Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina dubawa naga new Num. Tattara hankali na nayi waje daya, na Bude text din
"ina miki jaje "
Abinda nagani kenan, qaran wani text din nasake ji, bayan na karanta na duba number, number da bazan taba mantawa da itaba arayuwata
Fita nayi daga wajan massage din, ina sakin wani matsiyacin tsaki
Mama data futo daga falo ta kalleni, tasake kallona, ta girgiza kai gamida fadin Allah yabaki lafiya, 🤣inba haka ba mutum yayi ta tsaki shi kadai
Kallanta nayi cikin raina nace mama kenan bazaki ganeba
Nima daki nakoma nazauna agefen gado, naci Gaba da tagumi abina, ni abinda yafi damunama yanda nake Jin jikina wani iri, saboda magungunan dasu husna sukai ta dirkamin kamar ba gobe, Gaba daya jina nake cikin wani irin yanayi, Babu abinda nake buqata idan ba mijinaba, gashi kuma al'amari ya banje 😃
Oh ya Allah gani gareka kayimin zabi na alkhairi ya ilahi!


** *** **

"Man yanaga Kanata murmushi kana typing ne?"

"Nida matata ne," inji ahmad kenan
Tahir yace "ok au wai tsohuwar matarka laila?"

Ahmad yayi masa kallan tara saura kwata, yace
" inada wata Mata ne data wuce nafeesa?"

Tahir yace "au Yau kuma Babu feenah, sai nafeesa kai tsaye?"
Ahmad yace "a a wai Dan kafi ganewa shiyasa nafadama sunanta na gaskya,
Nafada Mata ne, ta shirya karbar sabon ango, tunda wancan ya kasa"

Tahir yace "ahmad, wallahi de ka kiyaye dakyau, Dan kaima idan aka saceka, Babu ruwanmu"
Ahmad yasaki murmushi yace "sata! Saikace a film, kai nifa yanda nakejina yanzu, gani nake kawai kamar ma andaura, Dan wallahi ina Santa tahir, ina kaunar feenah, shekara da shekaru tamin nisa yanzu tadawo gareni, to saboda me zanyi sanya?"

Tahir yace "hakane, gaskya kunyi kokari dukanku,"

ahmad yace "kamarya dukanmu?"

Tahir yace "kasan abinda yafi bani mamaki Dan gane da yarinyar nan, ace namiji boyfriend dinka yayima haka, Amma saboda tsabar soyaiyar datake ma takasa fadawa iyayen ta, kaine kayi Mata laifi, ai kaima kasan ba duk matane zasuyi wannan jajircewar ba, soyaiyar ma dayaya akeyi, "

ahmad yace" to ai tahir ni feenance yanda take iya tsaya wa ta kalli idona tafadamin magana sai al'amarin nata ya dinga bani tsoro kamar tafi kowa tsana ta wallahi tahir "
Tahir hararar wasa yayi masa yace" to saika tsaya ai ta renaka," ahmad yace
" Allah mutumina,"

tahir yace" to tsaya wasa"

** *** **

Abin duniya ya yiwa laila yawa, kullum tana gida, bata Zuwa ko'ina, bata isa takai qarar dad dinta wajan hajia salaha ba, sai tace tayi hakuri, to hakuri har yaushe zai qare, daganan bata wuce ko'ina ba, kai tsaye sai wajan mahaifinta, inda ta bashi hakuri, Akan abubuwan dasuka faru, takuma nuna tayi DANA SANI Dan haka nan da nan alhaji bukhar yahadata da wani abokinsa, Dan Garin misau, alhaji Bala, yanada Mata biyu, laila Zata je ata uku, a hakanma shine yaga zai iya, yace yaji yagani zai aure ta, saboda shi mutum ne maisan haihuwa ita kuma Babu halin hakan
Allah yakaremu duniya da lahira yarabamu da sharrin zuciya


