Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

harara kawai ta bita da ita
Itama harar maryam din tayi hadi da tsaki ta shige  cikin lifter fita suka yi   dama nan suka nufo
"Aikin bazan harara a cikin duhu, yar wahala kawai" maryam ta fada hadi da jan hannun hidaya suka wuce , itama tsakin tayi hadi dacewa "oho dai dr ne dai saina rabata dashi,  kuma kema zan dawo kan kine inna gama da ita"
Haka dai taita ban baminta a banza har ta kai inda zata sauka

A chan kuma hidaya ce ke ce ma maryam "nifa  kinsan  gani nake Victoria kamar bata  da gsky,"
"mikika gani? "Maryam ta tambaya
"bakiga tana ganin mu ba duk tawani sha jinin jikinta,  bayan haka ma mita zo yi floor ɗin  su Dr yanzu ba lokacin fara aiki ba, ni sai nake ganin kamar wani abun tayi"
"Uhmm haka ne kumafa hidaya, ke ita ta sani chan taje taji da rashin gaskiyarta,  si Allah na sama yana kallon duk wani abu da zatayi, koma mi tayi dan kanta hidaya ita da Allahn daya halicceta"

"Wlh kuwa ita da mahaliccinta" hidaya ta fada abun da ya kawo  su suka shiga yi, suka ture zan chan Victoria gefe

Tana shiga  office din su destiny ta samu  da wasu  daga cikin nurses din da suke  zama office din
wurin destiny ta kara sa tana fadin "sister shigowar ki kena? "
"Eh yanzu nazo, nama yi tuna nin bakizo ba sai da  naga ka yanki a locker sannan, amma daga ina haka.? "
"Mufita daga waje na fada maki,  nan kinga mutane,  kuma kinsan su da bakar gulma yanzu zakiji magana wani wuri."
"hakane kuma" destiny ta fada hadi dajan hannun Victoria suka fice daga office din
sai da suka shiga wani dan corridor ku sada office din su sannan Victoria tace"daga office din dr nake"
"kai da gaske kike"
"da gaske nake mana, kaji destiny na taɓa maki wasa ne, daga chan nake"
"Amma ina fatan ba wanda ya ganki  ko, kuma kinyi yanda gurutu yace muyi"
"Sosai ma kuwa, ai kamar yanda yace nayi haka nayi"
"Yawwa yanzu sai dai mu tsaya jiran saka mako kawai"
"hakane kam, kinga mu koma office kar wanima ya fito"
"kumafa haka"
Office din suka koma dumin shirin fita dan da suka shiga office din ba kowa ciki duk sun fita , suma basu wani jima ba suka fice..

