Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "wanake gani Kamar amadu?"
Cikin murmushi yace "nine kaka"

Matsowa tayi takama taba fuskar sa tashafa kansa, tace "yauwa yanzu nasan ba mafarkin dana saba bane, yanzu amadu kana duniyar Nan, muka nemeka muka rasa,"
Sai kuka Kuma
Cikin sauri yace "a a kaka kiyi Hakuri, kiyi shiru," tace "ashe zamu sake ganinka "
Yace "eh wallahi"

kaka,tace aure Kuma yazo kusa
Murmushi yayi baice komai ba

tashi tayi tace "lalle yau inada babban baqo Ina Zuwa" ,

hanyar kitchen ta nufa
Shikuma ya zauna akujera
Yana juyowa hannunsa na dama yaganta akwance tana baccinta Cikin kwanciyar hankali
Gashin kanta yabazo Mata Har fuska, dan qaramin bakinta ya kallah, bazai manta dandanon wannan bakin ba, idonta ya kallah, Gashin idonta daya hadu da dan'uwansa saiya qara yimata kyau, Kamar tasaka gashin ido

Ahankali yatako Yazo Har inda take, agaban kujerar ya tsugunna
Yasa hannunsa yagyara mata gashin kanta
Matso da fuskar sa yayi gab da tata,
Cikin baccinta taji qamshin turaren da bazai Iya gogewa a qwaqwalwarta ba, murmushi tasaki taji baccin yaqara mata dadi, danhaka tasake gyara kwanciyar ta taci gaba da bacci

Murmushin datayi shine yaqara shagalar dashi, baisan lokcin da dayakai hannunsa Kan Dan qaramin lips dinta ba, Ahankali yake shafawa Yana hurawa idanunta iska
Jitake Kamar numfashinta Yana haduwa da wani, kasancewar kusanci da fuskar su tayi, Ahankali ta Bude idonta, aitana ganinsa tatashi tana zare ido
Kenan ba mafarki takeba shine akusa da ita, meya kawoshi gidan Nan? Waye ma yace masa Ina gidan? take tambayar kanta

Murmushin sa Mai tsada yasakar mata, yace
" kinata baccinki nikuma kin barni Sai gadinki nake"

, harararsa tayi tatashi tayi daki, bayanta yabi da kallo yanda hips dinta yake juyawa yayi bala'in tafiya da imaninsa, aransa yace wayyo Allah wannan yarinyar zata kasheni

Toilet tashige tayi brush tasake gyara kanta sannan tafuto falon, Ahankali Kamar bataso tace masa "Ina yini"
Da sauri ya kalleta, saboda baiyi zaton hakanba
Yana Murmushi yace
" lafiya amarya"
Harararsa tayi, tabi kaka kitchen
Kaka tanata kimurtun hada abinci ita kadai, tana ganin feenah tace
" yauwa alhamdulillah dauki wannan kikai masa, Ina Zuwa da lemon Nima"
Babu musu taje ta tsugunna a gabansa ta ajiye abincin, Ahankali Cikin nutsuwa take zuba abincin
Kuskus ne da miya dataji naman sa Sai ganyaiyaki dangin su salat
Tsugunna war datayi ne yabashi damar ganin abinda yake Cikin rigar ta, Cikin ransa yace masha Allah, bulbul dasu farare gwanin sha'awa
Ya shagala a kallan wajan baisan tagama zubawa ba, saijin tashinta yayi
Ba yabo ba fallasa tace
masa "Ga abinci"
Muryarsa ashaqe yace
" bazaki bani ba?"

