Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka samu da laifin sata shine zaku ƙullama wannan sharrin , kuma abun ta kaici bayan ba ranshi, wallahi Allah bazai bar kuba"

wani daga cikin mutanen ne yace " hajiya ki kwantar da hankalin ki, mu bamu zo dan rigima ba aikin mu kawai muke yi, muna so ki fito mana da duk wani takarda daya shafi Abubakar in ba haka ba zamu sa jami'ai su duba mana"

ammy ta ce" sai dai kuyi duk abun da zaku yi amma ni bazan ba ku komai ba, tun da na san ƙarya kuke munafuncin ne kawai "

ganin dai da gaske bazata yi masu abun da suke so ba ya sa suka miƙe suna faɗin " to shikenan tun da haka kika ce, Ibrahim mu zamu wuce, amma bawai hakan na nufin baza mu sake dawowa ba " suna gama faɗar haka suka fice da harara ammy ta raka su, har inda suka yi parking Ibrahim ya raka su sannan ya dawo part ɗin ammy, magana ya fara yi ma ammy yana cewa "ina so ki fahimce ni "
"ina sau raron ka "ɗan nisawa yayi sannan ya ce " ina so ki gane cewa tun da kikaga an turo su to daga hukumar sune, kuma ba sharri zasu yi ma yaya ba dole akwai abun da mu ba mu sani ba, amma ina so kiyi haƙuri mu bi komi a sannu ko dan halin da kike ciki, insha Allah komi zai dai dai ta " ko mi akayi sai yace saboda halin da take ciki bai da wata magana bayan wannan
"to shikenan Allah ya shige mana gaba kuma zan yi magana da lawyern,  sadiq, tun da a high court yake aiki " uncle Ibrahim ya ce "hakane ni da kaina  zanyi magana da barrister, ba sai kin kira shi ba " sun ɗan jima suna tattaunawa ta yan da zasu bullowa al'amarin, uncle Ibrahim na barin part ɗin ya kira barristern sadiq ya faɗa mashi duk abun da ke faruwa,sannan ya samu uncle Ahmad  ya faɗa mashi  lokacin da suka zo baya gida,  ammy ma ta kira su malam ta sanar da su,lallashinta su kayi,ko da su uncle Ibrahim suka sanar da innah abun da ke faruwa cewa tayi to sai mi su ɗauki haƙƙin muta ne su ba su mana , sadiq ɗin waliyyi ne shi da bazai iya satar ƙuɗin mutane ba , abun yayi matuƙar basu mamaki dan basuyi tsammanin jin haka daga wurin ta ba, kwana uku da zuwan efcc ammy ta haihu ta haifi ɗiya mace    kyakyawa mai matuƙar kama da noraiz, farin ciki wurin ammy ba'a cewa komai dan tana matuƙar san ɗiya mace,kwanan ammy biyu da haihuwa turai ita ma ta haifi ɗiya mace kyakyawa, farin ciki wurin uncle Ibrahim ba'a cewa komai, duk wani abu da uba zai yima ɗiyar shi sai da yayima babyn ammy da tashi,da ranar suna ta zagayo aka sama babyn ammy fatima babyn turai kuma sa'adatu suna kiranta da sa'ada.

Shiru har tsawan wata uku efcc basu dawo ba kuma basu shigar da ƙara ba.
watan fatima da sa'ada biyar da haihuwa kwatsam sai ga sammaci kama uncle Ibrahim  da ga court  efcc sun shigar da ƙara, hankalin kowa  yayi matuƙar tashi musamman uncle Ibrahim da akayi arresting, Innah sai kuka take tana ma ammy masifa uncle Ahmad  na bata haƙuri akan tayi shiru , amma ina sai zagin ammy take tana cewa

" mijinta yaje yayi sata shine zata liƙama ɗan ta, wallahi duk abun da ya samu Ibrahim sai ta gane bata da wayau"

