Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana murmushi yace" nawan har naji dadi wallahi daka warware "
Ahmad yace" toya zanyi tahir Allah yadoramin abinda dole saide inyi hakuri in karbi kaddarata, Amma kuma fa yarinyar tayi, tayi, ba karya akwai zaqi, 🙈wallahi tana kukan nan banma San me take fadaba, "

tahir ne yakai masa duka, yace" Allah mutumina,"

ahmad yana murmushi gamida hawaye yace" serious tahir, gaskya yanayin akwai dadi "

Tahir yace" muma de zamu dage mu yi auren muji yaya akeji, "

ahmad yace" gaskya kam, nima zan nemi yafiyar nafeesa ne kawai inta amince ayi mana auren mu, "

tahir yace" why not"

Ahmad yace "yauwa ya mgnr abin nan,"
anan tahir yafada masa komai ahmad yace" acikin gidan nan ina zaune ake wannan qulla qullar lalle kuwa zan bincika, akwai rikici "

Tahir yace" kaide kabi komai a sannu insha Allah komai zai warware, "

" Hakane, "
inji ahmad

" Yawwaa Tahir ya maganar babyn ka din nan, dakake tunani, "

Tahir yace" ina tunani ahmad kana jinya, so nake ka warke saina kirata infada Mata "

Ahmad yace" no kakira ta Yau inka koma gida, ka tsarata sosai yanda bazata qi amincewa ba,"

" Toshiknn" inji Tahir

Ahmad wayarsa ya janyo gabansa na faduwa, yayi dialing number feenah, gara yakirata inma zaginsa zatayi kawai tayi inzata huce
Saide kuma wayar akashe, dole saide idan ruwan yakare yaje ya nemeta agida, Allah sarki rayuwa su kuma haka tasu kaddarar take
Wayar ya cillar gefe, Tahir yayi masa allurar bacci yace yakamata ya huta, shikuma yakoma bakin aikinsa

Saudat ce tanata shiri Zata je wajan feenah, tunda batazo Dan ziyara ba aitazo Dan jinyar yaya, Momy ce tashigo Dakin tace "kekuma ina zaki,"

saudat tace "Momy nayi ta Kiran wayar sister feenah ne, inasan magana da ita Amma wayar akashe shine nakeso inje inga ko lafiya,"

Momy tace "saudat rigima, banda abinki ai jibi zaku shiga exam
Dole zaku hadu, kiyi hakuri nasan insha Allah tana lafiya, kiyi karatu dakyau, idan Baku haduba Zuwa jibin daga school dinma saiki wuce, Amma yanzu de kije ki kula da brother dinki,"

"Toshiknn Momy"




** *** **




Bayan kwana biyu ahmad ya warke sosai, saide Gaba day ba shida walwala, Gaba dayansa ya canja, shiru shiru Babu magana, yayinda feenah sun Dade da fara exam, inda tabawa saudat uzurin cewa batada lafiya ne, shiyasa kuma ga exam agabansu ta karshe shiyasa ta kashe Wayarta, haka saudat ta hakura badan ranta ya soba, a bangaren feenah kuwa ita kanta saudat din haushinta takeji 🙊🤣


Ahmad yashiga Hali na wahala kullum cikin tunani ga tafiyarsa Cairo na matsowa ga shi yana so ya gyara tsakanin sa da feenah, Amma taqi bashi damar hakan
Kullum saiyaje kofar gidansu, haka kullum sai ance masa bata nan, kaka tayi tambayar duniya Akan su waye suke kiranta tace kawai samarin unguwa ne, wanda ita feenah tasan ahmad ne,
Akwai lokacin da kaka tace Mata taje ta duba ko yayan saudat ne, Amma qememe feenah tace ai suna waya dashi bashi bane haka kaka ta hakura



** *** **



Gidan yashigo ransa abace yayi part din Momy tadaga kai ta kalleshi tace "waladeey lafiya kuwa?"
Yace "Momy lokacin danayi rashin lafiyar nan waye yashiga part dinane?" Tace "gaskya Babu, kasan saudat tana karatun exam so bata shiga mabaruka kuma kasan dama akwai kasala saudat tafi ta gyaran, bana tunanin tashiga,"

"OK" kawai yace yatashi yafuta fuuuu
Momy tabishi da kallan mamaki, tome aka masa?