Shiru tayi masa tana kallan wani wajan

"Ungo"

Abinda yace mata Kenan, takai dubanta gareshi taga yabata hijabi, Shima kawai ganinsa yayi Akan kujerar baisaniba nata ne kona kaka, shikam koma na Waye
Gara tasaka inba hakanba Kuwa gaskya saide kaka tarufe idonta

Yana Bata hijabin still idonsa ba akanta yake ba, Yana kallan wani wajan, idanunsa tabi da kallo taga ya zubawa kirjinta wani mayan kallo, danhaka Cikin sauri takarbi hijab din tasaka, Cikin ranta tace wannan kallo haka Kamar za'a cinye mutum

Yana cin abinci kaka takawo masa lemon juice
Sai surutu take masa na Bayan saduwa
Haryadanci kadan, tace
" amadu wannan cin abinci Naka Kamar na yar taku"
Shiru yayi Yana Sosa kansa
Daga baya yadinga Bata labarin irin zaryar daya dinga yi atsohon gidanta, kaka tace "wallahi adamu ne yadawo Dani Nan shida ma'azu
Wai sun dawo danine kusa dasu, saboda can din yayi Nisa Kuma ni kadai"
, Ahmad yake "eh gaskya wannan haka yake,

Ashe shiyasa naketa Zuwa bakwa Nan qarshe ma akacemin ansaida gidan,"

kaka tace "eh wallahi Nan na nadawo, ai Ina yawan tambayar ka awajan nafi, tace min katafi masar shiyasa baka Zuwa"

Da sauri ya Kalle ta, wato boye laifinsa tayi, lalle yau yaqara yarda feenah tana sansa
Kaka taci gaba da cewa,
" to itama Kuma adamun yanema mata scholarship tatafi Sudan, saidata dawo ne nakejin labarin komai awajan ta Har abinda yafaru

Nace Toya za'a yi ai haka ubangiji ya qaddara, saide muce Allah mungode Maka daya bamu ikon cin wannan jarabawa amadu

Allah Kuma yayafe mana, yakore shedan azaman auren ku "

Ahmad yace " amin kaka
Yanzu ma naje gidan Tahir ne saiyace min zaizo yadauki nafeesa shine Nace kawai zanzo indauke ta, daga Nan ma naganki, Naga gidan da kike "

Kaka tace" a a ka kyauta babu laifi kayi kokari
Allah yamuku albarka"

Saida muka dade muna fira da kaka, Dan dole na nadauko kayana muka tafi, Ahmad kudi ya ajiye Akan hannun kujerar dayake zaune, aqallah zai Kai dubu hamsin, yace "kaka gashi kyasai goro"

Kaka tanata ruwan godia muka tafi, nikuwa naci hijabi Kamar matar liman

Muna tafiya amota narufe idona Kamar me bacci
Shiru ne yabiyo baya, shi Yana shakkar yimata Magana ita Kuma tanaso tana basarwa
Kamar daga Sama taji yace "Ina tsarabata?"
Still idonta arufe tace
" aibana Bawa irinku, kaga babu amfanin tambaya Kenan"

Cikin ransa yace "dama nasan za'ai haka"

Danhaka yace
" toshikkenan, yasu mama da Abba"
Agajarce tace "lafiya"

Daga haka babu Wanda yasake Magana acikinsu, sunyi tafiya sosai yatsaya awani waje, yace "Ina zuwa,"
Fita yayi yashiga wajan, baidade ba yadawo, suka Ci gaba da tafiya, Shiru Kamar wasu kurame

Sunzo kofar gidan Tahir Ana Kiran sallar magrib, fos dinta tadauka tace
" barshi ananma ya isa," tafara kokarin Fita, tana budewa taji kofa arufe
Juyowa tayi tana kallansa, yace "Amma my feenah Magana nakeso muyi, sannan koba hakaba kema kinsan Bazan barki awaje ba dole saina kaiki Ciki, sonake mugama Magana saimu qarasa Ciki"

Itafa batasan Zaman motor Nan tsakaninta da Ahmad 🤣

Gabana Yana faduwa cikin rawar murya nace
" nide banasan Zaman motor Nan, muje Ciki saimuyi koma wacce irin Magana ce"
Shi maganar tatama saita bashi Daria, yace
" my feenah ki yarda Dani babu abinda zanyi Miki"

Kuka ne yazomin naba gaira babu dalili, nace "ai abayama haka kace"
Yace "OK, OK, naji toyi Shiru banasan kukanki," Bata zataba taji tattausan hannunsa afuskarta, yashare Mata hawayan, yace "Muje"

