Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan bala'i mai kama da tashin duniya.

Daddy na kuka gwanin ban tausayi ɗan tsohon nan, haka ya haura sama da gudun ya nufi part ɗin Romeo dan ya kira shi yazo ya dakatar da kwarin nan karsu kashe pastor, dan yayi ta rokan Michael, Michael yace ba zai dakatar da su ba sai dai su kashe pastor ɗin.

Ganin daddy na kuka ba karamin ɗagawa lion hankali yayi ba, a sukawane ya miƙe ya taro daddy yana tambayar sa lafiya, cikin kuka daddy ya sanar da shi abun da Michael ya aikata, rai a matukar ɓace ya zaunar da dad saman bed nasa sannan ya nufi Palo, daman ga damuwa sun masa yawa ga batun James ga bincike a kan asibiti masu sai da koda da sassan jikin maza, ga bincike a kan kontenan mai ɗauke da mata daya kama jiya, abun ya haɗe masa lokaci guda

Yana sauƙa palo rai a matukar ɓace ya ɗauke Michael da wani gigitacen mari wadda yasa Michael zubewa kasa a kan gwiwowin sa yana ganin wasu taurari masu hasken gaske suna gilmawa ta cikin idon sa, saboda azaban zafin marin ma ya kasa kuka, daman hausawa na cewa duk ciwon da akewa kuka bai kai ciwo bane, idan ya kai ciwo neman kukan ake a rasa, to wannan ma hakane Michael dai ya nemi kukan sa ya rasa

Romeo kuwa bai kara bi ta kan ba dan sauri yake aiki na gaban sa, dakatar da kwarin yayi sannan ya koma sama da sauri, dad kuma yana zaune in da Romeo ya zaunar da shi.

Allah sarki pastor ya jama kan sa bala'i duk fuskar nan tasa ta sunduma luhu luhu kamar an hura palo palo, abun ka da fatar Bature jikin sa yayi jajir kamar jini da kyar da kyar yake fitar da numfashi.

A ɓangaren Michael kuwa good 40mins ya ɗauka a wajen zube a kan gwiwowin sa kafin ya samu marin Romeo ya sake sa, sai lokacin da marin ya sake sa ne ya samu damar fitar da zafafan hawaye daga idon sa, da kyar ya miƙe ya fice daga palon, bai ɗauki mota ba ya fice daga gidan da kafar sa, yana tafiya yana hawaye yana tunanin yau shi Romeo yayiwa wannan marin gaskiya dole ya bar musu duniyar baki ɗaya tun da basa son shi, da wannan tunani ya hau babban hanya wadda manya manyan motocin ke wucewa wai shi zai mutu, yana tafiya yana hawaye, duk motar da tazo da kyar take iya kauce masa, sai zagin sa wasu drivers ɗin suke idan suka kauce masa da kyar, shi kuma ko ajikin sa dan yace mutuwa zai yi kawai tun da ba mai son shi, Allah sarki bawan Allah matsalar daga kwakwalwan sane ba daga shi bane

Wata mota kirar Mercedes-Benz ne ta taho a guje ba tare da ta lura da shi ba ta kwashe sa, ji kake kiiiii gam, sai jinin Michael ya wanke glass ɗin gaba na motar, da kyar driver motar ya iya taka birki, nan take jama'a suka cika wajen, motocin dake wucewa duk suka dakata saboda haɗarin da akayi, driver da ya buge Michael ɗin ne ya fito da gudu duk da shima yaji ciwo da jikin glass ɗin motar dan glass ɗin ya tarwatse kaca kaca, sai dai shi bai mutuba a iya goshi yaji ciwon.

Duk da cewa gaba ɗaya jikin Michael yayi caɓa caɓa da jini hakan bai hana jama'ar dake wajen su gane daga family William jacop yake ba, duk wani halitta mai rai dake wajen babu wanda bai tsorata ba lokacin da sukaga diamond watch na Triplets a hannun Michael, dan duk wanda ya kwana ya tashi a Washington DC to dole zai san da wannan agogon a hannun The general of the army Romeo, sun tsorata sosai, an rasa mai karfin zuciyar kiran Family William jacop a waya a ranar da su an buge ɗaya daga cikin yan gidan da mota kuma ya mutu, dan ko ina jini ke zuba daga jikin sa.

