Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙosa na ganni kusa da ke, Allah dai ya dawo da kai lafiya,  ameen  ya fada,  kashe wayar tayi , mike wa tayi daga kan sallayar parlor ta fita kan sofa ta zauna  , number ilya ta shiga nema cikin wayar ta sai ga fatima ta dawo  daga Islamiyya wurin Ammyn ta nufo  hadi da cewa  " barka  da gida Ammy,  mikike yi zaune ke kadai  s parlor? , ta fada yayin da take samun wuri kusa da Ammy ta zauna, amsa Ammy ta bata da "number ilya nake nema saboda  zai dauko mai babban suna  , ya noor ya dawo  ne ta fada hadi da mikewa harzata nufi upstair Ammy tace " dawo uwar zumuɗi  cewa nayi zai dauko shi bawai ya dawo ba" da wowa tayi tana  turo baki gaba hadi da cewa "to Ammy ƙarfe  nawa  zai dawo , Ammy tace" ƙarfe 5:00 insha Allah jirgin su zai sauka,  shiyyasa yace a kira mashi ilya yaje ya dauko sa;; Ammy dan Allah zanbi ilya inzai tafi, cewa Ammy tayi" to shikenan maza kije " bata ma tsaya sauraron mi Ammy zata ce ba ta nufi dakin ta da sauri, wanka ta fara shiga bata jima ba ta fito sanye da bathrobe shaf shaf tashirya cikin doguwar riga abaya tayi rolling da gyelen  a kanta,  wayar ta kawai da jaka ta dauka ta fice daga dakin inda tabar Ammy nan ta sa meta,   ƙara sowa fatima tayi wurin ta tana fadi" yawwa Ammy na shirya kinyi ma ilyan magana "  A'a bari nayi sai kin shirya tukunnan , ai a kwai sauran lokaci,  duka  yanzu ƙarfe  4:00 kuma kinga cewa yayi sai 5:30 jirgin zai sauka
Ammy ai da kinyi mashi magana,  kinsan fa a kwai nisa Airport din zamu yi kusan 20 to 30 minutes bamu kai ba fah kuma ga go slow" Ammy tace "haka   ne nasha'afa ne shiyyasa amma bari na kira ilyan ya fitar da mota sai ku tafi ta fada yayin da take kiran ilya a waya yana picking  tace " ilya ka fitar da mota zakuje Airport kai da fatima domin dauko mai babban suna yana hanya, to Ammy insha Allah yanzu kuwa zan fito da ita ilya ya fada da yake shima Ammy yake cewa, to shikenan ga fatimar nan fito wa Ammy ta fada hadi da rejecting din kiran, mike wa Fatima tayi hadi da cema Ammy sai sun dawo a dawo lafiya  Ammy tayi mata sannan ta tashi ta nufi , kitchen innah Asabe ta samu a kitchen din tana gyarashi domin fara shirye shiryen dinner , Innah asabe na ganin ammy  tace " barka da fitowa hajiya, da yawwa Ammy ta amsa mata" kina bukatar wani abune ? Innah asabe ta fada saboda  ganin Ammyn datayi a kitchen a wannan lokaci " eh kinsan mai babban suna na hanya to shine nake son a daura dinner tun yanzu , kuma shima shazim bai ci komai  ba ya fita ga fatima ita ma kuma,  kinga in aka gama da wuri zai fi ai,  innah asabe tace"ah yaufa muna da babban bako,shiyyasa naga fatima ta wuce da gudu dan bata ma lura da niba Ammy tace" kinsan halin Fatima da zumuɗin,  ai ina ce mata yana hanya duk tabi ta rude tana chan tabi ilya Airport, dariya Innah Asabe tayi hadi dacewa" Allah dai ya kawo shi lafiya, ameen Ammy tace shirye shiryen daura dinner suka shiga yi..

