Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yazo mana da wata zance wai an bashi mata wata yar mai kuɗi ce ta ganshi tace shi take so dan haka Aure zai kara a lokacin nayi kokarin nuna masa illar hakan yaki yarda dana matsa yace to na tafi gidan mu jin hakan yasa nayi shiru na kyale sa kasan cewar bani da uwa mahaifiyata ta rasu kuma ba zan iya tafiya na bar su sadiq ba, yarinyar da yace zai aura yarinya ce karama bata wuce Sa'a Sadiq ba dan bata wuce 23 years ba Sadiq ma ya ɗan girme ta na nuna masa illar abun amma ya rufe idon sa yaki shi yaga kuɗi daman gidan da muke cikin nan gidan hayane alokacin sanadiyar Auren yarinyar baban ta ya sai masa gidan ya dawo mallakin sa yarinyar nan tun da tazo shikenan baban Sadiq ya tattara mu daga ni har maman Hanan ya watsar daman ni ya dade da watsar da ni ya tattara ya koma ya tare a gindin yarinyar sai abun da tace ya keyi ko waje idan tace karya fita tofa baya taka ko ina daman ba wani sana'a yake ba itace yake sayarwa a ɗan bayan layin mu baban yarinyar ya saya masa kaya dayawa da abubuwan amfani san nan ya gyara ma yarinyar ɗakin ta an mata ciki da palo har da fenti gashi yarinyar tazo da abubun ta dayawa har da su kayan kallo da su gas da kayan abinci na zamani kullun zata girka kaji da shinkafa bata taɓa tsanmana ba sai dai taci ta ragewa baban Sadiq ya fito waje idan ba wuta yana cin ragowar ta yana washe baki ni ko ajiki na dan Sadiq yana iya kokarin sa wani lokaci idan ya samu kuɗi a garejin su sosai har kaza nima yake sawomin gasashe muci da shi da Yasuf mu ɗebawa maman Hanan da Hanan ɗin ta, maman Hanan ma ta kasa jurewa shi ne suka fara sana'ar awara a kofar gida ɗan su ciyar da kan su baban Sadiq ya sallama mu ba ruwan sa da mu baya bamu ci baya bamu sha bare sutura ko idan bamu da lafiya ya nema mana magani kwata kwata ba ruwan sa da mu damu da babu duk ɗaya ne awajen sa daga ni har maman Hanan ya fita sabgar mu, ko mutuwa zamu yi mu mutu shi ba ruwan sa kullun yana wajen amaryan sa gashi yarinyar bata da kunya ga masifar bala'i idan rashin Kunyar ta ya motsa sai Sadiq na min wanki kaya na sai ta kwaso nata ta zuba masa tace ya wanke idan yaki sai ta sa baban shi, shi kuma gudun ta sanya babansa yasa sai ya ansa wankin nata ya wanke mata Yusuf ne dai baya ɗaukan iskancin ta shi yana da zafin rai sosai ga saurin fushi sau biyu baban sa na korin sa daga gidan saboda ita sai naje na bawa amarya hakuri san nan tasa babansa ya hakura ya barsa ya dawo gidan sau biyu wallahi yana korin sa ni kuma ba zan iya ganin sa yana yawon neman wajen kwana gidajen abokai ba gwara dai duk wuya ya zauna a gaba na ina kallon sa yadda rayuwar yanzun nan ya lalace yaro na gaban ka ma ya kacika bare baya ganin idon ka shi yasa ma bana damuwa nake zuwa na zube a kasa na roki amarya ta sa babansa ya hakura ya bar shi ya dawo, Sadiq da kuke ganin nan sai dai in ce Allah ya bawa yaron nan aljanna wan nan murmushi dake kan fuskar sa kullun dan dole yake yin ta idan kuka tona ciwon dake zuciyar yaron nan sai kunyi masa kuka" ta kai karshen maganar tare da goge hawayen dake idon ta "Tab ɗijam lallai maman Sadiq kina cikin jarabawa to Allah ya baki ikon ci, wannan wani irin zalunci ne duniya ina zaki da mu ya za'ayi ba zamu rinƙa fuskantar fushin Ubangiji ba irin wan nan zalunci har ina, ace mutun sai son abun duniya ka haifi yara ba ruwanka da su ba ruwan ka da cin su shan su suturan su bare tarbiyyar su ka zubar da su har ma da matan ka wan nan wani irin abu ne wan nan zamani Allah ka kawo mana sauki" cewar Mum "Amin" maman Sadiq ta amsa da shi ita dai gwaggo shiru tayi abun duniya sun taru sun mata yawa akai shiru wajen yayi ba wanda ya sake magana ita kuma Jehan tana ɗaki tana latsa waya.