Main falo yadawo yana kwalawa walaya kira," walaya! Walaya!! Walaya!!!"
Yasan cewa tana aiki afalo sosai may be zatasan wayashiga

Kai tsaye yace "Mata wakika ga yashiga part dina kwanaki acikin yaran gidan nan?"
Lokaci daya ta firgita da Jin furucin sa, har ahmad yaso yayi tunanin wani Abu, cikin duburcewa tace "wal..... Walla... Wallahi bansaniba ba," baice komai ba yajuya yayi wajan baba maigadi, ai walaya tana ganin yatafi wajan baba maigadi damm gabanta yayi wani irin faduwa, nan take ta dora hannun ta aka 🙆🏻








Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱



Writing by Amnah el yaqoub



Dedicated to my family



25



Tana shiga gida Dakin ta ta wuce ta dinga kuka, Bama wannan ne abin damuwar ba, yanda takasa cireshi acikin ranta, gaskiya so masifa ne, ta tabbata yanzu shi yana cikin kwanciyar hankali, kaka ce take Jin sauti kamar na kuka, ta futo, tana daga labulan Dakin tace "ah nafi ashe kin dawo, menene kuma abin kuka?
Dama rabuwa da abokai ai tazama dole, nima haka zaki tafi ki barni nafi nasaba dake agidan nan" kaka takarashe maganar tana kuka
Haka suka rungume Juna suna kuka itada kaka Babu mai rarrashin wani

Kwanana uku a kano, nayi shirin tafiya zaria, banajin kuma zan qara waiwaitar wannan Garin, danma na taya kaka hada kayanta dazata koma gidansu aysha



** *** **



"Husna najima ina bin kanki Akan ki bani dama na shiga cikin zuciyarki, Amma hakan yaqi samuwa ko?"
Husna tace "bahaka bane doctor kawai nayi tunani ne" yace "to me tunanin naki yabaki?"

Tace "nabaka"
Tahir yace "mefa?"
Tace "zuciyata" dif taka she wayar
Wayarsa yarike ahannunsa yana murmushi shi kadai




** *** **




"Wlh khadijaty haka mukai dashi,"

khadija tace "gaskya mutumin nan ya yanke mu, ashe dama yana ciki shine yake ta wani cin magani," husna tace" aini abin yabani mamaki da farko, Amma bakiji yanda yake min magiya ba Akan na aure shi," khadijaty tace" wlh ki amince, "
nace" ai nafada masa na amince, "daria suka saki Gaba dayansu suka tafa



** *** **



Aguje nafada kan mama ina mamaaaa! Da karfi, kai ta dafe tace" auta bansan yaushe zakiyi hankali ba, "

baki naturo nace" kai nayi missing dinku fa," tace" to dagani banajin dadi, "

tashi nayi nahau cire kayana agabanta
Tace" wai nikam haka kikewa maman ma acan kano din? "
Nace" kai mama ai kaka Babu ruwanta Dani, abinda nakeso nake yi wlh, bana aiki sosai, "
tace" to shige daki ki shirya "

Nace" wai sister bata dawo ba har yanzu," mama tace" ai sai wajan yamma,"

jakata naja nayi daki, bayan nagama shiryawa nayi wanka na futo falo na kwanta Akan kujera nadora kaina Akan cinyar mama

Tace" to ya karatun"

" nace wlh mama karatu mun barshi sai jiran results dinmu kuma,"
tace "to Allah yasa a dace" nace "amin"

Mungama cin abinci kenan husna ta dawo aikuwa da ihun murna muka dane Juna, mama kawai kallanmu take tace" Allah ya shiryeku," aifa nan aka baje sabuwar hira, ina bata labari tana bani anan take fadamin labarin ta da doctor tahir, nace" wlh ki amince" tace "ai na yarda muna gaisawa de kadan kadan, ta waya," nace "to sister nunamin pic dinsa" tace "bai turomin ba saboda Bama chting Amma zanyi mai magana ya turomin saina tura miki," nace "to"