Allah sarki ammy ban da kuka babu abun da take,noraiz ma sai kuka yake ganin mahaifiyar shi na kuka shazim kuwa in ban da haɗiyar zuciya babu abun da yake, zazzaɓi ne ya rufe ammy bayan ta shiga part ɗin ta,wayar ta shazim ta ɗauka ya kira malam ya faɗa mashi abun da ke faruwa, hankalin malam yayi matuƙar ta shi sosai, ya kuma cema shazim insha Allah suna nan zuwa shi da ummy.
innah taci kuka kamar ranta zai fita ta tsine ma ammy yafi aƙira akan laifin da bana ta ba, takuma ƙara jin tsanar ta, turai ma sosai taji zafin ammy in ta tuna saboda laifin sadiq aka kama mijin ta duk da bata nuna mata a zahiri ba,kwana biyu da kama uncle Ibrahim uwani da halimatu suka zo daga kurfi su da ƴaƴan su , har suka yi kwana ɗaya da zuwa ammy bata san sun zo ba, dama halimatu ce mai zuwa wurinta to innah ta hana, sai washe gari da safe ta shigo part ɗin ammy suka gaisa, sai a sannan ammy ta san da zuwan su, daga ranar kullum sai halimatu ta shigo sun gaisa saboda tun da abun ya faru ammy ta dai na fita tana part ɗin ta koda yaushe ita da ƴaƴan ta, ta ɗan samu natsuwa saboda kullum sai malam da ummy sun kira ta sun kwantar mata da hankali sun kuma faɗa mata sunan zuwa hakan yasa ta dai na damuwa sosai taci gaba da adu'a, kullum lawyern  sadiq sai ya zo har aka tsai da ranar shiga court, ana gobe za'a shiga court malam da ummy suka zo amma basu sauka a estate ɗin ba sai suka sauka a gidan da sadiq ya fara zama , can ammy taje ta same su ita da su noraiz, anan suka kwana, washe gari da zasu tafi court gida aka bar su shazim tare da mai aikin ammy, suna isa court ba'a daɗe ba alƙali ya zo aka fara gaba tar da ƙara, da lawyer ya fara gabatar da ƙara abun yayi matuƙar bama ammy mamaki dan anƙara akan abun da efcc suka faɗa time ɗin da suka zo gida, an mai da zargin kan ana zargin sadiq da reƙe hannun jarin abokanan kasuwan cin shi, sannan gomnati na zargin shi da satar maƙudan ƙuɗin da sunan aiki, an kuma kama container biyar da kayan maye da sa hannun shi, alƙali ya buƙaci ganin abokan kasuwan cin sadiq da wanda sune maƙa su dun shigar da ƙarar, abun yayi matuƙar ba ma ammy mamaki , saboda waɗan da suka shigar da ƙarar abokai ne ga sadiq na ƙut da ƙut  wasu daga cikin su tun kafin ya shiga shiyasa yake tare da su, haka ƙara ta ciga ba da tafiya duk yan da lawyer sadiq ya so kare sadiq abun ya ci tura dan mutanen sun gabatar da hujuji masu matuƙar ƙarfi, ammy na ji na gani aka ɓata sunan mijinta bayan ran shi kuma aminan shi,duk wani company  na sadiq sai da kotu ta amshe har da wasu gida jen shi, a taƙaice daga  gidan shi dake lagos sai estate ka ɗai kotu ta bari, rayuwa tayi ma ammy zafi, taci kuka kamar ranta zai fita, sai da malam da ummy suka yi ta bata haƙuri da nasiha, malam yace ta yita yi ma mijinta da ƴaƴen ta adu'a,sun kwantar mata da hankali sun kuma nuna mata mahimmanci haƙuri da ƙaddara, hakan ya sa ta ɗanji sauki a ranta,amma abun na damun ta  ba ita kaɗai ba har da  malam da su uncle Ahmad  dan sun san  wannan duk sharrine, innah kuwa kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha saboda tsabar  jin daɗi   an saki uncle Ibrahim,kwata kwata bata damu da halin da Ammy take ciki ba,  yanke shawara ammy tayi idan su malam zasu koma lagos ƙafarta ƙafarsu kuma da ƴaƴen ta zata tafi komi innah zata ce sai dai tace dan a yan da take ji har kotu tana iya kai ta idan tace zata amshi ƴaƴen daga wurin ta,ko da ta faɗa ma su uncle Ibrahim shawarar data yanke, haƙuri suka shiga bata har da halimatu amma ina, sunyi sunyi amma taƙi haƙura, har zuwa su kayi wurin malam ko zai sa baki ta zauna amma sai yace shima yana buƙatar ta a kusa da shi, ya dai yi masu alƙawarin zata riƙa ziyartar su insha Allah ita da yaran,sun so ko noraiz a bar masu amma malam yace a'a,ba yanda suka iya haka suka haƙura, tsab ammy ta haɗa duk kayan ta dana yaranta dake part ɗin su, duk wani abu da tasan tana so sai da ta ɗauka sannan ta fitar da wanda zai lalace taba ma'aikanta estate ɗin sannan ta kashe duk wani abu na wuta, har part ta samu innah tayi mata ban kwana tayi tunanin innah zata ce wani abu amma sai taga saɓanin haka, turai da asiya sun sha kuka da ammy  zata tafi ,maƙalewa kairiyya tayi akan dole sai ta bi ammy, haƙuri ammy taita bata, mansoor  ma sun shirya da shazim shima har da kukan shi  innah har gida ta samu su malam tayi masu sallama, tun da safe suka kama hanyar lagos cike da kewar mutanan abuja.

