Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai shazim yayi ya nufi part ɗin sa domin ba ƙaramin gajiya yayi ba dinner ɗin sa ma sai dai fatima ta kawo masa nan part ɗin sa, wanka yayi ya shirya cikin kayan bacci  white color, parlor ya dawo akan center table ya samu dinner ɗin sa da fatima ta kawo masa, serving ɗin kansa ya shiga yi yana kammala dinner ya wuce bedroom ɗin sa toilet ya wuce ba'afi five minutes ba ya fito jikinsa na danshin ruwa da'alama alwala yayi da brush, wurin wardrobe   ya nufa ya fito da  sallaya shimfi ɗawa yayi, shafa'i da wutiri yayi, ya ɗan jima yana adu'a, sannan  ya tashi ya nufi bed ɗinsa ya hau adu'a yayi sannan ya kashe bulb ya kunna bedside lamp....

Episode

 18  _19

A kwana a tashi babu wuya wurin ubangiji, har an ciye sati da wasu yan kwana ki da maganar tafiyar su shazim abuja, kullum da kalar excuses ɗin da zai ba ma ammy har  dai suka yi wannan kwana kin basu tafi ba, a gefe kuma innah ta addabi ammy kullum cikin kira take akan miyasa ba su zoba har yanzu sai dai ammy ta bata haƙuri, yau ma tun da sassafe ta kirata, tun da ammy taga kiran innah sai da gabanta ya faɗi tasan da tace mata ba yau ba zata rufe ta da cin mutunci, haka nan ta ɗaga wayar kamar yanda ammy tayi zargi hakan ce ta faru dan sosai innah ta cima ammy mutuncin san ranta, baiwar Allah ammy harda kukan ta, tashi tayi daga bakin gado da take zaune ta nufi part ɗin Shazim, bata same shi a parlorn shi ba hakan ne ya sata nufar bedroom ɗin sa tayi nocking buɗe ƙofar yayi, jikin sa sanye da uniform ɗin sa da'alama ma ya gama shirin tafiya hospital ne, ganin ammy tsaye bakin ƙofar bedroom ɗin sa yasa shi mamakin ko lafiya ta zo da kanta maimakon tasa fatima ko noraiz ya kirasa, gaishe da ita yayi, amsa mashi tayi da lafiya, daga yana yin da ta amsa mashi yasan cewa gaskiya ba lafiya, domin tun da yake da ammy bai taɓa ganin ta cikin irin wannan yana yin da ya ganta ciki ba yanzu, kafin ya sake cewa wani abu ya ji tace "wai ni kam shazim yaushe ka zama mara jin magana ne, wai har ace nizan saka abu amma kafi ƙarfin kayi abun da nake so koh" kallon ammy jin abun da  tace danshi aiya sanin shi baisan mi take nufi ba dan shi harga Allah ya manta sunyi wata magana ta zuwa abuja "ammy dan Allah kiyi haƙuri wallahi ban san akan mi kike magana ba" wani irin kallon ammy ta bishi da shi tana cewa"watau saboda kagama rainani shiyyasa ka manta da maganar da mukayi da kai koh, wai nikam Shazim wane irin yaro ne kai maganar zuwa abujar ce ka manta saboda ka raina mutane koh " sai yanzu ya ma tuna da wata maganar tafiya dan shi duk atuna nin shi ammy ta bar maganar ganin ta kwana biyu bata sake yi mashi maganar ba " dan Allah ammy ki daina cewa haka ta yaya zan raina ki dan Allah kiyi haƙuri wallahi yana yin aiki.... " bai ƙarasa faɗar maganar da zai faɗa ba ammy ta da katar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu tana cewa "da kata man bana son jin wani excuse naka, umarni nake baka ba shawara ba kashirya gobe tun da safe ku tafi " cikin rashin jin daɗin  hukuncin da ta yanke yace "dan Allah ammy kiyi haƙuri sai jibi " tsawa ammy ta daka mashi tana faɗin "wallahi kaji na rantse gobe zaku tafi  indai na isa da kai sannan kamar yanda su fatima zasu yi sati biyu kaima sai kayi shi ,  in kuma ban isa ba zaka iya yin duk yanda ka ga dama " tana gama faɗar haka ta juya tafice daga part ɗin, komawa Shazim yayi cikin bedroom ɗin shi ya zauna bakin bed yana dafe kansa dan harga Allah baya son tafiyar nan gashi ammy tayi fushi, bashi da wani zaɓi banda ya shirya kawai gobe su tafi ko hakan zai sa ta sauko daga fushin da tayi dashi, ammy na fita daga part ɗin shi main parlorn ta nufa, noraiz da fatima ta samu kan dinning suna breakfast gaishe da ita su kayi, amsa masu tayi tana tambayar su " kun shirya kayan ku da nace ku shirya? "fatima tace "eh ammy saura kaɗan ingama shiryawa yawale nake jira ya kawo kayan guga sai na gama " ammy ta ce "ok anjima zai kawo daya kawo kishirya su yau  " da to fatima ta amsa,  mai da kallon ta tayi kan noraiz tana faɗin "kai fah ka shirya naka "
"a'a ammy, wai ba anfasa tafiyar ba " kallon shi kawai ammy tayi bata ce komai ba, "wallahi ni ammy da kin haƙura da maganar tafiyar nan, dan ni wallahi bana son zuwa ko dan saboda wannan tsohuwar, tayi ta zagin mutum bayan ba wani abu mutum yayi mata ba, tana faɗin wai dama ba sonta kike ba shiyyasa muma bamu sonta wai da papah na raye bamu isa muyi nesa da ita ba " katse shi ammy tayi ta hanyar ɗaga mashi hannu tana cewa
"ya isa haka,  kar in ƙara jin kace wani abu inba so kake yanzu nan ranka ya ɓaci ba " shiru noraiz yayi ganin kamar ran ammy ya ɓaci.