✨Hidaya✨

Zaune suke ita da maryam da sauran nurses din asibiti fira suke yi kafin doctors su shigo kowa ya kama  gaban sa zuwa inda yake nasa aikin
suna nan zaune dr shazim ya shigo shi da dr  kabir da Noraiz, yana gaba  su Noraiz na bayan shi
gaishe da su nurses din su kayi  Noraiz da Dr kabir ne kawai suka smsa masu Shazim kuwa hannu kawai ya iya daga masu
Suna zuwa bakin office din shi briefcase dinsa dake hannun Noraiz ya amsa
saboda  shi Noraiz office din Dr kabir zai wuce
Office din ya shiga,  ko ina fes an gyara sai kamshin  fresheners
tarkacen sa ya ajiye saman table hadi da zama kan chair dinsa laptop dinsa ya jawo ya fara  aiki a ciki, nocking    aka yi "Come in" ya ba da izin, hidaya ce ta shigo bakin ta dauke da sallama,  hannun ta riƙe da  file,amsa mata sallamar yayi "GM Dr, dama nace zan iya fara turo patient"
kai kawai  ya daga mata alamar eh "ok" ta fada  hadi da ficewa ta koma wurin patient
wurin 12:00 ya gama  ganin patient din dazai gani time din har Noraiz ya dawo office din ,
"Yaya wai baka da wani abun cine a office dinnan"
Noraiz ya fada yayin da yake bude fridge  dake office din "to a cici ni bana  aje komai daya danganci abinci a eko , zaka iya bari Sai munje abnoor  tukunnan" kwalin lemu ya ɗauka sannan ya
rufe fridge ɗin , yana fadin "bari nasha wannan kafin mu tafi " wurin zaman shi kan sofa ya koma ya zauna hadi da bude marfin lemun, Dr kabir ne ya shigo da sallama a bakin sa  hannun shi ɗauke da  basket din abinci yana cewa "wlh Momma har yanzu kallon yaro take man, wai abinci tasa aka biyo ni dashi saboda kawai banyi breakfast  na fito ba"
"dama ai kai yaro ne" shazim yafa da yana murmushi "haba dai kai ka san wanene yaro wlh"
"ai duk auta yaro ne"da yake kabir shine auta a wurin momman shi
"lallaima Shazim wlh ka rainani" maganar  Noraiz ta katse su yana cewa
"wlh Momma ni ta tai maka kamar  tasan yunwa nake ji" kallon shi Shazim yayi yana girgiza kai da fadin
"wlh Allah ya shiryaka Noraiz, duka ƙarfe  12 amma sai wani complain din yunwa kake, sai kace wani karamin yaro"
"Yaya kasan fa ina fama da ulcer" ya fada yana shafa cikin sa
"bawani ulcer kawai ragon cine"
Shi dai dr kabir binsu kawai yake da idanu yana murmushi
"to yanzu dai ku kale wannan musun, kai Noraiz zo ka zuba abinci kaci" Dr kabir ya fada
dawowa Noraiz yayi kan sofar da Dr kabir yake , plate ya dauka da serving spoon ya buɗe  food flask farar shinkafa ce,  zubawa yayi sannan ya bude dayar flask din wacce pepper   soup ce ciki, duka dai y
sai da ya buɗe  kowane  flask dake cikin basket din sannan ya koma gefe yana ci, Dr kabir ya zuba ma Shazim yana cema noraiz "wato ɗan tsako sami ka ki dangi ko"
dariya kawai Noraiz yayi
"Ok bakin maganar ya mutu kenan" Dr kabir ya fada yana murmushi, shima dai Shazim murmushi yayi yana cewa "baka san waye noraiz ba a kan abinci"  daga nan su kayi shiru kowa na aikin bama cikin sa
sai da suka gama Dr kabir ya nufi fridge ya dauko masu lemu  da ruwa
Shi noraiz ruwa kawai ya amsa  saboda  ya dauko lemu tun dazu sai da suka gama tsab sannan suka tashi shazim Duka tarkacen sa ya haɗa saboda da sun dawo sallah abnoor  zasu wuce shida Noraiz.......

✨Aairah ✨

Alhmdllh jiki yayi sauki sosai dan yanzu haka zaune take parlor suna fira ita da Mom da Aaimah wacce taki zuwa school saboda Aairah bata je ba abie ne ya shigo daga masallachi sallar zuhur wurin su ya nufa zama yayi kan sofar da Aairah take yana faɗin    "ah lallai jiki yayi sauki Masha Allah" hadi da shafa kanta
Mom  tace"Jiya kana part ɗinka  da ka ga budirin yin allura"
abie yace "Allah dai ya shirya yaran nan da dan bazan tsoron allura, a haka zaku zama Drs din da ku ke so kuna tsoron allura"
Aaimah  tace"duk da haka abie muna iyawa Allah"
abie yace "to Allah dai yasa"
Aairah tace "ameen abie"
sun jima suna fira har wurin ƙarfe 3:00 sannan suka tashi

