Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Kawar da wannan tunanin yayi sbd agaskiya baida burin daya wuce suyi aure ba tare da komai ya gifta ta tsakanin suba, yaqi jinin zina haka yana Allah wadai da masu aikatata

Kaka Ana zaune akujera yar tsugunno sai ganinsu tayi, kallan mamaki take masa, saida ya tsugunna har qasa ya gaisheta sannan tace" Dan nan ban wayekaba,"
yayi murmushi baice komai ba, kasancewarsa bamai yawan maganaba
Feenah ce tace" kaka yayan saudat nefa, "

Sannan kaka a kace" au to, yanzu naji batu,yasu sauden yaro? "

Oh ya Allah feenah tafada da karfi tare da dafe kanta 🤦🏻‍♀


" to menene zaki fara iyayin naki, menene laifi dannace saude yaro,".

ahmad yayi murmushi yace" Babu komai kaka,"
" Yauwa kokaifa, yaya sunanka ne?"
" Sunana Ahmad Muhd marzuq kaka, "

" Oh Allah sarki amadu, (kawai sai kaka tafara kuka) amadu anacan karkashin qasa
Yaro ai sunan majina kaci, shima haka yake akwai shi da fara'ah
Allah yaji kanka amadu tafada tana goge hawaye, "
ahmad yace" amin kaka Allah yaji kansa, "

Dago kai tayi ta kalli feenah tace" nafi ko shine wanda kika cemin kwanaki yanada kyau?"🤣 🤣

" Wayyo kaka bashi bane "
Tabe baki kaka tayi," ke kika sani "

Tashi yayi zai fita Yabar wa kaka kudi masu yawa, feenah tabi bayansa suka tafi
Ajikin mota sukai ta firarsu daga karshe yace yagaji dole sai ciki suka koma, Gaba daya yagama kashe Mata jiki da sanyaiyar muryarsa

" Nafeesa tah"

yakira sunan ta, kafin ta amsa yaci Gaba da cewa "nafeesa ina kaunar ki, inaso Allah ya mallakamin ke ki dinga haifa min yara masu matukar kama dake,"

"Nafeesa," yasake Kiran sunana, kafin in amsa yaci Gaba da fadin" a koda yaushe idan na daga kai na kalli sama sai inganta cike take da taurari masu matukar haske, Amma haske mafi mafi haskaka kyawun fuska da yaye duhun zuciyata yana tare dake Nafeesa, ina sonki, ki kulamin da kanki pls"
ya qarasa a hankali tare da riqo hannu na, wani yarrr mukaji lokaci daya, dagani har shi, saboda Abu ne wanda bamu taba tsintar kanmu aciki ba sai Yau, Amma abinda yabani mamaki shine yanda nakasa yimasa musu, haka shima yakasa cikani,
Saida yagama jaddada min kaunar dayake min sannan yasakeni, ajiyar zuciya nasauke, yajuyo ya kalleni," na takura miki ko?" Nace masa" Dame kenan? "
Yace" gashinan narike miki hannun ki", kawai murmushi nayi, yacemin zai tafi, tare da miqomin leda nace a a yabarshi,

Yace "ashe kuwa bazaki fice daga motor ba, karbi mana baby bayan dazu aka Gama fasamin qwan, ashe nima ina da kyau" 🤣

Yafada yana murmushi

"Allah yaya zan ma kuka,"

to naji karbi ki shiga ciki, Dan dole na karba, nace ya gaida su momy da mami

Bina yayi da kallo saida na shiga gida sannan yatafi

Ina shiga gida kaka ta nunamin kudin daya bata dubu a shirin, haka tayi ta shimai albarka, muka duba kayan daya kawo min, nabaje mana mukasha
Saide kuma dazaran natuna yanayin da muka kasance tare dashi dazu, Gaba daya sai jikina yayi sanyi, inji dama kada lokacin ya wuce 🙈




** *** **


"Sofy Yau nayi babban kamu, gaskiya bazan iya hakura dashiba saina dandani zumarsa, yaron akwai kudi da gayu, bakiga yanda yake wasa da nera ba ingaya miki,"

"Kai qawata bani nasha" , anan tabata labarin ahmad," ke yanzu haka nasa amin bincike akansa da komai da komai nasa, sati daya yayi yawa na dandaneshi na wullar,"
dariya Sofy ta saki" Allah qawata,"

