Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tannan sai kyalli suke, wucewa shi ma yayi ya je yayi wanka, ko da ya fito bata ɗakin ta fice palo sauri sauri ya shirya cikin suit sannan ya ɗauki jakar computer sa da wayar sa ya duba time 7:02 sauri sauri ya fito zaune ya iskota saman sofa tana ta murmushi kamar ba ita ba a wan nan karon daddy ya kasa ɓoye mamakin sa yace "My baby what is happening ne?" Miƙewa tayi ta rungume sa tana faɗin "My daddy I want you to be happy everyday that's why" rungume ta yayi kawai amma bai yarda da maganar ta ba dan yasan halinta sarai, kafin ya sake ta yana faɗin "Muje muyi breakfast mu tafi kar lokaci ya kure" ba musu ta bishi suka zauna saman kujerar table, Nana tazo tayi serving na su sauri sauri suka yi breakfast, bayan sun gama daddy ya riko hannun ta suka nufi waje, suka je suka shiga mota gidan baya idi driver ya shiga gidan gaba ma zaunin driver yayiwa motar key suka bar gidan, a bakin gate na school na su suka tsai da motar daddy ya juyo ya kalle ta yace "Yau ba zamu shigar da ke ciki ba nayi late sauka ki shi ga school ina kallon ki" ba musu ta sauka daga motar da murmushi tace "Daddy na, ina kaunar ka sosai ka kula min da kan ka sannan kayi min alkawari ba zaka sake kuka ba komai zai faru da ni" daddy bai kawo komai a ransa ba yace "Na miki alkawari my baby ba zan sake kuka ba" sako kan ta tayi ta glass ɗin motar ta manna masa kiss a kumatu bata jira reply na shi ba ta wuce da sauri saboda hawaye da ya gangaro mata, zuba mata ido daddy yayi yana kallon ta, ya sha ruwan mamaki ganin yau bata juyo ta masa bye bye ba saɓanin kullun da take juyowa wani lokaci ma tafiyar baya baya take tana kallon sa, ganin su daddy basu tada mota bane yasa ta fahimci daddy na kallon ta dan haka sai ta kara sauri ta shige cikin school, tana shiga school Idi driver ya tada motar suka bar wajen sai mamaki daddy yake nan take yaji jikin sa ya mutu gaban sa na faɗuwa, haka ya daure dan bai kawo komai a ran sa ba har suka isa office na shi,

Ita kuwa jelly tana laɓe a wajen gate sai da taji motar su daddy ya bar wajen tayi Sa'a mai gadin ya zaga bayan gida su daddy na tafiya ta fito da sauri ta kariso bakin hanya ta tari abun hawa ta hau tana sauke ajiyar zuciya "Ina zan kai ki?" Mai mashin ɗin ya tambaye ta cikin sauri tace masa "In da ake hawa mota" ɗan juyowa yayi ya kalle ta kafin yace "Motar zuwa ina?" Sai lokacin ta tuna ita bata ma san a wani gari gidan su yaya Imran yake ba shiru tayi tana tunanin hiran da suka yi a baya da Imran "Motar zuwa ina nace?" Mai mashin ɗin ya sake gefo mata tambaya nan ta tuna last zuwan yaya Imran yace mata daga Kaduna ya fito da ta tambaye sa daga ina ya fito tuna haka yasa cikin sauri tace wa mai mashin ɗin "Motar zuwa Kaduna" ba tare da ya sake magana ba ya buga mashin ɗin sa suka nufi park sai sauke ajiyar zuciya take,
Ko da suka isa bai sauke ta ba sai da ya kai ta har wajen motocin Kaduna tayi Sa'a kuwa motar saura mutun ɗaya ya tashi, mai mashin ɗin yace "Kawo kuɗi na biya miki kuɗin mota" ba musu ta sauke jakar school dake bayan ta, ta zaro dollar dubu ɗaya tana faɗin "Nawane kuɗin?" Waro ido waje mai mashin yayi yana kallon kuɗin dake hannun ta nan take jikin sa ya fara rawa kasa kasa yayi da murya yace "Ki mai da kuɗin nan idan kina da kuɗin Nigeria ki kawo" miƙa masa dollar tayi tana faɗin "To kai riƙe na baka dan kana da kirki ina da kuɗin Nigeria" ta kai karshen maganar tare da sanya dayan hannun ta ta zaro dubu dubu guda biyar ba musu mai mashin ɗin ya ansa dollar da ta bashi ya mata godiya san nan ya ansa 5k da ta ciro ya sauka ya biya mata kuɗin motar zuwa Kaduna ya mata sallama tare da bata canjin ta ya wuce, shi kan sa driver ya sha ruwan mamaki ganin yarinya kamar jelly tazo hawa mota hakan yasa ya tambaye ta ina zata je dan ya tabbatar tana cikin hayyacin ta yarinya 14 years, cikin sauri ta sanar da shi Kaduna zata je da mamaki a face na shi na jin tana cikin hayyacin ta haka a ka loda kayan passengers a bayan mota, driver ya shiga kowani passenger ya shiga mazaunin sa jelly ta zauna kusa da wata tsohuwa mota ta tashi zuwa Kaduna.

