Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

atafe?" Husna tace "wallahi mama mune, kawo wanke wanken," mama tace "a a keda bake kadai ba husna jeki zauna,"
husna tashige daki kenan, tahir ma yashigo mama tace " au tare kuke dama?" Tahir ya Sosa kansa yace "wallahi tare muke mama,"
Mama tace "Amma wannan yarinya da shirme take, kuma shine taqi fadamin,"
tahir ya tsugunna ya gaisheta, tace "tashi ka shiga ciki mana,"
shima yayi ciki, mama ta qarasa falon suka sake gaisawa, tace "kuma Zuwa Babu sanar wa husna," husna tace " mama kawai fa dama ganinku zanyi,"
mama tace "to ai kinganmu saiki tashi kukoma," husna tace "kai Dan Allah mama,"

mama tace "yanzu tahir shine kaima ka biye Mata kuke yawo a wannan kamar tata?"
Tahir yace "mama dama mun shirya zuwan, kawai fada ce bamuyi ba,"
tace "to sannun ku Mungo de,"

tashi yayi yafita
Husna tace " mama ina baby?"
Mama tace "na siyar ta, ke yar karar da iyaye suke yima bakya yi, 😀to tayi bacci karkuma ki tadar min yarinya a bacci,"
husna tace "to bari in ganta kawai,"
aikuwa tana shiga Dakin taga izdihar anbaje Ana bacci ga window abude, husna taje taja kafarta a hankali, aikuwa baby aka Bude ido, tayi fici fici da ido tana kallan husna, husna akasa daria ta meqa Mata hannu tace

" baby na zonan,"
izdihar taqi meqa hannu, husna ta dauketa, suna Zuwa falo kuwa tana ganin mama ta rarrafa da sauri tayi wajan ta, mama tace "yanzu husna saida kika tashi yarnan, nasamu tana baccinta, kin ganta nan batada aiki sai bari, Gaba daya halin nafeesa ta dauko, haba tun yanzu inta fara wasa ta zubar da ruwa akofi, ta wargaza tsintsiya, rannan ma cajar abbanku tasa abakinta tana sha, gashi cajar na jikin socket, haka Yai tamin fada ranar, nikuma shaf banma kulaba wallahi,"

husna tace" lalle baby to mama kawai ki bani ita,"
harararta mama tayi, suna wannan firar almajirai suka shigo da kaya niqi niqi, su katan din lemo dasu kayan shayi, sai uwar alawa wai duk na baby ne, tahir ne ya shigo mama tace
" kaikam baka gajia da kashe kudi ko tahir," murmushi yayi, yace
" mama ai ba yawa kayan baby ne"
Muqullin motarsa ya karkada wa izdihar yace" fine girl, zonan, "

husna tace" hmm nima kaga daga wajena ta gudu," hannu ya miqo zai dauketa aikuwa ta qanqame mama tasa kuka, mama tace" nikam ku tashi ku tafi gidanku, subarmu mu biyu ko izdihar, mama taci Gaba da cewa maimuna fa ta haihu jiya, kinji haihuwar?"
Husna tace" gaskya bansaniba, kuma shima Ammu bai fadamin Ba," mama tace" a a ai ita yakamata tafada miki ba Shiba, "husna tace" zansa meta ne, idan mun koma yanzu saimu shiga ta wajan ta," mama tace" yakamata de kam, ta haifi namiji, yace ma sunan babanku zaisa," husna tace cikin daria" to Allah yaraya Abba," tahir yace" amin," mama tace
" kuma Abban naku ma baya nan, yaje kaduna, da yasan zakuzo shima nasan ba inda zashi," husna tace" inna dawo wani satin ma gaisa," tahir ya dago da sauri ya kalleta, mama tace" uwar sakarci sai kinzo "🤣

Sun Dade agidan mama sannan wajan yamma suka tafi


** *** **


Mun futo daga makaranta kamar kullum nida mukhtar muna shan fira, yace" nahau adedeta akaini gida, "
nace masa" a a kawai muje aqasa," muna tafiya muna firar makaranta da abinda ya shafi karatu, har mukazo inda zamu rabu, nace masa" to ngd da rakiya, zan wuce gida,"

saide da alama hankalin mukhtar baya tare Dani, kawai ya zubamin ido yana kallan Dan karamin bakina, saida na sake cewa" mukhtar "
da Dan karfi, gamida hura masa iska a fuska, sannan yacemin

