Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

to insa zai turo min kati yanzu, godia nayi masa gamida saka sim card din nawa

Aikuwa ya turo katin 1k, nakira shi nayi masa godia

Ina kwance adakina, da daddare, nakira layin Zahra, Allah yatemakeni nasameta, tace shine tun dadewa kikaqi dora sim card dinki, sai nemanki nake, nace "yi hakuri Zahra, wallahi bana cikin kwanciyar hankali nane"
Zahra tace "subhanallah me yake faruwa?"
Nan take nabata labarin abinda yafaru game da baby
Tace "anbada ita, abun kamar almara, Amma nikam banji dadi ba, saide ta wani Fannin kuma sunada gaskya," nace " hakane"
Tace "to kiyi hakuri feenah, haka Allah ya tsara mana, yanzu yaushe zakizo kiga babyn?"
Nace "cikin satin nan zanzo Zahra"
Tace to saikin zo, Allah yakawo ki lafiya, nace "amin Zahra Nagode ''


** *** **

Da asuba mama tajira taji shiru shiru bataji motsin tashi naba, aranta tace may be baccin gajia nake, anjima zan tashi

Da aka jima dinma de haka taji shiru, tana Zuwa ta leqa dakina, ta ganni na tuqun qune cikin blanket, tace "auta tashi kiyi sallah mana ''

Natashi dakyar, nace mama wallahi sanyi nakeji, tace yanayin ne haka, kinsan sanyi ya matso
Natashi nayi sallah nakoma bacci,
Da gari ya waye ma haka, mama tajira taji shiru ban futo ba, taleqa Dakin, kawai sai ganina tayi ina rawar sanyi, da sauri taqaraso tana tambaya ta lafiya?
Cikin rawar murya nace "zazzabi mama"

Dasauri tayi waje takira Abba, Babu bata lokaci muka tafi asbiti
Ansamin qarin ruwa, sai allurai da aka min, likita yace su kwantar da hankalin su babu abinda yake damuna

Kawai damuwa ce araina, yakamata su kiyaye abinda zaina batamin rai saboda hawan jinin danake tare dashi

Abba da mama lokaci daya suka hada baki wajan fadin "hawan jini doctor?"

** *** **

Tsawon kwana daya dayayi yana jiran Kiran feenah, duk yadamu, saida saudat tayi dana sani yafi aqirga,
wata sabuwar qaunar tace take shiga cikin jini da gangar jikinsa, fatan sa daya feenah takira waya


** *** **


" Yanzu auta saboda Allah dama baki cire maganar baby aranki ba?
Har hakan yasa doctor yace mana kinada hawan jini, haba nafeesa, kiyi hakuri mana"

"Abba kayi hakuri insha Allah nadena, Amma ku kwantar da hankalin ku, tun lokacin haihuwar baby dama inada hawan jini"

Sanin dasukai idan mutum zai haihu mafi yawan Mata sunada hawan jini, hakan ne yasa suka yarda da maganar ta, Abba yace
" to shikkenan, ga magungunan ki nan kidaure kisha kinji," nace
" to Abba"

Mama ce takawomin abinci naci sannan nasha magani na kwanta

** *** **

After 1week
"kaji Abba Dan Allah kabani, Allah a hankali zan tafi,"

Abba yace "a a mamana tafiya daga zaria Zuwa kano, ke kadai, kuma ni nasan hannun ki bai fada ba da driving din nan,"
Cikin shagwaba nace
" Allah Abba a hankali zanja, kaji Abba
Kaga inada kaya dayawa, ga tsarabar su anty husna da yara,
Amma kaga idan kabani motar shikkenan '
Abba yace "Toshiknn naji, Amma kitafi a hankali banasan gudu," nace" to Abba insha Allah"
Da saurina kuwa nasa duka kayan aboot din motar
Nayiwa su mama sallama tana cewa yaushe zaki dawo nace kawai sai kun ganni mama, tace" na gaida kowa da kowa'

Agidan kaka nasauka saida nawuni agidanta muna abinda muka saba, sannan natafi gidan husna,
Sunyi mamaki sosai dasuka ganni da motar Abba, tahir yace "gaskya nayarda autar ce, tunda Abba yayarda yabaki wannan motar," dukanmu mukasa daria, kamar mun saba dashi dama haka naware mukai ta fira
Sai jana yake da fira, harda cewa ban hadashi da mukhtar ba, nace karya damu gobe zan hadasu su gaisa
Husna ce tace" yaushe zanje inga baby" nace
" gobe da safe insha Allah"