shazim ne ya sauko daga part ɗin sa ya nufo main parlorn, fuskar shi cike da damuwa,  zuwa yayi wurin  ammy ya durƙusa gaban ta yana faɗin "dan Allah ammy kiyi haƙuri " kau da kai tayi kamar ma bata son ganin shi tayi banza da shi, haƙuri ya shiga bata amma ko ta ɗaga kai ta kalle sa, tashi  yayi daga durƙuson da yayi   yana faɗin"dan Allah kiyi haƙuri,  na wuce office " ko yan zu bata ɗaga kai ta kallesa ba, noraiz ne yace" yaya bazaka yi breakfast ba "ganin shazim ɗin ya nufi hanyar fita batare da ya kalli dinning ba"na ƙoshi "abun da kawai ya cema noraiz, ficewa yayi daga parlorn ko da ya shiga motar shi ya daɗe bai tada motar ba gaba ɗaya baya jin daɗin fushin da ammy ta ɗauka da shi, sai da ya kusan 15 minutes a motar bai tafi ba sannan yayi mata key ya bar gidan ko gaisuwar da megadi keyi mashi shida ilya bai amsa ba ɗaga masu hannu kawai yayi ya fice..
a parlorn kuwa noraiz ne ya taso daga kan dinning ya dawo kan sofa kusa da ammy yana faɗin "ammy wai mike faruwa, naga kamar kina fushi da yaya lafiya " amsa ammy ta bashi da "ba komai tafiya ce bai so kuma dole sai kunyi ta " noraiz ya ce "dan Allah ammy ki janye maganar tafiyar nan ni ban san miyasa kike son sai munyi wannan tafiyar ba,kinsan halin innah bawani son mu take yiba kema kinsani,su uncles ne kawai suka  damu da rayuwar mu lokacin da muke buƙatar  kulawar su " ammy tace "ya isa haka,dama kai da shazim na lura halin ku ɗaya, to tafiyace sai kunyi ta gobe ma bawai jibi ba kunji na faɗa maku "
" ammy gobe fa ki kace "
"ƙwarai kuwa gobe nace, idan kuma ban isa ba sai inji "noraiz ya ce "kin isa ammy, Allah ya huci zuciyar  ki , insha Allah ba zamu sake cewa komai ba game da wannan tafiyar ba, yanzu zamu fara shirya kayan mu goben zamu tafi insha Allah "ammy tace "da ma dai ya fiye maku " ta faɗa haɗi da tashi ta nufi bedroom ɗin ta,  da idanu kawai suka bita, sai da su kaga shigewar ta ɗaki sannan suka kalli juna noraiz ya ce "nifa gani nake kamar akwai abun da ke damun ammy, yan da tayi fushi akan tafiyar nan abun yayi yawa, kawai dai tana ɓoye mana ne, amma alamu sun nuna cewa tana cikin damuwa yan kwana kinnan, kuma nasan hakan da sa hannun innah "ɗan nisawa fatima tayi tana cewa "na daɗe da lura da hakan ya noor, kuma na tambayeta ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba tana ce man wai ba komi, abun da kawai ya ka mata shine mu shirya kawai gobe mu tafi, may be zata huce dan naga tayi fushi sosai"
"haka ne fatima, amma kinsan yaya baya son tafiyar nan "fatima ta ce "amma dole yayi ta ya noor tun da ammy ta nuna ɓacin ranta, na san ko dan haka dole ya tafi " noraiz ya ce" haka ne dan bansan mi ya haɗa su ba naga tana fushi da shi kuma daga part ɗin sa ta ke "
"ina tuna nin tayi mashi maganar tafiyar ne ya nuna bazai je ba "
noraiz ya ce "to ƙila, nima yan tashi zanyi naje na shiraya kayana, dan wallahi  nasan ta wai waye  mu baza mu ji da daɗi ba yanda tayi fushin nan"
"dama ni ya noor tun da tayi magana nashirya kayan ganin ba'a yi tafiyar ba ne yasa na saka wasu daga cikin kayan da zani walimar school ɗin mu"noraiz  ya ce " ki daman murna kike da wannan tafiyar"
"murmushi fatima tayi taan faɗin"ina son zuwa naga sa'ada da ya kairiyya ne kawai"
noraiz ya ce"za kuma ki haɗu da innah guyaba "dariya fatima ta kwashe da ita, tashi yayi yana faɗin "bari     nima tashi  yanzu na kammala shirya nawa kayan   tun da ba inda zani" ya faɗa hadi da tashi ya nufi part ɗin su, tashi ita ma fatima tayi ta nufi nata bedroom ɗin....

