Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sha'awa hakan ba karamin kyau yake karawa face nata ba, daman abu huɗu zuwa biyar ne a face ɗin Rimsha da yafi ɗaukan hankali duk wanda yayi ido huɗu da ita, na farko wayan nan kyawawan dara daran sleeping eyes ɗin nata farare kal kamar audiga, ba karamin tafiya da imanin ɗan adam suke ba, kasan cewar idon nata yayi daban, sai ka tara mutane sama da dubu baka samu biyu masu irin wanna idon ba, shine babban abun da yafi jan hankali mutane a face nata, na biyu kyakkyawan dimple nata, idan tana murmushi ko tana magana, ko baka son ta sai ka tsaya ka kalleta, saboda dimple ɗin nan, ba karamin kyau yake kara mata ba, ɗan siririn open teeth, dake tsakanin hakwaran ta da suke farare kal a baya amma yanzu saboda da hannu take brush babu brush hakan yasa hakwaran nata suka rage haske, amma still suna da hasken sai dai ba kamar lokacin da suke tare da daddyn su ba, abu na huɗu ɗan bakin ta, wow idan tana magana abun sai wanda ya gani, laɓɓan ta na sama design of heart ne ga bakin nata ɗan karamin dashi launin pink color kamar wadda ta sanya lipstick, hancin nan nata har baka ɗan siriri kamar karas Masha Allah, ga bakin saje kwance a gefen kumatun ta.

Sai hiran su suke duna ya tsare su da ido, can kome ya tunan ya miƙe yazo ya tsugunna a gaban ta, tare da zuba mata ido a hankali yace "Me yasa idan kuna magana kuke yawan sanya Annabi Muhammad? Waye shi?" Dawo da kallon ta kan face nashi tayi cikin nitsuwa tace "Shi ne Babban abun soyuwa a gare mu, kuma shine annabin karshen da baba ya faɗa maka ranar, duk wani cikakken musulmi yana son Annabi Muhammad" "eh nasan kuna son shi kam dan baku magana ɗaya biyu baku kira shi ba" yar murmushi Rimsha tayi kafin tace "Saboda son da muke masa ne yasa har a zamanin baya kafin yazo duniya ya samu takwara dayawa, sosai jama'ar zamanin da kafin yazo suka masa takwara" zaro ido duna yayi kafin yace "To bai zo ba kuma ya akayi suka san shi har suka masa ta kwara? Waye ya faɗa musu sunan shi da har zasu masa takwara? Bayan ni nasan sai an haifi yaro ake sanin sunan da za'a sa masa" ɗan kawar da idon ta tayi daga kallon sa kafin tace "Annabi Muhammad (SAW) an san shi ne tun kafin a ganshi, kuma an sanshi ne tun kafin a haife sa, domin yazo a littafai da dama, sunan sa ya bayyana a littafai irin su attaura, injila, zabura, so already wayan nan littafai sun bayyana zuwan sa da sunan sa da yanayin da zai zo, da kuma in da zai bayyana, waye shi da sauran su, shi yasa jama'a suka rinƙa masa takwara saboda son da suke masa, muma yan zamanin yanzu muna kaunar sa fiye da rayuwar mu, ni kullun cewa ma nake da azamanin sa a ka haifeni dana more" shiru duna ya ɗan yi kafin yace "Kwarai kuwa na san kuna son shi, nima shaidane dan kuwa akoi wata mata dana taɓa shanyewa jini a kasuwa, lokacin na riƙeɗe na dawo kamar yadda kika ganni yanzun nan, na shiga cikin mutane, a kasuwa na ga matar tana sai da kaya, kawai naji ina son shanye jinin ta, to lokacin akoi wata waƙa da ta kunna suna faɗin annabi kwarai kasan gaibu, na kasa manta wannan wakar ita kan ta matar na kasa mantawa da ita, ban san ya akayi ba ita ce mutun na farko dana taɓa shan jinin ta dana kasa mantawa, bayan na sha jinin nata sai naji ban ji daɗi ba, har yanzu na kasa mance ta" jinjina kai Rimsha tayi har idon ta ya kawo ruwa saboda tausayin matar a hankali tace "Baka kyau ta ba, amma dai karka ɗauka abun da suke faɗe a wakar gaskiya ce, domin Annabi bai san gaibu ba, dalili kuwa shi da bakin sa yace bai san gaibu ba, a lokacin da sayyidina Abubakar ya tambaye sa yaushe za'a tashi kiyama, sai yace wa sayyidina Abubakar sanin gaibu sai lillahi shi bai sani ba, Allah ne kaɗai ya san ranar tashin Al kiyama, kaga kenan idan da annabi yasan gaibu da muma mun san lokacin da za'a tashi kiyama dan da zai faɗa wa sayyidina Abubakar, shi kuma zai ruwaito mana hadisai, abu ɗaya ne yasa mutane ke ganin kamar annabi yasan gaibu, shine mafi yawancin lokaci Allah yana masa wahayi mala'ika Jibril yazo ya faɗa masa Allah ya bawa wanna sahabi aljanna, ko kuma Allah ya saukarwa wannan sahabi wata ni'imar, to idan mala'ika ya isar masa da wanna wahayi, shi kuma sai ya sanar da Sahabban sa, hakan yasa mutanen mu na yanzu suke ganin kamar annabi yasan gaibu tun da yana faɗin abubuwan da basu kai ga faruwa ba, kamar dai yadda ya bayyana Allah ya baiwa su sayyidina Abubakar aljannan tun suna raye, shi yasa rashin fahimter ce kawai da mutane ke samu, mafi yawancin mutane suna kan dai dai bisa nasu fahimter, basu kauce hanya ba kawai basu fahinci abun dai dai bane"