✨ Shazim ✨

Yau da wuri suka  bar abnoor  saɓanin kullum da sai yayi sallar magrib da isha sannan ya ke ko mawa gida, duk da  yanzun ma ba gida suka nufa ba gidan malam suka nufa domin sukara duba jikin sa 
Zaune suka same shi a parlorn shi yana duba littafi, sallama su kayi hadi da shiga cikin ,  cikin parlorn  amsa masu sallamar yayi yana tambayar  su ya aiki,  da alhmdllh suka amsa mashi
Shazim ya ce"ya ƙarfin jiki"
"Masha Allah jiki alhmdllh , yanzu ko ina ina iya  zuwa alhmdllh "
"Masha Allah Malam Allah ya ƙarl sauki da Nisan kwana mai amfani"
"Ameen ya Rabbi"
"Malam kodai lokaci ne yayi, muyi shirin cin gumba" noraiz ya fada yana dariya
dakkuwa malam yayi mashi "lallai nuraddeen  ni kake ma fatan Mutuwa koh, to sai dai mahaifiyar ka ta mutum amma bani ba, ja irin banza"
dariya Noraiz ya kwashe da ita yana fadin "yanzu nan malam baka san mutuwa"
Shazim dai na gefe yana jin su in ban da murmushi ba abun da yake
"mutuwa na kan kowa nuraddeen , yaushe musilmin kwairai zai guji mutuwa, kawai dai ana tsoron mi za'a riska in an je chan"
"haka ne kam Malam, Allah dai yasa mu  mutu muna masu Imani"
da Ameen suka Amsa su duka , nan mlm ya shiga yi masu nasiha a kan ruƙo da gaskiya da kuma aiki da ita da tsare mutuncin kai, sannan ya ƙara yima shazim fada a kan  ya fitar da mata  yayi Aure shekarun sa ƙaruwa suke ba raguwa ba,  kuma mahaifiyar su bata da wani buri daya wuce taga ta aurar dasu baki daya shine kwanchiyar hankalin ta, saboda dangin mahaifin su gani suke kamar ita da malam suka hana shi  yin aure, "Shazim ko baka so naga jikokin jajirtaccen jika na ne" duƙar da kanshi yayi ƙasa yana cewa "ba haka bane Malam, Insha Allah zanyi kokari nayi nan kusa"
"to Allah ya yarda, ya kuma za ba maka mace tagari kai da ɗan uwanka, itama fatima Allah ya bata miji nagari"
da ameen suka amsa su duka har da ummy   wacce shigo war ta kenan parlorn taji suna adu'a shine itama ta amsa da ameen.gaishe da ita su kayi , cikin kulawa ta amsa tana tambayar su ammy,  shazim  maganar kasuwancin shi da yake son noraiz ya cigaba da kula da su yayi ma malam da noraiz ɗin kan shi, "eh wannan shawara ce mai kyau,dama ya kamata ka rage ma kanka wasu abu buwan,"
"hakane,  dama jiran dawuwar sa nake
na tattara komi na miƙa masa "
"yayi hakan Allaha ya tai maka,amma ko da noraiz ɗin ya amsa ka bar hameed su cigaba da kula tare, duk da noraiz abun da ya karanta kenan, zai ƙara samun wasu daba ru wurin hameed"
"eh daman shawarar da na yanke kenan"
"to Allah ya tai maka"da ameen suka amsa
sun jima  sosai gidan malam dan sai wajen Karfe 10 na dare  sannan suka tafi gida ,  mlm ya sha maganin sa , kuma yana sa shi bacci .
Suna shiga gida parlorn Ammy suka nufa inda anan suka sameta ita da  Fatima zaune sallama suka yi , amsa masu Ammy tayi tana cewa "nayi tuna nin baba ya rike ku chan ku sai kwana,  ashe zaku dawo"
"Wlh kuwa zamu dawo, ya gida"
"gida alhmdllh gashi nan"
fira suka ɗan taba Ammy nace masu ga dinner din su chan kan dinning  suka ce sun koshi dan sun ci dinner gidan malam
basu  jima ba kowa ya nufi dakin sa saboda dare da yaja sosai.....

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wataran dadi wataran akasin haka su Aairah sun fara zana jara bawar gama secondary school  har sun  kammala, haka zalika fatima ma ta gama  Noraiz  watan shi 2 da sati 3 da dawowa kenan.  