   ✨SHAZIM✨

Zaune yake a office ɗin shi ya bar baza ta kardu kan table ɗin shi ya zuba masu ido yana kallon su da alama hankalin shi baya kansu, yayi zurfi cikin tunani ya ji ana nocking, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya bada izinin shigowa, hidaya ce ta shigo hannun ta ɗauke da files, gaishe da shi tayi hannu kawai ya ɗaga mata, ganin hakan ne yasa hidaya fahimtar yau baya san magana dan haka kawai ta matsa kusa da table ɗin ta ajiye mashi files, ɗago da kanshi yayi yana kallonta, fahimtar mi ya ke nufi ne yasa ta cewa "dama files ɗin patient ne dake waje" sai yanzu ya buɗe baki ya ce "kwashe su ki kaima dr kabir, bazan samu damar du ba kowane patient ba  yau" daga ganin yana yin da yake maganar zaka san cewa baya jin daɗin," dr baka jin daɗin ne" hidaya ta tambaye shi, kai kawai ya ɗaga mata,  ɗaukar files ɗin tayi ta fice, direct office ɗin dr kabir ta nufa, nocking tayi aka bata izinin shiga, shiga tayi bakin ta ɗauke da sallama, zaune ta same shi yana aiki a laptop "good morning sir "hidaya ta faɗa, ɗago da kansa yayi yana amsa mata gaisuwar da tayi tana kallon files ɗin sa ke hannun ta"lafiya dai koh hidaya, ina zaki da wannan files ɗin? " amsa ta bashi da "dr Shazim ne yace na kawo maka, bazai samu da mar duba patient ba yau"
"ok ajiye " ya faɗa yana maida kansa kan aikin da yake yi, hidaya tana ajiyewa ta fice daga office ɗin, saida ya gama aikin da yake yi sannan ya miƙe ya fice daga office ɗin, ya nufi office ɗin Shazim, shiga kawai yayi batare da yayi nocking ba, samun shi yayi zaune kan sofa dake office ɗin dafe da kanshi, jin alamar an buɗe ƙofa ne ya sa shi ɗago da kanshi yana kallon dr kabir da ya shigo, amsa mashi sallamar da yayi yayi, ƙara sawa dr kabir yayi haɗi da ne man wurin zama ya zauna kusa da shazim yana faɗin "hi dude, what's wrong with you, naga kasa nurse hidaya ta kai man file ɗin patient " kallon shi Shazim yayi sannan ya ce " am not feeling better "
"ya salam,  mike damun ka " ɗan nisawa shazim yayi sannan ya ce "wallahi ammy ce wai dole sai natafi abuja,  da na kawo mata excuse fushi ma tayi dani " kabir ya ce " to minene aciki da har zaka sama kan ka damuwa irin haka, shawarar da zan baka anan kawai kashirya ka tafi, hakan ka ɗai zai sa ammy ta huce  "
"baza ka gane ba kabir, kwata kwata bana son zuwa abujar nan "
"to ya zakayi haka nan zaka yi haƙuri ka tafi tun da ammy ta ce katafi, yaushe ne tace ka tafi  "
"gobe fah "kabir ya ce "to Allah ya kaimu gobe, kai ka ɗai zaka tafi "
"a'a harda su noraiz "
"ok, Allah ya kaimu goben,  karka wani damu "shazim ya ce "ameen nagode"
"bakomai kar ka damu "
"ina ma tuna nin tashi zanyi na tafi abnoor dan ban gaya ma majeed ba, sannan zan koma gida daga chan"
Kabir ya ce "eh gaskiya ya kamata, da ƙarfe nawa zaku tafi ko dai sai munyi waya "
"ina tuna nin da safe, dan wallahi ammy tayi fushi sosai "
"to Allah ya kaimu "
"ameen " Shazim ya faɗa hadi da tashi ya nufi table ɗin sa ya fara haɗa kayan shi yana maidawa cikin briefcase, yana gama haɗa wa kabir ya taso domin yi mashi rakiya, su hiday na zaune a reception suka zo suka wuce, suna wuce maryam tace "lafiya naga dr ya tashi lokacin tashin shi bai yiba " hidaya ta ce "baya jin daɗi ne, dan koda na kai masa files ɗin patient cewa yayi na kaima dr kabir, ina tuna nin ba zai iya zama ba shiyyasa zai tafi gida " maryam tace "Allah ya bashi lafiya " da ameen hidaya ta amsa, chan maryam tace"kinsan wane tuna nin nayi? " hidaya ta ce "a'a sai kin faɗa " maryam tace "kawo kunnan ki kiji" matsawa hidaya tayi kusa da maryam, magana ta faɗa mata, sauran nurses ɗin dake wurin suka ce "dan muna kusa shine abun harada su raɗa ko maryam" murmushi maryam tayi sannan ta ce "komai fa na son sirri, wannan magana ce tsaka nina da ita" wata acikin nurses ɗin ce ta ce "in tayi wari maji" ƴar dariya maryam tayi haɗi da cewa "bama zata yi ba "

