Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya nunfasa yace
" hakane daddy, Amma kuma bakusan menene abinda yasa yaje ya aikata hakanba
Ninasan ahmad, kuma nasan abinda ku Baku saniba nasa
Abinda yake faruwa shine ahmad yanada zurfin ciki, bai futo lokaci daya yayi muku bayani ba, Amma nasan yayi muku bayani Akan maganin da laila tasa masa
To daddy laila bawai tamasa illah bane wajan hanashi haihuwa ba, a a, asanadin wannan maganin dayasha ne yasa yaje yayi raping wannan yarinyar, alokacin shida ita suna soyaiya

Wannan dalilin ne yasa kai tsaye ya yiwa laila saki uku,
Alokacin da abin yafaru ninaje nataho dashi daga asbiti, wanda anan aka tabbatar da qwayar dayasha ne yasa shi aikata haka
Damuka zo gida duk kunyi bacci, auta ce kawai bata kwanta ba, kuma wannan yarinyar itama shaida ce Akan halin dataga ahmad aciki

Haba Momy, daddy, mamy ku yiwa zancena kallan fahimta, anan ina ahmad yake da laifi?
Laifinsa daya yaci amanar soyaiyar dasuke da wannan yarinyar, shima kuma idan ya nemi yafiyarta Zata yafe masa,

Maganar yarinyar nan baby kuma, ni kaina danake auran yayar ita nafeesa wallahi bansan yarinyar nan yar ahmad bace, saida suka fadamin dazu

Ita kanta nafeesa batasan agidan su ahmad aka bayar da yarinyar ba, "

Momy taja numfashi dajin wannan zance kamar almara
Tace" eh naji tace datasan agidan yakema da bata zoba
Haba nifa ince, wannan yarinya tunda tazo gidan nan kowa yadauki son duniya ya dora Mata, ashe jinin muce
, Amma yanzu tahir ace wannan babban al'amari yafaru ahmad yakasa Bude baki yayi mana bayani,
Yanzu ba Dan Allah yakawo wannan yarinyar ba, munsan gaskya, aida anyi batacciya, domin kuwa kullum Muslim bashi da aiki sai cewa yake yana San baby"🤣

Tahir yayi murmushi yace
" Momy soyaiyar jini ce kawai"
Mamy hakima tace "kace munkusa kashe danmu batare da munsan gaskiyar magana ba"

Daddy yace "to Allah yarufa asiri," Gaba dayansu sukace " amin"

"Yanzu abinda za'ai, tahir kayi mana jagora gobe muje gidan iyayan ita yarinyar nan mu basu hakuri kuma mu nemi yafiyarta"
Tahir yace "to daddy babu damuwa, yanzu ma zaku iya tafiya insha Allah zan kula da ahmad din"

Saida suka koma suka sake duba jikin ahmad din, daddy ne harda tattaba fuskar sa, aikuwa nan take yafarka, yana dora ido Akan daddy yace, "daddy Dan Allah kayi hakuri"
Daddy yace "karka damu my son, tahir yayi mana bayani, Amma karka sake boye mana komai nan Gaba kaji, Allah ya yafe mana baki daya," Momy tace "Allah yasawaqe mu zamu tafi, tahir yace zai kula dakai,"


yana murmushi yace "to Momy Nagode," mamy hakima ma saida tashafa kansa tayi masa addu'ah sannan suka tafi

Suna fita ahmad ya cewa tahir "kai meka fadawa mutanan nan kuwa? Naga kowa sai nan nan yake Dani,"

tahir yace "ai abinne saida siyasa, cewa nayi ciwon zuciya ne yake gab da kamaka, kana matakin karshe, ingayama nan da nan suka rikice," 🤣

ahmad yasaki daria yace
" kai Amma kai dinnan bakada dama wallahi"

Tahir yace "wallahi saina koma nafada musu gaskya,"

ahmad yace "haba abokina yi hakuri mana,"

tahir yace "har labarin abinda yahadaku da feenah nafada musu, kuma alhmdlh sun fahinceka,"
ahmad yace " babu abinda zance ma tahir saide godia,"
Tahir yace "karka wani damu, ai yiwa kaine, danna yiwa qanina abinda yadace" 🤣 🤣