** *** **



"Guy kaje ka zauna, please ka dawo mana,"

ahmad yace "wlh wannan tsohon ne yarikeni tahir, Amma jibi zan dawo,"
Doctor tahir yace "yauwa kokaifa, munyi missing Naka," ahmad yace "wlh nima haka, ga kuma feenah datake raina inaso inzo in bata hakuri Akan abinda yafaru"
Tahir yace "eh gaskya ne nima maje Gaba dayanmu in tayaka bata hakuri," ahmad yace. "Amma naji dadi sosai nawan," tahir yace "karka damu,"


"Friend ya maganar babynka ne?"
Murmushi tahir yayi yace" husna, tana nan acikin zuciyata, dazu muka Gama waya," ahmad yace" harka gyaro ta kenan, "suka sa daria Gaba dayansu, ahmad ne ya kwaikwayi maganar tahir yace"
Ahmad iklima, iklima tabarni ahmad wlh ina sonki iklima, "🤣 katse wayar tahir yayi




** *** **




" Mamana, "

" na'am daddy, "

" nasan ke mai biyayya ce, kuma nasan duk abinda zan fada miki bazaki qi yimin biyayya ba,"

tace" hakane daddy,"

" to munyi magana da Dan abokina, muna so mu hadaku aure nanda 3 months,"

gaban saudat ne yafadi cikin rawar murya tace" to daddy,". yace " yauwa, Allah ya miki albarka
Zaizo ku daidai ta sunansa farouq, "

" to daddy nagode,"

yace" tashi ki tafi "

Daki Takoma ta dinga kuka, Wayarta ta janyo ta kira feenah saide wayar akashe, tun lokacin da abin nan yafaru kwata kwata ma wayar tafita daga ranta
Momy ce ta shigo tace " sauda, haba kiyi hakuri mana, idan yazo inbai miki ba kawai kiyi rejecting dinsa ni sai nayiwa daddynku bayani, a hankali, shi dama abinda yake so shine ayi bikin kafin su fara zabe,"

"to Momy nagode,"
tafada jikinta tana kuka



** *** ***




One month later
"Feenah, feenah, tashi kiyi sallah mana,"

"kai anty husna ke akwai damu,"

nayi juyi naci Gaba da bacci na, kyaleni tayi taje tayi alwala tayi sallah, da taga de banda niyyar tashi, ta dakamin duka, na tashi ina goge idona, tace "ke miye haka, tun dazu ina tashin ki sallah sai wani magagin bacci kike min,"

baki naturo Gaba, na tashi nayi toilet

Bayan sati daya, su husna sun Gama school, haka soyaiyar su da doctor sai abinda yaqaru koda yaushe suna cikin waya, suna kaunar junansu sosai harma da alkawarin aure atsakani



** *** **



Farouq yazo yaga saudat, baida matsala, haka kuma yanada hakuri, hakanne ma yasa ta amince, yana zaune a Abuja, Dan haka aka ci Gaba da shirin biki, ya rage saura 2 month's



** *** **



Yayi zurfi cikin tunanin mafita, Gaba daya bayajin dadin wannan aikin dama Garin baki daya, yaje yaje yaje harba adadi, karshe ma ance masa kaka tabar gidan, wayar feenah akashe tun lokacin da wannan matsalar tafaru, Gaba daya yadawo wani shiru shiru
Saudat ce tafado masa arai,
Daga murya yayi yana kiranta, ta futo "
Yaya gani,"

wayarsa ya miqa Mata, tace "yaya bangane ba,"
Yace "sakamin Num feenah, kokuma number da kikasan zan same ta idan naje zaria"

Saudat tace "wallahi yaya bansaniba,"

mamaki shinfide kan fuskar sa yace "bangane ba, kamarya baki sani ba?"
Tace "wlh yaya nima kaina nema nake,"
yace "toko zamuje zaria din mu dubata,"

saudat tace "yaya to zaria ina?
Ina zamu nufa? Sannan ko jiya nadau mota naje gidan kaka an tabbatar min tariga da tatashi agidan, ni maganar bikinama nakeso nasanar Mata,"

alama yamata da hannu Akan tatafi, karta qara masa wata damuwar 😃




** *** **



"Mama ga maganin naki fa da doctor yabayar nasan baki shaba,"