  har parking lot dr kabir ya raka shi,  saida dr kabir yaga tafiyar Shazim tukun ya koma cikin hospital ɗin, ya zo zai shiga office ɗin shi yaji maganr hidaya tana cewa"doctor " juyowa yayi yana kallonta sannan ya ce "na'am " duƙar da kanta tayi ganin ya kafe ta da idanu "lafiya dai koh hidaya,?   kin tsayar dani kin kuma yi shiru " magana ta fara yi bata re da ta ɗago da kanta ba "dama dr tambayar ka zanyi mike damun dr ne " kallon ta kawai dr kabir keyi, sannan ya ce "baya faɗa maki baya jin daɗi ba "
"eh haka ne "
"to baya jin daɗi ne, gida ma ya tafi yanzu"
"ok, am dan Allah ko zaka bani number shi nakira shi nayi mashi ya jiki"magana take still kanta na duƙe,  wani kalar kallo dr kabir ya shiga binta da shi, ita kuma jin baice komai ba yasa ta ɗago da kanta, tana ɗago wa idanun ta suka sauka cikin nashi daya kafe ta dasu, kusan 5 seconds bai ce komai ba, chan ya ɗan nisa sannan ya ce "dama baki da number shi" girgiza mashi kanta tayi alamar eh, "ok shikenan ina wayar ki na sa maki number " hannu ta sa cikin aljihun rigar uniform ɗin ta ta ciro wayar ta ta miƙa masa,  amsa yayi ya sa mata number, miƙa mata wayar yayi tasa hannu ta karɓa tana faɗin" nagode" shi dai dr kabir kallonta kawai yayi ba tare da ya ce  mata komai ba harta juya ta bar waje bai daina kallonta ba, sai da ya ga ta ɓace ma ganin sa tukun ya murɗa handle ɗin ƙofar office ɗin shi ya shiga.....

