Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi ajiyar zuciya, yace" ahmad karka damu inde Akan wannan ne, idan ma basu yarda ba, nima zan shiga cikin maganar insha Allah zasu bamu ita,"

yaqarashe maganar yana murmushi, ahmad yayi masa wani irin kallo, yace" abamu ko abani?
Aiku kun nema anhanaku, yanzu lokaci nane, "
tahir yace

" to hammad baban izdihar, "
ahmad yasaki daria kamar bashida damuwa yace" kai Amma tahir naji dadi wallahi, idan aka bani izdihar wannan uncle din datake kirana dashi denawa zatayi, takirani da.... ''

Cikin sauri Tahir ya katse shi, yace "daddy?"
Ahmad yace "no banasan daddy
Nafisan takirani da Abeey," tahir yace "um kun koma larabawa kenan,"

ahmad yace "ka manta da jikansa kake tare, Dan renin hankali kawai,"

tahir yace " naji,"
Ahmad yaci gaba da fadin " idan kuma na auri my feenah, nasan itama inde taga baby Zata sota, kaga ita kuma saita dinga kiranta da ummi"

Tahir ya harare shi cikin wasa yace "wannan ai sata ce, da gasa" 🀣


Ahmad yace "edin mun sata,"

tahir yazuba masa ido yana kallansa cikin ransa yace Allah yabaka feenah ahmad, wato har yanzu de tana nan aransa, ahmad yace "gaye kallanfa?"
Tahir yace "kawai so nake naga yaushe zaka haihu, bansan wanne irin so zakayi wa yaranka ba, wannan yarinyar izdihar ma kana Mata irin wannan son"

Ahmad yabata fuska yace "oh tahir naroqeka kadena banbanta izdihar da yaran dazan haifa, itama yata ce"

Tahir yazuba masa ido yana ganin karfin Hali, yace "Toshiknn daddyn izdihar, magana yaqare"

Ahmad yayi shiru, sai can yace "tahir nikuwa kunada irin qwayar da aka sakamin nasha?"
Tahir ya kalleshi da mamaki, yace "eh akwai mana me zakai dashi?"

Ahmad yace "nikuwa me zanyi dashi tahir kawai ganinta zanyi"
, waya tahir yadauka, yabada umarni, nan da nan aka kawo masa ita,tahir yace "kaganta nan idan mutum yasha ta wuce guda biyu, shine take yi masa illah,"

ahmad yakarba ya karanta, yace "shikkenan nagani ungo abinka

Nizan wuce gida,"

tahir yace "Amma ahmad bamuyi magana Akan magungunan dazaka dinga shaba,"
Ahmad yace "no karka damu tahir, nafadama nifa izdihar ta isheni, kabar maganin kawai, latter mayi magana,"

tahir yace "ok,"
yafuto domin rakashi wajan mota, anan yajashi yafara nuna masa yanda yakeso ya maida fasalin hospital din


** *** **


"Mom wallahi bazan iyaba, dama nafada miki, ai wannan zaman danayi ma nayi hakuri, kinga kuwa yanzu tunda bazai iya haihuwa ba, mezan zauna inyi agidansa,"

hajiya salaha tace
" gaskya kam tayaya ma zaki zauna da mutum fanko, ai gara kibar masa gidan, wannan jaraba har ina, Allah yabaki wani kawai,"

laila taka she wayar ba tare datace amin ba, mai taxi din tabawa umarni yaqara sauri, tagaji da wannan tafiyar dayake kamar bayaso
Tana Zuwa gida batayi bangaren taba, Part din su mamy tanufa, suna zaune dukansu mabruka, yan biyu Muslim da bukhari, da auta maryam, laila tashigo duk bata hayyacinta
Mamy hakima tace "laila lafiya?"