hannu ya kai zai shafi kumatun ta, sai kuma ya fasa, cike da kaunar ta yace "To ni dai gaskiya addinin ku yana burgeni, ta in da kuma yake burgeni in da akace matar ka kai kaɗai zaka taɓa ta ba wanda zai taɓa maka ita, wannan abun yamin daɗi sosai, addinin akoi tsabta sosai, kinga a baya zamu kwanta da duk macen da muke so, kuma ina da tabbacin kafin mu wasu sun kwanta da ita, hakan tsam ba tsari, ace mace ɗaya maza dayawa suyi ta kwanciya da ita abun ba ɗaɗi, amma addinin ku yayi hani da wanna gaskiya naji daɗi kuma na jinjinawa addnin nan naku" cool murmushi ta saki taji daɗi duna ya fara yaba addinin musulunci, da alama ya fara hawa kan hanya ma dai'dai ciya hakan ba karamin farinciki ya sanya su ba, dukkan su har da su Ayla.

A wanna yanayi Mustapha yazo ya same su, dan yanzu yana zuwa suyi ta hira da duna sun zama kamar friend, yana zama Rimsha ta miƙe tana faɗin "Ina zuwa Ayla bari na je ɗaki na ɗauko apple na najiya" to kawai suka amsa mata da shi, sannan ta wuce ta bar wajen, su kuma suka ci-gaba da hiran su.

Tazo zata shiga ɗakin nasu, sai taga yar siririyar hanya daga ɗan gefen ɗakin nasu, Rimsha da karambani tace bari ta leƙo taga menene a wajen, ɗan karamin hanya ne, ga wani fitinanniyar wari bala'i dake fitowa daga wajen, haka ta kutsa ta wajen tare da toshe hanci ta tana lallaɓawa saɗaf saɗaf kamar wata ɓarauniya har ta kai karshen hanyar, ba tare da su duna sun ankara da ita ba, suna ta hiran su

ko da taje karshen hanyar sai taga ba wani abu a wajen sai wani katanga mai ɗan tsawo daya musu katanga, ma'ana ya raba su da wan can part ɗin.

Kamar a kafarki taji kafar ta ya tsunduma cikin wani abun, cikin tsoro a hankali ta kai kallonta kasa, nan taga wani irin jini mai bala'i kauri da yauki, cikin jinin duk guda gudan naman jikin mutun, ta wani gefen ma har da kashi ɗan adam, ɗago idon ta tayi a razane ta kalli gefe gefen wajen da kyau, gaba ɗaya kashin kwarangal na mutane ne, ga kuma naman jikin mutun wadda bai gama murmushe wa ba, kasan wajen wani daskararren jini ne mai balai wari, ga kuma wani sabon jini na malala a saman wannan daskararren, da alama yanzu ake zubar da wannan jinin, wani mugun tsoro ne ya dira mata a ranta lokaci guda, nan take jikin ta ya fara ɓari, wani irin wahalallan yawu ta haɗiye da kyar, nan take idon ta ya rena fata, wani gumin wahala ya fara karyo mata.

