Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyau, hips dina yafuto sosai akayan, Zahra tace "wow feenah kin hadu kin hadu kin gaji da haduwa, 🤣
keba mekyau bace feenah, kece shugabar kyawawan kawai,"

nace" Zahra kin isheni, Allah zan yi Gaba nabarki,"
Zahra tace" to naji jarababbiya,"

itama tashiga shiryawa



** *** **


Cikin sauri yafuto, daga daki, ya yiwa kakansa kiss tare matar kakansa ummi bara'ah, yace

" sabahul khair ya jaddy wa jaddaty, "

suka amsa masa cikin fara'ah, yahade cikin suit mai launin ash colour
, shima zama yayi,yafara break, bayan yagama ne marzuk yace "yakamata yaje wajan mutumin nan, Dan yaga motocin, yanaso idan zai koma Nigeria yatafi dasu, tunda manaja yace Ana neman su sosai," kada kai ahmad yayi, yana Gama cin abinci, yashiga motar sa qirar Benz s550 yafita da sauri

Adede wannan lokacin muma mun futo muna cikin bus, muna tafiya, Zuwa inda zamuje
Munzo daidai wata danja motar mu ta tsaya, muna jira abamu hannu


Haka shima Adede lokacin danjar ta tsaida shi

Zahra na kalla nace "kai Zahra zafi,"
ina kusa da window Dan haka kawai na Bude window, adaidai lokacin ahmad ya kalli agogon hannun sa ya furzar da iska, yace "wannan zasu batamin lokacin"

Kamar ance musu sujuya su kalli Juna, tana juyowa damanta tayi tozali dashi, shima yana juyowa hagunsa yaganta, gaban feenah yayi mugun faduwa, hakance ta kasance awajansa, da sauri ya nuna ta da yatsa yace "feenah"

Bazai iya manta wannan fuskar ba, shide burinsa da fatan sa kawai shine ta yafe masa, inde ta yafe masa, to shi yaji ya yarda saiya hakura da nemanta

Kasa dauke idona nayi akansa, yagirma, yaqara zama cikakken mutum, Zahra tanamin magana taga de hankali na baya kanta, ta juyo taga inda nake kallah, aikuwa tana ganin ahmad
Cikin daga murya tace "laaa ga AHMAD MUHD MARZUQ"
Aikuwa duk yan Nigeria dasuka sanshi, aka juyo yuuuuu Ana kallansa, Mata kuwa nan suka fara daga masa hannu, wasu suna "ahmad, ahmad, ahmad," wasu kuma suna "A'M marzuk," kowa da abinda yake fada, wata tace "pls zamuyi pictures,"
"ahmad hi," wasu suna "hello ahmad,"

Shikuwa idanunsa suna kanta, sauri yayi yafuto daga motar, yazo jikin motarsu yace "feenah,"

hade hannayansa yayi, yana fadin "feenah, feenah ki amsa mana"

Nikuwa zuwa yanzu ina kuka yaci karfina, cikin kuka nadago kaina, nadake duk da gabana yana faduwa nace "Ahmad"

Ahmad yace "feenah kece?"
"feenah,"

nace "nice ahmad, bakaso kaganni araye bako?"

Zahra tazama photo tana kallona, dama nasan shi 🤔

Sauran yanmata kuwa ganinsa a kusa da bus dinmu nan suka fara selfie, dashi

Hannu aka bada, nan bus dinmu tafara tafiya, ahmad yana bin motar da sauri, har yadawo yana bin motar da gudu yana Kiran
" feenah! Feenah!! Feenah!!! Ki tsaya kiji feenah"

Har motar tafara masa nisa, nikuwa kaina na sun kunyar ina kuka, Zahra kuwa saboda mamaki ma takasa min magana

Ahmad kuwa yana Kiran
" feenah fee... Feen... Feenah," nan numfashinsa yafara sama, nan da nan yafara tari, yariqe gefen da zuciyarsa take yafadi awajan







Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱


Writing by Amnah el yaqoub


Dedicated to my family


37

Kuka nake Sosai tamkar raina zai fita, Zahra ta janyoni jikinta tana Dan bubbugamin bayana alamar inyi shiru, ta sunkuyo daidai kunne na, tace "feenah kiyi hakuri kidena kuka, kar hankalin mutane yadawo kanki kuma yanzu"
, cikin kuka nace "Zahra wallahi ina sanshi
Inason ahmad Zahra, yaya zanyi da son danake masa acikin zuciyata?
Ban taba Jin inasan wani mutum ba kamar yanda nake sanshi Zahra"

