Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

securityn ku da ɓakar tambaya "
"kai kuma tambayar ce baka so?"
"ni dai ka kira su bana son surutun tsiya"
"ai kuwa sai dai kai ta tsayuwa, dama ba kace wurin mansoor ka zo ba, to mi ya hana baka kira mansoor ɗin ba, shi sai ya kira su   "
"ok dan na kira ka shine zaka ɓata man lokaci, Allah ko ka kira su su barni na shigo  ko na koma in da na fito "
"yo ka kuma "kashe wayar a hashim yayi ba tare da yace komai ba, number ɗaya daga cikin security ya kira  yana faɗin "ɗan rainin hankalin yana iya ko mawa " picking security yayi yana faɗin "good evening sir"ba tare da ya amsa gaisuwar ba yace  "friend  ɗi na na waje ku bar shi ya shi "
"ok sir "security ya faɗa, rejecting kiran yayi, aikin sa ya ci gaba.

security ne ya nufi motar A hashim da ke bakin main gate , baƙar mota ce ƙirar ferrari 250 ta sha tinted, security na ƙara so wa, hannu ya sa yayi  nocking window  motar , sauke glass a kayi a hankali, arba nayi da kyakyawar fuskar ( DR ABDALLAH MUHAMMAD HASHIM , A HASHIM,  BI MA'ANA YA ABDALLAH  ) sanye yake da farin yadi, ya sha ɗinkin zamani, kallon security yayi yace"barka da aiki"
"alhmdllh, dama yallaɓe shazim ne yace ka shigo" ok kawai ya abdallah yace, reverse yayi ya nufi cikin estate ɗin, direct part ɗin uncle ahmad ya nufa, parking yayi a parking lot,dai daita parking yayi, wayar shi ya ciro daga aljihun gaban rigar shi number mansoor ya lalubo haɗi da dialing, bugu ɗaya mansoor ya ɗauka yana faɗin "ka iso ne , kana bakin gate"
"gani a parking lot na shigo ciki"
"ok, ai da ka shigo "
"ka fito dai mu shiga tare"
"ka ji ka sai kace estate ɗin ba ƙon ka ne, gani nan zuwa " ok ya abdallah yace haɗi da yin rejecting,fitowa yayi daga cikin motar ya jingina da ita yana jiran isowar mansoor,  bayan kamar seconds goma sai ga mansoor ya fito, parking lot ya nufo wurin shi,yana iso wa suka yi hogging ɗin juna cike da farin cikin haɗuwa da juna mansoor ya ce"barka da zuwa, ya KT"
"KT alhmdllh yasu abbah da mama "
"lafiya lau suke, kwana da yawa"
ya abdallah yace "alhmdllh "
"ka kira shazim kuwa?" mansoor ya tambaya,  ɗan ya taine fuska ya abdallah yayi yana cewa "rabu da ɗan rainin wayau kawai"murmushi mansoor yayi yana cewa "ai kun fi kusa, da man can ku sababbo ne,sai in baku haɗu ba,  mu shiga daga ciki ku gaisa da mama  mun tsaya a waje muna ta surutu"ok ya abdallah yace, ciki suka nufa,main parlor suka shiga bakin su ɗauke da sallama, kairiyya ce da su fatima  a parlor, jin sallamar su ya sa su wai gowa, ware idanu fatima tayi,tana faɗin "ya dr a abuja" da gudun gaske  ta nufi ya abdallah zata yi hugging ɗin shi tana faɗin "ya dr a abuja, un believable "tare ta mansoor yayi yana faɗin "yau ina ganin ikwan Allah, hugging ɗin sa za kiyi a gaba na "duƙar da kai fatima tayi tana faɗin "a'a yaya nayi missing ɗin shi ne sosai"bin ta da wani kallon mansoor yayi yana faɗin" to sannu " ya abdallah ne yace" rabu da shi kawai fatima " ma tsowa tayi kusa da shi batare da tayi hugging ɗin shi ba tace "ya dr, nayi mamki sosai, dama kana abuja shine ko ka faɗa man zaka zo bayan ka san ina abuja "