✨ _SHAZIM_ ✨

  shigowa yayi main parlor bakinsa dauke da sallama, da alama daga waje yake baya cikin gidan, su Ammy dake kitchen suka amsa mashi sallamar, fitowa Ammy tayi daga kitchen din tana cewa" kai ashe baka gidan,  ka kuwa yi waya da ƙanin ka?  ya ce man ya kira wayarka baka dauka ba "
" Eh na ɗan fita ne tun dazu har bedroom din ki nazo na same ki kina bacci, wayar na silent ne sai daga baya naga kiran sa,  yace man ai kunyi waya akan kitura mashi ilya ya dauko shi, eh Ammy ta fada hadi da Komawa kitchen din shikuma part dinsa ya nufa,   bedroom dinsa ya wuce kayan jikin sa ya rage ya nufi toilet  bayan kamar  15 minutes sai gashi ya fito sanye da bathrobe dressing mirror dinsa ya nufa hadi da zama kan stool din dake gaban mirror din, ya jima yana yan shafe shafensa sannan ya nufi wardrobe , shiryawa yayi cikin kana nun kaya riga da wando, wandon baki  iyakar sa gwiwarsa sai rigar fara mara nauyi mai gajeran hannu, wurin dressing mirror ya koma  feshe jikin sa yayi da turare sannan ya fita  daga bedroom din ya nufi  down stairs parlorn Ammy, dinning ya nufa  yaga bakomi,  fita yayi daga parlorn ya nufi kitchen wurin su Ammy yana shiga yace " Ammy akwai abinci,  yunwa nake ji, gashi nan ana girkawa saura ka dan mukarsa Ammy tafada, gaskiya  Ammy bazan iya jiraba sosai nake jin yunwar babu wani abu koda mara nauyi ne?  Ya tambaya,  Ammy ta ce" bari na yanka maka fruit ta fada hadi da bude fridge ta dauko fruit ta wanke yanka mashi tayi ƙanana  ta zuba mashi a ɗan bowl ta mika mashi amsa yayi hadi da cewa " nagode sosai Ammy sannan ya fice daga kitchen din,  main parlor ya koma TV ya kunna hadi da daukar remote yana chanza channel zuwa TVC news,  zaman shi yayi kan sofa  yana shan fruit tana kallo
Wannan kenan............