Zahra tace "to naji kiyi shiru haka, zamuyi magana daga baya"
Awannan ranar haka na wuni sukuku
Babu abinda nake sai aikin tunani


** *** **


Dasauri wani driver yazo yatemaka masa, yakai shi wajan motarsa, Gaba daya baya cikin hayyacinsa
Mutumin yace "kwatanta min gidanku muje"
Amma ina ahmad yakasa magana kawai de yarike kirjinsa da hannun sa

Mutumin yarasa ya zaiyi, Dan haka cikin sauri yakaishi asbiti, kafin suje ahmad baya motsi
Suna Zuwa likitoci suka karbeshi, suka shiga bashi temakon gaggawa

Wani tunani mutumin yayi, Dan haka ya duba wayar ahmad dake hannunsa
Number yagani ansa daddy
Bai lura da number misra ce kota wata qasa ba kawai yakira

Daddy nadagawa yace
" hello my son"
Mutumin cikin harshen larabci ya yiwa daddy bayanin komai, Allah ya rufa asiri daddyn yanajin yaran 🤣

Godia yayi masa, yakira babansa, marzuk naganin kira yace "Muhd bakada kara, 🤣to inde ahmad ne cikin month din nan zai dawo "

Daddy yace "abbey bahaka bane,"
nan yamai bayanin komai ciki harda sunan asbitin
Gaba daya marzuk Yama rasa ina tunanin sa yake, bara'ah tana tambayarsa lafiya kawai shide yace" Mata futo mutafi"
Driver ne yajasu sai asbiti


** *** **


Har muka koma hotel din da aka saukemu Zahra bata cemin komai ba, kawai ta barni ne in samu kwanciyar hankali, hakika ta tabbatar ko menene yashiga tsakanina da wannan mutumin babban al'amari ne
Tunda nide nace banasan yan siyasa

Haka dazamu ci abinci ma, hakuri tayi tabani Akan naci, dakyar de nadaure naci kadan, koma menene akwai lokacin dazata tambayeni


** *** **


Gumi ne yake sake futowa bayan wanda yake gogewa duk kuwa da sanyin esin dake tashi a office din doctor din, bayan yagama Jin bayanin da likita yamasa, marzuk yayi masa godia yafita
Dakin da ahmad yake ciki nan ya koma ya tarar dashi, yana bacci, ga qarin ruwa anyi masa, bara'ah tana zaune agefensa, kujera yasamu ya zauna, yariqe hannun ahmad tare da rafka uban tagumi

Bayan wani lokaci ahmad yafarfado, a hankali yabude idonsa
Yakallesu, marzuk yayi masa sannu, bara'ah tafita ta kira doctor
Yazo yadubashi yace zasu iya tafiya, Amma Dan Allah a dinga kula dashi sosai

Bayan sun dawo gida, dakinsa suka kaishi, aka hada masa shayi, yasha tare da magani, bara'ah ta rufa masa bargo tafita
Shima marzuk din futowa yayi bayan yaga ahmad din yafara bacci

Falo yadawo ya zauna, bara'ah ta dubeshi tace "me yake damun ahmad ne? "
Anan marzuk yayi Mata bayanin komai, tace
" subhanallah, yanzu yaya za'a yi?"
Marzuk yace" ni kaina bansaniba "

Kiran daddy ne yashigo wayar sa, yadauka bayan sun gaisa ne yake tambayar jikin ahmad din, marzuk yace" jiki da sauqi, idan yatashi zan kiraka "
Daddy yace" to abbey "
Momy ta dubeshi tace
" me yake damun waladeey na," tafadi haka cikin damuwa
Daddy yace" nima bai fada min ba, Amma yace idan ahmad din yatashi zai kirani "
Momy tace" to Allah yasa de lafiya, "daddy yace
" amin "



** *** **


Bayan kwana biyu, su feenah sun Gama komai, sunyi pictures dayawa awajaje daban daban
Haka suka koma Sudan cike da kewar Garin masar domin kuwa yayi musu dadi sosai