** *** **

Yana gama cike ciken wasu takardu yadawo da hankalinsa ga baby datake game da kayan baccinta ajikinta, yace
" yauwa baby nikam Yama sunan sabuwar anty?"
Baby tasa daria tace
" uncle kawai haka sunanta, nima haka nake kiranta"

Ahmad yace "kai baby, kuma bata taba fada miki sunan taba?"
Tayi shiru alamar tunani sai can tace "yauwa natuna
Tataba cemin sunanta nafeesa"
Gabansa ne yayi muguwar faduwa







Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

52


Yace " me kika ce baby?" Tace "nima haka naji mama tana fada Mata, uncle sabuwar anty tana sona, kaima kana sona ko?"
Kamar wani dolo yace
" emana,"

tace "to kamar yaya?"
Yace "kamar cikin duniyar nan"
Daria tasaki tace " to ai itama haka tace,"

ahmad yace " wa?"
Tace "sabuwar anty mana," 🤣

Gaba daya jinta yake kawai Amma azahirin gaskya gabansa mugun faduwa yake, yace "baby tashi kije ki kwanta"
Turo bakinta tayi gaba tace "uncle nifa bangama game dinaba," yace " bani wayar nan kije ki kwanta,"

tace "to ai Babu school ko"
Yace "saboda babu school bazakije ki kwanta ba, oya tashi,"
Tashi tayi tatafi cikin fishi, yadauke wayarsa jikinsa asanyaye
Ganin tatafi ko sallama babu yace " baby,"

tajuyo yace "zonan,"

tana Zuwa yanuna Mata kumatunsa,
Tagane abinda yake nufi, Dan haka tayi masa kiss tace "bye bye, uncle," yace "yauwa baby na, bye"

Tana fita yafada duniyar tunani, karfa ace qanwar feenah ce wannan yarinyar
Nafeesa!
Ya maimaita sunan aransa, kai gaskiya da sake, dole gobe da sassafe yashirya yaje zaria
Kawai zai tambayi mama bayan husna da baby batada wasu yaran ne? To kuma bazatayi tunanin wani Abu idan yayi Mata wannan tambayar kai tsaye?
Kai da sake, gaskya de dole gobe yakira mama awaya, kokuma de yaje Garin da kansa yaji gaskyar al'amari

Da wannan tunanin ya kwanta, Amma zuciyar sa Gaba daya banda faduwa babu abinda take

Asuba ta gari hammad


** *** **


"Kawai kisa Mata su acikin wannan jakar nakega ai tafi girma ko?"

Nace " yauwa anty husna kin kyauta, ai danma wannan teddy's dinne dayawa, da bazasu cika jakar ba"
Tace "hakane, nikam da kinji tawama Dakin sani, dabaki siyo dayawa ba, tunda wannan gidan bana tunanin baby Zata rasa komai," 🤣


Nace "zanje de inga wannan gida, inga me ake bawa baby data manta da maman ta"

Husna tace "ok yanzu kinayin yar da ita kenan,"

nace "dama ina yi, alkunya nake muku," 🤣

cikin daria tace "Allah ya shiryeki feenah" nace "amin"
Ina gamawa nace "bazaki tafi wajan mijin kiba?" Tace "aikuwa kamar kinsani, nasan yana can yana jirana, bari natafi" , ta miqe Zata dauki
Mima nace "sister barsu kawai, barsu mu kwanta"
Tace " ok"
Adduah nayi musu nakashe wutar Dakin na kwanta, ina Allah Allah gari ya waye inje inga baby nah

Asuba ta gari nafisan mukhtar


** *** **


"Mom kudin hannu na fa sun qare, kozan samu ko dubu hamsin ne awajanki?"
Hajia salaha tace "yanzu laila bazakiyi wa kanki fadaba? Kikaga de duk abina nayi hakuri, ina zaune agida lafiya, har Allah yasa hankalin babanki yadawo kanmu yayi hakuri ya maidamu, Amma shine ke koda Yaushe kina cikin yawo?"
Laila ta yatsina fuska, tace "mom
Bazaki ganeba
Tunda nace bazaki ganeba, bazaki gane dinba
Inada party anjima kadan, bazan samu damar dawowa gida ba, sai wajan dare, nina tafi"

