Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "yanzu yaushe zaku tafi Spain din?"
Tahir yace "next week zamu wuce mu uku ne zamuje, insha insha bazamu wuce 1 year ba"


** *** **


Suna zaune shida ita adakin ahmad nada, komai tsaf kamar yana ciki har yanzu, "Kaji de abinda tazo mana dashi dazu,"
ahmad yace "Amma nayi mamaki mamy,"

ya furzar da iska mai zafi, yace "Amma Babu komai mamy insha Allah zan gyara,"
mamy hakima tasha fa kansa, tace "kayi hakuri ahmad nasan abinda kakeji akwai ciwo, Amma kadaure kaci jarabawar da Allah yadorama,"
dora kansa yayi Akan kafadarta, ya lumshe idonsa ba tare dayayi magana ba


** *** **


After 2 months, a wannan lokacin karatu yayi mana nisa, ina shirin kammala degree Zahra kuma tana shirin shiga level 4
Da ita muka shirya zamuje hutu mudawo, karatu muke sosai, Amma mukhtar ba zaije hutu ba, tare dashi zamuyi masters din, Dan haka shi zai zauna ya nema mana admission din

Agidan su ahmad kuwa rayuwa tana tafiya yanda yakamata, haqqi ne yana sauke Mata tunda tahadashi da mahaifansa, saide abinda yake Mata ciwo shine yanda yake Kiran sunan feenah, feenah, idan sun kasance tare yayin raya sunnar manzo, abinda yadami laila kenan, Amma Zata yi maganin hakan


** *** **


Lokaci na tafiya komai na sauyawa, harsu feenah sun kammala school, sunyi bikin graduation, Amma bata karbi result dinta ba, mukhtar zai karba musu yanema musu admission kafin tadawo

"Kinga wannan kayan zaiyiwa twins din sister husna kyau sosai ko?"

Zahra tace "sosai ma, kuma gasu iri daya babu banbanci,Amma feenah sai tsaraba muke siya banga kin siyawa izdihar komai ba,"
feenah tace "ke share ta," duk da acikin ranta, tanasan hakan,
Zahra tace "wallahi bazai iyuba,"
haka taita daukarwa baby kaya masu shegen kyau, dole saida feenah tasiya mata suka bar wajan, Gaba daya Cikin kwanakin basu da zama sune nan sune nan, suna shirye shiryen tafiya gida,
Agajiye suka dawo gida, suna Zuwa suka zube aqasa suna maida munfashi, feenah tace

" bari inkira kaka"
Tana kira kuwa kaka ta daga, cikin qara feenah tace "kakaaa"

Kaka tace "oh ni rabi'atu nafi zaki kashe min kunne"

Feenah tasa daria tace "to albishirinki"

Kaka tace "goro fari qal nafi"

Feenah tace "next week zan dawo"





Mrs Usman ce
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

42


Kaka tace "keni nafi wannan yaran naku saiku, nikam bazan gane Shiba,"
feenah tace "to rana itayau zan dawo," kaka tace "ayyiriri, alhmdlh har karatun, yaqare ko?"
Feenah tace" eh, Amma hutu zanzo inyi na wata daya saina dawo inyi shekara daya "
Kaka tace" to Allah yakawo ki lafiya nafi,
Amma idan ki kazo ai anan zaki sauka, saikinmin kwana biyu sannan zaki wuce ko? "
Feenah tace" kaka me kika ce? Inaaaa banyi miki alkawari ba kaka, bazan zauna ba, zaria zan wuce kai tsaye"
, kaka tace "to ai shikkenan nafi, dama wani abin dadi ne zan hada miki," 🤣


feenah tace "a a wallahi kaka rike abin ki, nikam wajan mama zani,"

kaka tace "to ai shikkenan," nace "eh din, sai anjima tsohuwa," nakashe wayata

Zahra tace "kai feenah bakida dama, Akan ki kwana biyu agarin namu, kika sanima kokiyi kwalli da gwanin ki," 🤣

nace "Zahra Dan Allah dena yimin zancan mutumin nan," kama bakinta tayi da hannun ta, tace "shikkenan zance ya wuce
Yaushe zaki rakani unguwa zanje inyi sallama da qawayena," "wanne unguwa?" Na tambayeta
Tace "ma'amura,"

nace "saide wajan yamma, sai muje"
Tace "ok"