Atare suka futo, takama kiciniyar daukar jaka

Sunkuyawa yayi, yace
" bani,"

tace "a a barshi zan Iya"


"Allah idan baki baniba zan daukeki daga ke Har jakar"
Sanin zai Iya aikata hakanne yasa tasaki dasauri
Kawai fos ce ahannunta, shikuma yadauki jakar, ahaka sukaje Har falon husna, suna zaune dukansu suna kallo, yaran suka taho da gudu suka rungumesu, Tahir yace "man, sainajika Shiru,"

Ahmad yace "maine yaqare mana ahanya"

Feenah cikin ranta tace
" haka de ka Iya" 🤣

Waje suka samu suka zauna, husna tanata tambayar ta Yan gida, suna firar gida abinsu gwanin sha'awa
Tahir ma Yana wasa dasu mama,
Shikuwa gogan Yana zaune Yana yiwa feenah pictures, Kamar danne danne yake

text ne yashigo wayar Tahir
Anutse yadauko wayar zai duba, yayi tunanin wani abune muhinmi

"Yaya Tahir please please kabani aron qanwarka inaso muyi Magana da ita kafin natafi "

Abinda yagani Kenan, yakai kallansa wajan Ahmad

Tashi yayi yadauki mama da mima afili yace "dole aceda mijin Iya baba" 🤣

Ahmad Sarai yasan dashi yake
Yana Tashi yace "muje nakaiku wajan ummi ko"
Yadubi feenah yace "auta, kaimuku abinci falon baqi mana, kisamu ladan wannan gwauron"

Husna tace "yau Kuma Kaine kake masa,"

Ta kalli yaran tace "mima, mama saida safenku ku gaida ummi,"

taja jakar feenah tayi Ciki

Nima kitchen nanufa, nadauko lemo da kofuna, nace masa muje
Ina gaba Yana bina abaya

Bayan munzauna nazuba masa lemon namiqa masa, maimakon ya karba saiya hada hannun ta da cup din yariqe gaba daya

Kaina na sunkuyar qasa, yace "matsoraciyar Mota"
kawai, inajinsa nayi Shiru
Sakin hannun yayi, ya ajiye lemon batare dayasha ba
Yace "kiyi hakuri feenah, nasan nayi Miki laifi, nafadawa su Abba da daddy Cewa mun daidaita tsakaninmu Bayan bahaka bane, kiyi hakuri Dan Allah kinji?"

Kaina nadaga alamar to
Yace "kin hakura?"
Sake daga Kaina nayi
Nace "Bari in koma Ciki, nagaji dayawa zan kwanta,"
Ina fadar haka namiqe nafara tafiya

Kawai jinayi anfuzgoni, Har munajin hucin numfashin juna, ido nazuba masa, Shima haka, yace "nafeesa meyasa kike San wahalar Dani Wai?
Narasa yanda zanyi Miki bayani ki fahinceni
, feenah inasanki, Ina sanki, Ina sanki feenah"

Abin mamaki hawaye kawai nagani Yana zuba a idonsa
Hannuna yaja yadora Akan kirjinsa saitin zuciyarsa, yace "kinji yanda zuciyata take bugawa a dalilin kaunarki, nafuskanci wahala feenah, a dalilin sonki hawan jini ne yakamani feenah, banda ciwon zuciya Shima dayake gab da kamani
Dan Allah naroqeki kiyi hakuri kiyafemin feenah"

Durqusawa yayi agabana
Tare da kama Hannayena duka biyun yace "please! Please!! My feenah"

Yana Magana hawaye Yana zuba a idanunsa, wani kukane ya kufcemin, dasauri yatashi tsaye Yace
" shikkenan yi hakuri nadena, Bazan sakeba kinji"
Hannu yasa zai sharemin hawayena
Banyi wata wataba nafada jikinsa ina cigaba da kukana
Bayana yafara bugawa alamar rarrashi Yace
" shikkenan yi Shiru banasan kukanki"
Dagowa nayi ga hawaye a fuskata dukan wasa Nakai masa a kirjinsa, nace "kaiko? Meyasa? Meyasa zakasa murabu?"