"sorry fatima , na ƙi faɗa maki ne dan nayi surprise ɗin ki,  ya kike "
"lafiya lau yaya, amma a nan zaka kwana ko? "
"a'a, anjima zan tafi "bubbuga ƙafa fatima ta shiga yi "haba dan Allah yaya, gaskiya nan zaka kwana" muryar kairiyya su kaji tana cewa "watao ya abdallah fatima kawai ka gani ko, har muke gaishe da kai ni da sa'ada  baka ji ba " murmushi yayi "no ba haka bane kairiyya, ya kike ya kwana da yawa"
"lafiya lau alhmdllh, ya hanya "
"Alhmdllh "
"ya abdallah nima kenan baka ganni ba ko"sa'ada ta faɗa tana turo baki "sa'adatu  sa'ar mata, ya gida"
"lafiya lau ya kt da su mom"
"suna nan lafiya "
mansoor ne ya ja hannun shi yana faɗin "mu shiga ciki ka zauna, idan ka biye masu za ku kwana ne a tsaye "bin bayan mansoor yayi har cikin parlor, zama yayi kan sofa, kusa da shi fatima ta zo ta zauna, sai sakin murmushi take kamar gonar auduga, ba ƙaramin farin ciki tayi ba da ganin abdallah ( su fatima ba zama, yau gata ga ya dr )
ya mansoor ya ce "sa'ada shiga kikira mama "da to ta amsa haɗi fa nufar bedroom ɗin mama, ta shi kairiyya tayi zuwa kitchen  "ruwa da lemu ta   kawo mashi " sake komawa kitchen ɗin tayi sai gata ta fito ɗauke  da wani bowl ci ke da yankakun fruit ta ajiye gaban shi, tnxs yace haɗi da ɗaukar ruwa ya sha,fitowa sa'ada tayi mama na bayan ta har suka iso parlor, zama mam tayi kan sofa,"abdallah yau kai ne a garin namu "
"eh mama, ina wuni, na same ku lafiya"
"lafiya lau abdallah, ya su momyn ku da uncle ɗin ka  "
"lafiya lau su ke "
" masha Allah " ta shi mama tayi ta koma ɗakin ta, kairiyya ma tashi tayi ta dalilin kiran wayar ta da a kayi, ya rage parlorn daga mansoor, abdallah, fatima da kuma sa'ada, sai zuba mashi fira fatima take wani ya bata amsa wani kuma yayi murmushi, sun ɗan jima tare da su fatima har aka fara kiran sallar magrib, sannan su ka shiga ɗakin kairiyya do min gabatar da sallah su kuma suka nufi masallaci,a can ya abdallah su ka haɗu da shazim, yi yayi kamar ma bai gansu ba, murmushi kawai mansoor yayi yana girgiza kai, ya san shazim yana wannan fushin ne saboda Abdallah ,  bayan an sallame sallah, suka fito daga masallacin,tsayawa su kayi har sai da uncle ahmad da uncle Ibrahim su ka fito abdallah ya gaisa da su, suna tambayar shi su mom da abie "suna nan lafiya "
uncle ahmad ya ce "masha Allah, ya uncle ɗin ka "
"yana nan lafiya "
"ina gaishe da shi "uncle ahmad yace, tafiya su ka yi shi da uncle Ibrahim,  sai a lokacin abdallah suka gaisa da shazim,ta fiya suke shazim  na faɗin "ai nayi tunanin tun tuni ka tsufa da komawa gidan uncle"
"ɗan rainin wayau ai ba dan kai na shigo ba"
"hmmm koma dai miye, sannun ka da zuwa,  ya hanya  "
"yawwa, Alhmdllh, ya kwana biyu  "
"Alhmdllh" ya faɗa a dai dai time ɗin da su ke kawowa part ɗin su shazim , ciki su ka shiga ba kowa a parlor,dama shazim ne ka ɗai ke zama part ɗin,noraiz da man tun ranar da suka zo ya koma part ɗin uncle Ahmad da zama,  direct sama su ka nufa part ɗin shazim, a parlor su ka ya da zango, abdallah na cewa "wai shazim yau she zaka je katsina "