Amma saboda fitina irin na Rimsha sai da ta kama katangar nan har da yar tsallen ta, ta leƙo, dan ta dage sai taga daga ina jinin nan ke fitowa.
Nan fa idon ta suka gane mata abun da kwakwalwa ba zai ɗauka ba, wani mahaukacin ihu ta fasa tare da sakin katangar, kamar zararriya haka ta bazama ta fito daga wajen, a guje su duna sokayo kan ta, saboda ihun ta da sukaji

Tun da yaga ta in da ta fito yace shikenan kuma mawuyacin abune yau Rimsha ta rayu a gidan nan, ita kuwa sai ihu take kamar wata zararriya, tunani duna ya shigayi ya zai yi ya kuɓutar da Rimsha daga sharrin su Gujungu, dan yasan definitely wayan nan magicians dake wajen zasu biyo bayan ta dan sun jiyo ihun ta, kuma tabbas bazasu barta da rai ba, dan ba'a ganin sirrin su a rayu.

Sai ihu Rimsha take da alama ta fita hayyacin ta, dan ta razana sosai da abun da ta gani, jin takun sahun jiga jigan magicians ɗin ne yasa duna kara tsorata dan yana ji a ransa sai dai yau ya mutu amma ba zai iya bari su ɗauki Rimsha ba, takun magicians ɗin sai kara kusan tosu yake, duk in sukayi taku ɗaya, sai kasa da katanga sun girgiza saboda girman su da larfin bala'i irin nasu.

Sai zaro ido duna yake, kasan cewar yasan duk bala'i sa su Gujungu wato masu gadin fadar Queen sun fisa bala'i, ko su Barbushi basu isa su tinkare su ba bare kuma shi, banda Queen ba mai iya ja da su Gujungu a gidan, manya manyan jiga jigan magicians ne masu ji da larfin ɗaga mota kamar yar baby da hannu ɗaya, tsabar girman jikin su da karfin su, idan suka taka kasa, sai katangar dake wajen ta girgiza, hakan yasa mafiyawancin ɗakunan gidan da dafaffun karafuna a kayi su katanga ɗai ɗai ne a gidan, dan katanga ba zai iya ɗaukan karfin takun su Gujungu ba rushewa yake.

Jin sun kusa isowa in da suke ne, dan ga alamar sautin takun kafar su da kuma amshin kasa nan ya kara karuwa, tsabar tsorata duna bai san lokacin daya batar da Rimsha da tsafin saba, a baya yayi alƙawarin ba zai sake amfani da tsafin ba, saboda Rimsha ta nuna masa tana tsoro kuma bata son hakan, idan har zai ci-gaba da amfani da tsafin to gaskiya ba zata ci-gaba da yi masa magana ba, shiyasa yace mata ya dai na ba zai sake ba, amma yau bashi da zaɓi dan Rimsha ta taɓo gidan rina ta tsokalo gindin dodo bala'i da yafi karfin su, shiyasa ya ɓatar da ita gaba ɗaya daga wajen

Bayyanar su Gujungu a wajen ba karamin haukata kwakwalwan yan gidan gaba ɗaya yayi ba, banda duna da ya saba ganin su, ba wanda kwakwalwan sa bai haukace ba a gidan sai Mustapha, saboda su Gujungu sun fi su Barbushi a muni uban ni su Barbushi ne, sanna a girman jiki sunyi biyun su Barbushi, sai dai basu da tsawo, gajeru ne, sai bala'i faɗi shiyasa kofar shiga wanna wajen nasu ma faɗin sa ya kai 2 miter dan su iya shiga da fita, amma duk da haka a takure suke, saboda girman jikin su, hancin su kawai ya kai girman kan bil adama, idon nan nasu bazai ganun wa ɗan Adam ba, ka fafun sunan ya kusa faɗin fridge, munin su kawai zai iya sanya ɗan adam zuciyar sa ta buga ya mutu, babu ko ɗigon imani a tattare da fuskokin su bare tausayi, basu fitowa kullun suna wanna part din nasu suna aikin sarrafa wa Queen ganganjikkin ɗan Adam da sauran ayyuka.

