Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yatako yazo har wajansu, har qasa ya tsugunna yagaidasu ya gabatar musu da kansa, sosai su Abba sun yaba da hankalinsa, "yaro daga ganinka naji hankali na ya kwanta dakai inde nafeesa kake so ka nemi soyaiyar ta, idan kun dedeta atsakaninku shknn ni bnda damuwa, Amma yanzu de makaranta Zata tafi, bazan iya yi musu auren dole ba Amma inde kun dedeta banda matsala," godia auwal yayi yana farin cikin Jin kalaman wannan bawan Allah, yatashi yatafi.
" kai wallahi bakiji gabanaba yanda ya yanke yafadi, husna tace" gabanki ko gabana nida na zaqe harda shiga gaban motar, 🤣"

" hmm Allah de yarufamana asiri, nikam gaskiya be minba",

" kai sister nikuwa kinga nayaba da hankalinsa shiyasa ma nayarda har muka shiga,"

nace" haba anty husna kinganshi fa, wani babba dashi, nikam ina bana sanshi, "
kallona tayi tace" wato ke sai yan zamani ko masu ajiye suma suna tafe suna kakkade takalmi da handkerchief"🤣
, nace" a a dede misali de, "

" auta kinga ki shiga hankalin ki da irin samarin nan, ni basa birgeni,"

" kai anty husna kuma de daga magana"

" to sai kiyi tayi ai kuma wlh saina ziga Ammu anbaki shi, inyaso ki mutu,"

aikuwa kan kace me na fara kuka ni wlh bana sanshi, haka kawai za'a min auren dole, ganin ina kuka kuma sai jikinta yayi sanyi, dafa kafadata tayi tace" feenah wasafa nake miki, haba keda kike auta waye zai miki dole bayan mama ma tana ji dake, "

dago kaina nayi ina murmushi Dan nikam inaso inji Ana zugani awajan mama, tace" yauwa kokefa, share hawayanki in baki wani labari, kawai rannan basai naga wannan maimunan taku ba,"
nace" wai anty maimuna"
tace "yes ita, wlh mun futo daga lecture kawai naji ance husna, ina juyawa naganta, ni mantawa ma nayi ban fada mikiba, tace kuma in baki hakuri wlh tarasa paper din data rubuta Number ki da address din gidan nan da tuni ta nemeki, harfa number mukai exchange tace ma inbawa Ammu number,"

😳 ido na zaro nace" sanshi fa take",

"aida gani sanshi take, shekara da shekaru takasa mantawa dashi, tace yanzu bari idan yashigo yana mana muzurai kawai zan bashi number shknn mun rufe bakinsa,"

"aikuwa haka za'a yi," dariya mukasa hade da tafawa.
"kun dawo ne? Mama yanzu muka dawo auta nake rarrashi yanzu ma wai Dan tayi miki suruki nace zamusha biki shine take kuka,"
murmushi mama tayi tace "Allah ya kyauta."

Da daddaren kuwa Ammu yashigo husna ta bashi Num. Kamar bayaso ya karba, nan kuwa wani sanyi yaji aransa, nikuwa sai washe gari nakirata mukasha firar yaushe gamo.
Kwance nake a dakinmu ina karanta novel a wattpad husna tace" ansamu wattpad anmanta da littafi yanzu andawo online, "
" dariya nayi nace wlh banyi tunanin karatun online zai kai na littafi dadiba ada nafijin dadi in rike novel ahannu na ina karantawa Amma yanzu inaaaa sai wattpad," husna tace" ai shine abinda nake fada miki kinki yarda, ya kikaji hafsatul ikhram, wannan yana so wannan anaso ahadasu ashe duk cikima Babu me dauka, pilot zaizo ya dauke abarsa, nace "wannan shi ake kira da rashin sani."
Da daddare saiga kira da wata new number nadauka, bayan mun gaisa yake sanar Dani auwal ne, tsaki nayi araina nace DANA SANI daban amsaba, anan yake sanar Dani yanda sukai dasu Abba, yaqara tabbatar min da cewa zai rikeni Amana idan na amince dashi hakade yayi ta yimin surutu nide nawa eh a a shikkenan, ahaka nace masa saida safe zan kwanta.

