" riƙe kayan ka bana buƙata "
"ke dai da kin karɓa " tsaki innah ta ja tana faɗin "sai yanzu kayi lokacin zuwa ka gaishe ni kenan, koko sai yanzu uwar taka tace kazo ka gaishe ni? "
"kusan haka, yan zunma sa'a kika ci har kika ganni "
"ba shakka mara mutunci, to koh ita  uwar taka in tazo bata isa ba tace sai lokacin da ta gadama zata gaishe dani ba, bare kai "
"kuma fa hakane, dole ta gaishe da ke kamar yanda ke ma kike gaishe da magabata so ina ganin bawani abun tashin hankali bane"mamaki ne ya kashe innah takasa cewa komi, mi shazim yake nufi,ta shi shazim yayi yana faɗin "big bro ta shi muje bacci nake ji" sannan ya kalli innah yace "asuba ta gari tsohuwa mai ran ƙarfe"  sannan yayi gaba abun shi sallama mansoor yayi mata haɗi da bin bayan shazim da harara innah ta raka shi tana faɗin " bauɗaɗɗe kawai maramunci " feenah ce tace innah "wai miyasa ya shazim yake maki haka ne?"
"mi yasa fa,ai ba komi bane face abun  da uwar shi ta koya mashi, ai zanyi maganin su daga shi har ita dani suke magana"
suna fita part ɗin uncle ahmad suka wuce zuwa bedroom ɗin mansoor, zama shazim yayi bakin bed mansoor na tsaye yana waya shazim ne yace " nizan tafi na kwanta naga ka kama waya"
"ok sai da safe " ficewa shazim yayi ya nufi part ɗin su, yana shiga ya nufi bedroom ɗin shi kayan jikin shi ya rage ya shiga toilet, bayan minti biyar ya fito ƙugun shi ɗaure da towel, clothes set ɗin shi ya nuf, pajamas ya ciro riga da wando masu taushi ya saka sannan ya nufi wayar shi dake haske alamar kira zama yayi bakin   bed haɗi da ɗaukar wayar dan yaga mai kiran shi,majeed ne picking yayi
  bakin shi ɗauke da  sallama  " on the other hand majeed yace "mutanen abuja, ya gajiyar hanya "
"alhmdllh majeed, ya aiki?"
"aiki alhmdllh, ina ka ajiye wayar kane ina ta kiran wayar ka bakayi picking ba "
" wlh kuwa majeed, time ɗin da kakira ina bacci ne dana tashi kuma naje part ɗin uncles ɗina ne,yan zu na dawo, ya ake ciki"
"dama maganar kayan da mukayi order ne sun iso "
"masha Allah, ka duba duk abun da mukayi order sun sako mana shi "
"eh na duba, sai dai akwai matsala"
"matsala, tami fah? "
"ina jin sunyi mistake ne, dan gaskiya kayan da mukayi order basu suka kawo mana ba amma ina tuna nin mistake ne suka samu, amma kakira kaji"
"ok to shikenan, amma abun da mamaki "
"wlh kuwa nima nayi mamaki sosai, musamman kayan dana gani a matsayi namu "
"wane irin kaya ne?"
"abun da mamaki, amma bari na turo maka kagani da idonka"ok kawai shazim yace haɗi dayin rejecting, ba'afi one minute ba sai ga saƙo ya shigo wayar, shiga cikin saƙon yayi,yana buɗe saƙon ya ci karo da kayan maye su  cocaine, India he ga alcohol iri iri masu matuƙar tsada da haɗari ga lafiya  ɗan zaro idanu yayi yana faɗin "ya Allah, miye kuma wannan , daga ina,  na waye? " ɗan dafe kanshi yayi, sai kuma chan yayi dialing number majeed tana fara ringing yayi picking
"kanaji majeed, kasan mi za'ayi "
"a'a saika faɗa "
"kawai kusa su a store, ba sai an maida masu ba, ina son na san ko na waye "
"to shikenan, amma ya za'ayi da magungunan da suka kusa ƙarewa "
"karka damu zan sake ordern wasu, amma waɗannan ku bar maganar su kawai har sai na dawo sannan "
"ok to shikenan, sai da safe"
"ok mu tashi lafiya" yace sannan yayi rejecting ɗin kiran,tashi yayi yashiga toilet ya ɗaura alawala 2 minute ya fito ya nufi   carpet ya shimfiɗa ya kabbara sallah, yana gama mawa ya ɗauki quran, ya shiga karantawa ƙarar shigowar message yaji awayar shi sharewa yayi sai ga wani message ɗin ya sake shigowa
bai koma takan wayar ba har sai da ya kammala karatun sannan ya ɗauki wayar ya nufi switch ɗin ɗakin ya kashe light nan take   bedside lamps suka kawo,hawa yayi kan bed haɗi da jan blanket ya rufe iya waist ɗin shi, sai sannan ya jawo wayar, message ya gani da baƙuwar number buɗa message ɗin yayi,yana gama karan tawa ya danna power yayi switching ɗin ta, adu'a yayi ya shafa sannan ya kashe bedside lamps,  ƙara jan blanket yayi zuwa chaist ɗin shi cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi........

