Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"yauwa"
Daga haka banma qara kallanta ba

Daniyya yake tashi, yaqara gyara zaman sa, duk Dan yahangota kasancewar tana kujerar Gaba shikuma suna can baya, "kai Allah ya mallakamin wannan babyn," yafada aransa😃

Awa uku muka diba muna tafiya takai mu ga Sudan, muna sauka, mukayi yan cike ciken takardu muka futo daga airport din, wakilinmu ne yakawo mana motoci muka shiga, bamu zame ko ina ba sai gidansa, maza kuma yakaisu wani gidan daban
Munci abinci munyi wanka, daga nan kowa ya nemi wajan hutu
Inajin yan uwana Mata sunata firarraki Amma nide bana cewa komai, kawai tunanin su mama nake

Da daddare, yazo yace mu shirya muje asiya mana sim card, haka muka fita, doguwar Riga ce ajikina kawai Dan mayafin rolling din nayafa akaina muka tafi, ina kallan wannan yarinyar da muka zauna tare tanata kallo na, Amma na share ta
Wata mota muka shiga takai mu wajan, na daga kaina na kalli wajan naga ansa AFRA da turanci da larabci, muka shiga, muna shiga wani sanyin esi ya bugoni na lumshe ido nace "um duniya" 🤣

Bamu bar wajan da wuri ba kasancewar saida aka gamawa kowa, sannan muka tafi gida, daga nan kowa yasai kati, yayi mana bayanin yanda zamuyi amfani dashi, ina kwanciya nasa nawa, nakira su mama, husna ihun murna kamar Zata fasamin kunne
Da zamuyi sallama nasawa mama kuka, itama de daurewa tayi ta kwantar min da hankali, bayan nagama wayar nakashe ta na kwanta bacci kasancewar lokacin ba daya ne dana Nigeria ba


** *** **


Hannu ya miqa masa gamida sallama yace" Malam Dan Allah ko masu gidan nan kuwa sun dawo? "

Me shagon ya kalleshi yasake kallansa yace" Amma bawan Allah ko yan'uwanka ne wadannan mutanan yaci ace ka rabu dasu, kazo kazo, ance basa nan Amma kaqi hakura, haba"🤣

"To sun saida gidan, sun siyar shi, yanzu haka wani alhaji ne zai rushe wannan din yasake sabo"

Ahmad yace "to Malam na gode,"
mutumin yace "to Allah yatsare,"
yana tafiya ahanya aransa yace shikkenan tafaru taqare tabbas nasan narasa ta, narasa feenah



** *** **


"Gaskya musa wannan zaifi,"

"kai ahmad fararan nan zasufi kyau, Allah,"

"nikuma sai naga blue din zasufi yi mana kyau tahir"

Tahir yace "a a ranace ta farin ciki, Dan haka gaskya musa farare,"

"ok" kawai Ahmad yace, yadi ne fari ahmad ya dinka musu, yaji aiki mai tsada, fararan agogo, farar hula, da babbar Riga wadda taji aiki mai kyau, shikuma tahir ya dinka musu blue mai kyau, daddy ne yakira su yace to shi zai wuce, su idan sun Gama batawa kansu lokaci saisu futo

Aida sauri suka futo, masha Allah kowa yagansu saiya sake waigawa sunyi kyau sosai kamar asace su a gudu, sunzo harabar gidan, tahir ya daga wayarsa yace "my man kalla,"
ahmad yana juyowa tahir yayi musu selfie, sunyi mugun kyau, daddy dayake zaune a bayan mota shida driver aransa yace wadannan yara saisu, kuda ake jiran ku kune masu photo😃 kallansu yasake yi, kamar su biyu ne angwayan, shima ahmad inda ace tasan tana nan aida an hada anyi musu auren shida abokin nasa