Zaune  ammy take bakin bed, wayar tace da ke kan bedside ta fara ringing ɗaukra wayar tayi tana kallon mai kiran, ya ahmad shine mai kiran, dafe kan ta tayi tana faɗin ya salam, Allah ya sa bawani abun bane, picking tayi haɗi da kara wayar a kunne tana sallama, amsa mata sallamar na ciki wayar yayi, gaisawa suka yi, tana tambayar yasu hajiya asiya ds su kairiyya, da lafiya lau ya amsa mata sannan yace"wai aisha mi kuke nufi ke da shazim ne, tun yaushe nake faɗin idan na kira shi bana samun shi"
"kayi haƙuri yaya, tun ranar da kakira na faɗa mashi ya kira ka, na yi tuna nin ya kira"
"yaushe zai kira, kar mi mashi maganar da ya tsana, ko ba mu kai matsayin da za muyi mashi ita ba"
"ba haka bane yaya, dan Allah kayi haƙuri, zanyi mashi magana ya kira ka  yau"
"to, daman na kira ne dan in faɗa maki ina son ganin shi shi da ƴan uwan shi cikin wannan watan"
"to yaya, zan faɗa mashi"
"to shikenan, sai anjima"
"to Allah ya kaimu"da ameen ya amsa haɗi da yin rejectin, a jiye wayar ammy tayi tana faɗin" na rasa gane halin shazim, idan har bai jaman abun magana ba wurin su hankali shi baya kwanciya, amma na san maganin shi ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi part ɗin shi, yana parlor zaune,  tambayar shi tayi ina wayar shi, "gata nan ammy, lafiya"
"kira ya ahmad yanzu nnan "
"amma ammy mi yasa"
"zaka kira shi kukuwa sai ka gama tambaya ta dalili"
"A'a kawai yace haɗi da ɗaukar wayar yayi dialing number uncle ahmad, tana fara ringing, aka ɗauka, sallama yayi haɗi da cewa "ina wuni uncle "da lafiya lai uncle ahmad ya amsa, sannan ya ɗaura da cewa "shazim laifin mi muka maka da idan mun kiraka baka ɗauka, kuma kai bazaka iya kiran mu ba? "
"bakomi uncle "
"to shikenan, ina son ganin ka abuja kai da ƙannan ka cikin watannan"shiru yayi baice komi ba, uncle ahmad ne yace "baka ji mi nace ba ne "
"A'a naji, amma uncle aiki na ya zanyi da shi"
"Ina sauraron zuwan ku kana ji na ko"
"eh naji" rejecting uncle ahmad yayi batare da ya saurari mi shazim ɗin zai sake cewa ba,
"sai ku shirya kai da su"
"haba ammy, ni bazan je ba "
"to wallahi bari kaji bazaka dinga ja man zagi ba wurin su kaji na faɗa maka, gara ma tun wuri ka shirya ku tafi"
"to, amma sai next week "
"Allah ya nu na mana"ammy ta ce haɗi da ficewa ta bar part ɗin ..... 🖊