Washe gari

bayan ya dawo daga masallaci sallar asuba komawa yayi ya kwanta, sai wurin 8:30 ya  tashi yayi breakfast bayan ya gama ya nufi part ɗin uncles ɗin  shi  domin gaishe da su,daya je part ɗin uncle Ibrahim, bayan sun gaisa yake tambayar shi  yaje ya gaishe da innah kuwa, ce mashi yayi eh bayan bai je ɗin ba yace eh ne dan ya san cewa zai yi yaje, shikuma bai shirya ma tujararta ba tun da safe, yana fita daga part ɗin bedroom ɗin mansoor ya nufa, yana shiga ya same shi yana shirin tafiya office, gaisawa sukayi, sannan mansoor yace mi zai hana ya bishi su tafi office ɗin tare, bai yi gardama ba, dan shi kwata kwata baya son zaman gida kamar mace, shiyyasa a kullum yake ma noraiz faɗa saboda zaman gida, shiryawa yayi  suka tafi tare,sai da yamma liƙis sannan suka dawo, a bakin ƙaramin  gate ɗin estate ɗin mansoor ya hango  feenah ta fito daga motar wani sauray, riga da wando ne a jikinta tayi rolling da ɗan ƙaramin gyale, sai waige waige take kamar tana tsoron wani ya ganta, kwata kwata bata lura da motar su ba tana sauri ta shiga , kallon ta mansoor  kawai yayi har ta shige ciki sannan yace" narasa gane mike damun ya rinyar nan, amma zanyi maganin ta " shazim ne yace
"lafiya dai ko bro,kai da wa??"
" ni da feenah mana kana nufin baka ganta ba  "girgiza kai yayi alamar a'a, sarai ya ganta amma sai ya fake a bai ganta ba,  dan shi gani yake kwata kwata babu abun da ya shafe shi da lamarin feenah, tun da iyayen ta suna sane da abunda take, kuma tushen lalacewar ta daga kakarta ne tun da ita ke goya mata baya akan duk abunda take so, so mizai hana tayi abun da taga dama tun da ta samu ɗaurin gindin kakarta da kuma mahaifin ta.ta babban gate suka shiga, sai masifa mansoor yake, shazim na jinshi bai ce komi ba
suna shiga ciki part ɗin innah  mansoor ya nufa, yana  parking yace ma shazim ya  fito su shiga su gaishe da innah,  shazim yace "gaskiya ni nagaji zan wuce ciki, anjima na zo na gaishe ta  kawai "
"miyasa bazaka shiga ba, duk fa yau bamu gaishe da ita ba yaka mata ace kazo mun shiga bafa wani jimawa zamuyi ba, dan nasan bawani anjimar da zaka zo, kawai ka fito mu shiga "
"nagaji ne bro, ka bari sai anjima  "
"pls bawani jimawa zamuyi ba "ok kawai shazim yace ba dan yaso,ya so mansoor ɗin ya bari sai anjimar fitowa yayi  haɗi da  bin  bayan shi suka shiga ciki,innah suka samu zaune a parlor mai aikin ta na mammatsa mata kafa,sallama su kayi    haɗi da ne man wurin zama,gaishe da su mai aikin tayi, amsa mata sukayi   mansoor na faɗin "barka da yamma innah, ya gida "
"lafiya lau, ya aiki"
"alhmdllh"
"shi wannan fanɗararen yafi ƙarfin ya  gaishe ni ne "
"a'a innah, kin tari numfashin shi ne "
"bana ra'ayi ne yau "acewar shazim, hararar shi innah tayi tana faɗin
"riƙe kayar ka,  bawai ina jiran taka ba"
taɓe baki yayi,yana faɗin"dama ance abun da baka samu haɗa shi da baka so " tsaki innah taja ba tare da ta sake cewa komi ba