** *** **


Bayan sungama cin abinci, ahmad yasha maganin sa, marzuk yakira daddy, bayan sungama gaisawa ne, yahadasu dasu Momy ma kowa ya yiwa ahmad sannu
, tashi ahmad yayi zai koma daki, marzuk yadakatar dashi, yadawo ya zauna, marzuk ya cewa daddy, "muhd har yanzu ban fadama abinda yake damun ahmad ba ko, to kayi hakuri nabari ne yadan warware tukun na,"
Daddy yace "Babu komai abbey"

Marzuk yasa wayar a hands free, yanda ahmad da bara'ah duk zasu ji, nan ya yiwa daddy bayanin komai
Daddy yace "subhanallah
Bani ahmad din," marzuk ya kalli ahmad daya sunkuyar da kansa qasa, kamar munafuki yace "ai yanajin ka muhd"
Daddy yace" ahmad," ahmad yace" na'am daddy "
" Yanzu ahmad dama har yanzu kana wannan tunane tunanen Naka na banza da wofi?
Mu muna nan, muna tunanin kadena, ka warware, ashe bahaka bane?
Yanzu my son bakasan kwanciyar hankalin ka da namu?
Shikkenan kai bazaka dauki qaddara ba?
Yanzu badan anyi gaggawar kaika asbitin ba, kasan mezai faru? "
Ahmad yayi shiru
Daddy yace" ba tambayarka nake ba? "
Ahmad yace" a a daddy "

Daddy yace" toda tuni ciwon zuciya yakamaka," ahmad Dasauri yakalli wayar, yace" zuciya kuma daddy "
Daddy yace" qwarai kuwa, likita yace idan baka dena wannan tunanin nakaba, tabbas kana gab da kamuwa da ciwon zuciya
My son idan kakamu da ciwon zuciya bazan taba yafewa wannan yarinyar ba, domin kuwa dalilin wannan rashin sukunin Naka mutane dayawa, sun shiga damuwa

Abinda nakeso dakai shine, ahmad ba rarrashinka nake ba, kaci Gaba da tunani kaji,🤣 zamu fidda hannun mu daga dukkanin al'amarinka
Sai magana ta biyu, badai Akan mace ne kake wannan haukan shirman ba? Har kanaso ka kamu da ciwon zuciya, to bari kaji abinda zan fadama, kahada yanaka yanaka, ka dawo gida cikin satin nan, kuma duk yarinyar da naga tayimin zan aura ma ita, kaje can ka qarata, "ahmad yace
" daddy kayi hakuri, insha Allah bazan sake ba, " daddy yace" nagama magana ahmad, "

Marzuk ya karbi wayar yace" muhd hakan yayi, zai taho insha Allah," nan sukai sallama


Momy ta dubi daddy tace
" anya kuwa alhaji wannan hukuncin baiyi tsauri ba? "
Daddy yace" dole sai mun rage soyaiyar damuke nuna masa sannan ne zamu dawo dashi kan hanya hajiya
Duk mace macece, abinda wannan zatama, wannan ma zatama, illa iyaka wata tafi wata, hanyoyin da waccan tayi amfani dasu harya sota, itama wannan Zata iya,
Hajiya idan ya rabu da wadda yake so bawai shine bazai iya San wataba, Dan haka nagama magana inde nasamu yarinya aure zan masa, yin hakan shine zai taimaka masa wajan manta waccan "
Momy ta numfasa tace

" hakane alhaji, Allah yasa hakanne yafi alkhairi "
Daddy yace" amin "


** *** **


After one day, ina kwance adakina ni kadai, Zahra tashigo, na kalleta da murmushi nace" Zahra sannu da Zuwa,"

Tace "yauwa," tana tsaye ta jingina da bangon Dakin, ta kalleni kallo na tsanaki tace

" feenah inaso kiban labarin ki"

Na kalleta banga alamar wasa atattare da itaba, nace "zan fada miki Zahra, Amma idan kinyi alkawari zaki rikemin sirrina," Zahra tadawo gefena ta zauna, tace "inde wannan ne karki damu nafeesa, ki daukeni tamkar husna"

Zamana na gyara, na fuskanceta dakyau, nace "Zahra, mahaifina mai qaramin karfine ba kamar yanda wasu daga cikin mutane sukemin kallan yar me kudi ba,
Arayuwa tunda nake, ban taba kula kowanne saurayi da sunan soyaiya ba, sai mutum daya auwal, shima kuma halin danake nuna masa na ko in kula yasa ya rabu Dani, tunda ya gane bana sansa

Hawaye nafara, bandamu dana goge suba, naci Gaba da cewa zuwana kano yin karatu shine mafarin komai, nahadu da saudat.......

