Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ammu yace" to Amma yallabai dakazo namaida ka gidan aiko? "
Ahmad ya girgiza kansa yace" karka damu tahir zai maidani"

" Toshiknn yallabai Allah yasawaqe,"
gyada kansa kawai yayi

Bayan ya fita tahir yace" Amma wannan mutumin yanada kirki, "

ahmad yace" eh wlh nima tun ganina dashi na farko naji y kwanta min, shiyasa bana shakkar bashi kowanne aiki daya shafi company" tahir yace "gaskya ne"



** *** **




Bayan sati uku, companyn su ahmad sun bawa ma'aikatansu wajan zama wadanda suke Zuwa daga nesa, cikinsu kuwa harda Ammu

Yakira waya gida yafada musu, anty maimuna murna kamar me Zata koma kusa da yan'uwan ta
Dakuma mijinta



** *** **



Baba adamu yayi duk wani zirga zirga Akan maganar gidan kaka, an sai Mata wani gida sabo gwanin sha'awa anan bompai saide fa sun kashe Mata kudi, shida Abba, ita kanta tana godia tana kuka, haka muka koma sabon gidan kaka nida ita, nikaina nafijin dadin zama agidan nafi sake wa, Dan haka dakaina nafita waje naje nasiyo sabon sim card, kuma alhmdlh naji dadin tafiyar danayi, tunda Babu inda nake Zuwa kullum muna gida amanne, nakira kowa na nuna masa sabon layina, banda mutum biyu, saudat da ahmad, a wannan lokacin cikina watansa shida, yayinda na mama yake wata bakwai



** *** **



"Ahmad! Ahmad!!
Ahmad!!!"
Tafada da karfi, cikin sauri yaduro daga kujerar daya kwanta akai,
" na.. Na... Na'am momy"

"Waladeey na me kake tunani hakane, tun dazu inata kiranka?"

"Momy kawai ina tunanin office ne,"
badan ta yarda ba, tace "kuma office kamar Yau kafara Zuwa Waladeey?" Shiru yayi

Saide ita aranta tasan karya yayi Mata, wani abun ma da sakacinta, bata fiya kula dashi ba, yakamata ta janyo shi jikinta harya sanar da ita damuwar sa,
Tace "munyi waya ne da hajia bilki tana min maganar kaya, tace tazubamin ido tayi zuru tayi zuru bataga kayaba, nace nikuma aina manta ma dana baka wannan kayan kuma nasan ka kai Mata,"

Ahmad yace " Momy wanne kaya kuma?"
Tace "lesuna dana baka kwanaki,"
ahmad yace "tab ni wallahi Momy nama manta dasu, suna can adakina, mabaruka taje tadauka takai Mata" , yana fadar haka yayi hanyar waje, tabishi da ido, tabbas akwai abinda yake damun yaron nan, shikuma yayi hakane Dan karma tace yaje yakai kayan, saboda bayasan ganin kayan kokadan, DAYA SANI ma tun farko bai karba bare wannan sabanin yashiga tsakaninsa da feenarsa



** *** **



"Gaskiya baby nide nagaji yakamata ki barni nazo na ganki hakanan, haba husna Allah nide ki barni kokuma inyi miki kuka," husna tace "haba doctor kuka kuma kamar ba namiji ba," yace "inde Akan kine zan iyayin komai ma husna, zaki haifamin twins idan mukai aure?"

Husna cikin mamaki tace "yan biyu de, a a bazan iyaba," tahir yasake gyara kwanciya Akan doguwar kujerar dake shinfide afalon nasu yace" aikuwa ke, danni inasan yan biyu, "tace" toka dena, danni kam banaso akwai wahala fa doctor, tafadi haka cike da shagwaba,"
nan danan mutumin ku ya rikice yace" to to naji baby ni karki min kuka shikkenan? "
Kafin husna tayi magana can cikin wayar taji Ana cewa" Dan ummi da yar tawa kake waya ne? "🤣