"zanje insha Allah, amma saboda mom da abie zani amma ba dan kai ba "
"ya kamata dai, har yanzu fa mom bata sanka ba, gara ma abie kun taɓa haɗuwa sau ɗaya" mansoor ya ce "gaskiya baka kyauta ba, ace duk tsawan shekarun nan baka taɓa zuwa katsina ba, gaskiya nayi mamaki"
shazim ya ce "to ni dai ya isa haka kar ku cinye ni, katsina dai ce ko to zani inasha Allah " Allah ya yarda, suka faɗa, fira su ka shiga ta yaushe gamo, sai da aka kira sallar isha sannan su ka tashi su ka nufi masallaci, bayan sun fito daga masallaci part ɗin uncle ahmad su ka nufa, suna tafiya shazim yace "amma zaka kwana nan ko"
"a'a komai dare sai na koma gidan uncle "
"pls ka kwana nan"
"sai ranar da kaje katsina sannan zan kwana nan"
shazim ya ce"kai ka sani kuma wannan, kar Allah yasa kwana " time ɗin da su ke shiga cikin main parlor,  kamar ɗazu ma fatima da sa'ada su ka samu a parlor suna kallo,sallama su kayi, amsa masu sallamar su kayi , sama mansoor ya wuce ya bar su a parlor "ya dr har na yi tuna nin ka tafi" fatima ta faɗa
"ina nan ban tafi ba"
"zaka kwana nan ɗin"
"a'a yanzu zan tafi "
"dan Allah ya dr ba dan ni ba " sa'ada ma tace "pls yaya,mi yasa ba zaka kwana ba "
"ba komi sa'ada " fatima tace "pls ya shazim kasa baki dan Allah ya kwana"
" idan ya kwana wani abun zai maki ne? "
girgiza kai fatima tayi tana faɗin "a'a kawai dai naga mun  daɗe ba mu haɗu ba " 
" to tun da babu abun da zai maki karki damu mutane" kwal kwal fatima tayi da idanu alamar kuka, kallon shazim abdallah yayi yana ta ɓe baki yana faɗin
"kar ki damu zan dawo gobe insha Allah "
"pls ka kwana dai dan Allah"
"shikenan fatima zan kwana saboda ke " taɓe baki shazim yayi yana faɗin "aikin banza "
abdallah ya ce "wannan kuma kai ta shafa, ɗan rainin wayau " tashi fatima tayi su ka je kitchen ita da sa'ada,
"wallahi kaji kunya wai fatima zata saka kwana "
"ina ruwan ka kuma " tsaki shazim yana faɗin "girma dai ya faɗi"
"ya daɗe bai faɗi ba" mansoor ne ya fito "ina ta jiran ku shigo, naji ku shiru" ta shi su kayi su ka bi bayan mansoor ba tare da sun ce komi ba, a parlorn shi suka zauna, fira suke cikin kwanciyar hankali, nocking su kaji, mansoor ne yace wanen,"fatima ce yaya, " ok shigo kawai mansoor ya faɗa, turo ƙofar su kayi ita da sa'ada kowace  hannun ta  ɗauke da tray, kan center table su ka ajiye fatima na faɗin "ya dr ga dinner "tnxs abdallah  yace, ficewa su kayi ita da sa'ada, mansoor ne yayi serving ɗin su. kan carpet su ka zauna suna cin abinci, da suka gama mansoor ya kira fatima ta zo ta kwashe dishes  ɗin, fira su ka ɗan taɓa, sai wurin 9:30 su ka yi mansoor sallama su ka nufi part ɗin su shazim, suna tafe suna fira,suna kawo bakin part ɗin su shazim, mota ce shararo da gudu  ta shigo estate ɗin ta ƙaramin gate,bin   motar su kayi da kallo har tayi parking a part ɗin uncle Ibrahim, mace ce ta fito daga motar, jikin ta sanye da hijab har ƙasa,fuskar ta da  face mask ,cire face mask ɗin tayi,  tazo ta gaban su zata wuce,taɓo shazim abdallah yayi yana faɗin.......