🌹~ _KAINAAT_ ~ 🌹

_MURTALA MUHAMMAD INTERNATIONAL  AIRPORT

Mutane ne iri iri wasu najiran time din da zasu  hau jirgi,  wasu kuma sun zo daukar yan uwan sune, wasu na cikin  mota wasu na zaune akan chairs din da aka ta nada domin masu zama.
Motar su fatima ce ta kara so cikin airport din parking lot din dake wurin ilya  ya nufa parking yayi, fatima ce tabfara fitowa sannan shima ya fito, cikin airport din suka nufa inda mutane ke zaune fatima ta nufa, wuri ta samu ta zauna ,  wayar ta da ke cikin bag ce ta fara ringing fito da ita tayi "YA DR" shine sunnan daya bayyana akan screen din wayar, picking call din tayi hadi da sallama,  on the other hand nacikin wayar ya amsa mata sallamar " ina wuni ya dr , ya gida ya kwana biyu, lafiya lau  Alhmdllh Bintalo, turo baki Fatima tayi cikin shagwaba tace" haba Yaya nace fa bana son sunnan amma baka dai na ceman ba,  ta fada tana dan bubuga kafafu, dariya na cikin wayar yayi, ai kuwa nan tashiga yi mashi kukan shagwaba tana cewa " dariya ma na baka koh"
"sorry fatimaaaaaa" ya fada hadi da jan sunan,
Uhmmm kawai tace,
sake mgn nacikin wayar yayi "bana ce kiyi hakuri ba, ai duk laifin kine kinsan fa nace kibar ceman ya dr nan da kika kware wurin kirana dashi, shiyyasa nima nace maki haka kinga nima na rama kenan,  amma kiyi hakuri bazan sake ba kinji" "shikenan Yaya ya wuce"
"Yawwah koke fa, yasu Ammy kina ina ne haka naji hayaniyar mutane?
amsa ta bashi da " Ina airport , munzo daukar ya noor  ne "
" ok yau zai dawo kenan, kice ina gaishe dashi ina mashi ya gajiyar tafiya "
" to zai ji Insha Allah yaya "
" ok take care of your self for me pls, bye" ya fada,  itama " bye" tace masa hadi da rejecting  call  din, game ta shiga  bugawa a wayar tana nan zaune aka fara sanar war iso war jirgin 5:30 tashi tayi ta koma inda mutane ke tsai tsaye domin tarbar yan uwan su passengers ne suka fara biyo wata kofa da aka rubuta EXIST da manya harafi wacce domin su aka tana de ta fatima dai na nan tsaye, mutane kuwa wanda suga yan uwan su nata rugawa da gudu suna tarbarsu, ita dai sai zare idanu take sokawai take taga ta ina ya noor din ta  zai bullo.  Wani matashin saurayi ne ya bullo jikin sa sanye da ƙananun kaya jeans and T -shirt na company gucci, jaka rataye a kafadar sa baka jikinta an rubuta ADIDAS  da farin paint da manyan haruffa, hannun sa rike da trolley yana ja  P-cap ce a kansa sai face mask akallah zai yi kimanin shekara 25 a duniya.
Fatima ce ta rugo da gudu tana fadin ya NOORRR tana nufar wannan saurayin, sakin trolley din dake hannun sa yayi fa dawa tayi jikinsa tana dariya hadi dacewa " shine kawani boye face dan nasha wahala wurin gane ka koh " janye ta yayi daga jikinsa yana cewa " Autar Ammy kedai haryau Allah baisa kinsan cewa kingirma ba koh, fatima tace " haba ya Noor haka ma za kace koh, shikenan tunda baka yi farin ciki da ganina ba " ta fada hadi da juyawa zata bar wurin, hannun ta ya riko yana cewa " sorry my yar qanwerh, wasa fa nake maki, kema kinsan nayi farin ciki da ganin ki autar mu  " ya fada  hadi da jan kumatunta tana dariya " koke fah " ya fada  hadi da cire facemask din da yasa MASHA ALLAH nafada daganin wannan kyakyawar fuskar ta Noraiz kamannin sa daya da fatima , dan dai shi namijine ita kuma mace.
ilya  ne yakaraso inda suke yana washe baki Noraiz  yace " kice tare kike da ilya  Ammy " ya fada yana mikama ilya  hannu domin suyi musabaha.
ilya   yace "  ina wuni, ya hanya, ya aka baro mutane turai " dariya fatima da Noraiz sukayi jin ilya yace wai ya aka baro mutanen turai, amsa mashi Noraiz yayi da " alhmdllh ilya  ya gida " amsawa ilya yayi da " lafiya qlu " ilya yace hadi da daukar trolley din Noraiz suka bar wurin, parking lot suka nufa booth ilya ya bude ya saka trolley da jakar Noraiz, shiga sukayi cikin motar Noraiz da ilya naga ita kuma fatima na baya, key ilya yayi ma motar suka bar airport din, hanyar gida suka nufa suna tafe suna fira Noraiz ne yace " wai ina ya shazim fatima " amsa ta bashi da "may be yana  gida ,  danni banjima da dawowa daga Islamiyya ba na biyo ilya"   "ok " kawai Noraiz yace yayin da suka iso  anguwar su horn ilya yayi time dinda suka iso  bakin gate din gidan, megadi ne ya bude masu gate din,  ilya ya danna kan hancin motar ciki, parking lot ya nu fa parking yayi, fitowa su kayi daga motar suka nufi cikin gidan, ilya na biye da su a baya hannun sa dauke da trolley da bag din Noraiz.
Shiga sukayi cikin gidan bakin su dauke da sallama
Da sauri Noraiz ya nufi shazim dake zaune kan sofa, hugging din sa yayi hadi da cewa nayi missing din ka yy sosai
shafa kansa shazim yayi kamar wani karamin yaro yana cewa " to ai yanzu komai ya wuce tun da gaka nan ka dawo"
" haka ne kuwa  yaya " Noraiz ya fada
Ammy ce ta fito daga kitchen ita da Innah Asabe wurin su suka nufa Ammy nace wa" oyoyo mai babban suna " tashi Noraiz yayi ya nufi Ammy hugging dinta yayi yana cewa " nayi kewar ki sosai Ammynah " nima nayi kewar ka mai babban suna " Ammy ta fada,  Innah Asabe ce ta matso tana cewa " marhabun lale mai babban mutum, ya hanya, ya kuma karatu " Amsa ya bata da " alhmdllh " nan suka shiga firar yau she gamo,  ilya  haurawa yayi upstairs domin kaima Noraiz kayan sa part din sa, baijima ba ya sauko yana cema kayan na part dinka nakaima maka.
godiya Noraiz yayi mashi, ficewa ilya yayi ya koma bakin gate wurin mai gadi dama nan take zama.

