Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake, Amma zataga gudun ruwasa ai
Gani tayi yadauki waya yana dannawa hakan yasa ta kawar da kanta daga kallansa
Bugu daya doctor Bashir yadauka, "abokina ya fama da jama'ah,"

tahir yace "wallahi gasunan alhmdlh kullum muna fama,"

tahir yace "yauwa Bashir nikuwa Yama sunan yarinyar nan daka nunamin rannan,"

aikuwa karaf akunnan ummi tayi murmushi aranta tace ai nasan arina wai ansaci zanin mahaukaciya
Doctor Bashir yace. "yarinya kuma wacce iri,?" Tahir yace "yarinyar nan daka nunamin har sukazo suka gaida kai muna tsaye menene ma naji kace sunanta?"

Bashir sarai yaganeshi Amma da niyya yake Jan maganar, yace "kai ban gane taba gaskya ko tayi ma wani laifi ne?"

Tahir dayaji kansa yawani sara yace
"a a kaida baka gane taba tayaya kasan ko tayimin laifi, wai nazo office dinka ina fadama abinda yarinyar tayi, har na hanata shiga aji," 🤣

doctor Bashir yace "oh abokina sorry sai yanzu nagane ta husna kake nufi" 🤣

, tahir yace husna aransa suna me dadi, afili kuma yace "no bande saniba,"

Bashir yace "to me kake so,"
tahir yatashi daga falon yayi daki yana waya yace" number ta nakeso ka nemomin kokuma kabata tawa number kace ta nememi yanzu,😳"

ummi
murmushi tayi akaro na biyu ta daga hannuwanta sama tace" alhmdlh addu'ah ta ta karbu Allah yasa wannan yarinya a dace kar a kuma irin ta baya, "
Bashir aransa yace lalle tahir wato shide bazai futo fili yace inasan yarinyar nanba, gara ya dinga wannan kwana kwanar 🤣
Yanzu banda abinsu wacce budurwa ce mai hankali kawai za'a bata number ace ta kira, kuma ma Abu kamar umarni ta kira yanzu yanzu 🤣
Bashir yace "a a bari inturo ma kawai ka kirata, Dan nikam bazan iya wannan karfin halin ba,"

"OK" kawai tahir yace, ya kashe wayar

Yana zama agadonsa yaji shigowar text yana dubawa kuwa yaga Num yarinyar, yawwa yafada a fili,🤣 yaude za'a yi ta takare, wannan labari dole yafadawa ahmad, a wannan lokacin kuma ahmad yana kwance baima farfadoba, doctor din daya duba shi, yana shirin fita daga falon yaji wayar ahmad din tana qara hannu yasa ya dauko wayar best friend yagani, doctor kai tsaye ya daga yayi masa bayanin halin da ahmad din yake ciki, tahir baisan lokacin daya tashi ba yace
"wanne asbitin?"
Nan doctor yayi masa kwatance
Falo ya futo cikin sauri ummi tana tambayarsa ina zaije yace Mata ahmad ne baida lafiya zaije wajansa, cikin alhini tace to Allah yabawa wannan yaro de lafiya, hankalinsa yayi Gaba baima ji abinda take fadaba, mota yashiga aguje maigadi yabude masa yadau hanya



** *** **



Yana Zuwa yafaka motarsa yashiga ciki cikin sauri,ahmad yagani a kwance ga doctor a gefe, anan doctor din yace kawai tashin hankali ne yayi masa yawa, ganin yazo Dakin matarsa bata nan kuma muma bamusan inda tayi ba, sannan mai gadi yace yaga fitar ta, da nasa aka tambayeshi
Tahir yace "matarsa kuma?"
Doctor yace "eh aishi da ita sukazo shiya kawo tama,"
tahir ya nemi waje ya zauna, yace "doctor in bazaka damuba kabani shi mutafi zan kula dashi dan'uwana ne," ID card dinsa ya nuna masa nan take yace Babu damuwa yafita, tahir hannun ahmad yakama yarike, yace ahmad cikin mamaki, tome yakawo ku asbiti bayan nasan sallama zakuyi

Yakai kusan minti talatin a zaune sannan ahmad yafarka, bai Bude idonsa ba, yafara magana