** *** **


Afalo ta sameshi yana aikin danna computer yana daga kwance, Dagashi sai singlet da gajeran wando, ga ruwa nan agefensa, tazo cikin shiri tace

"majnunun laila, ni zan fita,"

ahmad ya kalleta da kyau, shi sai maganar tata ma tabashi daria, wai majnunun laila,🤣duk yanda yaso boye dariyar sa saida ya murmusa, cikin murmushi yace Mata "aiba saikin tambayeni ba, kawai kije duk inda zaki,"

laila tacika tayi fam,😠 aranta tace wato saboda baya sona, baya kishina, shiyasa zai fadi haka, har murmushi yake yana murna, saboda Zata fita tabar gida, kallansa tayi tace "ok thank you,"

tayi gaba, da kallo yabita, yana murmushi, wai majnunun laila, ina laifin ma tace majnunun feenah, cigaba yayi da aikinsa


** *** **


"Mom nagaji, gaskiya nagaji da wannan zaman na kulle, haka kawai kullum mutum yana zaune agida, Babu fita yawon nan nabude ido,"

hajiya salaha tace" to menene laila, ai kema hakan kamar hutu ne agareki "
Laila tace" sannan mom duk lokacin danake tare dashi, bashida aiki saikiran sunan wata wai feenah, bazai iyuba mom, nida biyan buqata wata da samun waje azuciyar sa, wallahi dazan ga wannan yarinyar dayake kiramin ita cikin dare acikin kunne na, wallahi saina Mata illa "
(niko Amnah nace to ina zaki ganta, shima nemanta yake) 🤣🤣

" sannan har yanzu shiru, Babu alamar ciki awajena, mom ko batan wata bantaba yiba
Maganar data kawoni kenan, gaskya idan naqara wata uku, Zuwa hudu bansamu ciki da kudin da nakeso ba, to zaki ganni da kayana nakashe auren na dawo gida," hajia salaha tace

" Toshiknn yanda kikeso yata haka za'a yi, danni dama wannan auren kawai de Dan yaron yana da kudi ne shiyasa na yarda, Amma ace yaro kullum fuskarsa cikin qunci "🤣

Cikin ransa yace kina kashe auren ki kuwa daga ke har uwarki saide kufuce kubarmin gidana, nagaji da halinku, maganar alhaji bukhar kenan daya Gama Jin duk zancan dasuke


** *** **

" Momy kin ganta ko, Allah saikin bani alawa ta,"
inji mima kenan dasuka zo gida tare da maman su husna, Ana shirye shiryen zuwan feenah gobe 😃
Husna tace " baby, bakyaji ko, wannan fa yarinya ce, qanwarki ce kibata alawarta saina baki sabo,"

izdihar tace" to ai anty itace tafara daukemin nawa,"

mima tace" Allah bani bace mama ce, "

mama datayi shiru tana jinsu tace" kaiii Allah mom bani bace mima ce,"

husna tace" ke baby waye ya dauke miki alawa? "
Izdihar ta kallesu Gaba daya takasa banbance wacece ma mima balle mama,🤣 sai tace" dukansu, dukansu ne anty, shiyasa nima nadau wannan kuma bazan Baku ba "
Mima tasa kuka, tace
" mom kingani ko "

Husna tace" a a bazaku samun hawan jini ba, ina Zuwa, "daki tashiga ta dauko musu wasu tabasu
Mama datake gefe tace
" yafi miki de, ai wannan yaran su kadai ma aka barka dasu sun isheka,"🤣

husna tace" Allah mama baby bataji," daria mama tayi, tace" ai duk halayan nafeesa babu wanda wannan yarinyar tabari, Kuna yara itama hakan take "