Hajia salaha tana " laila, laila tsaya mana,"
dakyar ta tsaya, hajia salaha ta tashi tace
" yanzu ke laila Kodan abinda yafaru a asbiti ba zaisa ki nutsu ba?"
Laila tace "no ba damuwa mom, ni kinsan haihuwar mafa wani lokacin matsala ce
Yaran sun cika damuwa, so ni ban wani damuba
, am mom kina batamin lokaci, ni nayi nan" 🤣

Tana fadar haka tayi waje
Hajia salaha ta rafka uban tagumi tashiga DANA SANI Akan tarbiyar data bawa laila


** *** **


Yana tafiya Akan titi, yana waya sai murmushi yake, daka ganshi kasan yana cikin walwala
"Please feenah ta, kidaure idan kinje ki hadani da baby naji muryarta nima"

Feenah tace "karka damu mukhtar, insha Allah ina Zuwa zan hadaku," yace

" to shikkenan ki kulamin...." Maganar dabai qarasaba kenan yaga anrufe masa fuska da wani baqin qyalle
Wayarsa tafadi aqasa, daya daga cikin mutanan ne, yadauki wayar yashaqewa mukhtar wuya, yace" kana magana wallahi ina aikaka lahira"

Feenah tun tana hello hello, taji shiru saitace may be babu network ne, Dan haka tasaka Wayarta cikin hand back dinta
Baqar abaya nasaka, nayi rolling da Dan kwalin rigar, sai Jan baki danasa pink, nataje girata nagyarata, nayi kyau sosai acikin rigar, inata zuba qamshi na futo falo, naga husna tana hada break fast, naje nakarba ina kaiwa dining
Tace "bade harkin Gama shiryawa ba," nace
" wallahi inasone naje na dawo da wuri, inaso inje wajan Zahra"
, ina Gama kaiwa dining, naje na gaida ummi na dawo

Munfara break kenan tahir ma yafuto cikin shiri, husna tace " Amma de Yau Babu inda zakaje ko?" Yace "babu inda zanje my heart ina gida tare da iyalina"
Murmushi tasaki
Nace " yaya tahir ina kwana," kallo na yayi cikin ransa yace masha Allah, shi kam yanayiwa ahmad sha'awar yarinyar nan, Amma Babu yanda za'ai, tunda ita ansa Mata rana, shikuma ya liqewa wannan jarababbiyar yarinyar

Cikin sakin fuska ya amsa, nan muka ci Gaba da break, nariga su gamawa, husna tace
" aide kya bari ingama ko, sarkin gaggawa," tahir yace "a a banga laifin taba, barta taje taga yarta," nace "yauwa yaya tahir fada Mata de,shekara guda bangan taba"

Husna tashi tayi, taje ta daukomin sweet dayawa tace "gashinan idan kinje saiki kaimata wannan sweet din, nasan halin baby da mugun San alawa"
Nace "anty husna aike ta biyo"
Tace "wa,? Kema kinsan wata biyo"
Tahir yace "towa ta biyo acikin ku kenan?" Husna tace "wallahi ita ta biyo," dukanmu mukasa daria

Tahir yace "to kinsan gidan ne kokuma Asa driver yakaiki?" Nace " a a bansaniba saide inkira Ammu ince masa ya turo min address din gidan, tunda suncemin uban gidansa ne, kaga ai zaisan gidan ko?"
Husna da tahir suka sa daria baki daya, tahir yace " tunda kin sameni ai kingam samun address, abokina ne fa, tun muna yara, aminina ne sosai," nace

" to alhmdlh
Rubutamin,"

takarda yasamu yarubutamin, nakarba nayi musu sallama nafice da kayan baby ahannuna


** *** **


"Uncle Yau zaka kaini wajan wasa?"
Ahmad da gabansa yake faduwa tun jiya, yace
" baby banajin dadi, bazan iya kaiki ba, jekice wa mamy tabawa mabaruka abinci na takawomin daki, banasan sauka,"

Tace " to uncle," bayan ankawo masa break dinne ya zauna adaki yanaci, Amma still gabansa yana faduwa, baby tana gefensa, cikin ransa yace tomeke faruwa ne haka?