"wlh husna banasan maganin qarin jinin nan banajin dadinsa,"
"to mama kiyi hakuri kisha,"

"to bani nasha, tashi kiramin autata tazo ta dora abinci,"

"yanzu mama saura 7 months ki haihu,Amma kina ce Mata auta,"

mama tace "husna gidanku, kunji yarinya ke har wani lissafi ma kike, tashi kiramin ita"

Daki tashiga zaton ta, karatun novel nake, Amma sai taga sabanin haka, bacci na nake shararawa haiqam, kallo na tayi da mamaki, aranta tace Tome yake damun yarinyar nan, tashi na tashiga yi, dakyar na tashi, ina tashi na shaqi qamshin turaren ta, aikuwa da gudu nayi toilet na dinga shara amai, husna tabini da kallo gabanta yana faduwa
Ina futowa tabini da kallo, nace "sister wannan turaren naki bana sansa, Dan Allah fita daga Dakin nan,"

husna tace "yar renin wayo dagani har ke dashi muke amfani kafin kitafi school......

Kafin tagama magana nasake yin toilet da gudu nayi wani aman, aikuwa ina futowa tajani, ta duba idona, takama hannu na, ta duba, cikin loka ta dauko pt strip, tace" jeki iyo min fitsari anan"

tabata wata roba, aikuwa ba musu feenah taje tayi, jikinta duk yayi sanyi, ta futo tabawa husna
Jikin husna ne yadauki rawa ganin layi guda biyu Ajikin pt din, wato kenan abinda take tunani ne yake San tabbata, lokaci daya hawaye yasilalo daga idanunta tana hawaye tace "feenah"


Nakalleta da mamakin meyasa ta kuka, tasake cewa "feenah wayayi miki ciki?"

Kuka nafasa da karfi, nadora hannu na akaina, hakan yasanya mama dataji shiru daga kiramin auta itama tayo Dakin cikin sauri
Abinda kunnuwanta suka jiye Mata ne yahanata qarasawa Dakin








Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱


Writing by Amnah el yaqoub


Dedicated to my family



29


Ganin yaqi bata wayar yasa tasa hannu ta karba, "hello yata yagida?"
Husna cikin ladabi tace "mama ina wuni?"
Ummi cikin Jin dadi ta nemi wajan zama tace "alhmdlh ummin tahir ce"
Husna zare ido tayi tace "ummi ina yini ai ban ganekiba"
Ummi Ana murmushi a kace "a a ai ba komai yarinya, yaya sunan kine?"
Tace "husna"
Ummi tace "masha Allah, yaushe zakizo naganki?"

Husna tace "ai da nisa, saide wani lkcin idan munzo kano sai nazo"
Ummi tace "a a ba'a nan Garin kikeba?"
Husna tace "eh wlh muna zaria"
Ummi tace "Toshiknn yata Babu komai kinji, ki gaida ummanku,"

"to Ummi na gode sai anjima,"
ta kashe wayar
Ummi tajuyo ta miqawa tahir wayarsa wanda yazuba Mata idanu yana kallanta kamar tv

Tace "ita kuma wannan fa?"
Tahir yayi qasa da kansa yace "Ummi dalibata ce"
Ummi tace "um aikam nagani, yanzu ma ai naga karatu kuke, idan kun Gama karatun ne zaku samu yan biyun" 🤣

Tahir yace cikin shagwaba "kai Ummi nifa bance haka ba"
Ummi cikin Jin dadi tace "to koma de menene ka shirya kuje ku gana, idan da Hali ma ayi komai agama cikin wata daya," zaro ido yayi yana kallanta, tace" to menene?
Bakasan yanda na matsu kayi aure bane tahir shiyasa, kai kadai gareni
Banda kowa, mahaifinka ya rasu, koso kake nima in mutu banga auren kaba? "
Cikin sauri tahir ya girgiza kansa yace" a a Ummi insha Allah zanje cikin satin nan "
Ummi ta shafa kansa tace" yauwa Dan autana "