" t...to..to..nafeesa, sai munyi waya, "

nace" Amma me yake damunka haka?" Yace

" karki damu Babu komai,"
kafada na daga, nace" to shikkenan, sai munyi waya, "

yana tsaye yana kallo na najuya nabi ta wata hanya , takusa da wani faculty of madecine (kulliyati dib)

Hannun sa yatafa, yana kallansu ta tsallaken kwalta, yace anzo wajan,

kb kenan


** *** **


" Wash doctor zan mutu,"

tashi tahir, cikin bacci yaji kukan ta, asukwane yaduro daga kan gadon, yace "subhanallah husna, sannu,"
bari in kira ummi,
Dagashi sai gajeran wando yafuto, duk ya rikice, da sauri ya qarasa part din ummi, ummi cikin bacci taji bugu bana hankali ba, da sauri tatashi ta Bude kofar, tace "tahir haihuwa ce tazo ko?"
Tahir yace "eh ummi," tace "to muje," suna Zuwa yasa hannu ya tashi husna, yakamata har sunje kofa ummi tace "ahaka zaka tafi ne?" 🤣

Sai asannan yatuna da shigar datake jikinsa, komawa yayi da sauri yasa jallabia suka tafi hospital, suna Zuwa masu aikin dare suka karbeta, nurses din hanashi shiga sukayi Dan sunga gaba daya arikice yake, Babu daukan lokaci sosai husna ta haifi yarta mace, mai kama da tahir sosai, sauran nurses sunyi tunanin tagama saide nan su kaga tafara wata sabuwar naqudar,sunyi sunyi ta haihu takasa, saboda karfin ta yaqare, dole suka futo sukayiwa tahir bayani, nan yasa hannu, aka shiga da ita operation, ciki kuwa harda shi, sunyi nasarar ciro Mata wata babyn, itama Babu abinda ta dauko na husna, komai na tahir ne, saida aka musu wanka aka gyara su cikin kayansu, anan ne zaka tabbatar identical twins ne
Husna Dakin hutu aka kaita, yaran ma aka kaisu wani Dakin, ummi kuwa baki yaqi rufuwa Yau itace da jikoki har biyu,🤣 Allah abin godiya,

Kafin gari ya waye tahir yabaza labari ko ina, husna ta haihu, yadauki pictures din yaran yayi ta turawa, ahmad murna kamar shi akayiwa haihuwar, feenah kuwa kuka tasa, da mama ta kirata tafada Mata, wannan takaici dayawa yake,🤣 aure bata nan, haihuwar ma bata nan,🤣 gida suka dawo inda tahir yaci gaba da kula da matarsa, Jikin nata kuma yana warware wa a hankali, dangi kowa yazo ganin husna da yara, sati na zagayowa yara sukaci sunan ummi da mama, Amma Ana kiransu mama da mima, mai sunan ummi itace mima


** *** **


After 1 year, ahmad yagama masters dinsa, kawai yana jiran result ne, yaqara kyau naban mamaki, yayi wani fresh, Jin dadi ya zauna, daka kalleshi zakasan yana cikin hutu, bashida wata damuwa saita feenah 🤒

Yaran husna suna tsaiwa yanzu, baby kuwa an girma magana take gwaranci, tana yawonta ko ina, yarinyar akwai kyau kamar ita tayi kanta, dole inde kaganta kaji tashiga ranka, mama bata Zuwa da ita gidan biki ko suna, saboda kowa yaganta saiya tanka, shiyasa saita dinga barinta amakota inzata fita wajan taro

Kamar kullum yauma muna makaranta akazo aka sanar yan ajinmu zamuje occation, akwai University din dazasu je Dan haka za'a hadamu muje tare, duk wanda yake so zai bada kudi, ciki kuwa harda makarantar su Zahra, haka ta dinga magiya Akan muje, to qasa biyu za'a je, wasu zasuje Uganda wasu kuma misra
Dan haka nacewa Zahra nide zanbi yan Uganda, dannaga sister na aysha datake can, danma itama munyi waya tace saura 1month Takoma Nigeria Gaba daya, Zahra ce tadinga yimin magiya Akan Dan Allah na hakura mu tafi Egypt din, itama tayi shige da ficenta tashiga cikin wanda zasu tafi