Ahmad yace "yauwa wai meyasa ka kirani ne dazu kake min tambayoyi Akan feenah"
Anan tahir yabashi labarin komai
Yaci gaba da cewa "yanzu saide muje gidan kabata hakuri"

Ahmad yace "wa? Ni?😳 Wallahi ni tsoron tama nakeji"

Tahir ya kwashe da daria yace "ah haba kamar ba ahmad din dana saniba?"
Ahmad yace "wallahi tsoron ta nakeji, idan tahuce Zuwa gobe naje nabata hakuri"

Tahir yace "aikuwa su daddy ma sunce zasuje subawa iyayan ta hakuri,"

ahmad yace "shikkenan ma saina bisu nima
Amma yanzu kam

Inaaa wallahi bazan iya Zuwa wajanta ba, yanda naga lokaci daya ta rikide dinnan Takoma wata daban kamar ba my feenah taba"

Tahir yace "ai tunda naji baby tana cewa anty ta mari uncle araina nace ai abinma da sauqi" 🤣

Ahmad yace " infadama ban zataba wallahi kawai naji tasss
Kaga kuwa yanzu idan naje ai saide duka"
Gaba dayansu suka sa daria


** *** **


Ina parking gida nashigo ina kuka, ko motar ban rufe ba, baby ce a bayana tana janyo jakarmu daqyar 🤣
Abba dayake alwala atsakar gida yace
" subhanallah, uwata me yake faruwa haka?"

Ina kuka nace "Abba babu ansace mukhtar
Wai bazasu sake shiba saina rabu dashi
Shikkenan Abba so suke su rabani da mukhtar"

Kamani Abba yayi muka shiga falo, mama tana tambayar abinda yake faruwa

"Abba zoka dau jakar nikam bazan iyaba nakasa" 🤣 🤣

Sukaji muryar baby tana wannan maganar

Abba yace "a a ita kuma wannan daga ina haka?" 🤔
Kukanane yaqaru nakasa yin magana

Baby tace "mama kinga ko anty ce ta wanke uncle da mari, kuma tace masa yaci Amana,
Wai nima yarsa ce" 🤣

Mama ce ta rafka uban salati

Abba yace "innalillahi, uwata kina nufin ahmad...."
Tun kafin Abba ya qarasa cikin kuka nace "hakane, shine Abba"

Nan da nan Abba yacire hularsa yafara firfita da ita





Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family


54


"Mama zoki janyomin wannan babyn acikin jaka" 🤣

Mama ta kalli izdihar ita ko ajikinta ma, ta abin wasanta take
Dauko Mata tayi, tana karba tayi Dakin mama da gudu
Abba yadubi feenah yace "tashi kishiga ciki"
Ina goge hawayen idona nayi ciki, Abu yahadu yazamemin goma da ashirin, ga haduwa ta da ahmad ga batan mukhtar
Harara na zubawa bangon dakin kai kace ahmad dinne awajan, nace sai wani qiba ma daya qara dakyau kamar bai zalinci yar mutane ba 🤣

Kaina ne yasara, alamun ciwo, Dan haka kawai na kwanta tare da rufe idona

Mama ta janye ta gumin datayi ta dubi Abba tace "alhaji kayi shiru"
Abba yace "Tome zance maman nafeesa, ban taba tunanin yaron nan zai iya aikata wannan abun ba, abin baqin cikinma yanda yazo yashige mana, muka yarda dashi kamar dan'uwa, nine mai cewa ko bayan raina ban yarda akarbi baby daga hannun sa ba, ashe shinema uban yarinyar "🤣

Mama tace" to taya kuwa za'a ce zai aikata alhaji, yaronda saboda tsananin kunya bayama yarda kahada ido dashi
Har garama tahir zai zauna ayi fira dashi, Amma shifa wannan gim yake zaune, bazakace zai aikata wani Abu naqi ba"

Abba yace "ai shikkenan, bamu ya yiwa ba, kansa ya yiwa,"
mama tace "hakane, Amma nikam banda nafeesan tafada da bakinta babu wanda zai fadamin wannan maganar na yarda, wannan yaro bai kyauta mana ba"
Abba yace "jeki ga halinda ita nafeesan take ciki"

Tana Zuwa Dakin taga nayi bacci tajuya, nikuwa batasan idona biyu ba, a wannan halin wanne bacci zan iya

Abba ne yakira Ammu yace "hassan idan kasamu dama kazo gobe da safe inasan magana dakai,"
Babu musu Ammu yace
" insha Allah zai shigo"