Dagowar da tahir zaiyi yaga ummi a tsaye akansa, haba qasa Bude tahir yashige, yaji kunya ta Kamashi, Allah yasa de bataji zancan duka ba
Husna taji shiru har Zata kashe saita qarajin ance bani ita mu gaisa
Tahir ya daskare da waya akunnan sa





Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱



Writing by Amnah el yaqoub



Dedicatedg to my family



30


"Kinyi shiru nafi,"

nace "kaka ai baya nan, yatafi misra,"

" au to shiyasa naji shi shiru, nasan da yasan inda nake aida tuni ya zo"

Nace "um" 😠

Natashi nayi daki



** *** **



Akwana atashi Babu wuya awajan Allah, har cikina yacika wata tara, duk kafafuna sun kumbura, nayi wani fari, kaka bata barina inyi aikin komai, ina kwance kokuma in tashi inta zagaya gidan



** *** **



Baba adamu shine yayi shige da ficensa ya karbo min takarduna, yahada dana wajena yatafi dasu gidansa bansan me zaiyi dasu ba



** *** **



"Maman nafeesa anya kuwa ba zamuje asbiti ba aduba lafiyarki?
Tunda kika samu cikin nan bakida lafiya Yau fari gobe tsumma, gashi naga watan naki ma ya haura, ga kuma bikin husna dayake ta matsowa saura wata daya da sati daya"

Mama tace "Babu komai Abban husna, aidama Ana samun hakan, yanzu Babu abinda nakeji,"
Abba yace "Toshiknn"



** *** **


Su ahmad tunda bikin nan ya matso ake ta zirga zirga kai kace bikinsa ne za'a yi,🤣 baya zama Yau shine can gobe shine can

Kullum suna shirya yanda bikin zai kasance,
Haka a bangaren su mama ma, basu zaune basu tsaye, Ammu yayi kokari sosai wajan ganin ya qawatawa yar tasa gidanta, sosai yayi Mata siyaiya ta gani ta fada Babu abinda su mama zasuce sai godiya



** *** **


"Kaka ni banajin dadin jikina, tun jiya wani irin ruwa nake zubarwa,"

kaka tace "a a nafi to haihuwar ce ta matso inaga zaqi ne, shiyasa banasan wannan ciye ciyan naki,"

tunda kaka ta ambaci haihuwa gabana yafadi, gaskya ina tsoro, qila ma Garin haihuwar na mutu, sai hawaye, kaka ta kalleni tace "to nafi ki adana kukan ki ba yanzu🤣🤣 ba akwai lokacin da zakiyi mai dalili,"

maya finta taja, tace "bari inje in karbo miki rubutu kyasha," bata jira amsa taba tayi waje, na zauna ni kadai na rafka uban tagumi, tashi nayi naje nayi alwala domin gabatar da sallar la'asar



** *** **



"Wash Allah Abban husna mu tafi asbiti, ina tunanin haihuwa zanyi,"

Abba Gaba daya yarikice, Yama rasa yaya zaiyi
Husna yakira ta futo da sauri, suka hada duk wani abin buqata sai wani asibitin kudi
Suna Zuwa kuwa likitoci suka karbeta sai labour room, husna sai kuka take, Abu tun la'asar sai gashi mama takai kusan isha'i bata haihu ba, duk nurse din data futo amsar daya ce bata haihu ba tukunna



** *** **


Ina zaune kan sallaya na idar da sallah kenan da carbi ahannu na, naji wayar kaka na kuka, kira na qwala Mata, nace " kaka Abba yana kiranki,"

ta futo daga daki ta amsa wayar, sai ji nayi kaka tana salati,
"ma'azu to anya kuwa Babu wata matsalar ka boye min?"

"Mama Babu komai wallahi kawai de dama Dan in fada miki ne kisan halin da ake ciki,"

kaka cikin sanyi jiki tace" to Allah yarabasu lafiya"

" amin" Abba yace

Ta zauna akujera nace " kaka lafiya kuwa,?"

