Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ban da Jehan da a iya islamiyya kawai take ɗauka bai taɓa tunanin girman ilimin Rimsha ya kai haka ba, ba wanda bai yi mamaki da jinjinawa Rimsha ba ta girgiza gaba ɗaya hall ɗin ta karawa mutane da dama imani a ran su dayawa daga cikin wayan da suka halakci wajen sun kudurci niyar gyara ɗabiun su marasa kyau ta dalilin maganganun Rimsha, sosai suka shiga tashin hankali duk wanda ya manta da lahira yau sai da Rimsha ta tuna masa wani ma ji yayi kamar yaje ya sadakar da dukiyar sa dukka ya koma ga Allah yayi ta ibada,

da gudu Jehan ta miƙe ta hauro saman wajen ta rungumi Rimsha tana kuka tana faɗin "Kinyi gaskiya yar uwata duk abun da kika faɗa gaskiya ne amma jama'a da dama sun shagala da duniya sun manta da mutuwa da kwantatciyar kabari sun manta duhun kabari da siraɗi da hisabi idan ka dace ka shiga aljanna idan baka dace ba ka wuce wutar jahannama bayan ka gama ansan azabar kabari dana siraɗi ga tsayuwa kafin hisabi tsayuwar shekara ɗai ɗai har shekara dubu saba'in ga kuma rana a dai dai sai tin kan ku babu dare babu inuwa sai wan da yayi aikin Allah ne kaɗai zai shiga inuwar al'arshin Ubangiji Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah mun tuba mun tuba ya Allah" sosai jama'a suka ciro wayoyin su suka rinƙa yi musu video ciki har da director.

Da kyar daddy ya iya rarrashin Rimsha sai da tayi shiru san nan ya riƙo hannun ta suka miƙe ya dubi director yace "Mu zamu wuce gida ba zamu iya jira a gama taro ba dan jikin siha ya fara zafi saboda kukan da tayi" ya kai karshen maganar tare da kallon gwaggo dake zaune saman nata kujerar tana goge kwallan dake idon ta yace "Aunty A'isha muje ko?" Da kyar gwaggo ta iya miƙewa dan gaba ɗaya Rimsha ta kashe mata jiki, gaba ɗaya manya manyan baki da sarakunan dake wajen suka miƙe dan raka su daddy zuwa wajen mota, sunyi sunyi a kan daddy ya bari suyi hoto da Rimsha amma yaki haka suka hakura ba dan sun so ba suka bar su Rimsha suka tafi ba tare da sun yi hoton ba, da haka taron ya watse dan dukkan su sun kasa gudanar da komai jikin su ya mutu da har da kayan kiɗa suka kawo amma jin zancen Rimsha yasa suka manta da wani kayan kiɗa da suka kawo, kowa ya wuce gida taro ya watse

💞💞💞💞💞💞💞💞

KANO

Zaune jelly take saman mirror chair daddy na tsaye a kan ta yana ɗaure mata gashin kan ta da roba irin na kitson yara kasan cewar gashin nata yayi tsantsi sosai baya kitsowa sai dai a ɗadɗaure mata shi da roba, sai murmushi take fararen hakwaranta masu kyau suna jere kanana da su sai kyalli suke, shi ma daddy sai murmushi yake yace "My baby kinyi kyau over" kara murmushi tayi sosai a wan nan karon har fararen hakoran ta suka kara bayyana sosai "Daddy amma dai yaya Imran zai zo school na mu ko?" Tayi maganar cikin shagwaɓa "Eh my baby yace min zai zo In Sha Allah" tana kokarin sake yin magana daddy yace "Sauko na gama kuma surutun nan ya isa dan 07:00 am tayi yanzu taso na sanya miki uniform dan karmuyi late" make masa kafaɗa tayi cikin shagwaɓa tace "Daddy kai fa ka ɗaurani saman chair ɗin yanzu kuma kace na sauko da kai na ni ban iya ba" girgiza kai kawai yayi ya sanya hannu ya ɗagota cak suka nufi wajen gado dan bai son biye mata idan ya biye mata ba zasu wuce school da wuri ba,
saman gado ya ɗaura ta san nan ya wuce ya ɗauko mata uniform nata riga fari da wando blue sai ɗan hijabi fari ya dawo ya sanya mata sharp sharp san nan ya ɗauko perfume ya feshe ta da shi nan take ta fara zuba kamshi wuce wa yayi ya ɗauki suit nasa da zai sanya ya shige toilet,