Laila tace "mamy da momy zanyi magana bada keba" 😳

Mamy hakima najin haka aranta tace babu lafiya, mom tace "inajin ki laila meya faru?"
Laila ta kwashe komai tafada musu, tace
" nikuma bazan iya zama da juya ba, Dan haka ku fada masa yasakeni, bazan iya zama babu yara ba, ashe ma Dan naku Dan shaye shaye ne, inba Dan qwaya ba, meya hadashi da shan qwaya har takai shi ga samun matsala, to nide bazan iyaba,"

tana fadar haka tajuya tayi gaba

Mabruka dayake itace babba maidan hankali, nan da nan tafara kuka, momy tace" innalillahi wa inna ilaihir raju'un"
Mamy hakima kuwa itama kuka tasa, tace
" mun shiga uku, wannan wacce irin masifa ce Zata shigo mana gida, gaskya nikam ban yarda ba"
Mamy tace "hajiya ba'a shedar Dan Yau, Muslim dauko min wayata"
Yana kawo Mata wayar, ta kira ahmad tace
" waladee kazo gida yanzu inasan ganinka,"

ahmad najin haka yace cikin ransa sun samu labari kenan 🀣


** *** **


"Haba Abban husna, wacce irin magana ce wannan? Ahmad fa yayi mana komai, nikam yaron ya kwanta min araina, nayarda da tarbiyar shi, Dan haka inde nice babu damuwa na bashi baby," πŸ™†πŸ»

Abba yace "to shikkenan alhmdlh, yanzu zamu fadawa ita nafeesa ne kokuwa?"

Mama tace "haba alhaji ita take iko damu kokuma mune muke iko da ita, idan aka bada baby kamar qarin rufin asirinta ne ai, Akan abin kunyar data janyo mana, Dan haka ni aganina kawai aqyaleta,"

Abba yace "to insha Allah idan tadawo sai nayi Mata bayani dakaina," mama tace "hakan yayi,"

Abba Ammu yakira awaya, yafada masa shawarar dasuka yanke Akan maganar ahmad, Ammu cikin ransa yace gaskya ahmad yasamu karbuwa sosai awajan yaya
Shima kai tsaye yace " ai Babu komai, ahmad kowa yana masa shaidar kirki,"
Mama tace "to ai kaji alhaji, nikam wallahi banji dadi Bama daka bashi sati dayan nan, sai yaga kamar bamu yarda dashi ba, Dan haka kirashi kafada masa gobe yazo yadauke ta su tafi, tunda itama kanta yarinyar tana sanshi,"

Abba yace "hakane, Amma kinsan komai yana buqatar shawara, shiyasa na bashi sati dayan," sake daukar wayar yayi, yakira ahmad, alokacin yana kan hanyar sa ta Zuwa gida, Abba yana fada masa, ahmad ya dinga kwarara godiya, kuma yace insha Allah gobe zaizo gidan, dahaka sukai sallama, parking yayi agefen titi, yafuto daga motar yayi sujud shukur, yanata farin ciki, sannan yakama hanyar gida


** *** **


Yana Zuwa gidan,tun kafin yagama gyara parking din motar sa laila ta taho da sauri tace,
" dama jiran ka nake, ahmad inaso kasani zamana dakai yaqare, kasakeni kawai shine abinda nake buqata,"

ahmad yace " laila kanki daya kuwa? Meya kawo wannan maganar? Kinga kije ciki, ina Zuwa zanzo sai muyi magana,"
tana huci tayi part dinta

mabruka naganin ahmad yashigo falon tahada kan qannanta sukai daki, momy tatashi cikin fishi tace" ahmad mai nakeji? "
Ahmad yace cikin rashin damuwa" momy me yake faruwa naganku haka?"

Momy ta dauke shi da mari, cikin sauri ya riqe kumatunsa, cikin mamaki yace"momy?"
Mamy hakima tace "my son, meya kaika shaye shaye har hakan yahaifar ma da rashin haihuwa?" Ahmad yace "shaye shaye mamy, ni ban taba shaye shaye ba" ,
momy cikin fishi tayi kansa tace "laila karya Zata ma ne?
Kokuma mune zamuyi Maka karya?"
Ahmad zuciyar sa takarye, nan da nan yafara kuka, yace "momy ki yarda Dani mana, wannan bahali na bane,"

mamy hakima tace "munji Ahmad Amma me yake faruwa,"

cikin hawaye ahmad yace "momy, mamy, kuyi hakuri, ni ban taba shan qwaya ba, wannan dalilin ne yasa nakori walaya daga cikin gidan nan, wani yabata magani da kudi Akan ta sakamin acikin lemo nasha, kuma tayi nasara akaina, nasha, nasha momy"

ya qarasa yana kuka 😭

Yace "wannan qwayar datasamun itace dalilin dayasa likita yace bazan iya haihuwa ba, saboda nasha dayawa, sannan... zaici gaba da magana wani irin Baqin ciki yatokare masa maqoshi, har gobe idan yatuna abinda yayiwa feenah abun yana qona masa rai