Tunda suka koma lagos malam da ummy suke bama ammy kulawa ta musamman dan ganin ta kwantar da hankalin ta,hakan baƙaramin  kwantar da hankalin ammyn yayi ba ta rungumi ƙaddarar ta,  kullum cikin yima mijinta adu'a take da ƴaƴen ta, malam ya saka shazim da noraiz makarantar boko da islamiya,shazim na jss one noraiz kuma primary two, makarantar su ɗaya, su noraiz ƙarfe 12 ake tashin su amma noraiz baya komawa gida sai an tashi su shazim 2:30 pm sannan su tafi tare, da sun dawo wanka suke su ci abinci sai su wuce islamiya, malam ya tsaya tsayin daka akan rayuwar su duk wani abu na rayuwa wanda uba kema ƴaƴen shi malam na masu shi,hakama ummy babu abun da ba ta masu, uncle Ibrahim da uncle Ahmad ma suna matuƙar ƙoƙari akan su  sosai su ke basu kulawa duk da basa a tare da su, kuma lokacin bayan lokacin uncle Ibrahim yana kawo masu ziyara har lagos,   haka suka taso cikin soyayyar kakannin su da mahaifiyar su,
malam ya so ammy ta ƙara wani auren musamman da uncle Ibrahim ya nuna yana ra'ayin auren ta, malam ya so tayi ko da ba uncle Ibrahim ɗin ba mutane sun sha zuwa suna nu na ra'ayin aurenta amma tace a'a tafi son ta zauna tare da su malam da ƴaƴen ta, ƙyaleta malam yayi sai ma nema mata aiki da yayi, da farko ƙin amincewa tayi da aikin sai da malam ya zaunar da ita yanuna mata amfanin yin aikin sannan ta amince tafara aikin.
haka rayuwa ta cigaba da tafiya ammy na zuminci sosai  da su asiya, suna waya time to time, lokacin da turai da asiya suka haihuwa har abuja taje ita da fatima bata tafi da su shazim ba saboda makaranta.

