Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai ce komai ba, bai kuma juyo ba daga kwanciyar da yayi, kayan da ke hannun ta ta ajiye gefan bed ɗin, sannan ta hau kan bed ɗin, hannu tasa ta shiga shafa sumar kan shi, cikin lallashi ta fara magana

" wa ne mai tsau tsayin  ne  ya taɓa ɗan gidan momy yau ya kwana a kulle, faɗa man wanene yanzu na ɗau mataki a kan shi kaji ɗan gidan mama,ko na kira yayyen ka ne " shiru yayi nan ma baice mata komai ba

"yanzu Auta har  akwai ɓacin ran da zaka shiga kayi fushi da momyn ka tana magana kayi banza da ita" sai a lokacin ya ɗago da kanshi ya kalle ta ba tare da yace komai ba, murmushi tayi tana faɗin
" mike damun bugun zuciyata ne faɗa man naji yanzu nayi maganin sa"
hawaye ne suka kwararo daga idon shi, ɗuƙar da kai yayi ƙasa, da sauri ta sa hannu ta taro fuskar shi tana

" ya salam Auta mi zan gani haka, waye ya ɓata maka rai ne har haka yasa ka zubar da hawayen ka,  maza ka faɗa man ko waye yanzu na ɗau mataki saboda saman auta koka da yayi "  faɗawa yayi jikinta yayi hugging ɗinta so tightly, fashewa yayi da kuka kamar wani ƙaramin yaro, shafa bayan shi ta shiga yi

" dan Allah ka dai na wannan kukan ka faɗan man abun da ke damun ka, ko so kake nima ka sa ni kukan kasan kukan ka tashin hankali ne a gare ni "
shiru, ajiyar zuciya ya shiga saukewa, cikin muryar kuka ya fara magana ba tare da ya raba jikinshi da nata ba
"momy ashe wahalar banza nake bani take so ba " yana faɗin haka ta fahimci akan hidaya yake magana dan komai na shi na rayuwa ta sani ko shawara zai yi da ita yake yi babu wani sirrin shi da bata sani ba, ba ya iya ɓoye mata komai.

"ban gane ba, itace tace maka bata sonka?"
raba jikin su yayi , komawa yayi ya kwanta ya ɗaura kanshi saman laps ɗinta, shafa sumar kanshi ta shiga yi

" ka kwantar da han kalinka babana nasan tana sonka, babu wata ƴa mace da zaka ce kana so a duniyar nan ta ƙi amincewa da kai  insha Allahu hidaya matar ka ce bata da wani miji a duniyar nan bayan kai"

"to ai momy yau da kunne na naji bani take so ba "

"ba kai take so ba, to wa take so?"
"momy shazim wai take so bani ba "

"shazim dai "
"Eh momy, shi tace tana so "
"tofa ana wata ga wata, to shi shazim ɗin yana son ta ne"
"A'a momy, ai ya san ina sonta kuma ma anyi mashi mata a familyn su "

"to ai ta kwana gidan sauƙi tun da shi ɗin ba wai yana sonta bane kuma har kace an yi mashi mata "

"amma momy ta zubar man da mutunci, kullum faɗi nake tana da kamun kai tana da natsuwa amma ta buɗe baki tace ta son wani bani ba "

"kar ka damu ina tuna nin bata san kana sonta bane ai baka faɗa mata ba  "
"momy na faɗa mata kin manta ne "

"yanzu dai ka kwantar da hankalin ka ni zan san yarda zanyi zan sanar da dadyn ku , insha Allah sai ka Auri ta kar ka damu kaji " ta faɗa tana share mashi hawayen da suka ɓata mashi fuska, murmushi tayi haɗi da jan gemun shi tace

"babana kafa girma ka rage wannan yarintar ko so kake ɗiyar tawa ta raina man kai ne " ta faɗa haɗi da   lakuce mashi hanci, murmushi yayi haɗi da cewa
"momy ai bazan yi a gabanta ba, ke kaɗai zan mawa tun da daman ke maganin kuka na ce "

"duk da haka dai, kar ka haifa man jikoki masu kukan banza kamar kai "
murmushi yayi

"momy har kin fara maganar jikoki, duk wanda ke a gaban ki "

"to babana idan ban yi maganr su ba maganar mi kake so nayi, jikoki kuma ai na babana na da ban ne  "
"haka ne my lovely mom"
" ta shi kaje ka watsa ruwa, abinci na nan kan dinning yana jiran ka "

"momy ni a nan zanyi" 

"to shikenan tashi kaje kayi, amma ka kusa daina shigar man toilet "

"kai momy, saboda mi?"
"saboda ka girma, ka kusa aje iyali "
ta bashi amsa haɗi da miƙewa ta bar bedroom ɗin, tana fita shima ya tashi ya nufi toilet ɗin, bayan kamar 15 minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe.

