Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya suka bashi da kallo

Mamy hakima ta cewa momy," hajiya nifa yaron nan akwai abinda yake damunsa nalura tun barin walaya gidan nan yake cikin tunani,"
momy tace "to ai sai yayi tayi," mamy hakima tace " a a,
Bazamuyi tayi ba"

ta tashi itama tabi bayansa

Dakin tashiga, sai ganinsa tayi acan karshan gado, yana sheshshekar kuka, da sauri ta qarasa tace "Ahmad
Meyake damunka?
Please sanar Dani mana kaji"

Hawaye yagoge yace " Babu komai mamy"

ita mamy abin yabata mamaki, Gaba daya yasauya yaron kamar bashi ba, hakuri ta bashi taqara kwantar masa da hankali, waya tayi wa saudat tace takawo masa ko indomie ce yaci, bayan takawo tafice, tasan matsalar bazata wuce ta feenah Ba, Dan tasan basa waya tunda Wayarta akashe, to inbanda abin yaya Dan karasa budurwa awaya menene abin kuka? 🤣

Lalle sister tayi sa'ar saurayi mai sonta



** *** **



After 3 month's

Abubuwa da dama sun faru ciki harda bikin saudat inda ta Lula Abuja itada mijin ta farouq

Takarda yabata, ta karba tace "to Abban husna takardar menene kuma wannan?"
Yace "Bude ki gani yana murmushi"
Tabude tace " kamar qarin girma nake gani alhaji"

Abba yace "hakane maman nafeesa, nasamu qarin girma, nasamu lecturing awata NCE"
Mama tace" kai alhmdlh, gaskya Allah abin godiya
Ina kuke?
Mama tafada da karfi"

da sauri muka futo Gaba daya muka taya Abba murna, Abba ya kalleni Baice komai ba ganin cikin dake jikina yana qara futowa, yace " to a tashi aje ayi wasa yaran Abba"
Gaba dayanmu mukasa dariya, mama tace "haba alhaji yaran sun girma sai aure kana zancan wasa?"
Abba yace "aini yanda nake ganinsu wallahi maman nafeesa banqi ace na siyo musu yar baby ba suyi wasansu," mama tace "eh lalle Abban husna, aikuwa dole ku rabu Kodan aure ma," Abba yace "hakane," mude haka mukai daki muna daria



** *** **



Yana kwance awata "hadiqa" (wajan shan iska)
Ya lumshe idonsa, Zuwa tayi kwanta ajikinsa, yana Jin qamshin turaren ta, ya tabbatar itace ta qara so, hannu yasa yana shafa gadon bayanta

Idanunsa a lumshe Yace "haba my feenah meyasa zaki gujeni?"

Dora kaina nayi akirjinsa, ina shafa sumar kansa nace "my ahmad ina tare dakai a koda yaushe, kaima kasan bazan iya qinka ba, ahmad ina sanka,"
Bude idonsa yayi yayi tozali da kyakykyawar fuskarta, Dan lips dinta yasha pink din Jan baki, yayi kyau, tana magana ya Zuba Mata idanu, iska ta hura masa a fuska tace" haba hammad wannan kallanfa? "

Baice komai ba yahade bakinsu waje daya
Kokarin kwace wa take, dakyar de ta kwace tafara gudu yana binta sunata gudu suna dariya, tajuyo tayi masa gwalo" yeeee yakasa kamani"

Juya war da zatayi kawai ta afka cikin rami, da gudu yakaraso yace " my feeeeenahhhh!!!"

Azabure ya tashi daga baccin dayake, Gaba daya yahada wani uban gumi, Dakin ya kalla da esi da komai rigarsa ya cire Yabar best din ciki

Sumar kansa yashafa, ya kalli agogon dake ajiye a drowar gefen gadon karfe hudu na yamma, da sauri yatashi domin yagabatar da sallar la'asar




** *** **




"Yauwa maman nafeesa dama inaso zamuyi wata magana dake,"

"to Abban husna ina jinka"