Episode 28_29

..................... Taɓo shazim Abdallah yayi yana faɗin
"dude wannan ba ɗiyar uncle Ibrahim bace feenah" yayi maganar yana nuna ma shi ita lokacin da zata shiga part ɗin su, sauri kawai take bata ma lura da su ba
kallon sosai  shazim yayi, sai a lokacin ya gane ta , ce wa yayi "ita ce, wani abun ne? " girgiza ya Abdallah yayi yana faɗin "amma daga ina take a wannan lokacin, sai kace ba mace ba "
amsa shazim ya bashi da "sai ka bita ciki  ka tambayeta, tun da ka fara aikim jarida ban sani ba " murmushi ya Abdallah yayi yana cewa "kai fa matsalar ka ke nan, daga tambaya sai ɓakar magana" shazim ya ce "ai kai ne da shiga abun da ba ruwan ka, ni ina zan san daga ina take "
"dole nai magana, naga ƙanwar ka ce"
"duk da ƙanwa tace, ban san daga ina take ba a wannan lokacin ba, kuma iyayen ta suna sane" ya faɗa haɗi da jan hannun Abdallah yana faɗin "dan Allah ma wuce mu shiga ciki, kasa mun tsaya muna maganar da bata da amfani "ciki su ka wuce,a bedroom ɗin  shazim suka yada zango , zama Abdallah yayi kan bed, shazim kuma ya shiga toilet,Abdallah  wayar shi ya ɗauka yayi dialing number uncle,  ahmad bugu biyu ya ɗauka, tun kafin Abdallah yace wani abu uncle ahmad yace "Abdallah lafiya baka dawo ba har yanzu "
"a nan zan kwana ne uncle "
"ok to shikenan, sai da safe"
"Allah ya ta she mu lafiya" da ameen uncle ya amsa, rejecting ɗin kiran Abdallah ya yi, fitowa shazim yayi daga toilet jikin sa sanye da bath robe , clothes set ɗin shi ya nufa, pajamas ya ɗauko ash color ya sa, ta shi Abdallah yayi shima yayi wanka, pajamas shazim ya ɗauko mashi white color ya sa kwanaciya su kayi suna fira sama sama har bacci yayi awan gaba da su.

washe gari
tare da mansoor su ka dawo part ɗin daga sallar subhi
fatima da sa'ada ne su ka kawo masu breakfast.