** *** **

Haka auwal yake ta kokarin kirana a koda yaushe wataran in daga wataran inqi,haka rayuwa tayi ta tafiya har lkcin bada admission yayi.
Ammu shine yayi duk wani shige da fice yasama min, muna zaune yazo yake sanar Dani cewa nima nasamu admission a legal, mama tayi murna, nikuwa araina nace shknn nazama yar jigawa," to Ammu nagode yaushe zan tafi jigawan?" Yace '' me zakiyi a jigawa, haba nafisa dama abinda yasa nakaiki nesan saboda rashin jinki ne, Amma yanzu legal ta kano nake nufi, bansan lkcin danayi murmushi ba, sbd dangin mama dasuke kano.

** *** **

Agajiye ya dawo gida, yana sanye cikin qananun kaya bakin wando tare da jar Riga, kan nan yasha gyara, sai sheqi yake, yana sanye da agogo Gucci, fadawa yayi cikin daya daga cikin kujerun falon, "wash Allah, yafada" ,walaya ce tazo da sauri yallabai sannu da Zuwa, bai amsa bataba tajuya takawo masa ruwa mai sanyi, ta sake juyawa kenan taji yace kiramin sauda, to yallabai angama angama, ta Juya, wayarsa ce tayi qara akasalance yadaga guy ya akayi, bansan me a kace daga daya bangaren ba, yace tahir Babu wata Abuja da zamu je kawai ka share ta haba yrinya karama Tanata juyaka, kawani nace Mata, ba inda zani, naji naji ni karkamin kuka, Allah yakaimu jibin sai muje Amma gsky saide mubi flight bazan iya tuqi ba OK, right ya wullar da wayar Akan kujera ya lumshe idonsa, yagaji wallahi daga office din dady yake yagaji, gashi daga can ya wuce yadubowa saudat admission latter dinsu daya futo.
Yaya gani, sai sannan yabude idonsa, yafada Mata dalilin Kiran, yeeeee tasaki tsallan murna ta rungumeshi, bigeta yayi waike saudat yaushe zakiyi hankali ne, karkayi tunanin cikin zafi yake maganar a a da sanyinsa yake yi shi ala dole fada yake Mata, dariya tayi tace yaya murna ce fa, fari tayi da idonta shknn nakusa yin friends, inshiga lecture, idan kun kirani in daga ince yaya ka kirani alokacin muna lecture, ganin shirman nata bazai qare ba ne yasashi girgiza kansa yajuya yayi part dinsa, ita kuwa ta daga kai sama Tanata Zuba batasan ya silale yabar falon ba, tace indinga shiga motata, ina Zuwa siyan shawarma daga nan indawo gida koba hakaba ya... Ganin wajan tayi wayam lalle ma yaya hmm zamu hadu ne saina qarasama wallahi



Mrs usman ce🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

8


Tunda na fara karatu na tsaida hankali na waje daya, banda wasu qawaye, kawai abin gabana nake, banda burin daya wuce yanda na fara karatuna da Arabic in qarasa dashi, kuma sai nayi sa'ah suka bani faculty of Arabic din, kullum daga gidan kaka rabi nake tafiya, aysha tayi tayi in koma gidansu Amma naqi, nace sai na gaji da gidan kaka sannan zan dawo nasun.
Sanye nake cikin doguwar Riga me sauqin kudi, nayi rolling da farin mayafi, tafiya nake hankalina kwance kasancewar akwai sauran minti talatin kafin mu shiga lecture, "guy kaga cikar danake fadama, yarinyar tayi bala'in tafiya da imanina"

" haba salman karka bani kunya mana, kaida Mata ke rububi, suke burin ka kulasu Amma wannan abar kakasa tun kararta haba salman karka bada gayu mana,"

cike da takaici salman yace da abokinsa "kaga yaks karka qara kiranta da wata aba, babyn nawa zaka kalla kakira da wata aba,"

dafa kafadarsa yaks yayi yace "haba abokina menene abin zafi kuma naji sorry"

"karka sake nafadama karka sake,"