KANO

da sallama Dr ya dawo palon, jelly na zaune a wajen da ya barta rungume da dolly har barci ya fara ɗaukan ta, jin sallamar tasa ne yasa tayi saurin waro idon ta waje tana faɗin "Welcome Uncle" murmushi ya sakar mata kafin yace "Yauwa jellyn dady" ya kai karshen maganar tare da zama gefen ta ya sanya hannu ya ansa dolly ya haɗa allura ya fara mata, kuka jelly tasa tare da runtse idon ta tana faɗin "Wayyo Allah na" da sauri dr ya ɗago kan sa yana faɗin "Lafiya jelly?" Cikin kuka tace "Uncle dan Allah kayiwa dolly allura a hankali kaji? Nasan yanzu tana jin zafi" kallon ta da kyau yayi tsabar haushi kamar ya kwashe ta da mari a ransa yana faɗin "Wallahi ba dan cameran dake palon nan ba da kin sha mari yan iskan yara iyayen ku sun lalata ku dan rashin aikin yi irin na iyayen naku yanzu uban ki ya sa kuɗi ya sawo wan nan hauka ga talakawa can suna kwana da yinwa ba irin kuɗin da baya kashe wa kan wan nan ɗan iskan karen duk saboda ke, shigiya da wani fuska kamar anyi ɓarin kunu a cikin kasa" da sauri ɗayan ɓangaren na zuciyar sa yace "A'a Sadiq kai kan ka kasan Jelila kyakkyawa ce ajin farko" tsaki yaja a ransa tare da danna alluran da karfi yayiwa dolly har sai da ta fasa ihu da sauri jelly ta miƙe jin kukan dolly idon ta a rufe ta nufi staircase tana kuka tana faɗin "Uncle idan ka gama ka kirani" yana kokarin jan tsaki sai ya tuna akoi camera a palon hakan yasa yayiwa dolly aiki mai kyau ba dan yaso ba.
Bayan ya kammala komai ya sake dolly da gudu ta haura sama tabi bayan Jelly tana yar ƙara miƙewa dr yayi ya fice daga palon yana jan tsaki a ransa yana tunano irin kyan jelly.
Ita kuwa jelly tana shiga bedroom ɗin dadyn ta, ta haye katafaren gadon sa ta kwanta tana kuka tana yiwa dolly addu'a, bata san lokacin da dolly ta shigo ɗakin ba sai jin ta tayi a jikin ta cikin sauri ta buɗe ido tare da miƙewa zaune nan take murnushi ya kubce mata ta rungumi dollyn ta suka kwanta tare tana murna da murmushi a face nata har barci ya ɗauke ta.