✨LAGOS✨

EKO

zaune su ke a reception maryam ce ta kalli hidaya tana faɗin "wai har yanzu dr jikin ne yasa bai zo hospital ba tsawan wannan kwanakin" ɗan nisawa hidaya tayi sannan tace"maryam nima ban sani ba, gashi ina kiran shi bai taɓa ɗauka ba, amma ina tuna nin dan yaga baƙuwar number ne yasa bai ɗauka"
maryam tace"ba mamaki, may be shima yana cikin mutanen da basu ɗaukar baƙuwar number, Allah dai yasa lafiya, kwana biyu da bai zo ba ameen " hidaya tace "har nayi tunanin tambayar dr kabir sai kuma na fasa, kar yayi tuna nin wani abu "
"a'a da kin tambaye shi, ba abun da zai yi tunanin, tun da yasan dr boss ɗin ki ne kina da right ɗin da zaki tambayi lafiyar shi "
"haka ne kuma, idan naje office ɗin shi anjima zan tambaye shi naji, wallahi duk na damu da rashin shi  kwana biyu,fata na dai ace yana lafiya"
"insha Allah lafiya lau yake "
"Allah ya yarda " da ameen maryam ta amsa, canza firar su kayi zuwa wata, har lokacin da zasu fara aiki yayi kowa ya tashi ya nufi aikin gaban sa, hidaya tattara files ɗin patient tayi ta nufi office ɗin dr kabir, bakinta da sallama ta shiga, zaune yake yana du ba wasu paper's, gaishe da shi tayi tana faɗin "dr ga files ɗin patient, za su iya fara shigowa "
eh ya bata amsa,haka ta shiga tura mashi patient har lokacin sallah yayi, da katawa yayi ya nufi masallaci domin yin sallah, sai da ya dawo daga masallaci hidaya ta same da tambayar dr shazim, cewa kabir yayi "a fuwan ban faɗa maki ba, yana abuja ne wurin uncle's ɗin shi, shiyyasa ki kaga  
kwana biyu baya zuwa, amma ba kin amshi number shi ba ai da kin kira shi "
"eh, idan nakira ne baya ɗauka "
"gaskiya ba zai ɗauka ba dan ba kasafai yake ɗaukar baƙuwar number ba ba, amma nasan insha Allah next week zai dawo "
"to Allah ya kaimu nagode "
"ba komi "dr yace, ficewa tayi daga office ɗin ta koma reception wurin maryam, sanar da ita tayi yanda su kayi da dr kabir, maryam tace "dama duk yawan aikin da dr yake da shi, har yana iya barin garinnan da sunan ziyara ba aiki ba "
"to aiko gashi nan " hidaya ta faɗa, maryam tace "wai nikam na tambaye ki mana?"
"ina sauraron ki" hidaya ta faɗa
"kin kuwa tura mashi text ɗin da muka yi magana da ke "
"na tura mashi ma"
"kai aikuwa ina ganin shine dalilin da yasa da ki ka kira shi bai ɗauka ba"
"a'a gaskiya, saboda da number mama na kira shi, kawai dai baya ɗaga baƙuwar number ne"
"Allah dai yasa ya karanta "
" zai yi wahala ace bai duba ba  "
"haka ne "
"kar ki damu, ki cigaba da tura mashi nasan wataran zai du ba "
"to Allah ya sa " da ameen maryam ta amsa, tashi su kayi suka nufi office ɗin da suke zama, suna shiga tar kacen su su ka haɗa domin lokacin tashin su yayi.