** *** **


" Yallabai dama ina neman afwa ne, yarinya ta tagama karatu zatazo daga makaranta zanje in dauko ta, in kaita can gida, " cewar Ammu

ahmad yace" haba hassan, aibabu damuwa kwana nawa zakayi?" Ammu yace" jibi zan dawo insha Allah,"


ahmad yace" babu damuwa, Allah yakiyaye,"

godia Ammu yayi masa tare da ficewa


** *** **


Dagashi sai Abba ne amotar dayazo daga zaria yadauki Ammu anan kano suka wuce airport, dayake ta kano zasu sauka, saida suka biya gidan da company su ahmad suka bawa Ammu, suka dauki maimuna sannan suka tafi Gaba daya

Jira kadan sukayi, jirgin su feenah yasauka, bayan tagama komai ta futo, kawai ganinsu tayi daga nesa aikuwa da gudu taje ta rungume anty maimuna, Abba sai daria yake, yace "a a nafeesa angama karatu kuma,"

feenah cikin murna tace
" eh wlh Abba,"

Zahra ce tazo suka gaisa itama tayi wajan yan gidansu Abba yace "a a hassan mu qarasa mu gaisa dasu mana," har feenah duk sukaje suka sake gaisawa da iyayen Zahra, sannan sukai sallama suka tafi, feenah tace Mata "sai munyi waya,"
hannu kawai Zahra ta daga Mata

Direct zaria suka wuce, suna Zuwa husna ta futo da gudu ta rungume feenah, Gaba daya gida de kowa yana ta farin ciki
Mama baki yakasa rufuwa, gata ga feenah, ta kwantar da kanta Akan cinyar mama, Abba yace
" mamana Hali de yana Nan," aka sa daria, takama su mima sai kallansu take, tace "anty husna basa kama dake yaran nan,"

husna tace "eh da babansu suke kama,"

Taga kowa Amma bata ga baby ba, to ina take,🤔 kuma taga babu wanda yayi maganarta,
Batasan lokacin da maganar ta futo ba, kawai de ji tayi tace

" mama ina baby?" 🤣


Mama tace "aiji nake bazaki tambaye taba, tana nursery, yanzu zaki ga tadawo"
Anty maimuna tace "baby ta qwace Mata fada awajan mama kuma yanzu bata ganta ba ai dole ta tambaya," wannan maganar da anty maimuna tayi, shiya tabbatar min da batasan baby yata bace, kenan Ammu bai fada Mata ba, lalle wadannan mutane suna kaunata

Aikuwa kamar jira take su Gama magana, sai gata da gudu ta shigo, tana cikin uniform dinta da school bag dinta a bayanta, kayan yayi Mata kyau sosai, tana Zuwa falon taga baqi dayawa, batabi takan kowa ba tayi wajan mama da gudu, ta rungume ta, wata sallamar suka sakeji abayansu, wani yaro ne yashigo yace
" mama kice baby tabani kallo kallo na,"
saida yafada sannan mama takalli hannun baby, aikuwa yana hannun ta, mama tace
" bashi abinsa kafin na dakeki," baby tace "to wayace shima ya tsokaneni,"

yaron yace "karyane niban tsokanetaba," mama ta karbi abinsa tabashi, tace " baby nahanaki rigima, bakyaji ko," turo Dan qaramin bakinta tayi gaba, tace "to mama nadena"
Ammu ne yace "baby ba gaisuwa?"

Wajansa taje suka gaisa, tana juyawa taga husna Takoma wajanta da gudu, feenah tana kallanta, husna tace " baby ga anty Baku gaisaba,"

kallanta ta maida ga feenah, suka zubawa Juna ido, baby sai kallanta take, tasauri Takoma wajanta, tace" ya sunanki? "

Feenah tace" baki sanni ba?"
Baby tace" daga ina kike? "
Feenah tace" makaranta," baby tace" Amma zaki zauna damu bazaki gudu ba irin na anty husna"
Feenah tace "eh zan zauna," baby tace

" to Amma... "

Mama tace "baby barta ta huta tagaji banasan tambaya kinji,"