Momy tayi jagwab ta zauna Akan kujera, mamy hakima tace "mun shiga uku, meyasa baka fadaba ahmad? Aida an tambayeta waye yasa ta aikata hakan"


Ahmad yace "mamy na tambayeta harma tabani number datake magana da mutumin, Amma alokacin ina cikin fishi, saina fasa wayar"

Mamy hakima tace
" innalillahi, kaga tashi kaje kabawa matar ka hakuri, zamuyi magana anjima"
Ahmad ya share hawayen sa, yatashi yafita

Yana Zuwa part din, yaga laila bata nan, Dan haka yabita daki, tura kofar yayi a hankali yashiga, Amma kuma waya take bataji shigowarsa ba, taci Gaba da waya tana fadin

"Wallahi sofy kede bari, ai nake fada miki, qwayar dana bayar asaka masa ne kwanaki, πŸ˜³πŸ™†πŸ»toya zanyi sofy, nakira shi nayi nayi dashi tawaya ina kaunar sa, yabani dama inbaiyana masa son danake masa, Amma yaqi, shiyasa kin sanni ba jira nabawa musa aikin, Naso kawai dana dandani zumar sa in wullar dashi, Amma bansamu hakan ba, Dan haka nayi amfani da yar aikinsu kawai, kuma still shima abun yaci tura, kinga kuwa dana sameshi yanzu sama taka, ai kinga saina kyaleshi kawai, yasakeni kawai, akwai alhazan dasuke jirana "

Idonsa ne ya rufe ruf, yadena gani, kamar makaho haka yajuyo baisan inda yake jefa kafarsa ba, yanabin bango ahaka ya qarasa falo, kan kujera yafada, yana ambaton

" innalillahi wa inna ilaihir raju'un 😭 "







Mrs Usman ce πŸ–Š
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my lovely sis golden girl

44

Tsugunna wa yayi daidai tsawon ta, yafara kallanta, itama zuba masa ido tayi, tana aikin kallonsa, ahmad yace "ya sunanki? Kuma keda waye kike gudu haka?"

Tace "sunana Baby" , ahmad yace "baby kuma?"


Acan cikin gida kuwa, mama ce tanemi husna tace "yi sauri, naga su baby sun fita da gudu, nasan fada suke jeki kirasu"

Ahmad yace " nace keda waye kike gudu haka?"

Tace "nida qannai nane, gasu can,''
su mima ne suma suka taho da gudu, suka riqe ta suna" mun kamaki,"

mama tace" laaa uncle,"

nan da nan dayake su sun sanshi suka riqe shi, ahmad yace " kunga muje kushiga gida kudena guje guje,"

Ammu ne yahango shi tare da yara, yaqaraso da sauri, yace

"yallabai fada suke ko? Bari nakai su gida,"

cikin sauri ahmad yace "a a hassan bari in kaisu, kasan wannan yarinyar ne?"

Yafada yana nuna baby, Ammu yace "eh nasanta," ahmad yace "ok bari in kaisu,"

nan kuwa yafadi hakanne danya sake samun damar kallan yarinyar

Saida yakawo su har bakin kofar gidan, Amma hankalin sa yanakan wannan yarinyar, nan sukai kicibis da husna, cikin sakin fuska tace
"a a kaga angon lailah,"

ahmad yace "gwauruwa"
Husna aranta tace um Yau kuma yan wasanne akansa,
Gaisawa sukai, yace
" Mata nima nazo daurin aure ne, saikuma naqare arabon fada,"

husna tace "ai inde izdihar ce har ka gaji, haka take bataji, kuma fadan ma da qannanta ,"

ahmad yace "au haka sunan ta?" Tace "eh"

Cikin ransa yace "izdihar"
Suna mai dadi
Sallama ya yiwa husna, yajuya yana kallan baby yatafi