KADUNA

zaune suke cikin wani katafaren palo na alfarma mai ɗauke da manya manyan sofa set masu numfashi, set 2 launin Ash da milk palon ya kawatu iya kawatuwa yaji komai da ake buƙata idan nace zan tsaya zayyana muku kyan palon nan to zamu kwana mu wuni bamu kammala ba, tsala tsalan yan mata ne su biyu kamanin su ɗaya, sai dai babban farace tas karamar kuma chocolate color ce jikin su jikin hutu ne suna sanye cikin shiga iri ɗaya wandon jeans baki da t-shirt pink color kayan sun matse su babban cikin su zata kai 20 years ta zuba kitson uban attachment kanana a kan ta wadda yazo mata har bayan ta, ita kuma ɗayan bazata wuce 18 years ba bata yi kitso ba ta tara gashin ta ɗaure a tsakiyar kai ba laifi tana da gashi har bayan wuya ga gashin nata bakin kirin mai tsantsi da sheki dukkan su ba ɗan kwali a kan su babban cikin su na rike da wayar ta kirar iphone 13 ita kuma karamar tana rike da Samsung A72 suna zaune saman sofa mai zaman mutun 3 ko wacce kan ta na kan wayar ta tana latsawa, da sallama wata yar matashiyar mata ta shigo palon ta sauko daga sama bene tana sanye cikin wata dakakkiyar lace blue da ratsin fari ɗinki bubu gown wuyan ta da hannun ta sanye suke da dankareriyar sarka da abun hannu mai matukar kyau da kyalli tayi kwalliyar ta sosai ta fita ras yar cakwai da ita wankan tarwaɗa ce matar a shekaru bazata wuci 24 years ba kafar ta na sanye cikin takalma flat shoe fari duk in da ta taka sai takalmin yayi kwas kwas har ta kariso cikin palon kai tsaye ta nufi saman katafaren dining table dake shirye da kayan abinci kala kala tana faɗin "Aafia kuzo mu fara breakfast Abbin ku na fitowa yanzun nan" ko kallon in da take basu yi ba suka ci gaba da latsa wayar su suna turɓune fuska idan da sabo ta saba bata damu ba, dan basu tanka taba ta wuce ta zauna saman ɗaya daga cikin kujerun table ɗin tana kokarin buɗe kulolin abinci wani kyakkyawan mutun ya sauko daga saman benen mai ɗan jiki kaɗan fari tas da shi kamar balarabe gashi da kwantatciyar saje da gemu mai ɗan tsawo yana da manya manyan ido kamar bull ga dogon hanci, kaman sa ɗaya da wadda aka kira da Aafia, suna ganin ya sauko suka miƙe da gudu suka nufe sa suna faɗin Abbi oyoyo rungume su yayi tana faɗin "Good morning my Angle's" "Good morning Abbi how was your night?" Cewar Aafia kafin ya amsa cikin shagwaɓa Umaisha tace "Abbi I'm feeling hungry let's go and eat" shafa lallausan gashin kanta yayi kafin ya riko hannun Umaisha suka nufi table ɗin Aafia tabi bayan su lokacin Aunty su ta gama zubawa kowa abincin sa a plate ɗin sa ta zauna tana jiran su kariso, cikin nitsuwa Abbi ya zauna saman kugeran dake kusa da Auntyn su yana faɗin "Amarya barka da safiya har kin tashi?" Turɓune fuska Aafia tayi a kule tace "Ke Umaisha ni zan zauna kusa da Abbi fa" turo baki Umaisha tayi a shagwaɓe tace "Wallahi ba zan yarda ba ai nice karama" taɓe baki Abbi yayi yana faɗin "Ke Aafia baga waje kusa da ni ta ɗayan gefen nan ba ki barwa Umaisha gefen daman tun da itace karama" kallon gefen ido Aafia tayiwa gefen hagu na Abbi in da yake nuna mata ta zauna kara turɓune fuska tayi a ranta tana faɗin "Allah ya kiyaye na zauna kusa da wan nan stupid ɗin" ganin tayi shiru yasa Abbi yace "Umaisha na yi hakuri kizo ki zauna ta site ɗin nan kinji? Ki bar mata nan ɗin" ba musu Umaisha ta dawo ta gefen hanun nasa kusa da Auntyn su ta zauna ita kuma Aafia ta zauna gefen daman sa