Cikin jimami tafadamin abinda yake faruwa gabana naji yabada dam, araina nace nima fa inakan hanya, bayana naji ya riqe da sauri nasa hannu na awajan, nace " wash Allah, kaka bayana,"

ina yi ina yarfe hannu, kaka tace "subhanallah nafi karde kema haihuwar ce?"

"Wayyo kaka marata ciwo, zan mutu kaka,"
kaka tace " tsaya nafi bazaki mutu ba insha Allah,"
Wayarta ta dauko tafadawa baba adamu abinda yake faruwa, yace gashinan Zuwa

Kala taso ta biyo shi yace ta zauna tunda kaka tana nan, sai ihun kuka nake Mata ina yarfe hannu, yana Zuwa muka shiga bayan motar nida kaka, sai ihun kuka nake musu
Kaka tanaban hakuri, asibitin gwamnati muka fara Zuwa, saide sun shaida mana sun tafi yajin aiki, haka baba adamu yajuya kan motar sai wani asibitin kudi shi kansa ya rikice, yana tausayi na, ga halin danake ciki gani yarinya

Inata kaina banma kula da sunan asibitin ba nide nasan muna Zuwa wasu Mata suka karbeni aka dorani Akan gado, suka turani Zuwa labor room



** *** **


10:30 na dare, wata doctor tazo tace "alhaji saide fa kasa hannu anan, dole aiki za'a yi mata, Dan gaskya karfin ta yaqare, bazata iya haihuwa ba, sannan gashi ta manyanta,"

Abba cikin rawar jiki yasa hannu, anzo tura gadon za'a maida ta Dakin operation Allah cikin ikonsa ta sauka, ta samu danta namiji

Nurse dince ta futo, Abba da husna har rige rigen Zuwa gareta suke, tace musu " ta sauka,"

hamdala Abba yayi, yace" meta haifa,? "
Tace" tasamu danta namiji, Amma saide kayi hakuri yaron yarigamu gidan gaskya, sakamakon wahalar da babyn yasha, "

Abba yace" yanzu a wanne Hali take?"

Nurse din tace" alhmdlh munkai ta Dakin hutu, Amma kafin nan kaje wancan office din likita ya nasan ganinka, "

Abba ya wuce, yasamu doctor, anan doctor din yake masa bayani Akan abarta ta huta haka, yakamata ace a shekarun ta, tadaina haihuwa ma, yanzu ma Allah ne yatsare da saide ayi biyu, Amma sunyi iya kokarin su ganin kare lafiyarsu Gaba daya, shide yaron Allah yayi hukuncin sa, Abba yace " Babu komai likita, insha Allah za'a kiyaye"

Daga nan suka wuce Dakin da mama take ciki shida husna



** *** **



11:56 ahmad yace "to man ni zan wuce gida, kaga dare yayi, wannan de shine tsarin yanda dinner din zai kasance
, kaga har lokaci yaja ban tafi gida ba duk ka wani hanani sakat saboda wannan auren,"

Kafin tahir yayi magana, wata nurse ta shigo afirgice, tace "doctor ankawo wata Mata tana naquda, munyi iya yin mu Amma takasa haihuwa, batada jini tana buqatar jini, ko zakazo asan yanda za'a yi?"

Tahir yace "nawane group din jinin nata?"

Nurse din tace "wallahi bamu dashi doctor group O negative gareta"

Tahir yace " to ina yan'uwanta?"

gaskya suma mun gwada baiyi daidai ba

Tahir ya miqe da sauri, zai fita, ahmad ya tareshi yace " kaga muje kawai na bata nawa, ainima shine Dani,"
tahir yace "a a ahmad kaima fa bakajin dadi sosai," ahmad yace

"kaga da Allah muje," lab sukaje aka gwada jininsa, yayi daidai, haka kuma ba shida matsalar komai
Dan haka gado Aka bashi ya kwanta aka dibi jinin

Doctor tahir da kansa yasa mata jinin, kaka tana waje banda kuka Babu abinda take yi

