Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"kai zamani"

Tsaf ta futo cikin shiri na alfarma, taji sarka ahannun ta da wuyanta, mamy hakima ma tana falo, tace " hajia yaude an samu tafiyar bazata," momy tace "ni hajia dakinbi su kunje ma, ni saina zauna agidan"
Mamy tace "a a kiyi hakuri muje"

Ahmad ne yadawo shima yayi kyau sosai cikin farin yadi mai ratsin milk color
Yakama hannun baby yace "to mamy sai kun futo muna jiran ku"
Momy tace "driver ne zai kaimu ne?"
Ahmad yace "haba momy, tayaya zanbar mutanan dasukafi komai tsada awajena wani yajasu, bayan gani, me amfani na?"

Auta tace "yaya Dan Allah kaje Dani," ahmad yace "auta, kawai yan gidansu baby zamuje mu Gano mu dawo, kiyi hakuri kinji, bazamu dadeba"

Maryam tace" toshkn yaya, Amma saide in zaka dawo kasiyomin ice cream," yace" angama gimbiyata "

Muslim ne yace" baby! "
Tajuyo tace" bye bye na tafi wajan Abba "
Yace" ki tahomin da abin dadi "
Tace" to "
Su momy sunata kallansu
Bukhari ya dubi ahmad yace" yaya Muslim yana San baby, zaka bashi ita? "🙆🏻😳
Cikin tsananin mamaki ahmad yace " Bukhari me kace?
Karna sakejin wannan maganar abakinka kaji ko? "
Yace" sorry yaya, nadena fada "
Yace"ok"
Yaja hannun ta suka fita, su momy ma suka bisu abaya, suna shiga basu tsaya ko inaba sai zaria

Su Abba sunyi mamaki kwarai dasuka ga ahmad yakawo musu iyayen sa sun gaisa, sosai suka qara yarda dashi, sun San konan gaba bazasuyi DANA SANIN bashi baby ba

Kayan abinci sosai momy tasa aka kawo musu, duk da basu rasaba, shima dakyar Abba ya yarda yakarba, Dan yaga wahalar nasu yana nema yayi yawa

Dazasu tafi izdihar sai bye bye take musu, nan suka sake tabbatar wa kansu cewa tana cikin kwanciyar hankali
Mama tace "baby ko kewata ma bakiyi ba?"

Daria kawai tayiwa mama, mama tace
" toshkn Amma ai kinyi kewar sabuwar anty ko?"
Da sauri ta daga kanta, tace mama
" aitatafi tabarni "
Mama tace "a a bata barki ba baby Zata dawo nanda wata daya kinji"

Ahmad yana jinsu aransa yace zai zauna da baby de ya tambaye ta, wacece wannan sabuwar antyn?
Agidan take?
Yayarta ce?
Menene sunanta?

Dahaka sukai sallama dakowa, su momy sosai sun yaba dasu mama, kuma sunsan baby daga gidan qwarai take


** *** **


Yana zaune Akan motar sa aharabar gidansu, yaronsa yazo, yakawo masa wata takarda, yace
" gashi oga, angama komai, wannan shine abinda bincikenmu ya nuna Akan mukhtar"

Kb yace "toshkn ngd, zaka iya tafiya"


** *** **


"Oh feenah, wai kina nufin harkin fara hada kayanki?"

"To Zahra mezan jira, saura 5 days na wuce gida, kede nake bawa shawara ki tsaya kiyi masters" 🤣
Zahra tace "a a feenah bazan iya ba, shekarar mu hudu fa a qasar nan, gara mutafi kawai"
Feenah tace "hakane kam nima wallahi ganinki ne yasa na iya zama
Dakuma mukhtar Amma banda haka da iya degree na ya isheni, zaman duniya de bana qiyamaba,"

Zahra tace "ai shine"

Feenah taci Gaba da cewa, "wallahi wannan zuwan cike nake da darura Zahra, nakasa gane inda su mama suka dosa, kullum nakira waya nace abawa baby basa bata
Zahra anya kuwa baby ba mutuwa tayi ba?" 😭Taqara sa maganar cikin kuka
Zahra tace "haba feenah, haba qawata meyasa kike wannan maganar ne?
Insha Allah Babu komai sai alkhairi, Amma nikuma feenah sainake tunanin anya ba wajan husna ta koma ba, tunda kinga dama tanasan abata baby"
Feenah tace "aiko wajan kaka takoma ina Zuwa zan karbe 'yata,🙆🏻😳nima inasan ta, Zahra wallahi ina qaunar baby
Ban qara tabbatar da hakanba saida naje hutu, shiyasa namatsu nakoma inga halin da yata take ciki"