Husna tace "sarakan rigima saiku juya mutafi aiko,"

tayi gaba su mama suna bayanta, juyowa tayi kawai sai ganin baby tayi ta tsaya tanata kallan ahmad dayake tafiya, husna tace "wannan yarinya bataji,"
ta daga murya tace "baby taho mana,"

da gudu izdihar ta taho


** *** **


Gida yakoma cike da gajiya, kasancewar yatsaya gaishe gaishe duk yagaji, dining ya kallah, aransa yace " tofa Yau yaushe"
Daki yashige yayi wanka yafuto da kayan shan iska ajikinsa, afalo ya zauna ya kunna kallo, Amma Gaba daya tunanin sa baya tare dashi, yana tare da yarinyar nan, murmushi yasaki daya tuno ta, aransa yace meyasa nakejinta araina ne haka?
Allah sarki my feenah, bayan rabona dake Yau naga photo copynki,ya Allah!
Meyasa nakasa cire yarinyar araina, laila ce takatse masa tunanin sa, tace " Majnunun lailah, ga abinci a dining fa naga ko budewa bakayi ba,"
ahmad yace "ok aiji nake wani kika hadawa, tunda naga bayi kikeba, sannan laila naroqeki Dan Allah kidena fadamin sunan nan, banajin dadin sa," 🀣

laila ta harzuqa cikin fishi tace "ok bakajin dadin wannan sunan, saide feenah ko?"

Ahmad ya kalleta da mamaki, "ya akai kikasan wannan sunan?"
Laila tace. "ai dole kayimin wannan tambayar, kullum bakada aiki sai Kiran sunanta da daddare, wallahi zan nemi wannan yarinyar sai jikinta yagaya Mata" ,

Ahmad baisan lokacin daya saki daria ba, ya kalleta yace, "da gaske? Amma wallahi Dakin taimaka min, ni kaina nemanta nake, laila da kinyi babban jihadi idan kika shiga duniya kika nemota, ni kaina dana soki" 🀣


Zuciya tazowa laila wuya, cikin takaici tajuya tayi daki, wato Yama maidata mahaukaciya, itace Zataje yawon duniya ta Nemo masa mace, lalle 🀣


** *** **


After 2 months
"Uncle, idan nayi tsokana zaka dinga taremin?"

"To meyasa zakiyi tsokana? Bakya Jin magana ko?"
"To uncle kenan kai baka sona ko? Nikam ina sanka"
Cikin sauri ahmad yace
" izdihar ina sanki mana," turo Dan qaramin bakinta tayi, tace "nide um um, natafi tunda baka sona, bakasan ka taremin tsokana,"
ahmad yace "ina sanki mana, tsaya kiji,"

"a a uncle natafi baka sona,"
kawai tasa gudu, yana "baby! Baby!!"

Amma ina tatafi

Cikin baccinta taji yana fadin "Baby ! Baby!! Baby!!!"
Takaici ya isheta, fillon dayayi matashi dashi tajanye, cikin sauri yafarka daga baccin dayake, yace "laila, lafiya ina bacci zaki tasheni?"

Laila tace "wato abin Naka kullum qara ta'azzara yake,🀣
da kaine feenah, yanzu kuma ka dawo Kiran wata baby
Wacce shegiya ce baby kafadamin?"

Ahmad yace "Allah yabaki lafiya," 😏


yadauki fillonsa yakoma falo
Daga murya tayi yanda zai jiyota, tace "saide yabamu lafiya Gaba daya, bazan iya zaman wannan jarababban auren ba,"
tayi juyi gamida rufe idonta


** *** **


Ita kadai ta qyalqyale da daria, tana zaune afalo, da teddy ahannun ta, mama datake linke kayan Abba tajuyo ta kalleta da mamaki, tace
" izdihar kedawa haka yarinya kamar me aljanu? "

Baby tace" mama rannan na tuno, naqwace abin wasan su mima nagudu, ingaya miki ko mama ina fadawa wani mutum yaqi karbe abin daga wajena, kuma yake ta kallo na, shine nima naketa kallansa, kuma kullum kullum saina tunashi mama "

Mama tace" yaushe kika ce? "🀣


Baby tace" mama nace miki rannan "
Mama tasake kallanta cikin mamaki tace" toko amafarki kika hadu dasu? "🀣

Baby tace" mama rannan fa da mukaje auren anty aysha"
Mama tace "kekiji shirme, Abu kusan wata biyu,amma kicemin rannan"
Izdihar tasa daria, tace "to mama kema zakina taremin idan nayi tsokanar?"
Mama tace "ban fada miki ba, shima kuma bai kyau tamin ba, dabai dakekiba, tunda ke kullum kunnan qashi ne dake"
Mama tana wannan fadan Wayarta tadau qara, feenah ce ta kirata, bayan sun gaisa mama tabawa baby wayar, Ana bata wayar tayi daki da gudu, tana cewa, sabuwar anty, infada miki rannan nahadu da wani ya taremin tsokanar danayi 🀣