Anan nagama bata labarin komai, ina kuka tana kuka, rungmeni tayi ajikinta, tace "please feenah yi hakuri, kiyi shiru"
Dakyar nayi shiru, na dubeta nace" Zahra, tayaya kike tunanin zan sake saurarar ahmad?
Mutumin dana yarda dashi, na bashi dukkanin Amana ta, nadauki son duniya nadora masa, Zahra kuka nake ina tambayarsa yayi hakuri, idan wani laifin nayi masa yayafemin
Amma kamar qara zigashi nake"

Zahra ta share hawayen ta, tace "feenah abin kamar almara, yanzu feenah ke kin haihu, harma kinada 'ya mace"
Kallanta nayi nace
" Zahra, baby dakikaji ina cewa qanwata, ba qanwata bace 'yatace, nida ahmad Zahra," nakarashe maganar ina kuka, Zahra tace "feenah, Dan Allah ina neman alfarma daya awajanki, kiyimin wannan alfarmar koda kuwa itace karshan alfarmar dazaki min azamana dake feenah"

Nadubeta nace "inajin ki Zahra, wacce irin alfarma kikeso?"
Tace "feenah Dan Allah ki yafewa Ahmad"
Dasauri na kalleta, ta gyadamin kai, tace
'' kiyafemasa feenah na rokeki "

Nace" meyasa? Meyasa zan yafe masa Zahra?"

Tace" alabarin dakika bani kince lokacin da abin yafaru, dakansa yadaukeki yakaiki asbiti, feenah kiyi tunani idan yayi miki haka da niyya bazai kaiki asbiti ba

Sannan kin barshi a asbiti baki bashi dama yayi miki magana koda guda dayaba

Sannan yana zarya agidan kakarki, kinqi bashi dama ku hadu, feenah kiyi tunani idan baya sanki bazai dinga bibiyarki ba
Idan yaudararki yake yi, tunda yasamu abinda yake so bazai qara kulaki ba

Sannan yakiraki awaya, lokacin dazaki dawo kano, nanma baki bari kunyi maganaba,sannan kun hadu rannan still kin sake fada masa wata baqar magana

kinada numbers dinsu shida sister sa, baki nemesu ba, tayaya kike tunanin zai miki bayani feenah?

Tabbas abinda ya miki bai kyautaba, kowacce mace kamila wadda ta killace kanta, Tsawon shekaru, Amma rana daya wani ya keta Mata haddinta, tabbas abin da ciwo feenah, na tausaya miki,
Muna aikatawa Allah laifi, dayawa kuma yayafe mana feenah

Kikasan ce mai yafiya, Allah yana tare dake feenah, "

Kallanta kawai nake, hakika duk wanda yasamu qawa tagari, ya godewa Allah,
Numfashi nasauke nace
" hakane Zahra, nikam da bacin rai yahana ni gane komai, nayafe masa, nayafe masa Zahra "

Rungmeni tayi, muna kuka, daganan kuma tadinga yimin godia, nace "Babu komai Zahra wallahi har cikin raina nayafe masa"

Zahra tace "feenah kinsan me?"

Nace "a a, tace wallahi kunyi bala'in dacewa da ahmad, kawai ki bashi dama, yadawo, kuyi aurenku , ku rike yarku shikkenan, kinga kema kin huta da darurar, wani mijin dazaki aura, wajan yimasa bayani,"
nace "hakane Zahra

Amma kina ganin ahmad zai soni ne yanzu?"