a tare su suka jawo plate na abincin su gaban su ita da Umaisha shi ma Abbi ya jawo na shi a nitse ya ɗauki spoon Aafia sai satar kallon sa take ta kasan ido, yana kai abincin bakin sa a sukwane ya miƙe tsaye tare da fitar da abincin yana faɗin "A uzubillahi Halima menene haka?" waro ido waje Aunty tayi tare da miƙewa tsaye ita ma tana faɗin "Me ya faru?" Cikin fushi yace "Tambaya ta kike ki ɗan ɗana abin cin mana kiji yau shi ne ranar ki ta farko da kika fara girki a gidan nan a matsayin ki na amarya mai makon ki farantawa mijin ki rai shi ne zaki min wan nan shirme? Idan kin san baki iya girki ba tun farko me yasa kikace min baki son masu aiki sumin girki zaki min kamar abun kirki eh? Wannan wani irin abune buhun gishiri nawa kika zuba a cikin abincin nan saboda Allah?" Hannu na rawa Aunty ta sa hannu ta ɗauki spoon ta ɗebi abincin dan ta ɗan ɗana taji tana kai wa bakin ta ta fitar a sukwane tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun me hakan kuma wallahi Abbi Ni bansaka gishiri ba a girkina kwata kwata" a fusace Abbi ya juya ya bar palon ba tare da ya sake magana ba miƙewa Aafia tayi cike da rashin kunya tace "Ke idan kin san baki iya girki ba me zaki wani ce zaki yi eh? Yanzu duba asarar abincin da kika yi fa wato dan baki san darajan abincin bako? Dan ba tsohon ki ke nemowa bako? To wallahi kibi a hankali bazaki zo nan kimana shirmen ƴaƴan talakawan nan ba daman ance ku baku iya samun waje ba to ki shiga hankalin ki, ki nitsu ki dai na rawan jiki dan kinga abinci Available a nan babu a house kizo ki fara mana ɓarna kamar wata rat" zuba mata ido Aunty tayi tana kallon ta idan da sabo ta saba da rashin kunyan Aafia sai dai a sati ɗaya da tayi a gidan Aafia bata taɓa mata rashin kunya mai muni da zagi irin na yau ba kasan cewar iyayen ta basu da karfi talakawa ne yasa take hakuri da rashin kunyan Aafia dan kar taje ta kulata Abbi ya sake ta dan tun kafin suyi Aure ya sanar da ita akan ƴaƴan sa zai iya komai saboda sune ma yasa ya jima bai yi Aure ba,
Fuuu Aafia ta wuce ta haye saman bene tana surfa masifa, miƙewa Umaisha tayi ta nufi saman bene tana faɗin "Sorry Aunty sarkin iya girki" ta kai karshen maganar tare da kwashewa da dariya ta haye sama, shiru Aunty tayi ta kasa motsawa daga in da take tsaye tunani take yaza ta ɓullo wa matsalar gidan nan waye kuma ya zuba mata gishiri a girki ita dai tasan kwata kwata ma bata sanya gishiri a girki ta ba, tana tsaye a wajen har Aafia ta fito sanye da wandon jeans ja da riga fari mai dogon hannu ta ɗaura wani ɗan karamin handkerchief a kan ta wadda ya tsaya mata iya goshi kawai ta zubo kitson huɗu gaba biyu ta gefen nan biyu ta gefen nan ta sanya high heel fari a kafar ta tana riƙe da makullin motar ta da jakar ta da waya tazo ta wuce Aunty ta fice daga palon taje ta shiga dan kareriyar motar ta kirar discussion continue ta figi motar da gudu ta bar gidan,