  sallamar feenah suka ji,yanzu sanye take da doguwar riga ta material maima kon riga da wando  da suka ganta da su  ɗazu a bakin gate , amsa mata sallamar sukayi,harara mansoor na  watsa mata harara, gaban ta ne ya ɗan faɗin ganin hararar da ya ke jifanta da shi dan ita a sanin ta batayi mashi komi ba,   wuri ta samu kusa da innah sannan ta kalli shazim tana faɗin "ina wuni Ya shazim  "yi yayi kamar ma bai san da shi take ba,innah ce ta ja tsaki tana faɗin "Allah dai wadar mai wulaƙanta ɗan adam"banza yayi da ita duk da yasan da shi take, sosai sharetan da yayi ya sosa mata zuciya dan har idanunta sun tara kwalla, tana matuƙar son shazim amma sai wulaƙanta ta yake yana share ta kamar bai san daga inda ta fito ba, mai da idanun ta tayi kan mansoor tana faɗin "ina wuni ya mansoor "bai amsa mata gaisuwar ba sai ma hararar ta da yayi,innah ce tace "tofa yau ina ganin ikwan Allah, daga me shareta sai mai harara, kenan kai ma kakoyi baƙin hali irin nasu o'o "tsuke fuska shazim yayi dan ya san ba da kowa take ba face shi, kallon  yan da ya tsuke fuska tayi  tana faɗin "aikin banza aikin wofi,wai duk dan kar a raina shi" yanzu ɗauke kai shazim yayi kamar bai san dawa take ba, feenah da duk ta sha  jinin jikinta, tace ma mansoor  "Yaya  mi nayi kake hararata "
"zaki sani ne"innah ce tace
"kai wai  lafiya mansoor mi tayi ne"
"wlh sai na bata ɗan banzan kashi a gidannan "da buɗar bakin innah sai cewa tayi "ai sai ingani tun da kakoma zalunci"
"wai miyasa innah kike haka ne, duk ke ke ɗaure mata gindi take duk abun da ta gadama "
"to na ɗaure mata gindi sai aka yi yaya"kallon feenah mansoor yayi yana faɗin "wlh kinji na faɗa maki duk ranar da kika bari na kama ki jikin ki sai ya faɗa maki shashasha kawai"turo baki tayi tana faɗin "dan Allah kayi haƙuri yaya ni ban san minayi maka ba "
"uban waye na ganki da shi yanzu a bakin gate, kinyi shiga kamar ba musluma ba "
gaban ta ne ya faɗin, dan bata yi tunanin wani ya ganta ba ,duk dan kar a ganta ne yasa tabiyo ta ƙaramin gate, kenan tanan shima ya biyo kuma hakan na nufin shazim ya ganta,ya salam, ƙatse mata tunani yayi ta hanyar cewa "tambayar ki nake? "
kame kame ta fara"am.... imm dama wani class mate ɗina ne "wanka mata mari mansoor yayi, ai ba shiri tayi bayan innah tana kuka, mansoor ne ya ɗaura da cewa  "ni zakiyi ma ƙarya,saboda kin rainani, ban hanaki bin wannan ɗan iskan yaron ba,saboda ban isa in faɗa maki kiji ba shine kuka koma haɗuwa waje yana ajiye ki a baya dan kar wani ya ganki ko"fashewa ta sake yi  da kuka tana faɗin "dan Allah kayi haƙuri, wlh ba shi bane " hannu mansoor ya kai zai jawota daga bayan innah, kakkare ta innah tayi tana faɗin "wai miye haka mansoor so kake kaji mata ciwo ne, to wai ma miye a ciki dan ta kula shi kai waya san adadin matan da kake kulawa"duk wannan budiri da ake shazim na zaune yana daddana wayar shi hankali kwance kamar baya ɗaki,mansoor ne yace
"wlh ko mi feenah tayi laifin ki ne innah, tun da ke ke goya mata baya "
"eh na goya mata bayan sai aka yi yaya, da Allah ni ku tashi ku bani wuri"
"haka zaki ce innah? "
"Eh haka na ce, sai akayi yaya"
"to shikenan "shine kawai abun da mansoor ya ce yaja hannun shazim suka fice, da harara innah ta rakasu har suka fice , suna fita ta rufe feenah da faɗa ta inda taje shiga bata nan take fita ba, haƙuri take ba innah akan bazata sake ba insha Allah
"wannan kuma ke kika sani, kar Allah ma yasa ki daina, dan ni ba ruwana tun da duk abu da nake faɗa maki bawai yana shiga kunnen ki bane, abun da kikaga dama shi kawai kike yi"
"dan Allah kiyi haƙuri innah  wallahi  bazan sake ba, yan zun ma ban san zasu ganni bane "
"karma ki daina, kina ji kina gani zakiyi ma kanki tsiya da kanki, kuma wallahi muddun baki shiga cikin hankalin ki ba, shi wan da kike son kinaji kina gani zaki rasa shi, a banza"
"insha Allah na daina "
"da dai ya fiye maki ".