Mama aranta tace ai Yau kuma mun shiga uku πŸ€”πŸ˜ƒ

** *** **


Wayarsa yadauka yakira hassan, cikin sauri Ammu yasameshi a office dinsa, ahmad yace
" yauwa dama inasan inma wata tambaya ne, yarinyar dana gani kwanaki, shine nace Dan Allah inane gidansu, inaso inje inganta"
Ammu ya kalli ahmad da mamaki, yace "wai izdihar?"

Ahmad yace "eh itafa, wato hassan inajin kaunar yarinyar ne acikin raina, yanda baka zato, tun lokacin dana ganta, naji inasan kasancewa da ita, please a wacce unguwa suke?" πŸ™†πŸ»

Ammu yayi murmushi yace "ai yallabai a zaria take,"

gabansa ne yafadi, cikin ransa yace zaria, garinsu feenah fa kenan

Ammu yaci gaba da fadin "ai yarinyar yaya nace, itace qaramar yarsa,"

ahmad yace cikin "mamaki yayanka?kenan kanaso kacemin sister husna ce?"

Ammu yana murmushi yace "hakane yallabai,"

ahmad yace ikon Allah, to bani address din gidansu please, saboda bazan gane ba, rabona da naje Tun bikin su Husna "

Babu bata lokaci Ammu yabashi, ahmad baiyi wata Wataba washe gari yatafi zaria,πŸ€”
da rana ya isa gidan, yafaka motarsa a gefe, manyan kaya ne ajikinsa, yatsaya awaje, yarasa wazai aika ayi masa sallama damai gidan
Kamar anjefota saigata da gudu tazo Zata shiga gida, aransa yace yar halak, wato itade da'iman tana cikin gudu, daga murya yayi yace "baby!!"

Juyowar dazatai ta ganshi, wajanshi ta qaraso da sauri, ahmad yace "daga ina kike da gudu haka ?"

Tace "daga school"
Saida tafadi haka sannan ya lura da uniform din jikinta, da kuma lokaci, yasan yanzu ne ake tashin yara a school, yace "to zo nan"
Matsawa tayi kusa dashi, ahmad ya tsugunna daidai tsawon ta, yace
" kin gane ni?"
Baby tace "emana, kullum saina tunaka, jiyama nabaiwa sabuwar anty labarin ka" 😳

Ahmad cikin ransa yace kullum saita tunani, tome yake shirin faruwa ne? Yace "nazo ne nima naganki,"
washe baki tayi tace
" Allah?"
Kafin yabata amsa tace
" ina sonka,"

tafada jikinsa, ahmad yayi saroro, baiyi wata Wataba shima ya rungume ta 🀣
Tsayuwar motar dasuka jine ya ankarar dasu, baby tatafi da gudu wajan Abba, tace "sannu Abba,"

Abba yace "sannu izdihar"
Yafada yana kallan ahmad, kamar yasan fuskar
Ahmad yaqarasa suka gaisa, Abba yace "kamar Naso in gane ka"
Ahmad yayi murmushi yace Abba "ahmad ne abokin tahir"
Abba yasaki murmushi yace "yauwa nifa ince,"

nan suka sake sabuwar gaisuwa, Abba yace
" qaraso mana"
Cikin gida suka shiga, mama takawo masa ruwa da lemo, Abba yayi shiru shima ahmad yayi shiru,🀣

shi dama gashi ba damunsa maganar tayi ba, can de yadaure yace
" Abba dama nazo ganin baby ne,

" Abba yace "wai izdihar,? ikon Allah, izdihar mai jama'ah," 🀣

kiranta Abba yayi, tana Zuwa tace "Abba ga wanda nabaka labarin sa rannan nace yataremin tsokana,"
mama da zuwanta kenan tace "au wai dama shine yatare miki tsokanar? Ikon Allah, ai labarin ka babu wanda baiji ba agidan nan," 🀣

ahmad yayi murmushi
Baby wajansa Takoma, tazauna a kusa dashi sosai, tasan idan tazauna ajikinsa Abba dukanta zaiyi
Mama da Abba fita sukai suka barsu
Abba ya kalli mama yace
" ina tasan shine?"😳