" wallahi nake fada miki, "

" Gaskiya ne qawata dole ajinjina miki,"


Tace" waya fada miki LAILA CHILLING WASA CE"



Tofa


Mrs usman ce🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱



Writing by Amnah el yaqoub



Dedicated to my family



17




Laila bukar kenan, 'yace guda daya tilo awajan iyayenta, mahaifinta mutumin kirki ne haka yanada kudi sosai, wannan ne dalilin yasa Laila take wadaqa da kudi San ranta, mahaifiyar ta hajiya salaha mace ce mai izza Sam taqi jinin talaka,
Ita take daurewa yarta gindi tayi abinda ranta yake so
Acewarta me amfanin kudin ta inde Laila bazataji dadi ba, tana aikata komai Dan Jin dadin yarta, yayinda alhaji bukar baisan wainar da'ake toyawaba,
Saide in sunce suna buqatar kudi kawai zaice su dauka ne
Laila tana kyau dai dai ita, babbar mace ce, meji da aji, da kuma gayu, qawarta daya sofy
Basa komai sai shashanci Yau sune gun wannan alhaji, gobe sune gun wancan
Duk wannan kudi na mahaifinta hakan bai hana Laila zurma zuciyarta Akan masu kudi ba
Itade kawai abata
Idan Laila ta qyalla ido akanka tofa saita samu abinda take so take barinka
Babbar yar iskace ta bugawa a jarida



** *** **




After one week
Zaune muke aqasan bishiya, saudat ta kalli agogon hannunta, tace "wannan bawan Allah fa ya shanyamu dayawa,"

hararar wasa nayi Mata "nifa banasan raini, bazaki yiwa majina ba wallahi,"

zaro ido tayi, "lalle feenah yaushe yaya yakoya miki rashin kunya ina zaune a gefe?"
Nace" bawani rashin kunya ai inda mutunci nima anty yakamata kina cemin "
Baki ta riqe," lalle soyaiya mai raba sis da sis, ni banda yace kar direba yazo dauka na da tuni nayi tafiya ta, inyaso ku qone ma bayan soyewa," budar bakina kuwa nace "wallahi kuwa "

Tace "kaji masoya,
Wannan idan kunyi auren ma Babu mai Zuwa gidanku,"
nace" toda waye zaije yaga abinda yafi karfin idonsa, "

Zata sake magana, waya ta tayi ringing
My ahmad yafuto baro baro Akan 'shaasha' (screen) cike da shagwaba na daga, Itade saudat tazama yar kallo
Nace" gaskiya my man, nayi fishi, tun dazu muna ta jiran ka bayan da tuni ina gida, Amma shine ka shanyamu ko? "

Yace "a kowanne lokaci, kowanne sa'ah kowanne minti kaunar ki sake qaruwa take acikin raina my feenah, soyaiyar ki kamar assignment ne Allah yabani, kinga kuwa bazan denaba, Tuba nake sarauniyar kyawawa,"

nace "anyi Maka, irin wannan kalaman ba dole mutum yayi hakuri ba"

Bansan me yace mataba tace "ok gamu nan Zuwa,"
Najuyo da nufin in cewa saudat tazo mu tafi sai naga tayi sakare tana kallo na, tace "um duniya Gaba dayanku naga alama kunyi nisa,"
nace Mata "yes kuma bazamuji Kiran kiba"

Muna fita daga gate muka ga motarsa a gefe yayi parking, tun daga nesa yazuba Mata shanyaiyun idonsa, tana sanye da atamfa ja mai ratsin baki, da hijabinta har qasa,
Ni kaina kasa dauke idona nayi akansa, ahmad karshene wajan tsafta da gayu da kuma kyau, yana sanye da wando jeans da Riga yellow da kuma jacket kalar jeans din, yana jingine Ajikin motarsa Mercedes brabus, gaisawa mukai dashi duk ya zubamin ido, nide nakasa hada ido dashi, saudat tayi zuruf tashige baya, gamida rufowa, yaqi dauke idonsa akaina, Gaba daya sai naji na takura, ashe saudat idonta yana kanmu ta cikin motar dayake glass din tinte ne ita tana ganinmu, mune de Bama ganinta, "sannu sarkin kunya duk kin wani boyemin beautiful face dinki, tun daga nesa nake ganin wani haske agate din, ashe kece sinadarin dake haskaka wannan hasken"
, dago daradaran idanuna nayi nace "ni din?"