Zahra tana murmushi tace "ga kuma bikin dayake tunkaro muba,"

Feenah tace "shima kinga yakamata nakoma a fara shirye shiryen yanda abin zai kasance" , Zahra tace "eh wlh, to Allah yakaimu lafiya de," nace "amin"

"Zahra zaki rakani afra, da kasuwar sha'abi, gobe inje inyiwa baby siyaiya, daganan ma sai muje top galary musai takalma"
Zahra tace "babu damuwa, naga alama de wannan zuwan siyaiyar baby daban ce"
Nace " eh wallahi Zahra, ai sosai nakeso naje naga sagiraty na, mu kwana muna firar yaushe gamo 🤣
, Zahra bazaki ganeba saikin haihu"

Tace "to Allah yakaimu feenah, Amma yanzu de please tashi muje imtiyaz musai shawarma,"

nace "a a gaskiya muje baiti shami (shami house)"

Zahra tace " to naji muje, dole ai nayi miki abinda kikeso tunda nanda 5 days muna gida ba ganinki zanyi ba"

Nan nadau mayafina muka tafi





Mrs Usman ce ✍️
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

50


Washe gari mukaje nayi siyaiya, Zahra ma haka, nasaiwa twins kayan wasa Sosa, da Abban anty maimuna, saikuma baby daduk nata yafi na kowa

Da daddare muna zaune nida Zahra, tace "nikam feenah akwai abinda yake damuna game dake,"

nace "Zahra menene wannan Abu kuwa,?"

Dawowa tayi kusa Dani tace "wallahi wata alfarma nake nema awajanki,"
Nace "inde batafi karfinaba mezai hana nayi miki Zahra, ai kinfi karfin komai awajena," Zahra tace "feenah mezai hana ki fadawa ahmad baby yarsa ce?"

Da sauri na kalleta nace "saboda me?"
Tace "to saboda me bazaki fada masaba? Har sai yaushe feenah? Sai lokacin da yarinya tagane basu Abba ne iyayenta ba?
Kice Mata me alokacin?
Kokuma sai alokacin zaki fara nemansa Akan wannan maganar
Kinsan de duk daran dadewa dole yarinyar nan tasan gaskiya
Aganina gara kifada masa yasan cewa yanada wata yarinyar, tunda gashi harya fara haihuwa da wata, yasan cewa ba 'ya' yanta ne kawai nasaba, akwai wata "

Ajiyar zuciya nasauke nace" hakane Zahra, kinyi gaskya, Amma kinsan de abinda yamin bai kyauta bako?" Zahra ta dora hannun ta Akan kafadata tace" feenah banasan kina tuna baya
Idan kikace zakina tuna baya da kuma abinda aka miki, bazaki taba yafe masaba, idan baki fada masaba, ke kadai zaki zame Mata uwa da uba ne? Idan ta girma tace ina mahaifina cemata zakiyi nice mahaifinki? Bazai iyuba! "

Nace" to ai nafadawa su Abba bansan wanda yamin cikin ba,"
Zahra tace" Amma kuma keda shi kunsan kanku ba "

Nace"hakane Zahra, Amma ni gaskya bazan iya kiransa ba," Zahra tahade hannayenta waje daya, tace "please feenah, rabuwa fa zamuyi"

Kallanta nayi nace
" Toshiknn, Amma kinsan de, yanzu baya Nigeria, tunda a Egypt muka ganshi, kuma ni number sa ta Nigeria na riqe"

Zahra tace "toga shawara,"

nace "menene shawarar ki?"
Tace "mezai hana kikira saudat
Kinga ta dalilin ta zaki samu number sa koba hakaba, kokuma in kina ganin bazaki ki rashin ba, kawai sai kiyi Mata bayani ita saita fada masa,"

Murmushi nasaki nace "Zahra uwar yan shawara, Toshiknn zan kirata insha Allah"
Rungume ni tayi tace
" Nagode feenah"