Daga karshe dai motar asibiti suka kira ya zo ya ɗauki gawar Michael dan kowa na tsoron a fara jin maganar daga bakin sa, gara suji zancen daga asibiti zaifi

Yau saboda tsoron da jama'a kewa Romeo an rasa mai karfin zuciya da dauriyan kiran over over'n cikin gidan William kai abun dai babu daɗi ko kaɗan.

Allah sarki Michael ba zan iya ganin tashin hankali da dad da lion zasu shiga ba idan suka samu labarin mutuwar ka, dan haka mu koma Nigeria mu leƙo wata kila kafin mu dawo anyi jana'izar Michael.

💞KADUNA STATE NIGERIA💞

Zaune Su Umaisha suke wajen gaban department nasu Aafia suna hira sama sama ita da Aafia

Babu ko sallama Rufee ta kariso wajen, da sauri Aafia ta miƙe ta rungumo ta tana faɗin "Rufee ya mukaji da hakurin rashin Amal" hawayen munafurci Rufee ta fara yi tana faɗin "Wlh ji nake kamar na mutu nabi Amal yanzu ma saboda ke nazo school nan, nazo na baki maganin nan ne sai na koma ana can ana zaman makoki" Allah sarki Aafia da yake ba yin kan ta bane sai ta karɓa maganin da Rufee ta kawo na zubar da cikin Aunty, kuma daga nan Abbi zai tsane ta, sai murna Aafia take Abbi zai tsani Aunty ya koreta daga gidan, ita kuwa Umaisha yar ba runa ko ajikin ta dan da zaman Aunty a gidan da babu duk ɗaya ne a wajen ta bata da matsala da hakan, sai kitsawa Aafia mugun abu Rufee take, nan Aafia ke sanar da Rufee'n zuwan daddyn Jelly gidan su, ko kaɗan Rufee bata ji daɗi ba musamman ma da Aafia tace mata daddyn Jelly zai hana su fita da ko wani kaya sai atamfa da kuma hijabi, ba haka Rufee take so ba, ita tana son ne ta koyawa Aafia bin maza dan haka sai ta fara shirya yadda zasu yi da daddyn Jelly.

Suna tsaka da wannan zancen nasu ne kamar daga sama, sukaga wani handsome guy ya diro wajen ya danki hannun Umaisha, ita kan ta Umaisha bata gane Akil ɗin ba dan ya canza sosai ya kara girma ya kara tsawo da cika yayi bul'bul gwanin ban sha'awa, daman Akil ba baya ba wajen kyau, duk da ita ma Umaisha ɗin ta canza dan shakara uku ba wasa ba hakan bai hana Akil gane taba, dan Imran na tura masa hotunan ta, shi kuma Imran wajen Irfan yake samun hotunan nata.

Kokarin kwace hannun ta tayi dan bata gane saba kwata kwata musamman dayayi shigar kananan kaya abun ba'a magana, wani mahaukacin mari ya sakar mata wadda yasa ta game ko wanene, cikin fushi yace "Kina matata ne zaki fita da wannan ɗan iskan shiga ko? To yau zan koya miki hankali sai kin yi nadama wlh" sai da yayi magana sannan Aafia ta gane wanene, da farko ta ɗauka wani saurayi ne daban har ta fara kamuwa da son shi dayake basu da aiki sai faɗawa soyayya da kyawawan maza, ita kuwa Rufee baki ta sake tana kallon Akil taga kyau nan take taji ta kyatsa da shi kuma tana son shi amma ba da aure ba da iskanci kawai dan ta sawa ran ta Abbin su Aafia kawai zata aura bayan ta gama barbaɗancin ta da tambaɗancin ta a titi.

Cak Akil ya ɗauki Umaisha kamar yar baby ya saɓata a kafaɗar sa tana ta bubbuga masa bayan sa tana faɗin "Ka sauke ni bana so" bai saurare taba ya wuce wajen motar sa, yana zuwa yayi wurgata gidan baya na motar ya shiga gidan gaba ya datse marfin motar tare da tada motar da gudun gaske ya figeta suka bar cikin school ɗin, sai wani hucin ɓacin rai yake, kamar shi ace matar sa ta fita da wannan kaya kai ina dole yayi maganin ta yau, makarantar ma daga yau anyi cancel na shi ba zata sake zuwa ba, sai saka zancen zuci yake a zuciyar sa yana zuba uban gudu da mota.