tana zaune har ya fito shirye cikin bakin suit da ya ɗauka ya dube ta yace "Let's go my baby" shiru ta masa kamar bata ji me yace ba, sake mai mai ta maganar yayi dai dai lokacin da yake ɗauko jakar computer sa nan ma sake masa shiru tayi kamar bata san da mutun a ɗakin ba, da sauri ya juyo dan yaga wai ko barci tayi ne ganin idon ta kar a kan sa ta turo baki kamar biro ne yasa ya dafe kan sa da hannun sa yana faɗin "Yanzu kuma menene? haba my baby zamu makarafa" kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin "Ni daddy yanzu ka dai na sona baka ɗauka na sai kace na tafi da kafata" "Haba my baby yanzu fa 11 years kike da shi gaskiya kin min katuwa ba zan iya ɗaukan ki ba" sauka kasa tayi daga saman gadon ta kwanta a kasa ta fara birgima tana masa kuka girgiza kai yayi ya ratiyo jakar computer sa ya kariso wajen tare da sanya hannu ya ɗauke ta cak kamar yar baby suka nufi waje, ganin ya ɗauke ta yasa tayi shiru kamar an kashe gen.

Ko da suka fito palo su Zuwaira sun kammala shirya musu breakfast ga kuma basket na school ɗin Jelly sun shirya mata abincin ta a ciki roban cool Yoghurt ne mai ɗan girma da snacks a cikin wata kyakkyawar transparent roba sai pepper chicken a cikin foodflask, daddy bai tsaya yin breakfast ba dan time ya tafi basket na lunch nata kawai ya ɗauka mata suka nufi waje lokacin 7:45 am yayi.

Suna fita harabar gidan wata dankareriyar mota kirar Mercedes-Benz ta danno hanci cikin gidan ihu jelly ta fasa mai rikita ƙwaƙwalwa tana faɗin "Daddy ka sauƙe Ni" ba musu ya sauƙe ta da gudu ta nufi motar zata runguma ba ruwan ta da tafi motar yake, saura kaɗan yabi ta kan ta dan irin shigar da tayiwa motar, a sukwane mamallakin motar ya taka birki, ba karamin tsorata daddy yayi ba ganin saura kaɗan motar ya take ta, ita ko, ko a jikin ta bata ma san me tayi ba da gudu ta karisa wajen marfin motar tana faɗin "Yaya Imran nayi kewar ka" gently a ka buɗe kofar motar a hankali ya zuro kyawawan kafafun sa dake sanye cikin cover shoe baƙi waje kafin ya fito gaba ɗaya, cikakken namiji ne chocolate color yana da dogon hanci da dara daran idon ga kyakkyawan saje kwance a face na shi kaman sa ɗaya da daddyn Jelly sai dai shi chocolate color ne sosai, yana sanye cikin dakakkiyar shadda fara tas da hula baki sai cover baki a kafar sa kyakkyawa ne a jin farko, da sauri Jelly ta faɗa jikin sa tare da sakin kukan shagwaɓa, ɗagata sama yayi yana faɗin "Rabin rai na nima ai nayi kewar ki yanzu dai a dai na min kukan haka ya isa kin san ban son kukan ki ko?" kwantar da kan ta tayi saman kafaɗar sa tana yar dariya kamar ba ita ke kuka yanzu ba, wucewa Imran yayi ɗauke da ita a jikin sa ya nufi daddy dake tsaye sai murmushi yake bakin sa yaki rufuwa yana bala'i kaunar Imran sosai,

Risinawa kasa Imran yayi ya gaida daddy, da fara'a daddy ya amsa yana murna "Daddy muje ko lokacin ya tafi" cewar Imran yayi maganar tare da ansan basket ɗin Jelly dake hannun daddy,
a tare suka ranƙaya zuwa wajen motar Imran,
daddy ya shiga gidan gaba tare da ansan Jelly shi kuma Imran ya koma mazaunin driver ya zauna tare da yiwa motar key yana satar kallon face ɗin Jelly yaja motar suka bar gidan suka nufi School ɗin su Jelly