Hararata tayi tace "shidin me, ba dolen saba," nace "a a Zahra ba dole,"
tace "serious feenah zai soki fiye da da insha Allah,"
Nace " to shikkenan zan kira shi tawaya insha Allah"

Zahra tace "kinada number sa ta Egypt ne?" Nace "gaskya banda,"

tace "ga shawara,"

nace " mecece shawarar ki?"
Tace "kawai ki nemeshi ta Facebook dinsa,"
nace "ko?"
Tace "emana"
Nace "to shikkenan insha Allah zan nemeshi, duk yanda mukai dashi zakiji"

Rungumeni tayi tace da karfi "na gode sister feenah"








Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

39


Kan gadonsa yafada gamida rufe idonsa, takardar hannunsa ya wullar, Yama rasa wanne irin tunani zaiyi
Wayarsa ya janyo yakira tahir, bugu daya ya amsa
Cikin sanyin muryarsa yace "tahir please zo"
Tahir yace "ahmad Allah yasa de lafiya"
Ahmad yace" ina kuwa lafiya please yi sauri "
Yakashe wayarsa
Tahir ya dubi husna yace

" ina Zuwa zanje wajan ahmad, "
mama da mima sukace daddy zamu, yace" a a kuje wajan ummi,"

mama cikin muryar kuka tace" to ai ummin ta koromu, "🤣

mima tace" toba kece kika zubar Mata kayanta ba,"
mama tace" bawani nan ai kece"
Tahir ya kallesu ya girgiza kai yafita
Yasan renin wayon dasuka saba yi ne sukayi wa ummi shiyasa ta korosu, 😃sai daya tayi laifi saboda tasan ba'a ganesu saitace dayar ce, itama dayar tace ba ita bace dayar ce, Dan dolenka ka hakura

Yana Zuwa part din ahmad ya nufa, yaganshi a kwance kamar mai bacci, waje yasamu ya zauna yace "gaye ya akayi ne?"
Ahmad yatashi idanunsa sun kada yace "tahir auren dole za'a min," 🤣

yanda yayi maganar ne yabawa tahir daria, cikin daria yace "auren dole kuma, kamar ya? Kana namiji? Dama Ana haka?"
Ahmad ya numfasa nan yabawa tahir labarin abinda yafaru tsakaninsa da daddy
Tahir yace" to menene abin damuwa ahmad
Maganar de itace bakasan ta, tofa itama bata sanka, 🤣 a hankali zaku saba ahmad"

Ahmad yace " tahir bazaka ganeba, feenah"

Tahir ya dafe kansa da hannunsa yace "feenah, feenah, feenah, koda yaushe maganarka feenah, na tabbatar yanda kake Santa ita bata yima wannan soyaiyar"

Ahmad yace" a a tahir nasan tana sona kawai laifin dana matane yasa ta tsaneni kuma nima nayi DANA SANI"
daddy ma inajinsa yana cewa wai bazai yafewa wannan yarinyar ba, baisan daya ji abinda namata shine ma, zai nemi yafiyar taba, tunda shi sanannan mutum ne, abinda yafaru tsakanina da feenah yana iya taba mulkinsa "
Tahir yace "hakane, na feenah bada kanka asare" 🤣

Harara ahmad ya aika masa
, tahir yace "yanzu menene abin yi,?" Ahmad yace "ni kaina bansaniba shiyasa na kiraka," tahir yace" a ina yarinyar take?" Ahmad yace" kaga paper da daddy ya rubutamin address dinta can na wullar ta, "kallan p.o.p din Dakin ahmad yayi, afili yace" Naso ace feenah nafara aura, bantaba yiwa iyayena gardamaba dole yanzu ma inyi musu biyayya tahir koda aikata hakan yana nufin fitar numfashi na ne karshe"

Tahir ya dafashi yace
" kayi hakuri ahmad, idan feenah matarkace, duk daren dadewa zaku kasance ma'aurata," ahmad yace" hakane, shiyasa nake sanka "🤣


Harararsa tahir yayi, yace
" saboda nayi maganar feenah ba, oh duniya feenah! feenah!! feenah!!! , nikuwa zanso haduwata da feenah "
Ahmad yace" me kakeci nabaka na zuba, kamar yaune ai"
Tahir yace "yanzu me kake ganin za'a shirya?"