** *** **

"Yanzu de damuwa da kuka da tunani duk sun qare tunda kaga feenah"

Ahmad yace "wallahi tahir kalau nake jina yanzu, banajin ciwon komai, kai farin ciki ma nake ciki, Tsawon shekarun dana dauka ina nemanta Yau naganta, tazo har gida tasameni"

Tahir yace " kawai dande haka Ubangiji yatsara ne, Amma ai haduwa kam kun kusa haduwa"
Ahmad yace " kamarya?"
Tahir yace " wai kasan anan asbitin ta haifi baby?"
Cikin mamaki ahmad yace "bangane ba"
Tahir yace "tonima alokacin bansan taba, Dan ko ita husnan banma hadu da itaba alokacin
Da'aka kawo ta batada jini, ga kuma haihuwar tazo kusa,kuma anrasa irin jinin ta, in bazaka manta ba, kaine kace adebi naka abata, batare dakai koni munsan itace feenah ba, ni bansan taba, kai kuma bakaje wajanta Bama bare kaganta"
Ahmad yace "wai kana nufin feenah nabawa jini na tahir?
Ashe alokacin aka haifi baby na
Ashe nima na temaka wajan zuwanta duniya"

Tahir yace "abin de kamar almara
Itace fa wadda nake cema nayima budurwa qanwar matata
Kacimin mutunci Akan feenah, ashe ma itance"
Ahmad yace "to aide kaganta, yarinyar tayi tahir, zan iya yin komai saboda ita, har Yau nakasa manta yanayin danajini aciki, lokacin da wannan abin yafaru, yarinyar tanada...."

Gyaran murya tahir yayi yace "wai koka manta qanwata ce ne? Kaini fa yayanka ne yanzu, yaya tahir yakamata kace"

"Allah ko yayan zamani," inji ahmad
Tahir yace "kacika baki, wallahi tsaf zanje in zigata," ahmad yace "haba nawan kaifa na hannun dama nane"


** *** **

Kaina ko dankwali babu sai qananun kalba, mama nasamu afalo ita kadai tayi shiru, kai tsaye cinyarta nadora kaina, mama tace " kai nikam dagake har baby ne zaku qarasani" 🤣
Murmushi nayi nace "kai mama, dande mu biyun"
Wayata na janyo na duba text din da aka turomin ta layin mukhtar

"bazamu sake Shiba har sai kinyi alqawarin zaki rabu dashi, shima yayi wannan alqawarin "

Mama na nunawa tace "Allah yarufa asiri," nace "mama bari nakira naji,"
Ina kira nasa wayar a handsfree
Nace "Dan Allah kuyi hakuri ku sakeshi,"

"Wacece kedin?"
Nace " ni kuka turowa text Akan in rabu dashi
Naji zan rabu dashi, Amma Dan Allah karku taba lafiyarsa, Dan Allah ku rabu dashi, banaso komai yasame shi"

Qit aka kashe wayar batare da ancemin komai ba
Mama na kallah da mamaki tace "wannan yaro ko a wanne Hali yake ciki, nasan iyayansa hankalinsu ba a kwance yake ba"
Nace "hakane mama, Allah yasa suyi hakuri su sake shi," tace "amin"

Batamin zancan ahmad ba, nima banyi mataba


** *** **

Next day, maqota da yan'uwa ne suka cika gidan kowa yana fadar albarkacin bakinsa Akan dawowar mukhtar
Wasu gulma ce take kawo su, wasu kuma jaje
Iyayansa sunfi kowa murna da dawowar dansu lafiya batare da komai ya sameshi ba

Saida suka kebe da iyayansa ne baba yake tambayarsa babu de abinda suka masa ko? Yace babu komai
Ko zaginsa basuyi ba, kawai sude fatansu na rabu da ita, baba yace ikon Allah to ai Allah yafisu
Inna ce tace nikam Malam yaron nan daya hakura da al'amarin nan, tunda Abu yafara Zuwa da matsala
Baba yace "a a haba de zainabu
Yaza'ai mu zama qananan mutane a idan iyayen yarinyar
Bayan kuma suma kansu yaran sunason junan su"

Tace "Toshiknn, Allah yashige mana Gaba"