Ficew yayi daga bedroom din yanufi parlor ,zaune ya samu momy ita da su ya mustafa ( yayyan shi, su ba kwai  ne y'ay'an momy ,maza biyar mata biyu ,dr kabir shine karamin kanin su shi ka dai ne bai yi aure ba ,ya mustafa shine babba sai umar,khalid,aliyu,safeenah,azeema sai dr kabir,duk acikin gidan  maza suke zaune da matan su   )
binshi da kallo suka yi , ya mustafa ne yace " yau ina ganin ikwan Allah ,wai kai da man har yanzu baka girma ba ,wanka a bedroom din momy ko kunya "

  turo baki yayi gaba yana fadin

" wallahi da na san kuna nan da ban fito ba ,haka nan ku hana mutum saket "

rike baki ya umar yayi yana fadin " Allah ya shirye  ka junior"

( da yake haka su ke ce mashi  )

"Ameen" ya ce yana murgud'a ma ya umar baki kamar wata mace ,tsaki ya khalid ya ja ba tare da yace komai ,

ya aliyu kuwa cewa yayi " gaskiya ku kyale shi ya huta,idan bai ma momy da mu  ba wa zai mawa ,ku barshi ya shana wata rana sai labari"

Matsowa kabir yayi kusa da Aliyu yana fadin

"yawwa ya Aliyu shiyyasa nake sonka"

"mu kuma baka son mu ko saboda muna fada maka gaskiya  " ya khalid ya fada

Ya mustafa yace " ai shima jirgi daya ya kwaso su shi da Aliyu dama ce kawai shima bai samu
ba "

"fadi kanka tsaye ,da ace ni ne shi sai nayi abun da yafi wanda yake yi Allah" ya Aliyu ya fada ,momy dai na gefe sai murmushi take tana kallon su cikin alfahari.

Ya Aliyu ne yace " kaji Autan momy ta shi kaje ka sa kaya ka dawo na san baka ci abinci ba ,kazo da kai na zan baka a baki "

"Allah dai wadaran naka ya  lalace ,yanzu wannan katon zaka ba abinci a baki amma dai gaskiya kaji kunya Aliyu "

"A'a ya khalid bari ,wane irin naji kunya ba wata kunya da naji kanina ne fa  ko ba haka ba momy " ya fada yana kallon momy dake bin su da idanuwa

"rabu da shi Aliyu na lura adawa yake da babana"

"haba momy wane irin adawa ,wannan katon ne zai ba abinci a baki "

"Ai ba haramun ba ne ,idan kai bazaka bashi ba ,sai ka bar mai bashi ya bashi "

"Allah ma ya kiyaye na zauna ina ba junior abinci a baki sai kace ban da aikin yin "

"to ni zan bashi idan kai bazaka iya ba,je ka sa kaya kaji Autan momy  " ya Aliyu ya fada yana kallon dr kabir

gwalo dr kabir yayi ma ya khalid ,tsaki ya khalid din yaja yana fadin

" wallahi kaji kunya kato da kai kana abu sai kace wata mace "
Dariya su ya mustafa su kayi suna fadin

" da gaske dai adawa kake da shi "

Tsaki ya khalid yaja ba tare da yace masu komai ba ,kwata kwata baya son ganin kabir na taɓara  abun haushi yake bashi .

Shaf shaf ya sa kaya ya dawo parlorn samun su yayi zaune a dinning su duka har da dady wanda shigowar shi kenan ,kusa da dady yaje ya zauna ,shafa kanshi dady yayi yana fadin

" likita bokan turai yau da wuri aka dawo kenan? "

"Eh dady"

"sannu to ,ya aikin?"