Mama tace"to wa yasani ne alhaji, nide cemin tayi awajan auren aysha,"

Abba yace" tofa ikon Allah, Allah mai hada jini "

Sai yamma lis ahmad yace zai tafi, sweet, yar baby, teddy, Babu abinda bai kawo wa baby ba, dazai tafi yanda kasan tashige motar, saida mama ta riqeta 🀣

Awannan dare Baby rasa inda Zata dora ranta tayi saboda wannan kayan wasa
Ammu ne yakira Abba da daddare, suna zaune shida mama a tsakar gida, bayan sun gaisa Ammu yace "yaya dama yallabai ne yace in bashi address dinka, zaizo yaga izdihar,"

Abba cikin mamaki yace "waye kuma yallabai?"

Ammu yace " wanda nake aiki akamfaninsa,"

Abba yace "wai dama kaine kabashi address din gidan nan?"
Ammu yace "wai yazo ne yaya?" Abba yace "dazu dazu yatafi,"

Ammu yace " jiya jiyafa na bashi, Amma har yazo Yau?" Abba yace "wallahi yazo, nayi mamaki ma dayace ganin izdihar yazo,"
Ammu yace "wallahi yaya nima nayi mamaki, da yacemin yana qaunar baby," Abba yace " Allah kenan mai hada soyaiya
Anan sukai sallama"

** *** **

After 5 months
Abubuwa dadama sun faru,ciki harda shaquwar baby da ahmad, harya kasance ahmad baya sati daya batare daya zo yaga baby ba, ta saba dashi yanda mai karatu baya zato, harya kasance yanada number mama da Abba, kowa yakira acikin su zasu bashi ita awaya suyi ta fira kamar ba kudi yake sakawaba, sosai abin yake daurewa su mama kai πŸ€”
Sun yarda da ahmad sosai, sun dauki son duniya da yarda sun bashi, har bashida iyaka da gidan, yana Zuwa zai shiga kamar dan gida, saide abinda yake damun ahmad guda daya ne, duk lokacin dayazo idan zai tafi da kuka yake rabuwa da baby, yariga yayardewa kansa cewa kawai Allah ne yahada jininsa dana yarinyar, kuma yake qara Santa saboda kamar dasuke da feenah


** *** **


Cikin office dinsa yakira Ammu, ahmad yace
" hassan dama wani aiki zan saka,"
Ammu yace "to yallabai,"

check ahmad yarubuta yabawa Ammu yace gashi kaje bank kaciro wannan kudin, ka gyarawa su izdihar gidansu, su Dan koma wani wajan arushe nasun ayi musu sabo, duk abinda babu kayimin bayani, banaso kwandalarka tayi kuka aciki,"😳
Ammu kasa godia yayi, kawai yariqe hannun ahmad yace" bansan Dame zanyi ma godia ba yallabai," ahmad yace
" karka damu, zan iya yiwa baby komai,"

dasu mama sukaji wannan labari kuka tasa, Abba kuwa har kano yazo ya yiwa ahmad godia, haqiqa sun tabbatar izdihar alkhairi ce agaresu, Babu yanda suka iya, gidan Ammu daya tashi suka koma dazama, dayake aikine da kudi, cikin wata biyu aka Gama komai, su mama suka tare agidansu, wannan abun yasa suka qara ganin qimar ahmad da kuma daukarsa da muhinmnci


** *** **

"Serious baban yan biyu?Gobe goben nan? Wayyo Allah, irin wannan surprise haka, to fadamin mai mijina yake so namasa?"
Tahir yace " duk abinda kikamin yayi,"
husna tace "ka fadawa ummi?" Tahir yace "nafada Mata yanzu,"

tace "Amma ahmad fa?" Tahir yace " ban fada masa ba so nake saide yaganni kawai"
Husna cikin Jin dadi da murna tace "wayyo my heart, to naji yanzu de fadamin abinda zan girka Maka gobe in tashi yanzu nafara shiri"
Tahir yace "aiba saikin wahalar da kanki ba, ke kadai ma kin isheni," husna cikin sauri takashe wayar, tahir yace "zamu gamu ne"