Ganin Akil ya tafi da Umaisha ne yasa Aafia ta nufi motar ta da sauri dan tabi su taga ina zasu je, sai tambayar ta Rufee take waye Akil? Aina yake? Shima a School ɗin nan yake ne Amma ina Aafia bata bata amsa ba dan hankalin ta a tashe yake burin ta kawai ta isa wajen su Akil, da gudu itama ta ja motar ta tabi bayan su ta bar Rufee tsaye a wajen,

Juyawa Rufee tayi tana faɗin "Tun da kin saka maganin a jakar ki ai bukata ta tabiya shi kuma guy ɗin can ko ki faɗamin wanene ko karki faɗa sai na nemo ɗan gidan uban waye ne dan na ji shawarar sosai ya kamani gaskiya" sai surutu take har ta isa wajen tsohon motar Irfan da Abbi ya bata ta shiga itama ta bar school ɗin.

Akil kuwa kai tsaye gidan su ya wuce da Umaisha sai ihun rashin kunya take masa tana maganganu marasa kan gado, hakan ba karamin fusata shi yake ba, yana parking a parking space na gidan su ya fito ya ɗauke ta kamar yar baby sai zagin sa take, bai kula taba ya wuce cikin gida, a palo yaci karo da Ammie su tana zaune, da sauri Ammie ta miƙe tana tambayar sa wace ce wannan ya ɗauko

Ina hankalin sa baya jikin sa part nasa ya wuce kawai, da sauri Ammie tabi bayan sa cike da tashin hankali, ita da take zaune take jiran anje ɗauko shi a airport ko ina kuma ya samo yar mutane oho masa, tana tafiya tana zancen zuci kafin ta isa bakin part nasa, tuni ya shige ya murzawa kofar key, tsayuwa Hajiya Umaiya ko in ce Ammie tayi tana ɗan bubbuga kofar tana kiran sunan sa, amma ina ya shige can cikin bedroom nasa

Yana zuwa yayi wurgi da Umaisha saman gado tana kokarin tashi ta gudu ya sake mai data, yasa kafa ɗaya ya take mata hannaye dan kar ta tashi, a fusace ya cire kayan jikin sa duka yayi wurgi da su gefe, ya rage daga shi sai Short, hayewa saman gadon yayi ya damkota, Ammie na tsaye a bakin kofa tana buga mashi kofa, amma ina baya jin ta.

Jin Umaisha na kuka ne yasa Ammie ta tsorata dan tasan halin Akil sarai baya son reni tun yana yaro, idan ka rena shi to ba abun da ba zai iya aikatawa ba, son girman bala'i gare shi

cikin sauri ta koma palo ta ɗauko wayar ta, takira Abba ta sanar dashi abun da yake faruwa, shima Abba ya tsorata sosai yace yayi nisa amma ba zai wuce 1h ba yana zuwa, amma kafin nan Hajiya ta dakatar da Akil dan basu ma san ko yar waye yaje ya sankamo ba, sai zare ido Hajiya take.

To jama'a ta ko ina ba sauki Washington DC Triplets suna can cikin tashin hankali gashi shima Akil yana neman ɓata komai, bari dai mu leƙa daular mutuwa mu dawo kila a can mu dace mu ɗan samu sassauci, amma idan ba haka ba akoi matsala, wannan tashin hankali dame yayi kama🥺

👹DAULAR MUTUWA👹

Wani irin turnukin bakin turɓayan kasa ne ke tashi kamar guguwa, gaba ɗaya girman Daular mutuwa sai da ko ina ya karaɗe da wani masifaffen duhun bala'i, ga wani iska mai karfin gaske mai karfin ɗaukan ɗan adam sama abun gwanin ban tsoro, wasu muryoyi mara sa daɗin ji masu bata amo mai sauti ne ke tashi daga fadan Queen, sai juyawa gaba ɗaya gidan yake yadda kasan ba daga kasa a ka yi ginin ba sai ka rantse da Allah a saman iska gidan yake saboda yadda yake juyawa, wannan guguwa mai bala'i karfin gaske ne yasa gaba ɗaya wayan dake cikin gidan kowa ya shige cikin ɗakin sa