Tun kafin su iso daman duna ya koma asalin halittar sa na Magicians, Ayla da kausar tuni sun sume a wajen, shikuwa Mustapha, kamar mahaukaci haka ya bazama yayi ɗakin da ya samu a buɗe ya shege, haka sauran yan gidan da basu suma ba, suma duk ɗakin da suka samu kawai shiga sukayi dan cetan ransu, kuma basa hayyacin su.

Duna na tsaye har suka ƙariso wajen, Gujungu ne ya fara tambayar ina wadda ta leƙa su take, cikin yaren su na matsafa, da muryan sa mai doɗe kunnen ɗan adam ya daina ji gaba ɗaya, nan fa duna ya fara musu kame kame na cewar bai ganta ba, wani mahaukacin kururuwa Gujungu ya sa wadda yayi sanadiyar tada guguwa mai karfi gaske bakin kirin kamar bakin hayaki na itacen damuna, jijjiga jikin sa yayi tare da ɗaga kofatan kafa ɗaya zai sauƙe a kan Ayla, duna yayi saurin kwanciya kasa ya shiga tsakanin su, kafar Gujungu ya sauka ma shi a cinyoyin sa ta baya

razanannen ihu mai bala'i sauti duna ya sake mai razana kwakwalwar duk wani halitta mai rai, kan kace me cinyoyin duna sun rugurguje har kashin sa sai da suka rugurguje saboda takun kafar Gujungu fa ba wasa ba.

Wucewa su Gujungu sukayi suka nufi cikin gidan dan neman Rimsha, shi kuwa duna sai ihu azaba yake na cinyar sa da ta daddage, haka suka wuce zuwa tsakar gidan dukkan wadda suka samu a kan hanya ya suma bi ta kan sa suke su wuce, duk kuma wanda suka sauƙewa wanna gofaton kafar nan tasu, tofa namar sa daga'daga yake ya daddage, wasu ma har lumewa cikin kasa suke idan suka take shi, banda jini ba wani abun dake malala a tsakar gidan, sai fantsala musu a fuska da jikin jinin yake, amma da yake yan datti ne ko ajikin su basu damu ba.

Bayan sun tsaya a tsakiyar gidan ne suka fara jawo duk wata halitta dake cikin gidan suna fito da su, da tsafin su, sai dai kagan su fiw sun jawo mutun waje ya fito, haka suka jawo Mustapha ma fiw ya fito kamar iska, har da baba suka fito da shi, duk a tsakar gidan suka tara kowa, kafin su juya idon su ya koma kalar na tsafin su, wato light green, da tsafin nasu suka fara neman in da Rimsha take a cikin gidan, domin kuwa madubin Queen ya nuna musu babu Rimsha cikin wayan da suka tara a wajen, sai zazzaro ido suke suna jujjuya idon nasu gwanin ban tsoro da tashin hankali

Bayan Mustapha da duna da baba ba wata halitta mai rai da ta rage tana cikin hayyacin ta a gidan, har ita Rimsha ɗin da duna ya ɓoyeta bata cikin hayyacin ta, mai iya kallon su Gujungu ido huɗu kuma ya iya rayu bai mutu ba, tofa sai mai tsawon kwana kuma mai karfin imani, irin dai mutanen part ɗin su Rimsha, dan sune masu imanin gidan, tun da har suka iya wace part 1 suka wuce part 2 suka zo nan to tabbas sune jiga jigan masu imani, dan mai raunin imani baya iya tsallake wa su Barbushi.

Can cikin duhu ɗakin duna idon tsafin su ya hango musu Rimsha tana kwance tana ihu, da karfi, Gujungu ya fisgota, da tsafin sa zuwa tsakar gidan

Saƙabo ne ya wage wanna gabjejen bakin nasa ya fara ɓaɓɓaga dariya irin nasu na gunguma gunguman matsafa, nan take gidan ya ɗauka da karfin sautin dariyar tasa, juyawa sukayi, suka nufi hanyar da sukabi suka zo, da tsafi suka fara jan Rimsha tana bin su a baya daga kwance, Allah sarki jikin ta sai kukkujewa yake a kasa tana ihu kamar ranta zai fita....


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞




TRIPLET'S💞



💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)



*Gargarɗi*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_




WhatsApp me for more information 09162620621






Episode 32-33



Saƙabo ne ya wage wanna gabjejen bakin nasa ya fara ɓaɓɓaga dariya irin nasu na gunguma gunguman matsafa, nan take gidan ya ɗauka da karfin sautin dariyar tasa, juyawa sukayi, suka nufi hanyar da sukabi suka zo, da tsafi suka fara jan Rimsha tana bin su a baya daga kwance, Allah sarki jikin ta sai kukkujewa yake a kasa tana ihu kamar ranta zai fita.