Shima cikin kukan Yace
" kiyi hakuri kinji nadena Bazan sakeba"
Sake rungumeshi nayi, babu gardama Shima ya rungume abarsa 🤣

Tsawon minti biyar suka dauka ahaka, itace tafara kokarin janye jikinta, cikin rada yaqara rungume ta Yace "please!!!"

Tsayawa tayi, tareda lumshe idonta, Shima Hakan yake awajansa, jinsa yake Kamar ba'a duniyar ba, baiqi ace sun dauwama ahakaba
Dataga Abin nasa ba sarki Sai Allah 🤣Hakan yasa taqwace kanta cikin sauri
Sakinta yayi, Amma still hannunta Yana cikin nasa, Yace "my feenah thank you"
Murmushi nayi masa kawai, yace "mekuke shiryawa ne? Medame kukesanyi Kuma nawa kike ganin zai isheku?" Nace "katambayi Zahra, zansa takiraka," yace "Ok"

Shiru ne yabiyo baya kawai muna kallan junanmu Kamar za'a sace dayanmu, Hakan yasa Nace

"My Ahmad"
na'am "my feenah,"

"kayimin alqawarin bazaka sake gudunaba"

Cikin rada Yace "Har abada
Bazan sake tunanin aikata abinda zai rabamu ba,"
kema kiyimin
Babu kunya nace "nayima"

Hannu na yakama yasanya min zobe Mai kyau da harafin A'N ajiki
Hannun nakalla yayi kyau sosai
Wani zobe yasake bani tareda miqomin hannun sa
Sanya masa nayi, yayi masa kyau sosai, shikuma ansa Harafin N'A ajiki
"Kiyi alqawarin barina acikin zuciyarki, Nima nayi alqawarin haka"

Daga masa Kai nayi alamar nayi masa

Matso da fuskarsa yayi dab da tawa, cikin rada Yace "kinyi alqawari?"
Nace" nayima my Ahmad"

Ahankali yaturo bakinsa daidai nawa ganin abinda yake shirin yi yasa na lumshe idona

Gyaran muryar da mukaji ne yasa cikin sauri muka kalli kofa

Yaya Tahir!!! Nafadi haka cikin zuciyata, aikuwa da gudu nayi cikin gida

Ahmad kuwa Sosa qeyarsa yayi, Yakalli agogon sa qirar Gucci dake daure a tsintsiyar hannunsa yace "ashe Har lokaci yaja haka
Bari intafi"

Tahir yace "Dan renin wayo, kazo kasamin qanwa agaba kana so kakoya Mata rashin kunya, wannan kuwa idan mukai muku auren zamu Iya zuwa gidanku?"

Ahmad yace "besty saida safe"

Tahir yace "ai baka isa ka tankaba, oh ni Tahir qarshan duniya yazo," 🤣

Ahmad yace "Tahir ya isheka haka Dan Allah"

Tahir yace "au Har kanada bakin Magana?"

Sunkuyar da kansa yayi Yana murmushi zai fice, Tahir yace " to Sai yaushe?"

Yace "ba Rana abokina, bazan dawoba, saboda idan nacika zuwa za'a samu matsala,"
Yana fadar haka yayi wuf yafice

Tahir yace "daka tsaya ai"

yanunashi da hannu yace wannan, wannan mutumin Ina tausayawa wannan yarinyar

Ina zuwa dakin danake nafada Kan gado, na lumshe idona, afili Nace "I luv u Ahmad"
Dakin husna naje tana shirin tafiya wajan mijinta Nace mata "saida safe," tace "to Sai Allah yakaimu," futowar dazanyi nahadu da Yaya Tahir, aikuwa kaina aqasa nawuceshi, ban yarda munhada idoba, shine de Yace "amarya saida safe," nikam babu bakin Magana

Har bacci yafara daukana naji qaran wayata, Ina dubawa Naga number Ahmad, cikin muryar bacci nadauka Yace "natasheki kina bacci kiyi hakuri," Nace "babu komai"