Episode

    13
   
✨Noraiz-Fatima✨

zaune suke  parlorn Ammy, fatima na duba wani novel  yanzu ba school  sai Islamiyya,  shikuma yana aiki a laptop ɗin  sa, aje novel din tayi tana cewa
"ya noor  ka kuwa tuntubar man big bro maganar school  ɗin   dan Allah " ture laptop ɗin  yayi yana cewa "kima bar wannan maganar , dan wlh yace kusa da Ammy za kiyi karatu , ki tambayi  Ammy ma a ga banta yace haka, har sa baki tayi amma yace a'a"
"hai wai shi ya Shazim miyasa yake haka dan Allah , to yaya ita Ammy mi zai hana tace sai nayi "
"kawai kiyi haƙuri  kiyi karatun ki anan a kwai makarantu masu kyau kamar na can zaki samu duk abun da kike so, kuma na san zai sama maki mai kyau da tsada"
"ya noor ya zanyi dole na hakura, Allah ka ɗai  yasan da lilin sa na hana ni"
"nasan bazai wuce saboda innah ba ya hanaki "
"anya dai,  Allah yasa haka alkairi ne"
"ameen "Noraiz ya faɗa 
(Suna da saurin fahimtar dan uwansu saboda sun ɗauke  shi tamkar mahaifin su da suka rasa tun basu san kansuba,   saba nin wasu yan uwan idan akace mahaifin su baya da rai,  zaka samu insuna son abu dan uwan su yanu na masu illar abun maimakon su fahimce shi, sai kasamu suna kullatar shi a rai wasu harsu kai da faɗin  dan yaga mahaifin su baya da rai shiyyasa yake masu abun da duk  yaga dama,zasu dunga ɗaukar shi a matsayin mai tauye masu haƙƙi 
abu buwa dai iri iri, Allah kasa mana ƙaunar  ƴan uwan mu  da fahimtar su ka bamu ikwan rufa ma junan mu asiri ameen 🙏 )

Ammy ce ta fito daga bedroom dinta tana cewa "yaya da kanwa mi ake shiryawa ne, aketa ƙusƙus"
"sirri Ammy ki zauna ayi dake"
Noraiz ya fada  yana nuna mata  kan sofa,  zama tayi  tana faɗin " ina sauraro kuwa, wane sirrin ne ake shiryawa"fatima tace "ammy maganar makaranta ce"
"mi ya faru "
"bakomi, ya noor ya sanar dani yan da ku kayi da ya shazim"
"hakane sai dai kiyi haƙuri "
"dama ya zanyi ammy dole na haƙura, amma ban san mi yasa ya shazim bai son zama na abuja ba "
"nima kaina ban san dalili ba nasan dai bai wuce innah"
sun jima suna tattaunawa kan maganar,  sai ga shazim ya shigo da alama daga abnoor  yake saboda yau friday dama bai cika jima wa ba saboda zuwa masallaci,  wurin su ya nufo ya na faɗin " Ammy ina wuni,  mi a ke shiryawa ne nagan ku zazzune a parlor"
"lafiya lau ya aiki, sirri ne kaima zoka zaune" murmushi yayi yana neman wuri kusa da Ammy ya zauna, gaishe da shi su fatima sukayi noraiz nace wa " ashe dama na bika naga ka dawo  da wuri"
"ai  kafi son zaman gida ne  saikace wata mace, zan ga yan da zaka ƙare idan kafara business "
"ai koh lallai " Ammy ta fada hadi da mangare ma shazim  kai, sosa wurin yayi yana fadin "Ammy haka ne fa, in ba mace ba miya haɗa  namiji  da zaman gida" dariya fatima da Noraiz suka yi ganin yan da shazim ke bata fuska , maka masu harara yayi, shiru suka yi suna ƙumshe dariya, basu wani jimaba suna fira suka tashi domin shirin zuwa masallaci ammy kuma da fatima suka tafi daki domin yin sallah suma....