" feenah karki barni wallahi ba laifi na bane, please feenah ki yafemin,"

tahir ne yace "ahmad, ahmad, ahmad tashi, ba feenah bace nine"

Bude idonsa yayi, yana ganin tahir ya rungume shi yana kuka,

" tahir feenah bazata yafemin ba, wallahi nayi mata laifi"

Kamashi tahir yayi suka fita daha hospital din

Amota ahmad banda kuka babu abinda yake, tahir bai hana shi ba, yasan akwai abinda yake faruwa babba, suna Zuwa gate din gidansu ahmad tahir yabawa driver gidan key din ahmad din yayi masa kwatance yace yaje yadauko masa motarsa

Suka shiga ciki, maryam tafuto da gudu tana musu oyoyo, ahmad bai kula taba, sai tahir ne yace "auta me kike bakiyi bacci ba?"

"Tace banga yaya ba shine naqi yin bacci,"

tahir yace "to yaya bayajin dadi jeki kwanta ki huta kema"

Tatafi da gudun ta,
Bangaren ahmad din suka nufa, ahmad ya zauna a qasa yajingina da bangon Dakin, hawaye suka ziraro masa, tahir yace "ahmad me yake faruwa ne?"

"Tahir na ha'inci feenah, yarinyar tana sona dayawa, Amma na yaudareta,"

kansa yafara bugawa da bango, tahir yatashi da sauri ya rikeshi, "haba ahmad, meyake damunka haka wai meke faruwa ne,"

ahmad ya rike tahir yace" tahir meyasa baka bini ba?
Meyasa tahir?
Kasan me hakan yajamin? Tahir nayi abinda ban taba tunanin ko amafarki zanyi ba, wallahi inasan feenah nasan duk abinda zan fada Mata ayanxu bazata yarda daniba, "

Tahir ne yarike shi, suka zauna abakin gado, tahir yace" ahmad fadamin meyake faruwa? "
Nan ahmad yafada masa komai
Salati kawai tahir yakeyi, yace" ahmad Amma ina tunanin ka yatafi? Tun muna yara bamuda wannan dabi'ar ahmad"

yafada yana goge qwallar idonsa

Ahmad yace "tahir nayi asara, wallahi na cuci wadda ta yarda Dani sosai"

Tahir yace "to Amma menene sanadi? Meyakawo hakan?"

Ahmad yace "Allah ne masani tahir, nayi DANA SANIN daukarki feenah har zaki fita nahanaki, wallahi nayi DANA SANI Akan abinda na aikata miki feenah"

Tahir kawai kallansa yake, shi kanshi ahmad din yabashi tausayi,
Tahir yace "ahmad toko akwai abinda ita yarinyar tayima har hakan ya kaika ga aikata hakan, Dan nasan kaide wannan ba halinka bane,"

ahmad yace "tahir wallahi batayimin komai ba
Kawai de nasan kalau nafita daga gida, nayi nisa ne ahanya naji cikina yana murdawa, haka marata tanamin ciwo kadan kadan, to saida mukai nisa da ita ahanya shine al'amarin yafaru wanda nide a wannan halin ji nayi bazan iya hakura ba, inde bansamu abinda nake soba, "

Tahir yadago cike da mamaki yace" to kaci abinci ne kafin kabar gidan? "

Ahmad yadago kansa yace" banciba, banci komai ba tahir.... Tunanin sa ne ya tsinke dayaga lemon dayasha kafin yabarshi Akan fridge kafin ya fita
Tsaye ya Mike yana nuna just din da hannunsa, tahir ya Mike yace "me kake nufi?"

Ahmad yace "nasha... Tabbas nasha wannan, shine last abin danasha nafita,"

tahir cup yaje yadauko, ya tsiyaya lemon aciki, nan su kaga kalar lemon ta sauya kadan
Tahir yace "kagani ba?Ahmad tabbas ansama wani Abu acikin lemon nan, kabani kwalin lemon zanje gida gobe zan bincika duk abinda nagani zan fadama"

Ahmad kawai yazama mutum mutumi

"Aikuwa akwai rashin mutunci agidan nan, 🤣inde nagane dasa hannun wani aciki, wallahi duk wanda yayi silar bacin ran feenah to tabbas shima saiya tabbata cikin bacin rai,"

juyowa tahir yayi yana kallansa Jin irin furucin dayake futowa daga bakinsa





Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱



Writing by Amnah el yaqoub



Dedicated to my family



24



Baba naganinsa yatashi tsaye cikin ladabi yace" sannu maigida, yakarfin jikin Naka? "

"lafiya baba yauwa nace kwanaki kuwa lokacin danake rashin lafiya bakaga yaran nan sun shiga part dinaba?"