Suna shiga mota driver yaja, sannan tawagar mutane sukabi bayansu

Amasallacin juma'ah aka daura auren tahir da husna bisa sadaki naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba, ango yaja ahmad suka sulale suka futo waje, ahmad yace " shikkenan de alkawari yacika," tahir yace "wallahi kuwa gwauro"
Ahmad yace "iyee yaushe akama auren dazaka fara min tsiya zaka sameni ne inde nine," abokansa ne su doctor Bashir duk sukazo suna masa tsiya wai y dauke musu dalibarsu, to daga yanzu sun dena nemansa,🤣 Dan kar yaga wata ya yiwa dalibarsu kishiya, haka sukai ta masa tsiya da fatan alkhairi suka juya gida
Tahir yakira husna yace yanaso yaganta kafin yatafi, Babu yanda ta iya haka ta cewa mama zataje su gaisa dasu tahir
Mama tace to ai nan akwai cikowar mutane kuje can gidan ammunku saiku gaisa anan
Anty maimuna ce mai cewa karde ki bari komai yafaru🤣🤣 husna tace to my anty

Duk inda tayi Ana ga amarya
Haka ta futo taje gidan Ammu, tayiwa su tahir din kwatance sukaje
Ruwa takawo musu da lemo suka zauna afalo, sannan ta futo domin su gaisa, dama a kace jini daya yafi karfin wasa, ahmad yana ganinta yaji gabansa yafadi
Duk Dade ba wata kama suke d feenah ba saide kama ta yan'uwan taka, bayan sun gaisa ne tahir yace " husna ga babban abokina aminina kuma dan'uwana ahmad," husna tace "au dama shine?"
Ahmad daya Zuba Mata ido yana kallan yanayin ta da muryarta kusan ta feenah yace "eh nine yakike?"
Husna tace "lafiya,"
yace "to alla yabada zaman lafiya," 🤣

daga haka yatashi yayi waje
Husna ta dubi tahir tace" my heart dama haka yake? Daga gaisawa sai tafiya?" Tahir yace" haka yake, dama budurwarsa ce tadan sauya mana shi, kuma yanzu basa tare shine yakoma halin sa nada, "

husna tace" Allah sarki, to Allah ya bashi ta gari"

tahir yace "amin,"

daddy ne yakira wayar tahir yana jiran su suzo su tafi, Dan haka tahir yamike ya yiwa husna sallama, harya fara tafiya dayaga de batada niyyar tashi yazo yatsugunna agabanta yakama hannun ta yayi kissing, yasake yi Mata akumatu sannan yafice da sauri, kunya tasa husna rufe idonta da hannun ta 🙈

Yana fita ahmad yace" gaye ka shanyani da yawa fa, kaje ka wani liqe Mata,"
tahir yace" to kasan masu aure, ai Baza ayi sallama Babu dan hugging ba bare kiss,"🤣

ahmad yace" nawan nema kake ka fitsare tun ba'a je ko ina ba, gara ma d Allah yasa agaban ummi zaku zauna," tahir yace" eh wlh banasan zaman nan Dan gaskya nafiso ina jina ajikin iyalina," ahmad yace" tahir kafi karfina muje daddy najira "
Awajan su daddy can masallacin da aka daura aure anan sukaga Abba, tahir ne yaja ahmad yace " ga Abba nan muje mu gaisa "

Sosai suka birge Abba yaji aransa dama ace duka su biyun surukansa ne, saide haka Allah yatsara, haka sukai sallama da mutane ko gidansu husna basu jeba suka tafi kano
Wasu daga ciki kuma suka dakata saboda daukan amarya


** *** **


Cikin kwana biyu aka nema mana gida awata unguwa mujahideen kusa da makarantar danake, an tambayeni me nakeso in ci Gaba da karanta kai tsaye nace inaso inci Gaba da Arabic dina, nan da nan kuwa aka kaini wata mkrnta Khartoum international instute of Arabic language, kuma inajin dadin karatuna kasancewar inajin larabci shiyasa wasu abubuwan basamin wahala
Dana dawo daga mkrnta zan shige dakina nini kadai, inyi wanka inyi bacci idan Natashi kuma inyi karatu
Gida daya nake da wannan yarinyar damuka zauna da ita a jirgi, saide kowa dakinsa, kullum ta ganni zatamin murmushi tamin magana, nikuwa daga wajena bahaka bane