** *** **



After 3days
12:6 suna manne da Juna awaya, ba abinda yake Mata sai aikin shagwaba, husna tace" wai nikam doctor bakada qanne ne? "
Tahir yayi murmushi yace" banda qanne banda yaiyu, ni kadai Ummi ta haifa, kafin daga baya Allah yadauki ran mahaifina, itace ta tsaya wajan kula da komai nasa har na mallaki hankalin kaina, har Zuwa yanzu "

Husna tace " Allah sarki shiyasa "🤣

Tahir yace"shiyasa me?"
Tace "shiyasa kake shagwaba,"

daria tabawa tahir, yace "yanzu ahakan inada shagwaba?"
Tace "sosai ma,"
yace "lalle Dan bakiga dan'uwana bane,"
tace "waye hakan?"
Yace "aminina ahmad, shi agidansu shine babba, Amma idan ya kwaba miki wani abin, saiki dauka shine auta"
Husna tayi daria tace " lalle, nima kuwa Dan bakasan autar mama bane, Babu abinda tabari, Amma ganin batada qani ne shiyasa,
Kai karshe ma rikicin ta ne yasa Ammu yace akaita boarding, kwata kwata bataji"
Tahir yace "um kaji manya wato ke babba ko?"
Husna tace "bakasan rikicin yarinyar nan bane, idan na share ta saita rainani"
Tahir yace "um kaji manya," husna cikin shagwaba tace "Allah my one zan kashe," cikin sauri yace "no yi hakuri nadai na, shikkenan?
Yanzu fadamin yaushe zanzo?"
Tace "duk lkcin daka samu dama," yace "toshkn zaki ganni jibi insha Allah" tace "to Allah yakaimu"
Yace" to yanzu fadamin abinda zanji dadi indinga tunashi har inyi bacci "
Husna tace" to rufe idonka"



** *** **


Yayi neman number ta harya gaji
Gaba daya yarasa me yake masa dadi
Daga karshe ya saduda yamiqa lamuransa ga Allah, yasan Babu wani bawa da zai kaucewa qaddararsa, abinda yasa aransa dayane shine kawai shida qara kula wata mace da sunan soyaiya har abada
Itama azal ce ta fada masa harya furta Mata kauna, Dan tunda yake shide ba ma'abocin kula Mata bane, saide ma su soshi, zai sawa ransa dangana, yayi addu'ah Allah yakawo masa karshan wannan matsala

Gaba daya yazama shiru shiru, dama yaya aka qare
Kamar kullum yauma yana kwance adakinsa yazuba wa P. O. P din Dakin ido
Tayi sallama ta shigo, tashi yayi zaune yace" momy kece? "

Tace" waladeey, menene yake damunka? "
Ahmad yace" Babu komai momy kawai aiyukane sukai yawa"
Tace "Ahmad bakada wata mahaifiya bayan ni, bansan meyasa kake San boyemin damuwarka ba, ko kanaga kanada wadda tafini?"
Cikin sauri ya girgiza kansa, nanda nan idanunsa suka ciko
Momy janyo shi tayi jikinta ta dora kansa Akan cinyarta
Tace "yi hakuri to, menene abin kuka kuma, yi shiru kaji waladeey na"
Haka tayi ta rarrashinsa daga karshe tace yadaure yafada Mata abinda yake damunsa, tiryan tiryan yafada Mata budurwarsa ce tunda tagama karatu har Yau ya nemi number ta yarasa, kuma baisan gidansu ba,
Momy jikinta yayi sanyi tasan tunda ahmad yashiga damuwa Akan Abu to tabbas ya nasan abun sosai

Momy ta nisa tace" ahmad kayi hakuri mana, kamiqa lamuranka ga Allah insha Allah zakaga abinda zai biyo baya ka dinga addu'ah Allah yabaiyana mana ita "
Kasa magana yayi saide kawai ya daga kai alamun to

Kansa taci Gaba da shafawa har taji jikinsa yasaki alamun yayi bacci sannan ta gyara masa kwanciya ta fita



** *** **


Gaye kayi sauri fa, nasan halinka, ahmad cikin kasala yace" dallah Malam ni majima da shiryawa zakaje gidan surukai kamar zakaje wata qasa "