Saida yasa Mata jinin sannan yaje, wajan ahmad,

"man mungode fa," ahmad yace "Babu komai, bari in wuce," tahir yace " no kabari na kaika, jini aka diba ajikinka kada kayi wani abin wahala yanzu,"

haka ahmad y hakura, suka fita shida tahir yasaukeshi agida, shikuma tahir din yadawo

12:30 daidai na haihu, nahaifi 'yata mace, muna Dakin hutu nida ita, tana kwance a gabana ansa Mata kaya farare masu shegen kyau, gata bul bul da ita yarinyar, masha Allah wannan yarinya badai kyau ba, na zuba Mata ido ina kallanta, Babu abinda ta dauko na uban ta, komai nawa tayi,
Daga farin har hancin hatta yan yatsun ma irin nawa ne, idonta kar Akan glof din wutar Dakin
Na shagala ina kallanta kaka ta shigo Dakin, maganar tace tadawo Dani da duniyar tunanin dana afka
"Um yaran zaman, su nafi ko kunya Babu anzubawa ya ido" 🤣

, kallanta nayi, ni banma San tana kainaba, tunawa nayi da yarinyar nanfa bata hanyar aure nasameta ba, sai wani baqin ciki ya to kare ni, nan take na juya Mata baya

Kaka tace '' zancen yaushe kuma nafi, 🤣"

Wata nurse ta shigo tabani magani nasha da tea mai kauri, baba adamu ma yazo yaga yar sosai yarinyar ta shiga ransa, yarinya kamar wata yar baby 🤣



** *** **



Karfe goma nasafe nayi wanka, naci abinci na shirya tsaf Dani, ga jaririyar dana haifa nan a gefe na, kaka sai magana takemin Akan na bata nono tasha naqi bata,
Wayar tace tadau qara, ta daga kawai ji nayi tace
"to Allah yaji kanshi ita kuma tunda de Allah Yabar mana ita to Allah yabata lafiya"
Can naji tayi shiru, bansan me take jiba, sai tace "eh hakan ma yayi ma'azu, insha Allah gobe zan taho, sai nabar nafin awajan kalatynsu to, to sai nazo,"
ta juyo tafadamin komai, nace "kash dama yaro maman ta haifa, to Allah yabata lafiya,"

kaka tace " amin,"

Amma batamin zancan tafiyar ta taba goben

Rarrashi na tashiga yi, Akan nabawa yarinya nono, dakyar de na dauketa nasa Mata aikuwa cikin sauri takama tanasha
I nayi ina rintse ido

Kofar Dakin dr Tahir ya turo yashigo,kaka tashiga toilet, saini kadai, sai muka birgeshi a yanda ya ganmu, ina shayar da yarinyar, sannu d jiki yayimin, ya tambayeni ko akwai abinda yake damuna nace a a, yarinyar yadauka yaji dama abashi ita yarinya saikace yar turawa, wasa yayi Mata gamida yimin sannu yafice daga Dakin

Mundawo gida da yamma yin duniya kaka tamin yar nan tana kuka in bata tasha, nayi mirsisi nahana, araina nace kyayi kya Gama kaka Amma bazasu zubar min nono ba itada ubanta
Haka kaka ta kyaleni taje tasiyo madara tabata tasha daqyar sai kuka take, duk da inajin kukan a raina haka na qyaleta

Washe gari da safe muna zaune afalo nida kaka ta tashi tahau shiri, zani naga ta dauka ta goya yarinyar, tacemin " to ni na tafi saina dawo"

Cikin sauri nace "kaka ina zaki kaita?" 🤣 🙈







Mrs Usman ce 🖊[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub


Dedicated to my family


31



Kaka tacemin "siyar ta zanyi,"

turo Dan qaramin bakina nayi Gaba, nace "to ki kawo ta in bata tasha," tace "riqe abinki nafi," tajuya ta fice

Bata zame ko ina ba sai gidan baba Adamu tayi masa bayanin komai da gashi har qanwar mama kala, sun amince da wannan batu sosai sunji dadi, daga nan kuma ta wuce sai tashar mota, cikin sa'ah suna Zuwa saura mutum daya lodin zaria yacika, saboda haka tana shiga suka dau hanya




** *** **



Suna zaune adakin da aka kwantar da mama, danma jikin nata da sauqi suna Dan taba fira kadan kadan, husna tana shan tea, yayinda mama take shan farfesun kayan ciki wanda husna takawo daga gida, shikuma Abba yana zaune akujera a gefe, yana waya da Ammu

Da kuma abinda ya yanke, Ammu yace "yaya hakanma yafi, mu kanmu shine rufin asirin mu, da kuma ita kanta nafeesan"

Abba yace "to shikkenan dama shine, ka gaida ita maimunan"
Ammu yace "to zasuji"

Wayar Abba ce tasake ringing ya daga tare da fita

Bayan wani lokaci sai gasu sun shigo tare shida kaka

Mama ta tashi zaune, husna tace "ga kaka ga kaka"
ta cacimeta
Kaka tace " kai bari karki karyani, duk sai kunga bayana daga ke har nafi"

Husna tasa daria
Kaka ta kunto babyn bayanta, Abba ya meqa hannu zai karbeta husna tace "a a Abba bari in fara daukanta"

Tayi zuruf ta karbeta, Abba yace "eh lalle husna yanzu de kin nunamin yarinya taku ce" 🤣

Su mama suka sa daria

"Masha Allah kaiii mama wallahi kin ganta kamar baturiya, Dan Allah nide kiban ita wallahi ina Santa" 🤣

Abba yace "husna banasan shirme kinji ko, bani ita,"
dakyar de husna ta bashi ita, yace "masha Allah, Allah yaraya," kaka tace " amin,"

"gatanan batada aiki sai kallon wutar lantarki, kamar agidansu Babu"

Mukasa daria, husna tace "kaka aike ta biyo"

Abba ya miqawa mama yarinyar, ta karbeta tace " to Allah yatayamu riko," kaka tace "amin"
Husna tace "mama yanaga tana kama dake ne"

Kaka tace "kamar uwar ta ta iyo, bakya ganin yatsanta sak irin na uwar ta, abinda yasa zakiga haka itama nafin kamar mahaifiyarku tayi shiyasa"

Abba yace "eh hakane kam

Kinyi Mata bayani ne mama?"
Kaka tace "bance Mata komai ba, ai ita nasan dadi ma zataji anrabata da qaya, wallahi ma'azu Yau yar nan ba tasha nono ba, madara kawai nake bata har mukazo nan, uwar taqi bata, nayi nayi da ita taqi, shiyasa nima na dauko ta ko bayani banyi mataba" 🤣

Abba yace "to bari ayi Mata huduba,"
ya karbeta, idan ta cikin na Abba, 🤣

Abba yace "husna yar nan taku batada kara, kallo haka ido cikin ido," 🤣
kallanta yayi yace "
To bazan aure kiba de,"

duk mukasa daria

Husna aranta tace lalle feenah tayi kokari, nikam idan yata ce wallahi bazan yarda ba, gara abar min abata 🤣

Ina kwance afalo ina kallo, naji wayata na ringing ina dubawa naga Abba bayan mun gaisa yace
"
Uwata dama akwai maganar danake so muyi dake, Akan maganar yarinyar nan na yanke shawara maman ku Zata rike ta, kema hakan zaifi miki rufin asiri,"
cikin sanyin jiki nace" to Abba na gode, "Abba yace" a a Babu godia atsakanin mu
Sai magana da biyu wanne suna kikaga ya dace asamata? "
Nafada masa, yace" Toshiknn ki kwantar da hankalin ki kinji, idan kin Gama hutawa kema sai ki dawo gida a fara shirin bikin yar'uwar taki, "nace

" to Abba a gaida su mama "

Bayan nakashe wayar bansan meyasa ba kawai naji kuka yazomin, shikkenan kuma nida baby, sunan danaji zuciyata tasa Mata kenan, ina kaunar yarinyar saide tabon mahaifinta bazai goge ba a idona

Abba yayi murmushi aransa yace wannan suna nafeesa ai saiku yan zamani, ya daga baby yayi Mata huduba, husna tace" Abba ya sunan ta? "

Abba yace " IZDIHAR," husna tace "wallahi yayi dadi," mama tace "aikam wannan suna kamar na larabawa," Abba yace "eh sunan larabawa ne"
Kaka aka Tabe baki a kace
"Lalle nafi Babu kara, yanzu Akan ta dubi irin wahalar danasha tun daga kano Zuwa zaria ai yaci ace Rabi'atu tasawa wannan yarinyar 🤣🤣"

Husna tace "tab lalle kaka, ai sunanki yanzu saide inna haihu na tausaya miki nasa sunan ki, Amma wannan fine girl din a a bazamu samata ba"
Kaka tace "kyaji dashi"



** *** **


Babu yanda na iya haka na tattara nakoma gidansu kala, saboda kaka taqi dawowa tace sai anyi suna, kala tayi kokari akaina haka ta dinga bani magunguna na matsi ina amfani dashi, da kuma wanda zai taimaka min wajan zubar nono na, cikin yan kwanaki kuwa, yadena zuba, na dawo normal kalau nake jina kamar ma ban fidda wata halitta daga jikina ba



** *** **



Sati na zagayowa akayi suna yarinya taci suna IZDIHAR kamar yanda nafadawa Abba, kaka saida taqara kwana biyu bayan suna sannan tadawo gida

Haka na baje inacin kayan suna kamar ba gobe musanman nama🤣😃

Takawo pictures din da akayi na suna, duk sunyi kyau Babu wanda zai ce ba mama ce ta haifetaba, haka kuma husna ta tutturomin wasu ta whtsp, kawai nace Allah yaraya



** *** **



Bayan sati daya na wuce zaria, lokacin bikin husna saura wata daya daidai

Tunda nakoma gida kwata kwata bana kula yarinyar, saide in tana wasa inta kallanta, mama Zata barta Akan kujera a kwance idan ta gaji da baccin tafara kuka inaji zanyi mirsisi na kyaleta

Saide husna ta goyeta, har tayi shiru
Hatta wankin fitsarinta bansaniba, bana tsinana Mata komai

Akwai lokacin datake kuka tana kan doguwar kujera Garin daga kafa datake yi irin na jarirai qiris yarage ta fado qasa , Allah yakawo mama tayi sauri ta rike ta, ina zaune Akan kujera, mama ta kalleni, tagade abin nawa harda rashin hankali aciki, 🤣anan tamin tatas daga karshe tacemin shashasha dabatasan ciwon kanta ba balle tasan na wani

Haushin yarinyar yakamani, duk itace sila dabatazo duniya ba da mama batamin wannan fadan ba

Kalatynmu takira husna tace taje kano, ta huta kafin bikin, ganin haka yasa nima nace zan bita, Babu wanda yahanani, mama tace min ala raka taki gona 🤔

Dasafe muka shirya zamu tafi, nasa doguwar Riga nayi rolling da Jan mayafi, har zamu tafi naga baby afalo, nasa hannu na dauketa, nabawa husna wayata nace tayi mana pictures
Aikuwa cikin sauri ta karba tayi ta mana, tana bani style, har saida nace ya isa sannan tabari, na ajiye ta, mu kayiwa mama sallama muka tafi



** *** **


Kala takanas takira mai gyaran jiki take gyara husna, nima kuwa nace ayimin, cikin sati uku muka wanke fes damu, kamar hardani za'a yi bikin
🤣


** *** **



Saura sati daya biki, lokacin muna gidan kaka baba Adamu yazo da wata magana, yayi mana bayani Akan yasama min Scholarship kamar yanda aysha tasamu tatafi Uganda, tonima ya nemamin Dan haka na shirya kayana, cikin satin nan zamu tafi, kaka tace " to Adamu wacce qasa zataje?"