"haba salman wannan yawane kawai komai ya wuce kabasar kawai, yanzu de jeka karka bada gayu,"

"kuma fa haka ne"

yafada tare da saukowa daga kan motor
Kaina aqasa ina tafiya kawai sai ganin mutum nayi agabana "Malam lafiya?" miye haka? Ko bakaga tafiya nake ba? Duk maganar datake kawai Dan qaramin bakinta pink color yake kalla yanda take sarrafa lips dinta, "Malam ko da kurma nake magana ne, bakajina?"
Murmushi yayi yace" salman, salman guy kenan, wannan shine sunana, tun ranar dana fara ganinki naji kinmin, so abinda nakeso dake shine kiyimin biyayya, ban taba son mace tace bata sonaba, kinyi sa'ah da nazo dakaina nace ina sonki, surarki tamin Gaba daya idan ina tunanin ki kasa bacci nake, ki amince Dani kiga harka yanmata"

, bakinsa na kalla yanda kasan nayi amai, Gaba dayansa mashayi ne ga dukkan alamu, kakarin amai na fara, cike da hanzari yace "baby menene"
nace" Malam zakasani amai, Dan Allah ka matsa daga kusa Dani kar mutane su ganmu tare ace nima na fara shaye shaye kamar ka,"

"kut"
Jin yafara zagi yasa nayi Gaba abina, yasake shan gabana, ya daga hannu zai mareni nace" karka fara, "

"ke har kin isa kifadamin magana nine ma mashayin?"

Nace "to waye zaiyi abinda kayi inba mashayi ba, kuma da kake cewa baka taba San mace taqi kaba, to kazo inda za'a qika, idan ko wacce budurwa tana sanka Toni bana sanka, kayimin kazanta, inyi soyaiya dakai,"
Mari yasake kaimin akaro na biyu, na bige hannun sa nayi Gaba, ihu wasu daga cikin dalibai sukasa, ashe wai har taruwa akai Ana kallanmu.

" kekuwa baiwar Allah meya kaiki yin rikici da namiji, namijin ma irin wannan? Bayan daga ganinsa kinsan baida mutunci, ko bakya tsoro amatsayinki na mace?"

Kallanta nayi daga sama har qasa, daga ganin kayan jikinta kasan nera ta zauna, kyakykyawa ce ajin farko, daga ganinta kasan ta hada jinsi da larabawa, abinda zan nuna Mata wajan kyau kadan ne.
Ganin yanda nake kallan ta yasa tacemin" karki damu, tun ranar dana fara ganinki naji nutsuwarki ta birgeni, bakida kule kule irin na qawayen banza, kuma koba niba duk wani wanda yake faculty din nan zai yabeki Akan tarbiyar ki, idan bazaki damu ba, zanso mu qulla qawance, "

tafada tana murmushi,tareda miqomin hannu sunana" SAUDAT MUHD MARZUQ"

hannun nima nabata nace "NAFEESA MU'AZ (FEENAH)"

"nice name" tace, mukayi murmushi atare.

Daga wannan lokacin muka qulla qawance nida saudat, tanada kirki sosai, haka kuma tanada sauqin kai, kokadan bata bani hanya nagane cewa itadin yar wani ceba, saboda bata daukar kanta a komai, nunawa take itama mutum ce kamar kowa, duk inda ka ganni zakaga sauda, munzama kamar wasu taurari, duk inda mukai sai mun haska.


** *** **

Agajiye na dawo gida Yau, kaka rabi a kace" sannu, "

nace" yawwa tsohuwa,"