Baba maigadi yace "yara kuma ranka ya Dade, ai yanbiyu da auta basa shiga su batama kofa"
Ahmad yace "eh baba basu ba haka de Babu wanda kagani yashiga?
Yara ko manya"
Baba maigadi yace "gaskiya banganiba ahmad"
"OK" ahmad yace zai juya yatafi
Sai yaji baba maigadi yace "saide ko in kafin rashin lafiyarka de nake tunani"
Ahmad asukwane ya juyo yace "wacece? Wakaga ta shiga?"
Baba maigadi baiboye komai ba ya kwashe komai yafadawa ahmad
Yaci gaba da cewa tabbas naganta da idona tana gyaran firinji (fridge) ta futo da lemuka tana maidawa
Huci ahmad yake kamar wani tsohon zaki
Har baba maigadi yace" lafiya kuwa? "
Ahmad baice komai ba yajuya ciki, walaya tasaki labulan data rike ahannunta jikinta yana rawa ta tsaya Ajikin window
Kawai shawara ta yanke tahada kayanta tabar gidan, saide kafin ta juya taji taku abayanta, yanayin dayaganta shiya tabbatar masa dacewa itace ta aikata masa wannan aikin kai tsaye yace Mata "zo"
Moper hannun ta tayar Garin sauri kafarta tana hardewa ta tuntsirar da ruwan da take moping din, tabishi abaya har part dinsa
Bakin gado ya zauna itama ta zauna aqasa kanta asunkuye
Ahmad yace "menamiki kika cutar Dani walaya?"
Walaya shiru ba amsa
Yasake tambayarta cikin tsawa "nace uban Mena miki kika cutar Dani?
Kudi ko?
Nawa aka baki kika zabi ki lalatamin rayuwa?"
Walaya cikin kuka tace" Dan Allah kayi hakuri, wallahi bazan sake ba "

Dauuu kakeji ahmad ya wanke ta mari, kafin ta dago yaqara Mata wani,
Idanunsa sunyi jajir yace" uban waye yasaki, "
cikin kuka tace" wallahi wani ne nima bansan Shiba, kawai cewa yayi na temaki shi, "ahmad yace" owk shine kuma kika temakeshi kuka hadu kuka cutar Dani
Nayi DANA SANIN zaman ki agidan nan walaya,
Bazaki fadamin waye ba,? "
Cikin kuka tace" wallahi bansan Shiba, "

belt dinsa yacire yafara dukanta dashi
Ganin yana neman illatata ne yasa tace" ga wayar danake magana dashi, "

karbar wayar yayi ya dokata da qasa
Nan take ta tarwatse
Ihun ceto walaya take nema, Amma ahmad ko ajikinsa, su momy ne da mamy sukaji kamar ihu ake agidan, aikuwa dukansu suka futo afalo suka hadu momy tace" me yake faruwa ne," bukhari ne yace" a bangaren yaya ne," aikuwa suka tafi Gaba dayansu
Zuwansu yayi daidai da Suman walaya, salati momy tafara tana tafa hannaye" anya kuwa ahmad kanka daya?" Jin sunan data kira shi shiya tabbatar masa da cewa ranta yabaci, kuka yafashe dashi yace" momy wallahi Yau ko ni ko wannan yarinyar," momy kawai saita fara hawaye, wannan wacce irin masifa ce ace danka kuma ma babba mai hankali yakama mace yana duka, hawayan idan ta ta goge tace" shikkenan gatanan kakashe ta ahmad "
tajuya tayi waje, suma yan biyu ganin tana kuka abinda basu taba ganiba sai suma suka fara, sukabi bayanta, mamy hakima tace" my son me yayi zafi hakane?"
Ahmad cikin kuka yace" mamy wannan yarinyar ta cutar Dani, Allah ya'isa tsakanina dake walaya," mamy bata kula shi ba, taje ta debo ruwa a fridge ta shafawa walaya, nan take tafarka, ai tana ganin ahmad ta tashi Zata gudu, yace" basai kin gudu ba, "