Abinci mukaci nayi wanka na tafi daki nakwanta, baby ce tashigo Dakin ta tsaya abakin kofa, tace
" sabuwar anty in shigo?"
Feenah tace " shigo," tana Zuwa tahau jikinta, takama kallanta, feenah tace "baby lafiya? Wannan kallan fa,"

baby tace "ina sanki,
Nan dinki nake kalla irin nawa," takai hannun ta kan dimple din feenah,
Feenah tace "um nagani, yanzu bacci zanyi, nagaji, tashi kije wasa,"

baby tace "tonima zanyi baccin," 🤣

feenah tace "to kwanta kiyi" , kwanciya baby tayi, feenah tana rufe ido bacci ya dauketa, baby tatashi a hankali taci Gaba d kallanta, tanata daria ita kadai
Matsawa tayi jikinta tashiga jikinta sosai nan itama tayi bacci

Mama ta kalli husna tace, "kiramin baby nasan tanada home work, yanzu haka wasa take," husna na fita ta duba ko ina babu baby, Dakin feenah tashiga, kawai tagansu sunata bacci, husna tace "mama zokiga" 🤣

, mama nazuwa tagansu aranta tace Allah sarki, uwa da d'a kenan soyaiyar nan de dole saita wanzu atsakanin su
Juyawa tayi, tace "ashe bacci suke," tabar husna anan
Itakuwa husna kallansu take cikin birgewa

Gab da magrib nafarka, ina juyi naji mutum ajikina, kallanta nayi da mamaki, yanzu yarinyar nan saida ta kwanta ajikina, kallanta nake da mamaki nashafa kanta, Natashi zan shiga wanka, ina motsawa itama tatashi, cikin muryar bacci, tacemin "nima natashi," 🤣

nace "to jeki wajan mama," tace "wanka zakiyi?" Nace " eh,"

tace "nima to kiyimin wankan"
Nace cikin raina Yau nagamu da jaraba,🤔 nace "jeki mama tayi miki," tace "um um ni kece zakimin" , girgiza kai nayi nashiga wanka, na shirya nabarta,dataga zan fita nabarta adakin kawai yarinya tasa kuka,🤣

tace "Allah saikinmin," kallanta nayi kawai, Babu yanda na iya dole saida nayi Mata wankan

da daddare nabawa kowa tsarabarsa yan biyu sai murna suke, kayan su iri daya su ribom su takalma, saina husna itama kaya, sai na Abba da mama kuma,
Baby cikin sanyin kuka tace" Toni ina nawa?" Feenah tace " ai banda ke"
tajuya wajan mama tace
" wai mama banda ni,"

mama tace "yi shiru mana baby kefa sai ragwanta ko?"
Feenah tayi daria tace
" toga naki," cikin murna izdihar tace "yeeee"

Haka ta ishi kowa da surutun kayanta ranar, washe gari su Ammu suka koma suma da tasu tsarabar, tare suka koma da husna, gidan ya rage daga su sai su, da yamma su aysha sukazomin sannu da Zuwa da ita da kala da kaka sai baba Adamu, sun jima sannan daga baya suka koma gida

Sati na daya agida, ina kwance afalo, ina kallo, dayake da weekend ne Babu school saiga baby ta futo daga daki tace
" sabuwar anty"
Nace "menene,? Kinfa dameni baby,"

hannun ta ta dora Akan maqogaronta tace "anty kinji zuciyata tauri ne da ita" 🤣

Na kalleta naga inda hannun ta yake, batama San inane zuciyar ba,🤣

nadaura hannu na Akan maqogaron nace "um aikuwa zuciyar taki tauri ne da ita kamar ta ubanki" 🙆🏻😳

Mama da futowarta kenan daga daki taji wannan firar tasu, cikin mamaki tace " nafeesa kinada hankali kuwa?"






Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

43


Baby ma tazaro ido takama bakinta,🙊cikin mamaki tace "da Abba kike?"
Mama ce taqaraso wajan da sauri, ta dakawa feenah harara, taja hannun baby sukabar wajan

Dafe kaina nayi da hannu na, oh ya Allah, meyasa na aikata haka? Yakamata indinga daidai ta kaina Akan yarinyar nan

Tashi nayi natafi daki

Mama ta kalli izdihar tace "baby, idan anty tana hutawa kidena Zuwa wajan ta kinji?"
Baby tace "to mama, Amma ina Santa,"

mama tace "naji, naji baby nasan kina Santa, Amma kidena damunta kinji, oya dauki littafin ki, kiyi karatu"