" ga abinci," nace" haba kaka, saikace azamaninku, aikya bari inyi wanka ko, "

tabe baki tayi, tace" 'ya'yan zamani iyayinku bai isheku ba, "

nace "eh munji,"
bayan nagama komai nahuta nazauna na fara assignment din da aka bamu tun ranar Monday kuma jibi alhamis ne yakesan karba,bayan nagama ne nahau chting bansan ma bacci ya daukeni ba, sai Jin muryar kaka nayi tana cewa "nafi, ke nafi ki tashi kiyi sallah yanzu haka nasan qila kina nan kina watsar, (whatsapp) koba watsar ba, nasan in kika maqa daki aka jiki shiru to shi kikeyi," 🤣

nide ko kulata banyi ba, hammam (toilet) na wuce nayi wanka Dan naji karfin jikina sannan nadauro alwala domin gabatar da sallar magrib.
Washe gari, bayan na shiga school ina tare da saudat, "qawata wlh na gaji da school din nan, harma Garin, Gaba daya nayi kewar su mama, da sis husna,"
sauda tace "haka ne, dole zakiyi missing dinsu Amma yazakiyi hakuri zakiyi, gashi keba wani yawo kikeba bare kiji Dan sauqi, Dan Allah Yau kizo muje yawo da motata Babu me kulamu, kinga ni yaya bazai yimin fadaba idan yaji da qawata zan fita yasan bazanyi shirme ba, zai barni, kema kuma kina yiwa kaka bayani shikkenan, "

nace" sauda bazaki ganeba, wlh bansan yawo kokadan Amma ki bari wani lkc zaki ganni har gida nace miki nazo ne mu fita yawo,"

dariya tayi tace" tab bade wannan feenan ba,"

nace" shikkenan sister zanyi miki "mufaja'ah"(surprise) tace "shknn nide kisani su momy da twins har damuna suke Akan yaushe zan kaiki,"

nace "karki damu zanzo"

tace" to Allah yasa "

" amin "
Bayan wasu mintina tace" nifa banyi assignment din lacturer nan ba, "

" meyasa?"

Tace" wallahi yaya ne yasani aiki kuma kinsan shidin ba wasa wlh bazaiga girmana ba, tsaf zansha na jaki,"🤣

murmushi nayi nace" aikin kenan kede koda yaushe complain din ki, yaya yaya, bansan yaushe zaki sauyaba, ki fada masa idan yasake sakaki aiki toya tabbatar ya karbi "bahas" (assignment) dinki yayi miki, inba hakaba kozan baki nawa saikin koyamin larabci sannan nima zan baki,"

😳ido ta zaro cike da mamaki tace
" yayan zan fadawa haka? "

Nace" to miye? "

Tace" na gwammace inyi ta koya miki larabcin bakisan yaya bane"





Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to Mrs Abdallah

6


Husna tayi gaba, nagama kwalliya nakalli kaina amadubi, gskyr Zeey ne datace idan nayi wata shigar ta larabawa bazaka taba cewa ni din jinin hausawa ceba, kamar yanda kuka gani a bangon littafi na.
Kalatinmu ce ta tahaihu zamuje wajan taron suna, (muna kiranta da kala ne kasan cewarta qanwa awajan mama kuma duk nice silar fada musu wannan sunayen) kowa yagama abinda yake ni kadai suke jira, dana futo kowa ya miqe "masha Allah" mama tace aranta , Abba yayi waje da Ammu mukuma muka rufe gidan, munje kano mun sauka gidan kaka Rabi dake hotoro, mama de bata tsayaba tawuce gidan suna, nida husna da aysha cousin dinmu muna zaune agidan kaka muna mata shaqiyanci, "a'i tashi ku tafi gidan sunan kinji kun zauna sai zancen makaranta kuke, ke usena naga Babu ruwanki jasu ku tafi Nafi tashi,"

"gsky kaka ki dena cemin nafi, haba saikace azamaninku,"
daquwa tamin, "ke nafi nafiki rashin mutunci wlh nafi zance, su nade guda daya a dinga yanyankashi saikace albasa haba"

, kyaleta mukai tana ta sababinta mukuwa dariyar mu muke.
Sai yamma muka tafi gidan kala yaro yaci sunan sultan, agidan muka kwana mama kuma gidan kaka rabi, sai washe gari muka dawo gida muna yiwa aysha murnar samun qani, Amma da ita kadai qwal.