** *** **


Tana tuqi taji qara shigowar text, ta duba number taga number mukhtar ce, afili tace
" wannan ina tuqi, banaso na kalli waya, idan naje gidan sai naduba," ta ajiye wayar taci Gaba da tuqinta


** *** **


Suna zaune afalo, husna sai sakin tsaki take, tace
" wannan yarinyar ina takai Wayarta ne, sai kira nake naji ko taje lafiya Amma bata dagawa,"

tahir dayake kwance Akan kujera yace" wacce yarinya kenan?"

Tace" FEENAH mana, ta wani bar waya awani waje "

Kansane yasara lokaci
daya dajin wannan sunan, yace" me kika ce?"🙆🏻 Cikin mamaki husna tace" kamarya?" Yace"sunan nakeso naji,"

tace "feenah nace,"

yace "wai dama haka sunan ta?"

Husna tace "kajika da wani magana wai kana nufin kacemin bakasan sunan da qawaye da yan'uwa suke Kiran taba? Ai sunanta feenah"

Gabansa yayanke yafadi, taci Gaba da cewa " idan kace nafeesa aiba kowane yasanta da wannan sunan ba" 🤣

"Dan dakata "

Abinda tahir yace kenan, yadauki wayarsa yakira ahmad
Bugun farko ahmad ya daga, yace tahir yanzu nake shirin kiranka, wallahi tahir gabana faduwa yake tun jiya,tahir cikin ransa yace ai dole,
Amma afili saiyace

" subhanallah to Allah yasa lafiya, nawan dama tambayarka zanyi, nikam Yama sunan budurwar nan taka?"

Ahmad yace "feenah mana,"
tahir yace

" no na gaskya,"

ahmad yace " nafeesa"

, tahir yace "kuma a zaria take ko?"

Ahmad yace "emana,"

"Amma please yaya kammaninta suke?"

Ahmad yace "zaka ganta yar fara, me dimple, yar doguwa kadan, wai meke faruwa ne? Kokuma inturo ma pic dinta?"

Dif tahir yakashe wayar, batare daya bawa ahmad amsaba, yadubi husna yace "Mata, akwai matsala ba yar qarama ba🙆🏻"


** *** **


"Malama kiyi hakuri Akan aikinmu muke dole sai ansanar damasu gidan koke wacece sannan zamu barki kishiga,"

feenah tace "kace musu yayar izdihar ce,"

Baiyi musu ba yashiga gidan, duk yan gidan suna falo Gaba dayansu, dayake weekend ne, ma'aikacin yacewa mamy hakima Hajia kunyi baquwa wai yayar izdihar, mamy da momy kai tsaye sukace suyi sauri su shigo da ita, aikuwa yana komawa, yakarbi jakar hannun feenah, yace "Hajia kawo jakar" 🤣

Babu musu tabashi, gabanta sai faduwa yake
Ta kalli harabar gidan tace cikin ranta masu kudi suna abinda sukai niyya, yanzu anan baby take rayuwa
Mamakinta bai qareba saida suka shigo falon, taga wata sabuwar aljannar duniya, momy tace "sannunki da Zuwa zauna mana, ya hanya?"

feenah ta zauna, nan suka sake sabuwar gaisuwa, mamy hakima tace wa momy Hajia kiduba kiga yanda suke kama da baby, banda shirme irin na ma'aikata aida sunga kamar ma yaci ace sun barta tashigo, ta dubi su mabaruka tace" ku Baku iya gaisuwa bane? "

Nan suka fara gaisheta tana amsawa, mamy tace" bari inkira alhaji yazo ku gaisa,"

tayi sama, momy tasa ma'aikata su kawo Mata abun motsa baki, nan da nan suka cika Mata gabanta da kayan ciye ciye su dangin fruit, daddy ne yasauko feenah tayi sauri tasauka qasa ta gaida shi, daddy sosai yayaba da tarbiyar yarinyar
Itama cikin ranta tana cewa a a wannan sunada mutunci 😃
Momy kaunar yarinyar take har ranta, tace

" baki zuba lemon ba yata, yaya sunan kine?"