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu

💞Star Lady💞

*💞TRIPLET'💞

*💞The beginning💞*



STAR 🌟 LADY..✍️



Episode 8

*KADUNA*

Zaune Abbi yake saman sofa a cikin palon sa ya buga uban tagumi yayi shiru, kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin matsanancinyar damuwa, duk da sanyin Ac dake cikin palon hakan bai hana shi zufa ba, jikin sa sanye da jallabiya baki gaba ɗaya a hargitse yake,

da sallama Irfan ya shigo cikin palon, Abbi yayi nisa cikin tunani bai ji sallamar da Irfan ɗin yayi ba,

````Irfan````

Cikakken namiji ne yana da tsawo dai dai san nan yana da ɗan kiba kaɗan yana da faffaɗar kirjin ga hancin sa dogo har baka idon sa dai dai ne basu da girma sosai kuma ba kanana bane yana da ɗan karamin baki laɓɓan sa na sama brown color na kasa pink color kyakkyawa ne sosai fari tas da shi kamannin sa ɗaya da Umaisha sai dai shi fari ne a shekaru ba zai wuci 26 to 27 years ba sanye yake cikin shadda brown color ɗinkin half jomfa ba karamin kyau kayan suka masa ba kasan cewar fatar sa na da haske.

......Jiki ba kwari ya kariso cikin palon, ya shiga damuwa sosai ganin halin da Abbi ke ciki, kusa da shi Irfan yazo ya zauna ya ɗan taɓa shi yana faɗin "Abbi lafiya?" Yar firgigit Abbi yayi ya ɗago idon sa da suka sauya launi zuwa ja, dogon numfashi yaja tare da sauke wa a hankali,

"Abbi me yasa kake yawan sa kan ka cikin damuwa ne? Karfa wani ciwo ya kama mana kai" jinjina kai Abbi yayi murya a dashe yace "Irfan dole na shiga damuwa Alhaji Ma'azu ya cuce ni yaci amanar yarda" riƙo hannun sa Irfan yayi cike da tausayawa yace "Abbi ba komai Allah zai saka maka yanzu dai ina son ka dai na sawa ranka damuwa muyi hakuri muga me Allah zai yi" girgiza kai Abbi yayi kafin yace "A'a Irfan dole mu sai da Company nan, mu fara business da kuɗin dan kar muzo mu rasa na cin abinci" shiru Irfan yayi yana tunanin mugun ta da Aminin Abbin ya masa, duk wani abu mai amfani a company su na sarrafa shinkafa sai da ya kwashe cikin dabara, saboda yadda da shi da Abbi yayi yasa bai farga da wuri ba, har injuna da sauran kayan amfani bai bari ba Abbi yayi reported na shi a police station amma ba wani abun da ya samu sai ma kuɗin da ya rinƙa kashe wa kuma ba'a masa adalci ba saboda Alhaji mu'azu ya saye jami'an tsaron, Alhaji mu'azu ba abun da ya barwa Abbi a company sai kangon gini kawai duk wani abun da ya sace kuma sai da yaje ya musu takardun karya wadda zasu tabbatar da nashi ne,

"Irfan tashi muje muyi Sallah azahar lokaci yayi idan muka dawo sai kaje ka ɗauko su Aafia a school" a lokacin Aafia na ss2 ta rubuta waec and neco yau suke graduation Abbi bai samu daman zuwa ba saboda damuwa da ta masa yawa shi kuma Irfan baya nan ya manta ya tafi wajen friend na shi a cikin Zaria City, Umaisha kuma tana ss1,
a lokacin Aafia na da 17 years Umaisha na da 15 years