Shazim suna fita daga part ɗin innah part ɗin su ya wuce shi da mansoor
a parlorn shi suka ya da zango, mansoor ranshi duk a ɓace saboda feenah yasha hanata mu'amula da wannan saurayin amma ta ƙi daina wa saboda yasan halin yaron ɗan isaka ne amma bata ji,ga shigar banza iri iri ta iya,  ta kasa gane abun da yake nuna mata,shazim ne ya fito daga bedroom ɗin shi ya cire kayan da yasa daga shi sai boxer da vest, dafa kafaɗar mansoor yayi yana faɗin "lafiya, tuna nin mi kake"ajiyar zuciya mansoor ya sauke yana faɗin "wallahi banajin daɗin abun da feenah take, ita kuma innah sai goya mata baya take "
"haba bro miyasa zaka damu kanka, duk fa wani abu da take laifin innah ne kuma uncle na gani"
"hakane shazim, amma da ban haushi kwata kwata innah bata kyautawa, ace yarinya na aikata ba dai dai ba amma ta hana a tsawatar mata "
"gaskiya kam bata kyautawa, amma da Allah ka share da komi ka je ka watsa ruwa "
"ok to shikenan "ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi hanyar fita yana faɗin "sai na dawo "
"ok sai ka dawo" shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi bedroom ɗinshi, toilet ya shiga bayan 5 minute sai gashi ya fito sanye da bath robe, dressing mirror ya nufa mai ya shafa ma jikin sannan ya fesa turare bakin bed ɗin shi ya dawo haɗi da ɗaukar wayar shi yayi dialing number ammy, tana fara ringing tayi picking, sallama yayi sannan ya gaishe da ita, on the other hand ta amsa mashi cikin kulawa haɗi da tambayar shi ya su innah da su uncle ahmad, amsa ya bata da suna nan lafiya lau, sannan ta tambaye shi sun faɗa mashi dalilin kiran shi da sukayi
amsa ya bata da "a'a basu yi faɗa man  ba"
"to shikenan, ina auta da me babban suna? "
"auta na part ɗin uncle Ibrahim wurin sa'ada, mai babban suna kuma na part ɗin uncle ahmad wurin mahmud, ni ka ɗai suka bari "
"a'a kaima laifin ka ne, ai da sai ka sauka wurin mansoor "
"a'a nafi jin daɗin zama ni ka ɗai ne "
"to ai kaika sani " sun ɗanjima suna waya sannan sukayi sallama, malam ya kira suka gaisa har da ummy, shima malam sun ɗan jima suna tattaunawa sannan shima sukayi sallama, kwanciya yayi kan bed ɗin cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi, hara sai da mansoor ya zo sannan ya tashe shi suka wuce masallaci saboda anfara kiran sallar magrib, sai da suka tsaya akayi har  isha sannan suka fito, daga masallaci part ɗin uncle Ibrahim suka shiga, a part ɗinshi suka same shi, bayan sun gaisa ne yake tambayar sunyi maga da uncle ahmad, amsa shazim ya bashi da a'a
"amma mi yasa muke kiran ka ba mu samun ka?? " ɗan sunnar da kai yayi dan bai taɓa tunanin uncle Ibrahim zai mashi magana akan haka ba duk da yasan dole zasu tambaye shi, jin yayi shiru ne yasa uncle Ibrahim cewa "magana nake kayi shiru baka ce komi ba " amsa ya bashi da "bakomi kawai  yana yin  aiki ne" ɗan jin jina kai uncle Ibrahim yayi duk da ya san yana sane yasa ba'a samun shi a waya, amma a fili sai ya ce "to shikenan Allah ya kyauta gaba" da ameen suka amsa, chanza firar uncle Ibrahim yayi zuwa wata, sun ɗan jima  awurin shi dan anan sukayi dinner tare da shi, sai wurin shaɗaya saura suka baro part ɗin,ra buwa suka yi da mansoor  kowa ya nufi part ɗin su, shazim ko daya shiga part ɗin su bedroom ɗinshi ya nufa, laptop ɗinshi ya ciro daga cikin bag ɗin shi ya shiga aiki, ba shi bane ya kwanta ba sai ɗaya saura sannan ya kashe laptop ɗin ya nufi toilet ya ɗauro alwala, ya dawo ya kabbara sallah, ya jima yana nafilfilo sannan ya tashi ya nufi bed ɗin shi bayan ya kashe bulbs ɗin ɗakin, kwanta yayi haɗi da jan blanket ya rufe jikin shi, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awan gaba dashi....