, feenah tayi murmushi tace "sunana Nafeesa ," gamida daukar robar ruwa tafara tsiyayawa a glass cup din gabanta

Adaidai wannan lokacin su baby sungama break fast itada Ahmad yariqo hannun ta suna saukowa daga beni, Jin takunsu ne yasa feenah dagowa, aikuwa karaf idonta yahadu dana baby, baby da gudu ta iyo wajan ta tace "yeeeee ga sabuwar anty"
Feenah tatashi da niyyar rungume ta, gabanta yayi mugun faduwa ganin fuskar dabazata taba mantawa ba
Cikin mamaki tace

"Ahmad!!!"

Daskarewa yayi awajan cikin mamaki shima yace

" feenah!!!"

Jin wannan sunan yasa momy tatashi tsaye tace "a a wai feenah ce qawar saudat?"
Ahmad bai kula momy ba yaqaraso wajan ta yace

" feenah kece da gaske ko mafarki nake?"

Murmushin takaici nasaki nace "yanzu ma kayi mamakin ganinako?"

Nan danan kuka ya qwace min
Nace "danasan agidan nan kake wallahi dabanzo ba Ahmad , mayaudari kawai,"

Ahmad yasake matsowa kusa da ita yace "feenah kibari nayi miki bayani"

Tass kakeji ta daukeshi da mari🙆🏻
tace cikin kuka 😭 "mezanji ahmad? Ka lalata rayuwata, ka zubarmin da mutuncina na ya mace, karshe kaje kayi auren ka, kafadamin meya hadaka da 'yata?"

Cikin mamaki yace "yarki?"

Cikin takaici nace "au baka ganeba kenan shine kake tambayata? To yarka"


Jiri Momy tafara gani, tana daga tsaye, sai luuu tafadi qasa Allah yaso akwai kujera awajan

Feenah kuwa taja hannun baby sukai waje, kotakan kayan data kawo Mata batabi ba 🤣

Ahmad tsugunna wa yayi awajan yana ambaton

" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un"

Yayinda sauran yaran sukai kan Momy suna kuka









Mrs Usman ce
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Wannan shafin nakune kyauta, iyalan maman khaleel jama'ar 😍LOVELY FANS😍


53


Daddy ne daya daskare a tsaye, yayi karfin halin cewa adebo masa ruwa, mamy hakima ce tafara kokarin kamata Zata gyara Mata kwanciya, ahmad yatashi zai gyara Mata, cikin fishi daddy yace "karka kuskura"
Mamy hakima cikin kuka tace "haba alhaji, ka barshi mana, Dame zamuji ne?"
Shiru yayi, batare daya tankaba, ganin hakane yasa ahmad yadauke ta cimak, yamaidata kan doguwar kujera, aka kawo ruwa aka yaiyafa mata, ba'a dauki lokaci mai tsawo ba tafarka, Amma banda kuka babu abinda take
Itakam tacire hannun ta a al'amarin ahmad,ace mutum kullum kaine cikin matsala


** *** **


Ina kuka inajan baby muka futo daga gidan, masu gadi sai kallo na suke, sunga nashiga kalau, na futo da kuka, inajin wani yana tambaya "hajia lafiya kuwa?''
Kyaleshi nayi, na fice daga gida
Muna Zuwa wajan mota dayake awaje na barta, baby tafara tirjewa tareda alamun kuka tace

" anty ina zamu? "

Kai tsaye nace Mata
" gida,"

tace" to anty nide ki tsaya uncle "

Nace" baby zaki shiga mutafi kosaina bigeki?"

Tace" nide anty Allah da uncle zan tafi "

Ganin Zata batamin lokaci ne yasa nadauketa nasata agidan baya, sannan nashiga naja motar muka tafi
Ina driving ina goge hawaye

Ashe shiyasa gabana yake ta faduwa, ashe da wannan azzalumin zan hadu shiyasa

Ina parking agidan husna na futo, nacemata "idan kinga dama ki futo, in kuma wajansa zaki koma saiki ja motar kije" 🤣


da sauri ta futo ta riqeni, tace "to anty yaushe zaki mayar dani wajan uncle din?" 🤣

Nace "baby Dan Allah kimin shiru"

Cikin gida kuwa husna tayi tayi yafada Mata wacce matsala yake nufi, yace babu komai, yadauki hannu ya rafka uban tagumi 🙆🏻😳🤣
Shi kansa tausayin kansa yake, bare idan yatuna ahmad, ko yaya zasu qare da feenah? 🤣