** *** **


Ankawo amarya lafiya ummi ta karbesu hannu bibbiyu, kowa ya yaba da part din husna, haka suka tafi suka barta, angwaye sun rako tahir inda ahmad yaja masa kunne Akan wallahi yabi musu yarinya a hankali, Dan shikam bai manta karan su da mutuniyar tasa ba🤣
Haka suka tafi suka barshi

Tahir ya umarci husna ta tashi suyi nafila saisu kwanta, gabanta yana dukan tara tara ta tashi




Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱


Writing by Amnah el yaqoub


Dedicated to my family


33


Toilet tashiga ta dauro alwala, suka gabatar da sallah, bayan yayi Mata tambayoyin daya yakamata, yatashi yakawo musu kaza gasashshiya ya tura Mata gabanta, ya tallabe kumatunsa da hannayansa guda biyu, yazuba Mata ido yana Mata wani mayan kallo, husna tace " ya haka?"
Tahir yace "um so nake kawai inta kallanki," murmushi tayi batace komai ba, Dan haka ya janyo da kansa ya yago kadan yace to Bude bakin inbaki, bakinta ta Bude ahankli yana kallanta yana bata saida ya tabbatar ta qoshi sannan yakyaleta shima yaci kadan, yadauke sauran yakai kitchen, yadawo Dakin tana nan zaune inda yabarta saide yanzu ta cire mayafin sabanin da data lullube jikinta dashi, idonsa yasauka Akan kirjinta yakasa dauke idanunsa yace Mata "ki shirya ki kwanta zanje wajan ummi, "
husna ta daga masa kai tana kallan idonsa inda yake gani daban kuma yana Mata magana 🤣

Tana gani yafita, tashiga cire kayanta, doguwar Riga marar nauyi ta dauka tasaka, takashe wutar Dakin tashige cikin bargo ta kwanta

Acan kuwa yana Zuwa ummi ta kalleshi da mamaki tace "a a ya ango da yawo cikin daren nan," tahir yace "ummi sha biyu saura fa shine daren?"
Daquwa tayi masa tace" toda da yanzu ba daya bane kaje ka kula da amanar da aka baka"
Tahir yace "to ummi dama saida safe zanyi miki," tace "to Allah yakaimu"

Yafice, yana Zuwa dakinsa yatafi ya shirya cikin kayan bacci, sannan ya koma Dakin husna, yana tura Dakin yaga harta kwanta, Dan haka shima ya kwanta agefenta, ya janye bargon data rufa dashi cikin rada yace Mata "amarya," tana jinsa tayi kamar bacci take, ganin ta kyaleshi yasa ya janyo ta jikinsa, husna tace " doctor bacci fa nake," yace "nasani nan dinma baccin zakiyi,"

yafara bubbuga bayanta, qamshin turaren datake ne yaqara fizgarshi har yahade bakinsu waje daya, daga nan labari ya canja


** *** **


Ina zaune afalo, da yamma, ina duba hand out, gajeran wando ne ajikina iyakarsa gwiwata sai vest, na daura dankwali kalar wandon jikina, da madara a gabana ta ruwa kamfanin kapo, wannan yarinyar cede tazo wajena tace "sannun ki"
Nadaga kai nace Mata " yauwa," tace "Dan Allah in bazaki damuba inasan Sanin sunanki,"

nace Mata "sunana nafeesa mu'az Amma feenah ake cemin"

Tace "nikuma Zarah Ali Bashir, ni yar kano ce, unguwar rijiyar zaki,"
nace "ok nikuma zaria"

Haka Zarah taitamin tambaya ina amsa Mata, har tace "a wanne school kike,"

nace Mata "ina jami'atul daulil Arabia,"

tace "no da English,"

nace "Khartoum international instute of Arabic language"
Tace "laaa ai kusa da makarantar mu ne,"

nace "ke kina ina?"

Tace "ina international University of Africa,"

nace "jami'ah ifriqiyya kenan?" Tace "yes"
Taci Gaba da cewa "nafara karatu a yusif maitama sule, dake kano to kuma dana samu scholarship saina barshi na dawo nan, kinsan kasar tamu lokaci kadan sai ace yajin aiki,"

nace
" hakane to Allah yabamu sa'ah"

tacemin "amin"
Tasake cewa "kina level nawa ne yanzu?"