Noraiz ne yatashi yana cewa " zanshiga na watsa ruwa na fito naga time din sallah magrib yakusa" ya fada yayi da yake haurawa upstairs.
Ammy c tace  " shazim   abincin fa koba yanzu ba "
"A'a Ammy sai an jima  in mun dawo sallar magrib sannan" to shikenan " Ammy ta fada , tashi yayi ya nufi upstairs shima
Ammy ma da Innah Asabe nasu bedroom din suka nufa aka bar fatima ta gyara kitchen da jera abinchi kan dinning (  sbd bata sallah )  tana gama wa itama ta nufi nata bedroom din wanka tashiga (  dama tana yin wanka kusan sau hudu arana intana period )

✨ _NORAIZ_ ✨

Fitowa yayi daga bathroom sanye da bathrobe   (  part din sa shima ya hadu sai dai bai kai na shazim girma ba, amma dai masha Allah yayi kyau ) dressing mirror  yanufa mai kawai yashafa ma jikin sa yanufi clothes set dinsa jallabiya ya dauko black color yasa wurin kayan sa da ilya ya kawo masa ya nufa, turare ya dauko cikin jakar sa ya fesa gadi da mai dashi
Ficewa yayi daga part din dama yayi alwala tun a toilet ,  part din shazim ya nufa  dake kusa da nashi
yana shiga shazim din na fitowa daga bedroom din shima sanye ya keda jallabiya
Ficewa kawai sukayi suka nufi masallachin dake chan main gate din gdn basune suka dawo cikin gidan ba sai da su kayi har isha tukun suka dawo cikin gdn
parlorn Ammy suka yada zango fatima kadai suka samu zaune a parlorn suna  zama sai ga Ammy ta fito wuri ta samu ta zauna tana cewa " to a tashi ga abinci chana najira "  to suka cemata hadi da nufar dinning din Fatima ce tayi serving din su.......

✨ _KATSINA_ ✨

Zaune suke kan dinning suna dinner su duka gidan baka jin komai sai karar plate da spoon
Suna gamawa abie  da  abdallah  da Mom suka koma kan sofa yayin da su Aairah ke gyara dinning din, suna gamawa wurin su abie  suka dawo suka zauna fira suka shiga yi abie  na tambayar su yaushe zasu fara exam din SSCE " saura 3 weeks abie  " suka bashi amsa " to Allah ya bada sa'a, da Ameen suka amsa  " abie  wace school  zaka kaimu  in mungama " Aaimah  ta tambaye  shi" ban gane inda zan kai kuba , kuda kuke da  school a cikin grinku, a i ba sai kunje wani gari ba " abie  ya fada yana tsare su da idanu " A'a gaskiya abie  Muyi primary school da secondary school a nan sannan kuma ace munyi high school a nan gaskiya abie  s chanza mana " to sai dai kunga ma exam din tukunnan,  to shikenan abei " chanza firar sukayi zuwa wata, sai kusan 9:30 sannan su Aairah suka nufi dakinsu sbd sun fara karatun exam gakuma zuwa school gobe
Suna shiga bedroom din su wanka sukayi hadi da sanya pajamas dinsu sannan suka dauki books dinsu suna dubawa sai wurin 12:00 sannan sukayi bacci.......
Episode 9_10

Sanye suke da uniform din su na school, ko wacce rataye da school bag din ta,  ficewa su kayi daga bedroom din suka nufi main parlor su Mom suka samu kan dinning  suma basu jima da zuwa dinning area ba, gaishe dasu su kayi hadi da samun wuri kan dinning din suka zauna,  abie  ne yace " yau yan biyu an shirya dawuri kenan " amsa suka bashi da " eh abie  "
"to Allah ya taimaka ya ba da sa'a"
da ameen suka amsa, mom  ta miko masu tea  da ta hada masu " thanks Mom" suka fada hadi da sa hannu suka Karba, basu fi minti 10 ba suka tashi suna goge bakin su da tissue paper suna fadin sai mun dawo , a dawo lpy su mom suka yi masu fice wa su kayi suna fadin Allah yasa.