Ahmad yace "shiri kuma tahir, ai Babu wannan maganar, Babu wanda zan sanarwa zanyi aure, biyayya de zanyi inyi auren, Amma maganar sanarwa Babu ita"

Tahir yace "ahmad wanne irin aure ne wannan?"
Ahmad yace " tahir mubar maganar nan Dan Allah"

Tahir yace "ok, to yanzu yaushe zamuje wajan yarinyar sai muji wanne tsare tsare ne yakamata ayi," ahmad yace" Babu inda zani tahir, aide so suke su ganni da auren ko, to ayi auren, Amma maganar gaskya banajin zan iya San wata bayan feenah "
Tahir yace" a a kadena fadar haka "


** *** **


"Mom nafada miki Babu abinda zanyi, haka kawai dad baiyi shawara daniba zai tashi yabadani saikace wata mage"
Mom ta dafa kafadar ta tace "
LAILA
meyasa wani lokaci bakya tunani ne, yanzu ashekarunki baici ace kinada yara ba?
Nide abinda nakeso dake shine kiyiwa mahaifinki biyayya, inba haka ba,tun baya fishi dake to zai fara yanzu"
Laila tace "mom nikam banasan wannan auren, nafisan rayuwa ta haka, mom bansan fa wanda zan aura ba, saboda me dad zaimin haka?"
Dafa kafadarta hajiya salaha tayi, tace "laila zaki auri yaro, yaron ma me tashe, me facaka da nera, kuma yaro danye domin kuwa kin girmeshi" , laila tace "mom kamarya? Me kike nufi?"
"Dan gidan alhaji muhd marzuk zaki aura laila, ko banza zaki zauna cikin daula kiyi yanda kikeso da kudi laila, ki hau motar da kikeso"


** *** **

"Momy gaskya ankon nan yayi kyau, ina farin cikin auren nan na yaya, Amma zan so ace da qawata feenah akayi," Momy tace "saudat muma munso hakan Kodan farin cikin my son
Amma toya za'ai, haka Allah ya qaddara,"
saudat tace "hakane, Allah yabasu zaman lafiya," mamy hakima datake shigowa Dakin tace "amin" , tace "saudat abinci yazama ready, yakamata kije ki zubawa farouq din ko, kada ace munyi baqo mun barshi da yunwa"
Saudat tace "ai mamy Dakin barshi ma nayi masa da kaina, Dan bayasan abincin masu aiki," mamy hakima ta kalli Momy, suka hada ido, mamy hakima tace
" um lalle zamani sannu saudat"
Shiri suke sosai yan wannan gidan, kowa yana walwala saide uban gayyar baya maraba da wannan aure


** *** **


Kan gadonta tafada, tasaki ihun murna tace, "cikin sauri haka?
Abinda na Dade ina nema ne Yau yazo har gida yasameni, ta shege da wata uwar daria
Tace ahmad zanyi yanda nakeso dakai, tunda kazama mallaki na, dana Gama da mangoro zan yarda qwallansa in huta da quda


** *** **


Rana bata qarya

Ayau ne dubban mutane suka shaida daurin auren ahmad muhd marzuk, da laila bukar
Wanda akai Akan sadaki naira dubu dari, lakadan ba ajalan ba
Ana daura auren ahmad ya sulale Yabar wajan, tahir ne mai kula da komai
Haka kuma har wannan lokacin shide bai nemi laila ba, bayama ta kanta, dakinsa yashiga ya kulle yaita kuka shi dakai (toya zakai Malam amadi)


** *** **


"Mom ni narasa gane wannan wanne irin aure ne, angonfa har yanzu bai zoba, sannan akwai dinner da qawayena suka shirya shima kuma naga alamar bazai zoba, tunda nima bansamu matsayin dayazo yaganni ba,"

Hajia salaha tace "laila 'yata yi hakuri bari nakira step momynsa"
Mamy hakima ta kira tayimata bayanin komai, nan mamy hakima tace
" karta damu aci Gaba da hada komai insha Allah zaizo"

Nanfa su laila aka fara shiri baji bagani
Tun magrib aka fara ta ruwa awajan dinner, ango de bayan Mamy hakima tayi masa fada, saida tahir yadage sannan yayarda suka tafi

Amarya ta Dade awajan itada qawayanta, tun daga nesa data hangoshi ta shagala akallansa, yana Nan yanda yake, sai kyau da haske da kuma hutu dasuka sake baiyana atare dashi, daga kallo daya bai sake yi Mata na biyu ba, yana qarasowa tazo ta rike hannun sa sai kwarkwasa take, aikuwa nan masu pictures suka ce in bakayi ban waje🤣