"Munyi magana da Adamu akan maganar gidan mama, Toni shawarar dana bayar shine kawai asaida gidan ta nada mu siya Mata wani anan kusa da gidan adamun, toshi adamun yace minma akwai gidaje dayawa alayin zaije ya duba kawai sai asiya Takoma cikin satin nan, saboda can hotoron karya zama can din tana zaune ita kadai koda wata matsalar Zata tashi kinga kalatin tasu taje ta ganota"

Mama tace "eh hakanma yayi wallahi, Allah yasa hakanne yafi alkhairi, Allah kuma yaqara budawa," Abba yace "amin"

Yace "sai kuma magana ta biyu, Akan maganar uwata, nace saboda mutane masu shigowa meze hana Takoma can kano da zama gidan mama, kafin Allah yasauketa lafiya sai asan ya za'a yi, tunda kinga bazai iyu mu qara daukar wani zunubin ba wajan zubar da cikin kokuwa ya kikace "

Mama tace" gaskiya alhaji Babu abinda zamu ce dakai sai godia hakan ma yayi idan ta zauna anan muna tare ni na haihu itama ta haihu Babu dadi, "Abba yace" nima shine abinda nagani

Yanzu saiki fada Mata tahada kayanta Zuwa jibi saita tafi, nikuma zan kira maman nayi Mata bayanin komai, mama" tace "Toshiknn Abban husna Mungo de," yace
" da cikin wata nawane?" Mama tace " watansa biyar"
Abba yace "to Allah yaraba lafiya"
Mama tace " amin"

"Nafeesa!"

"Na'am mama"
"zo nan zamuyi magana dake"






Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱



Writing by Amnah el yaqoub




Dedicated to my family




26




Wani dumm takeji akanta, Gaba daya ganinta yake neman daukewa hakan ya haddasa Mata zama aqasa dabas
Cikin daki kuwa kuka na dinga yi hannu na yanakan kaina, ina na. "shiga uku na, Ahmad ka ha'inceni,"

husna ce ta zabga min mari, tace "zakimana shiru kosai na qara miki?"

Amma ina kojinta ba nayi kuka na nake haiqam, tace "nacemiki uban wa ya miki ciki, tun muna yara nasan wannan ba halinki bane, meyasa zuwanki makaranta kika sauya daga yanda muka sanki nafeesa,"

Jin Kiran sunana datayi kanta tsaye, shiya tabbatar min da lalle ran husna ya baci

Ban boye Mata komai ba, ina kuka nafada Mata, tana kuka itanma ta rungume ni kamar masu zaman makoki muna kuka, tace" ki shirya kawai gobe muje gidansu"

Nace Mata "bansan gidan ba"

Sake wani kukan tayi, mu kadai adaki muna koke koke, husna ce ta tuna da Aiken da mama tayi Mata, ta miqe da sauri tayo falo, kanta ne yayi wani mugun sarawa ganin mama datayi a zaune a kofar dakinsu, tana kallan waje daya kamar mutum mutumi, saurin goge idonta tayi tace "mama bari indora girkin autar bacci take,"

tayi hanyar waje, kallanta mama take, wato so suke su biyu Susan maganar ba tare da I yayansu sun saniba, basasan asirin daya daga cikin su ya tonu, tashi mama tayi ko magana bata yi Mata ba, tashige Dakin
Ina zaune abakin gado ina goge hawaye tare da tsinewa ahmad🤣 mama tashigo ta sameni

Tace "auta"

dagowa nayi cike da tsoro qarara Akan fuska ta, tace "ki fadamin tsakanin ki da Allah abinda naji haka yake"

kuka nafashe dashi nace " mama Dan girman Allah ki yafe min, wallahi mama ba laifi na bane Dan Allah mama ki rufamin asiri, wallahi mama badan duk wanda ya kashe kansa yamutu Dan wuta ba, wallahi mama dana kashe kaina da wannan abin kunyar, nayi DANA SANIN zuwana kano ma Gaba daya mama, "

Mama kasa hakuri tayi, ta rungume ni tana kuka, husna ma datake tsaye abakin kofa tashigo mama duka ta rungume mu muna kuka, tace" auta kiyi hkr, haka Allah mukuma ya jarrabemu da wannan masifa, "

tafada tana kuka kamar ba mama ba

Mike wa tayi tace" husna ku dauko mayafinku mu fita, "