Akwana a tashi shazim harya kammala secondry school lokacin noraiz na jss one fatima kuma na nursery one, uncle Ibrahim yazo lagos ya roƙi ammy da ta bashi shazim yayi karatu a hannun shi tare da su mansoor,  ƙin amincewa ammy tayi da zaman shazim a abuja saboda innah, tana tsoron zaman su tare saboda ta lura kwata kwata innah bata ƙaunar shazim,   da kuma shi kan shi  shazim ɗin ta san bazai taɓa raga ma innah ba tana tsoron abun da zai biyo baya, babu yan da uncle Ibrahim bai yiba amma tace a'a,ganin bazata amince bane yasa ya sanar da malam da ummy, faɗa malam yayi ma ammy dan mi zatace a'a, Ibrahim ba uba ne wurin shazim ba yana da ikwan da zai iya mai da shi wurin shi da zama bama karatu ba, ba dan ammy ta so ba ta haƙura,sosai uncle Ibrahim yaji daɗi da ta amince kafin ya tafi sai da ya amshi takardun shazim duk, ko da ya koma abuja addimission ya nema ma shazim da mansoor cikin ikwan Allah suka samu
kiran ammy uncle yayi ya sanar da ita ya kuma faɗa mata time ɗin da  zasu fara lectures, malam ta samu ta sanar da shi yaji daɗi ya kuma kira uncle Ibrahim yayi mashi godiya, ya kuma ce mashi insha Allah ana saura sati biyu su fara lectures ɗin shazim zai zo,hakan ce ta faru ana saura sati biyu su fara lectures ɗin shazim ya shirya ya tafi abuja, da zai tafi noraiz harda kukan shi, ko da ya isa abuja mansoor ne yazo har airport shi da driver ɗaukar shi, farin ciki sosai  mansoor  ya nuna na zuwan shazim ɗin da kuma kasan cewa da zasuyi a tare,ko da suka isa estate ɗin tarba ta musamman   shazim ya samu daga wurin uncle's  ɗin shi da matan su,  sosai suka nuna farin cikin zuwan shi har da yaran su,  feenah  ce dai da  innah sai luqman  ko a jikin su, lura da hakan da shazim yayi ne yasa ya ɗauke kan shi daga innahr yayi kamar ma bai san da zamanta a estate ɗin ba,  feenah kuwa ko kallon banza bata ishe shi ba daga ita har luqman ɗin dama ba son rainin wayau yake ba kuma ita da ma yar rainin wayau ce ga  rashin kunya, da zasu fara zuwa makaranta uncle Ibrahim ya sai masu motoci masu kyan gaske, sunyi farin ciki sosai, da farko shi da mansoor kowa tafiyar shi yake shi kaɗai har da haɗi da  ba department ɗin su daya ba shazim na karantar medicine and surgery mansoor kuma yana karantar medicine,abokin shazim ɗaya a department mai suna  A hashim,shaƙuwa ce sosai tsakanin shazim da A  hashim, mansoor kuwa yana da abokai ba laifi ,  sai  daga baya mansoor ya ce mizai hana su dunga tafiya tare, amincewa shazim yayi suna tafiya tare, ta dalilin haka shaƙuwa sosai ta shiga tsakanin su kowane lokaci suna tare da juna ko a school ko a gida, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma uncle's ɗin shi ba dan dama burin su yaran su haɗe kan su, innah ce kwata kwata hakan bai mata daɗi ba dan ba haka taso ba, har kiran mansoor tayi tana mashi faɗa dan mi zai shige ma shazim, shazim ɗin ba ba son su yake ba san da suna yara, shikuma   ya ce mata ko ada laifin  su ne , su suka nuna ba su son shi shiyyasa shima ya nuna bai son su, ba ƙaramin haushi maganar mansoor ta ba innah ba hakan yasa ta ƙara jin ta tsani shazim musamman ma yan da yayi fatali da ita a estate ɗin, dan sai ayi sati bata sa shi a ido ba kuma kullum sai mansoor ya zo gaishe da ita da safe amma bata taɓa ganin shazim ba, ƙarar shi ta kai wurin uncle ahmad akan bai zuwa yana gai she ta, kiran shi uncle ahmad yayi yayi mashi faɗa da nuna mashi hakan bai dace ba, haƙuri ya bashi ya kuma yi alƙawarin gyarawa, tun daga ranar kullum da safe idan mansoor zai je gaishe da ita tare suke zuwa, kullum kuma yaje gaishe da ita ta rinƙa faɗa mashi baƙaƙen maganganu, in tana yi yi yake kamar ma bai san mitake yi ba, hakan kuwa ba ƙaramin haushi yake bata ba, sai daga baya daya lura abun nata ba mai ƙarewa bane yasa intace mashi a to sai ya kai mata har z, bata yi mamaki ba tun da daman tasan halin shi tun yana yaro ba ragamata yake ba, wata rana suna dawowa daga makaranta mansoor ya ce suje su gaishe da ita ko da  suka je gaishe da ita basu same ta ba tana part ɗin uncle Ibrahim sai su feenah da kairiyya suka samu a part ɗin suna kallo, gaishe da su kairiyya tayi amma feenah mansoor ka ɗai ta gai da, dama tun da shazim ya zo kowa na gaishe shi amma ban da ita, lura da bata gaishe da shi bane yasa mansoor rufe ta da faɗa maimakon ta gaishe shi sai tashi tayi tafice tana ƙunƙunai, a kwai wata rana da uncle Ibrahim ya kira shazim part ɗin shi daya je part ɗin ba kowa a parlor sai ita kaɗai da yayi sallama ta ƙi amsawa sai ma ɗago da kai tayi ta kalle shi ta kauda kai tana jan tsaki , abun yayi matuƙar bata ran shi ya tsani rainin wayau da rashin kunya  hakan yasa ya ɗauke ta da mari har sau biyu har sai da ta duƙe saboda zafin da taji ai kuwa ba shiri ta nufi ɗakin momyn ta tana kuka, da ta shiga ko da ta sanar da momyn ta taso ƙeyarta tayi har parlorn ta bashi haƙuri, dole ta bashi haƙuri tun da ga ranar kuwa ta dai na yi mashi koda kallon banza bare aje ga tsaki.