** *** **

Bayan sati daya muna zaune afalo dukanmu muna kallan shirin gari ya waye atashar Arewa 24, Ammu ne yashigo bayan mun gaida shine yake tambayata exam dinmu yafuto na duba ne? Nace "ai ban San ta futoba ba,"
"yacemin aikuwa wani abokina yacemin takai kusan sati da futowa, number ta yakarba yace bari yaje yadubomin, husna tace" Ammu zanje"

"me zakiyi"

" Dan Allah Ammu ai harda feenah ma,"

toshkn kawai yace muka shirya muka tafi.
Result dina yayi kyau sosai, nan muka dau hanyar gida, Ammu kuma yayi wani wajan, muna tafiya a hanya muka ga mai balangu husna tace" wlh yabani sha'awa"

nace" nima haka," anan de aka yanke shawarar siya Dan akwai wata guntuwar dari ukunmu, bayan mun siya husna tace" gsky wannan naman kamata yayi sai mun Gama abinda muke munyi wanka idan zamu kwanta saimu ci, "

nace" hakane kam" ina tura tsokar naman daya abakina, muka dawo gida bamu bi takan mamaba kasancewar tana Dakin Abba, muka wuce dakinmu da nama husna ce mai cewa inboye mana, nikuma banyi wata wata ba na tura nama qasan gado, muka dawo falo muna Dan fira kafin mama ta futo, husna ta shiga wanka Abba yafuto da buta ahannun sa, anan na bashi results din nawa, "masha Allah uwata sakamako yayi kyau, insha Allah dazaran anfara bada admission kema sai anema miki" , nace "to Abba"
Bayan nima nayi wanka muna falo nida mama kaina yana kan cinyarta" feenah! Feenah!! Feenah!!! Husna ce take qwala min kira, kafin na amsa tacemin ina yake?" Nace "Mata me?"

Tacemin" abinda muka siya nabaki ki ajiye", tuni nagano ta, mama tace" menene? "Mukai shiru, nace" ki duba yana kasan gado, ta duba can tasake cemin "na duba baya nan,"

nace" a a sake dubawa de, "🤣

Tasake cemin" na duba banga komai ba, Amma de nagano wata takarda acan karshen gado", ai inajin haka bansan yaushe na sauka daga cinyar mama ba, nayi daki, nakarbi fitilar hannun husna kasancewar Babu wuta, haskawar da zanyi saina gano takardar balangu akarshen gado,🤣🤣" ita ce, wallahi itace anty husna," daqyar dai mukasa Abu muka janyo takardar balangu, anan mukaga takarda ayaiyage nama sai tsoka uku, 😱atare muka hada baki wajan fadin kaiiii, "bera ya cinye" mukaji maganar mama a kanmu, tai juyawarta falo tana ta dariya, aida ku nan din nama ne aka siyo za'a yi qurmusu, wlh wannan bera ya kyau tamin tafada tanaci Gaba da dariya, meqomin sauran in bashi ya cinye inji mama, na kalli anty husna data rike sauran takardar nama ahannun ta, nice nayi karfin halin cewa garama ni naci tsoka daya, husna sai lkcin aka samu bakin magana a kace" shege wlh bamu yafeba, "munaji muna gani haka muka hakura

** *** **

" Momy wai yanzu yarinyar nan dady yadage saitaci Gaba da karatu, me saudat ta nema tarasa Momy," hmm numfashi hajiya hafsat taja, tace" kaima kasan de halin alhaji idan yafada din nan bazai fasaba, Amma kai kayi masa magana may be yajika, "toshkn Momy,"

da daddare bayan sun Gama dinner ahmad yasamu dadynsa da zancen karatun saudat, dady yace "wato ahmad saudat bata rasa komai ba, Amma inaso in inganta Mata rayuwarta banaso ta dogara Dani, sannan koda ace batayi aiki ba, bamusan me gobe Zata haifar ba, Yau mune gobe bamu bane, to gara de tayi karatun ko yaya ne, kuma wannan karatun bawani dadewa zatayi ba diploma ce zatayi, kuma nasan saudat Zata riqe mutunci ta, "

"hakane dady to Allah yasa hakanne yafi zama alkhairi" amin my son.