Babu musu muka tashi, itama taje daki ta futo cikin hijab dinta
Waje muka fita, muka tari taxi, bamu zarce ko ina ba, sai wani private hospital, bamu dadeba muka nemi ganin likita, aka nuna mana office dinsa, zamu shige Gaba dayanmu wani yace mana" bayin Allah mutum dai dai ake shiga,"

mama tajuyo tace" dukanmu lalurar dayace,"🤣

mukasa kai ciki
Kujerar mama ce ta zauna, doctor ya kalleta da mamaki yace" mama yanaga ku uku,"

tace" kayi hkr dana "

Anan mama tayi masa bayanin tana so acire cikin dayake jikina, ko nawane yafada Mata sai su bashi kudin, likitan ya kalleta da mamaki
Yace" mama ni musulmi ne kema kuma nasan hakance, meyasa kun aikata laifi abaya kukesan qara wani laifin? "

Mama tace" yaro ka taimaka mana, bansan halin dazamu fuskanta ba daga wajan mahaifinsu dagani harsu,"

likita yace" mama kiyi hakuri gaskya bana wannan aikin

Kema ina baki shawara kiyi hakuri, kuje kuyi masa bayani idan bai yarda ba, ki sanar Dani nayi miki alkawari zan auri yarinyar ki ahaka, koda kuwa ata biyu ne,🤣"

mama tace" to yaro Mungo de "

Muka futo dukanmu jiki asanyaye,
Gida muka koma direct anan muka ga Abba yadawo yana zaune afalo, gabana ne yayi mugun faduwa, ganina shima zai gane halin danake ciki, yace" maman nafeesa ina ku kaje ne?
Tun dazu na dawo Gaba dayanku bakwa nan gida Babu kowa gashi ko abinci ma Babu,"

mama tace" ayi hakuri Abban husna yanzu za'a dora,"
tafada tana cire hijabin jikinta, nida husna muka zauna ahannun kujera kamar wasu baqi
Abba yakalllemu yace

" kukuma miye haka kamar wasu yara, Yau Babu hatsaniyar da kuka saba kenan? "🤣


Mama tayi karaf tace" to alhaji munje gidan gaisuwa ai dole jikinsu yayi sanyi, can bayane wata baquwa datazo ziyara, ta haihu danta ya mutu shine take kuka abin tausayi shine suma nan kagansu haka🤣😳"

Idanu muka hada nida husna, lalle iyaye Mata sunyi a rayuwa, Abba ne yace" kajiku da shirme to mutuwa ai tana kan kowa
Ke auta zonan ki hadamin wannan takardun,"

jikina yana rawa nace" to Abba,"
nakarba ina shiryasu




** *** **




After one month

Biki biki biki
Awannan nan lokacin anata hidimar bikin Ammu, kowa yana busy, musanman mama, saide duk ta rame, wannan Abu na nafeesa yana nukurkusarta, Gaba daya batada nutsuwa, ta kasa sanar da mahaifinsu, bangaren feenah kuwa, sai abinda yakaru Dan ciki yana Nan yana qara girma abinsa, watansa biyu yanzu yayinda na mama yake wata uku

Anata hidimar biki agidanmu duk dangi da yan uwa sunzo, munyi bala'in kyau cikin anko nida husna, dinkin Riga da sket
Yan'uwa kowa sai tankani yake, kai nafeesa kinyi fari, wannan yace kai kinyi qiba, haka de aketa min magana, basusan abinda yake raina gara ace ina zaune a yanda nake da ne ba
Boobs dina yawani ciko, haka hips dina sun qara baiyana, dinkin yamin dam dam ajikina

Hayaniyar mutane ta haddasa min ciwon kai, haka de na daure naketa kai kawo, muna tsakar gida, muna hada kayan miya, husna tana waya da doctor
Abba ya shigo da leda a hannun sa ta Maggi
Yace "uwata zoki karbi wadannan zan fita"
da sauri
Natashi nakarba kenan jiri ya debeni sai yarafff aqasa,
Abba yafara fadan" subhanallah husna batada lafiya ne? "

Husna tayi wulli da wayar hannun ta, tazo ta taimakamin mukayi ciki, tana fadawa Abba banajin dadi dama

Dakinsa na kwanta saboda ko ina akwai baqi
Yace wa husna" kiramin maman ku "
Bayan mama tazo yace" Mata meyasa mu yarinyar nan ne ba kuje asbiti ba har jiri nadibanta?"