"Amma Abbi me yasa ba zaka tambayi bappa Yaya ya baka kuɗi ba ko da bashi ne sai ka tayar da company namu" cewar Irfan yayi maganar yana kallon cikin idon Abbi "A'a Irfan ko na tambaye sa Hajiya Umaiya ba zata taɓa bari ya bani ba kasan halin ta shi kuma Abdul Malik yanzu haka yana cikin matsala ba zan iya tambanyar sa ba, na san idan na tambaye sa ko bai da shi zai nemomin bashi amma bana son sashi cikin damuwa in kara masa damuwa kan wadda yake ciki" waro ido waje Irfan yayi yana faɗin "Abbi Bappa maik ɗin ne yake cikin damuwa? To damuwar me kuma?" Gyara zama Abbi yayi san nan ya fara magana "Akoi wani abokin Takarar sa a fagen aiki su da ya sako sa a gaba a kan company sa *filman Nigeria limited* wai sai dai maik ya sai da masa da company kuma mutun ne mai haɗari sai barazana yake wa maik, kawai dan company maik yafi nasa sanuwa a duniya maik ya fisa farin jini shi yasa yake son dole dole sai ya tankwarar da maik yanzu haka a koi wani aiki da company maik dana abokin takarar nasa dana wasu su kayi applying, aikin gina wani katafaren asibiti ne a Villa to shi Alhaji Auwal ɗin yasan duk in da aiki ya fito kuma company maik ta nuna sha'awar sa a kan aiki to shi a ke bawa shine ya ɗaga masa hankali dan aikin babban aiki ne sosai duk company da tayi Sa'a ta samu aikin to zata samu makudan kuɗaɗe shiyasa ya sako maik a gaba da baraza a kan dole maik ya janye neman wan can aikin kuma ya sayar masa da company sa" kara waro ido waje Irfan yayi cike da damuwa yace "Abbi to me yasa daddyn jelly ɗin ba zai yi report na shi ba" girgiza kai Abbi yayi yana faɗin "No Irfan idan baka iya kama ɓarawo ba sai ɓarawo ya kama ka ai wan nan mutumi baka isa ka kai karan sa ba Alhaji Auwal ya wuce tunanin ka yana da wani ɗan iskan yaro mai suna Muneer wan nan yaron har gida yake zuwa yayi wa maik abun da yake so ba yadda maik zai yi da su, addu'a ita ce kaɗai zata raba su dan haka ka taya bappan ka da addu'a Allah ya raba shi da su, amma kuma Maik ɗin ya ce min ya turawa Nawazudden later a kan matsalar kuma na san in dai Nawazudden ya samu later nan to ba makawa zai taimaka wa Maik sosai dan shi ɗin mai yi ne yana da zuciya mai kyau kuma kaga yanzu sune gomnatin gaba ɗaya, In sha Allah zaɓe mai zuwa sai ya zama shugaban kasa dan yace tabbas zai tsaya takara ku tayasa da addu'a" dogon numfashi Irfan yaja tare da saukewa a hankali yace "Abbi duniyar yanzu mutane ba abun yarda bane yanzu dubi yadda kayiwa Alhaji mu'azu gata ka jawosa inuwa ya turaka rana ashe ba ma kai ka ɗai ba har da bappa maik ga kuma maman su Imran ta hana bappa Yaya taimakon ku ta raba zumunci ta rabamu da yan uwan mu gashi Bappa yaya yana da kuɗi na fitan hankali amma ta hana kowa yazo kusa da shi yanzu fa bappa yaya ma ina ga ya manta da ku gaba ɗaya a rayuwar sa nifa idan ba Imran ba ba wan da na sani a gidan shima Imran ɗin dan yana da son zumunci yana zuwa nan kuma muna waya da shi shiyasa amma ba dan hakan da shima ba zan san shi ba" ajiyar zuciya Abbi ya sauƙe san nan yace "Ba kai ka ɗai ba nima nan iya Imran kawai na sani ban san sauran yaran yaya ba amma naji daddy'n jalila yace ƴaƴan yaya uku ne bayan Imran a koi Akil da Akila amma ni ban san su ba ban taɓa ganin su ba ko shi maik ɗin ai sau ɗaya na taɓa kallon jalilan sa lokacin tana yar shekara biyu yanzu ko a hanya muka haɗu ba gane ta zan yi ba ni ma kuma bana jin maik ya san su Aafia kai kaɗai ya sani dan kai kaɗai ne mai zuwa wajen sa" cikin sauri Irfan yace "Ae, kuwa dole wan nan hutun na kai su Aafia wajen sa dan ya san su suma su san shi dan zumunci nima daga nan naga jelly dan rabon da na ganta tun tana da shekara 6 duk lokacin da zanje gidan tana School kuma ban taɓa kwana ba amma wan nan karon zan kira Imran ya zo mu haɗu a can gaba ɗaya muyiwa bappa koda 1 week ne muga juna su Aafia su ga jelly ita ma ta gansu nima kuma na ga su Akila ɗin dan zance Imran yasan yadda zai yi yazo da su" kakalo murmushi Abbi yayi kafin yace "Wallahi har kasa naji daɗi ba dan ina cikin wan nan matsalar ba ai da tare zamu tafi dan nima rabona da ganin maik wajen shekara 6 kenan yanzu sai dai muyi waya kawai" murmushi shi ma Irfan yayi yana faɗin "Abbi karka damu komai zai warware yanzu dai muje muyi Sallah gashi nan har an tada Kabbara"