** *** **

Ina kwance adaki ina waya da mukhtar sai farin ciki nake saboda futowarsa
Nace "wallahi naji dadin yanda ka futo lafiya mukhtar," yace "Allah ne abin godia feenah tah, kinsan yanzu fa baba yahanani fita ko ina
Banda masjid babu inda nake Zuwa, kullum ina gida ina tunanin feenah tah"
Daria nayi nace" wallahi gara haka, tunda ai bazasu zo har gida su daukeka bako, mukhtar abin nan yana dauremin kai, narasa waye yakesan rabani dakai
Basusan cewa duk wani farin ciki na yana tare dakai ba
Fatana da burina shine ka kasance uban 'ya'yana"
Mukhtar yace "me kika ce? Please Dan Allah maimaita"

Kashe wayar nayi ina daria, daga cikin blanket na futo, baby duk ta yaye jikinta anatashan bacci, falo na futo da murna ta nace "mama ansakeshi!"
Turus nayi ganin Ammu da Abba da mama ne afalon, ko yaushe yazo oho

Rissinawa nayi na gaida shi, yace "nafeesa kiyi hakuri fa Akan abinda yafaru, ni nasan ahmad bawai haka kawai yayi ba, dole nasan akwai sanadi, saboda wannan ba halayyarsa bane"
Nide bance komai ba nakoma daki, mama tace "zonan ina zakije kuma"
Dawowa nayi tace "yaushe aka sakeshi," nace cikin murmushi "yacemin de dazu ne da safe"
Abba yace "to alhmdlh, bari nima nakira iyayan nasa"
Ammu yace "eh gaskya kam, Allah yaqara kiyayewa Gaba," cikin murmushi nayi daki na


** *** **

Wandon jeans ne ajikinsa blue, sai baqar Riga body hug, daidai jikinsa
Sai yar sama daya dora kalar jeans din jikinsa mai laushi
Sumarsa tasha gyara
Agogo yasa qirar plaget
Sai zuba qamshi yake

Falo yatafi kai tsaye, yana Zuwa yaga iyayansa suna break
Har qasa yagaida su, mamy hakima tace "yajikin Naka?"
Daddy ne yabata amsa da fadin " kya tambaye shi jiki, mutumin dayayi irin wannan wankan" 🤣

Kansa ya sunkuyar yana Sosa qeya, yace "mamy jiki yayi sauqi"

Tace "alhmdlh ga break fa"
Tasowa yayi, yana zama qannansa suka fara gaida shi, auta ce tajefo masa tambaya
"Yaya yaushe baby Zata dawo?"
Mabruka ce ta doketa
Momy tace "a a Mabruka kya daketa?
Dan tayi tambaya? Ai yanada kyau taji, 😃"

Ahmad ne yahade ransa, ya kalli Mabruka yace "idan kika sake dukanta saina tsinka miki mari"

Momy tace "daga tambaya sai duka? A wanne dalili?"

Shiru kawai yayi, yaga alama Momy so take ta dora masa laifin komai
Maryam yaja, yamaidata cinyarsa yace "kiyi hakuri Zata dawo, kinji?"
Hawayen ta ta share tace "to yaya"

Sun Gama kenan tahir yayi sallama yashigo, yasa yadi fari mai kyau, Amma baisa babbar rigaba, yayi kyau sosai
Yana gaidasu Momy da da daddy, dukansu sukai haramar tafiya

Har sunzo shiga mota, ahmad yace "tahir kawo key din saina kaimu"
Daddy da haushi yacika shi, yace "kakai suwa? 😳

Saide kakai wasu, Amma mukam bazaka bimu da wannan shigar ba, haba kullum mutum cikin qananun kaya," yadubi tahir yace "ka dinga yimasa fada, tunda naga kai ka fishi Dan hankali"

Sunkuyar da kansa yayi yace "daddy "ma'alesh" (kayi hakuri)

Juyawa yayi cikin sauri yaje yasauya kaya, shima farin yadin yasa, tahir sai daria yake masa, mota biyu sukayi suka tafi


Suna Zuwa zaria guards suka Bude musu mota

Tahir ne yakira Abba awaya yace sunyi baqi
, ahmad kuwa kasa futowa yayi daga motar
Daddy ya kalleshi yace tunda mu mukai laifin aimune yakamata mu futo