Tahir yace" eh naji, futo nazo kofar gidan zan daukeka "
Futowa yayi cikin baqin yadi da baqar hula yasa agogo shima baqi, da takalmi shima de baqin, kalar fatarsa saita qara futowa fara tas acikin kayan duk da yanada Dan duhu kadan, Amma mai karatu kaso kaga ahmad a wannan kayan

Su momy suna falo, yazo ya tsugunna har qasa ya gaida su, mamy hakima tace "dana duk wannan kwalliyar ta office dince?"
Shide kawai murmushi yayi ya miqe yace musu saina dawo

Momy kawai da ido ta bishi Dan tasan abinda yake damun Dan nata

Yana fita ya ganshi acikin motarsa fara, shiga yayi yace" muje, "tahir yace" abokina irin wannan kwalliya haka kamar kaine saurayin? "🤣
Wannan ai saikasa husnan ta dawo wajanka"

Ahmad yace "kaga Malam Dan Allah muje haba, sunyi nisa sosai wayar ahmad tadau qara, yana dubawa yaga hassan ne, ya daga can daya bangaren Ammu yace" masa" yallabai baqin turawannan sunzo, wanda kace idan sun zo ayima magana zaka gana dasu, ahmad yace" ya Salam wallahi na manta gani nan Zuwa," bayani ya yiwa tahir, badan yasoba haka yasaukeshi, ahmad ya leqo ta glass din motar yace saika dawo abokina dama ni wannan tafiyar wallahi gabana faduwa yake," tahir kawai harara ya miqa masa yaja yatafi, daga baya ahmad yayi waya company su azo a daukeshi

** *** **

" Abban husna yaufa muna da baqi, "
Abba yace" waye zaizo ko mutanan kano? "
Mama tace" a a bakaga mutuniyarka ba tun safe takasa zama, ayi wannan lemo ayi wancan
Girki, Abba yace "me yake faruwa?"
Mama tafada masa komai yayi murmushi yace" to Allah yakawo su lafiya "


** *** **

Kasan cewar unguwar ba boyaiyiwa bace yasa tahir ya gane da wuri
Motsi kadan husna zatai saiya dubeta, duk ta takura da irin kallan dayake zuba Mata

Husna ta kai shi har cikin gida yagaida mama, inda Yabar kudi Akan kujerar kusa d mama yace "gashi asiyawa auta alawa"

Dasuka futo husna daria, tahir yace "menene?" Tace "autan fa kanmu daya da ita,"
d mamaki yace" haba?" Anan ta dinga bashi labarin feenah har yaji yanasan ganinta, suna tsaye Abba yadawo daga unguwa

Tambayoyi ya yiwa tahir Babu bata lokaci ya amsa, Abba ya yaba da hankalin sa, gudin kada azo ayi DANA SANI irin na nafeesa 🤣shiyasa Abba yace yabashi dama ya turo magabatansa ayi maganar bikinsu, duk wani bincike daya kamata ayi, zaiyi insha Allah

Bai barta haka ba saida yacika ta ta alawa da kuma less, sai takalmi da jaka su kayan kwalliya sannan yatafi yana mai farin ciki


** *** **

Kaka gaskiya nikam kwadon nan kiyi shi da yaji, "
" a a nafi banasan yaji,"

" gaskya kaka nito da yaji nakesan nawa, inyaso ke sai kiyi taci Salam, "

kaka ta kalleta da mamaki" , kyaci gidanku keda yajin, kina fama da kanki Amma kina wani neman yaji, "turo bakina nayi Gaba, na kyaleta, gashinan idan zakici kici, idan bazakici ba meqomin zogale na, kwadayaiya kawai," harararta nayi na shige daki, tace" kyaji dashi, da kanki zakizo ki dauka "

** *** **

Abba yayi duk wani bincike Akan tahir, sosai yaji dadin sakamakon daya samu akansa
Dan haka iyayensa suna Zuwa aka tsaida ranar aure nanda wata hudu