Nace " level 2"
Cikin mamaki tace
" kamarya?"
Nace "eh ai nayi amfani da kwali na na diploma ne saboda haka sai suka bani direct level 2"
Tace "ok kinyi diploma agida"

nace "emana"
Tace "eh dama sunayin haka,"
"to Allah de yabamu sa'ah ni, ina level 1 yanzu"
nace "Allah ya temaka," tace "amin"

Cikin lokaci kankani Zarah ta shigemin dayake tanada surutu Dan danan tadinga jana da fira tun bana sake wa har yazamo nasaki jiki muna ta daria
Hakan yasa naji dadi Dan dama ina cike da kewar yan gida


** *** **


"Yi hakuri mana daure ki taka,"
tana yarfe hannu tana hawaye tace "doctor bazan iyaba,"

Dan haka yadauketa ya kaita toilet yahada Mata ruwan wanka sannan yafuto, shima Zuwa yayi yasake wanka, sannan yadawo Dakin yana zuba qamshi, lokacin tana zaune agefen gado tana shafa mai, kayanta yadauko Mata yazo yace " to taho insa miki," batayi musu ba ta tsaya, yana saka Mata Riga hannun sa yatafi yawo wani wajan hakan yasa tace "nide Allah nahakura kabani rigata,"
ganin idonta yaciko da qwallah yasa yace cikin murmushi "to naji saka, shikkenan?" ta gyada masa kai
kansa yasa atsakanin kirjinta yayi kissing sannan yace "natafi wajan ummi" 🤣


Yafice da sauri
Yana Zuwa part din nata yaganta tana hada break yace "ummi morning," tajuyo ta ce "Dan ummi har antashi?" Agogo ya kallah yaga 11:30yace" ummi yanzu ne har? "
Tayi murmushi tace" ashe kasan ka Dade kaima, kunata baccin gajiya najira Baku tashiba nace to nide bari inci abinci na, ku kuma ga naku nan nagama hada muku yanzu, "tahir yace" to ummi thank you "
Dining yanufa yaci abincinsa ummi tana kallansa saida yagama taga yatashi tace" a a yanaga ka cika cikinka ita kuma husnan ko nemanta bakayi ba?"
Tahir yace" zanje in kira tane, "

girgiza kai kawai ummi tayi, yana Zuwa yaga tana fesa turare yaje ya janyo ta jikinsa, yace" muje kiyi break "tace" to"

suna tafiya a hankali kamar me koyon tafiya husna tace " Allah nide nagaji," tahir yace "yanzu yaza'ai,"
husna tace "kuma ni wallahi kunyar ta nake naje ahaka," tahir sabarta yayi ahannu suka tafi, husna tana "kasaukeni" yace "haba yarinya," saida sukaje har falon ummi tana ganinsu ta kawar dakai kamar bata gansu ba, aranta tace oh ni yasu wannan yara ko kunya, saida ya kaita har gaban ummi sannan ya ajiye ta, husna idonta aqasa tace "ummi ina kwana?"
Ummi ta shafa kanta tace "sannu husna ya gajiyar biki"
husna tace "alhmdlh," ummi tace "tahir kuje kazuba Mata abincin mana,"
cikin sauri tahir yace "a a ummi batajin dadi ne bari inkawo Mata nan," ummi aranta tace waini za'a yiwa wayo, oh tahir ko yaushe ma yagirma
Abincin yahada Mata taci Dan kadan, ummi tace "a a husna ci mana," tace "wallahi ummi na qoshi," tahir yayi qasa da murya ita kanta husnan taqyar takeji, yace "meyasa bazakici ba?" Tace "bakina ba dadi doctorcc
Aikuwa ya daga murya yace" ummi wai bakinta ne ba dadi," husna kamar kasa ta zaqe ta shige Dan kunya, ummi tace" a a to ai sai Asa ayi Mata wani abin "
Me aiki ta kwalawa kira tazo cikin sauri, tace" dafawa husna ferfesun kaza medan yaji, batajin dadin bakinta,"🤣 me aikin ta juya cikin sauri