Lokacin da su shazim su kayi hutu da zai tafi lagos tare suka tafi da mansoor har hutun su ya ƙare suka dawo, haka rayuwa ta cigaba da tafiya shaƙuwa ce sosai tsakanin shazim da A hashim dan A hashim yana yawan zuwa lagos wurin shazim hakan ne yasa kowa ya sanshi tare da shazim musamman fatima ba ƙaramin son a hashim take ba idan ya zo lagos  to tana nan maƙale da shi, tun wata rana da noraiz ya ji ciwo yayi mashi alura shine ta tambaye shi daman ya iya alura kamar ya shazim sai yace mata eh ai su dr ne tunga ranar ne ta sa mashi suna ya dr.

Cikin ikwan Allah   sun kammala degree zasu joining masters,maganar aure su uncle ahmad suka yi masu amma sai suka ce su ba yanzu ba sai sun kammala masters sun fara aiki tukunnan, ko da suka ce haka su uncle ahmad sunyi na'am da hakan, tunga time ɗin basu sake masu maganar auren ba sun barashi a sai sun fara aikin,business malam yace  shazim ya fara kafin su fara masters, da zai fara malam ya bashi jali, cikin ikwan Allah san da zasu tafi business ya haɓaka Allah ya sa ma abun albarka,da zasu tafi malam ya samo   wani yaro mai gaskiya da ruƙwan amana ya ɗaura shi akan business ɗin kafin  shazim ɗin ya kammala karatu,cikin ƙanƙanin lokaci business ɗin ya ƙara haɓaka,saboda   yaron na kula da business ɗin shazim cikin aminci ga gaskiya da ruƙwan amana,
lokacin da suka kammala master business ɗin shazim ya haɓaka sosai dan malam na kula da komai ga kuma hameed hakan yasa business ɗin haɓaka.

lokacin da suka kammala  masters lokacin su noraiz shi da mahmud da luqman suna aji biyu a jami'a.

Basu jima da kammala masters ba suka samu aiki su duka,har da a hashim,  uncle Ibrahim ya so shazim yayi aiki a abuja amma yace ya fi son lagos saboda business ɗin daya ke hakan yasa uncle Ibrahim haƙura,shazim yana aiki awata babbar asibiti dake garin lagos, haka rayuwa ta cigaba da tafiya shazim yana aiki hameed na  kula mashi da  business,yanke shawarar yin phd yayi, ko da ya sanar da uncles ɗin shi da malam goya mashi baya su kayi ,amma sai malam ya bashi shawarar yin phd ɗin ta online, sosai hakan yayi mashi daɗi ko ba komi zai samu ya dunga zuwa aiki wani lokacin yana kuma kula da business ɗin shi,cikin ikwan Allah yana kula da aikin shi da business ɗin shi ya kammala phd,ƙarin girma ya samu a wurin aikin shi  bayan nan kuma yana visiting wasu hospital ɗin,ganin komai na tafiyar mashi dai dai yasa ya yanke shawarar buɗe privet hopital, daya  samu malam  da maganar , goya mashi baya malam yayi ya kuma tai maka mashi da wani abun wurin gina hospital ɗin, cikin ikwan Allah aka gama gina hospital ɗin , ammy ma ta tai maka mashi da wani abun da zai zuba kayan aiki, sosai yaji daɗi ya kuma yi ma ammy godiya,kayan aiki masu inganci ya zuba, sai da komi ya kammala sannan ya ɗauki ma'ikata,ya kuma ɗaura wani abokin shi mai suna majeed wan da su kayi islamiya ɗaya,da yake iyayen shi talakawa ne masu rufin asiri, kuma da man yayi karatu a harkar  lafiya hakan yasa shazim ya ɗauke shi aiki ya kuma ɗaura shi  a matsiyin babba mai kula da harkokin Hospital ɗin idan baya nan ko yana wurin aiki...........