** *** **

Washe gari da yamma ahmad nashirin fita daga office, kansa aqasa yaji yayi Karo da mutum agabansa, yana dagowa yaga tahir, yace " mafarki nake ko gaske?" Tahir ya mintsineshi, aikuwa nan ahmad ya rungume shi, suka saki ihun murna, ahmad yace" tahir kamar kasan inasan ganinka yanzu, wallahi wata muhimmiyar magana nakeso muyi, kuma sai gashi Allah yakawo ka adaidai lokacin daya dace," tahir yace" ina jinka ya akai "
Ahmad bai boye wa tahir komai ba yafada masa, tahir tace" ahmad kayi kokari, gaskya soyaiyar dakake yiwa feenah babba ce, kawai daga ganin kama? Amma guy kana ganin abinda kake shirin aikatawa kuwa zai iyu? Saboda husna tasha fadamin yanda suke kaunar yarinyar, "

ahmad cikin jimami yace
" karka damu tahir zan gwada, "
tahir yace" Toshiknn, yaushe zakaje zarian?" Ahmad yace" yanzu, yanzu zanje tahir, inasan yarinyar sosai, "

tahir yace" toshkn idan ka dawo kayimin waya, sai nazo musha fira," ahmad yace" basai kafada ba tahir, har gidanka zanzo, "
tahir yace" serious ahmad"
, ahmad yace "serious tahir, ka fadawa madam tuwon dare tayi Dani"

Dahaka suka rabu ahmad yadau hanyar zaria

Karfe uku daidai a kofar gidansu izdihar tamasa, kamar kullum suka gaisa da Abba, Abba yace
" ahmad shigo mana," ahmad yace "Abba dare yayi, inasan komawa ne da wuri, dama Abba magana nakeso muyi dakai, Dan Allah Abba katemaka kabani izdihar, inaso koda yaushe inganta kusa Dani, inzame Mata uba da uwa kamar ku Abba," 😳
πŸ™†πŸ»

Abba ya numfasa yace
" ahmad babu abinda zaka nema awajena karasa, nide ta wajena babu damuwa, Amma kabani sati daya, zanyi magana da maman ta duk yanda mukai zakaji," ahmad yace" toshkn Abba na gode insha Allah zan dawo inji yaya kuka yanke," dahaka sukai sallama


** ** **

After 2days
" Ahmad da kaifa nake, ka tashi ka shirya muje asbitin nan, nagaji da wannan rashin haihuwar," ahmad yace" laila, saunawa zan fada miki haihuwa ta Allah ce idan yanufa zamu samu"

, laila tace "a a nikam nagaji kawai katashi muje,"
Babu yanda ahmad ya iya, dole ya shirya suka tafi, ba suje ko inaba sai asbitin tahir, tahir yana office shida wani doctor suna tattauna yanda zasu sake tsarin asbitin Gaba daya, su ahmad suka shigo, daya doctor din yafita yabasu waje,
Tahir yace" a a kaga amarya da ango," laila Ana yatsina aka amsa, tadau kafa daya ta dora Akan daya, Ahmad ne ya yiwa tahir bayanin komai, tahir yace
" ok Babu damuwa "

Cikin minti arba'in da biyar yagama bincike akansu, duk suna zaune, tahir yadawo yace" gaye kayi hakuri fa", ahmad yace " karka damu dahiru," 🀣

tahir yace " laila kiyiwa angonki magana yadena fadamin wannan sunan," laila tace "kaga tahir kafada mana abinda yakawo mu, ba wannan maganar dakake ta sunace takawo muba,"

Jikin tahir yayi sanyi dajin furucin ta
Ahmad yace "tahir ya ake ciki?"

Tahir yace "kuyi hakuri, musanman ke laila mijin ki bazai iya haihuwa ba, qwayoyin halittarsa basuda qarfin dazasu samarda wata halittar, kuma hakan yafaru ne a dalilin wata qwaya dayasha kwanaki





Mrs Usman ce πŸ–Š
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

48


Hannu yamiqa masa yace "Nagode sosai yallabai,"
principal ya dubeshi dakyau yace "haba ahmad ai Babu komai, daka aikoma za'a yi Mata komai basai kazo da kanka ba,"
ahmad yace "a a Babu komai, yanzu yaushe kake ganin Zata fara Zuwa school din?"

Yace " aiko gobe ma Zata iya Zuwa, Babu abinda zakuyi mata, duk abinda ake buqata makaranta Zata yi Mata," ahmad yace "ok ngd sosai,"

Please Login or Register in order to submit comment