janyo ta yayi kamar kayan wanki, yayi waje da ita, mamy tana" ina zaka kaita? Ahmad dakai nake fa,"
Amma ko juyowa baiyi ba, haka yajata har compound din gidan yayi wulli da ita, kowa kallansa yake yana ganin ikon Allah, shigowarsa gidan kenan saura kadan yabi ta kanta da mota, da sauri yafuto yana gyara malun malun din dake jikinsa,😃 a daidai lokacin ahmad yana nunata da hannu "karna qara ganin kafarki agidan nan, ko ahanya karki nuna kinsanni, fice ki barmana gida mayaudariya, azzaluma,"


"saboda gidan Kane? To Babu inda zataje" inji daddy daya tsaya yana ganin wannan karfin Hali
Danme zaka kama yar mutane kayi da duka kowa yanajin kukan ta agari, irin tarbiyar danama kenan? "
Ahmad cikin share hawaye kawai yajuya Yakoma part dinsa, daddy yajuyo da nufin ya yiwa walaya magana Takoma ciki, saiyaga wayam ba ita ba alamar ta, maigadi ne kawai yaga fitar ta, shikuma yasan maigida yanada gaskya shiyasa yabarta tafi ce, inba neman magana ba ina ita ina shiga bangarensa?
Daddy ne yayi ciki, suma su saudat dasu mamy suka bishi abaya

Momy suka gani afalo tana zaune yan biyu suna gefenta, daddy ya zauna yana cewa "meyasa mu wannan yaron?"
Momy tace "aida ka barshi ya kasheta, shima sai akashe shi,"

"haba hajiya wai meyasa kike hakane?"
Inji mamy

daddy ne yace" ke mabaruka kiramin shi "

Part din taje, yana zaune agefen gado yarike kansa da hannu biyu "
Tace yaya Dan Allah kayi hkr, kabarwa Allah komai," dagowa yayi yaga mabaruka ce, cikin tsawa yace" ke tashi ki fita, "

Tace" to daddy yace kazo,"

wuf tayi waje tun kafin itama yahada da ita

Tashi yayi yaje, duk suna falon, ya zauna aqasa idonsa jajir, daddy yace." ina jinka metayima? "

Ahmad shiru, aransa yace Tome zance musu magani tasamin nasha naje nayi wa yar mutane fyade?
Kansa ya girgiza yace" ba komai daddy, "
Daddy yace" au haka kace toshkn, tashi kaje kahada yanaka yanaka katafi Cairo, da tafiyar ka jibi ne Tona fasa, kaje kahada kayanka katafi yanzu, banasan tashin hankali "

Auta ce tafashe da kuka tafara birgima" Allah daddy a a, nide bazai tafi ba"mamy hakima tace" maryam kin rufe min baki kosaina bigeki anan?" Momy tace" kyaleta mana hakima, haba yarinya cefa "

Saudat ce ta dauki maryam tana rarrashinta sukayi sama, suma sauran yaran mabaruka da twins suka bisu,
Mamy hakima cikin sigar rarrashi tace" my son kayi hkr kayi mana bayani menene tayima? "
Ahmad kansa aqasa yace" mamy Babu komai "
Momy kuwa dama bata tambaye Shiba, yaje can yaqara ta

" Tashi katafi, Allah yakiyaye, zanyi waya yanzu anemama ticket na kowanne jirgi ne inde zaije masar, ka gaida abi, Allah yatsare," inji daddy

Ahmad baice komai ba, yatashi yayi part dinsa, kayansa yadauka kala uku, sai su singlet, yadau trolly dinsa Babu wanda ya yiwa sallama agidan yatafi "mad'aar" (Airport)
To dama zaman me zaiyi aqasar ma, feenah taqi tsaya wa yayi Mata bayani, iyayensa sunajin haushinsa, gara ma Yabar qasar ya huta




** *** **




Yadade yana faman kiranta Amma wayar akashe, Amma Yau cikin sa'ah sai gashi ta shiga, yana zaune afalo baidade da dawowa daga hospital ba, yana tsiyaya ruwa a glass cup yaji ta daga

"Amincin Allah yatabbata agareki, ma'abociyar nutsuwa da kamala"

Sake duba wayar tayi, anya kuwa da ita yake? Itade tasan batada biye biyen samari balle tace

Husna tace "pls wake magana?"