Babu yanda na iya, saboda Zahra nace na amince, saimuje Egypt din





Saimun hadu a egypt fans💃🏻



Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱


Writing by Amnah el yaqoub



Dedicated to my family


34

Tsawon wata daya ahmad yadauka amasar, Babu abinda yake banda yawo sai kwanciya, sai chting, dayaga de zaman Babu inda zai kaishi saiyayiwa kakansa magana Akan kawai yanaso yakoma gida, yarasa wannan tafiya ta mecece 🤣
Marzuk ya dubeshi yace" yaro man kaza, ai mahaifinka yafadamin abinda yake damunka, to nide daga cikin dangina Babu Rago, Dan haka banaso kasa tunanin mace aranka har haka yataba lafiyarka "
Ahmad aransa yace taba lafiya na nawa kuma?

Marzuk yaci gaba da cewa" Dan haka ma nayi magana da mahaifinka jiya zaka koma makaranta kayi master's degree dinka, "ahmad yadago kansa yace" kaka masters kuma? "
Marzuk yagyada kai



** *** **


"Innalillahi, nikam wannan hand out din bana ganeta wallahi,"

ni kadai ina faman karatu a masallaci, wata yar Sudan ta dubeni tace " me kike fada?"

Na kalleta nace "wannan hand out din bana ganeta"


Saitace "mazai hana ki samu wani ko wata suyi miki bayani?"
Sainace "eh hakane," Natashi nafita
Ina fita naga wani Dan Nigeria nayi masa magana nace "da Allah ko zai iya yimin bayanin wannan hand out din?"
Yakarba yace "eto gaskya saide nahadaki da wani yayi miki" 🤣

Kai tsaye nabi shi, mukaje wani aji, yana zaune yana daddanna wayarsa
Kansa yasha gyara, yasa qananan kaya, wannan mutumin ne yayi masa magana, yana juyowa muka hada ido nagama ashe nasanshi Dan ajinmu ne
Bayani yayi masa Akan Dan Allah yayi min bayanin wani waje daban ganeba, baiyi musu ba yakarba, shikuma yamana sallama yatafi
Waje nasamu nazauna na fuskanceshi, nasake gaida shi, ya amsa
Hand out din na bashi, yace "a a rike, kawai ki dinga karantowa saina dinga yi miki bayani" 😳

Kallansa nayi da mamaki araina nace lalle me Abu da abunsa 😃
Karanta masa nake kamar yanda yafada, ya dinga yimin bayani filla filla, har saida yagama, nayi masa tambaya inda bangane ba, yaqara yimin bayani sosai, daga karshe nayi masa godia kuma na rokeshi Akan idan Babu abinda yake yi a irin wannan lokacin Dan Allah ya daure ya dinga yimin karatun, Babu bata lokaci ya amince Natashi na tafi

Cikin lokaci kankani nasaba da mukhtar, har cikin weekend da safe muna Zuwa makarantar yana min karatu, kuma sosai inajin dadi saboda dama ance ko kanada kyau to ka qara da wanka



** *** **


"Sis wallahi Yau, sha'awar bread nake da gyada,"

nace " lalle Zahra, yanzu ina zamu samu wata gyada?"
Tace "muje gaban jami'ah, Allah nagani," nace "to gaskiya kibari rana tayi sanyi sai muje"

Yamma nayi, ni har namanta ma, naganta ta futo ta sameni adakina ina kwance, tace " yanaga haka?"