Suna wannan halin nashigo falon nida baby ina kuka
Sallama nayi muryata ciki ciki, ina Zuwa nafada jikin husna nasaki wani uban kuka mai ciwo

Tahir kasa magana yayi cikin ransa yace shikkenan tafaru ta qare, 🤣 ruwa yaqarewa Dan kada
Dagani har ahmad din Yau babu me wata dabara, kawai inma zagi ne ayi mana, in hakan zaisa a huce

Husna tace "me yake faruwa kika taho da babyn?"
cikin kuka nace " anty husna shine, wallahi shine azzalumi"
Husna tace "wai menene hakane? Kai kacemin akwai matsala ba yar qarama ba, ita tacemin shine,"

baby ta kalla tace "ke baby me yake faruwa? Me akayi Mata?"

Baby tace "nima bansaniba, nide naga ta mari uncle,"

tahir cikin ransa yace "ai kadan ma kenan, nayi Zatan abin zaifi haka" 🤣

Cikin mamaki husna tace
" mari!"

"Feenah, tahir wai kuyi min bayani mana,"

feenah tace "anty husna ashe mutumin dayaci mutunci na, ya keta min haddi na, shine wanda su Abba suka dauki baby suka bashi"

Husna tace "subhanallah" 🤦🏻‍♀

Tadubi izdihar tace "baby jeki wajan su mama suna daki kuyi wasa"

Tana tafiya husna tace
" innalillahi, mun shiga uku!" 🙆🏻

Sannan Ta kalli tahir tace

"Tahir!!! "

Tahir yakasa magana, sai can yace "shiyasa nace miki akwai matsala babba, Amma meyasa kika cemin nafeesa batasan baban baby ba?"

Husna tace "haka tace mana ai, gatanan ka tambaye ta" ,

cikin ransa yace wato saboda soyaiyar datake masane yasa takasa tona masa asiri,
afili yace "ai ni yanzu bana buqatar dogon bayani, nasan komai
Itama kuma tasani"

Husna ta dubi feenah tace " hakane?"
Gyada kai nayi kamar kadangaruwa nace
" nasanshi anty husna,"

Husna tasake maida kallanta ga tahir tace "wai kana nufin itace wadda kabani labari kace ahmad yana Santa harma yakasa sauraron kowa saboda ita?" 🤣

Cikin sauri nace "wallahi anty husna karya yake
Mayaudari ne, bayan saida na yarda dashi yaci amanata karshe yaje yayi auren sa" 🤣

Tahir ne yace "am feenah kingane ahmad bashida laifi anan idan kika tsaya kika saurari abinda zai....."

"Ni kadena min maganarsa yaya tahir, wallahi na tsaneshi"

Husna ma tace " to Amma ya ahmad zai Mata haka?"

Tahir yace "kamarya ya zai Mata haka, kin tsaya kinji yayi miki bayani ne?"

Wayar feenah ce ta dauki qara,
New Number tagani, tana dagawa taji ance
" nafeesa"
Cikin nutsuwa ta amsa, yace "mahaifin mukhtar ne,"

cikin ladabi tasake gaida shi, yace "kema sun turo miki saqon ta layin mukhtar dinko?"
Sai alokacin tatuna da saqon da mukhtar ya turo mata, tace " baba, naga anturo de, Amma ban budeba,"

muryarsa na rawa yace
" kayya sun saceshi nafeesa, abinda suka fada kenan, wai bazasu sake Shiba har sai yace yabarki "
Wani ihun kukan naqara sakawa, bansan yaushe baba yakashe wayarba

. Nace "na shiga uku na, wannan wacce irin masifa ce ne?"
Husna da tahir ne suka hada baki wajan fadin "menene?"
Nace "ansace shi, wai wasune suka sace mukhtar"

Husna tace "Yau munga ta kanmu
Satar ango kacokam" 🙆🏻


** *** **


"Momy Dan Allah kiyi hakuri, kiyafemin, daddy, mamy kuma kuyi hakuri Dan Allah, banyi hakan da niyya ba, nasan duk abinda zan fada muku bazaku fahinceniba"