** *** **


"Gaskya my heart yakamata kazo mana hutu, yanzu fa watanka biyar," tahir yace "maman mima, tunda nayi wata biyar ai kamar yaune zan dawo, ki qara hakuri, yakika ga autar mama?Da fatan tazo lafiya,"

husna tace "lafiya kalau, takusa Zuwa minma," tahir yace "eh gaskiya kam yakamata, Allah yakawo ta lafiya,"
husna tace "amin"


** *** **


"Mama zanje maqota mu gaisa na dawo,"

"to saikin dawo, ki gaishe su,"
baby tayi sauri tatashi, tana kade hannunta, zatabi bayan feenah,🤣

mama tace "zo nan izdihar, karkije aturaki titi da niyya mota ta kashe ki, 😃"
buta tadauka Zata shiga toilet, feenah ta girgiza kai kawai ta fita, izdihar naganin mama tashiga toilet, tayi wuf tafice da gudu, 🤣
Nayi nisa atafiya, naji anjamin hijabi na, cikin murna tace
" yeee nataro ki, "
kallanta nayi da mamaki nace" ke meya futo dake daga gida? Ba mama tahanaki ba?" Kallo na tayi, tana murmushi tace

" to ai inaso inbiki, Dan Allah zaki tafi Dani wajanki idan zaki koma inda kika zo?"
Feenah tace" nima inasan tafiya dake, Amma bazai iyu ba, kiyi hakuri kina Zuwa school kuma gasu mama da Abba, da qawayen ki na school,"
cikin murna tace

" eh tona fasa binki, Amma de ina sonki"

Nima nace "ina sanki baby," tafiya mukaci Gaba dayi, nace "baby baki gaji bane? Oya zona goyaki,"
tsugunna wa nayi tahau bayana, muka tafi, tace " sabuwar anty, kina goyani kullum, mama bata goyani,"

nace "baby bakisan sunana bane?"
Tace "emana, ya sunanki?"
Nace "sunana baby nima, irin naki,"
tace "laaa ashema sunanmu daya,"

nace "keni bansan shirme sunana nafeesa," tace "nide baby zance," 🤣

nace "kina fada ina bige wannan bakin naki," daria tasa, ahaka mukaje unguwar kafin mudawo tayi bacci, mama na falo taga mundawo, tace
" ashe ta biki," nace "eh mama, ai tayi bacci ma," mama tace " itama de batada zuciya,"

murmushi nayi kawai na kyale mama
Naje na kwantar da ita

Da daddare ina karanta novel awayata, nayi wanka nayi shirin bacci, saiga baby tazo da littafi tace, "sabuwar anty inzo ki koyamin karatu?" Nace

" eh, zo ki zauna,"
ta zauna nafara yi mata, kuma sosai nafahinci yarinyar tanada kokari, nace "to yimin bayani,"

filla filla tafara yimin bayanin, nashagala ina kallanta, har muka Gama, nace "to ki tashi kije ki kwanta,"

matsowa tayi jikina tace
" um um, sai anjima tukun," 🤣

nace "to karfa kimin bacci mama tazo tanata nemanki," tace "nifa anan zan dinga bacci, nabar Dakin mama," 🤣

nace "a a baby yahaka,"

tace "Toni wajanki nakeso," tafadi haka kamar zatayi kuka, nace
" toyi shiru, kwanta,"

Maimakon ta kwanta Akan gadon, saita matso jikina ta kwanta, tace
" sabuwar anty,"

nace "baby kidena fadamin sunan nan,"
tace "to, taci Gaba da cewa kema kina sona ko?"