Ihun wasu halittu masu kama da zakuna ne ya fara tashi a cikin gidan mai bala'i sautin doɗe kunnen ɗan adam

Duk wannan duhun da iska da guguwa duna na tsaye a tsakiyar part nasu, yadda kasan an dasa shi ko motsi bayayi ya tsaya kekam

kamar daga sama Rimsha ta faɗo gaban sa, tana faɗowa yayi saurin sake tsafin nasa ya duka gaban ta yana kiran sunan ta

Yana sakin tsafin nasa kuma cikin kankanin lokaci gidan ya fara washe wa, sai dai kuma me, nan fa jiga jigan matsafan Queen suka biyo sahu dan basu barin bashi

Ganin yana yin gidan ya fara canzawa alamar jiga jigan mutanen Queen suna zuwane yasa duna miƙewa da sauri ya riƙo hannun Rimsha ya miƙar da ita sai nishi take da kyar da kyar, dai dai lokacin Ayla da Kausar suka fito dan sunga gidan ya ɗan wastsake

Ganin Rimsha yasa suka kwasa da gudu sukaje suka rungume ta, itama ganin su ya kara mata karfin jikin ta, gidan nasu kuwa sai kara riƙiɗewa yake zuwa jawur kalan jini dan dama ita Queen kalar jini ce shiyasa komai nata yake ja kamar jini

Wasu irin halittu ne suka bayyana a tsakiyar wajen masu bala'i girman gaske wadda zasu iya haɗiye dan adam kamar paracetamol, wayan nan halittu su shidda ne suna da kafofin guda huɗu kamar damisa, sai dai kafofin nasu kanana ne jikin su yafi kamar basu girma, munin wayan nan halittu kawak ya isa ya kashe mutun idan ya gansu, gadan gadan wayan nan halittu suka nufi su Rismha yayin da su Barbushi suke biye da wayan nan halittu a baya

Ganin haka yasa duna yaja hannun Rimsha da gudu ita kuma tana riƙe da hannun Ayla yayin da Ayla ke riƙe da hannun Kausar, da gudu wayan nan halittu suka rufa musu baya, suma su Barbushi suka rufawa halittun baya

Duna ya ɗan yi gudu a cikin gidan mai nisa dasu Rimsha kafin ya tsaya dai'dai wajen wani katon gunkin Queen tare da sakin hannun Rismha ya caka hannun sa cikin kasa da iya karfin sa yana ihu ya ɗago wata kofa ya buɗe wajen, cikin sauri yace da su Rimsha ku fi ta wannan hanyar idan kuka fara gudu karku tsaya kuma karku juyo baya, kuyi gudu ku ceci ranku, ni nasan kashe ni zasu yi ba zan rayuwa ba, amma dai ki sani ina son ki ba zan iya bari su kashe ki ba dan haka ki gudu, ya kai karshen maganar tare da fitar da wani ɗan gora mai ɗauke da ruwan tsafi yace "Idan kuna da rabon tsira in kuka kai kofar karshe na hanyar nan, ki buɗe wannan ruwan ki zubawa kofar kaɗan zata buɗe sai ku fita, ragowar ruwan kuma ki ajiye wata rana zai miki amfani ku gudu" sosai su Rimsha suke hawayen rabuwa da duna musamman ma da sukaji yace yasan kashe shi zasu yi sai Rimsha taji wani irin duk babu daɗi a jikin ta

Ganin ta tsaya shiru taki tafiya ne ga kuma wayan nan munanan halittu sun kusa cin musu hakan yasa duna ya turata ta cikin ramin mai kama da rijiya

A tare Rimsha suka faɗa da Ayla da Kausar dan suna riƙe da hannu juna

Yana turasu wayan nan Halittu na isowa wajen, riƙiɗewa shima yayi ya koma irin su suka fara gwabza faɗa a tsakanin su, sai dai daya ke suna daya sai suka fara dukan sa suna ji masa rauni abun tausayi, su kuwa su Barbushi bayan su Rimsha sukabi dan su kamo su su cinye su ɗanye, dan ba zasu barsu su karya musu tarihin gidan Daular mutuwa ba, a tarihin Daular mutuwa duk wanda ya shiga baya fita ya shiga kenan sai a lahira.