** *** ***

Alhmdlh anyi zabe lafiya angama kuma muhd marzuk mahaifin ahmad yayi nasarar samun kujerar daya nema, gida kowa yana farin ciki, shi kansa marzuk saida yazo daga masar shida matar sa baraa'ah tsoho mai ran karfe, gida yacika da yan'uwa da abokan arziki, su saudat da farouq duk sun zo
Ana ta zance kowa da kowa saide baraa'ah da bata iya hausa sosai ba itama tana kwabawa Ana daria
Amma ahmad yana danne danne awayarsa, marzuk ya kalleshi yace "me yake damunka ne abokina?" Ahmad yace" tsoho Babu komai "
Haka sukaci Gaba da firarsu, saida daddare bayan daddy da mahaifinsa sun kebe, anan daddy yake fadawa mahaifinsa abinda yake damun ahmad din, anan alhaji marzuk yace" to ni inaga abinda za'ai shine, zan yanke hukunci Akan hakan kafin natafi "daddy yace" to abeey "


** *** **


Muna zaune afalo dukanmu mu hudu Ana ta fira dayake weekend ne Babu makaranta, ina karanta novel awaya ta, Zarah tana gefan kaina zaune suma sauran biyun suna zaune , Zarah tace" gaskiya feenah kanki yaci tsifa," nace

" wallahi wannan makarantar ce tasa banda lokaci," kaina ta dora Akan cinyarta tace

" zona tsefe miki gobe sai muje wajan wankin kai," nace" ok," tanamin tsifa da hannu daya, kasancewar gashina yanada laushi dayan hannun tana chting
Kawai mukaji tasa qaran murna, dukanmu muka kalleta kowa yana tambayarta menene? tace wallahi yaci, inasan mutumin nan wallahi, MUHD MARZUQ sunci zabe
Aikuwa kowa yadau murna, gabana yafadi araina nace muhd marzuk, mahaifin su saudat kenan, bangama tunanin ba, naji daya daga cikin mutum biyun nan tace "ni wallahi dansa ne yake birgeni," 🤣
gabana yabada dam
Taci Gaba da cewa "har a Facebook ina dashi saide matsalar ba kullum yake hawaba, wallahi gayan yatafi Dani, ina sansa dama ya aureni, ya iya dressing, ga shiga mota kala kala,"

zarah ma tace "to ba dole yashiga motaba, shida a kace yanada kamfanin mota,"

sauran suka hada baki wajan cewa "kamfanin mota!!!" 😳

Zarah tace "eh wlh, ai kwanaki gwamnatin kano tayi bincike Akan kamfanin tana tunanin da kudin gwamnati babansa yabude masa kamfanin, saida akayi bincike sannan aka gano kakansa ne dayake Egypt yabude masa kamfanin"

Wadda tace tana sansa, tace "um kamfanin mota wallahi harna qaraji na tsunduma asansa" 🤣

Itama dayar tace "niko dazan ganshi ma kawai so nake muyi pic, Dan Allah sister da wanne suna yake amfani a Facebook?"
Ta tambayi yar'uwarta, dayar tace "da AM MARZUQ yake amfani, kuma nasan Dan kar agane shine yasa yake amfani da hakan
maimakon yabarshi a Ahmad muhd marzuk dinsa,"
Zara tace "tab aikuwa kema kinsan irin wannan ba ganinsu ake sosai ba," ta kalleni tace "feenah kinyi shiru," 🤣

cikin takaici nace "Tome zance nida ba jihar muba,"
cikin raina kuwa jinake kamar na shaqesu su duka, wai sunasan my Ahmad

Zarah tace "au gaskya kam bazaki sansu ba, suna da kirki sosai mahaifinsa kowa yana sansa,"

nace "uhm,nide karasamin tsifata" 🤣


** *** **


Tsoho marzuk ya kalli ahmad yace, "nayanke shawarar zamu wuce dakai Zuwa Cairo nanda kwana biyu, Dan haka kayi shirin komai kabar komai na kamfanin ka a hannun mutum mai Amana," ahmad daya rasa dalilin tafiyar yace "to Allah yakaimu," yatashi yatafi, marzuk ya kalli daddy yace "inaga hakan zaisa ya manta da yarinyar harya warware kamar da," daddy yace "abeey hakan yayi sosai shukran (na gode)" marzuk yace "afwan (you're welcome)"


** *** **


Tahir yace" inaga hakan yafi saboda mutumin yanada kamala, zai iya komai yanda ya dace", ahmad yace "toshkn," sakatariyar sa yakira yace takira masa hassan, Ammu yana shigowa suka miqe suka gaida shi, Ammu yace "haba menene kuma abin tashi?"