** *** **

After 2 days
Suna zaune tana yanke masa farce, yace "qawar iklima, yaushe zan kaiki wajanta ku gana da Juna ne?"
Husna tace "Allah kacika baki kagani, kafarka ce ahannu na"
Tahir yace "kina yankani babu asbitin da zanje, kece zaki dubani
Kanki kika janyowa aiki, nida nakeda Mata likita," tace "nide kadena yimin zancenta"
Yace "angama my heart"

Husna tace "yaufa saura 3days sister tadawo," tahir yace "manyan yan boko kenan, kice munada manyan baqi, kinga ranar saiki shirya da wuri muje Airport mu dauko ta ko"

Husna tace "abinda nace Mata kenan, tasauka anan idan ta huta, saita tafi, kokuma Washe gari ta wuce
Amma saita cemin, bazata iya Zuwa kano tazauna ba tare dataga mama da baby ba"

Tahir yace "to ai babyn tana nan, basai taje taganta ba," 🤣
husna tace "ai kasan har yanzu batasan an bayar da itaba"

Tahir yace "to menene Dan bata saniba, mu munsan anbada itane?"

Husna tace "saboda yarta ce,"

tahir baisan lokacin dayakai kallansa gareta ba


** *** **


"Baba yarinyar nan inasanta, tana sona, aurawa danka ita hakan yana nufin barazana ne ga rayuwata"

Baba ya kalleshi dakyau yace "yaro ni bangane abinda kake nufi ba,?"
Kb yace "inaso danka mukhtar yarabu da nafeesa yabarmin ita, nizan aure ta, konawa kakeso zan baka, kudi ba matsala bane"

Baba yasaki murmushi yace "yaro kasan kuwa wannan yarinyar dakake magana Akan ta ansa Musu rana?"
Kb yace "to menene Dan ansa musu ranar? Aure aka daura musu?"
Baba yace "to kaje da kudin ka, Bama buqata mu yarinyar mukafi buqata"
Kb yace "Allah tsoho? Haka kace? Toshiknn zakaga abinda kudi zaiyi," yana fadar haka yajuya yatafi, Yabar baba da budadden baki


** *** **


Husna ta share hawayen idonta, tace "nadade da burin infadama wannan maganar Amma ina darurar ta ina zan fara?
Tare muka tashi da ita tun yarinta, bamuda wani Hali na rashin kirki, tarbiya daidai misali anbamu, daga bayane itama wannan qaddarar ta fada Mata

Wani marar imanin ne yayi raping dinta, anan Garin, harta samu ciki, wadda kacemin kun karbi haihuwar ta a sbitin ka, har kace ahmd ne yabata jini, auta ce tahir

Alokacin data haihu lokacin yayi daidai da haihuwar mama, ta haifi namiji, Amma ya rasu, hakan ne yasa Abba ya karbi baby daga wajan auta, yabawa mama ita, saboda rufin asirin ta "

Tahir daya mutu da mamaki yace"yanzu kina nufin baby dama ba 'yar mama bace?" Husna tasake goge hawayen ta, tace "hakane, bamusan yar waye ba, tunda tun lokacin anyi Mata tambayar duniya tace wallahi batasan wanda yayi mataba, inda ace tasanshi, nasan cewa Sai inda karfin Abba yaqare"

Gaban tahir ya dinga faduwa yace "kuma kikace raping akayi Mata?"
Husna tace "eh"
Cikin ransa yace " to ai kuma ita wannan tace batasan waye yayi Mata ba, bare yayi tunanin wani Abu"
Janyota yayi jikinsa yafara rarrashinta, yace
" Allah yasaka Mata, kiyi hakuri kinji,"

kanta ta dora Akan kirjinsa


** *** **


Next day

"Wallahi alhaji gabana har faduwa yake idan na tuna yarinyar nan jibi Zata dawo"

Abba yace "menene abin faduwar Gaba kuma maman nafeesa?
Saikace ba kece kika karfafamin gwiwa Akan abinda mukai ba
Nafeesa de mune muke iko da ita, dan munbada wannan yarinyar ni aganina kamar rufin asirinta ne
Saikiga anyi Abu, kana tunanin babu wanda yasani, Amma daga baya sai kiji maganar awaje

To kinga inde ubane, izdihar tasamu, bana tunanin ko mutumin dayayiwa nafeesa wannan abun yakai ahmad son izdihar
Dan haka ga uba nan tasamu, mamanta kuma nafeesa

Koda tayi aure zaman baby awajan ahmad yafi sauqi
Dan haka tana dawowa zanyi Mata bayani da kaina "
Mama tace" to shikkenan Allah yakaimu alhaji "


** *** **


"Kinga ni kawai kiyimin baqin lallan, banasan Jan"
Zahra tace " meyasa feenah,? Kawai ayi mana, duka, baqi da Jan"

Nace "Zahra Jan lalle yana dadewa ahannu na bai fitaba, Amma baqin baya wuce sati daya"

Zahra tace " ok, kumafa hakane, to kawai ayi mana baqin, kar muje ayi mana Jan yaqi fita da wuri
Kuma ga biki yana matsowa"
Feenah tace "emana, nima shi nagani"

Zahra tace "Amma de ai a kano za'a yi miki dilka dasu qunshi ko, kinga sai Amana Gaba daya"
Nace "emana insha Allah"

Mai qunshi takama hannun Zahra tafara yi Mata, saida aka Gama musu, su kabar unguwar

Da daddare sunyi wanka, kowa yana kwalliya, Zahra takira mukhtar tace "ango, to anjima din zaka turo mana motar dazata kaimu airport ne kokuma kawai mutafi?"

Mukhtar yace "a a ku zauna nima sai nazo gidan naku, daga nan saimu kira Tirhal kawai takaimu Airport din Gaba daya"

Zahra tace "a a yanzun kai kana ina?" Yace "ni ina unguwar Salamah yanzu ina sallama da friends dina, kuma daga nanma
Meenal barri zanje daganan inje hilla soba,"
Zahra tace "am mukhtar naga al'amarin Naka bana qare bane kawai sai kazo anjima din" 🤣

Ta dubi feenah datake kokarin saka Riga doguwa abaya mai kyau, tace "wannan angon naki yacika zirga zirga"

Feenah tace "toya za'ai kinsan shi mutum ne na mutane"

Zahra tace "to waye bana mutanan ba, me kike nufi?"
Feenah tace "ahmad mana, tunda nake dashi bai taba nunamin daya daga cikin abokansa ba, kullum saide yacemin yaso yazo da abokinsa Amma abokin nasa bashida lokaci
Dayake abin nasa bana gaskiya bane, Amma inda ba yaudara ce takawoshi wajenaba mezai hana yanunamin wani nasa"

Zahra tace "aikuwa inkina neman mutum na mutane ma kika samu ahmad kinga ma yarinya
Ke shaida cede, kingani da idonki lokacin da mukaje masar
Kinga yanda mutane suke rububinsa"

Feenah tace "um aikam nagani, zahra'u Ahmad muha marzuk" 🤣

Zahra tace "edin kiyi ta fada
Yauwa kin kira saudat kuwa?" Feenah tace "gara dakika tunamin namanta"

Wayarta ta dauko, tasa number saudat, tasa wayar a handfree
Zahra tadena kwalliyar datake tazauna zataji ya zasuyi

Kiran farko a kace call end, feenah tace "Zahra kode tadena amfani da layinne?"
Zahra tace "sake gwadawa muji"
Sake kira tayi, aikuwa bugu uku Ana hudun aka daga

Feenah tace "sister saudat, yar'uwata takaina, amaryar farouq maman baby"

Har abada bazata taba mantawa da mamallakiyar wannan muryar ba

Saudat tace "Dan Allah mafarki nakeyi ko a gaske ne?
Feenah kece? Sister feenah
Kiyi magana mana,"

Tuni kuka yazomin, nace "nice saudat, kwana dayawa yagida, yayaranki?"
Saudat itama kukan take tace "feenah ina kika shiga? Neman duniya muke tayi miki nida yaya"

Nace "saudat ina nan," tace "to kina wanne qasa, naga number bata Nigeria bace"
Nace "eh ina Sudan saudat
Gobe zan dawo Nigeria, inaso zamuyi wata muhimmiyar magana dake, idan nazo insha Allah inasaka wani layin awayata zan kiraki"

Saudat tace " to feenah Dan Allah kikirani, Allah inasan ganinki sosai,"

nace "saudat zankiraki, ina yaranki, sai tambayarki nake kinyi shiru?"

Saudat tace "ban haihu ba feenah, ina fatan de nasamu cikin"
Nace "Allah sarki yar'uwa, nima to zan dinga yi miki addu'ah Allah yabaki," tace "amin"

"Dan Allah feenah ina kika shiga Tsawon wannan lokacin?"


Nace "saudat zamuyi magana idan na dawo kasar"
Tace "to shikkenan, I miss you sosai"

Nace "wallahi nima haka, sai anjima, sai munyi wayar"

Saudat tace "feenah banji kin tambayeni yaya ba, ko akwai abinda yake faruwa ne?"

Nace "saudat babu komai karki damu"
Tace "To shiknn" , nan mukai sallama

Saudat tace wannan daddadan labari ai dole in fadawa yaya, nan take takirashi, saide baya kusa bai dagaba

Sai wajan 11:30 pm yaga Kiran nata, yace gobe ya kirata yasan yanzu tana tare da mijin ta

Ajiyar zuciya nasauke me nauyi, nakalli Zahra ba tare danace komai ba, Zahra tace " to yanzu ke bakifijin dadi Bama"

, nace "wallahi naji dadi Zahra,
Nayi missing saudat
Tana sona sosai
Zahra tace mukuma banda mu ba,

nace nina isa nace haka
Aike ce first lady

Karfe uku na dare muka tafi airport, bamuyi awa dayaba muka tashi


Bye bye Sudan

dayake jirgin Ethiopian mukahau

Saida mukayi transit a Adis-ababa, na Tsawon awa biyu, sannan mukahau wani jirgin Zuwa Nigeria, karfe 11 nasafe, cikin Airport din Malam aminu kano tayi mana








Mrs Usman ce 🖊[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

51


Bayan mun futo, nayi sallama da Zahra Akan sai munyi waya, mukhtar yace "wai yanzu bazaki bari azo daukan naki ba?"
Nace "emana dakaina zanje,"

Dan haka yaje yanemomin taxi
Shiya bashi kudin, nan mukai sallama dashi nikuma na shiga sai zaria

Muna sauka a kofar gida, naga gidan ya canja, na futo da mamaki Akan fuska ta, Abba naganin motar mu ta tsaya yaqara so da sauri, yace
" sannu mamana "
Nace "yauwa Abba,"
Nafadi haka hankali na nakan gidan
Muna qarasawa gate mama tazo ta rungume ni, tana "sannu autata," nace "sannu mama"

Afalo muka zube, nadora kaina Akan cinyar mama inata kallan falon da tsananin mamaki

Mama tace "taso kici abinci kiyi wanka kihuta,"

nace " kai mama barni nagama Jin duminki tukunna," 🤣

saida nahuta Abba yashigo yanamin sannu
Yace " yarinya ki dage ke kadai zaki taho basai munje ba,"

nace "Abba banaso kusha wahala, ai gashi nazo," yace "hakane to Allah yasa angama a sa'ah" nace

"amin Abba"

Mama na kallah nace
" mama ni banga baby ba, tana ina ne?"
Abba da mama ne suka hada ido lokaci daya


** *** **


Yana juyi Akan kujerar office dinsa, wayarsa na hannun sa yana kallan pictures din baby

Wata folder yabude saida yasa security sannan naga yashiga, pictures dinta ne rututu aciki, wani da saudat wani ita kadai
Murmushi yasaki yace
" my feenah I luv u"

Hada pic din yayi dana baby, yace afili, " narasa banbanci tsakanin su,
Allah kenan mai hada kama
Saikaga mutum bakasan Shiba baisanka ba, Amma kaga suna mugun kama"
Pic din yashafa yace "ina sanku dukanku"
Ganin pictures din saudat ne yatuna masa da kiranta da baiyi ba
Fita yayi daga cikin folder ya kirata
Bugu daya ta dauka tace
" yaya!!!"
Ahmad yace "sauda karki kashemin kunne Dan Allah"
tana daria tace "yi hakuri yaya, munyi waya da feenah jiya
Shine nakiraka zan fadama Amma ban same kaba"
Ahmad daya tsinci zancan kamar a mafarki yace " me kika ce?" Tace
" yaya serious nayi magana da ita jiya"
Yace "please turomin Number,"

tace "yaya bazaka sametaba,"

"Kituromin nace," yakatse Kiran, ita kuwa batayi musu ba, tatura masa, yana ganin number yakira
Taqi shiga, yasake kira taqi shiga, haka yayita gwadawa
Daga karshe de yakira saudat yace "meyasa bata shiga ne?"


"Yaya dama fa nafadama bazaka sametaba
nima jiyan tacemin ne tana Sudan kuma Yau Zata dawo Nigeria, Amma idan tasa sim card din Nigeria Zata kirani"
Cikin mamaki yace
" Sudan kuma?"
Saudat tace "eh haka tacemin, wai tana karatu ne"
Cikin ransa yace "Tome ya kaita Egypt?"

Yace "to shikkenan idan ta kiraki please Kituromin Number,"

sauda tace "wallahi yaya nima na matsu takiranin saboda tacemin wai zamuyi wata muhinmiyar magana," gaban ahmad yayanke yafadi, bade abinda yafaru Zata fadawa sauda ba

Zancan nata ya katse da cewa " Amma bata yi miki magana taba?"
Sauda cikin murmushi tace "a a batamin ba, da zamuyi sallama nede nace bata tambayeni yaya ba ko akwai abinda yake faruwa?
Saitacemin karna damu Babu komai"

Wata nannauyar ajiyar zuciya yasauke, yace
" Toshiknn, Amma de tana kiranki Kituromin number karki manta,"

Tace " insha Allah yaya"
Sallama yayi Mata, yafada duniyar tunani, Sudan, Egypt, tana karatu a Sudan, tome ya kaita Egypt? Duk wannan tambayoyin yana wajan feenah
Muhinmiyar magana, tome Zata fada Mata?
Innalillahi
Gara tunda wuri yadamu saudat Akan tabashi number nan, yabawa feenah hakuri, tayafe masa, tunma kafin suyi maganar, duk da bashida tabbacin wannan maganar zasuyi


** *** **


"Yanzu mamana menene abun kuka, saboda mun dauki yarinyar nan mun bayar da ita? Nayi tunanin zamu iya iko dake da abinda yake naki ne
Sannan karki manta duk daran dadewa akwai ranar da zatazo wannan yarinyar tagane ba mune iyayanta ba
To wannan bawan Allah yana kaunar yarki kamar shine ya haifeta, nafeesa bana tunanin kema kina Santa kamar yanda yake Santa
Izdihar de tana kano, tana wajan uban gidan ammun ku, idan kinasan ganinta ne kya iya Zuwa ki ganta 🙆🏻
Kokuma ayi masa waya idan yasamu dama yakawo miki ita ki ganta "

Hawayen idonta ta share tace" Toshiknn Abba Nagode Allah yasa hakane yafi alkhairi"

Abba yace "yauwa mamana, haka nakeso naji, yaron yanada hankali, duk mutumin daya nuna yanasan Naka ba qaramin masoyinka bane, to nide abinda nakeso dake shine ko bayan raina, inde ba mahaifin wannan yarinyar ne ya baiyanaba to banaso naji kince ahmad bashine ya haifi Izdihar ba "
Cikin sauri tadago kanta Jin sunan da Abba ya ambata

Ahmad!
Sunan da bazata taba mantawa dashi ba, kuma mutumin dayaci amanarta karshe yaje ya auri wata, me sunansa ne zasu dauki yarta su bashi

Abba yace" mude mun yarda dashi, Dan haka kema inaso kisawa zuciyar ki salama, kinji ko? "
Nace" to shikkenan Abba,"
Yace" yauwa Allah ya miki albarka," nace" amin "

Daki na shiga, ina kuka ni kadai, Amma abayar da yarinya kyauta, aka sa kirana a fadamin, Amma aiko husna yaci ace takirani tafadamin
Wayata nadauko zan kirata, kawai ma nafasa

Wanka na shiga, adakin da aka nunamin a matsayin nawa, duk abubuwana suna ciki

Ina futowa awanka, na kwanta da niyyar hutawa nan bacci ya daukeni

Wayar da mama takeyi ne ya tasheni, tace
" gatanan bacci take,"
juyi nayi, nace "mama wace?"
Wayar tabani tayi waje
Nace " hello,"

tace "Allah sarki sis, kina bacci nasa antasheki ko?
Na matsu naji ya kikazo ne"
Nace " anty husna ai fishi nake dake"
Tace "subhanallah, me yake faruwa,"

nace "yanzu har abada baby Amma koki sanar Dani?"
Husna tace " sister bahaka bane, nasan abin da ciwo, tunda nima inada yaran, nasan yin hakan babu dadi, wallahi shiyasa ma naji tsoron fadamiki"

Nace "to ai shikkenan, Abba yafadamin," tace "kiyi hakuri
, komai mai wucewa ne, kuma hakan shine yafi, idan kikai tunani"
Nace "hakane, aina hakura ma
Ina twins?"