Su Rimsha kuwa gudun cetan rai suke, tsabar gudun da suke basu san lokacin da suka saki hannun juna ba, kasan cikin ramin duk kasusuwan jikin ɗan adam, sai suke musu kafofin su kashin yake jini na zuba, duk da haka basu damu ba, sun daure suna ta gudu.

Kamar ance Rimsha ta juya, ta manta duna yace karsu kuskura su juya kome zai faru da su, tana juyawa sai taga babu Ayla iya Kausar ce kawai, ihu Rimsha ta saki wadda ya sa Kausar dakatawa da gudun da take tare da juyawa, a guje Rimsha ta nufi hanyar komawa Daular mutuwa dan ba zata iya tafi ba tare da Ayla ba, itama Kausar bata da zaɓi dole tabi bayan Rimsha dan su gudu tare su tsira tare. Tashin hankali

Abun da ya faru shine lokacin da suke cinkin gudu Ayla ta taka wani kashin mutun mai bala'i tsini ya fasa mata kafa, hakan yasa ta faɗi kasa, taki yin ihu tayi shiru dan bata son ta dakatar da su Rimsha har azo a kama su dukan su, tafi son ko ba ita ba wani daga cikin su ya tsira, kashin ya fasa mata kafa sosai ta yadda ba zata iya gudu ba har su Barbushi suka cin mata a wajen, shine suka kama ta, Barbushi ya goyata a bayan sa ya ci-gaba da bin su Rismha, ga kuma su Rimsha sun juyo suna tinkarar su.

Wayyo ni jikan mutun huɗu gaba ɗaya ta ko ina ba sauki, zuciyata ba zata iya jure ganin wannan azaba da my Rimsha take ciki ba.

Masu karatu nan na kawo karshen Book 1 wato The beginning kuma shine free, yanzu zamu shiga The struggle masu son ci-gaba da karanta Book nan ku hanzarta kuyi payment naku dan wasan yanzu zai fara, ya kuke ganin wannan cakwakiya, ya kuke tunanin rayuwar lion zai kasan ce bayan mutuwar Michael da ɓatar James?!!, Ya kuke ganin anya Rimsha zata tsira kuwa? Dan ita da kan ta ta juya ta koma Daular mutuwa ga kuma su barbushi ɗauke da Ayla a kan hanya suma suna tinkaro ta!! Yaya Akil zai kare da Umaisha? Meke shirin faruwa tsakanin su?! Anya Abbi zai bawa Akil auren Umaisha kenan? Ya makomar cikin Aunty? Shi zai sube kuwa? Yaya rayuwar Jehan zai kasan ce? Yaya makoman Jelly da Abbo? Yaya makoman Musharraf a gidan Dr William jacop? Gashi dai ya sa hannu a takarda zai yi zaman 4 years, gashi mai tausaya masa wato James baya nan ya ɓace!! Wanene Alhajin dake bibbiyar Aafia?!! Yaya bakoman baba da Mustapha a Daular mutuwa?!! Anya lion zai yafewa mum ɗin sa kuwa?! Anya akoi wanda zai iya rusa Daular mutuwa kuwa?!!!! Shine wace ce ma Queen?!!! Waye ya kafa Daular mutuwa?!!! Menene kama sudin kafa shi?!! Anya kuna ganin Jehan zata iya aikin restaurant har ta biya Ibraheem kuɗin sa?!!! Ina James ya tafi?!! Shine sace sa akayi ko menene?!! Abbo zai auri Jelly kuwa?!!! Idan ta kasan ce ya Imran zai yi?!!! Cakwakiya ziryan domin samun amsoshin ku dole ku kasance da alkalamin *PRINCESS TEEMA*

Domin ci-gaba da karanta book ɗin *TRIPLETS* ki hanzar ta kiyi payment naki 500 Naira ne only 👌3167987863 Musa Fatima Zahra first bank, masu Opay bank kuma 9162620621 Musa Fatima Zahra opay bank, sai ku turo shaidar biya ta wannan number 09162620621, kada ki bari a baki labari dan yazu wasan zai fara, na barku lafiya Much kauna 🥰


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞




















An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment