Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

to yar nan waya riqeki"🤣

"haba kaka ni kenan koda yaushe saboda karatu ace baza kaga yan'uwan kaba,"
nafadi haka tare da turo bakina, "to ai sai kiyi tayi nafi" cewar kaka, "ni kaka ki dena cemin nafi"

"aikuwa nafisa nasani haka zan fada, nafisa uwar ma'azu "🤣

dafe kaina nayi da hannu na" haba kaka kuma abin harda 'bankaro sunan mahaifi,"🤣

"to ai nafada miki saboda kisan itace sa'ar yina,😃"

"hmm kaka kenan, kinga ni Yau banajin rikici kiyi tayi, ni kinga tafiya ta,"

nayi cikin daki na kwanta,

Zeey nakira itada Atu, mukasha fira, inda take cemin itama tana legal ta jigawa, Atu kuma bikinta za'a yi, anan de mukasha fira
"Nafi! Nafi!!"
Kaka ce take kwalamin kira, nace "na'am kaka ya akayi" , tace "namanta ban fada miki ba, dazu aisha tazo bakya nan, tace inkin dawo ki kirata, ita ta nemeki bata sameki ba, in kuma bakida kati ki nemeta a watsar (whatsApp)" jijjiga kai nayi wannan matar bazata sauyaba

Kwanci tashi Babu wuya awajan Allah gashi har muna shirin Gama semester farko, karatu nake Babu kama hannun yaro, musamman damuka samu interval nayin karatu, saiya kasance bana Zuwa ko'ina koda yaushe ina karatu na

Mun futo daga "imtihan" (exam) ta karshe, sauda ta dubeni tace "yanzu sisi har semester ta qare bakije gidanmu ba,"
nace "sister kemafa baki je gidan kakaba,"
tace "haba feenah karki manta bakuda yawa dagake sai kaka, nikumafa qanne na koda yaushe suna tambayata yaushe anty feenah zatazo, bini bini suna tambayarki aike kuwa kodan wannan yaran kyaje,"
nace "shknn yanzu de insha Allah nayi miki alqawarin idan Allah ya aramin lokaci idan na dawo daga hutu zanzo," tace "shikkenan idan kinje ki gaida su mama, nace" zasu ji, "
haka muka rabu cike da kaunar Juna, ita tahau saman gada, tana jiran driver nikuma nahau adedeta nayi gidan kaka

** *** **
Kaka Yau sai gida insha Allah,"

"to nafi yanzu tafiya zakiyi ki barni,"
haba kaka ta ai kamar yaune na dawo, "
tace" shikkenan, Amma ai kyaje gidan uwar taku kiyi Mata sallama ko," nace" to kaka bari intafi,"

bayan nagama shiryawa tsaf nahada kayana, sannan nayi gidansu aysha, munsha fira sosai, anan take fadamin tasamu admission na scholarship babanta ya nema Mata, kuma tayi sa'ah tasamu, yanzu haka next month Zata tafi Uganda, Amma kafin tatafi zataje zaria nace Mata ai dole, bayan mun rabu nazo gidan kaka nadau kayana, nahau adedeta yakaini tasha, Allah sarki kaka harda yar qwallarta. 🤣

** *** **

Zaune yake a part dinsa, yana falo, yazubawa katuwar plaxmar falon nasa ido, saika rantse kallan yake, Amma Gaba daya hankalinsa da tunanin sa baya tare dashi, yana tare da ita.
Ya lumshe idonsa ya Bude itande yake gani "oh ya rabbi, wannan wacce irin masifa ce" yafada abaiyane, Ace kullum yarinya ta hanani aikata komai, banda aikin tunanin ta bana tsinana komai,shiru yayi kamar wani zautacce ya zubawa p.o.p din Dakin ido
Momy tayi tambayar harta gaji, saide ya zauna a Dakin shi kadai yana faman tunanin ta, wai yanzu shida baya shiga sabgar yanmata shine soyaiya take wahalar wa haka
"ya rabbi, ukrijni fi hazihil mishkila ya Allah (ya Allah kafitar Dani daga wannan matsala) ya fada abaiyane
Wayarsa ya janyo yashiga inbox dinsa, text din da saudat ta turo masa da number ta yake nema, kasancewar akwai massages din yanmata dasuke turo masa dayawa, dakyar de yagano number, tuni yayi saving dinta,
Sake kallan Number yayi, yana murmushi dialing Number yayi, saikuma ya katse,
To ai dole ya katse, idan ya kirata meze fada Mata,? nine Ahmad sanki nake?
Gani nayi ya shafa fuskar wayarsa yana murmushi ina leqawa sainaga ansa FEENAH TAH

Wani tunanin yayi kawai sai naga yasaki murmushi, "yes haka za'ayi"
Yafada abaiyane






Mrs usman ce🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

11


Sati na daya agida, muna dakinmu nida husna, datake karatu, dayake tana shirin shiga final year ne yanzu, waya nake nida auwal, yana qara jaddada min yanda yake sona, nide ina jinsa, araina nace dama ace yanda auwal yake sona yakasance kamanninsa kamar yayan saudat ne,🤣 danaji dadi, da Babu abinda zaisa naqi shi, saide kuma shi yayansu saudat din ne, naga alamun zaiyi dagun kai, maganar auwal ce tadawo Dani daga tunanin dana fada,
"Nafeesa kina jina kuwa?"

"Eh inaji, am Dan Allah kagane, wlh nadan gaji ne, inaso in Dan huta, mayi waya "ba'aden" (latter) "

" OK to to my heart, rabin raina, gaskiya kam gara ki huta din, nima ai zanso ki huta dakyau,"

nace" ok bye,"

banjira amsarsa ba nakashe wayar.
Husna kallo na tayi gamida girgiza kai, dariya namata, nace" wallahi girgiza kanki dakyau, bana sansa yanzu har Sai kinyi aure sannan nima zai samu kaina, har in aure shi, Amma yanzu kam, ban shirya ba,"

sake girgiza kai tayi batare datace komai ba


Chatting nahau, ina fira da fan's dina, ta whatsApp, naga new number tayimin magana, sallama akamin, araina nace yanzu haka irin samarin nan ne masu Jan magana, zanyi maganin ku, nafada araina, larabci zanyiwa koma waye, bayan na amsa sallama nace "man?" (waye?)

Murmushi yayi, yarinyar nan yaga alama tanasan larabci
"ma'aki Ahmad "(kina tare da Ahmad)
Gaba nane yafadi, Ahmad, Ahmad kuma, dp natafi na duba Babu pic din mutum sai na flawer, sunansa na duba still naga ansa, hammad, nace to waye kuwa wannan tambayarsa nasake yi"

" Aiyi ahmad "? (wanne ahmad)

"AHMAD MUHD MARZUQ"

😳zaro idanuna nayi, ahmad yayan saudat fa, tome zemin me yake faruwa ne?
Tuni nakoma hausa, nace "au ashe kaine, yakake, yagida?"

Yanake, wato bazata iya cemin ina wuni Bama, to Amma ya zanyi tunda ni nake nema 🤣

" lafiya "

shine kawai abinda yace
Nakalli text din dana tura masa, Amma amsata kawai itace lafiya 🤣

Nace "masa yasu saudat da momy"


" kowa lafiya "

Nace "Ok"



Daga nan kuma kowa shiru, shi yarasa me zai ce Mata, ita kuma tana jiran taji dalilin maganar,
Ya Salam yafada aransa, yarinyar nan datasan halin dayake ciki da itace zatake yin maganar nan, yanzu haka yana kwance agadonsa Amma fillo ya janyo yarike yana kare fuskar sa dashi, kai kace itace agabansa🤣
Feenah dataga shirun yayi yawa, karshe de tace,

"
Allah yasa de lafiya?

"lafiya "

shima yabata amsa
Araina nace kaji mutum, kana yimin magana kamar namaka dole, nida bansa ka kamin magana ba

Can har Zata sauka taji ya turo Mata text

"ya labari?"

Nace masa "yana wajanku"

" mu kuma suwa "

Nace masa "ina nufin ku samari
Kokuma kai bakada labarin yacemin

" inada "

Nace" ok, "
feenah shiru shiru tanajiran taji labari, harde ta hakura Zata sauka tace masa" saida safe
Ka gaida su saudat,"

yace" tun yanzu? "nace masa" eh aina Gama abinda nake. "

yacemin " to ai nikuma banajin bacci yanzu"
Nace masa "to Allah yakawo ma"

Shi kansa saida yafada yakejin wani iri, to bayajin bacci yazata masa, kawai de saiya share,

Kujimin mutum toda tare nake kwana dakai dazaka cemin wani kai bakajin bacci yanzu hmm

"yanzu sauka zakiyi"?

Nace "meze hana koda wani Abu? "

Yace "a a"
Yasake cewa "kona hadaki da qawarki naga ni kamar bakisan magana Dani"

Nace masa "a a kyaleta dazu munyi waya ai, kabarta ta huta"

Yacemin "wanne hutu ai ba abinda take"

Nace masa "a a kyaleta de, ko gyaran Dakin da ake sasu ai yaci ace mutum ya huta, kullum mutum yana cikin gyara"

Murmushi yayi, wato saudat tabata labari kenan, yace "bawani gajiya"

Nace "yakamata de ka dinga barinta tana hutawa kodan tasamu sukunin yin assignment"

"haka kike so? "

Nace "eh"

"angama gimbiya "

Juya idanuna nayi kamar yana yana ganina afili na furta gimbiya kuma

Husna ta juyo ta kalleni," Ana luv dinne yar luv," nace "a a," tabe baki tayi taci Gaba da karatu abinta

Nikuma nace masa " to saida safe bye,"

" ki kulamin da kanki,pls "

Araina nace wannan gayen ba kalau yake ba

Nide nace masa" ok"

Wait yace, natura masa da alamar quation mark "?"
Yacemin ni bazaki cemin in kula miki da kaina ba?





Mrs usman ce🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family



12




Dafe kaina nayi da hannu na, 🤦🏻‍♀kai wannan man din akwai damu, "toka kula da kanka,"

"no haka zaki ce inkula miki da kaina "

" saudat tacemin kai Dan gatan mom ne, nasan cewa Zata kula dakai"

"no mom daban ke daban "

Oh" ya rajil "(man) nafada araina

" Toka kulamin da kanka,"

banjira amsar saba nakashe data na, nasauka

Shi kam mutumin ku, murmushi ne saman fuskar sa, ya maimaita chting din nan yafi sau biyar, kissing din chting din yayi, yanayin back, mezai gani?
Text ne rututu akayi ta turo masa, shi bema luraba, shide yasan yanajin qaran shigowar text din
Dayawa daga cikin text din na yanmata ne, kowa yana tururuwar yimasa magana, wai Yau shine online, abinda ba wani hawa yake ba
Tabe bakinsa yayi gamida kashe datarsa, yayi addu'ah ya kwanta, ba tare daya duba saqon nin da aka turo masaba


** *** **

Dariya suke sosai, kaida ganinsu kasan sunajin dadin firar tasu"
Wallahi hajiya ingaya miki haka mukai da ita,"

mamy hakima tace" ai wallahi kin kyauta, kinsan hajiya Asma'u akwai ta da wayo "

Falon ya shigo fuskar sa dauke da murmushi, shi kansa Yau yana jinsa asama, tun jiya saide kaga shi kadai yana sakin murmushi, kamar sabon kamu, 🤣kuma duk ta dalilin ta ne, yadubi step mom dinsa," mamy ina abinci na?"

Hada ido sukai itada momy, Yau ahmad ne mai neman abinci?
Momy ce ta bashi amsa, "da mu muke tashi muje mu dauko ma? Bakasan dining dinba ne?"

Murmushi yasaki, dimple dinsa suka lotsa, yana susar kai yayi hanyar dining
Mamy hakima kuwa kasa yin shiru tayi, saida ta tanka

"Dan mamy kode kode? "
Juyowa yayi "mamy kode me?"

" kode surukar tamu ta amince ne mu tura"? Irin wannan walwala haka

Sosa kai yayi, cike da shagwaba kamar wani qaramin yaro yace "kai mamy abinda bata sona ma?"
Zaro ido momy tayi😳," wai da gske ne abinda kunnuwa na, sukeji hajiya?
Wacece?
Gaskiya kakawo mana ita mu ganta"

Mamy hakima tace" Gaskiya kam, yakamata mu ganta, Amma wannan yarinya ko wayece tayi sa'ah "

"wayyo mamy, yayi wuf hanyar dining "

Awannan ranar ahmad yahau chatting kusan sau shida, Amma abin mamaki banda text na group dana yanmata Babu abinda yake, wanda shi kuma baida lokacin su
Harya gaji yana tunanin ma bazata hau ba kawai saiya ganta online alokacin kusan goma na dare
" yes" yafada da karfi kamar wani tababbe, shi kansa yana mamakin kansa, wai shine yake San mace har haka, abinda bai taba faruwa dashi ba, murmushi yasaki, daya hangosu a idon zuciyar sa, gasunan awani waje harda yaransu, kai Gaskiya dole ya seta kansa awajan yarinyar nan, saboda yanajin Santa aransa, a koda yaushe qaruwa Santa yake aransa, kamar yadda yake shaqar numfashi, haka Santa yake qaruwa aransa

Yauma a chting din bai barta ta hutaba, saida ya isheta, kullum hakane yake kasancewa, atsakanin su, har yanajin Yau idan bai ganta ba bayajin zai samu nutsuwa aransa

Da yamma, ya shirya cikin wani yadi light blue, yasaka hula baqa, takalmi baqi gamida baqin agogo kirar Rolex, falo yasauko sai zuba kamshin turaren Ahlamul Arab yake, duk ya Bude Falon da qamshi,

Saudat yasamu afalo sai rabon fada take tsakanin maryam da bukhari da Muslim, Akan game, yana saukowa aka fara kawo masa qara, yace" ku banda lokacin ku, akwai inda zani,"
maryam yaja gefe yayi Mata rada akunne, aikuwa tuni ta saki murmushi ga hawaye shabe shabe a fuskar, tayi sama da gudu abinta

" Ke tashi ki rakani,"

yafadawa saudat, to yaya, mayafi ta janyo ta yafa, saida suka futo harabar gidan taga de ba shida niyyar fada Mata inda zasuje, tace "yaya ina zamu ne?

Yace" aike zan tambaya,"
tace" kamar ya? "

Yace" to nima ina nasan wajan, gidansu wannan yarinyar zaki rakani, "🙈

Tace." oh wai binta, Allah sarki, jiyama saida tazo nemanka, Allah sarki yaya ashe kun dedeta,😃 wallahi dama nasan mahakurci mawadaci, ta Dade tana sanka baiwar Allah, ashe wannan ranar zatazo 🤣"

Cike da tsawa wadda ita kanta tayi mamaki, yace "ke dallah kiyiwa mutane shiru kinbi kin wani cikawa mutane kunne da wata binta binta"

"Wannan yarinyar qawar kin nan, mene sunanta?"

Saudat tace "oh wai feenah?"

"eh" yabata amsa kamar bayaso,
"To ai yaya dare yayi,"

Yace "dare yayi "kaif ya'ani" (kamar yaya) "

" To yanzu yaya karfe hudu ne da rabi, tayaya zamu dau hanyar zaria? Yaushe mukaje muka dawo? "

Kallanta yayi sosai yace" zaria kamar yaya? "

" Yaya feenah yar zaria ce, nan din agidan kakarsu take, kuma tun da mukai hutu aranar tatafi gida hutu, ai nan kawai karatu take, Amma da munyi hutu can take tafiya, "

"ok" kawai yace,

Ita kuma tayi gida, ta dinga dariya, oh su yaya, da anci kwalliya za'a je zance, ko ya yake yi idan yaje zancen, wannan baqin rai nasa, hmm wallahi sister zan gamu dake, ashe soyaiyarku kukeyi a gefe, bansani ba, ko tayaya suka hadu oho musu!




Mrs usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

13


"Yasalam,"

shine kawai abinda ahmad ya furta, wayarsa ya janyo yakira tahir, number busy
Mtw tsaki yaja, yanzu haka yana can yana waya da wannan yarinyar ya wani liqe Mata kamar gam,
Yana tunanin yankewa kanshi mafita, yaji Kiran tahir din,

"yakai, kana gida ne?"

"Yes ina nan, ya akayi?"

"No gani nan Zuwa kawai,"


"OK" inji tahir

** *** **

"Abokina yade naganka cikin damuwa, waya tabamin kai ne?" Dagowa yayi ya zubawa abokin nasa ido, shi dinma duk yafada, yara me,

"tahir me yake damunka? "
"soyaiya

iklima tanamin yawo da hankali, narasa gane kanta, ga ummi koda yaushe tanamin magana Akan aure, tace min tana so taga yan dagwai dagwai suna yawo agabanta,"

ahmad kwashewa yayi da dariya, "wai yan dagwai dagwai, to kai kayi auren mana, kawai kazabi wata acikin babies din da suke binka, kufa likitoci Ana sanku, yanda yan Mata suke rububinku,"
yafada cikeda zola ya, tahir yakai masa duka ya kauce

"Kai bance yanmata suna binka ba saini, ni ai zuciyata nariga na yiwa iklima kyautarta,"

"Gaskiya ne" inji ahmad "kaji masoya"

"No bazaka ganeba ahmad dande Babu wadda tayi sa'ah ka budewa zuciyarka ta shiga shiyasa zaka ce haka"

"Hmm tahir kenan, da kasani, Amma ita wannan bata nemi iznina Bama ta Bude zuciyar ta shiga ciki tayi bake bake," 🤣

tahir yace "serious ahmad"


"Serious abokina, wlh ban taba Jin so yamin mugun kamu kamar yanda na yarinyar nan yakamani ba"

Tahir yace," pls abokina wacece Dan Allah"

"Zinariya," inji ahmad,

" kamar ya, haka ne sunanta?"

Ahmad yace "inaaa ina nufin Zinariya acikin Mata, yarinyar tayi, akwai sura me kyau wallahi, saide Amma fa yarinya ce Gaskiya, bansani ba ko Zata iya daukar nauyina, sa'ar saudat ce, kuma qawarta"

Tahir dayayi sakare yana kallan abokin nasa, yace" kuma sa'ar saudat dince yarinya?"

" Emana to nima shekara nawa nabawa saudat din? "
Tahir yace" karka ce haka, ai Mata bahaka suke ba, sai kaga kana renasu wallahi sun baka mamaki a karshe "

" to ai shknn "inji ahmad, sannan yasake cewa

" Allah yabani ke my feenah "

" Gaskiya abokina ka shiga dayawa,"

" wallahi sosai," inji ahmad

" Am kagane tahir, kawai kayi hakuri da halin iklima, wataran komai zai wuce, kuyi magana da ita ta fahimta, idan batayi kawai kasamu wata, idan kuma tana yi dakai, kawai ta ajiye wani Jan aji, tabada kai bori yahau, ko muma masamu yan dagwai dagwai"

Tahir dariya yasaki "wato nabaka sara ko? Hmm qilama kai saika rigani samun su, tunda naga da gske kakesan wannan yarinyar"

Ahmad yace "gsky kam, aini kasan ba jira, tana Zuwa Zata samu"

Zaro ido 😳tahir yayi, "Zata samu me?"


** *** **

Washe gari sunacin abinci, kowa yayi shiru kawai abincin su, sukeci, ahmad yadubi saudat yace Mata," yaushe zaku koma school,?"
Kafin ta bashi amsa, Muslim yace,
"yaya tun rannan kake tambayar ta kode kaima school dinsu zaka shiga?"

Maryam ce tace, "yauwa yaya na tuno, infada?"

Shi ahmad shaf Yama manta yayi wani magana da yarinyar,kai tsaye yace" auta fadi mana,"

tace" yaya kace zaka kaini wajan anty tun waccan ranar Amma har yanzu baka kaini ba,"

bukhari yace" haba?" Wai haka yaya? Wallahi muma sai munje ko Muslim,"

"eh wlh" inji Muslim daya cika bakinsa da chips 🤣

Cikin tsawa yace musu" wai ba anhanaku yin surutu idan Kuna cin abinci ba? "🤣

Tsit kakeji kowa yadawo taitayinsa

Saudat ce a hankali tace" saura kwana biyar, wai ita nan babba, 🤣

itama da harara yabita
Su kuwa su momy mamaki suke, kayi tambaya anbaka amsa, Amma kana ta harara,🤣 shide daddy yanajinsu yana murmushi bai sa musu bakiba

Shima gogan naku, shiru yayi, saide yayi alkawarin yadena sirri da Maryam,🤒 haka yatashi yadau tissue yana goge bakinsa, ya fita yanata faman harare harare😊


** *** **

Akwana atashi gashi har mun dawo hutu, munci Gaba da karatu cikin nasara, aranar da muka fara "muhadara" (lecture) saudat tayimin tas
"Yanzu dama sister soyaiya kuke keda yaya, Amma shine ko naji labari?"

"Soyaiya,? soyaiya fa kika ce sauda
Shine yafada miki muna soyaiya?"

"a a ni bai fadamin Ba alama nagani kawai "

"Nace Mata to nide wlh bamuyi wannan mgnr ba," saudat ta cika da mamaki tace "Amma fa koda yaushe tambayata yake yaushe zamu dawo hutu yaushe zamu dawo?"

Dariya nayi nace "wlh Bama wata soyaiya kawai de muna gaisawa a chting, shima bansan waya bashi number naba"

Saudat tace "harfa cewa yayi inrakashi gidanku"

Zaro ido feenah tayi tace" gidanmu? Wlh da baba aure zaimin shikkenan, 🤣dama ga auwal shima yadameni "

Tace" to koma de menene idan tayi tsami maji, "
nace" hmm sauda kenan, Babu abinda zaki ji sai.... Kafin na qarasa tayi karaf tace "sai soyaiya"

Nace "saudat banda abinki, inani ina yayanki, Dan gayu yafi karfina, sannan ni bamu taba haduwa dashi Bama fa"

Saudat hararata tayi tace," wlh nikuma kinga ban taba ganin wadanda suka dace da junaba kamar ku, kuma kina cewa Baku taba haduwa ba, ranar da muka kaiki gida fa
Ina kallan ku ai, sai wani kallan Juna kuke Kuna basarwa
Har kikasa Dan bawan Allah yakusa zubar damu
Wlh feenah yaya yana sonki, pls idan yazo miki da maganar karkiyi rejecting dinsa, feenah ina sanki a family din MARZUQ
Duk fa yan gida sunsan yaya yafara soyaiya, ke karshe ma har cewa yayi zai kawo miki auta "
Anan tabani labarin baran baramar da Maryam tayi masa,
ni abin ma saiya bani dariya🤣

Ahaka de muka rabu, muna masu farinciki


** *** **


Da daddare bayan nagama komai, ina chting nida husna, tana bani labarin practical dinsu da aka turasu, kuma Ana turo musu manyan doctors suna qara yi musu bayani da wayar musu da kai Akan wasu ciwukan
Anan nake qara Mata qwarin gwiwa takara dagewa, Allah kuma yabasu sa'ah

Shigowar text din ahmad dana gani ne yasa nasaki murmushi, ni kaina Zuwa yanzu nasan cewa ahmad yatafi da tunani na, inajin sansa araina sosai

Sallama yayimin na'amsa masa, "feenah"

"Na'am yaya"

"Ashe bakiyi bacci ba,"

nace masa "um, banajin bacci,"

"to ko inzo intayaki fira?"

Nace " nabaka dama yaya"

yace "are u serious?"

Nace "eh,"

"to idan nazo me zaki bani?"

Gabana ne yafadi nace me ahmad yake nufi?
Kawai sai nace bari naga gudun ruwansa, sainace masa, "duk abinda kake so,"
saiyace "um um fa, abinda nakeso babba ne" , nace "kamar me kenan?" Gabana yana ci Gaba da faduwa

Yace " idan nafada kinyi alkawarin zaki bani?"

Nace masa "insha Allah"

Yace "I LUV YOU FEENAH
inaso ki mallakamin zuciyarki"

Zaro ido nayi 😳gabana yana faduwa.



(nide nace to feenah, gashi de kinyi alkawari)




Mrs usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family


14



Karfe goma sha biyu na dare, yana kwance adakinsa, haka itama daga bangarenta, suna maqale da waya akunnan su.
"Kinga nide ba qaramin yaro bane, yakamata mu tsaida magana daya atsakanin mu, kema kinsan nadade ina kaunar ki, tun lokacin dana fara dora idanuna akanki, koda yaushe banada nutsuwa kullum cikin tunanin ki nake, zuciyata ta nesanta da abinda take so, ki temaka ki kasance agareni tun kafin zuciyata taqara afkawa acikin damuwa,
Aduk lokacin dana zauna adaki ni kadai ina tunani Akan soyaiyar mu, saina dinga hasashen cewa dama ace inada fiffike tamkar tsuntsu, ta yanda zan iya daukarki inkai ki qayatacciyar fadar datake can babban birnin masoya, domin sada ki da kujerar alfarma, ta muqamin sarauniyar yanmatan duniya, dana Dade da baki,
Wallahi soyaiyar ki, tana neman ta zautani, pls pls maimuna yakamata ki bani dama inturo magaba tana domin ayi maganar auren mu "

Gaba daya yagama kashe Mata jiki da kalamansa, yaushe zatayi sakaci ta rasa Ammu, yanda yake Mata wannan soyaiya, idanun ta a lumshe, tace "nabaka"

"Me kenan maimuna?"

"Nabaka dama ka turo, iyayena sun Dade da sanar Dani cewa idan nasamu mijin daya kwantamin zan iya turoshi domin suyi bincike akansa,"

"Da gaske kike farin cikina?"

"Serious abin alfahrina"

"Gaskiya naji dadi nagode, zanyiwa yaya magana Yau, duk yanda mukai dashi zakiji,"
haka sukaci Gaba da firarsu ta masoya.

Asuba tagari maimunan Ammu.

** *** **

Dif takashe datar ta, Ahmad yana jiran amsa yaji shirun yayi yawa, kawai yana dubawa yaga wayam Babu feenah Babu alamarta, kansa ne yasara, badai yarinyar nan bata sansa ba, innalillahi, yanzu ya zaiyi, dama hakane yanzu shida yake qin wasu shine, shima ake gudunsa, bai Gama tunanin saba yaji dumi akumatunsa, hannunsa yakai wajan

"hawaye?"

Shine abinda ya furta da bakinsa, shi wallahi ko durqusa mata sai yayi, inde Zata so shin,
Agogo yakalla yaga 12:45 bai tsaya shawara da zuciyarsa ba, kawai ya kirata, saide kuma harta gama ringing bata amsaba,
Shikkenan hasashe na yazama Gaskiya,

"Nafeesa bata sona,"

yafada abaiyane,
Dama nasan tana kulani ne saboda qawarta saudat
Kwallar idonsa ya share,

"wallahi saina sake kira"🤣
yasake fada abaiyane, shi kadai adaki sai sunbatu yake

Acan bangarenta kuwa duk ta rikice, tayaya wannan Dan gayun zaice yana Santa ta yarda, anya kuwa ahmad ba yaudarar ta yake ba? Amma ace mutum mai aji, da kudi da gayu kamarsa har yana kiranta bayan kuma taga abinda yace, yanzu menene mafita, yaya zatayi dashi?
Wani bangare na zuciyarta yana masa kwadayinsa sbd ahmad yayi Babu qarya, saide wani sashen kuma yana fada Mata yafi karfinta karta jawa kanta abinda yafi karfinta itada iyayenta
Saide maganar da saudat tafada Mata data tuna da ita sai taji bazata iya kyale ahmad dinba
Amma dole zai bata lokaci tayi tunani

Wayar tasa aqasan fillo, tayi addu'ah ta kwanta, saide tana rufe idonta qarar wayarta yasake tashin ta
Hannu tasa ta dauko, tana dubawa kuwa ahmad ne, samun kanta tayi da amsawa tunda tariga ta yankewa kanta mafita,

"feenaaah"

ya kirata gamida Jan sunan nata

"Na'am yaya,"
kayi hakuri naga kiranka bana kusa da wayar ne

"a a feenah, ban yarda ba"

"feenah "
yasake Kiran sunana, na amsa

" feenah bakya sonako? "
Nace "a a"

" to meyasa kika sauka a chatting Babu amsa Babu sallama bayan ba haka kika sabar min ba?"

Nide nayi shiru inajinsa yana magana a hankali cikin nutsuwa badan dare neba nima nasan ba lalle naji komai ba
Nace "yaya bahaka bane kayi hakuri"

"Shikkenan anyi miki afwa, Amma pls yanzu fadamin yaya kike jina a zuciyarki?"

Saida nayi Jim sannan nace "kamar yanda nakejin saudat mana,"

yace "um um, niba wannan nake nufi ba, kema kinsan me nake nufi,
"Feenaaah" yasake Kiran sunana
"Na'am yaya,"

"Feenah kinaso namiki kuka?"
Nace "kuka kuma yaya,?"

"Emana tunda bakya sonaba, nafeesa tunda nake bantajin nakamu dasan wata yarinya lokaci dayaba sai akanki, pls kisoni feenah Dan Allah kinji
Yaqarasa maganar cike da shagwaba ni sai yabani mamaki ma," ganin yanda yake magana cike da shagwaba
Nace "yaya to kabani lokaci zanyi tunani,"
Yace" nide um um yanzu nakeso naji, "

nace" yaya.....

Yayi saurin tarar

Please Login or Register in order to submit comment