✨KATSINA✨

Abie ne da uncle mustafa a garden suna tattaunawa game abokin abie da za'a sallama daga asibiti zai dawo nigeria, uncle mustafa ne yace "yau she safwan ɗin yace zasu sallame shi"
"yace man next week su ke sa ran a sallame shi "
"to Allah ya kai mu next week ɗin" ameen abie yace
" amma yaya kana ganin ko a nan baza su iya bibiyar shi ba "
"insha Allah baza su taɓa sanin yana raye ba, har sai lokacin da asirin su zai tonu, su duk a tunanin su ya daɗe da mutuwa "
"Allah dai ya toni asirin mutanen nan, sun cutar wannan bawan Allah kamar mi, da da ƙarar kwana da tuni sun kashe shi "
"haka ne yaya shi da yake mahaifin safwan kwanan shi sun kare  ,ai sun kashe shi"
"kisa na wulakanci ma ,amma ai Allah na nan zai toni asirin su tun a nan duniya kafin kiyama "
"haka ne kam "
Abie tace"burina bai wuce naga memoryn shi ya dawo ba,da a ce lokacin da na mai da shi China na rika bibiyar iyalin shi da ko baya nan zan iya hada hujjujin da zan maka su court ,amma yanzu dole sai yana cikin hayyacin shi zan iya hada duk wata hujja da nake nema "
"haka ne kam dole sai ya dawo cikin hankalin shi ,Allah dai ya bashi lafiya"
"shiyyasa nace idan an sallame shi zan dawo da shi Nigeria,saboda dole sai a nan zai iya ganin abun da zai sa yatuna da baya har a samu memory shi ya dawo"
"haka ne ,amma yaya idan su ka dawo ina zasu zauna"
"shi kadai zai dawo ban da safwan da mahaifiyar shi ,saboda mahaifiyar shi ta tsorata sosai ,ko da safwan din yace zai zauna bazata bari ba  "
"ai dole ta tsorata ,baji bagani aka kashe mata miji,kisan wulakan ci"
Su Aairah ne su ka shigo garden din dauke da  bowl din fruit da ruwa da lemu ,kan table din dake wurin su ka ajiye masu ,suna gaishe da uncle mustaf ,amsa masu yayi yana fadin "anata hutu ko ,ya hutun " da Alhmdllh su ka amsa hadin da barin garden din ,kallon abie uncle mustafa yayi yace"yaushe za su yi joining university ne ,naji wasu makarantun har sun fara lectures "
abie yace "Abdallah nake jira ya dawo daga abuja ,komai na makarantar su yana hannun shi "
"gaskiya ya kamata ya hanzarta ,yaushe ya ce zai dawo "
"yace man dai next week za su dawo shida Ahmad din ,na san ya san wasu makarantun sun fara lectures"
"ya kamata gaskiya ya hanzarta "
abie yace "su matsalar ne sun nace ne akan dole sai sun tafi wani gari ba su son nan"
"da gaskiyar su yaya ,fara su fita inda idanun su zai kara budewa ,ko ba komai zasu iya mu'amula da mutane "
"haka ne ,ni ba komi yasa bana son su yi Mesa dani ba ,kasan halinsu wani lokacin ba jin magana suke ba"
"haba yaya duk rashin jin su sun kai ihsan ne ,amma haka nan na turata jos karatu  duk da a gidan kanwar mahaifiyar ta take da zama ,ka bisu da adu'a kawai ba abun da zai faru da su insha Allah, idan ma tsoron tura su kake inda ba su san kowa ba ,ai ga abuja sai su zauna gidan Ahmad ,kaga duk lokacin da su ka tashi lectures gida zasu dawo"
"hakan dai ne zai fi ,dan zaman hostel ne ban so ,zan kira Ahmad din inyaso kafin su zo sai su  nema masu admission"
" to shikenn yaya  hakan yayi,Allah ya taimaka "

ameen abie yace ,canza firar su kayi zuwa wata ,sun jima a garden din suna tattaunawa har sai da lokacin sallah yayi ,sannan su ka tashi su ka nufi masallaci .