"Dama Kira nayi ince Miki I luv u kafin nakwanta," 🤣
Nace "to ngd"
Yace "me kikace? Ai baki isaba saikin fadamin Nima"
Cikin muryar shagwaba Nace "Kai Yaya Dan Allah, kanasani Jin kunya fa, gashi Nan Kasa Sai kunyar Yaya Tahir nakeji,"

Ina jiyo murmushin sa Yace "tokiyi hakuri, shikuma Tahir Ai nayi masa Magana babu abinda zaice Miki kinji?
Amma kiyi hakuri bazan sakeba"

Nace "toshikkenan, saida safe," Yace "um um nide Sai kin fadamin"

Ahankali Nace " I luv u too"
Dif nakashe wayar

** *** **

Gyara sosai nakesha, Ciki da waje, banda magunguna danake amfani dasu, na tsugunno daban na wanka daban, fatata tasauya duka, naqara fari, nayi kyau sosai, jikina banda laushi da tashin qamshi babu abinda yake, gashin Kaina kansa qamshin dayake na dabanne, babu abinda zance da husna Saide Allah yabiyata,

biki yarage saura Kwana hudu muka taho nida husna da Zahra, Amma su anty za maimuna su Kala su kaka sundade Azaria

** *** **
Rana Bata qarya

Ayaune dubban jama'ah suka shaida daurin auren Ahmad muhd marzuq Tare da nafeesa mu'az Akan sadaki nera dubu tamanin lakadan ba ajalan ba, Wanda manya manyan Yan siyasa suka halarta, cikinsu harda gwamnonin wasu jihohin

bakin Ahmad Kamar gonar auduga, yayinda suka hade cikin farar shadda, tareda babbar Riga, agogo fari qirar Rolex, farar hula me sirkin ash, sunyi mugu mugun kyau irin na qarshe din Nan

Kawai pictures suke tayi shida abokansa, banda masu video dasuke nasu, cikin su harda Yan gidan TV, domin sunaso su haska bikin akafafen Yada labarai









Mrs usman ce🖊
[5/4, 6:08 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

Second to the last page


64


Abba gaba daya Yama rasa inda zaisa baqi wasu daga kusa wasu daga nesa
Tahir Yana fama danasa jama'ar Ahmad haka
Ana gama daurin aure, jama'ah suka fara raguwa
Kansa ne yafara sarawa saboda hayaniyar datayi yawa
Nan da Nan yace "muhd yakamata mudau hanya kokuwa?
Ina su wadannan yaran suke?"
Marzuq ne ke wannan maganar, tsoho Mai ran karfe
Daddy yace "to abbey, Bari akirasu"
Awannan lokcin suna cikin gidan tareda abokansu, suna gaida mama da danginta, duk inda sukayi Sai an kallesu, saide idan Kun gaisa ne, zakaji Ana cewa Ina angonne, shikuwa banda waige babu abinda yake Wai kozai danga matar tasa
Suna futowa daddy yahango Tahir

Dan haka yayi masa Magana Akan yakamata su tafi Tahir yace "daddy Bari inkirashi"
Wajan Ahmad yatafi Wanda yatsaya ake tayi musu pictures shida mutane, babbar Riga Sai tashi Sama take,🤣 Tahir yace " Kai to wallahi mutafi, daddy da wancan tsohon suna jira"
Ahmad yace" yaza'ai natafi Tahir Bayan banga matata ba "
Tahir yace" yau munga ta kanmu, daga daura auren,?" Yace" Tahir bafa zan tafi ba saina ganta"

Nikuwa Ina zaune tareda qawayena dasu aysha, Zahra, dawasu daga cikin Yan unguwa, wayata ce tadau qara, Ina dubawa Naga Ahmad ne, Kai tsaye Ina picking cewa yayi zasu tafi infuto mu gaisa
Aikuwa nazaro mayafina nafuto, Ina zuwa kofa muka hadu da husna tace "Ina zakije," nayi Mata bayani, tace babu inda zakije, kikirashi kifada masa yayi hakuri

Nikuwa ba musu najuya, "feenah "
Takira sunana, Ina juyawa tayimin nuni da dakin Abba tace kije can dakin kikirashi
Saida taga nashige dakin sannan tatafi cikin ranta tana fadin badai mutanan su Tahir bane, tasan Sarai ba hakuri,🤣 musanman ma Ahmad yanda yake wannan rawar kafar
Nikuwa Ina kiranshi yafara fadin, "kina dede Ina?" 🤣

Nace "Yaya anty husna tace bazan zoba, kayi hakuri Yaya tunda ai anjima zamu hadu ko"

, 🤦🏻‍♂dafe kansa yayi da hannunsa yace " my feenah yanzu kowama haka yake ganina ko?" Nace "kamarya?"

"To my feenah gashinan Bana Iya boye soyaiyar danake Miki agaban mutane, ai duk laifinki ne kekika maidani haka"

Nace "Yaya kabani Daria" , yace "tobani abata"

"Yaushe zaku tafi?"

"Yanzu zamu tafi tunda anhanani ganinki" , Tahir yaduba yace " muje Tahir"

Tacikin wayar naji Yana masa Magana, Nace "Wai tare kuke,"

Yace "emana, menene?" Nace "kaiiii"
tare da zare Ido, dif nakashe wayar
Wayar ya kallah Yana murmushi yace "su Tahir manya Wai Kai akejin kunya"
Tahir yace "to menene kana mamaki?"
Yace "no bawani mamaki kawai de Naga kunyar marar kunya ai bata lokaci ne" 🤣

"Kacika baki dayawa yaro"
Inji Tahir
Ahmad yace "yaro Kuma? Yaro de? Yanzu nine yaro? Zakayi mamaki na"

Tahir yace "kamarya?" Shima Ahmad din yace " a a abar zancen"

"Ina kuka tsayane tun dazu ku ake jira,"

"kayi hakuri daddy" inji Ahmad
Mota suka shiga inda su daddy suka sake yin sallama da Abba dasu ammu sannan suka tafi

Mukuwa muka ci gaba da hidimar biki, photuna de anyi su selfie kuwa ba'a Magana
Inyi wannan shiga incire asake wannan, ko Ina zani Ina tare da Zahra
Anyi kidan qwarya, inda su Kala suka taka tasu rawar

Da magrib aka fara shirin kaini kano, kuka de Kam nashashi dakyar aka rabani da jikin mama
Shikansa Abba saida yayi qwallah
Ammu ne yadaukemu
Har mukaje kano
Gidansu Ahmad mukaje nide kaina Yana qasa, dazamu shiga yace inshiga da Bismillah haka kuwa a kayi

Saida ammu yakaini Har dakina Wanda yaji furnitures na gasken gaske, sannan yaqaramin fada Shima yatafi

Ina hawaye husna dasu aysha da Zahra ne suketa ban baki
Kala ce tareda wasu Mata tace nataso muje part din su hajia
Aikuwa haka akayi
Muna zuwa su momy suka karbemu hannu biyu, mamy hakima kuwa janyoni tayi jikinta, Sai Nan Nan take Dani
Saudat kuwa takama hannu na tariqe, su kalatynmu suna ganin wannan tarbar da aka mana, sukace tosu zasu tafi, saikuma gobe idan sunzo dinner insha Allah
Dahaka suka tafi gaba dayansu, Ina riqo Zahra tana fizgewa

Dagani saisu momy saikuma baqi Wanda sukazo bikin dasuke ta tururuwar zuwa wajena
Dansu ganni
Mamy hakima tace "hajia inaga wannan suje daki ko, Kota samu tahuta"

Momy tace "eh Hakanma yayi," tadubi Saudat tace
" sauda kuje daki tayi wanka taci abinci saita kwanta tahuta"
Saudat tace" to momy "
Kaina aqasa muka tafi, Wai nice a cikin Gidansu Ahmad, amatsayin matarsa, babu nacin da saudat batamin ba, Akan nazo tun muna diploma naqi zuwa, Amma yanzu gashi nazo amatsayin surukarsu

Husna nafita harabar gidan takira Tahir tace
" sweety kazo kadaukeni," alokcin suna tare da Ahmad Yana masa naci su tashi su rakashi wajan matarsa

Tahir yaceda husna "wai harkun gama ne?"