** *** **

Muna zaune afalo nida husna muna kallan film din india atashar bollywood, "nace sister kinsan me, wlh soyaiyar yan India tana birgeni,"

tabe baki husna tayi tace" nikuwa banga abin birgewa ba, kiss hug shknn aikinsu", nace" hmm anty bakisan soyaiya ba, shiyasa nifa nake San Korean film Babu tashin hankali sosai aciki sai zallar "hub" (so)"

" malama kawai kice aure kikeso shiyasa kike fakewa kina cewa wai soyaiya kede kawai kice kina kallan "qubla"( kiss) koba haka kika ce sunan kiss da larabci ba,"

murmushi nayi nace" su anty husna anji larabci"

fari tayi da ido tace "to ya ranki, nafi San soyaiyar bahaushe mutum ya rike mutuncinsa sai yayi aure" , nace "sis hakan yanada kyau Amma fa suma wannan din bawani Abu ne yake faruwa ba bayan wannan din" , tace "wasunsu ba,"

nace" to Allah yaqara kare mu"

tace "amin."







Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

9


Murmushi nayi nace" aikuwa kya koyamin din,saboda rashin kirki irin naki kinajin larabci kakanki balarabe Amma bakyasan yimin larabci nikuma inaso saboda ina girmama abinda nake karanta, "
tace" toshkn aikuwa zan dinga yi miki, yanzu de sister Tuba nake bani inyi, "
bayan tagama mukaje mukai submitting, mun Gama abinda zamuyi zamu fita tadau waya ta kira driver yace hajiya ta aikeshi Amma yayansu yace zaizo yadauketa, OK kawai tace, tayi dialing number ahmad, saide kuma baturiyar nan tafada Mata cewa batada kati," bani aron wayarki sister zan kira yaya, tawa kudin sun qare,"

bayan nabata takirashi, Amma no answer, tunawa tayi da baya daga sabuwar number, saita tura masa da text cewar saudat ce yakirata, sai bayan kusan minti biyar sannan yakira, alokacin wayar na hannu na, bansan number sa bace zuciya daya nadaga tare da fadin " hello,"
sake kara wayar yayi akunnansa saboda Jin wata irin zazzaqar murya ta daki dodon kunnansa,
" hello, hello! Wai waye ne?"
Saudat ce takarbi wayar tace "kode yayane?" Tana dubawa kuwa taga shine, dasauri tace "hello yaya,"

dasauri yadauke wayar daga kunnansa Jin muryar saudat na shirin fasa masa dodon kunne,😃
"saudat gani nan Zuwa 2 minutes"

"OK yaya," takashe wayar, araina nace wannan yayan nata Dan renin wayo ne wato shine ina masa magana ya shareni sai ihu nake da waya akunne hmm. 🤣

Munzo gate nace "sis zan hau adede ta, sai mun sake haduwa,"
"haba sister Dan Allah ki tsaya ku gaisa da yayana, Baku taba haduwa bafa,"
nace "karki damu "Marra jay" (next time) zamu gaisa insha Allah,"

tace" ke bazai iyuba sai kin tsaya,"🤣
nikuma nace" bafa zan tsaya ba, ki bari da week end sai nazo gidan, "
tace" a a, muna wannan musun wata hadaddiyar mota ta tsaya agabanmu kirar Mercedes-cls63, saudat tayi sauri ta Bude gaban motor, "

yaya tare nake da qawata ko zamu sauketa kafin mu qarasa gida,"

"ok" kawai yace tajuyo tace "sister muje,"