** *** **

Next day
Tana zaune awani wajan shan iska, ita kadai, tana tunanin rayuwar ta, oh yanzu shekarunta sai qara Gaba suke Amma Babu wani mashin shini
Sallamar da akayi ne yakatse Mata tunanin data Lula, daga kanta tayi tare da amsa masa sallama, babban mutum ne kamili, aqalla shekarun sa zasu kai hamsin da wani abu, yace "sannu fa yanmata," tace "yauwa fa"
Yace "tun dazu nake ta kallanki kina zaune ke kadai, idan Babu damuwa maizai hana inrage miki tunani," murmushi tasaki tace "babu damuwa bissmilla," tafadi hakan tare da nuna masa wajan zama, zama yayi tare da daukan lemon dake gabanta ya tsiyaya a cup yasha, yadubeta yace
" kiyi hakuri fa nasha miki kayanki batare dana nemi izni ba," murmushi tasaki akaro na biyu, tace
" karka damu Babu komai "
Yace "ok, thank you, ni sunana honorable sani Abdul qadir, ni mutumin kano ne, Amma nafi zama a Abuja, inada Mata daya da yarana hudu, yanzu haka nazo nan wajan ne Akan wani taronmu na siyasa

Maganar gaskya tunda na dora idona akanki naji kinyimin idan bazaki damu ba, zan so ki kasance Mata agareni, idan har banyi miki tsufa ba "

Cikin ranta tace" to wanne tsufa ma, nima dana Dade agidanmu ai gara ma amince tun kafin nima na tsufan, Allah sarki rayuwa, ni iklima naga ta kaina, inda ace tun farko na amincewa tahir da tuni na auri yaro kusan sa'a nah, Amma nabi Rudin duniya ninan sai governor, gashi yanzu zan bige a honorable
Nan take tayi DANA SANI yafi cikin carbi, batare da bata lokaci ba ta amince masa


** *** **

Yayi kyau Sosai cikin manyan kaya, yadi ne Dan uban su mai tsadar gaske, kalar golden, sai zuba qamshi yake
Cikin sauri sauri yake saukowa qasa, yana Zuwa falo yaga sauran yan gidan suna break, agurguje yaqarasa suka gaisa
Mamy tace "yauwa my son qaraso ga break dinka nan yana jiranka Yau harda mutumin Naka akai kunun gyada"

Yatsina fuska yayi, gamida dafe cikinsa yace "mamy wallahi inaso Amma kuma ina sauri ne"
, Momy ce ta dago babu alamar wasa tace " kai zauna!"
Babu musu ya zauna yana shafa qeyarsa, shikam yanzu Momy bata sansa, tun Akan abinda yafaru shida feenah
Amma aishima bayin kansa bane ko
Kofi daya yasha agurguje, bukhari yace

" yaya zaka qone fa idan kana sha da zafi,"
ko kula shi baiyi ba, yakafa kai babu wani yanga yashanye Gaba daya 🙊

Tissue yaja yagoge bakinsa ya miqe yace

" Momy, mamy, naje zaria saina dawo"

Baby tace "uncle nima zani please"
Kallanta yayi yace "next time zanje dake kinji, Amma banda yanzu,"
Yaci gaba da tafiya

Mamy hakima tayi karaf tace, "zaria kuma? To Allah yasa de lafiya Dan naga Kanata sauri"

Kafin yabata amsa Momy tace "ina kuwa lafiya hajia zaije ya kashewa yar mutane de aure yadawo" 🤣

Cikin sauri yakai kallansa gareta
Baice komai ba ya girgiza kai yafice cikin sauri
(nikuwa cikin raina nace ina ruwan kanku akeji 😃)

Bai Dade da tafiyaba saudat takira su Momy suna gaisawa, kowa saida aka bashi suka gaisa, baby kuwa saida aka qwace wayar,🤣 saboda surutun nata bana qare bane

Zasu yi sallama ne, Momy tace "ya maganar zuwan naki? Zakizo bikin ne da wuri kokuma sai abin ya matso?"

Ajiyar zuciya saudat tayi, tace "hmm wanne biki Momy da anfasa"
Momy tace "bangane ba, kamar yaya?"
Saudat tace "wallahi munyi waya da ita rannan tacemin anfasa bikin nata, daga bangaren angonne aka samu matsala,"
nan de ta basu labarin komai
Momy tasa salati tare da kashe waya

Ta dubi mamy hakima tace "hajia ashe shiyasa danki yake ta rawar kafa zashi zaria" 🤣

Mamy tace "me yake faruwa hajia?"
Momy tace "ashe wai kinji anfasa bikin yarinyar nan ne, shine dagajin labari yadebi kafa yatafi, banda rashin hankali irin na ahmad daga faruwar Abu yadiba kaje musu gida salon suce dama murna kake da hakan?" 🤣