A tare suka miƙe suka nufi waje suna yar hira suka nufi masallaci.

💞💞💞💞💞💞💞💞

*ABUJA*

Da sallama ɗauke a bakin daddy ya shigo palon da sauri Mum dake zaune tana kallon abun da ke faruwa a school ɗin su Rimsha a Tv ta tashi ta nufo su tare da buɗe hannu ta rungumi Rimsha tana murmushi, rungumarta Rimsha tayi tana ɗan murmushi ita ma "My Siha Allah ya miki albarka, Allah ya inganta min rayuwar ki Allah ya dafa muku gaba ɗaya daga ke har babayn daddy" tayi maganar tare da jawo Jehan ta haɗe su ta rungume, sai murmushi daddy da gwaggo suke,
mum ta ɗan jima rungume da su tana zuba musu Addua'o'i daddy da gwaggo na amsawa kafin ta sake su ta riƙo hannun su suka haura saman bene dan taje tayi wa Rimsha wanka ita kuma Jehan tayiwa kan ta wanka, duk wan nan dukiya da Allah ya bawa daddy bai yarda da yar aiki ta kula masa da yara ba mum ɗin su ke musu komai dan gani yake ba wadda zata musu abun da ya dace kamar mum, ko itama mum ɗin wani lokaci idan tana musu wani abun zuwa yake ansa da kan sa ya musu sai yace bata musu yadda ya dace sai dai ta girgiza kai kawai tana masa dariya.

Wucewa shi ma daddy yayi ya haye sama dan yaje yayi wanka ya shirya yazo ya ci abinci ita ma gwaggo ta wuce nata bedroom ɗin dan yin wanka ta huta.

After some hours

Mum na zaune saman sofa ita da daddy da gwaggo suna hira a palon, sai murmushi suke suna anna suwa da alama hiran na musu daɗi,

da gudu Jehan da Rimsha suka sauƙo suna rige rige zuba musu ido daddy yayi yana kallon ikon Allah ita kuwa mum da ta saba sai ta ɗaga ido ta kalli agogon dake manne a bangon palon ta saman Tv 2:30 pm dai dai girgiza kai kawai mum tayi tana faɗin "Bismillah" da sauri Rimsha ta ɗauke remote ɗin Tv ta canza tasha zuwa news, nan take murmushi ya bayyana a kan face nata ta koma saman sofa ta zauna tana faɗin "Allah na gode maka da kasa TGA ya yarda ya amsa wan nan gayyatar yauma dani za'a fara hira da shi kuma har a gama" tayi maganar cikin harshen larabci, bata gama rufe baki ba Jehan ta anshe remote ɗin ta canza tasha tana faɗin "Daga yau kin dai na kallon wan nan kafurin Krista a gidan nan" a kule Rimsha ta miƙe kamar zata yi kuka tace "Dan Allah Jehan ki bani remote nan wallahi yanzu fa TGA zai shigo kin hanani kallo a bedroom na hakura na dawo nan to dan Allah a nan karki hana ni ki bar ni na kalli jarumi na" kallon sama da kasa Jehan tayi mata kafin tace "eyee ina cewa ɗazun ba cimawa kika gama mana jawabi a school like good girl shine yanzu zaki zo ki fake da kallon wan nan kafurin da ma bai san da zaman ki a duniya ba, gaskiya ne wan nan magana do what I say don't do what what I do" su daddy dai sun zuba musu ido suna kallon ikon Allah "No Jehan wan nan abun da nake kallo ba hara mun bane a musulci kuma dan na faɗi magana a school hakan ba yana nufin ni bazan yi nishaɗi a rayuwa ta ba ko kuma wasu ba zasu yi nishaɗi a rayuwar su ba abun da nake nufi kar ku shagala da duniya ku manta