Tahir ma yafara yi musu pictures, laila sai wani kanannadewa take ajikinsa, shide tahir yanata musu pic, azahiri shide yarinyar bata wani kwanta masaba, Amma Babu yanda zasuyi da hukuncin Allah
Ahmad yajuyo yace Mata "kewai miye haka eye?"
Daidai lokacin daya juyo kuwa tahir yayi musu pictures sai ka dauka wasu zunzurutun masoya ne 🤣

Kusa da ahmad yaje daidai kunnansa yace, "abokina bani aron wayarka mana"

Ahmad ba tare da tunanin komai ba yabashi, yace "haba ahmad kadan saki ranka mana," yajuya yakoma wajan zamansa

Yana karbar wayar ahmad whatsApp dinsa yahau yayi posting pictures din ahmad da laila, a status, aikuwa nan da nan mutane suke masa fatan alkhairi, yanmata kuma suke DANA SANI da cizon hakori, daga baya kuma ya koma Facebook nanma yayi posting cewa nayi aure ina buqatar addu'ar ku fans
Sannan yadora pictures din guda biyu, aransa yace nasan ahmad zaiyi fishi Dani Amma zai dawo yahuce, yaya za'ai ace mutum yayi aure Amma kace Babu wanda zai sani

Dahaka aka Gama dinner din
Washe gari ne ranar kaiwa amarya, alhaji bukar ya yiwa laila fada sosai Akan tabi mijin ta, saide ita aranta bahaka bane,
Hajia salaha kuwa, ta gargadeta Akan kada ta kuskura tayi aikin wahala, laila tace "haba mom kamar baki sanni ba, nifa mom banajin auren nan zai wuce 3 months, gaskya dana samu abinda nakeso,kuma nagama samun kudi, to zan kashe auren ne indawo gida, daga baya dad saiya yafemin"
Hajia salaha tace "lalle sai Yau na tabbatar bakida wayo laila
Daki Debi kudi kidawo gida, bagara ki zauna kisamu ciki ba, daga bisani kibar masa gidan,saimusa agama dashi , kinga yayinda aka raba gado kinada tarin dukiya mai yawa"
Laila tace "wow mom banyi wannan tunanin ba"
Hajia salaha tace "toki kula de yata"
Dahaka aka dauki laila aka kaita gidansu ahmad cikin part dinsa dayasha gyara


** *** **


After one week, tunda akai auren ahmad bai taba takawa wajan ta ba, dasafiya tayi yake fita, bazai dawoba sai can dare yayi sosai,🤔 laila abin duniya duk ya da meta, daga baya ne ta kira mom dinta, nan tabata shawara


** *** **


Yau da safe nagama karatu na, ina kwance ina chting, kamar wasa nace bari de Yau in duba inga ko ahmad yahau Facebook dinsa

Hawana keda wuya, naje nayi searching sunansa, kai tsaye wajan photos na shiga, abinda nagani ne yayi mugun dagamin hankali

Afili na furta, "ahmad! Ahmad!!
Aure ahmad, sai kuka," nan danan gabana yafara faduwa, nace "na shiga uku
, ahmad yayi aure, ahmad da gaske dama aure zakayi ka kyaleni?"
Ihun kuka nasa nayi wulli da wayar, wannan ihun ne yajanyo hankalin Zahra da dakinta yake kusa da nawa
da gudu ta shigo Dakin tace "feenah lafiya?"
Ban iya bata amsa ba, sai kuka nake
Ta cacimeni tace "menene wai feenah kiyimin bayani mana"
Wayata na nuna Mata cikin sheshshekar kuka, nama kasa magana nace Mata "Ah.. Ahm... Ahmad ne"

Zahra da sauri taduba wayar, nan take tafara salati

Cikin kuka nace "Zahra kingani ko? , yanzu kin yarda yaudarata yake ko Zahra"
Zahra ita kanta hawaye take, nace "Zahra...."
Kafin nayi magana naji qirjina ya rike, durqusawa nayi na dafe qirjina da hannu na
Dif numfashi na ya dauke





Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

38


Haka na wuni ranar cikin sa'adah

After 2 days
Waya nake ina cikin farin ciki, nida husna, ni kaina

Please Login or Register in order to submit comment