"Alhmdllh dady"

"to masha Allah" dadyn ya fad'a

"juyo na baka abincin kar ya khalid yaji dadi"

ya Aliyu ya fada yayin da yake d'ebo abincin a spoon ,bude baki  kabir yayi ya Aliyu na ba shi a baki dady ma na bashi sai murmushi yake yana ma ya khalid dake jifan shi da harara  gwalo ,karshe dai daya gaji ganin abun kunya  jifan shi yayi da spoon da sauri ya duke yana fadin " wayyo Allah dady zai cire man ido "

_kai dr ban da dai sharri_

"wallahi zan sa k'afar wando d'aya da kai khalid idan baka fita harkar junior ba "

"haba dady baka ga yanda ya  k'ara sangar cewa ba kuma fa duk dan kuna goya mashi baya ne "

"An goya mashi bayan " momy ta fad'a ,shiru khalid yayi bai sake cewa komai ba, dr kuwa sai murmushi yake  kamar wani zautacce

Haka suka cigaba da lunch suna fira cikin ni sha di ,da suka gama ma kan sofa su ka koma momy ke sanar da dady maganar hidaya, haƙuri ya ba dr ya kuma ce insha zaiyi iya bakin ƙoƙarin shi ganin ya amsar mashi auren hidaya, da dady ya faɗi haka da sauri ya rungume shi yana faɗin
"na gode sosai dady " saboda sangarta da rashin kunya har da su rawa.
Su ya mustafa nayi mashi dariya, ya khalid kuwa ban da tsaki babu abun da yake.

_nace daman dr haka kake, dole shazim ke ce maka yaro duk da shima yaron ne_🤓

Wannan ahali akwai nisha ɗi a tattare da rayuwar su, Allah ya dawwamar da farin cikin a gare su, hidaya ina taya ki murna idan kika shigo wanna ahali mata ga junior ɗan gata momy da dady da su ya khalid 😜.

wai zaki sha gata abun ba'a magana, amma fa idan kin ƙyale wannan mai kan kwakwar, bari dai na zuge baki na kar um um um ta watsa man tafi  ba sai dai na ƙasara ba  bakina a lekum 🤐

Haka suka cigaba da fira cikin nisha ɗi sai da lokacin sallah yayi tukun suka nufi masallaci.

_*✨HIDAYA✨*_

"Wai hidaya zaki buɗe ƙofar nan ne ko sai ranki ya ɓaci"

zuwa tayi ta buɗe ƙofar idanuwan ta duk a kumbure alamar taci kuka, tana buɗe ƙofar ta koma ciki, bin bayan ta ummah tayi tana faɗin
"yanzu abun da ki ka yi kina ganin shi ne dai dai ko, wai zaki faɗa man abunda ke damunki ko sai na kira Abban ku"

"Ummah kai na ne ke man ciwo "

"Ƙarya kike hidaya,har ni zaki ɓoye ma damuwar ki  "

"umma ki yarda da ni kaina ke man ciwo "
Shikenan shine abun da ummah ta faɗa
"kije to ki watsa ruwa kizo ki ci abinci ki sha magani " ummah na gama faɗa ta fice ta bar bedroom ɗin, komawa tayi ta kwanta a rigingine kanta na kallon ceiling , tayi shiru gaba ɗaya ta rasa mike damunta, dagske dr kabir yake anyi ma shazim mata a familyn su,hawaye ne suka gangaro mata daga cikin idanuwanta, hannu tasa ta share
turo ƙofar ɗakin akayi, tsaye tayi tana binta da kallon daga baya ta shigo, zama tayi kan bed ɗin, ta dai ji almar shigowar mutum amma bata san waye ba duk a tunanin ta umma ce sai fa taji shiru ne yasa ta tashi daga kwanciyar, zuba mata ido maryam tayi tana kallon ta
"lafiya kike man wannan kallon " ta faɗa cikin kasalalliyar murya

"idan ma da akwai abun da yafi kallo kin cancanta hidaya,yanzu kan dr kike son sama kanki ciwan da zai zame maki masifa a rayuwa, miyasa bazaki rabu da shi ki kama wanda ke sonki naga dai ba wani abu da dr shazim zai nuna ma dr kabir, kuma tun da ki kaga kina roƙon Allah a amma kuma baki samu abun da kike so ba ki haƙura mana inaga haka shine mafi alkairi a rayuwar ki "

"maryam amma kin fi kowa sanin yanda nake son dr, mi zai sa kice in rabu dashi "

"idan baki rabu da shi ba ya zakiyi hidaya, bafa a so dole kin sani, tun da kikaga ya nuna baya ra'ayin ki ki haƙura mana ko dan ki sama ma kanki sauƙi"

"ni dai shawarar da zan baki shine ki fitar da shi a zuciyar ki ki roƙi Allah idan har dr kabir alkairine a rayuwar ki Allah ya tabbatar maki amma idan kinji "