Mama tace" zazz...zazzabi.. Ne yake damun ta, "

Abba yace" haba maman nafeesa kuma sai abarta haka? Ko husna aita rakata asbiti
Dauko hijabi muje mu kaita,"🙆🏻 gaban mama yayi wani mugun faduwa
Tace" Abban husna muna da baqi, tayaya zamu fita yanzu? "
Yace" ai yanzu zamu dawo ga husna nan ta zauna agidan "
Mama tace" a a kawai a bata magani tasha zataji sauqi "
Abba yace" to mahaifiyata, ina fada kina fada,😃 "
yayi Gaba
Mama tasan fishi yayi shiyasa yafadi haka
Dan haka taja hijab dinta ta rike feenah sukai asbiti tare da Abba




** *** **




Acan kano kuwa iyayan amarya maimuna sunata hidimar biki suma, daidai misali komai yana tafiya yanda yakamata
Zuwa dare kuma amarya Zata tafi zaria gidan mijin ta




** *** **



"Am likita kayimin bayani yanda zan gane, wannan yarinyar na kawo ma ba maman ta ba, 🤣maman ta itace mai Juna biyu,"

doctor Bala ya cire glass din idonsa, yace "alhaji haka bincikemu ya nuna, batada wani zazzabi ko malaria, munyi Mata text abinda sakamako ya nuna kenan"
Abba Gaba daya ya nemi nutsuwarsa yarasa duk jikinsa rawa yake, yajuyo yace "mamana,"
kawai yaga ina share hawaye

Yajuyo ya kalli mama yaga takasa hada ido dashi, kenan abinda likita yafada gaskiya ne,
Awannan rana dayake farin ciki zai aurar da qaninsa mafi soyuwa aransa Amma wannan yarinyar ta dauko masa wannan abin kunyar

Tashi yayi yana kade binjimar jikinsa yana fifita da ita ya cewa doctor "toshkn likita na gode sosai,"

yayi waje cikin sauri
Su mama ma sum sum suka bishi abaya

Amota Babu abinda kakeji sai sautin kukana, nasan tunda Abba yayi shiru tabbas akwai abinda yake shiryawa

Mama kanta tama kasa kallansa bare ni

Har muka zo gida Babu wanda ya cewa uffan acikin mu, muna Zuwa nafice daga motar da gudu nayi cikin gida, Abba yafuto ya kalli mama yace Mata "kin kyauta"

shima yayi hanyar masallaci



** *** **



Bayan sati daya, amarya ta tare agidan ta, suna zaune lafiya, Amma ta bangare na, Babu wannan lafiyar, Gaba daya Abba fishi yake damu

Ko gaishe shi nayi baya amsawa haka zan qaraci zamana Natashi, ta bangaren mama kuwa har gara nima
Ita kwata kwata bata ganin fuskar gaisuwar ma
Na rame nakara lalacewa

Cikin jikinane kawai yakesa aga kumari na

Washe gari Abba yana zaune afalo, yakira mama bayan tazo yace taje takiramu Gaba daya

Gabana yana faduwa naziro hijabi na na futo kaina aqasa
Husna ma tana Bina abaya muka zauna aqasa kanmu a sunkuye

Abba yace "Nafeesa"

Gabana yayi mugun faduwa yace "kafin nace dake komai nafeesa tashi ki dauko min jakar ki"

Mama ta kalle shi da mamaki me zaiyi da jakarta?
Daki nakoma ina kuka ina hada kayana, kusan kala biyar nadauko na futo, na tsugunna agabansu ina goge hawaye

Hannu yasa a aljihu ya dauko kudi dubu biyu yabani, nakarba

Yace "yauwa kama hanya kifice ki barmin gidana,"

mama batasan lokacin data tashi ba, tace "alhaji kamar yaya?
Ina kake so taje mace cefa," Abba yace "taje koma inane, nide bazata haifamin shege agidanaba, wallahi nayi tirr da halinki nafeesa nayi DANA SANI Akan karatun dana turaki kano, maza fice ki barmin gidana.










Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱



Writing by Amnah el yaqoub



Dedicated to my family



28



"Gani mama,"

"to autar mama, kinji de abinda Abban ku yace, kuma ni aganina hakan ai yafi ko auta?"
Nace "hakane mama, yanzu yaushe zamu tafi?"

"A a kibar husna anan taringa tayani wasu abubuwan kokuwa?
Idan kuka tafi Gaba dayanku kuma ai Babu me taimaka min,"

"hakane mama Toshiknn bari inje in shirya kayan"



** *** **



"Mama wallahi kinji de abinda yafaru,"

kaka cikin kuka tace "Amma ma'azu Baku kyauta minba, yanzu yarinyar mu zauna tare da ita Tsawon lokaci, wannan Abu yafaru bazaku sanar daniba, haba ma'azu,"
Abba yace "mama kiyi hakuri, wallahi abin ne ba shida dadin fadi, nasan kuma hankalin ki zai tashi Akan hakan,
Shiyasa nace kada su bari ma kisani, Amma yanzu de ga halin da ake ciki,"

"to yaushe Zata taho nafin"

"Gobe Zata taho insha Allah"

"To Allah yakawo ta lafiya"

"Amin mama"

Bangaren qanwar mama ta nufa, tana kuka ta sanar da ita komai, haka kalatynmu itama tahau kuka abin, gwanin ban tausayi



** *** **



"Salamu Alaikum,"

"wa'alaikumussalam," Abba yace "ah hassan anyi aure kuma shiru ake jinka" 🤣

Ammu yace "yaya kayi hkr wallahi awajan aikinmu ne suka doramin abubuwa dayawa, kuma dama gashi sai weekend ake samun damar Zuwa gidan,"
Abba yace "to Babu de wata matsala ko?"
Ammu yace "a a Babu komai, yaya dama ita maimunan ce tasamu Juna biyu, yana Gama fadar haka ya kashe wayar" 🤣

Abba yace "kai yaran zamani al'amarin su, saisu hassan ko kunya, to Allah de yaraba lafiya"


Haka yayi ta farinciki aranar



** *** **



"Sis kisa wannan ma may be zaki buqata,"

"kai barshi anty husna, wannan kayan ma sun isa,"

"tokisa books dinki, karki zauna kina tunani gara kina dubawa ko?"

"Ok" nace nakarba nasaka acikin jaka, tsaf nagama hada komai

Abba zai wuce school yabani dubu goma yace in rike, koda abinda zan buqata, mama ma tabani kayan miya da komai tace na kaiwa kala, husna kuma tace idan naje na mintsini kaka 🤣

Su dukansu ne suka kawoni inda zan hau mota, hijabin dana zirma ajikina shine ya boye abinda yake tare Dani

Saida motar mu ta tashi, sannan su Abba suka dawo gida, shikuma ya wuce mkrnta daga nan

Anty maimuna anata fama da laulayi, danma husna tana Zuwa wani lokacin tana taimaka Mata, ga kuma mama da itama kusan kullum batajin dadin jikinta



** *** **



Ina hanya araina nace, Allah sarki su mama koyaya suka koma gida, abinda na tuna ne yasa natura hannu na cikin jakata da sauri
Wayata na dauko wadda ni kaina namanta lokacin dana kashe ta, so nake kawai inji muryar su mama da husna

Ina kunnata tafara hooking, text ne suke ta shigowa ba ma adadi, wasu na qawayen mu ne wasu na Zeey Akan tayi missing dina, saina Atu tana fadamin takirani bata sameni ba, Amma tanamin albishir Akan ta haihu tasamu mace, murmushi kawai nakeyi, text mafi yawan kuwa daga ahmad sai saudat

Kuka nafara lokacin dana karanta na saudat

"sis mene duniyar kuma? Kin wani tafi zaria kin share ni "

" sister feenah wallahi nayi kewar ki, wai kinsan ma meya faru, wallahi daddy yayimin miji "