Haka suka wuce da ita, duna yana ji yana gani dan kuwa babu abun da zai iya shima neman a kawo masa ɗauki yake.

A wanna yanayi su Barbushi suka shigo part ɗin suka same sa, kasan cewar mutumin sune kuma dole su taimaka masa saboda aikin da yake musu, cikin sauri suka ɗauke sa suka wuce da shi, dan suje su nema masa ruwan tsafi wajen Queen ko kafafun nasa zasu gyaru.

Su Ayla kuwa bayan tafiyar su Barbushi Mustapha ne ya taso yazo ya taimaka musu ya jasu zuwa ɗakin su, sanna ya mai da baba ma ɗakin sa, ya dawo ya zauna shiru ya buga uban tagumi sai haɗa zufar wahala yake, yau yaga abun daya kwance masa notikan kansa, duk sai yaji duniya ta isshe sa, ban da addu'a a ransa babu abun da yakewa Rimsha, shi kan shi baba addu'a kawai yake mata tare da tausaya mata da kuma su Ayla idan suka tashi ya zasu ji a ransu ace musu an kashe Rimsha.

Haka baba da Mustapha suka zauna jugum jugum suka buga uban tagumi kamar wasu marayu, suna yiwa Rimsha addu'a.

Wanna kenan mu leƙo Washington DC mu dawo


💞WASHINGTON DC💞

9:20am

Sai sauri James yake ya sauko kasa daga saman bene, kamar wani mara gaskiya yana tafiya yana waigen bayan sa yana waya kasa kasa, jikin sa na sanye da suit ashe colar mai shegen kyau da tsada, kayan sun kara masa kyau sosai.

Dai dai tsakiyar palon yana waigen bayan sa bai ankara ba sukayi karo da wani bodyguard wadda ya ɗauko tray mai ɗauke da kyawawan glass cup wadda a ka cike su da drinks.

Gaba ɗaya drinks dake cikin cups ɗin nan suka kware a jikin James, zaro ido bodyguard nan yayi Allah sarki nan take jikin sa ya fara kerma, ya kasa magana saboda tsoro, James kuwa ransa ya ɓaci iya ɓaci, a fusace ya wanke wa bodyguard nan fuskar sa da wata mahaukaciyar mari, ji kake tass, dai dai lokacin Romeo ya sako kafar sa saman benen yana kokarin saukowa

Cikin jin haushi abun da James ɗin yayi rai a ɓace ya dakawa James tsawa "Are you mad James!!? Tsabar tsorata da bodyguard nan yayi na tsawar da Romeo ya daka sai da zuciyar sa ta buga a wajen ya yanke jiki ya faɗi kasa gawa, Allah sarki ya ɗauka shi Romeo ya dakawa wanna tsawar shiyasa ya tsorata haka har zuciyar sa ta buga ya mutu, dan dukka gidan idan Romeo yayi magana a hankali ma firgita su yake jikin su yayi ta kerma bare kuma tsawa ai sai mutuwa, criminals da dama tsawa Romeo ke daka musu zuciyar su ke bugawa saboda tsoro su mutu, dan duk wanda ya kwana ya tashi a Washington DC tofa yasan hukuncin GAR babu kyau, yasan GAR baya hukunci mai daɗi, mutuwar tsoron sa jama'a keyi, ganin face nashi yana cikin farinciki ma razanar da hantar manyan maza yake bare kuma in ya ɓata rai, Subhanallah ba sai ya kai ga hukunta mutun ba tsawa kawai ya wada wa mutun zuciyar sa zata iya bugawa ya mutu, sai dai in mai sauran tsawon kwana.