"Ke kuwa, aike kamar hasken wata kike mai hasken dake haskaka zuciyata, haka kuma kalaman ki tamkar suger suke, ma'abocin zaqi, tabbas kinyi kama da...... Dakatar dashi nayi nace" my ahmad saudat fa tana jiranmu "
nafada cike da shagwaba,
Shafa kansa yayi "to ai kece my feenah" shima ya kwaikwayi muryata yafada
Amma kinsan me, maimaita abinda kika fada saina barmu mu shiga mu tafi, wannan sunan da kika fada nakeso ki maimaita,"
nace" nide Dan Allah mu tafi, "yace" saifa kin fadamin, "
da naga da gske yake yanaso yabata mana lokaci saina kalli idonsa nace" my ahmad, shikkenan? "Kafin yabani amsa nasa hannu zan bude gaban motor in shiga, dai dai lokacin shima yasa hannun sa, haduwar hannayenmu waje daya shine ya haifar mana da wani yanayi, tuni narigashi janye hannu na, cikin sauri yabudemin na shiga, kafin ya zagayo yashiga mutafi, saudat tace" wallahi saina Rama kun wani shanyani sai soyaiya kuke, ai ina kallanku, "najuyo na kalleta ina murmushi kafin nabata amsa, yashigo motor, muka dau hanyar hotoro
Babu wanda yake magana acikin mu, kawai wa'azi muke saurara, har mukazo gidan, saudat tayi sauri tabude tashige ciki, nima zan Bude in fita naji kofar a rufe, da niyya yarufe kenan, najuyo na kalleshi, yace "yanzu Babu sallama kawai saiki tafi?" Nide nayi shiru ina wasa da yatsun hannu na,
"FEENAH"

yakirani acan kasan maqoshin sa
Kasa amsawa nayi saboda Gaba daya kwarjininsa ya cikani, "nafeesa bazan gaji da fada miki ina sanki ba, pls nafeesa ki daure kici Gaba da kaunata pls," yana magana kamar wani qaramin yaro,
"Bansan adadin kaunar danake miki ba, Dan Allah kema ki soni ni kadai kinji,
Nafeesa wani lkcin idanuna sukanyi kishi da zuciyata, saboda a koda yaushe kece mafi kusanci da zuciyar tawa, su kuma idanuna kin kasance maiyin nesa dasu,
Feenaaaah, yakirani gamida Jan sunan nawa, har saida hakan yayi tasiri ga jikina, ya haifar min da kasala, banyi auneba naji ya ruko min hannayena duka biyun
Jin haduwar hannayenmu shiya haddasa mana Jin wani yanayi, shi kansa yaji abin har ransa, yanaso koda yaushe yaji hannun ta anashi, saboda yanayin dayake tsintar kansa aciki yana masa dadi
Babu yanda ya iya dole yasaki hannun nata gudun afkuwar "mishkila" (matsala)



** *** **

"Saude kina jinako, ki dinga yiwa nafi fada, sannan ban isa inyi magana ba, yarinya saita fara zinburamin baki, na matsu ku Gama karatun nan, kotayi aure muhuta," saudat tayi dariya, "to kaka ki daina damun kanki zanyi Mata magana,"
"Yauwa Saude nikuwa da gske yayanki yake Santa?"

"Emana kaka sosai yana Santa, ai shine ma zai aure ta insha Allah"

"To ai shikkenan, zanyi magana da babanta, ni gara ayi auren ma nahuta,"
Saudat ganin karfin halin kaka take, kebada 'yaba kece mecewa zaki aurarta ki huta 😃



** *** **


"Yaya zan shiga gida kasan halin kaka, yanzu saita fara sababi danma saudat tana ciki, banaso ta futo saboda kaima yanzu Zata hada dakai,"

"a a my feenah ni fa angon tane bazatamin ba"
Dariya nayi nace" Toshiknn wataran zamu jiku ai inde ka kace "
" To yanzu ki fadamin kalma daya dazan tafi ina tunanin ta "