"Kina tare da doctor tahir"

Tace "doctor tahir kuma?"

"Yes wanda yayi muku lecture kwanaki harna hanaki shiga" 🤣

Husna ta zaro ido tace" Dan Allah kayi hkr, wallahi bansan kai bane "
Murmushi yasaki yace" no karki damu, dama zan gaisheki ne kuma nabaki hakuri Akan abinda nayi miki "🤣

Husna tace" Babu komai na gode "

Yace" cewa zakiyi nayafema, "

husna da mamaki yagama cikata tace" to komai ya wuce "

Yace"good girl, dama inasan tambayrki,"

husna tace "ina jinka" yace "kina sona?"

Husna cikin kaduwa da kalamansa tace "so kuma?"

Yace, "nasan bakya sona husna, Amma ina neman alfarma awajanki Dan Allah ki aure ni, wallahi nakasa samun nutsuwa tun lokacin dana fara dora idanuna akanki, zan baki lokaci kamar kwana biyu kiyi tunani zan sake kiranki inji me kika yanke game Dani"
diff ya kashe wayar Yabar husna da waya akunne kamar photo




** *** **




Text ne yashigo wayarsa, yana dubawa yaga company dayayi apply sun daukeshi aiki, cikin murna yafuto yazo zai fadawa yayansa wannan labarin
Yana Zuwa falon yaga yana shiri yace" yaya lafiya naga kana shiri cikin sauri haka? "
Abba yace" hassan yayarka ce batajin dadi inaso nakaita asbiti ne,koda yaushe jikin nata ba dadi, "

" husna! Husna!! "


" Na'am Abba gani nan,"

Ammu ne yace" to yaya kawo key din saina kaiku Gaba daya, "
Babu musu Abba yabashi key din motar suka tafi asbiti dukansu
Gwajin farko doctor ya shaida musu mama tanada jaririn ciki na wata daya

Da murna suka dawo gida bakin kowa yaqi rufuwa, anan kuma Ammu yasake fada musu labarin samun aikinsa awani company mota sabo da aka Bude a kano, ance ma wani balarabe ne ya budewa jikansa, haka sukai ta farin ciki ranar




** *** **



After 2 weeks, hannayensu sarke cikin na Juna, saudat na kuka feenah na kuka, saudat tace "yanzu feenah mun rabu kenan," feenah tace" haba saudat meyasa kike wannan mgnr, "saudat tace" Toshiknn yaushe zaki tafi zaria?"

Feenah tace" eto sai nanda 3days, "

saudat tace"ki qara sati daya kafin nan yaya yadawo daga masar, kakanmu yarikeshi yace sai yayi sati uku kafin nan yahuta zai dawo," feenah saita nunawa saudat tasan komai tace" ai zaizo zaria," saudat tace" nasani duk da haka
Gashi zabe yana matsowa, "

feenah tace" to menene? "
Saudat ta kalleta da mamaki tace" wai kina nufin bakisan babanmu Dan siyasa bane?" Girgiza kai feenah tayi gabanta yana ci Gaba da faduwa, saudat tace" kiyi hakuri laifi nane daban sanar dakeba babanmu sanata ne, nasan kema da a kano kike dole zakisan yan siyasar Garin, yanzu kuma suna neman takarar deputy governor, "
hawaye feenah ta share tace" to Allah ya tabbatar da alkhairi sister", saudat rungume ta tana kukan rabuwarsu, yayinda feenah take kukan bakin cikin abinda ahmad yayi Mata, haka suka rabu

Tana cikin adaidaita tana goge hawaye, inda tasan ahmad Dan gidan Dan siyasa ne da bata saurareshiba, domin kuwa tasan yafi karfin ta, yagama cutar ta yatafi wata qasa wai yana hutawa hawayen idonta ta goge aranta tace nayi DANA SANI ni nafisa






Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family



23



Tahir yace "haba ahmad, meyasa kake neman sauya halinka ne? Bahaka nasan ka ba ahmad, pls kadauki kaddara mai kyau ko marar kyau wannan shine abinda manzonmu yace"

shiru kawai ahmad yayi
Saida tahir ya tabbatar yabashi kulawar data dace sannan yadauki lemon yatafi gida
Tashin motar sa ne ya farkar da mamy hakima daga bacci, Amma sai tayi zatan ko ahmad ne yadawo, tayi juyi taci Gaba da bacci