Tahir yace "to ai kai yanzu gaisuwa har qasa,"
Ahmad yace "tunda muna auren yarsa ba" 🤣


Dukansu suka sa daria
Anan ahmad yayi masa bayanin yanaso yabashi ragamar manaja na wannan kamfanin, saboda akwai tafiyar data kamashi Zuwa Egypt, Ammu ya dinga godia da kuma alkawarin kula da komai insha Allah, tahir yasosa kansa yace "aimune da godia Ammu," 😉

Ammu yace wa ahmad, "yallabai wannan sirikin nawa kaja masa kunne," 🤣 Yafice yana daria

Ahmad ya kalli tahir yace "to kai kaji,"
tahir yace "ah to ai gaskya ne, mune da godia bakasan abinda nake ji bane shiyasa" 🤣

ahmad yakai masa duka yace "wallahi bakada kunya"


** *** **


Next day, su ahmad shida kakansa suka Lula kasar Egypt





Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱


Writing by Amnah el yaqoub


Dedicated to my family


35


Tahir yajanyeta daga jikinsa yatashi ya zauna dakyau da wayar ahannunsa, husna ta dafashi tace "doctor lafiya?" Tahir yace "ai nasan wannan yarinyar," husna tace "Zata iya yiyuwa tunda anan tayi karatunta
Amma A'ina ka ganta?" Bai bata amsaba fuskarsa cike da mamaki yace "Amma tanada aure ne?"

Husna cikin mamaki tace "gaskiya bata dashi, wai a ina ka ganta?"
Doctor yace "Amma in hakane kamar ta baci, husna anya kuwa ba yan biyu bane su?"
Husna ta dafe kanta da hannun ta, tace "doctor please a ina kaganta?"

Yace "wallahi kwanaki aka kawo mana wata yarinya kamar de ita wannan din asbitinmu Zata haihu Amma kuma batada jini, cikin mamaki yaci gaba da cewa to ni dakaina naje nasa Mata jinin, Ahmad abokina shine ma yabata jinin," 🤔

gaban husna yayi mummunar faduwa,😳🙆🏻 karde feenah hospital din doctor sukaje lokacin haihuwar baby, Amma koma menene Zata tambayeta taji, tahir yace
'' ya kikai shiru,"

husna aranta tace dole ne inrufawa auta sirrinta, tace cikin in-ina "gaskya ba... ba.. Ba'ita bace, kawai karatu tayi anan kuma taqi dawowa gida tayi zaman ta gidan kaka"

tahir cikin ko in kula yace
" ok shikkenan Amma gaskya kuwa dama nasan waccen yarinyar inkawo miki ita ki ganta"

Husna cikin faduwar Gaba ta kwanta akirjinsa ta rufe idonta alamun bacci duk Dan Yabar firar 😔


** *** ***

Waya nadauka nakira kb, cikin zaquwa ya dauka yace "my sweet feenah," nace "please kb inbaka wani Abu muhadu a ahadiqar siniya (wajan shan iska)"
Cikin hanzari yace "karki damu feenah karfe nawa?"