Guda mamy hakima tasaka tace "alhmdlh
A a hajia banga laifinsa ba, gara yaje tun kafin wani Yarigashi"
Murmushi kawai Momy tayi
Dan ita kanta tana yiwa danta fatan samun feenah


** *** **

Yana faka motarsa a kofar gidan, yashiga ciki, batare da tunanin komai ba, saide idan yatunada abinda yafaru abaya sai yaga da wanne ido zai kalli wadannan bayin Allah
Kawai shahada yayi yashiga
Mama tana tsakar gida tanashan hantsi
Sallama yayi, ta amsa masa da mamaki, tace
" a a ahmad ashe kaine atafe"

Kansa aqasa bai yarda sun hada idoba yace " eh wlh mama, dama zan wuce ne nace bari in qaraso mu gaisa daku tukunna" 😉

Mama tace "ahhh aikam ka kyauta, ya wajansu hajia da izdihar din,"

ahmad yace "sunanan kalau, daddy ma yace a gaishe ku, Yama bani saqo yace akawo muku"

Bai jima da rufe bakinsa ba, samarin dayace su taimaka su shigo masa da kaya suka fara shigowa dasu doya ne, taliya, macaroni, jarkokin mai, su indomie,yasan idan yace shine yasiyo fada Zata masa

Mama tacika da mamaki, shida yace Akan hanya yake me kuma yahadashi da kaya?🤣 Tasan sarai aikinsa ne
Dan haka tace "kaide kullum baka gajia ahmad"

Shiru yayi tare da Sosa qeyarsa

Abba ne yafuto daga falo yaci binjimar Riga, saboda yanayin sanyi, nan yagansu a tsakar gida
Mama tace "Abban husna ai yanzu nake shirin kiranka ku gaisa da ahmad"
Abba yace "kice baqi mukayi"
Hannu yamiqawa ahmad, ahmad yaqi bashi hannun yakoma ya tsugunna yagaida shi har qasa
Hakan dayayi saiya birge Abba

Abba yace "kace Yau da safe kake take, kuma ahmad baka gajia da wahala haka"

Murmushi kawai yayi Baice komai ba, dama kuma shima Abban baisa ran Jin amsar sa ba,🤣 saboda yasan Hali
Dan haka yaci gaba da cewa, "wannan nasan ai ko break fast ma bakayi ba

Shigo falon azuba mana abinci"
Babu musu sukai cikin falon dukansu harda mama

Mama ce tafara hada musu,abincin Abba yace "a a kekuma bazaki hutaba, kira yarinyar nan tazo tahada mana"
Daga murya mama tace
"nafeesa!"
Gogan naku cikin ransa yace "alhmdlh" 🤣

Da sauri na futo daga daki kaina ko dankwali babu,kasancewar nasan Babu kowa agidan, dagamu saimu rigar jikina robace, Dan haka shafe dina yabaiyana acikinta, yan madaidaitan breast dina dasuke a tsaye, sai suka qaramin kyau
Ina futowa falon dashi nafara tozali
Cikin sauri najuya daki

Cikin ransa yace "ya Salam
Karfa yarinyar nan tasa yaji kunya agaban surukai"

Shima sunkuyar da kansa yayi qasa cikin sauri

Nadau lokaci kafin na futo cikin dogon hijabi na har qasa ina hada musu shayi
Tsintar muryar Abba nayi yana bashi labarin fasuwar aure na da mukhtar 🙆🏻😃

Cikin tashin hankali ahmad yace "subhanallah Amma Abba Garin yaya,?Tome akayi musu haka mai zafi?" 🤣


Ina zuba musu sukkar (suger) a shayi cikin raina nace lalle mutumin nan Dan renin hankali ne



(nikuwa nace na gaske feenah)






Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family


59


Abba yace "wallahi matsala aka samu daga shi yaron mukhtar..." Nan Abba yaci gaba da bashi labari harya Gama
Ahmad yayi shiru kamar gaske, can yace "to Abba Allah yarufa asiri, Allah yasa hakane yafi alkhaairi"

Abba da mama suka hada baki wajan fadin
" amin"
Ina Gama zuba musu najuya zan koma daki, Abba yace "uwata kinci abincinne ke?"
Babu abinda naci Amma saboda banasan zama kusa da ahmad yasa nace "eh Abba naci,"

mama ce tace "yaushe kika futo falon ma bare kici abinci?"
Abba ne yakarbe zancan da fadin, "naga alama yarinyar nan tunda abinnan yafaru batasan zama acikin mu ma, bare ta kwantar da hankalin ta, har ta murmure tadawo kamar da
Dan haka babu inda zaki, zauna kici abinci,"

mama ya kalla yace "meyasa kike barinta ita kadai ne, bayan kinsan lalurar datake tare da ita ba'a San ta cika tunani?"

Mama tace "to alhaji ai gatanan agabanka, kai kayi Mata fadan ko kai dabata renaba zataji maganarka"
Kaina a sunkuye, na dawo nazauna, shayi kawai nakesha, sai wainar qwai, shima inaci kamar banaso

Shiru ne yabiyo baya, ahmad cikin ransa yace lalurar menene take damunta? Dole zai tambayeta yaji, Dan shikam bazai juri ganinta cikin damuwa ba, ya gwammace shiya fuskanci matsalar ita kuma ta zauna cikin kwanciyar hankali
Dan yasan tabbas abaya ta fuskanci abubuwa dayawa, wanda bai saniba
Abba ne yace " ahmad kaima naga bakasan cin abincin, kamar uwata,"

dagowa nayi da nufin kallonsa, adede lokacin da shima yadago kansa
Harara na balla masa, cikin sauri ya sunkuyar da kansa, mama datake kan kujera tana kallansu ta gefen ido

Murmushi ahmad yasaki, yace"Abba inaci"
Hamdala Abba yayi, ya miqe zai fice, mama ma tafara kiransa tabishi suka fita tare
Shiru ne yabiyo baya
Mantawa nayi dashi awajan, naci Gaba da shan tea
Ajiye nasa cup din yayi, yayi tagumi da hannun sa biyu, yazuba Mata ido, yana sakin murmushi
Ina kallansa na share shi
Wainar danake ci yasa hannu ya karyo kadan, ya nufo bakina da ita
Harararsa nayi, yace "koki karba kokuma in miki dura yanzun nan wallahi"
Yatsina fuska ta nayi nace "kamarya, miye hakan Malam?"
Daure fuska yayi yace
" zakici ne kokuma inmiki dole?"
Tashi nayi zan shige daki, yayi saurin riqo hannu nah, yatashi tsaye, cikin Daure fuska yace "kikarbi wainar nan ko"

Ido nane yacika da hawaye, cikin rawar murya nace "toka rabu Dani mana, dole ne?"

"Zauna"
Yafadi haka babu alamar wasa, zama nayi na sunkuyar da kaina, tausasa muryarsa yayi yace "my feenahhh"
Har cikin raina naji sunan
Amma ban amsa ba na qyaleshi
Yaci gaba da fadin,
" meyasa bakya sona ne yanzu? Meyasa kika tsaneni feenah?"

Shiru nayi ina ajiyar zuciya
Yace "nide kowanne lokaci kina nan acikin zuciyata, bazan iya cireki daga ciki ba,"

sake tausasa muryar yayi, kamar rada, yace
" my feenah ki yafemin mana, naroqeqi kiyi hakuri feenah"

"Nide ka barni natafi"
Abinda nace kenan, yace
" zan barki Amma idan kin tsaya kinci abinci
Kiyi hakuri kici abincin to,banasan ki zauna da yunwa, kinji? Yi hakuri ci abincin badan halinaba"

Shiru nayi, nasa hannu naci Gaba da cin abinci na, shikuwa yazubamin ido yana kallo na kamar tv
Tsintar maganarsa nayi yace "me yake damunki?"

Kallansa nayi nace " lafiya nake"
Yace "Amma naji Abba yace bakyajin dadi, menene yake damunki?
Kokuma mu tafi asbiti bayan kin gama?"
Ido nazaro nace "dawa zakaje asbiti? Saide wata Amma bada niba"

Shiru yayi yana aikin kallona, wainar de yasake karya yanufo bakina, nakawar da kaina, yace "please," banza nayi dashi
Yace "naga bakyaci ne dayawa,"
araina nace renin wayo, kamar shi din ci yake
Nace "Dan Allah ahmad karabu Dani nahut..."

shiru nayi Jin ya turamin wainar abakina
Adede lokacin mama tashigo
Tace "ahmad har yanzu tana nan tanacin abincin nata kamar mage ko?"

Nace "mama aina qoshi ma"
Flet din naharhada zanmaida kitchen, natafi zankai, shima ahmad yayi sauri yadauki flask din tea yace "bari intayata mama," 🤣

shima yabiyoni kitchen din, mama murmushi tasaki tabisu da kallo, yaro me kunya, Amma yarinya duk tana nema ta susutar dashi
Nikuwa cikin raina nace Yau naga ta kaina da jaraba
Ina ajiye wa najuyo zan fice daga kitchen din, daidai lokacin shima zai ajiye flask din, aikuwa sai ji kake garam munyi Karo
Nabige agoshi na, hannu na nadora awajan ina shafawa yace "oh sorry, aina biyo kine, kiyi hakuri bansan zaki juyo bane, sannu kinji"
Yafadi hakan da sigar rarrashi, matsowa yayi dab Dani yafara huramin iska awajan, hakan dayayi shiya haifar min dajin wani yanayi atare Dani, shima daga wajansa hakan take
Cikin muryar rada yace "my feenahhh
Ina kaunar ki sosai, please Dan Allah kisoni kema, inaso kibani dama in aure ki, inbaki kulawar data dace"
Dasauri nabar wajan nayi falo, ina Zuwa naga mama bata nan Dan haka nima nayi daki

Ina shiga daki nafada kan gadona ina sakin numfashi, idan banyi da gaske ba tabbas ahmad zai wargazamin tunani na

wuta aka kawo, mama ta futo daga daki zatai kallo, taga ahmad a zaune shi kadai, da mamaki tace "a a ina nafeesan take? Ai nayi Zatan tare kuke,"

ahmad yace "tana daki mama"

Bata ce masa komai ba, ta kunna kallan, ta wuce Dakin danake, tana Zuwa adaidai lkcin ina saka kaya, kasancewar nayi wanka
Tace "miye hakan kikeyi ne? Mutum yatako yazo har inda kike Amma ki barshi afalo? Dan nasan sarai wajanki yazo, banasan shirme kinji ko?"

Tana Gama fadar haka Takoma Dakin ta
Shima ahmad din danna wayarsa kawai yake

Falon nafuto inata zuba qamshi, nanemi waje nazauna, bance dashi komai ba
Adaidai lokacin wayar ahmad tadau qara, amsawa yay ahankli saikace wani basarake
Tahir yace" man kagama shiryawa ne zaka wuce zarian?"
Ahmad cikin mamaki yace" wanne zaria? Aini 12:00 ma a zaria tayimin
Yanzu ma gani ga matata"
Yafadi hakan yana kallona
Tahir yace "tab, gaskya dole inziga su mama sudena Bude gida da wuri, Dan wataran da asuba zasuji Ana qwanqwasawa"

Ahmad yace "haba de, kaima kasan ai ko cikin dare ne zasu bude min"

Bayan sun Gama wayane yadubeni yace "ki cewa mama zan tafi,"

bance dashi komai ba, naje Dakin ina Zuwa naga tana bacci Dan haka na dawo cikin sanyin murya nace masa "tana bacci"
Yace "ok, to zan tafi, sai yaushe?"

Nace "ka gaida su Momy,"

yace "bakya buqatar qara ganina kenan?"

Ko kunya nace "eh,"

yace "Toshiknn kinsan mu kuma inda ba'a neman mu munfi Zuwa wannan yankin, Dan haka ki saurari ganina a kowanne lkci,"

yana fadar haka yafice
Harya shiga mota zai tafi sai ga Abba yadawo, futowa yayi sukai sallama, Abba har yajuya zai shiga gida yajuyo yaga ahmad a tsaye awajan, da mamaki yace" ahmad lafiya kuwa?"

Babu kunya ahmad yace" Abba dama inaso zan fadama ne mun dedeta kanmu nida nafeesa dazu "🤣

Cikin mamaki Abba yace
" a a ikon Allah, "

kafin yasake wata maganar kan ahmad a sunkuye yashige mota Yabar wajan cikin kunya, shikuma Abba yayi gida yana fadin yaran zamani kenan

** *** **

Kiran sallar farko ne yayi sanadin farkawarsa daga daddan mafarkin dayake shida feenah, kai aure me dadi, gaskiya yakamata yayi da gaske ayi ayi ayimusu aure, Dan gaskya shikam yagaji da wannan halin dayake ciki
Kallan kansa yayi yaga abinda mafarkin nata ya haddasa masa, Dasauri yadiro daga gadon, yayi toilet, yana fadi cikin ransa dole Yau yaje wajan feenah Susan a inda suka tsaya, wannan boye boyen yafara isarsa, Tsawon sati daya banda wahala babu abinda take bashi, haba Dame zaiji? Da wannan jarababban mafarkin koda fitinar ta,?

Dan haka da safe yana Gama shiryawa ya cewa mabaruka ta shirya baby zasuje zaria, bata dauki lkci mai tsawo ba, tagama shiryata, bayan sunyi sallama da kowa suka dau hanya

Da azahar sukaje, adaidai wannan lokacin nikuma naje maqota, ina futowa wani saurayi yatareni yana tambayata sunana
Muna tsaye ni dashi a kofar gida, daidai lokacin motar ahmad ta tunkaromu, cikin bacin rai ahmad yace "baby, waye nake gani wancan tare da antynki?"

Izdihar ta ware hannayenta biyu alamar bata saniba tace "to uncle ina zan sani?" 🤣

Dasauri ya qarasa wajansu, feenah kawai ganinsa tayi agabansu kamar an wulloshi, da mamaki take kallansa, ahmad yamiqawa saurayin hannu suka gaisa, daga baya yace
" Dan samari nasan baka saniba shiyasa kake tsaye tare da matar aure ko? "
Saurayin yace
" subhanallah kamarya ina tsaye da matar aure? Me kake San fada bawan Allah?"

Ahmad yadaure fuska yace "qwarai kuwa abinda kunnanka yajiye Maka shi nake nufi, matata ce, duba nan, yayi masa nuni da baby, yace kaga yarmu nan, Dan haka banasan naqara ganin kafarka anan, inba haka ba wallahi hukuma ce Zata rabani dakai"

Yajuyo kan feenah yace
" kekuma wuce mu tafi gida kafin ranmu yabaci anan"

Cikin takaici nace "babu inda zani, tunda ba iko kake daniba" , ahmad yace "ok haka kika ce?"

Nima cikin dakewa nace
" qwarai kuwa haka nac..."

Maganar daban qarasaba kenan ahmad yasa hannu yadaukeni cak, yayi cikin gida Dani, har key din dayake hannun sa yana faduwa, aikuwa baby tasa hannu tadauka itama ta biyo bayanmu

Saurayi dayaga abinda yafaru nan yace astagfirullah, haqiqa wannan mutumi yafini gaskya tunda gashi ya nunamin hakan

Allah ka yafemin, Dan haka shima yadau hanya yayi yamma


(nikuma nayi gabas🏃🏼‍♀)




Mrs Usman ce 🖊🌱
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

60


"Kasaukeni banaso, wannan ai wulakanci ne,"

abinda nake fada kenan, ina zillewa alamar qwatar kaina
Mama tana zaune atsakar gida taga an shigo Dani ahannu, tsintsiyar datake hannun ta ce tafadi, tace
" subhanallah meya faru?"
Kokarin saukowa nake raina yayi mutuqar baci
Kafin insauko ahmad yace "kiyi a hankali mana karki fama ciwon naki"

, yadubi mama yace,
" mama faduwa tayi awaje, shine muka ganta takasa taka kafar, shine ni kuma... Am shine"

Yadubi baby datake tsaye yace "ko baby?"

Aikuwa baby tadaga kai, alamar eh hakane

Mama tace "subhanallah, to Allah yakiyaye, kaita falo, muje, muje"
Mama tariqo hannu na tana min sannu, Gaba dayama mamakin ahmad yacikani, ciwo kuma!
Lalle wannan mutumin Dan duniya ne
Akujera ya ajiyeni, mama tace "bari adauko ruwan zafi saita dunduma wajan"
Tana fita, baby ta tashi tafado kaina, shima ahmad din aqasana ya zauna batare daya hau kan kujerar ba, tace
" antyyyy"
Hararar ta nayi nace "niki dagani, tunda kinfi sansa akaina"
Baby tace "anty kiyi hakuri, kinga tunda safe muke ta murna zamuzo wajanki nida uncle"
Nace "to karku sake Zuwa banaso"

Tace "to ai anty mu muna so, ni inasonki, kuma uncle ma yana sonki, kuma anty tunda dadewa naketa cewa kema ki dawo gidanmu kikaqi, ai dole ace kinji ciwo, tunda bazaki iya tafiya ba" 🤣


Cikin bacin rai, nadaga hannu zan daketa, ahmad daya zuba ido yana kallanmu yayi sauri ya riqe hannu nah, yace
" haba! Haba feenah, yanzu saiki daketa? Kamar wata qanwarki? Yanzu kema ai saiki zama yarinya irinta, kokuma kin manta da matsayin ta ne awajanki?"