** *** **



Awannan daren ahmad bai runtsa ba, kawai hango kanshi yake yana Dakar wanda yayi masa wannan aikin, sai gab da a suba sannan bacci ya daukeshi gamida zazzabi mai zafi, hakance ta faru awajan tahir ma, dakyar yasamu baccin ya daukeshi




** *** **




Karfe 6:48 natashi, kafafuna na ziro kasa, ba laifi jikin nawa da sauqi, banajin komai saide abinda baza'a rasaba, falo na futo anan naga kaka tana lazimi, tace" sannu nafi, da naga bakya Jin dadi shiyasa ban tashekiba, "

nace" aikuwa kaka yanzu ma baccin bai isheni ba,"

tace" sannu, aide da sauqi ko? "

Nace" kaka da sauqi sosai ai jiyan an yimin allura nasan shiyasa naji dama dama, "

tace" to sannu, Allah yasawaqe "

nace" amin, "

nayi "hammam" (toilet)
Bayan na idar da sallah awajan bacci yaqara fizgata dakyar de natashi nakoma gado, naci Gaba da bacci, saide har yanzu bandaina Jin wani Abu a maqogaro naba, hakan kuma baya rasa nasaba da bala'in dana shiga jiya




** *** **




Da break suna zaune kowa yanacin abincin sa, shiru shiru suna neman tashi basuga ahmad ba, mamy hakima tace "nifa banga Dan gidanaba, kode har yanzu murnar company din ce, jiya ma ina bacci naji shigowar motarsa,"

auta maryam datasa indomie dinta agaba tanaci tadago tace

"laaa ai yaya tahir ne yatafi, ba yaya ne ba,"

kowa yajuyo yazuba Mata ido cikin mamaki,
Tace" nima jiya inata jiran yaya yazo naga baizo ba shine naqi bacci, saida naganshi shida yaya tahir, wai yayama ba shida lafiya "

Momy ce tace" auta"
cikin mamaki
Mabaruka da basa ga maciji tace "kuma Dan iskanci kiyiwa mutane magana shine zaki zauna kina ma cin abinci ko Ajikin ki?"
Cikin shagwaba maryam tace" to ina ruwanki, Momy kin ganta ko," tafada tana kallan momyn ahmad,
Momy tace" yi shiru auta, kyaleta keda yaya ai mutu ka raba"

mabaruka harara ta zabga Mata ta tashi tayi part din ahmad,
Akan gado ta ganshi ya takure kansa yana bacci, qarasawa tayi ta yayeshi, wani zafi ya bugota, tace " subhanallah, yaya, yaya,"
dakyar ya Bude idonsa tace" ashe bakada lafiya, sannu,"
gyada kansa yayi kawai
Ruwa ta hada masa na wanka mai sauqin zafi, tatashe shi yaje yayi wanka, yana shiga wankan ta gyara Dakin sannan tafita

Komawa tayi ta sanar dasu halin da ake ciki, aikuwa dukansu suka diba yuuuu suka tafi ganinsa, ita kuma taci Gaba da cin abincin ta

Yana zaune Akan gado harya futo, suka zo suka zagayeshi, idan kagansu anan ne zaka tabbatar gidan akwai kwanciyar hankali da hadin kai
Saudat, Muslim, bukhari, Momy, mamy hakima, yayinda auta ta dane jikinsa, bata damu da zafin da jikin nasa yake yiba
Momy ce tace "waladeey ya jikin Naka? Meyasa bazaka kira waya kasanar mana ba?"

"Momy ai ban kwanta da zazzabin ba, kuma yanzu ma da sauqi,"
mamy hakima tace" sannu my son, "

Yace" yauwa mamy,"

" bani wayarka, "

dauka yayi yabata, ta Nemo number tahir
Yana dagawa yace" ahmad ya jikin Naka?"