"maganar gaskiya ina son dr so mai ƙarfi wanda nake jin bazan iya daina son shi ba "

"to aikuwa kina da aiki mai girma a gaban ki"

"ba wani aiki insha zan cigaba da roƙon Allah wataran na san zai so ni "

"gaskiya hidaya baki cikin hankalin ki, naga Allah kika roƙa akan idan shi ba alkairi bane a rayuwar ki ya sauya maki da alkairi, yanzu ga alkairin ya zo amma kin kasa fuskantar gaskiya "

"bazan ɓoye maki ba maryam wallahi bana son dr kabir  idan nace na amince da soyayyar sa zan cutar da kaina ne kawai tunda bana son shi "

"ba cewa nayi ki amince da shi ba, A'a ina son ki fitar da tunanin dr shazim a zuciyar ki ki roƙi Allah idan har dr kabir alkairine Allah ya tabbatar maki, amma kina ɓata lokacin ki ne akan shazim "

"bazaki gane yanda nake jinshi bane a raina maryam"

"bazan gane ba ko dai bazaki gane ba " 
Haka suka cigaba da magana a tsakanin su  kowa so yake ɗan uwan shi ya fahince shi har dai ummah ta shigo ta same su, tana shigowa su kayi shiru binsu da idanu tayi daga baya tace,
"maryam ɗan bamu minti biyu baban ta na san magana da ita " da to maryam ta amsa, kallon hidaya ummah tayi tace

" ta shi ki wuce Abban ku na kira "  gabanta ne ya faɗi , yanzu idan Abba ya tambayeta mike damun ta mi zata ce mashi

"ummah nace maki fa kaina ne kawai yake ciwo "

"zaki tashi ki wuce ko kuwa " tashi tayi ta nufi ƙofa ta fice zuwa parlorn Abban ta zaune ta same shi kan carpet yana duba jarida, sallama tayi ta shiga ciki, amsa mata sallamar yayi yana nuna mata wurin zama, zama tayi inda ya nuna mata kusa da shi, gaishe da shi tafa ra daga bisani tace "Abbah gani ummah tace kana kira na"

"miyasa kika dawo gida yau da wuri,  sannan mi ya sameki a wurin aikin na ku da har yasa kika dawo gida kina kuka, sannan miye haɗin ki da kabiru ɗan gidan minister mai wada daya kawo maki jakar ki sannan wannan kwalin na minene ??? " ya faɗa yana nuna mata jakarta da wani ƙaton kwali  da ke gefan shi.

gabanta ne yayi wani mumunnan faɗuwa jikake daram, a zuciyar sai faɗin " mi ya kawo dr gidan nan sannan wannan kwalin na minene " katse mata tunani yayi ta hanyar cewa
"da ke nake magana kinyi man shiru "

"Abbah bana jin daɗi ne kaina na ciwo shine na dawo gida"

"to shi wannan kwalin na minene??,
hidaya kin san dai bana wasa da ke ko? "

_lokacin da dr kabir ya zo ashe Abba na bayan shi harya bada jakar da kwalin, da ya tafi ne ya tambayi mai gadi kayan miye kabir ya bashi, a nan ya sanar dashi cewa hidaya yace a ba_

"Eh Abbah da gaske nake maka bana lafiya ne shine ya ɗauko man jakata wannan kayan kuma na maryam ne  "

"Yau kika fara rashin lafiya ne da zaki kama kuka "  shiru tayi

"idan kika bari na bincika na gano ta ƙamai mai abun da ke damunki baza kiji da daɗi ba "

" da gaske nake Abbah "

" shikenan ɗauki jakar ki da kwalin ki wuce"

da to ta amsa haɗi da ɗaukar jakarta da kwalin  ta fice, da ummah taci karo zata shiga part ɗin Abbah , fuskarta  a ɗaure  babu alamun sassauci, fasa shiga tayi tace " biyo ni ina son magana dake " kawai ta faɗa, ajiye kwalin tayi a main parlor ta  bi bayan ummah har bedroom ɗin ta, tsaye ta samu ummah a bakin gado, kallon ta ummah tayi tace.
" hidaya miye haɗin ki da kabir yaron mai wada?"
" ummah ba komai "
" kar kiyi man ƙarya hidaya,  maryam ta sanar dani duk abun da ke faruwa"
"ummah maryam ƙarya take"
"ƙarya?  , maryam ɗin ce zata yi maki ƙarya "
"A'a ummah"
"ki shiga hankalin ki dani hidaya kinji na faɗa maki "
"to ummah "
"tafi amma ba wai mun gama maganar bane kina jina ko "
"eh ummah " ta faɗa haɗi da kama hanya ta fice, da idanu ummah ta bita hara ta fice.