" sis feenah yasu mama Allah yasa de lafiya Bama samunki, dan'uwana yana cikin tashin hankali feenah, har kuka yi yake a dalilin ki "

" sister andaura aurena Yau, shikkenan kinji dadi tunda kinsan banda hanyar dazan sameki balle in fada miki "

" sister sunan mijina faruoq, yana sona sosai, mun tafi Abuja, kema ina muku fatan kasan cewa tare keda yayana "

Ire irin wannan text din saudat taita turomin, nagama karantasu ina hawaye

My ahmad, shine sunan da na ambata araina, text dinsa rututu, harma narasa wanne zan Buda

" my feenah, ina kika shiga ne, Dan girman Allah ki yafemin"

"nafeesa nime laifi ne awajanki, kuma gani na durqusa kafafuna aqasa ki yafemin "

" my feenah, bansan wacce kalma zanyi amfani da itaba wajan neman yafiyarki, ki yanke min kowanne hukuncin da kikaga ya dace Dani "

Ina karanta wannan afili na furta zakaga abinda ya dace dakai kuwa, na goge hawayena

" Haba yarinya tun dazu sai kuka kike, haba ni wallahi kinsa duk jikina yayi sanyi, ni natsani kuka wallahi, ai sai kisa muyi zatan mutuwa zamuyi ahanya, a a, muka sani koke alama kika gani" 🤣

Wata tsohuwa ce a kusa da feenah take wannan mgnr,
Ban kula taba kawai nagoge hawayena,
Su mama nakira, saida naji muryarsu hankali na ya kwanta, ina sauke wayar a kunne na, kiransa yana shigowa

My ahmad yafuto baro baro a fuskar wayar, yana zaune a office kamar wasa ya gwada number, aikuwa yanaji ta shiga ya miqe tsaye
My feenah daga mana, yi sauri ki daga Dan Allah, shi kadai yana magana kamar zautacce

Har wayar tayi ringing ta kare ban dagaba, wani Kiran yasake shigowa, nayi rejected, dana uku ya shigo a fusace na daga, nace

"waye?"

Acan bangaren baiyi mamaki ba, yace "feenah,"
nayi shiru
Yace "Dan Allah kiyi hakuri"

Nace "hakuri? Ahmad ashe kasan hakuri?"

Cikin kuka naci gaba dacemasa "ahmad wanne irin hakuri ne ban baka ba Akan ka kyaleni?
Menayima ahmad? Kasan halin daka sani kuwa? Wallahi nayi DANA SANI Akan kula ka ma danayi tun farko,"

kuka yaci karfina, cikin sheshshekar kuka nace" Dan Allah ka fita daga rayuwata, bana sanka na tsaneka ahmad karka sake nemana, "

nasauke wayar daga kunne na

" Kayya yarinya kiyi hakuri, haka mazan suke, rayuwar aure da kika ganta sai hakuri,"🤣

kawai tafara goge hawaye, kallanta nayi da mamaki ni shaf ma namanta tana kusa Dani

Cikin sauri nayi copy din number's dina suka dawo kan waya, nakarya layin, na wullar dashi ta tagar motar




** *** **



" Wash Allah kirjina,"

yafada yana dora hannunsa Akan kirjinsa, kansa ne yasara yagaza zama, har saida yadora kannasa Akan tebir din dake gabansa



** *** **



Adedeta na saukeni, naja jakar kayana nayi cikin gidan, kai tsaye bangaren kaka nayi, tana ganina tataho da sauri tazo ta rungumeni, sai kuka, ni kuka ita kuka
Zama mukai afalo tace" sannu nafi, ashe wannan ne abinda yafaru, Amma kika kasa fadamin,"
nace" kaka to ai nima bansan Shiba, "

Tace" keee nafi
Ki fadamin gaskya, nasan yaron dayake Zuwa wajanki kawai yayan saude ne, kifadamin idan shine wallahi anbinciko min shi, kokuma inbada cigiyarsa agidan radio"

Bansan meyasa ba kawai de na tsinci kaina da fadar " ba shi bane kaka," tace "to koma wanene Allah yasaka miki," nace "amin kaka"