Mamy hakima tace" pls tahir, zoka duba shi yanadan Jin zazzabi kadan, "

doctor tahir yace" to mamy gani nan insha Allah,"

takashe wayar

Mabaruka ce tadawo Dakin cikin shirin school tace to saiku tashi mu tafi ai, bukhari da Muslim ne suka tashi, auta ko motsi batayiba, Muslim yace" toki tashi mana,"
tace" nide bazaniba tunda yaya ba shida lafiya, "

saudat ce tace" a a auta, karma ki fara wannan rikicin danba me bullewa bane, oya tashi, "

aikuwa yarinya tafashe da kuka, ahmad ne yace " auta naji sauqi fa, idan kika dawo zamuyi wasa da jirgi da mota, "tace" to yaya Amma saide in Zata goyeni," saudat tace" wa zai goyeki yarinya, garama ki warke," maryam tace" Allah saikin goyani," ba yanda saudat ta iya haka ta goyeta saida ta kaita har mota sannan tajuyo



** *** **



" Salamu Alaikum,"

" wa'alaikumus Salam, "

" a a adamu kaine agidan namu Yau, "

" eh wlh nine mama, yagida, "

" lafiya kalau adamu, ya su aisha mutanan Uganda,"

"wallahi aisha tana can karatu yafara nisa,"

"to Allah ya temaka,"

"amin mama,"
Daga murya tayi tace" nafi, nafi, "

" Na'am kaka, gani nan,"

" zoki karbo wa adamu ruwa yi sauri, "

futo wa nayi da hijabi a hannu na, nace" baba ina wuni "
yace" lafiya kalau nafeesa ya karatu,"

" alhmdlh baba jibi ma zamu fara jarabawar karshe, "

" to Allah ya temaka,"
" amin baba "

Kaka tace" yi sauri mana nafi, "

" Ka ganta nan batajin dadi ne kwana biyu, "
baba adamu yace" kaiya, haba mama aida kin kyaleta, dawo ki zauna nafeesa Allah yasawaqe"

" amin baba,"

nakoma daki
Baba adamu yace "mama dama munyi magana da baban husna ne, Akan zamanki agidan nan, da yace kikoma can zaria kokuma ki dawo gida na da zama, muna so zamuyi wa gidan naki gyara,"

Kaka tace "gyara kuma adamu me yasamu gidan nawa,"
baba adamu yace "mama ai muna so ne a maida miki shi na zamani"
Kaka ta fashe da kuka tace "adamu Allah yasaka muku da alkhairi, na gode na gode adamu, shima mu'azun zanyi masa godiya,"

baba adamu yace "haba mama ai mun daukeki tamkar mahaifiyar mu, Babu komai," tace "to ngd kawai zan dawo gidan Naka, basai naje zaria ba," yace "to nima hakan Naso dama, to Dan inji ra'ayinki shiyasa nabaki zabi," haka
kaka ta dinga godiya ga surukan nata, mutanan kwarai




** *** **




Gumi ne yagama wanke masa fuska ganin irin illar da maganin yake dashi, sosai ansa maganin dayawa acikin just din, kuma ko waye yayi hakan da mugunta, domin kuwa Babu marar imanin dazai aika ta haka, dama yasan wannan al'amarin akwai sa hannun wani aciki, sannan bayan haka qwayar tanada hatsari sosai, Amma bazai tabbatar da shin ahmad din yasamu abinda yake tunanin ba, saide idan yayi aure ne zai tabbatar, zubar da lemon yayi, Yabar asbitin yayi gidansu ahmad din




** *** **




Duk suna zaune inda suke da, saide saudat da hand out ahannunta tana dubawa, tahir yayi sallama yashigo, shi kanshi sun bashi tausayi, gaskya suna kaunar ahmad dayawa, wai nan zazzabi ma kenan an zauna anyi jugum inaga sun San gaskiyar abinda yafaru kuma.

Abinci yagama ci dama, Dan haka yabashi magunguna da qarin ruwa,sannan su Momy suka fita suka barshi ya huta,
Ahmad ya kalli tahir yace" kai Malam nifa na warke kawai idan na tuna abinda yafaru ne banajin duniyar tanamin dadi "

Tahir yace" dole kacire abin nan aranka, kar hawan jini ya kamaka,"

ahmad yace" hakane insha Allah zan kiyaye dahiru, "

harararsa tahir yayi
Ahmad yace" toba dahirun bane, dahirun ummi "
Tahir kallansa yayi,

Please Login or Register in order to submit comment