ɗaukar kwalin tayi da jakar ta ta wuce ɗakin ta, zaune ta samu maryam kamar yanda ta bar ta ɗazu, mai da ƙofar ɗakin tayi ta rufe, tana zuwa tsakiyar ɗakin tayi jifa da kwalin harda jakar ta, da sauri maryam ta kalleta tana faɗin

" ke kuma lafiya miya same ki kike jifa da kaya"
"Ki barni kawai maryam, wai ashe dr gidannan ya zo har Abba ya ganshi " wani wawan tsaki maryam ta ja tana faɗin
" aikin banza da wofi, shine zaki shigo kina wannan jifar da kaya, wai dan Allah miye laifin wanda yace yana sonka ne, kuma kema kin sani in ban da so na so wallahi bazai ce yana sonki ba dan kin fi kowa sanin shi ba sa'anki bane kawai dan Allah ya jarabce shi da son ki shine zaki riƙa yi mashi wannan wulaƙan cin"

"maryam na lura bazaki taɓa fahimta ta ba "

"in dai akan wannan haukan da kike yi ne bazan taɓa fahitarki ba, kuma ki sani zan sanar da ummah duk abun da ke faruwa tsakanin ki da dr shazim kin dai san abun da zai biyo baya idan taji kin buɗe baki kince kina son wani ɗa namiji "

" maryam bana son irin wannan wasan, ke yanzu sai ki faɗa mata "

"kina wasa ne ki cigaba da wulaƙanta dr ki gani idan ban faɗa mata ba, ke  har ma abun da bakiyi ba sai nace kinyi wallahi"

"komai zakice sai dai kice, amma maganar gaskiya bana jin son dr a zuciya ta "

"zaki ma koya ne malama, kwalin minene wannan da kika jefar " maryam ta faɗa yayin da take nufar kwalin da ke ƙasa yashe, ɗaukar shi tayi ta buɗe,  wani kyakyawan teddy bear ne pink sai heart fari a gaban cikin shi   an rubuta am sorry dear da baƙin fenti, kwashewa maryam tayi da dariya tana faɗin
" soyayya ruwan zuma, lallai dr " ta fa ɗa haɗi da sake buɗe kwalin ta fito da sauran kayan da ke ciki, sweet ne da uban chocolate masu ɗauke da sorry a jikin ledojin su, ba maryam ba har ita kanta hidayar sai da ta dara...........

_Episode  58_59_

............. "Amma fa dr na matuƙar son ki hidaya " maryam ta faɗa yayin da take buɗe wani chocolate ta kai baki, taɓe baki hidaya tayi
"ke ki kaga haka "
"wai ke haryanzu kina a kan bakanki na baki son shi "
Kwanciya tayi haɗi da juya mata baya batare da tace komai ba, binta da ido maryam tayi tana faɗin
"karki fasa zaki sha mamakin abun da zanyi maki kuwa "
"ke maryam kin daɗe ko mi za kiyi ana so dole ne "
"haka ki kace? "
"eh haka nace "
tashi maryam tayi zata fice, da sauri hidaya ta riƙota
"wai ke ƴanzu ko kunya bakiji sai kije ki faɗama ummah "
"sakar ni" maryam ɗin ta faɗa taba fisgewa daga riƙon da hidayar tayi mata ta nufi ƙofa, a sukwane hidayar ta rigata isa bakin ƙofar, abun ma dariya ya so ba maryam amma sai ta ɗaure fuska bata yi ba tace " ki matsa man a gabana "
"wallahi bazan matsaba tun da ke baki san wasa ba "
"wasa ko zakiga wasa " maryam ɗin ta faɗa tana ƙoƙarin janye hidaya
"dan Allah maryam kiyi haƙuri wasa fa nake "
"Ina ruwana da wasanki ni bani hanya na wuce " haka su kai ta jayayya har ummah tayi nocking ta hidaya sai roƙon maryam take akan dan Allah kar ta faɗa ma ummah, gajiya ummah tayi ta sake wani  nocking ɗin tana faɗin
"wai lafiya kuke da baza ku buɗe man ba " da sauri hidaya tasa hannu ta buɗe tana yima maryam alama da da ido akan dan Allah kar ta faɗa ma ummah, ummah na shigowa kallon su tayi tana faɗin "ku lafiya  naga duk kunyi wani tsaye cirko cirko " hidaya ce tayi carb tace
" ba komai ummah magana muke"
"maganar ce har sai kunzo bakin ƙofa? "
maryam tace " tafiya zanyi ne daman"
"tun yanzu zaki tafi maryam?, ga abinci can a dinning, ki bari sai kinci sai ki wuce gida  "
" naci abinci ummah kafin na fito daga gida  daman saboda naga ta dawo ne da wuri kuma ina kiranta bata ɗauka ba  yasa nayi tunanin ko lafiya "
"to shikenan, ki gaishe da mamar ku "
"za taji insha Allah " jinjina kai ummah tayi haɗi da ficewa ta ba ɗakin
"shine zaki wani ce zaki tafi "
"idan ban tafi ba mizan yi maki ne, ko so kike na zauna ki cigaba da ɓata man rai "
"haba dan Allah wane irin ɓacin rai kuma "
"koma dai minene ni tafiya zanyi yi "
"Amma ai kin tsaya na baki wancan kayan "
"bana so" shine kawai abun da maryam ta faɗa ƙofar ta nufa ta buɗe bin bayan ta hidaya tayi tana bata haƙuri amma taƙi sauraronta,ba yanda ta iya haka maryam ta tafi ba tare da ta amshi chocolate ɗin ba ko ban kwannan arziƙi ba su yi ba, juyawa tayi ta koma ciki dinning  ta nufa wurin ummah .