Nace" I love you my ahmad, "
Shima Bude idonsa yayi dasuka kankace," I luv u too "yace can kasan maqoshin sa
Badan munyi kusanci ba, Babu abinda zaisa nima nakasa jinsa
" gawannan ki shiga dashi "

" na menene?" Na tambayeshi

" Idan kin shiga kya gani," nace" Allah yaya um um kabarshi, "
Hade rai yayi yadawo ahmad yayan saudat

" Bansan musu karbi "

Nakarba nace" toshkn nagode, "
ina turo bakina," feenah"

yakirani, najuyo "pls yimin murmushi Dan Allah"
Dole murmushin namasa sannan ya budemin nafita ina masa bye bye








Mrs usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family


18


Gida na shiga na tadda kaka da saudat sai fira ake suna raha, kaka tace" irin wannan dadewa haka nafi, Allah yasa de ayi damu, "🤣

Uffan bance ba danna lura neman magana take

" Bari ma'azu yazo muji ta bakinsa, "🤣


" Wai kaka miye haka, nida ko dedetawa bamuyi ba, "
Kaka tace" eh gaskiya kam, inaga sai kun kwana Kuna fira shine zaku dedeta, inba hakaba awarku nawa? "
Tajuya ta kalli saudat tace
" ke saude awarsu nawa?"

Saudat tanata dariya tace" kaka minti talatin nefa, "

" Au to minti talatin me marabarsu da awar,
Mugani meya baki aledar",🤣

ko kula ta banyi ba, ta zari ledar ta bude, "
Aikin kenan yaran zamani bakuda aiki sai shan zaqi, idan watanku yazo ciwon mara yakusa yimuku illa, wallahi Allah yakaimu idan watanki yazo kikazo kina cemin kina ciwon mara, ba asbiti ba ko chemist bazan rakaki ba
Saide shi daya daure miki gindi yazo ya kwashe ki yakaiki "


Saudat tana dariya tace" kaka nide bari intafi wannan drama taku bamai qarewa bace, "

" Um saude tunda kin hada ai dole ki zame, saikuma ki fada masa zamu hadu ne, zamu gauraya "

Nide nace" saudat ki gaida twins sai munyi waya," tace" aiwa "

Kaka tace" yara kuyi ku Gama duk tsiya de iyayenku hausa suke, ahh mu ayi mana karyar larabci,"🤣

itade saudat tana dariya ta fice suka tafi

Mujima da yawa hammad da sauda


** *** **

" Hassan tunda kun dedeta tsakanin ku, ai ina ganin Babu wata matsala, kawai kafada Mata zamuje kano din domin muyi magana da iyayenta, akwai gidanmu na gado nasa anfara gyara makashi, saikuje can ku zauna, maganar kayan lefe kuma zamuje nida yayarka maman nafeesa zamu siya nadauki nauyin wannan, inyaso kai kuma saika basu sadakin "

Ammu Yama rasa bakin magana kawai saiya rungume yayan nasa," yaya nagode Allah yasaka da alkhairi, "

" haba haba hassan
Idan banyi maba wanake dashi dazanyiwa, karka mantafa mu kadai iyayenmu suka bari, hassan kadena yimin godiya
Ka cancanci ayi Maka komai,"

Haka Ammu yatashi yana fara'ah, bakin nan kamar gonar auduga 🤣

After 5 day's

Su Abba sunje gidansu anty maimuna dake kano rijiyar lemo, kuma alhmdlh anyi musu karba ta mutunci an tsaida ranar aure nanda 4 month's


** *** **

Kwanci tashi rayuwa na tafiya har muna semester qarshe, yayinda soyaiyar mu nida ahmad tayi nisa, har idan bamu haduba Bama Jin dadi.


** *** ***


"Musa ya maganar aikin dana baka,"

jikinsa na rawa yace. "hajiya anfara de saboda aikin yanada yawa, Amma yanzu nafara nasamo number sa da kuma gidansu"


"OK to ka turomin Number ko,"

"To hajiya laila,"

"Dan waye shi?"