Saida naganta na tuna, da sauri na shige toilet nawatsa ruwa, sannan na futo, abaya nasa, nayi rolling da mayafin abayar, muka futo, muna fita muka tsallaka titi, nace "to mu fara Zuwa musai bread din kawai
Me "raksha" (adedeta) muka tare, yakaimu Wani waje Tasamoh mukasai bread, daganan mukasai kayan miya da kaji
Muka wuce gaban jami'ah tasai gyadar sannan muka dawo gida, muna Zuwa muka zube afalo nace "wallahi kin gajiyar Dani"
Tace "to yanzu ba shikkenan mun huta ba"
Nace "hakane," sauran yan gidan mune su biyu suka mana sannu dakyar na amsa nide,🤣 Dan har yanzu ban manta ba da cewar sunasan my ahmad, "feenah lafiya kuwa kika amsa da kyar?"
Nace "wallahi gajia ce kawai," basu kawo komai aransu ba suka yarda

Sau dubu zan kirasu mama awaya mu gaisa haka sau dubu zan manta da baby
Duk da yarinyar tana raina Amma kuma wani lokacin sai naji raina yana baci Akan ta itada mahaifinta
Yauma da daddare nakira su mama muna Gama waya nace to saida safe, mama datake kusa tace "Amma auta ke mahaukaciya ce ko?" 🤣 🤣
Nace "na shiga uku mama me nayi kuma?" Tace "Amma ko dabba kika bari agida aikya na tambayarsa ko ya yake ko?"
Qasa nayi da kaina kamar tana ganina nace
" mama kiyi hakuri"
Tace "a a bani zaki bawa hakuri ba nafeesa, gyarawa nakeso kiyi
Yarinyar nan ba itace tayi miki laifi ba Dan haka banasan shirman banza" , nace "to mama kiyi hakuri, ki gaishe ta." 🤣

Haushi yasa mama kashe wayar ta wai ki gaishe ta, Babu irin tafara zama,? tana daria?Babu komai, Allah ya shirya😃

Husna nakira mukasha fira, har tanamin tsiya wai tunda na tafi bantaba turo Mata pictures dinaba, nace tayi hakuri zan turo Mata idan nasamu lokaci nayi


** *** **


Kamar kullum yauma na shirya ina tafiya zanje school dayake ba nisa akafa nake tafiya saide idan na gaji ne zan dawo a adedeta
Kawai sai ganin mutum nayi a gabana, cikin sauri naja baya, nace" subhanallah Malam lafiya? "
Yana sakin murmushi yace" wallahi tun ranar da kikazo Garin nan nake nemanki bansameki ba sai Yau, kamar wasa naga giftawar ki," nasake kallansa da mamaki nace" kamarya tun ranar danazo? Kasanni ne?"
Yace" sosai ma, ai tun acikin jirgi naganki kuma daga nan naji ina bala'in kaunar ki "
Nakalleshi dakyau nace" to na gode, Amma inada wanda nakeso kayi hakuri, "ban jira amsar sa ba nayi Gaba
Ina Zuwa gate din makarantar mu nayi shige wata, makarantar ya kalla yayi murmushi yajuya

Kabir yusif Bala kenan, da ne awajan tsohon gwamnan katsina, yana karatu a bangaren kimiyya, bayaji kwata kwata, akwai shi da harkar hutu, yana sakarwa yanmata kudi inde zai huta dake, baya shaye shaye saide neman Mata kawai, yana zaune awata unguwa mai suna balabil, gida aka kama masa shi kadai, kullum cikin kawo yanmata yake, Yau shine da waccan gobe shine da waccen, kwatsam yazo gida hutu ahanyarsa ta dawowa yaga feenah, tunda ya dora ido akanta yaji duniya Babu wadda yake so sai ita, shifa inde Akan feenah ne to zai iya rabuwa da kowa



** *** **


Acan misra kuwa ahmad yamiqa takardunsa jami'atul azahari, cikin sa'ah da nasara yafara karatun master's dinsa dayake ba kullum suke da lecture ba, saide yadawo gida yayi ta karatunsa, saide har Zuwa wannan lokacin tunanin ta yana ransa, har lokaci ya ware musanman na tunanin tane, idan lokacin yayi har fara'ah yake, haka zai kwanta shi kadai yana magana kamar tana gabansa, hakan dayake shine kwanciyar hankalinsa