  Episode 24_25

WASHE GARI

tun da safe suka fita shi da mansoor, sai da yamma liƙis suka dawo a gajiye, shazim part ɗin su ya nufa, wanka yayi ya ɗan kwanta, duk da ya san bacci a lokacin bai da amfani, amma haka nan ya kwanta saboda ba ƙarmar gajiya ya kwaso ba, cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi, ba shine ya tashi ba sai gab da magrib, toilet ya shiga ya sake wani wankan da alwala, sannan ya shirya cikin wani farin yadi, ficewa yayi zuwa part ɗin uncle ahmad wurin mansoor, a parlor ya ci karo da mansoor, juyawa yayi suka wuce masallaci, sai da suka yi har sallar isha tukun suka fito daga masallacin, part ɗin uncle Ibrahim suka nufa, aliyu ka ɗai suka samu a parlor yana kallon cartoon, ya na jin sallamar su ya nufi shazim da gudu, ɗaukar shi shazim yayi yana faɗin "sai kai ka ɗai ina su momy "
"tana part ɗin dady "sauke shi shazim yayi yana faɗin "to yayi, tafi ka cigaba da kallon ka " to aliyu yace haɗi da komawa kan sofa ya zauna yan cigaba da kallon shi, mansoor yace"aliyu shazim ka ɗai ka sani ko"
"a'a, ai kai kullum muna tare " murmushi kawai mansoor yayi, haɗi da cewa "ok haka ne, ai shazim ɗin zai tafi zai barni da kai, babu ruwana da kai daga yanzu"
"sorry ya mansoor, wasa fa nake "
"ba wani nan"shazim yace "ƙyale shi kaji, idan zan tafi da kai zan tafi ai, kana zuwa lagos koh" ɗaga mashi kai aliyu yayi yana dariya, mansoor yace "zamu gani ai "aliyu sai tsalle yake zai bi shazim lagos.
sama suka wuce zuwa parlorn uncle Ibrahim, zaune yake shi da momy da alama suna tattaunawa ne, sallama suka yi haɗi da shiga ciki, amsa masu sallamar su kayi, wuri suka samu kan sofa suka zauna,gaishe da uncle Ibrahim da momy su kayi, amsa masu gaisuwar su kayi uncle Ibrahim na tambayar su ya aiki, da Alhmdllh suka amsa, ta shi momy tayi ta fice,fira suke jefi jefi, luqman ya shigo kamar wan da aka jeho yana faɗin dady! dady!! ,binshi suka yi da idanu, mansoor ne yace "lafiya kake luqman zaka shigo wuri ba sallama kamar wanda aka jeho"
"kullum faɗa nake masa saboda ɗabi'ar banza da ta wofi,ko kafiri bai shiga wuri ba sallama bare kai ɗan muslimi, kiran mi kake man haka?" duƙar da kan shi yayi ƙasa yana faɗin "ba komi" bai son yin maganar saboda su shazim daya gani,mansoor da shazim sun fahimci bai son yin maganar ne saboda ya gan su, fahimtar hakan ne yasa uncle Ibrahim cewa "fice to ka bani wuri" ba musu ya kama hanya ya fice,tsaki uncle Ibrahim yaja yana faɗin "lamarin luqman sai adu'a"
mansoor ya ce
"narasa mike damun shi uncle, tun da suka fita karatu waje ɗabi'un shi suka canza"
"hakane, Allah ya shirya"da ameen mansoor ya amsa, shazim dai na jinsu amma baice komi ba, sai da uncle Ibrahim yace" shazim kayi shiru kamar baka a wurin"
"uncle wai ni "
"a kwai wani shazim ɗin ne anan bayan kai "murmushi kawai yayi ba tare da yace komi ba, uncle Ibrahim yana lure da shazim duk wani abu idan ya shafi luqman da feenah to fah ba ruwanshi , ko kau mizai same su .