tashiga Gaba nikuma na Bude gidan baya nashiga, ina shiga naji wani sanyi ya dakeni na "mukayyab" (ac) hadeda wani daddadan qamshi, bansan lokacin dana lumshe idona ba, haduwar gashin idona waje daya, sai hakan yaqara yimin kyau, daidai wannan lokacin shima ya kalloni
ta glass din gaban motor,yanaso yaga wacece wannan dabazata iya gaidashi ba, hankali na yanakan wayata idona aqasa, nadago da niyyar ince masa ina wuni, karaf idanunmu suka hadu, yana sanye da farin yadi, farar hula da agogo qirar Gucci yayi kyau sosai, subhanallah yace aransa, anya wannan kuwa mutum ce? Ya tambayi kansa,
Qarar da waya ta ta dauka shiya dawo dashi daga tunanin daya afka, wata yar "kulliyarmu" ce (faculty) daukar wayar nayi tare da cikakkiyar sallama, magana takemin tana neman saudat, Zata bata book dinta, sai a kace Mata mun shiga mota tare, kuma takira saudat din wayarta akashe, shine take so nahadasu, kafin nabata amsa wayar ta katse, still wani Kiran yaqara shigowa nadago nace saudat, da zazzaqar murya ta, "ittasil biki fittal fon" (Ana kiranki awaya)
Ahmad najin haka aransa yace no wonder ashe balarabiya ce shiyasa bata gaishe niba, ashe batajin hausa, 😃
kafin yagama tunan sa yaji nace masa " ina wuni," kallo na yayi ta madubi, yakasa dauke idonsa akaina, nice na fara janye nawa idon, qiiiii kakeji yaja wani wawan birki, saudat dasauri tace "subhanallah yaya me kake tunani saura kadan kabige me wancan motor,"
saida yaseta kansa sannan muka ci Gaba da tafiya, har layin unguwarmu suka kawoni, na leqo ta window nacewa saudat "nagode sister, yayan sister nagode,"

lalle ma wato yayan sister, baikai matsayin dazata kira sunan saba 🙄

Bayan sunje gida suka zube afalo cikin gajiya, saudat Zata fara surutun nata taga hankalinsa yanakan aminiyar tasa wato waya, saita yunqura Zata tafi daki taji yace" sauda", juyowa tayi tare da fadin "na'am yaya,"

"wacece wannan?" Kasan cewar hankalinsa nakan waya yasa tayi tunanin wata yake nuna Mata, ta leqo fuskar wayar tana so taga wayake nufi, Amma bataga komai ba
"qawarki nake nufi "
"yaya feenah cefa qawata danake Baku labarin ta kullum, wannan yar zariyan," alama yayi Mata da hannu alamun tatafi kawai, tabe bakinsa yayi bayan wucewarta shide baisan wata feenah ba, tunda ba sabgar labarin qawayanta yake shigaba, tashi yayi daga falon yayi banqarensa.


** *** **

" Kaka ingaya miki saura kadan Yau muyi hatsari,"

dafe qirjin ta tayi tana fadin "subhanallahi ni badawiyya, Garin yaya? shiyasa banasan kina hawa adedetan yara masu ji da karfin balaga,🤣 yanzu saisu nemi halakaka,"

🤦🏻‍♀dafe kaina nayi da hannu na, "haba kaka tun bakiji komai ba harkin fara sharhi, nifa a mota nazo,"
"waye yakawo ki a mota,"

"yayan saudat nefa wannan qawar tawa,"

"oh naji naji, to Garin yaya zaku fadi a mota," nace "wlh tsautsayi kaka,"
rike haba tayi tace" to Allah ya kiyaye Gaba, nan Gaba karki sake shiga motarsa bazai halakaki yabarmu da koke koke ba, "🤣

nace" kaka baki ganshi ba me kyau wallahi," daquwa tayimin da hannu nide nayi daki ina dariya.






Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to yar'uwa rabin jiki, mabaruka

10


Fadawa kan gado yayi tare da lumshe idonsa, itan dai yake gani, alokacin data rufe idanuwanta, bacci yake so yayi Amma yakasa banda juyi Babu abinda yake yi, wayarsa ya janyo da niyyar Kiran tahir yafada masa halinda yake ciki, tsawon sati biyu, sai kuma yafasa, yaga shima macen ce take wahalar dashi

Yayi ajiyar zuciya dole de yakawo qarshan wannan matsalar bazai iyaba, ina da sake, shida Bama kula matan yake ba, tayaya wata tunanin ta zaiyi ta wahalar dashi, shida ake sansa, ya mutsa sumar kansa yayi sai sheqi take (ahmad abinda kayi...)
Dayaga dai tunanin Babu inda zai kaishi saiya tashi yayi shirin masallaci.




** ***

"Kaka na gaji, na gaji da wannan karatun wallahi, so nake naganni kusa da iyayena,"

"a a

Please Login or Register in order to submit comment