** *** **


"Haba yata ki dinga aiki ke kadai, bakya gajia," husna tace "ummi Babu komai ai aikin baida yawa"
Ummi tace "to na aiki yarinyar nan me aiki, bari ni indora girkin kafin ta dawo,"

husna na wanke wanke, ummi ta dauko albashi tafara yankawa zatayi jalop, kamshin albasa na tashi husna ta to she hancinta, kafin ummi tayi magana sai amai
Aida gudu ta qarasa toilet din dayake falon taita amai sai kakarin amai take, ummi tazuba Mata ido tana kallan ikon Allah, ba shakka yarinyar nan ciki gareta, ummi tai murmushi tabita toilet din,
Husna ta dafe kanta, ta juyo kenan taga ummi ta qaraso, tace '' sannu husna, me yake damunki ne? "
Husna cikin jigata tace" nima bansaniba ummi "

Ummi ta kamota suka dawo falo, tace" kwanta akujera ki huta, ko nakaiki daki? "
Suna wannan jayaiyar tahir yashigo
Yace" ummi me yake damunta "
Ummi tace" a a tahir ai kaine likita, kai zan tambaya, "🤣 🤣

tahir yace Mata" sannu "

Tace" yauwa,"

" me yake damunki? "

Tace" zuciyata ce take tashi banasan Jin kamshin albasa saikuma kaina kadan"
Yace "to sannu tashi muje nabaki magani kisha," 🤣

ummi tace "a a wanne magani? Kaga muje asibiti,"

tahir shide Gaba daya kunya ma yakeji Dan yasan abinda zai biyo baya
Dan haka yace "ummi Dakin barta inta Dan huta saimu tafi," 🙈

ummi tace "a a mutafi"
Ba yanda ya iya haka yakaisu asibitinsa gwajin farko kuwa sakamako ya nuna tana dauke da Juna biyu
Nurse din tazo har office dinsa tasamesu tace

" doctor congratulations madam na dauke da Juna biyu,"
husna ta dago cikin mamaki suka hada ido da tahir ya kashe Mata ido daya, ummi kuwa baki yaqi rufuwa, nan take ta cire zobenta na gold tabawa nurse din, tace "to tasheta ka maida mu gida" 🤣

Tahir yaqi hada ido da ummi ya cewa husna" to tashi mana "
Ummi tace" kamata mana sai wani sunkuyar dakai kake kamar munafuki "🤣


** *** **


Cikin wata biyar danayi a Sudan nashaqu da mukhtar sosai
Dan takai yanzu kullum sai munyi waya dashi kokuma chting
Haka kb duk inda yasan ina nan to sai yazo wajan
Kamar Yau ma munshirya zamuje taron graduate na wata makaranta ahfat, munyi kyau Sosa nida Zahra, atamfa mukasa sai Dan qaramin mayafi da muka dora a kafada, inajinshi yana "feenah
Feenah pls ki tsaya mana" ,najuyo nace
" kabir, Dan Allah ka kyaleni na huta, haba nacema karabu Dani, kaqi ji ya kake so nama?"
Yace "so, shinakeso kibani"
Bai qarasa magana ba nayi Gaba abina, gabana yadawo ya tsugunna a gabana ya hade hannayansa yace " pls feenah"
Aifa nan kallo yadawo kanmu Gaba daya mutane aka zubamin ido
Harda masu dauka awaya, ganin saurayi maitashe, wanda aka sanshi, ya tsugunna agabana, raina nabata nace " miye haka kabir?

Kabari zamuyi magana daga baya," yace "kinyi alkawari?" Nace "nayi"
Aikuwa duk inda mukayi anata kallo na, Dan haka nacema Zahra gaskiya mutafi, nikam atakure nake
Tace "eh kawai mutafi, kinga akwai Dan nisa daga umdurman Zuwa Khartoum,"

muna tafiya ahanya Zahra tace "nikam feenah, meyasa bakya San kula kb?
Yana sanki sosai, kuma na tabbatar idan kin saurareshi watan wataran zaki soshi, inma yanzu bakya sanshi"

nace "Zahra bazaki ganeba," tace "to ganar Dani," nace " bawai sansa ne ba nayi ba, shidin Dan gidan Dan siyasa ne"
Tace " to menene danya kasance hakan? Kina so kicemin bakya San yayan yan siyasa?"
Nace "Zahra mayaudara ne, basuda adalci, dana saurareshi zaici mutunci na yatafi,"
tace "haba feenah kiyi tunani mana, menene aibun yan siyasa?"
Nace "still bazaki ganeba Zahra, kawai mubar maganar"
tacemin "Toshknn" dahaka muka qarasa gida