✨ Shazim ✨

yana barin eko direct abnoor ya nufa, yana parking ya fito ya nufi main entrance ɗin hopital ɗin ba tare da ya ɗauki briefcase  ɗin sa ba, yana shiga direct office ɗin dr majeed ya nufa
nocking yayi, daga ciki aka bashi izinin shiga, kama handle ɗin ƙofar yayi ya tura ya shiga, bakin sa ɗauke da sallama, zaune dr majeed yake yana duba files dake gaban shi, amsa mashi sallamar yayi, wuri shazim ya samu ya zauna, hannu ya miƙama dr majeed suka yi musabaha, dr majeed ya ce  " lafiya kuwa yau nagan ka a wannan lokacin? "
"lafiya qlu majeed, maganar tafiya abuja nan ce ta taso, ammy tayi fushi dole sai mun tafi gobe "majeed ya ce "to fah, kwana nawa zaka yi "
"kai dai bari kawai wai sai nayi sati biyu  inji ammy"
majeed ya ce "shiyyasa fa tun time ɗin da kace tace ku tafi ya sa nace maka ka tafi kawai ni zan kula da komai, amma kaƙi, yan zu ga irinta nan ta soke kwana biyar ɗin da tace "
"bazaka gane bane kawai majeed, wallahi bana son zuwa ko nan da chan shiyyasa "
"to ya zaka yi zumunci ne dole ayi shi"
"haka ne"
"yanzun goben da ƙarfe nawa zaku tafi? "
"da safe"shazim ya bashi amsa " ok Allah ya kaimu " da ameen ya amsa , sun ɗan jima suna magana akan magunguna da allurai da zasu yi order, sai da shazim yayi sallamar asr bayan yaba ma majeed duk abun da zai bashi, sannan suka yi sallama ya nufi gida, tsit ya iske parlor alamar ba kowa, hakan yasa shi nufar bedroom ɗin ammy amma nan ma ba kowa, fita yayi ya nufi up stairs part ɗin noraiz ya shiga, samun shi yayi a parlor zaune kan sofa yana aiki cikin laptop, ɗagowa noraiz yayi jin anbuɗe ƙofa , yana ganin shazim ya miƙe yana faɗin "sannu da dawowa yaya"da yawwa shazim ya amsa yana cewa "ina ammy? , naga kamar bata gida kuma banga motarta ba a parking lot, nama yi tuna nin kokai ka fita da motar"
"tun da ka fita ta fita ko breakfast bata yi ba, na tambaye ta ina zata, sai cewa tayi yanzu zata dawo, amma haryan zu bata dawo ba" jinjina kai kawai shazim yayi haɗi da ficewa ya nufi part ɗin sa, yana shiga parlorn shi wayar shi dake cikin aljihun wandon shi ya ciro number ammy ya shiga kira, tana ringing amma ba'ayi picking ba harta katse ya sake kira sai da yayi kusan 3 times amma bata ɗauka ba, fita yayi ya koma part ɗin noraiz, yana shiga yace "noraiz ina wayar ka? "
"gata nan yaya " noraiz ya bashi amsa "kira number ammy "da ok noraiz ya amsa, nan shima ya shiga kiran wayar amma ba'ayi picking ba, ƙofar parlorn suka ji an buɗe fatima ce ta shigo da waya a hannun ta "yaya na shiga ɗakin ammy naji wayar ta na ringing, sai da na duba naga ashe kai ke kira, shazim bai ce komai ba ya fice daga part ya koma nashi, number malam yayi dialing, picking malam yayi haɗi da Sallama yana faɗin "likita bokan turai"
"ina wuni malam"
"lafiya lau, ya aiki"
"alhmdllh "
"to masha Allah "
ɗan shiru Shazim yayi, jin yayi shiru ya sa malam ce wa "lafiya dai koh shazim? "
"lafiya lau malam, dama ammy ce " sai kuma yayi shiru,  malam " yace miya samu aishar? "
"bakomai malam, tayi man magana ne akan zuwa abuja to nace mata ina da uziri wirin aiki, to sai bata sake maganar ba tun daga ranar, yau kawai " nan ya shiga  bashi labarin yan da suka yi da ammy yau , har fushin da tayi da kuma dawowa da yayi yanzu bata gida da kuma kiranta daya ke bata ɗauka, ɗan nisawa malam yayi sannan ya ce "ta faɗa man  komi ke faruwa, gaskiya banji daɗi ba, baka kyau ta ba, shi zumunci Allah ne yace ayi sa, kuma komi ya faru tsakanin ka da su ai kai ne baka kyauta ba " sosai malam yayi mashi faɗa da nasiha, akan bai kyauta ba daya bari har sai da ran ammy ya ɓaci "ayi haƙuri malam insha Allah hakan bazata sake faruwa "
"shikenan Allah ya kyauta gaba " da ameen malam ya amsa, sannan shazim ya ce "to malam ammy tana nan ne "
"eh tana nan " ajiyar zuciya shazim ya sauke, sannan suka yi sallama da malam, bedroom ɗin shi ya wuce, jifar da wayar shi yayi kan gado yana shiga, kayan jikin shi ya cire daga shi sai boxer yanufi bathroom, kusan 15 minutes ya fito ƙugun shi ɗaure da towel, shiryawa  yayi ciki ash ɗin jallabiya wuri ya samu kan sofa ya zauna, laptop ɗinshi ya jawo yashiga dan dannawa....