Suna fita daga gidan sai ga school bus dinsu ta shigo anguwar, sai da ta kawo dai dai inda suke tayi parking, kofar bus dince ta bude shiga su kayi daga ciki suka nemi wuri suka zauna kusa da wannan friend din ta su Aeesha
Aeesha tace "twin friends yau wace rana kun fito da wuri kun hau bus first round " ta fada  da  murmushi a fuskar ta " kedai bari kawai Aeesha sa'a ce kawi yau " Aairah tafada yayin da Aaimah ke cewa " sai kace kema kullum da wuri kike zuwa Aeesha " dariya Aeeshar tayi hadi da cewa " ai wlh duk da haka gara ni dai "
"bawani nan, wlh kema muguwar let comer ce " Aaimah tafa da yayin da bus din keshiga cikin School
bus stop, bus din tanu fa parking tayi aka bude kofar student nata fita suna nufar assembly ground
Inda ss 3 ke tsayawa nan su Aairah suka nufa annan suka samu sauran yan class din su wanda suka zo dawuri, gaisawa suka shiga yi.
bayan 30 minutes aka gama assembly kowa ya nufi class din su

✨SHAZIM✨

Saukowa suke daga upstairs shi da Noraiz parlor Ammy suka nufa,  kan dinning suka same ta ,  gaishe da ita su kayi Noraiz yace  " ammy ina fatima nagan ki ke kadai kan dinning?  " amsa  ta bashi da  " Fatima ai ta wuce school"
" kai na manta fah, amma Ammy yau she take gama wa ne "
" tace man dai next month zasu fara exam,  daga wannan week din ma ta gama zuwa school sai kuma exam "
" Allah  ya taimaka ya bada sa'a, yaya " Noraiz ya kira Shazim dake zaune yana sauraron su, da na'am ya  amsa mashi  , Noraiz yace " amma dai yaya  fatima a abuja zatayi   university kamar yanda take bukata intagama secondary school  "sai da yayi kusan 5 seconds sannan yace "A'a nan za tayi  school din ta gata ga ammy,  " ya fada fuskar sa babu a lamun wasa, hankan yasa dole Noraiz ya kama bakin sa yayi shiru amma baiji dadin shawarar da yayan nasu ya yanke ba,  saboda  fatima ta ƙwallafa rai akan zuwa abuja saboda sa'ada , " Allah ya taimaka " kawai yace yaci gaba da breakfast din sa,  Ammy duk da  ta fison fatimar  tayi karatu kusa da ita.amma sai tace "wai shazim mi yasa kake haka ne, tun da kai ka janye jiki da  abuja, mi yasa suma zaka sa dole sai sun janye jiki da abuja ne wai, miye ai bun dan tayi karatu a can, duk ni ma nafi son tayi kusa da ni" ɗan nisawa yayi sannan yace "ammy ni ba haka nake nufi ba, kwai naga zaki yi kaɗai ci ne, ke kaɗai a gida "katse shi ammy tayi da cewa "in dai dan ta nine karka hanata zuwa abuja, idan bata nan baga ku nan ba kai da noraiz "
"ammy mu ba zama muke ba, idan muka fita tun safe sai dare fa muke da wowa"
"to naji sai dare kuke da wowa, itama idan ta je makaranta ba sai da yamma zata riƙa dawowa ba?  " ta ƙarasa faɗa da sigar tambaya tana tsare shi da idanu
"ammy dan Allah kiyi haƙuri tayi karatun ta nan, itama sai ta fi jin daɗi karatun, chan haya niyar innah kawai ta ishe ta " uhmm kawai ammay tace ba tare da ta sake cewa komi ba ,
Ba wanda ya sake magana cikin su har suka kammala  breakfast din , shazim ne ya fara ajiye fork din da yake cin arish hannu ya mika ya yagi tissue din dake kan dinning ya goge bakinsa sannan ya dauki robar ruwa ya sha,  ya  mike ya nufi sofar da ya ajiye briefcase dinsa ya na fadin "Ammy nizan wuce" cup din tea din da ta kai baki ta janye tana fadin " a dawo lafiya , Allah ya  ba da sa'a, an jima ka dan zanje gidan baba may be baza ka same ni sanda zaka dawo, dan zanjima kilama sai dare ma zan dawo "
" ameen, ina gaishe da malam,  sai na dawo" ya fada yayin da yake shirin barin parlorn, Noraiz  yace " a dawo lafiya Yaya, Idan na ajiye ammy gidan malam zan biyu ta wurin ka insha Allah "
" Allah ya kawo ka  lafiya " kawai ya fada hadi da ficewa, parking lot ya nufa motarsa wacce yasa aka wanke masa ya nufa, bude kofar motar yayi briefcase din sa ya aje da lab coat, sannan ya zagaya driver seat ya zauna , key yayima motar ya nufi main gate , gaisawa yayi  da ma'aikatan gidan sannan ya fice daman mai gadi yariga da ya bude masa gate,eko  ya nufa yana tafiya yana sauraron karatun alqur'ani a motar....