Sai a sannan yafuto, Gaba daya jikinsa yayi sanyi, yarasa tayaya zai fuskanci wadannan bayin Allah
Haka de yafuto kansa asunkuye
Su Momy kai tsaye cikin gidan suka shiga
da Abba suka hadu suka gaisa ba yabo ba fallasa
Kofar gidan ya qarasa ya yiwa su daddy iso

Abba cikin mamaki yace "haba alhaji, harda kai ake tafe ashe,"

daddy yace "ah babu komai wallahi, ai takamane"

Dukansu Abba yace ku shigo mana, su Momy suna Zuwa suka zauna afalon, nan su Abba da daddy ma suka shigo falon
Gaba dayansu, ahmad da tahir ne aqarshe

Mama tace "nafeesa tashi kikawo musu ruwa mana,"
Dan kwalina nafara lalube
Ina dagowa karaf muka hada ido dashi
Da sauri na janye idona

Cikin ransa yace masha Allah gashin ta de yana Nan da yawanshi
Da kallo yabita kamar zai hadiyeta
Saida tahir yalura, ya mintsineshi, sannan yadawo hayyacinsa 🤣
Kallansa yakai kan Momy, ta balla masa harara

Shi kam Yau yaga ta kansa
Abba ne yace "tahir ku zauna mana"

Kansu aqasa kamar munafukai, suka shigo aqasa suka zauna

Ina kawo ruwan da lemuka, nafara zuba musu

, su kuwa ko kallansu banyi ba, mama ce ta harare ni, afakaice
Aikuwa na matsa nakai musu
Idonsa kyar akaina
Kamar bazan Bude bakiba nace "yaya tahir gashi"
Tahir yace " yauwa autar mu, mun gode"

Shikuwa Dan qaramin bakinta yake kallah yanda take budeshi kamar bataso


Baby ce ta futo daga daki, tana kallan mutane afalon ta tafi da gudu wajan daddy
Tace "ga daddy"
Daddy yace "izdihar, ashe kina ciki,"
saikuma Takoma wajan su Momy, tana ganin ahmad kuma sai Takoma wajansa da gudu
Saita bawa yan falon daria
Tace "yauwa uncle, ashe kazo tafiya Dani
Anty to kema debo kayanki saimu tafi Gaba daya" 🤣

Nikam ko inda suke ban kallah ba

Daddy ne yayi gyaran murya, anan aka sake sabuwar gaisuwa
Daddy ya dubi Abba yace "alhaji munzo ne Akan abinda yafaru tsakanin yaran nan, Dan Allah Dan annabi kayi hakuri
Kuyafewa yaron nan
Dan Allah alhaji," saukowa daddy yayi yadawo qasa, Abba Da sauri yatashi ya tareshi yace "haba alhaji
Ni danasan zaka zo da kanka ma, dana hanaka wallahi
Babu komai ai Dan Adam baya wuce qaddarar sa"

Daddy yace "hakane
Tahir kayi musu bayanin abinda yake faruwa, kamar yanda muma kayi mana bayani"

Aikuwa tahir tiryan tiryan yabada labarin komai

Abba yace "babu komai, adade nayiwa zancan mummunar fahimta, Amma ayanxu dana gane komai, to alhmdlh nikam komai ya wuce awajena, wallahi har cikin raina, nida mahaifiyar wannan yarinya, mun yafe masa"

Cikin sanyin murya Ahmad yace" Nagode Abba, Allah yasaka da alkhairi"
Abba yace "babu komai ahmad karka damu, Allah yakiyaye Gaba kuma"
Gaba daya falon a kace

" amin"

Abba yace "saide ita, gatanan saika bata hakuri, ku sasanta kanku, tunda Allah yanufa da rabo atsakanin ku, koba komai kudinga gaisawa ma, albarkacin wannan yarinyar Allah yasa mufi karfin zuciyar mu"
Aka sake cewa "amin"

Momy da mamy ma, sun nemi yafiya, kuma anyi musu, anan de aka fahinci Juna

Daddy ne yadubi Abba yace "alhaji ina neman alfarma awajanka, idan bazaka damuba,"

Abba yace " haba alhaji aikafi karfin komai awajena, kasauke mulkin da Allah yadorama kazo nan da kanka saboda abinda yafaru ai kayi komai"