ammy bata dawo gidan sai da yamma liƙis, ta shigo, gaishe da ita fatima da noraiz dake parlor zaune, amsa masu tayi, haɗi da samu wuri ta zauna kan sofa, hijaba ɗin ta ta cire ta miƙa ma fatima tan cewa "kai man ɗaki" da to fatima ta amsa ta tashi ta kaima mata, tana fitowa ammy ta ce "ina innah asabe?   " amsa ta ba ammy da "tana ɗakin ta"
"ok "
Noraiz ya ce "ammy wai ina kika je ne, yaya ya dawo tun ɗazu yana ta ne manki " fuska a ɗaure amma ta ce
"in da ya aike ni chan na tafi"
noraiz ya ce "dan Allah ammy kiyi haƙuri ki dai na wannan fushin,  goben zamu tafi kamar yanda kika ce"
"karma ku tafi " ammy ta ce, magana noraiz zai yi, ta ɗaga mashi hannu tana ce "ya isa haka kar ka takura man daga dawuwa ta " da jin haka dole noraiz ya kama baikin sa yayi shiru, sau kowa shazim ya ke daga up stairs  ya nufo parlorn, hango ammy da yayi, yana isowa parlorn ammy ta miƙe ta nufi ɗakin ta, tsayawa yayi chak ganin tana ganin shi ta tashi, binta yayi har ɗakin, yana shiga ya ganta tsaye bakin dressing mirror, ta cikin mirror ta hange shi, yi tayi kamar ma bata san da shigowar shiba, ƙara sowa yayi har gaban dressing mirror ɗin yana faɗin "ina wuni ammy" amsa mashi tayi  da  "lafiya " daga nan ta ɗauke kanta ta koma bakin gado ta zauna, binta yayi har bakin gadon, durƙu sawa yayi yana dafa gwiwar ta,  haƙuri ya shiga bata, da ƙyar ta haƙura, ganin ta haƙura yasa cewa "dan Allah ki rage satin da ki kace zanyi zuwa kwana biyar "
"idan har kana son zaman lafiya da ni to kawai kayi shiru "da to kawai ya amsa mata, sannan ya fice daga ɗakin ya koma part ɗin shi domin yin alawala saboda lokacin sallah da yayi,yana fita   ita ma ammy tashi tayi ta nufi toilet domin alawa,  yana ko mawa   part ɗin shi  alawala kawai yayi ya fito suka wuce masallaci da noraiz dake parlor yana jiran shi yana saukowa suka wuce, anagama sallah suka wuce gidan malam  basu bane suka dawo gidan ba sai wurin ƙarfe 10 sannan suka dawo, koda suka dawo ammy da fatima har sunyi bacci, suma part ɗin su suka wuce kowa ya nemi ma kwancin shi .........🖊

Episode 20 _21

Washe gari...

Iliya ne ke  saka trolleys ɗin su fatima a booth ɗin  mota da zai kaisu airport,
ammy da fatima da noraiz sai Shazim  zaune suke kan sofa a main  parlor, ammy nayi masu nasiha sai da ta gama faɗa masu duk abun da zata faɗa masu sannan suka tashi suka kama hanyar fita daga parlorn, fatima da noraiz harsun fice ammy ta tsaida shazim, tana faɗin "dan Allah shazim karnaji kar na gani dan Allah, kayi haƙuri da komi zaka gani har Allah yayi maku dawowa "
"to ammy insha Allah "fitowa suka yi ammy ta raka su har parking lot suka shiga mota, tana masu Allah ya tsare hanya da ameen suka amsa mata, sannan ilya yaja motar suka fice daga gidan ammy na ɗaga masu hannu, saida taga mai gadi ya rufe gate sannan ta juya ta koma ciki,  cike da kewar su yanzu sai ita kaɗai cikin gidan, fatan Allah ya kaisu

Please Login or Register in order to submit comment