"Dan gidan sanata ne meci ayanxu,"

murmushi ta saki
"OK jeka saikaji alert"

Tundaga wannan lokacin laila kullum saita kira ahmad, shikuma baya amsa new number, daga nan ta koma text, ganin yanda ta da meshi da kira ne yasa, ya amsa, anan ta zayyana masa yanda take sansa kawai sai yayi rejecting Kiran

Ran laila ya baci, kuma tunda yayi Mata haka ta qudurta bazata barshi ba, saita samu abinda take so awajansa.



** *** **



"Khadijaty yakamata fa, gobe mu shirya da wuri, tunda kinga doctor din da aka gayyato mana, ance baida mutunci, ba shida wasa Akan aikin sa,"

"wallahi husnaty haka naji Ana fada, baida fara'ah, kullum fuska atsuke, to kinga kuwa ai gara mu kiyaye, da ayi mana rashin mutunci"


"Ato shiyasa nake miki tuni khadijaty Dan nasanki da nawa, in kika fara kwalliya zaki dau lokaci,"

"to husnaty ni kece da bazan tsaya inyi kwalliya ba, haka kawai Dan kinga da kyanki ni saiki hanani,"

"to khadijaty naji pls nide kiyi sauri,"

"karki damu qawata, insha Allah zamu rabu lafiya dashi,"

"Allah yasa qawata
Wallahi bakijiba gabana har faduwa yake"


"lalle husnaty, nikuma yanda kike da ilmi har addu'ah nake dama nice ke
Kawai ki kwantar da hankalin ki, Babu abinda zai mana, munga doctor marafa ma, kuma mun rabu dashi lafiya,"


"Toshiknn khadijaty sai anjima, sai mun hadu goben"






Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱



Writing by Amnah el yaqoub



Dedicated to my family



19



Ta shirya tsaf cikin atamfarta pink da sirkin green, dinkin Riga da sket, sosai dinkin ya karbi jikinta, ta dauko lapcourt dinta ta saka, taje gashin kanta tayi, tayi faking dinsa, powder kawai ta shafa, ta dansa pink lipstick, taja mayafinta pink tayi rolling, Jakarta ta dauka tafuto,
"Mama na tafi,"


"Zonan husna, yanzu duk jiya cikin dare kika hanamu bacci, saboda bakyajin dadi, Amma bazaki hakura da Zuwa asbitin nan ba?"

Agogon hannun ta ta kallah, goma da rabi, kuma adaidai wannan lokacin doctor dinsu zaizo
"Mama ai nasha magani naji relief,"

"to shikkenan idan bazaki iya bade ki nemi izni ki dawo gida"

"To mama insha Allah"


"Saikin dawo,"

"to"

Wayarta ce tafara ringing, "hello khadijaty,"

"husna kina inane, doctor fa yazo, wallahi ba fuska awajansa meya zaunar dake ne?"

"Khadijaty Babu lkcin bayani, kawai sai nazo gani nan, ta katse wayar"

11:6 dai dai tayi Mata agaban Dan qaramin ajin dasuka shiga domin qarin bayani Akan lemonia dawasu daga cikin cutukan da yara suke fama dashi

Yana sanye da suit baqa tayi masa kyau sosai, kansa sai sheqi yake, bayani yake cikin qwarewa da salonsa na qwararran doctor
Yanmatan kan Gaba daya yadau hankalinsu yana bayani Amma duka tunanin su yana kansa, gaskiya basu taba haduwa da likita maiji da kai da iya bayani kamar doctor TAHIR ba

Takai kusan minti ashirin a tsaye, ita bata nemi iznin shiga ba, shima kuma sarai yaganta bai bata damar shiga ba, kawai bayaninsa yake
Sam baya San yara masu sakaci Akan aikinsu, ahakan suke tunanin aiki bayan abinda zai amfanesu ma, basu maida hankali sunzo Akan time ba

Su yan ajin dayake bayanin dansu dayawa hankalinsu baya kan bayanin nasa, ita kuma baiwar Allah dataga ba shida niyyar bata iznin shiga, kawai saita nutsu ta maida hankalin ta Akan bayanin nasa,
Tun tana tsaye harta nemi waje Ajikin window ta jinkina tana jinsa
Har 12:30 tayi
Su kansu yan ajin sun gaji bare ita datake tsaye 🤣🤣

Shiya fara futowa daga ajin yana takun qasaita yazo daf da ita ya kalleta ya wuce

Khadija ce tafuto, tajanyota jikinta, "husnaty meyasa haka?"