Yace "Sudan,"

kaka tace "eh hakanma yafi idan Allah yakawo mijin sai ayi Mata auren,"

baba Adamu yace "eh wlh, Allah yakawo nagari"

dukanmu mukace "amin,"



cikin kwana biyu akayimin passport, kawai jiran visa nake, su mama ma kansu sunji dadin wannan batu



** *** **


Muna kwance a gado nida husna ni ina chting, ita kuma tana waya da tahir, tace masa "yaude ga auta ku gaisa,"
nakarbi wayar yace "autar mu, kin buya,"

nace "doctor ai kaine ka buya bamu taba haduwa ba,"

yace "tunda biki yazo kinsan abubuwan zasuyi yawa, Amma insha insha zamu hadu ai, keda mukeso ma ki taro gidanmu," 🤣

nace "a a mama bazata Baku ba,"
haka muka sha raha dashi daga qarshe nabata wayar



** *** **



Bikin husna saura kwana uku visar mu ta futo, gwamnati ta nememu, Dan haka muka shirya washe gari muka tafi, ina kuka mama ta nayi, muka rabu haushi na daya bazanga bikin sis ba, Abba ne me dauriya, kaka ma kuka haka kowa de jiki yayi sanyi suka rakani airport anan nahadu da abokan tafiyar mu, kafin lokacin tashinmu yayi, inaji ina gani su mama suka tafi, na sunkuyar da kaina Akan cinyata ina kuka,

Tunda tazo wajan hankalinsa yake kanta Gaba daya tatafi da imaninsa, yarinyar tahadu ba qarya 🤣

Karfe 9:30 jirginmu yatashi sai Sudan





Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub


Dedicated to my family


32


Umarni aka bayar musa belt, nima nasa nawa na rufe idona, ina tunanin rayuwa ta


** *** **


Suna zaune afalo, daddy yana karanta jarida, ahmad da waya ahannunsa, Amma Gaba daya hankalin sa baya kan wayar, daddy yace" my son ina fatan de komai yana tafiya yanda ya dace Babu kowacce matsala ko? "

Kamar da gunki yake magana
Daddy yace" my son "

Amma shiru, cikin tsawa yace "ahmad!!"

Azabure yajuyo har wayarsa tana faduwa, "na.. Na'a... Na'am daddy"

Daddy ya kalleshi da kyau yace "me yake damunka ne ka zauna kana tunani kai kadai?"

Ahmad ya shafa sumar kansa yace "Babu komai daddy"
Daddy yace "tashi kaje ka kwanta"

"To daddy gud night"

Yana fita daddy yakwala wa momy kira
"Hajiya! Hajiya!!"
Sai gata tazo, ta nemi waje ta zauna, "me yake damun yaron nan ne?"

Momy tace "alhaji halin ahmad fa ba'a iya masa, nan nasamu waje nazauna nayi masa nasiha, Amma kamar qara zigashi nake"
Daddy yace "cewa nayi me yake damunsa? Yazaku barmin yaro ya lalace haka, duk yafita a haiyacinsa, yaro me kuzari duk ya susuce,😃"

momy tace "alhaji kayi hakuri insha Allah zamu kiyaye
Amma ba komai ne yake damunsa ba, kaji kaji," nan momy tabashi labarin komai, daddy yace "kai halin ahmad ma saishi, to ai dasai yasamu wata kafin Allah ya baiyana masa wadda yake so din,"
momy tace "to nide namasa fada," daddy yace" shikkenan tashi kije zan sa meshi muyi magana," momy Takoma Dakin ta


** *** **


Ina jikin window ina kallan gajimare munyi nisa a tafiya, narasa yaya zanyi in manta dashi, koda yaushe yana cikin raina, ko menene dalilin sa na yaudarata?
Kome namasa dazai sakamin da hakan,?

"Ahmad kenan"

nafada abaiyane, watace a kusa Dani ta juyo ta kalleni, tace "sannu fa"
Nace

Please Login or Register in order to submit comment