Share fisabilillah 👏

💋Star Lady 💋


💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞

https://chat.whatsapp.com/DOMGC0F7nAm6qQt6zWFwcf



STAR 🌟 LADY..✍️


*💋The beginning💋*


Episode 4


.....Still Aunty na tsaye a wajen har Umaisha ta fito shirye cikin atamfa ɗinkin doguwar riga kayan sun mata kyau sosai kuma basu wani matse ta sosai ba sun dai zauna cif cif a jikin ta, ta ɗaura ɗankwalin kayan ɗaurin ture kaga tsiya ta yafo gyale yar karama fari a kafaɗa, ta sanya flat shoe fari a kafar ta hannun ta ɗaya riƙe da yar jakar ta fara, ɗayan hannun kuma riƙe da wayar ta da key ɗin motar ta tayi kyau sosai,
har ta kai bakin kofar palon zata fita sai kuma ta juyo tace "Aunty idan Abbi ya fito kice masa na wuce School" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta fice daga palon taje ta shiga motar ta kirar continue continue ta bar gidan,
Jiki a mace Aunty ta koma ta zauna saman kujerar table ɗin tana mamakin waye ya sanya mata gjishiri a abinci ta, shirye cikin suit Abbi ya fito hannun sa riƙe da jakar computer sa kai tsaye wajen da Aunty take zaune ya nufa a takai ce yace "Zan fita kina bukatar wani abun ne?" Da sauri ta miƙe tsaye tana faɗin "Dan Allah Abbi kayi hakuri" guntun murmushi yayi kafin yace "Shike nan komai ya wuce amma dai ki kiyaye gaba zan sa akawo wasu masu aikin tun da kin sa mun sallami wayan can kuma gashi kin zo baki iya girkin ba dole nasa a nemo wasu" ya kai karshen maganar tare yin hugging nata ya manna mata kiss a goshi kafin ya sake ta ya juya ya nufi hanyar fita yana faɗin "Ki kula min da kan ki na baki amana" "To mijina sai ka dawo Allah ya tsare min kai yauwa Abbi Umaisha tace na faɗa maka ta wuce School" jinjina kai yayi kafin yace "okey ki musu addu'ar Allah ya tsare min su" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga palon murmushi tayi tana godewa Allah daya sa Abbi shi mutun ne mai saurin sauko wa idan yayi fushi, cike da kwarin gwiwa da fara'a ta kwashe kayan abincin ta mai da su kitchen ta haɗe abincin waje guda ta zuba cikin kwando ta wanke kwanikan ta gyare ko ina san nan ta fito ɗauke da kwandon abincin taje ta miƙawa baba mai gadi akan yaje waje ya zubar sannan ta dawo ta haye sama ta koma bedroom nata ta haye gado ta kwanta tana mai da numfashi.