✨HIDAYA✨

Tsaye take gefen titin anguwar su  tana jiran  abun hawa, kusan 5 minutes tana nan bata samu abun hawa bata samu ba, wata bakar motace ta shigo anguwar tasu, tunda motar ta shigo anguwar tasu take ma motar kallon kamar tasan mamalakinta, motar na ƙarasowa  kusa da ita tana rage gudu,  kallon motar kawai take sai da ta kawo dab da ita sannan aranta tace" wannan ai kamar motar dr kabir " parking motar a kayi hadi da sauke glass din motar, kyakyawan saurayine fari amma ba sosai chan ba, akallah zai yi kima nin shekara 28 zuwa 30, sanye yake da blue din kaya complete riga da wando sannan fuskar sa sanye take da glass, hidaya  tace" ina kwana dr" amsa mata yayi da " lafiya lau , mikike yi tsaye anan " hidaya tace " ina jiran abun hawa ne dr" ok yace sannan kuma ysake cewa " to shigo ciki mu wuce  "
" A'a dr katafi kawai zan samu abun hawa insha Allah " hidaya ta fada,  glass din dake fuskar shi ya cire hadi da cewa " to fah, hidaya ko dai kina tsoron  na sayar dake ne iye " murmushi tayi hadi da cewa " A'a ba haka bane "
ajiyar zuciya ya sauke hadi da cewa " to inhar ba haka  bane, to kishiga mu wuce " to kawai tace hadi da zagayawa ta shiga ciki, key yayima motar yana cewa " wlh kina bani mamaki hidaya, sai kace wata ƙara mar yarinya in ki ka yi wani abun " murmushi kawai tayi masa ba tare da  tace komai ba, haka sukai ta tafiya yana janta da fira har suka iso  eko , parking lot din asibitin ya nufa hadi dayin parking, har tasa hannu zata bude kofa ya da katar da ita yana cewa " wai hidaya tsorona ki keji ne, naga har wani sauri kike ki fita"
"A'a " kawai tace hadi da duƙar da kanta ƙasa, " shikenan bakomi kina iya tafiya "ya fada ficewa tayi daga motar shikuma ya tsaya tatara kayan sa dake back seat, tana fitowa motar shazim na parking, dr kabir ne ya fito hannun sa riƙe da  tarkacen sa yana cema hidaya su tafi , tafiya suke sunkusa kawo inda motar shazim take sai gashi ya fito,miƙa masa hannu  dr kabir yayi  sukayi musabaha,   hidaya ta gaishe  da shi, da  lpy kawai ya amsa mata , wuce wa tayi tabar su shi da dr kabir tayi cikin asibitin, office din su da nurses kezama ta nufa, ba kowa ciki sai friend ɗin  ta maryam da alama wadan da suka zo duk sun fita.
" lafiya  yau ki ka yi late ? " maryam ta tambaya , ƙarasowa  inda take hidaya tayi tana cewa "ke dai bari,  banyi bacci bane jiya dawuri shiyyasa nayi late" dafa kafadar ta maryam tayi tana cewa " kingama yanke shawara yan da zaki tunkari dr da maganar koh "
" a'a gaskiya,  maryam ina jin tsoro ne, ban san ya dr zai dauki maganar  tawa ba " hannun hidaya maryam taja suka zauna sannan tace " ki kwantar da hankalin ki hidaya Insha Allah alkairi ne zai biyo baya,  kinji" ajiyar zuciya hidaya ta sauke tana cewa " to Allah yasa haka maryam " da ameen maryam ta amsa mata hadi da cewa " tashi mufita" ta fada tana jan hannun hidaya, fice wa su kayi suka nufi inda yan uwansu nurses suke, gaishe da junan su  suka shigayi , office din dr Shazim hidaya ta nufa tana cema maryam " sister bari naje office din dr na dawo"
"ok  sai kin dawo " maryam ta fada, office din hidaya ta nufa hadi da tura kufar ta shiga  bakinta ɗauke  da sallama.
amsa mata

Please Login or Register in order to submit comment