_*✨KATSINA✨*_

Abie ne da uncle Ahmad da uncle mustafa zaune a parlorn suna magana

Uncle mustafa ne yace

" yaya yanzu yaushe zaka tafi kenan"
Amsa Abie ya bashi da

"da wannan week ɗin nace amma yanzu ina jin sai wani week ɗin saboda safwan da za su zo gobe "

"to shikenan Allah ya kaimu " da Ameen abie ya amsa,

uncle Ahmad ne yace

" wai yaya idan sun zo su safwan ɗin anan za su zauna?"

"eh mana Ahmad idan ba nan ba ina zasu zauna "
"a gaskiya yaya da zaka ji shawara ta da ba su zauna anan ba "
"saboda mi? "
"yaya bawan Allah nan yana cikin tashin hankali, rayuwar cikin barazana take, sai nake ganin zaman shi a nan kamar akwai gangance "

"Ahmad bawani gangance nasan da lilin da yasa nace ya zauna nan "

"to shikenan yaya,bawani abu Allah ya bashi lafiya "

"Ameen shi ne kawai, yaushe zaka koma Abuja ne " abie ya tambaya
"tuna ni nake ranar friday zan tafi "

"ok Allah ya kaimu, wai addimisson ɗin su Aaimah shiru "

Uncle Ahmad yace
"Inajin fa basu fara ba dawa ba kuma kaga late aka nemar masu addimisson ɗin Amma na san bazai wuce wannan week ɗin ba tun da makarantar next month su ke fara lectures "
"to shikenan Allah ya kaimu " da Ameen su ka amsa su duka, dadi ce ta fito ta zo wurin su ta zauna kan sofa gaishe da ita su kayi, amsa wa tayi da kulawa a fuskar sannan tace
" mi ake tattaunawa ne tun ɗazu? "
uncle Ahmad ne yace " magana muke ta yanda zamu nemo maki yaron ki "

"mai makon naji kunce kun nemo shi sai kuce magana kuke ta yanda zaku nemo shi, na lura so kuke mu sa ƙafar wando ɗaya da ku kafin ku nemo shi "
Abie ne yace
"ba sai an kai ga haka ba"
"to yauahe zaku kawo man shi gidannan? "
Amsa Abie ya bata da
"insha Allahu nan bada jimawaba, da wannan satin zan tafi kadunar to amma saboda zuwan su safwan yasa na fasa sai wani satin"

"Allah sarki gobe ne kenan zasu zo, to Allah ya kawo su lafiya "
"Ameen " su ka amsa su duka, fira suka shiga yi cikin nisha ɗin har sai da lokacin sallar zuhur yayi sannan suka nufi masallaci dadi kuma ta nufi ɗakin ta.

_*✨SHAZIM✨*_

Lokacin da hidaya

Please Login or Register in order to submit comment