Kallanta nayi nace," sosai ma baby, ina sonki, kamar cikin duniyar nan baki daya,"

murmushi tasaki bata sake magana ba, bacci yadauketa

After 1 week
Nagama shirya kayana tsaf, nace " to mama zan tafi, Abba saina dawo,"

Abba yace" to mama na idan kinje ki gaida su husna," nace" to zasuji Abba, "
Jakata na dauka, aikuwa baby tasa kuka tariqe jakar
," Allah Abba zan bita, nide bazata tafi tabarni ba,"

Abba yace" ke izdihar, banasan shirme kinji ko, idan kin bita makarantar fa? "
Nima idona yayi ja, Inason tafiya da ita, acikin raina, to naga su mama basu ce intafi da ita ba,
Na dago kai nace" to Abba kabarta mutafi," Abba yace" mamana school dinta fa?" Nace
" zan shiga makarantar inyi musu bayani", mama tana kallanmu tace "nide nafeesa karki dauki yar nan kinga babu idonmu ki cutar da ita," 🤣

nace "mama wallahi Babu abinda zai faru," tace "Toshiknn"
Aikuwa aka hada mana kayanmu awata jakar, dole Abba ne yace shi zaije school din ya nema Mata alfarma
Amota haka taita bani labarin school dinsu, gidan husna direct muka sauka, ummi sai nan nan take damu, Gaba daya bangarenta muka dawo, sai dare muke komawa part din husna, washe gari agidan kaka muka wuni, nida baby dasu mima
Har mijinta tahadani dashi mun gaisa, yace shima yaso yana gida nazo, Zahra ma takawo min ziyara, haka muka wuni muna bawa anty husna firar Sudan
Munje gidan kala ma, mun wuni, aysha anata shirin biki, mai gyaran jiki tanata fama, wani watan za'a sha biki

Duk wani wajan yawo da wasan yara babu inda bankai baby ba, muyi ta pictures nida ita, muna wanka zan zare ta mu shiga gari, mune gidan zoo, mune Park, sosai munsha yawo,
Nima na kaiwa Zahra ziyara nida baby, haka tabawa baby sweet sosai, har su pictures sunyi dasu video sunata shirmansu
Satin mu daya a kano muka dawo gida

Cikin sati biyun danayi agida, sosai muka shaqu da baby, bana iya bacci ba tare dana jita ajikina ba, pictures, videos duk haka nake yi Mata da wayata, wani kuma muyi tare, mun shaqu sosai, kuma mun saba, ahaka har sati biyu na tacika, nafara shirin komawa makaranta
Ranar dazan koma, saida aka yiwa baby wayo tatafi school sannan muka tafi kano, nahadu da Zahra muka tafi airport, ina kuka mukai sallama dasu mama da husna dasuka rakoni
Kuka na daya baby, bansan yaya zataji ba idan taga bana nan

Muna sauka kuwa nakira su mama nace musu mun sauka, tacemin ga baby nan tana zazzabi, tun rana take kuka, taga bana nan, ni kaina kuka nasawa mama, tace" to yanzu kukan zakiyi kokuma so kike nima ki karyamin zuciya, ga yarinya babu lafiya", haka mama taita min fada har mukai sallama


** *** **


After 1month, alhmdlh nafara karatuna cikin kwanciyar hankali, kusan kullum sainaji muryar 'yata nakejin dadi,🤣
wani lokacin ina karatu, haka nake bari, sainaji muryar ta sannan zanci Gaba da karatun, Allah Allah nake ingama karatun nan in koma kusa da yata, inde ina missing dinta videos dinta nake kallah kokuma in kalli pictures dinta, haka mukhtar ma, har pictures dinta natura masa


** *** **


I V yake ta rabawa abokansa na office, yana cewa "wallahi wata yata ce, za'a yi bikinta wannan weekend din, Dan Allah ku daure kuje"
Ahmad yafuto cikin sauri yana waya, zai fita daga company, Ammu ya karasa suka gaisa, ya miqa masa iv din shima yace "yallabai ina gayyatarka Zuwa wajan bikin wata yata da za'a yi,"
ahmad ya karbi iv din yace "hassan ko itace wadda kadauko daga school kwanaki?"