_Episode  54_55_

........ Uncle Ibrahim da uncle ahmad tasa shazim da mansoor gaba suka yi akan su fito da mata suyi aure, amma sai su kace  ba yan zu ba, faɗa suka yi masu sosai suka kuma ce sun basu nan da wata huɗu ko dai su fito da mata ko kuma su zaɓa masu da kansu
ganin haka ne yasa mansoor ya gabatar da wacce yake so amma shazim shiru ta business ɗin shi kawai yake dan ya ma manta da wata magana ta aure,ganin mansoor ya gabatar da wacce yake so amma shazim shiru yasa uncle Ibrahim  shiryawa yaje har lagos ya samu malam da batun, ya kuma sanar da shi sun yanke shawara kodai ya fito da mata yayi aure ko kuma su aura mashi duk wacce suka ga dama, malam bai  ba da goyan baya ba akan  hukuncin da suka yanke  yace su bar shi da shazim ɗin shi da kansa zai sa ya fito da matar , kwata kwata ba haka uncle Ibrahim  ya so ba yaso ace malam ya goyi da bayan su, ba dan ya so ba ya amince ya koma abuja, koda ya koma ya sanar  da uncle ahmad yan da suka yi  da malam faɗa ya kama yana cewa  kenan malam ke goya mashi baya shiyyasa da suka yi mashi magana yayi kunnen uwarshegu da su, ya kuma yanke hukuncin dole tare za su yi mashi aure shi da mansoor da su feenah dake shirin kammala makaranta, {su noraiz sun gama masters kawai suke jira} ko yana so ko baya so, sosai uncle Ibrahim da innah suka amince da hukuncin da uncle ahmad ya yanke, uncle ahmad da kan shi yakira malam ya sanar da shi cewa sun ƙarama shazim ɗin wata biyu kacal ko dai ya fito da mata kokuma su aura mashi duk wacce ransu ya so,abun yayi matuƙar ba malam mamaki yan da suka ɗau abun da zafi sosai har haka, shima yana so yaga shazim ɗin yayi aure amma ya fiso abi komi a sannu gudun dana sani.

Ammy da ummy malam ya kira ya sanar da su abun da uncle ahmad ya ce, suma basu ji daɗin hukuncin da suka yanke da zafi haka ba,suma babu abun da suke buri sama da shazim ɗin yayi aure.

Kiran shazim malam yayi ya sanar da shi hukuncin da uncle ahmad ya yanke,sannan yace mashi komi yake ya fito da mata suma sun fi son yayi auren tunda dai dai dai gwargwado Allah ya bashi rufin asiri, to sai ya gode ma Allah shima yayi aure ya tara iyali, cewa yayi insha zaiyi ƙoƙari ganin ya fitar da mata yayi auren, malam yaji daɗi da ya amince zai yi auren ya kuma yi mashi adu'a Allah ya zaɓa mashi mata tagari.

Tun ranar da su kayi magana da malam har tsawan wata biyu shazim bai kawo matar ba bai kuma sake maganar ba, tun su uncle ahmad nasa idon ya zo  yace ga wacce yake so  har suka gaji,su kai fushin har suka gaji ganin wanda suke yi dan shi yayi kamar ma bai san suna yi ba,gajiya malam yayi da shirun nashi ya sake mashi maganar, ko da yayi mashi maganar sai cewa yayi gini yake yanzu so yake sai ya kammala tukunnan,malam yace to ya kamata ya kira su uncle ahmad ya sanar da su, da to ya amsa, ya kuma kira su ya sanar da su, balbale shi da faɗa uncle ahmad yayi dan mi bazai sanar da su ba tuntuni sai yan zu da lokacin da suka bashi ya ƙare, haƙuri ya bashi ya kuma sanar da shi ya kusa kammala gini ai saura ka ɗan , jin yace hakane yasa uncle ahmad haƙura ya ƙara mashi wasu wata uku, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma shazim ba dan shi kwata kwata bai shirya yin aure yan zu ba neman kuɗi kawai yasa a gaban shi,tun da uncle ahmad ya amince da maganar gini daya ce yana yi yasa ya fake da ginin har akayi shekara ɗaya bai kammala ba bai ce ga mata ba, sai da malam ya tasa shi gaba da faɗa sannan ya kammala,gida ne mai girman gaske kusan part uku ne

Please Login or Register in order to submit comment