"Wallahi sister ciwon kai cikin dare, dakyar mukai bacci nida su mama"

"Ayya sorry kinji,"

"Ok ngd" cewar husna

"Muje muci abinci muyi sallah Ana jimawa zai dawo"
Munci abinci a capteria, mun idar da sallah muna jiran lokaci ya qarasa mu tafi, khadijaty tace "wallahi doctor din nan baida mutunci
duk yanda akai baida Mata, Dan da yanada iyali bazai bar mace awaje ba, tunda baiji dalilin lattin ba,"

nace
"Toya za'ai sai hakuri"
Jakarta ta janyo, tafara kwalliya saida ta kammala sannan tajuyo ta kalleni
"Gashinan gyara fuskar ki mu tafi,"

"Share kawai khadijaty,"


"A a husnaty gaskiya ko powder ne ki shafa,"

Haka Babu yanda na iya nakarba nasake gyara fuska ta
Kai tsaye ajin muka tafi, duk Ana zaman jiransa, 1:45 yashigo muka dora daga inda muka tsaya
Saida yagama bayanin sa kaf, kafin yayi tambaya
Nanfa yan aji kowa yayi shiru, yasake maimaita tambayar nan de dakyar wani acikin maza, yayi bayani shima doctor tahir yace bai gamsu ba,ko akwai me qarin bayani?

Aji akai shiru, khadija sai zungurin husna take da kafarta

Husna tana jinta ta share ta,
Muryarsa suka tsinta yana cewa

"dama ku dakikai ne?🙈😳 In bata lokaci ina koya muku Abu karshe cikin ku arba'in da daya, mutum dayane zai iyamin bayani?
Ina hankalin ku yake?
Zanyi magana da director dinku, ni kwata kwata ma bai dace ku fita this year ba, 🙆🏻
Ahakan zakuje asbiti?"

Haka yake ta banbamin fadansa saida yagama, sannan acikin Mata wata ta daga hannu, tana ta kwarkwasa itama de bayanin kamar na namijin ta kwashe ta sake fada 🤣

Yasake tambayarsu Babu mai qarin bayani?

Khadija tayi kasa da murya tace" husna ki fada nasan kin sani sarai
Pls ki fitarmu kunya, ni wallahi ko na tashi, inna fara bayani murya ta rawa Zata fara karshe ya tsinka min mari yace in zauna 😱🤣🤣

Dariya taso kama husna, aikuwa kai tsaye ta daga hannu

Shi kansa mamaki ne yakamashi, ganin bata shigo ajiba, Amma ta daga hannu
Aransa yace zanyi maganin ki 🤒
Yace Mata "futo kiyi bayani,"
aikuwa yan aji aka bita da ido yuuuu👀
Tafita gaban ajin tafara bayani cikin nutsuwa, kawai ruwan bayani take zubawa
Shi kansa tun kansa yana sunkuye saida yadago kai ya kalleta, saboda shi a tunanin sa yarinyar bazatayi wani abin kirki ba
Aikuwa ya zuba Mata ido, kamar yasamu TV, kawai Dan karamin bakinta yake kallah yanda take bayani filla filla harma da abin da ba'a tambayeta ba, take qarin bayani akansa, maganar gaskiya itace shi kansa baiso tagama bayanin ba,🙈🤣 Takoma wajan zaman ta ta zauna,

Sake qarin bayani yayi sannan yayi musu sallama yafita, Amma zuciyarsa tana ingizashi Akan yaqara kallanta ko sau daya ne, haka ya share, saboda gudun renin dalibai

Office din abokinsa yanufa kai tsaye, doctor Bashir yana daddana system din gabansa, yace "kaga manyan likitoci, yaya daliban namu?"