Ganin bodyguard ɗin ya faɗi kasa yasa James yayi saurin tsugunnawa yana taɓa shi, ina rai yayi halin sa, ɗago ido James yayi a tsorace ya kalli Romeo dake tinkaro su "He died" ya faɗa a razane, har cikin ransa Romeo bai ji daɗin mutuwar bodyguard ɗin ba, yasan dai jama'a da yawa a wajen suna tsoron tsawan sa, a wajen aikin su ma, wasu idan ya waro musu dara daran blue eyes na sa ya kalle su ma kawai suma suke, wasu criminals ɗin ma da ance musu GAR ne zan yanke musu irin hukuncin da ya dace da su, a wajen suke murɗe wuyar su su kashe kan su, dan a cewar su, da hukuncin GAR gwara mutuwa, da GAR ya kalleka da fusatacciyar fuskar sa kamar wani lion ɗin nan gara su mutu, bai taɓa tunanin bodyguard nasu na gida suna tsoron tsawar sa har haka ba, kasan cewar su bodyguard ɗin wajen dining table ba sojoji bane, su kawai an ajiye sune dan miƙa musu tissue paper da kuma ruwa da drinks sai serving nasu abinci.

Abun bai ma Romeo daɗi ba, wuce wa kawai yayi ya nufi hanyar fita daga palon ba tare da ya kara tanka James ɗin ba, yana fita ya turo jibga jibgan sojojin sa a kan suzo su ɗauki bodyguard ɗin su fitar da shi, aje a shirya sa zuwa mutuware,

Wanna ma ba cikin ɓacin rai Lion yayi wanna tsawar ba, da ransa a ɓace yayi ta ina ga da har shi kan shi James ɗin sai zuciyar sa ta buga.

Haka sojojin suka zo suka ɗauki gawar bodyguard ɗin suka fice da shi

Gaba ɗaya James yaji ba daɗi kuma ya ɗaura alhakin mutuwar bodyguard ɗin a kan sa, a cewar sa komai ya faru shine sila, da yayi hakuri bai mari bodyguard ɗin ba da Romeo ba zai yi wanna tsawar ba, zai zo ne kawai ya wuce su ya fice daga palon, amma gashi yanzu saboda nuna masa kuskuren sa da Romeo ke kokarin yi yasa zuciyar bodyguard ya buga.

Jiki ba kwari James ya wuce ya koma bedroom na sa dan sake wanka ya canza kayan jikin nasa.

After some hours

Shirye cikin wando jeans baki three quarter James ya fito da riga Turtle high blue, kai tsaye wannan fili na Romeo ya nufa, dan yana da tabbacin suna can.

Da excuse ɗauke a bakin sa, ya iso wajen, Romeo na zaune saman sofa daya saba zama yana latsa waya, while shi kuma Michael yana tsaye ya ɗaure wasu kwalaɓe wadda Romeo ke ɗaurewa sojojin sa idan suka masa laifi, sai ya ɗaure musu wayan nan kwalabe suna lilo ya ce su ja baya sosai su saita kwalaben da bindiga su harbe su dukka su fashe su, kuma kwalaben ba tsaye suke waje guda ba kaɗawa suke sosai suna lilo idan kayi missing na bullet ɗaya baka fasa kwalbar nan ba, to horo mai tsanani Romeo zai baka, a koi wani ruwa mai kankara, gaba ɗaya ruwan waje ice ne haka Romeo zai jefa ka ciki, ta kofar da yasa aka yiwa ice ɗin, ka zauna cikin ice nan tsawon 3 hours kafin ya sa a fitar da kai ya sanya wasu sojojin su zane ka, kana rawan sanyi suna zane ka, idan suka maka kamar bulala hamsin sai a sake mai daka cikin ice ɗin na 3 hours again, duk wanna hukuncin na missing bullet ɗaya da kayi ne ba'a kai ga na laifin da kayi a ka kawo ka wajen harbin kwalaben bama tukun nan, wanna dalili yasa criminal da dama suke kashe kan su in dai suka san lion ne zai yanke musu irin hukuncin da za a musu, wanna ma idan yana farincikin kenan, duk wata kalar hukuncin mugun ta Romeo ya iya shi, gashi da zuciyar bala'i, ga kafiyar masifa idan yayi magana yayi ne ba wanda ya isa ya sanya shi ya sauya, baya mai mai ta magana idan yayi yayi ne, koda bakaji me yace ba to yazama dole kayi abun da yace dan ba zai mai mai ta maka ba idan kuma ba ka aikata abun da yace ɗin ba hukun taka zai yi, ga bala'i zafin rai kamar wuta, ga zafin kai, ba mai iya tankwara shi ya canza masa abun da yayi niyar yi, babu wanna mahalukin dan shi kaifi ɗaya ne, sannan miskiline na karshe, dan baya

Please Login or Register in order to submit comment