Tace "suna wajan ummi, ga tahir"

Wayar tabashi muka gaisa, yace "irin wannan qin zumunci haka auta, memakon ko kwana biyu ne ki tsaya kiyi mana"

Nace "kuyi hakuri yaya tahir, wallahi na matsu nazo naga mama ne da baby"
Yace "to ai muma gobe zamuzo ko jibi, kar muyi laifi," nace "a a yaya tahir, kawai ku zauna nima zanzo, inaso naje naga baby, this week insha Allah zan shigo,"

tahir yace "to shikkenan, da fatan de Babu matsala ko?
Karfa kisa tunanin abin aranki," murmushi nayi nace "babu komai yaya tahir, sai anjima,"

yace "toshkn ki huta lafiya"

Baccin daban komaba kenan, sai kirana suke ta layin mama suna min sannu da Zuwa, daga karshe ma a cinyar mama na kwanta muka kafa sabuwar fira, sai zance muke munata daria, kamar babu abinda yake damuna,
Nace "mama wai nikam yaushe Abba yasake mana sabon gina ne?"

Mama tace" ba abbanki ne yayi ba, baban Izdihar ne yayi mana "
Cikin raina nace wai baban Izdihar, ga babanta acan wani waje ga nan Ana liqawa wani ita, nace" Allah sarki, Allah yasaka da alkhairi"
Abba ma daya shigo yaga nasaki raina saiyaji dadi


** *** **

Awannan rana saida saudat tayi DANA SANI Akan Kiran ahmad datayi, domin kuwa damunta yayi da jarabar Kiran waya, Ajima kadan yakira ta yace har yanzu bata kiraba?
Saudat tace wlh yaya bata kiraba, nima jira nake, ai tana kira zan turoma insha Allah
Allah Allah yake yasamu number ya kirata, ya matsu yaji muryar ta, lumshe idonsa yayi yace my feenah, please kikira mana


** *** **


"Momy albishir inkin"
", goro sauda, menene?"
Tanada fara'ah tace
" Momy Yau sis takirani," Momy cikin rashin fahimta tace "wacce sister?"
Saudat cikin shagwaba tace "kai Momy sister feenah fa, budurwar yaya"

Momy cikin mamaki tace "wai wannan qawar taki dakukai karatu?"
Saudat tace " emana" , Momy tace " um Amma nayi miki murna, yanda kika shiga damuwa dakika rasa number ta,"
Saudat tace "Momy muka shiga de nida yaya" 🤣

Momy cikin mamaki tace "wai kina nufin itace yarinyar dayake so, yace yanemeta yarasa?"
Sauda tace "emana, itace fa Momy"
Momy tace "to ina tashige kuwa duk dadewar nan?"
Saudat tace" wallahi Momy bata qasar ne, karatu takeyi a Sudan," Momy tace" kai alhmdlh Allah Nagode ma,
Yanzu shi ahmad din yasamu labari? Sunyi magana da ita? "
Saudat tace" ai bamuyi waya da itaba a Nigeria, jiyane fa takirani, tace Yau Zata dawo qasar, idan tazo Zata kirani inga number ta", Momy tace

"Kai Amma naji dadi wallahi, Allah ya karbi addu'armu Yau

Kice mutumin naki, sai murna," saudat tace "ai Momy Yau kadai ma yakirani yakai sau biyar, wai takirani? Nace har yanzu de nima jira nake"
Momy tace "to Allah yasa ta kira" , nan sukai sallama


** *** **

Daddare Ammu yakirani awayar mama, yayimin sannu da Zuwa, yace yakira number ta taqi shiga, nace wallahi ban dora layin bane
Yace

Please Login or Register in order to submit comment