da lahira kuma ai ni ban shagala da duniya ba kema sheda ce a kan hakan kiyiwa Allah ki bani remote ɗin nan" ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka duk wan nan magana da suke cikin harshen larabci suke yin sa, a kule Jehan tace "Ba zaki sake kallon wan nan mummunar mutumin mai kama da zunubin a gidan nan ba" a fusace Rimsha ta wanke mata fuska da mari tare da sanya hannun ta ta fisge remote ɗin ta canza tasha ta mai da News, ta koma ta zauna saman sofa ta ci-gaba da kallon ta, cikin zafin nama da ɓacin rai Jehan tayi kanta da niyar dukan ta da sauri daddy ya miƙe ya ɗauki Jehan ɗin cak suka haura sama ihu ta fara yi masa tana wuntsilo kafofin ta,

Kallon Rinsha mum tayi cikin harshen shuwa arab da kakkausan murya ta fara magana "Daga yau idan kika sake marin sister ki Rimsha sai ranki ya ɓaci koma me ta miƙi ba muna zaune a wajen ba ai kin san ba zamu bari ta hana ki kallon ki ba zamu ansan miki, karki sake yin wan nan kuskure ko da sunan wasa kada ma ki sake tana magana kina bata amsa gaba take da ke, ki rinƙa mata biyayya kuma ki gama kallon idan daddyn ku ya rarrashe ta kije ki bata hakuri kina jina?" Cikin ladabi da biyayya tayi kasa da murya tace "Naji mum kiyi hakuri ba zan sake ba" har cikin ranta mum taji daɗi Rimsha yarinya mai biyayya ga hakuri kamar damo bata son yawan hayaniya,

A ɓangaren daddy kuwa kai tsaye bedroom na shi ya wuce da Jehan dake ta wuwwuntsilo masa kafofin ta sama tana masa ihu, saman katafaren gadon sa ya sauƙe ta san nan ya zauna gefen ta tare da ɗaure fuska ya fara magana cikin harshen turanci "Why Jehan you always look for troubles, amid you are a senior, you know Rimsha is patient, but you vividly push her to fight you at most?" Shiru tayi tana turo baki "As from Today kar na sake ganin kina neman Rimsha da faɗa kina ji na ko?" Gyaɗa masa kai tayi alamar eh ba tare da tayi magana ba.

Miƙewa Rimsha tayi zata bar palon mum tace "A'a Rimsha kin fasa kallon ne kuma?" Turo baki Rimsha tayi kamar za tayi kuka tace "Mum hankali na ya kasa kwanciya ne zanje na bawa Jehan hakuri sai na dawo na ci-gaba da kallon" "No my Rimsha zo kiyi zaman ki karki damu ki bari sai kun shiga ɗaki sai ki bata hakuri" ba musu Rimsha ta dawo ta zauna ta kafe Tv da dara daran sleeping eyes nata masu ɗaukan hankali,

sosai ta kafe Baturen dake magana a Tv da idon ta yana sanye da face mask a face na shi, farine tas yana sanye da kananan kaya sai jacket da ya ɗaura a saman kayan nasa kasan cewar sanyi dake wajen nasu, duk da rabin face nashi a rufe da face mask hakan ba zai hana ka gane kyakkyawa ne ajin farko ba yana da murɗaɗen jiki ga faffaɗar kirjin kamar wani zaki kirjin nasa a cike ɗamtsen hannun san nan kamar zasu fashe saboda training da yake, "Rimsha ni ko in da tambaya a kan wan nan boss ɗin naki" cewar gwaggo ɗago sleeping eyes nata tayi ta kalli gwaggo, calmly tace "To gwaggo Allah yasa na sani" "Jarumin nan naki mutun ɗaya ne ko biyu?" Cikin sauri Rimsha tace "Shi kaɗai ne wajen mum da daddyn sa dukka" shiru gwaggo ta ɗan yi kafin tace "Amma wani lokaci zaki gan shi da ido ligh ash wani lokaci kuma ligh blue shi yasa nace ko su biyu ne" girgiza kai Rimsha tayi tana faɗin "Eh gwaggo nima ina ganin hakan sai dai ina tunanin sanya kalar idon nasa yake dan shi kaɗai ne

Please Login or Register in order to submit comment