Ammu yace "a a ya'uwarta cede,"
ahmad yace "Toshiknn insha Allah zanyi kokari inzo nima,"

daga haka yayi waje


** *** **


"Izdihar karfa kiyi wani wajan, wanka kawai zanyi inzo mutafi, kinga abbanki yaji ma da shirya wa,"
baby tace "to mama"
Yar babynta ta dauka, tafara yimata kitso, tanata waqa, har mama ta futo, cikin shiri, izdihar ta kallah duk tabata kwalliyar ta, janyota tayi tagyara Mata, taqara gyara Mata parking din gashin ta, sosai idan ka kalleta zakace yar turawa ce, kwata kwata bazakace tanajin wani yare hausa ba, Riga da wando ne ajikinta ja, tayi kyau sosai yarinyar kamar ka sace ta kagudu
Mama nagama komai, suka dau hanya
Gidan kala suka sauka, anan suka tarda su husna da yan biyunta harda ummi
Anata hidimar biki, husna na wajan amare anata shirya amarya 🤣

Karfe biyu daidai aka daura auren aysha da angonta nasir,akofar gidansu,
izdihar na Zuwa wajansu mama da mima, nan suka fara wasa, Ana wasa rimi rimi, anan ta nuna halin nata na tsokana, 🤣🤣
mama da mima suka biyo ta da gudu, suna saisun Rama
Tafita waje da gudu

Suna tsaye shida abokan ango sunata gaida shi, kasancewar sa sanannan mutum, sai murmushi yake, yaci manyan kaya cikin farin yadi mai tsada

Kawai yaji anbigeshi, kuma anriqe masa kafa anacewa
"boyeni, boyeni," 🤣

juyowar dazaiyi yaganta, gabansa yayi mugun faduwa, tsananin kamar dasuke da itane yasa cikin rawar murya Ahmad yace "MY FEENAH"






Mrs usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub


Dubun godia gareki, yanda kike bibiyar novel dina, nima ina tare dake, kyautar wannan page izuwa Garki
@RESPECTABLE



45


Tahir yaci gaba dacewa, "Amma hakan bawani matsala bane, idan muka dora shi Akan magani insha Allah za'a samu abinda akeso"
Ahmad shiru kawai yayi yana kallan tahir
Laila nagama Jin wannan batun tasaki tsaki, fuuuu ta tashi tafice daga office din har tana bigewa da kujera Amma ko juyowa batayi ba

Ahmad ya sunkunyar da kansa, tahir yayi shiru,shi kansa ya rasa da wanne kalma zaiyi amfani da ita wajan bawa aminin nasa hakuri, saboda haka yatashi daga kujerar dayake kai, yadawo ya tsaya agefen ahmad yafara bubbuga bayansa alamun rarrashi,

ahmad yadago kansa cike da damuwa yace
"meyasa tahir? Meyasa?" Nan danan qwalla ta cika idonsa

Tahir idansa yakada yayi jajir, yace. "Ahmad kayi hakuri mana,ni dakai duk dayane ahmad, kaga karkasa damuwa aranka, akan abinda yafaru, ni inde haihuwa ce wallahi nahakura ahmad kadauki su mama, nabaka su, inde Akan yara ne zaka daga hankalin ka, nina hakura, banaso ka sake shiga cikin damuwa ahmad, tunda kasan abinda yake damunka, ba'a San kacika tunani "

Ahmad ya kalleshi yace
" tahir tabbas abin da ciwo, Amma Babu komai, damuwa ta daya tahir meyasa baka sanar Dani hakanba tunda farko?"
Tahir yace" ahmad tayaya zan tabbatar da abinda nake tunani bayan bakada aure alokacin?
Ni kaina hasashe nake a wancan lokacin
Ashe abinda nake tunani zai zama gaskiya, kaga yanzu tashi muje mu lallaba madam mu bata hakuri "
Ahmad yace" tahir yi zaman ka, kabarta kawai idan nakoma gidan zamu tattauna nida ita,ni fishinta bai wani dameni ba, saboda bana kaunar ta, ni badan kada nayiwa Allah butulci ba, danace gara ma da bazan iya haihuwar ba, dade inhada jini na da laila,saboda banga tarbiya awajanta ba bare yaran dazamu haifa su samu, sannan tahir kabar maganar su mama, kaimafa su kenan awajanka tahir, ummi tanasan yaran Sosai saboda me ni zan dauke muku su,
Tahir inajin kaunar izdihar sosai araina, banajin iyayen dasuka haifeta ma, zasu kaini sonta 🙆🏻
ni idan aka bani itama ta isheni rayuwa
Katayani da adduah tahir Allah yasa iyayenta su amince da buqatata "

Tahir

Please Login or Register in order to submit comment