Nace "karfe biyar da rabi,"
yace "toki huta lafiya masoyiyata,"
nide kawai na kyaleshi nakashe wayar

Karfe hudu nagama komai, wandon jeans nasa nadora abaya akai, nayi rolling, inde ba wanda ya sanni ba, Babu wanda zai ce ni bahaushiya ce, Gaba daya na sauya

Biyar nafita, saida nayi tafiya mai nisa, har naje dede sharka-addal (kamfanin Mota na dal) sannan nasamu adedeta
Nahau muka tafi, naje na shiga na nemi waje nazauna, jakata na dauko nafitar da computer ta yar qarama mai kyau, na shiga ina duba lectures aciki, wani balarabe ne yazo yace " zai iya zama?"
Nace masa "maizai hana,"
Yama hanani karatun sai tambaya ta yake ina bashi amsa, yacemin "shima yana jiran habibiyarsa ne,"
nace " yayi kyau,"

Yace " kinyi kyau,"

nace masa "shukran,"

can saiga kb yazo, nace "masa "kadib" (wanda zan aura) yazo zan tafi," yana min daria yadagamin hannu, alamun bye bye

Waje muka samu muka zauna na fuskanceshi dakyau nace" kabir kasan me? "


** *** **


" Gaye ka koma kasar larabawa kayi zaman ka,"

ahmad yace" tahir bazaka ganeba wallahi nima Garin ya isheni,"

tahir yace" to ai kamar Yau ne zaka dawo, kayi hakuri na feenah "
Ahmad yace" kamar kasan kuwa lokacin ta ne yanzu kakirani, kasan fa kawai wannan lokacin na ware Mata kawai na tunanin tane, yanzu haka photonta nake zanawa, Dan haka Malam sai anjima, ka kirani latter anawa lokacin,"

tahir yace"wallahi Baku isaba daga kai har ita, Allah inka kashemin waya ko hmm"
Ahmad yace "to naji me yake tafe dakai yanzu?" Tahir yace "kawai jinka zanyi," ahmad yace "to na gode ya madam? Ana nan anata fama ko?"


Tahir yace "wallahi," ahmad yace "to gaskiya inta haihu sunana ne na farko, ban yarda da wani suna na daban ba," daria tahir yayi, yace "kasan me? Kuma wallahi twins Zata haifa, jiya jiyan nan mukaje nayi Mata scanning, Amma ban fada Mata ba, Dan batasan yan biyu, kajifa rigima kamar ita ba yar biyun bace"
, ahmad yace " twins tahir, wow dama ace nawa ne, gaskya to Ana haifarsu zan qwace su," tahir yace "saboda mudin zubama ido zamuyi ba aure ko?"
Ahmad yace " kaga mubar zancan Dan Allah"
Tahir yace "serious nifa harna ma Mata ma, wallahi sister husna ce yarinyar ta hadu ba qarya, Dan gaskya yarinyar nan ko kaffara bazan yi ba, tafi feenanka duk da banganta ba,"

Ahmad yace " please tahir, gara ka kusheni daka kushe rayuwa ta, 😏😠saboda haka sai anjima"
dif ya kashe wayarsa, tahir yazubawa waya ido, yace "wannan yarinyar ba kalau ta barka ba ahmad, dole in tayaka da addu'ah" 🤣


** *** **

Hawaye ya share yace "wannan dalilin ne yasa bakya sona?
Menene aibu na danna kasance Dan gidan Dan siyasa?"
Feenah tace "kawai
Hakanan bana so"
Hannu ya miqo zai rike hannu na, na daga masa hannu cikin fishi nace " kb ya'isa haka, nafadama dalili na Dan haka toka kyaleni,"
nayi Gaba yabini da kallo kawai, afili ya furta "zaandau mataki, bazan iya hakura dake ba feenah"



** *** **


After 4 months, shaquwa ta da mukhtar sai wanda yagani, naje Dakin Zahra muna kallan film a computer, mukhtar yakirani, nadaga mukasha fira, ta zubamin ido tana kallo na, saida nagama tace "feenah Amma soyaiya kike keda wannan gayen ko?"
Nace "a a me kika ga,"

"gani nayi bini bini bashida aiki sai kiranki,"

nace "Zahra bahaka bane, kawai mutunci muke," tace to "koma de menene banga abinda wannan ustaz din zai gayawa kabir ba" 🤣

, nace "Zahra nabaki kb din ke," 🤣

Zahra tace "banasan kb, shima baya sona, Dan haka ki rike abinki," nunfasawa nayi nace "a bar maganar to," nan mukaci Gaba da kallo


** *** **


Mama na wanke wanke taji sallama, ta dago da mamaki tace "husna, kune

Please Login or Register in order to submit comment