✨ABUJA✨

Momy ce ta fito daga bedroom dinta ,numfashi taja a zuciyar ta tace "wannan kamshin daga ina kuma " kitchen dan tana kyautata zaton daga canne , tana tun karar kitchen kamar  ana huro mata mashi , tun a bakin kofar kitchen take fadin "wai yau mi ake girka  mana ne ,gida duk ya cika da kamshi " ta fada yayin da take Shiva cikin kitchen din ,turus ta tsaya ganin fatima da sa'ada sai kai kawo a kitchen aiki kawai suke bilhakki
"to fah kace yan mata na ne a kitchen,duk su ka ciki gida da kamshi, ashe yau zan ci girkin manya  " fatima tace "yawwa momy daman neman mai testing   muke "
"to a zubo man, naji ƴaƴan nawa sun iya girki"
sa'ada ta shiga  buɗe ma momy  warmers, bin abinci da kallo momy tayi tana faɗin "kai masha Allah, wannan ko bakai testing ba kasan ya yai daɗi " plate da serving spoon sa'ada ta ɗauko ta zuba ma momy fried  rice da cos low spoon ta sa mata haɗi da mi ƙa mata tace " momy gashi "amsa momy tayi ta samu wuri  kan kujerar da ke kitchen ɗin ta zauna,spoon ɗaya tayi, sai kallon su tayi tana zaro ido,faɗuwa gaban su yayi kar ace abicin bai yi daɗi ba sai faɗin "momy miya faru "su ke, murmushi momy ta saki tana faɗin "kai masha Allah, wannan girki naku yayi daɗi sosai masha Allah " rungume juna su kayi suna tsalle suna faɗin "mun gode momy " feenah ce ta shigo tana ya tsine fuska da alama daga bacci take "kukuma lafiya, kuke ta ihu duk kunbi kun addabi mutane "  tsayawa su kayi da murnar da su keyi su kai, sa'ada tace "girki fa mu kai, kuma momy tace yayi daɗi, shine muke murna " tsaki feenah taja "girki kodai ja gwal gwalo,ku nan har wani girki kuka iya " hararar ta momy tayi tana faɗin
"ki fara ci kiji kafin ki kushe masu girki " zaro ido feenah tayi tana faɗin "wah ni, Allah ya kiyaye " sa'ada tace
"wallahi Aunty feenah kin dai san munfi ki iya girki "  jinjina kai feenah tayi "ke ni kike faɗama haka "
"yo ai gaskiya na faɗin " duka ta kaima sa'ada da sauri ta ɓoye bayan momy "momy wai daga faɗar gaskiya zata dake ni " dukan ta sake kai mata a bayan momyn, fatima dai na tsaye tana binsu da idanu, riƙe hannun feenah momy tayi "kar ki sake ki dakar man yarinya, koma mi ta faɗa maki ke kija, idan bazaki yabi girkin su ba ai bai kamata ki kushe masu ba"
"amma momy baki ji mi tace man ba "
"koma mi tace, ai ba ƙarya tayi ba, kin iya girkine " ran feenah in yai dubu to ya ɓaci jin momy ta goyi bayan sa'ada
"momy wai miyasa kike haka duk abun da sa'ada zata man idan na ce zan dake ta sai ki hana "
"dole na hana, saboda komi tai maki laifin ki yafi yawa "
"shikenan momy tun da haka ki kace " tana gama faɗa ta wuce fuuuuu kamar zata tashi sama, sa'ada tace azuciyar ta  "nasan daga nan sai part ɗin innah"
babu wanda ya bi ta kan feenah daga momy har  fatima, aikin dake gaban su suka kama, sai da suka kammala komi suka jera abincin kan dinning,Abdallah kuma cikin basket suka jera mashi shi da shazim, dama girkin saboda shi su kayi shi bayan sun gama su ka wuce bedroom ɗin sa'ada domin yin wanka, fatima ta fara shiga wanka sa'ada kuma ta ɗauko masu kayan da zasu sa, fatima na fitowa sa'ada ta shiga , shaf shaf suka shirya su ka fice zuwa kitchen, basket ɗin da suka jera ma Abdallah suka ɗauka, direct part ɗin su shazim suka nufa,tsit part ɗin kamar ba kowa, sama su ka wuce zuwa bedroom ɗin shazim, sa'ada ce tayi nocking shiru ba'a basu izinin shigaba sake nocking ɗin tayi still shiru, fatima tace "ko dai suna part ɗin uncle Ahmad "
"ba mamaki suna can "
fatima tace "amma bari nayi nocking ɗin ɗakin ya noor may be shi yana nan" juyawa tayi zuwa bedroom ɗin noraiz tun kafin tayi nocking a ka buɗe ƙofar , noraiz ne  ya fito   shi da mahmud da alama fita zasu yi, bim su da kallo su kayi noraiz yace "ku kuma lafiya ku kayi curko curko da basket a hannu  "
fatima ce tace "daman su ya dr  muka kawo ma abinci, munyi nocking shiru"
"to ku ajiye kan dinning mana"
"a'a gaskiya ya noor, idan kuma basu dawo part ɗin ba da wuri fa, zai iya yin sanyi "
"to tun da gudun yayi sanyi kuke mu sai ku bamu muci "
"a'a wallahi ya noor, ba fa naku bane, idan zaku ci yana can part ɗin momy" mahmud yace 

Please Login or Register in order to submit comment