✨KATSINA✨

Abie ne da abdallah   ke sauko wa daga up stairs zasu tafi masallaci, da Mom suka ci karo a parlor ta fito daga kitchen hannun ta ɗauke  da food flask" Masha Allah irin wannan kyau haka barrister, gaskiya  kar ka sa matan mutane suyi ta kalle man miji" dariya abie yayi abdallah  kuwa duƙar  da kai yayi yana murmushi a zuciyar shi yana fadin " Mom duk da an tsufa amma ana kishi, Allah ya bani mace irin Mom" nace ameen dr
"da har ina cewa zan ƙara maki a bokiyar zama, amma kike faɗin  haka"
"tab wallahi  kaima kasan wasa kake, ai auren mu inkaji ana auren zobe, ba saki ba yaji ba kishiya"
dariya abie ya sake kwashewa da ita yana faɗin  "za kuwa kisan ba wasa nake ba, dan daga nan zance zan wuce" in ban da dariya ba abun da abdallah  ke ma iyayen nasa, yana kallon su cikin birgewa
"ka dai faɗa , nawa jine kawai"
"ai kuwa zaki san bawasa nake ba, kaga abdallah  wuce mu tafi kar mu makara" ficewa su kayi suna jin Mom na masu a dawo lafiya
bedroom ɗin  su Aairah ta wuce bude ƙofar  tayi ta shiga
shiri ta same su suna yi  "yawwa kun shirya kenan"
"eh"suka bata amsa
"yawwa kuyi sauri ku ƙarasa , ga abinci can kitchen mungama,  ku jera kan dinning sannan su mudi ma ku tabbatar kun kai masu nasu nizan shiga nayi wanka ne kunji"
Aairah tace
"ok Insha Allah za muyi yan da kika ce, amma Mom wai ya maganar walimar mune, munga ba'a fara shirin komai ba,  kuma fa jibi ne"
Mom tace" tana nan mana ba jibi bane, jira nake anjima yayan ku ya kaimu shopping ko kuma abie dinku, saimu siyo duk abun da ya dace"
Aaimah tace"to shikenan Mom Allah ya kaimu an jimar" ameen Mom tace hadi da fi cewa daga dakin tana sake tuna masu aikin da ta sa su, suna gama shirin suka fita domin yin abun da Mom tasa su, suna kammalawa nan main parlor suka tsaya suna kallo
su abie ne da ya abdallah  suka shigo,  sannu da dawowa su kayi masu hadi da gaisawa, amsa masu su kayi abie ya samu kan sofa kusa dasu ya zauna  ya yin da shikuma ya abdallah  ya haye up stairs, fira su qka shiga yi da abie akan walimar da za'a yi masu , sun jima suna fira har Mom ta sauko tana cewa "shiyyasa naga barrister bai shigo ba, ashe kuna nan kun tasa shi gaba da abun da kuka saba watan surutu "
Aairah tace"kai Mom bafa surutu muke masa ba, maganar walimar mu fa mu keyi" dinning Mom ta nufa tana faɗin 
"to yayi,  sai ku taso ga abinci na jiran ku" ta sowa suka yi har da abie suka nufo dinning din, abie nace ma
"Aaimah jeki ki kira yayan ku, kinji"
"to sbie" ta fada hadi da nufar up stairs ta nufi part din abdallah , samun shi tayi yana waya jira tayi sai da ya gama sannan tace yaya kazo mu ci abinci, da to kawai ya amsa mata, ya yin da ita kuma ta fice  tabar ɗakin  ko mawa  dinning din tayi wurin zaman ta na ɗazu  ta koma ta zauna plate taja wanda Mom  tayi serving ɗin  kowa, shiru kowa yayi anata bama ciki hakkin sa, sai da suka kusa kammalawa sannan abdallah  ya sauko ya nufo dinning ɗin,  Mom  tace "lafiya baka fito ba tun time din da aka kira ka"
"Ina wani ɗan aiki ne shiyyasa" ya fada hadi da neman wurin zama ya zauna plate ɗin  abinci Mom ta miko masa, thanks ya faɗa  hadi da dau kar spoon ya fara cin abincin, suna gama wa su Aaimah suka gyara wurin yayin da  su Mom suka koma kan sofa, suma suna gamawa wurin su Mom ɗin  suka dawo,  firar walimar da za'ayi masu suka shiga yi,  basu  tashi ba sai da lokacin sallar asr yayi sannan su abie suka wuce masallaci, suma daki suka shiga domin gabatar da tasu..