Da daddare ina kwance adakina ina tunani, araina nace bazan iyaba, bazan iya sake afkawa cikin wani tashin hankalin ba, ahmad ya yaudareni, daga karshe ma wata qasa yatafi kamar ya yiwa kiyashi laifi, wannan ma idan na saurareshi hakan ce Zata kasance, zan fada masa gaskya bazan iya hulda dashi ba, baby ce tafado min, afili nace

"nasan yanzu kina rarrafe baby, ko ya kike yanzu,? Inasan ganinki, inasan Jin duminki ajikina"

da naga tunanin bazai kaini ba, kawai saina hau chting, aikuwa naga anty husna online, pictures din da mukai dazu awajan taro nida Zahra natura Mata, nace me ciki, ga pictures din nan yaude sai ki barni nahuta, pictures dinane masu masifar kyau natura Mata, adaidai wannan lokacin kuma wayar na hannun tahir husna tana kwance ajikinsa text din yashigo wayar, yace

" Mata maman twins ga text nan auta ta turo miki,"

husna tace "nide banasan sunan nan,"

ya bubbuga bayanta yace
" to sorry baby nadena,"

tace "Bude mugani,"

aikuwa tahir yabude, yana budewa yaga pictures din, husna tace
" wayyo auta wallahi tasake fari kalli kagani doctor,"
tahir yana kalla yasake Bude idonsa yace

"wai shin wannan itace auta?"





Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱


Writing by Amnah el yaqoub


Dedicated to my family


36

"Anty husna albishirinki," husna tace "goro auta,"

"wallahi ingaya miki zamuje misra," husna cikin mamaki tace

" misra?"
Feenah tace "eh wlh," anan de tabata labarin komai, husna tace "ok nagane to Allah yakaiku lafiya auta
Yaushe zaku tafi?"
Nace "cikin satin nan insha Allah," tace

"to Allah yakaremin ke auta," nace "amin sister"
Husna tace "yauwa feenah, nikuwa lokacin haihuwar baby wanne asbiti kuka jene?"

Feenah tace "gaskya bazan iya tuna sunan asbitin ba, Amma menene yafaru?"

Husna tace "wallahi pictures din da kika turomin rannan doctor yagani yacemin wai yasanki, wai kin taba Zuwa asbitin su, kin haihu
wai bakida jini ma lokacin haihuwar, abokinsa ne yabaki, to Amma nide nace masa gaskiya bake bace, saboda abinda yafara tambayata shine kinada aure nace masa bakida, tunda keda bakida aure tayaya har zaki haihu, anan de yake cemin Amma kamar tayi yawa idan bake bace, shine nakeso na tambayeki ko kinga wani likita aranar? "

Feenah ta numfasa tayi wani murmushi mai ciwo, tace " eh washe gari, lokacin kaka tashiga toilet tabbas akwai likitan daya shigo Dakin, lokacin ina shayar da baby, Amma gaskya yanzu de namanta shi,
Ko zaki turomin pic din mijin naki, in gani ko shine mutumin dana gani?"

Husna tace "zan turo miki insha Allah,"

"OK" inji feenah, dahaka sukai sallama
, wayar ta wullar agado, tace "ahmad ka cuceni, ka lalatamin rayuwa, har tunanin mutumin dazan aura nake, tayaya zai fuskanci bayanin dazan masa?