Mama ce tashigo falon da ruwan zafi ahannun ta
Tacemin "ungo wannan kidan gasa kafar taki"

Araina nace nikam Yau naga ta kaina, Babu abinda yasameni Ana nema adauramin jinyar qarya
Ruwan nakarba nafara dundumawa a hankali, mama tace "a a wannan ai Bayi kikeba, kawo kigani"
Ahmad dayayi shiru yadan matsa kadan yabasu waje
Mama tana saka Mata ruwan tasaki qara, batasan lokacin datayi jifa da handkerchief dinba
Mama tace "au! dankin samu ma nayi miki shine kikemin wannan abin, to gashinan sai kiyi da kanki, kokuma kafarki tayi tsami, kanki ki kayiwa"
Tatashi Takoma wata kujerar, baby ma tabi bayanta, tace "mama, ina abbana?"
Mama tace "ai munyi fishi izdihar
Kina ganina dazu kika shareni" 🤣

"To mama ai anty nagani"

Mama tace "aikam nagani baby, shine sai yanzu kika lallabo wajena, nasan yanzunma akwai abinda kikeso ne shiyasa"

Handkerchief din yadauka a hankali, yamiqa Mata cikin muryar rada yace "gashi kiyi"
Banza nayi masa

Mama tajuyo tace "ka kyaleta ahmad , ai kanta Zata yiwa"

Baisake magana ba yadauka yadan tsomashi kadan acikin ruwan
Kafar tata yakama ahankli ya zubawa ido, maimakon yayi abinda zaiyi, saiya zubawa Zara zaran yatsun kafarta ido
Ahankli ya ajiye handkerchief din yasa dayan hannun sa yana shafa kafar a hankali, dayake sunbawa mama baya, Babu wanda zai fuskanci wani Abu

hannun sa yamaida tafin kafarta yana shafawa ahankli, wani Abu nakeji yanamin yawo tun daga kaina har tafin kafata

Dasauri nafara kokarin qwace kafata, hakan danayi ne yadawo dashi daga duniyar daya Lula, firgigit yadawo daga tunani, yadauki handkerchief din ko acikin ruwan baisaka Shiba, yafara goge Mata kafarta cikin sauri

Qwace kafata nayi, nafara tafiya ahankli na shige daki, mama ce tabini da kallo

Wajan data tashi ya zubawa ido yana kallo
Ajiyar zuciya yasauke yatashi yadawo kujera,

nan mama tafara tambayarsa mutanan gida, suka sake sabuwar gaisuwa
Baby tace "mama nikam yunwa nakeji," mama tace "af kuyi hakuri, bankawo muku abinci ba,"
tashi tayi, takawo musu jalof din taliya dataji kifi da ganyaiyaki
Hankalinsu kwance sukaci abincinsu shida baby
Mama ce ma me kokarin jansa da fira, shikum yayi gim babu um bare um um
Mama cikin ranta tace wannan kam bazan iya wannan halin nasaba, bari inturo masa wacce ta iya dashi
Dan haka Tatashi ta wuce dakina, tana Zuwa tace "Toni zanje maqota, yanzun nan zan dawo, kidawo falon ke"

Tana fadar haka bata jira amsataba tayi waje
Inajin fitar ta na futo kalau Dani, naware ina tafiya
Baby tace "anty mu munci abinci kema kizo kizuba kici"
Nace "kude dakukejin yunwa sai kuyi taci"
Waje nanema nazauna, baby tasake dawowa jikina tace "anty muyi wasa, ki rufamin idona ki buya, saina kamoki kema kuma sai arufe naki"

Nace Mata "ni?Saide kiyi da wata,"
bikinta taturo Gaba, tace
" ke anty komai ma bakyaso, laaa anty muga hannun ki,"
da mamaki na miqa Mata hannun kamar wata doluwa, nayi

Please Login or Register in order to submit comment