mansoor ya ce
"uncle bari mu wuce sai da safe, shazim tashi mu tafi" tashi shazim yayi yana cema uncle Ibrahim "sai da safe uncle "
"Allah ya tashe mu lafiya"da ameen suka amsa, haɗi da ficewa suka bar part ɗin, tashi uncle Ibrahim yayi ya fita daga parlorn shima,bedroom ɗin luqman ya nufa, tura ƙofar yayi ya shiga, samun shi yayi yana safa da marwa, sai kai kawo yake cikin ɗaki, a hanzarce ya juyo jin an buɗe kofa , ganin mahaifin shi ne yasa ya nufe shi da sauri yana faɗin "dady daman wannan cp dake bincike ne ya kira ni yace sun samu idan suke sai dai basu da tabbaci, amma suna nan suna bincike da sun tabbatar zasu kira ni, ya kira wayarka baka yi picking ba shi ne ya kirani, shi ne nazo faɗa maka ban san wannan ɗan rainin wayau yana nan ba shi da ya mansoor "
uncle Ibrahim yace "ok,wayar tana bedroom ɗina ne ban san ya kira ba, naji daɗin jin haka"
"dady yanzu zaka mai do man da motata da ka amsa ko"
"cewa nayi sai sun bayyana sannan"
"pls dady "
"kama bar bani haƙuri, dan ba baka zanyi ba har sai na gansu ido da ido tukunnan, kaga daga yau idan na saka ka abu ba zaka sake shashanci ba"
"dan Allah dady ka bani, insha Allah hakan ba zata sake faruwa "
uncle Ibrahim yace
"ni kaga tafiya ta , daga yau sai ka kiyaye " yana gama faɗa ya fice daga ɗaki.

Suna fita daga part ɗin uncle Ibrahim, part ɗin su shazim suka nufa, a parlor suka ya da zango, wayar mansoor dake cikin aljihun wandon shi ce ta fara ringing,ciro ta yayi yana kallon screen ɗin wayar baby shine sunan mai kiran shi , murmushi yayi haɗi da picking yana faɗin "sorry beb, yanzu nake shirin kiran ki" muryar mace ce tace "bawani nan, da ban kiraka yanzu ba da ba zaka kirani ba "
"haba dear ya zaki ce haka, kin san da ace na gama abun da nake da zan kira ki"
"uhmm dama haka zaka ce "
"haba dear, pls kiyi haƙuri "
tsaki shazim yaja yana faɗin"rainin wayau" hararar shi mansoor yayi yana nuna shi da ɗan yatsa, taɓe baki yayi haɗi da cewa "rainin wayau mana, ka zauna ƙaramar yarinya ta maida ka kamar wani wawa" harara kawai mansoor ya maka mashi ba tare da ya ce komi ba ya cigaba da wayar shi.
hannu yasa ya riƙe kunnan shi yana faɗin "afuwan na kama, bazan sake ba pls " ta shi shazim yayi ya fize wayar daga kunnan mansoor yayi rejecting,da kallon mansoor ya bi shi , rasa mi ma zai ce mashi yayi, gaba ɗaya ya kashe shi da mamaki sai kace shi akace ya kama kunne, komawa yayi mazaunin shi ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai wani cin magani yake, matsowa kusa da shi mansoor yayi yana faɗin "ɗan rainin wayau bani wayata"
"wallahi bazan ba da ba"
"saboda wayar ka ce?"
"ko ba tau bace bazan ba da ba, tunda kai zubar ma kan ka aji ba komi bane a wurin ka ba"
"dallah ka bani wayata, ina ruwanka koma mi zanyi"
"wallahi kaji kunya, wai yarinya zata saka ka kama kunne, kamar wani teddyn wasan ta "
"ko ƴar tsana ta ɗauke ni ina ruwanka tunda ba kai ta ɗauka ba"
"Allah ma ya kiyaye, wane ita sai dai irinku da kuka raina kanku"
"wallahi ina tausayin ka shazim, duk randa so yayi maka mugun kamu, zaka gane baka da wayau"
"haba dai, ko zanyi so ba irin naka ba na rainin wayau "
"indai da rai zamu gani, zaka zo nan ne ka same kana kuka saboda mace"
"Allah ma ya kiyaye, nafi ƙarfin mace tasa na zubar da hawaye, sai dai kai, dan da alama har kuka kake mata"
"uhmmm shazim kenan, idan da rai da lafiya zamu

Please Login or Register in order to submit comment