mom  ce ta fito daga bedroom ɗinta  jikinta sanye da atamfa ɗinkin  riga da zani da mayafi sai jaka a hannun ta,  ɗakin  su Aaimah ta nufa  samun su tayi duk sun sha abaya black color  sunyi rolling da gyelenta sai side bag da ko waccen su ta rataya sai glass irin na gayu ɗinnan,  shirin fita suke daga ɗakin  sai ga Mom ta shigo "yawwa kun shirya  kenan to ku fito mu wuce abie dinku da yayan ku na waje mu ka dai suke jira" Aaimah tace
"Mom ba kice munyi kyau ba" yan yatsu kawai Mom ta haɗa  al'amar komai yayi,  ficewa su kayi zuwa compound din gidan inda anan suka samu abie da ya abdallah,   shiga su kayi cikin motar ya abdallah  ke driving yayin da abie ke kusa da shi, sukuma suna baya su da Mom,  a dawo lafiya su mudi su kayi masu yayin da abdallah  ya fice da motar suka hau kan titi, wani ƙaton  shopping mall ya nufa dasu, parking su kayi a parking lot dake wurin wanda aka tana da domin masu siyayya, sai da ya gama dai dai ta parking din motar,  fitowa  suka yi,  cikin  mall din suka nufa,  barka da zuwa waiters  su kayi masu,inda ake ajiye cart suka nufa,  guda biyu suka ɗauka,  Aaimah na tura daya tana biye da abie da ya abdallah ,  yayin da Aairah ke tura daya tana biye da Mom,siyayya suka yi sosai,  sun jima  a shopping mall sai da suka tabbatar sun tanadi abun da suka san zasu buƙata  sannan suka nufi wurin biyan kudi, abdallah  ya biya duk abun da suka siya  ma'aikatan wurin suka ɗaukar  masu kayan zuwa booth, 
wurin da ake sai da snacks suka wuce pizza  da shawarma da ice cream     ya abdallah  ya sai masu  daga nan suka wuce  gidan dadi, suna isa bakin gate din gidan ya abdallah  yayi horn, mai gadin  ne ya leƙo,  ganin motar  abdallah  yasa shi  komawa ciki da sauri hadi da bude masu gate, ciki ya shiga da motar parking lot dake compound din gidan ya nufa  hadi da yin parking,  sannan suka fito,booth abdallah ya buɗe, snacks ɗin da suka siya ya ɗauko haɗi da miƙama   su Aairah , cikin gidan suka nufa,  parlor ne dan dai dai matsakaici yasha royal sofas masu kyan gaske , wata yar tsohuwa ce (dadi kenan)  zaune ita da wata mata aƙalla  zatayi kima nin shekara 38 zuwa 40 ( Aunty Rabi kenan, ƙanwar  abie ce,  zaune take  da dadi tun lokacin da Allah yayi ma mijinta rasuwa,  kuma gashi Allah bai bata haihuwa ba shiyyasa ta dawo kusa da mahaifiyar ta tana kula da ita)    sallama su kayi, aunty rabi   ce ta amsa masu sallamar  hadi da cewa "wannan  shi ake kira  tafi da gidan ka, wannan ziyarar bazata haka yaya"
dariya abie yayi hadi da cewa "ke dai bari kawai rabi, munje siyayya ne saboda walimar su Aairah, shine muka biyu ta nan" nan suka shiga gaisawa, wurin  dadi  suka matsa itama suna gaishe da ita amsa masu tayi cikin kulawa hadi da taya su Aairah murnar kammala makaranta da hadda nan suka shiga fira "Muhammad  yaushe ne walimar su yan biyu" dadi  ta tambaya,  amsa abie ya bata  da"  jibi ne Insha Allah"
"to Allah ya kaimu" da  ameen suka amsa , miƙama aunty rabi snakcs ɗin dake hannun su suka yi, amsa tayi tana ma abie godiya,   Aairah  tace "amma dai dadi  zaki zo koh"
"Insha Allahu kuwa, ai audu zai zo ya ɗauke  ni da kansa, koh audu" tafada tana shafa kan  abdallah  dake kusa da ita, ɓata rai yayi yana cewa, "wai dan Allah dadi bazaki daina ce man audunnan ba,  nifa suna na abdallah , ba audu ba" dariya su ka

Please Login or Register in order to submit comment