RIMSHA

Gudu yake da motar sosai kamar zata tashi sama a tsakiyar dokar daji mai cike da dogayen bishiyoyi masu ganye kore shar, saboda cikan ganyen bishiyoyin yasa wajen yayi duhu sosai kamar dare, baka jin motsin komai a wajen wajen shiru, gudun bala'i yake shararawa da motar nan wadda da ka gan shi kasan gudun cetan rai yake ko kuma na rashin gaskiya,
Sun shafe 2 hours suna sharara gudu a dokar dajin nan suna keta bishiyoyi kafin su isa wani katon waje mai girman gaske wan da ke cike da yashi fari tas mai laushi har kyalli yashin yake, suna shiga wajen yashin ya rage gudun motar kasan cewar yashin yayi yawa tayar motar ba zata iya wani gudu sosai a wajen ba waje ne mai girman gaske dan sai da suka safe 1 hour suna tafiya cikin yashin kafin su fita ya keta ta cikin wasu bishiyoyin masu ban tsoro sun kewaye wajen sun yi kamar raun ta cikin su ya biyo duhune mai tsananin gaske a wajen haka ya kutsa motar sa ya wuce su ya ɓullo gaban wani katon gunkin kan mutun wadda jini ke zuba daga bakin gunkin kasan gunkin an kewaye kamar rijiya a nan jinin ke taruwa kamar kogi, gunkin shi kaɗai ma mutun ya gani ya isa ya sa shi mutu ko suma saboda ban tsoron sa idan ka ganshi kai kace yana da rai dan an gina idon sa a buɗe ga fari da baki irin na idon mutum ga kuma hawayen jini da ke fita daga idon na shi da baki da hanci yana da hanci mai girma gari guda girman kan gunkin nan ya kai girman kan traila ga tsawo ga faɗin daga saman goshin gunkin an rubuta *DAULAR MUTUWA* da manyan baki sun fito ɓaro ɓaro san nan aka zuba jini a wajen ya dawo ja kai da ganin wan nan ko ba'a faɗa maka ba kasan gidan mutuwa ne ba gidan zaman lafiya ba,
Yana zuwa dai dai gaban gunkin motar su ta ɓace ɓat ta fito cikin wani katafaren gida mai girman gaske kamar gidan fursina kashe motar yayi a tsakiyar gidan ya fito yana miƙa kamar wadda ya taso daga barci,
wasu kartin mutane su biyu masu kama da samudawa bakaƙe kirin kamar wayan da aka yiwa fenti da gawayi kai da gani kasan wayan nan cin namar mutane suke idon nan nasu jawur kamar jini ga katon hanci kamar tukunya suna da tsawo ga kiɓa wayan nan idan suka ɗaura maka hannun su ɗaya a kan ciki to fa sai dai wani ba dai kai ba, gashin kan nan nasu a tsai tsaiye kamar ƙawo gashi dogo ya musu kamar jijiyar bishiya suna da bala'i muni kamar a yanka a ɓuye wuka, duk in da suka yi taku ɗaya sai kaji kasa ya bada dim ɗim saboda girman su, matashin saurayin nan na tsaye har suka kariso wajen sa ɗaya daga cikin sune yasa hannu ya shafa kan mata shin, nan take matashin ya riƙiɗe ya dawo jibgegen kato baki mummuna mai katon hanci sai dai bai kai su girma ba ɗayan ne ya buɗe kofar motar cikin wata iriyar murya mara daɗin ji mai bada sautin amo mai kara kamar ganga da yaren su na matsafa yace "Barbushi yau ma yara huɗu ne aka samu fa" wadda aka kira da Barbushi ne ya kalli matashin da ya rukiɗe yanzu ya zama kato yace "Zaka iya tafi aikin ka ya kammala sai mun haɗu a aiki na gaba" ba musu Saurayin ya wuce ya nufi cikin gidan yana taku kasa na bada dum dum kamar ganga saboda girman ƙafarsa, dawo da kallon sa Barbushi yayi kan ɗayan daya buɗe motar da murya kamar an tada injin markaɗe in jin ma irin lalataccen nan mai kara mara daɗin ji mai rikita ƙwaƙwalwa yace "Kai Santilago ka kwashe su ka kai su ɗaki daban daban zuwa gobe da safe idan gimbiya ta fito sai muji me zata ce" Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya nufi hanyar komawa cikin gidan yana taku ƙasa na bada dum dum har ya shige ta wata ƙatuwar kofa mai ɗauke da tambarin wata mata tsaye ba kaya a jikin ta, ga malalen jini nan kwance cikin idon matar ga idon nata sun yi ja bakin nonon ta duk jini ke zuba aka zana ta,
shi kuma Santilago ya sanya hannu ya ɗauko Rimsha dake sume da hannu ɗaya ya ɗauko ɗaya daga cikin yaran ma da hannu ɗaya ya saɓa su a kafaɗar sa san nan ya ɗauko saura biyun yariko kafofin su kan su na lilo na kallon ƙasa haka ya wuce da su ta wata faffaɗar hanya dake ɗan gefe da kofar da Barbushi yabi yana tafiya kasa na amsawa nan ya rinƙa wuce ɗakuna masu burglaries kamar gidan fursina ba abun da ke tashi daga ɗaku nan face bala'i warin jini wani ɗakin kuma kaga akoi yara a ciki wani kuma sai dai kaga kashi ko wani sassa na jikin mutane, dai dai wata katafaren gate dake wajen ya tsaya, da gudu wani mutun wadda da ka gan shi kasan cikakken bil adama ne, yazo da gudu ya ɓuɗewa Santilago gate ya wuce da su Rimsha ciki, yana shiga wasu kantin mutane kusan kamar sa suka rufa masa baya su uku, ko wacce ɗaki daban ya kai ta Rimsha itace ta karshe suka kai ta wata ɗaki dake karshen ginin suna kokarin buɗe kofar ta farfaɗo daga doguwar sumar da ta faɗa kafin tayi wani yun kurin Santilago yayi wurgi da ita cikin ɗakin suka jawo kofar dafaffiyar karfe mai karfin gaske suka kulle suka sa key suka juya suka bar waje.
Ɗaki ne mai matikar duhu baka iya ganin komai a ciki ko yatsun hannun ki baki iya gani, ga bala'i wari jini mai sa tashin hankali da tashin zuciya dake fitowa daga cikin ɗakin.
Da kyar ta iya miƙewa zaune jiri na ɗibar ta sabida bala'i yinwa da take ji a sukwane ta toshe hanci lokacin da ta fara dawowa hayyacin ta waro dara daran fararen idon ta waje tayi ko zata samu daman ganin wani abu sai gwale idon take tana bin ɗakin da kallo tana toshe da hanci da hannu ɗaya ko tsillin tsinke idon ta ya kasa iya gane mata a ɗakin saboda tsananin duhu, motsin ta fara ji daga ɗan nesa da ita, a sukwane ta takure jikin ta waje guda saboda tsoro ta runtse dara daran idon ta tana ambaton sunan Allah ji tayi an ɗan taɓa ta a bayan ta hankali tashe ta yi saurin waro idon ta waje tare da juyawa a sukwane tana faɗin "wanene? akoi wani a nan ne?" ji tayi an kwashe da wata mahaukaciyar dariya da wata murya mara daɗin ji kamar na aljanu,
daga ɗan gefe kuwa wata iriyar siririn murya mai kama dana baby's taji ana kuka da shessheka kasa kasa, a razane tamike tsaye tana ja da baya tana faɗin "Dan girman Allah idan akoi mutane a ɗakin nan kumin magan kar

Please Login or Register in order to submit comment