** *** **


Kice " mama,"

" ma.. ma..",

" yauwa yata to kice Abba, "

tace" ab-ba,"

" yauwa izdihar
To kice Ammu"

tace "am.. Mu,"

"yauwa yata"

Abba dayake kallansu yace maman nafeesa karfa kuso kanku, su kuma iyayen natafa ba za'a koya Mata sunan suba? 🤣

Mama tace " rabu da wannan iyayen nata, ai suma basa 'ya da ita,"

Abba yace " a a yazakice haka, bayan husna tayi tayi dake kibata ita tahadasu dasu mima, Amma kinqi,"
Mama tace "wallahi alhaji, husna ce me nemanta kawai, kaga auta, koda munyi waya bata neman yarinyar nan kwata kwata, nima shiyasa ko sunanta ban koya Mata ba, Amma ai tasan husna,
Izdihar kice anty husna"
Yarinya kuwa tafada🤣mama tace "yauwa, suma wanda basa sonmu suje can suyi zaman su ko?"
Baby ta daga kai, duk da batama San abinda ake nufi ba


** *** **


Agajiye yashigo gidan,yana sanye da suit baqa, rigar cikin fara, yana, Zuwa yafada jikin matar kakansa, ummi bara'ah tace" wallahi zaka karyani,"
Ahmad yace" shikkenan sai kaka ya auro wata," ranqwashi takai masa, da sauri yadagata, yace" gaskya dole kaka yasake sabuwa, "yafada yana gyara kwanciya Akan cinyarta, kansa ta shafa tace," zan kuwa koraka kasarku," ahmad yace

" wallahi Dakin temakeni, na gaji da zaman nan," data gane so yake yatafin sai tace" aikuwa zama daram, anan zamuyi ma Mata,"
ahmad yace" aiku kishi ne daku larabawa, dasai in yarda kuyimin auren," bara'ah tace" gaskya mukam bazamu yarda kahada yarmu da wata ba," ahmad yace" to ai kinji nikuwa inasan na auri Mata hudu,"

bara'ah takai masa ranqwashi tace" kai tafi can Rago, jinake mace daya ce tasa duk ka sauya," ahmad ya sauya fuska yace" to shikkenan naji abar maganar" yafada yana lumshe idonsa, tace "eh de saina fada din," kansa taci Gaba da shafawa, jimawa kadan tana dubansa taga yayi bacci


** *** **


Juyowa tayi ta kalleni tace, "sister wallahi murna nake, zan fita wata qasar, ban taba tunanin Sudan dinma zanzo ba, Amma gashi zan sake fita wata qasar," kallanta nayi, lokacin danake daura belt dina, nace "Zahra kenan, ki godewa Allah, nasan duk tsiya mahaifinki yafi nawa komai da komai, nice yakamata nafadi wannan maganar," Zahra tace "to Allah yasaukemu lafiya, Amma feenah ko sau dayane, inaso kiban labarin ki, koda yaushe idan namiki magana Akan Abu, to sai naji kin kawo min wani abun daban, wanda yake sani cikin mamaki," kallanta nasake, lokacin jirginmu yafara tafiya aqasa, ina daukar video, nace" Zahra kenan, insha Allah wataran zan baki inde labari ne, "
tace" toshkn,"
video nakashe, najuyo nace" Zahra,"

Tace" na'am, "
nace" gaskya ayi video," aikuwa ta matso mukai ta video muna shirmanmu iri iri, ahaka har kowa yagaji

Karfe uku na yamma muka sauka agarin, kasan cewar ba dadewa zamuyi ba, kwata kwata sati daya zamuyi, Dan haka aka kaimu wani hotel mai kyau da tsada, awata unguwa Alqaddamiyya , kowa dakinsa, Amma nida Zahra mukace abarmu adaki dayama ya isa, sukace bazai iyu ba, haka qa'idar take, dole muka rabu, Amma Zahra kulle nata Dakin take tadawo nawa muyi zaman mu

Duk wani Abu da ake buqata anyi mana, washe gari aka fara fita damu waje waje, har gidan tarihi ankaimu
, ahaka har muka kwashe kwana hudu
Akwana na biyar dinne a kace za'a kaimu wajan tarihi na irin gidajansu nada, daga nan kuma zamu wuce yawo, wajaje daban daban,
Tun bayan sallar asuba bamu koma bacci ba, muna ta shiri nida Zahra, doguwar Riga nasa gown light blue, ta kama jikina tamin daidai, daga kasan kirjin akwai dutsuna ajikinta, daga kasa kuma rafa ce, sai daga bayanta kuma net ne akai ado dashi, ina tafiya net din yana Bina abayana, sai mayafin rigar shikuma nayi rolling dashi, sosai nayi

Please Login or Register in order to submit comment