"Eh mungama"

"Amma kina ganin babu damuwa kubarta ita kadai?"
"No ba ita kadai bace, tana wajansu momy," Tahir Yace" eh hakanma yayi, gani nan zuwa "

Yadubi Ahmad Yace" to ango muje nakaika gida, Nima zan dauko maman twins"
Ahmad Yace " yauwa dama namatsu naje wajan matata," Tahir Yace "tome mata, ai tana wajansu momy, saide kabita can,"
Ahmad Yace "kamarya bangane ba? Menene amfanin namu part din?"
Tahir Yace " to saide Nakai ka katambayi su momyn" 🤣

"Dan Allah Tahir Kadena batamin Raina, haba Dame zanji, danaka ko danasu"
Kafadarsa yadafa Yace
" man kayi hakuri
Matarka cefa, nasan cewa koma menene yafaru yanzu tana matsayin matarka ne, kawai idan munje kaje kadauketa saiku koma part dinku ai shikkenan"
Ajiyar zuciya yasauke Yace "shikkenan"

Suna zuwa gidan Tahir yarakashi ciki, daganan yadauki Husna, shikuma yayi part dinsa
Yana zuwa kuwa yanda yazata din hakane, Bata nan, Amma da alamun anshigo part din, koma menene zaije wajansu momyn ai yanzu
Kan gadon yadafa yarufe idonsa, daga bisani yatashi yashige toilet domin watsa ruwa

Saudat tace "sister gaskya wannan kunyar ta isa haka, kunaso Kuna wani noqewa," mayafin kaina nayaye nace
" jarababbiya, Ina ruwanki,"
kaina tafado tace "sister amarya,"

"wash Saudat Zaki karyawa mijina ni"
Tace "lalle amarya, yaude gaki a gidan nan, sister Kinga yanda kika koma kuwa? Wallahi kin qara kyau," nace "kema haka ai, kin girma"


"Eh lalle ma feenah nice nagirma ko ''
Nace" Ina farouq," tace
" Yana nan wallahi, ai zaku gaisa kafin mutafi "

Wanka nashiga, nashirya cikin kayan bacci nakwanta, nan da nan bacci yayi awon gaba Dani
, Saudat taja bargo tarufeni, sannan itama tafice

Wajan 11:30 yashigo part din, duk baqi sun kwanta, kasancewar sanyin da akeyi
Momy yagani afalo tana bawa ma'aikata umarni, domin su gyara gidan sosai kafin safiya

Da mamaki ta kalleshi tace "bakayi bacci bane dama?" Kansa ya Sosa Yace cam momy dama inajin yunwa ne, ko Zaki sa akawomin abinci? "
Tace" OK,"
Mai aiki ta qwalawa Kira, Yace"a a Barta momy kawai Bari in kwanta," tace "kace yunwa kakeji ka tsaya mana takawoma abincin," 🤣

Yace "to momy Ina Saudat, ko yaran gidan, kokuma...."
Tace "kokuma me? Kaga walady banasan shirme, wuce kaje ka kwanta dare yayi"

cikin shagwaba
Yace "momy Ina nafeesa?"
Kai tsaye tace "tajima da bacci, tace afadama saida safe" 🤣

Babu yanda ya Iya, haka yajuya Yana shafa qeyarsa, Yana waiwayen falon yayi part dinsa
Cikin bacin rai yake fadin mutum da matarsa Amma ahanashi ganinta, wannan wacce irin rayuwa ce
Yana tafiya Yana mita dahaka yaqarasa part dinsa, a wannan dare dakyar bacci barawo yasace Ahmad