Feenah Babu wanda yakaita murna, Akan auren nan, har kaka tagaji dajinta tace" kai ni rabi'atu kamar akanku za'a fara aure, wannan kekam idan naki auren yatashi ba musan irin rashin kunyar da zakiyi ba, "
Nace" kaka kenan kinci naki zamanin nima saiki barni naci nawa, ke wayasan abinda kukayi a naku bikin keda Amadu "

Kaka aka murmusa a kace" Allah sarki Amadu, a nacan sai Hali sai sallah, Allah yaji qanka," nace" amin kaka, "

Can kuma tace" nikuwa nafi ina yaron nan Dan albarka? "
Nace" kaka wakike nufi?"
Tace" ah Amadu mana yayan saude, wazan tambayeki inba Shiba? "

Dif kakeji nafi ta dauke wuta






Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱



Writing by Amnah el yaqoub



Dedicated to my family



27



Ihu nasa da qarfi ina fadin "na shiga uku na, Abba Dan Allah kayafemin wallahi ba laifi na bane,"

mama ce tatashi tace. "gaskya alhaji Babu inda Zata, yaya baka tsaya kaji abinda yafaru ba zaka yanke hukunci cikin fishi,"

husna ganin iyayenta zasu fara samun sabani abinda basu taba ganiba tunda suke, nan itama takama kuka, tana rokon mahaifinsu Akan Dan Allah yayi hakuri
Abinda yabasu mamaki shine yanda shi kansa Abban su kaga yana hawaye

Mama ce tasauko tafara bashi hakuri, yace "to shikkenan tunda bazata barmin gidan ba ni bari in bar muku gidan"

Mama ce tayi sauri ta riko kafarsa, tace "Abban husna Dan girman Allah kayi hakuri,"

tana kuka tana bashi hakuri, tace "yanzu yaran nan su biyu garemu, meyasa kake so su fuskanci matsala arayuwarsu?
Karfa ka manta Amana ce Allah yabamu tasu"

Abba yace "haba me zaku fadamin, ina zaune agidan kunsan abinda yake faruwa Amma kukasa sanar Dani, to so kuke saita haihu sannan zaku sanar Dani?"

Mama tace "kayi hakuri alhaji munsan munyi laifi, Amma kayi hakuri ka fuskanci abinda zan sanar dakai

Mama bata boye masaba ta bashi labarin komai, idanunsa yayi jajir

Yadago yace" uwa ta kin tabbatar haka abin yake? "
Ina kuka nace" Allah Abba hakane, wallahi fyade yayimin, Allah bahalina bane hakan "
Yace" to shikkenan kuskure de anriga da anyi
Hakika kuma nayi DANA SANI Akan zuwanki kano ma baki daya
DANA SANI lokacin da yaron nan auwalu yanuna yana sanki dana baki shi kunje can kun qarata, nayi DANA SANI nafeesa, "

dago kai nayi ina kallansa Jin sunan daya kirani sunan mahaifiyarsa Amma tashin hankali yahanashi boyewa

Yace " uwa ta ki fadamin inkin San inda yake ko Dan uban waye inje in qwato miki hakkin ki,"

nace" Abba wallahi bansan inda yake ba,"
Wanda saida nafadi hakanne mamakin kaina yakama ni, meyasa ba zance Dan gidan sanata ne ba?

Yace " kinyi kuskure uwa ta, shikuma duk daren dadewa zaizo ya sameni, insha Allah sai yayi DANA SANI"



** *** **



sun nutsu kowa yana cin abinci Amma Gaba daya hankalin sa bayama kan abincin

Mamy hakima tace "a a son, me yake damunkane, Gaba daya kamar bakai ba, kana juya spoon cikin abinci Amma kakasa ci,"

auta maryam ce tace " yauwa yaya dama kace zaka yi mana ankon anty sauda, kaga Yau ba school sai muje ma har wajan shan ice cream ko yaya"


Mabaruka ce ta kalleta tace " kekam bansan yaushe zakiyi hankali da tunani ba wallahi"

"To ina ruwan ki Dani, ko yayanki ne?" 🤣 Inji auta,

Banza tayi da ita, Dan tsaf Zata bige bakinta yanzu
Baice musu qala ba, yamike gamida ture abincin yayi daki
Gaba

Please Login or Register in order to submit comment