Murmushi yayi, yace" daliban ku, sai alkhairi, nagama dasu Amma bazan sake dawowa ba koda kun turamin requesting "

" Haba doctor tahir, me yayi zafi haka,? "

Anan yabashi labarin abinda yafaru, yace" saida qyar wata yarinya tayimin bayani filla filla, Amma abinda zai baka mamaki shine wallahi ta window taji lecture, hanata shiga ajin nayi, saboda tazo late, wallahi yarinyar ta birgeni sosai "

D. Bashir yace" Amma wacece wannan kuwa, kode husna mu'az ce? "

Tahir yace" doctor taya zan sani nida Yau nafara ganinsu, "🤣🤣

Bashir yace" gaskiya tunda naji kace bayani filla filla nasan cewa ita kadai ce me wannan qwarin gwiwar, "




** *** **




" Khadijaty yi sauri mu tafi, wallahi banasan ciwon kaina yadawo, mama bazata min ta dadi ba, saboda dama saida tace karnazo"

Riko hannun ta khadija tayi suka fara tafiya abinsu gwanin birgewa, adaidai lokacin su kuma sunata qyaqyata dariya, sun futo daga office dinsu, ai suna ganin doctor Bashir har hada baki suke wajan fadin" Malam ina wuni? "

" Lafiya khadija, husna sannun ku ko, "
sukace yauwa suka wuce abinsu

" Khadija kiga mutumin nan Dan renin wayo, yanda yake dariya mukuwa yawani daure mana fuska kamar tsohon kumurci, "🤣

" hmm husna kenan abinda zan fada kenan kika rigani "




** *** **





" Yes doctor Bashir me pink din kayan ita nake fadama labarin ta dazu,"

" OK aidama nafadama husna ce
Sosai tanada kokari yarinyar
Gata saliha Babu ruwanta "

" OK" kawai yace


anan sukai sallama yashiga motarsa yadau hanyar kano

Fata nagari doctor tahir



** *** **



After one month
Karatu nake tuquru saboda zamu fara jarabawa ta karshe, nida saudat saide waya, kaka tayi mitar indena zaman daki ina futowa tana ganina Amma nayi mirsisi da ita, 🤣wuni nake ina karatu na, ahmad kuwa yayi nacin mu hadu naqi yarda saboda karatu



** *** **



Wayarta ce tayi ringing, cikin hanzari ta daga, "musa ya ake ciki?"

"Hajiya laila, hajiya laila ikon Allah, ai angama komai hajiya, nayi shige da fice na, nayi magana da yar aikin gidan,
Dafarko ta nuna gardama Amma dataga ruwan kudi, tuni ta amince, yanzu haka angama komai, nabata saqon kuma nayi Mata bayanin yanda zatayi amfani dashi, yanzu haka da ita nagama waya, tacemin taji mahaifiyar sa tana shirin aikensa gidan qawarta hajiya bilki, to zatayi kokari tasa maganin, kuma zatasa ido da kunne tasan lokacin dazai futo daga gidan saita fadamin, dazaran yafuto kuma zaije inda aka aike shin, saiki tareshi acan kawai kisan yanda zakiyi tunda de abun ansaba, kawai sai kuma me afkuwa ta afku, ya fada yana dariyar keta "

Laila cikin farin ciki tace" aikinka na kyau musa, zakaji kyakykyawan alert"

Musa cikin murmushi yace "nagoge sosai hajiya laila"

Tsalle tayi ta dira Akan gadonta, shikkenan burin ta yakusa cika, takusa dena mafarkin ahmad, yanayin datake so tagansu aciki shida ita zai tabbata kenan







Mrs usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

20



Tunani take adakin ta, ita kadai, anya kuwa Zatayi amfani da maganin nan?
Shin idan aka ganota yaya karshenta zai kasance?
To Amma kuma ai sunyi yarjejeniya da mutumin nan, sannan yace Mata idan komai ya kammala zai qara Mata wani abun
Idan tasamu kudi kafin ma agano ta saita bar musu gidansu

"Walaya! Walaya!!"

Taji Ana kiranta da gudu ta futo, "hajiya gani,"

"yauwa ga yan biyu nan da maryam zasuyi lattin school tun dazu suna jira baki shiryasu ba"

"To hajiya, ayi hakuri,"

Hannun maryam taja," taho qawata, tana Mata dariya gamida Jan kumatun ta.



** *** **



" My feenah yakamata inganki fa, gaskiya na gaji, haba wannan wanne irin karatu ne, "

" Tokayi hakuri my ahmad yanzu yaushe zakazo?"

"Yaushe zaku fara exam"

"nanda 3 days"

"ok kafin lokacin inasan naganki pls ki amince"

"toshkn yaya, bye bye"

"OK bye," shima ya ajiye waya






Please Login or Register in order to submit comment