Daddy yace "hakane Nagode sosai, dama inaso ne ka temaka kabawa yarona auren yarka
Kaga shikkenan saisu riqe yarsu, batare da kowa yasan halin da ake ciki ba"

Abba ne yace, "wallahi alhaji nafi kowa San wannan al'amari, Kodan izdihar ma, Amma hakan bazai iyuba"

Gaba daya falon akai shiru dajin furucin daddy
Musanman ahmad

Abba yace "saboda anriga anyi Mata miji, yanzu haka saura wata daya da yan kwanaki yarage bikinta"

Kansa ne yaji yasara
Idonsa yakada yayi jajir lokaci daya


Daddy yace "Toshiknn alhaji, ai duk daya, dama haka Allah yatsara"

Mama ce ta cewa su Momy, "hajia ku shigo daga ciki"
Babu musu suka bita, baby ma tabisu

Daddy ma fita sukai tare dasu tahir,

Wajan yarage dagashi sai ita







Mrs Usman ce ✍️
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

55


shiru ne yabiyo baya, kanta asunkuye takasa dagowa ma bare ta kalleshi, ada kam yanda zuciyar ta take yi Mata zafi, gani take Zata iya yimasa rashin mutunci
Saide gashi kuma gata gashi, Amma kuma tama kasa dagowa bare ta kalleshi

Shine yayi karfin halin tashi daga inda yake ahankli, cikin nutsuwa yaqarasa dab da ita ya zauna, duk da yana tsoron yimata magana saboda baisan mai Zata maida masaba, Amma kuma wani bangare na zuciyarsa yana qara qarfafa masa gwiwa

Cikin muryarsa mai dadi da sanyi, yace
"My feenah"

Har cikin qwaqwalwarta taji sunan, meyasa takeji ahmad yafi kowa iya fadar sunan ta? Meyasa duk lokacin daya ambaci sunan ta take jinta cikin wani yanayi na daban?

Karfin halin dagowa nayi nace, "meyasa zaka fadamin wannan sunan? Alaqar datake tsakanin mu ai ina tunanin tariga data qare
Nasan maganar yafiya ce, zakamin, tona yafema
Shikkenan zaka iya tafiya"

Kansa ya sunkuyar, Yama rasa maizai fada Mata, tsareta yayi da idanunsa dasuke sumar da ma'abocin qaunarsa musanman feenah
Furzar da iska yayi,yace
" Nagode da yafiyarki agareni, duk nasan cewa abune mai wahala hakan, Amma bayanin da tahir yayi muku nasan zai gamsar dake, ni tunda nake babu mutumin dana taba zalinta saide cikin rashin sani, bare kuma abar danafi Santa fiye da kowa aduniya, bayan iyayena, "
Kallansa nayi nace" ok inka Gama nizan shiga ciki "

Miqewa nayi da nufin tafiya, caraf naji ya riqe hannu na, yace "meyasa feenah?
Meyasa koda yaushe kikesan ganinmu cikin tashin hankali ?"

Shima tasowa yayi yaci gaba da fadin

"Yanzu shi wannan lusarin ya zaki dashi? Dan nikam ban taba sawa araina zan rasaki ba, kuma bazan fara yanzu ba,"

Takaici yacikani, wai mukhtar ne lusari
Fizge hannu na nafara, Amma riqon dayamin yasa nakasa qwacewa, kallansa nayi cikin ido, nace "karka sake aibatamin abinda nakeso
, koma abinda yafi lusari ne naji inasan abina, ina qaunarsa haka"
Wani zafi ne yaji ya ziyarci zuciyarsa, kansa ya sunkuyar
Yana dagowa taga idonsa yayi jajir, ita kanta saida ta tsorata
Kallanta yayi babu alamar wasa atare dashi, yace "karki qara cewa kinason wani a gabana
Inba haka ba wallahi zaki gane kurenki"

Kuka ne ya kufcemin, cikin shagwaba nace

"nafadadin, nima cikani, kuma koda babu mukhtar babu abinda zanyi kai"
Cikin tsawa yace "nace karki sake ambatarsa a gabana ko!!"