** *** **



Cikin sauri yake tafiya har yazo gaban office din nasa, hannun sa dauke da takardu, sakatariyar ya yiwa magana cewa" yallabai kuwa yana Nan? "
Tace" eh yana ciki tun dazu "
OK kawai yace, yasamu waje ya zauna yace" kiramin shi, kice masa maganar takardun sababbin motocin nan ne"

Takira 2 time's Amma bai dagaba, Dan haka tace kawai yashiga may be, wayar bata kusa dashi ne

Ahankli ya tura kofar office din yashiga, gaskya office din ya tsaru, ga photon sa nan yasa manyan kaya farare yana murmushi amanne Ajikin bango,
Nishin dayaji ne yadawo dashi daga tunanin daya tafi
. "Subhanallah yallabai, Garin yayi haka?"
Kamashi yayi, ya kwantar dashi Akan doguwar kujera wayar office din yadanna, nan da man likita yazo,
Yayi Dan dube dubensa yadago yace "gaskya oga saide muje asbiti" "Ok" kawai Ammu yace

Ya cicciboshi, sai mota, shawara kawai yasake yajuya kan motar sai asbitin doctor tahir

Dayake ahmad sananne ne, nan da nan aka karbeshi aka kai shi wani daki

Office din tahir yanufa, yamiqa masa hannu suka gaisa, tahir yayaba da kamala irin ta Ammu, haka shima Ammu nan take yaji tahir ya kwanta masa arai, bayanin abinda yakawo su yayi wa tahir, ai cikin second da basu wuce biyar ba yanayin tahir yasauya, cikin hanzari yayi Dakin da ahmad din yake



** *** **



Naci abinci dakyar, inajin wani daci amaqogarona, dakyar de nadan caccakali abincin, nayi wanka na kwanta, kala ce ta shigo, tace "idan na huta saina tashi nakoma bangaren ta"
Ai kaka najin haka tace" a a Babu inda nafi Zata ina nan tare da ita,"🤣

ba yanda kala ta iya haka tahakura,
Ina kwance ina tunanin duniya na shafa cikina araina nace kome zan haifa? Ko idan ya tambayeni mahaifinsa yaya zance?
Wai nice da ciki, cikin ma na shege
Hawaye naji ya ziraro min nasa hannu na goge wallahi banasan cikin nan, tunda de shima jinin ahmad dinne
"wallahi bana sanka"

nafada afili hannu na nadauke daga kan cikin, nasake cewa "nikam bana sanka," 🤣

wani motsi naji cikin yayi, nace "shikkenan qarasa ni ma kamar yanda shima yanemi kashe ni, ranar nan"



** *** **



Tahir yace "haba ahmad, meyasa kake San saka kanka cikin matsala ne?"

Ba tare daya kalleshi ba, yace "tahir najima acikin matsala ai, har Zuwa Yau dana same ta"
Tahir yace "bangane ba," ahmad tiryan tiryan yabawa tahir labarin komai
Tahir yace "gaskya tadau zafi dayawa, yanzu yaya za'ai?"
Ahmad yace "wannan mgnr da fadamin itace takemin yawo akaina tahir ta tsaneni, nafeesa ta tsaneni," sai hawaye
Tahir jikinsa yayi sanyi yace "ahmad kasan Mata, zafi ta dauka dayawa, nanda wani lokacin Zata huce komai ya wuce ka kwantar da hankalin ka, muci Gaba da addu'ah kaji, kaga yanzu jinin ka yahau, kuma sosai ma hawan jinin dole saika rage tunani, kayi hakuri abokina haka tamu qaddarar take, "


ahmad baice komai ba, ya lumshe idonsa

Turo kofar Ammu yayi, yace" doctor yajikin yallaban? "
Tahir yace" alhmdlh jikin da sauqi, dan Allah abokina ka dinga kula dashi nabaka amanar amini na,"🤣

Ammu yace" Babu komai insha Allah "

Bude idonsa yayi a hankali ya cewa Ammu," kaje kaci Gaba da kula da komai, zan wuce gida ta nan,"


Please Login or Register in order to submit comment