** *** **

Yana zaune adakinsa yaharde Yana kallon tashar arewa 24 Kamar wasa yaga photon ta
Tuni yatashi zaune, abin Bai qara daure masa Kai ba saida yaganta tare da mijinta Ahmad muhd marzuq
Mekenan? Meyake shirin faruwa ne? Yaushe haka tafaru? Feenah ta auri Dan gidan Dan siyasa, Kenan dana Rabata da mukhtar masu qasar ta aura
Ato masu qasar mana Dan gidan deputy governor, gobe Kuma ai Dan gidan governor ne, gashi Yaron yaji Ana shi Kansa Mai kudi ne, Bayan babansa, ga kakansa dayake ji dashi

Lalle kuwa Idan hakane ya zalunci mukhtar, gashi yanzu yarabashi da feenah, shi yahanashi aurenta, Shima Kuma Bai same taba
Gashin Kansa ya hargitsa, ya ilahi, yayi zatan tunda yarabata da mukhtar dole zata hakura idan yakoma wajanta ta saurareshi, ashe shi cutarsu yayi gaba daya
Lalle dole yanemi yafiyar mukhtar


** *** **

Washe Gari
Ina tashi Wanka nayi, Ina futowa Naga Mai kwalliya tana jirana, zama nayi aka tsaramin kwalliya tagani tafada, sosai nayi kyau acikin material Mai shegen kyau launin ash color
Mamy hakima ce dakanta tazo tatafi Dani wani falo, tsararre, daddy da momy da marzuq suna zaune kaina aqasa nagaida su, kowa Sai Jana yake da fira, nide cikin kunya nake amsa musu maganarsu

Marzuq Yace "Toya kwanan baqunta" nace
" alhmdlh,"
Yace "kinajin dadi ai babu wata damuwa ko?" Nace "babu komai wallahi"

"Amma baki ganeniba?" Nace "ehh,"
"to nine marzuq" 🤣

Kallansa nayi da mamaki yanda naji hausa radau abakinsa, murmushi nasaki batare danace komai ba
Yace " to alhmdlh, Zaki tashi kuje unguwa yanzu zaku dawo"
Babu musu natashi muka tafi, bamu zame ko inaba Sai wajan passport muna tsaye yafuto aka bamu, wajan visa aka wuce Dani dayake Abu ne nakudi Yace zuwa anjima za'a kawo Har gida

Yayi mamakin lokcin daya dauka Yana bacci, ahanzarce yashirya yafuto yayi kyau cikin manyan Kaya
Sai sauri yake yazo yaga feenah, Yana futowa directly Dakin daddy yayi domin su gaisa, Yana zuwa kuwa yagansu gaba dayansu, suna gaisawa yakoma wajan marzuq
Daddy Yace "my son abeey yasa akai nafeesa wajan passport, yanaso gobe kushirya ku tafi sharil'asal (honeymoon)"

"To daddy itadawa suka tafi,* daddy Yace" itada Saudat da driver "
Cikin ransa Yace" driver"

Wato dawani qato aka hada amaryarsa suka fita, Bayan shi jiya babu yanda baiyi ba aka hanashi ganinta

Baiyi musu maganaba, Har suka qari firarsu suka gama

Da yamma aka shirya kowa yafara haramar tafiya wajan dinner
Nayi kyau sosai cikin yadi Mai tsada launin pink
Nasha kwalliya sosai nayi kyau, Ina Bayan Mota Ina jiran Ahmad yafuto, Yana shigowa driver yaja motor muka tafi, Har mukai Nisa baicemin komai ba, nice nayi qarfin halin cewa
" Yaya Ina yini?"
"lafiya"
Shine kawai abinda Yace
Cikin Raina nace tooo yau abin yazo
Ban daddara ba nasa hannu na naruqo nasa, shiru Yamin Yana Jina,
Taushin hannun ta neyake ingizashi Akan yadan murza hannun
Amma haka ya dake, yaqi kulata
😀
Har sukaje wajan dinner, Prince and Princess dake rijiyar zaki
Sosai an qawata wajan
Duk abinda kake buqata da kanka zakaje kazuba sosai abin ya qayatar da mutant sosai
Washe Gari akayi wata dinner a country mall, Iya

Please Login or Register in order to submit comment