Gyaran murya sukaji akansu, atare suka juya, tahir ya kallesu yace

" daddy yace kafuto mutafi," sannan yamaida kallansa ga feenah yace
" auta, ki turo su Momy, kice su futo mutafi"
Sai a sannan ahmad yacikata
Yana sakinta tashige ciki da kuka

Atare suka futo da tahir, kirjinsa banda zafi babu abinda yake, tahir ya fuskanci halinda yake ciki, Dan haka kawai ya bubbuga kafadarsa suka qarasa wajan daddy
Suna Zuwa yashige baya ya zauna, tahir naganin haka aransa yace Yau kuma saita Allah, 😃
shiyasa shima baiyi masa maganar driving ba
Su Momy sosai sukai sallama da mama, inda mama tace izdihar tana Gama hutawa Zata dawo, Dan tasan kawaici suka Mata, suma suna son tafiya da yarinyar


** *** **

Kuka nake Sosai adaki,
" meyasa sai yanzu ahmad ya baiyana agareni? Meyasa saida na mallakawa wani zuciyata sannan ahmad zai bayyana?
Dole ne inyi maganin wannan matsalar tunma kafin ayimin aure in shiga gidan wani da soyaiyar wani a zuciyata, mukhtar yamin komai, bai qiniba alokacin dayaji dukkanin labari na, wanda a wannan zamanin ba kowanne saurayi ne zaiyimin ba"
Share hawayena nayi, nafita falo, nafara tattare kayan da sukai amfani dashi namaida kitchen
Ina kaiwa nakira mukhtar awaya, mukasha firar soyaiyar mu, duk Dan in manta da abinda yake damuna


** *** **

Su Momy sai firarsu suke a mota, suna tuna shirman baby, mamy tace "nikam hajia banji dadin wannan al'amari ba, wallahi Naso wannan yarinyar ta auri ahmad, sun dace da Juna sosai, Naso kasancewar ta cikin family n MARZUQ"

Momy tayi ajiyar zuciya, tace "wallahi hajia nima haka"
Mamy tace "ko yaya ahmad zaiji?"
Momy tace "Ana can de su tahir ne daganin, bacin rai" 😃

Acan daya motar kuwa, daddy ne suke Dan taba hira da tahir, wasu Akan tituna ne, wasu kuma abinda yadanganci siyasa, shikuma gogan yayi gim kai kace babu halittarsa amotar 🤣

Cikin ransa tunani ne fal, wai bata sansa, mukhtar take so, ko waye wannan gaulan?
Yasan de duk tsiya Babu abinda zai fada masa, Amma kome tagani awajan wani dahar ta iya budar baki tace shi Zata aura?
Tsaki yasaki cikin ransa baisan afili yayi ba
Daddy ya kalleshi
Yadubi tahir yace "tahir akwai tsakane acikin motar nan?"
Saurin kallan daddy yayi, anan ya gane abinda yake tunanin azuciyar sa yayi, afili yayi 😃


** *** **

"Mabruka bawa Momy wayar mana, kude kullum aka kira waya sai wani acikinku yadaga"

Daria tasaki tace "to ai basanan masu gidan, yanzu mune masu gidan" 🤣

Saudat tace "kamarya?"

Mabruka tace "wallahi basa nan sunje zaria dukansu"
Cikin mamaki tace
" lafiya? Me akeyi a zaria?''

Tace" wallahi anty sauda bansaniba, Amma de gidansu anty husna suka tafi, matar yaya tahir, wai wata yayar baby ce tazo ganinta
Shine fa tana Zuwa taga yaya, tana ganinsa ta tashi, nan suka fara fada"

Saudat tace "fada kuma? Tome yahadasu?"

Mabruka tace "harfa marinsa tayi anty, wallahi muna tsaye sai tassss kakeji ta mareshi,🤣 ta qwace baby tace yarta ce, shima kuma yarsa ce,Dan haka bata buqatar sake ganinsa arayuwarta, Dan haka yabata yarta,"

Shikuma fa yaqi Rama Marin kawai sai kira yake
" feenah" 🤣

Saudat tace "keeee mekikace?😳 Wai kina nufin feenah ce tazo gidan?"
Mabruka tace "wallahi hakade naji yace, Amma kuma ta cewa su Momy sunanta Nafeesa"

Saudat dafe kanta tayi da hannunta
Takashe wayar kawai,
Subhanallah, me yake shirin faruwa ne? Me sister da yaya suke boyewa atsakanin su?

Babu wanda yasan wannan amsar tambayar sai yaya da feenah da kuma yan gidan, Dan haka Zata jira su dawo taji kan batu




Please Login or Register in order to submit comment