Daddy kawai kallansa yake, saida yagama bayaninsa, yace
" kagama? To tunda kasan bazamu fahimta ba karma kasake kayimana maganar"

Ahmad yajuya ya kalli Momy yace "Momy Dan....."

itama cikin sauri ta katse shi, tace "karka cemin komai ahmad nikam na zare hannu na acikin al'amarinka," mamy hakima ita kanta wannan al'amari baiyi Mata dadiba, itada take Dan goyon bayansa, shiyasa itama tayi shiru

Rana zafi inuwa quna, Yama rasa ina zaisa ransa, Dame zaiji? Ita waccan taqi kula shi, suma iyayan nasa sun kasa fahimtar sa

Tashi yayi, zuciyarsa nayi masa zafi, idonsa jajir
Kofar fita ya nufa, yana Zuwa bakin Kofar, yaji kirjinsa ya riqe, yakasa numfashi, cak yaja ya tsaya, daga baya su Momy sukaji qara, suna juyawa su kaga ahmad a kwance shame shame babu alamar numfashi

Gaba dayansu sukai kansa da gudu
Daddy yafi kowa shiga cikin rikici, da sauri yace

"adauko mota,"
nan da nan suka tafi asbiti
Kai tsaye asbitin tahir sukaje
, gashi bayanan, Dan haka mamy hakima takirashi awaya tace yazo asbitin sa yanzu ahmad ba lafiya
Cikin sauri yafuto, husna tace "ina zakaje?"
Yace "ahmad ne wai bashida lafiya, kuma nasan hakan baya rasa nasaba da wannan rikicin
Zanje asbitin yanzu, ki kula da nafeesa"

Nikuwa ina daki ina kuka, ina hada kayana, husna tashigo tace "mekikeyi hakan?"

Nace "gida zan tafi anty husna, duk Garin yaficemin akai,"
Husna ta rungume ni itama, tana share qwallah, tace " kiyi hakuri, insha Allah, Allah zai bayyanashi kinji, kiyi hakuri"

Nace "to sister"

Tace " shima tahir din yatafi asbiti yanzu wai ahmad din bashida lafiya,"
yatsina fuskata nayi, nace "shiya jiyo"

Ina Gama hada kayana, nacewa anty husna na tafi, gara inje in sanar da Abba abinda yake faruwa dangane da mukhtar, ita kuwa baby daga Yau tadena zama agidan wannan mayaudarin
Babu yanda ta iya Dani, dole ta rabu Dani na tafi, baby tana dayan seat din, ina driving mukadau hanyar zaria, munyi nisa ahanya Zahra ta kirani tace " feenah Amma kin fasa Zuwa ko?"
Nace "Zahra ainakoma zaria ma," tace

" subhanallah Allah yasa lafiya," nace "lafiya Amma ba kalau ba, Zahra naje ganin baby
Wai ashe ahmad aka bawa baby bansaniba,"

Zahra cikin firgici tace

" wai wanne Ahmad" 🤣

nace "ahmad de nawa"
Zahra tace "innalillahi to tayaya?" Nace "ina nasani Zahra, nikam wallahi nadauko yata nabar musu gidansu,"

Zahra tace "matsala!"
Nace "ina kikaji matsala Zahra, wai ansace mukhtar, dazu dazu babansa yakirani yake fadamin," Zahra tace
" munshiga uku, wata sabuwa," nace "Zahra bana cikin nutsuwa ta yanzu, mayi waya daga baya,"
wayar na ajiye muka ci Gaba da tafiya


** *** **


Yana Gama dubashi yafuto daga Dakin din, yasamu su Momy awaje a tsaye, yace "Momy ku qaraso daga ciki,"
Babu musu dukansu suka shiga office dinsa
Tahir yace "daddy saide kuyi hakuri, Amma ahmad ayanxu kulawar ku yake buqata, yana gab da kamuwa da ciwon zuciya, kuma kunsan hakan, Amma bakwa kiyaye damuwar sa
To maganar gaskya, abin nasa yayi girma dayawa, yakamata a kiyaye abinda zai dinga bata masa rai"
Daddy yace "Amma tahir kasan abinda yaron nan kuwa ya aikata? Zinafa tahir
Ina hankalinsa yake? Har menene zai debeshi yaje ya aikata wannan mummunan aikin,?"

Tahir

Please Login or Register in order to submit comment