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💋Star Lady💋

*💞TRIPLET'S💞*


💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞





STAR 🌟 LADY..✍️


*💋The beginning💋*


Episode 7

💞💞💞💞💞💞💞💞

*3 years back*

*Abuja*

*7:10 am*

Wata haɗaɗiyar Hajiya ce zaune saman sofa mai zaman mutun 2 cikin wani katafaren palo, palo ne mai girman gaske mai ɗauke da sofa set manya manyan set biyu kowani set da kalan sa sai makekiyar Tv plasma dake manne a bango, daga gefe kusa da kyakkyawar staircase ɗin haurawa sama table ɗin cin abinci ne awajen mai bala'i kyau mai kujeru 8 daga wajen table ɗin kofar kitchen mai girma gaske mai ɗauke da duk wani abun da mace ke bukata a kitchen, ga manya manyan gas cooker guda biyu.
Sanye matar nan take cikin dan kareriyar Swiss lace pink color da ratsin baƙi, ɗin kin bubu gown ta sha kwalliya sosai, wuyar ta da hannun ta sanye da dankara dankaran gold tayi kyau sosai ta yi ɗaurin Zahra Buhari a kan ta da ganin ta kasan naira ta zauna mata sosai jikin ta jikin hutu yayi luwai luwai da shi gata fara tas kyakkyawa a jin farko, shiru ta zauna tana kallon News a makeken Tv plasma dake manne a bango, hankalin ta yayi nisa a kallon da take wani kyakkyawan Alajine ya sauko daga saman bene fari tas da shi kamar balarabe yana shirye cikin wata dakakkiyar shadda ash color kyakkyawa ne sosai yana da kwantatciyar saje da gemu bakin kirin ga gashin kan sa na fulani har wani curly yake yana nannaɗewa ya gangaro masa har gaban goshi ga wata kyakkyawar gashi da ta kewaye ɗan bakin sa tayi masa kamar raun ba karamin kyau hakan ta karawa face na shi ba, a hankali ya tako ya kariso cikin palon ya sanya hannu ta baya ya rufe idon hajiyar dake zaune sofa, cool murmushi ta sake har sai da fararen hakwaran ta suka bayyana ga wani siririyar wushirya a tsakanin hakwaran nata gwanin ban sha'awa cikin shagwaɓa tace "Barkama (sunan girmamawa ne na fulani) kayi latti ai to" murmushi ya saki wadda yasa dimple na shi lotsawa slowly ya zame hannun sa daga kan face nata tare da zagayowa ta gaban ta yana faɗin "bongel am (kyakkyawa ta) barka da tashi" murmushi tayi tana kokarin yin magana wata kyakkyawar yarinya chocolate color ta sauko daga saman benen da gudu, kyakkyawace ajin farko doguwa tana da dogon hanci har baka ga dara daran ido kamar ball farare tas kamar auduga idon nata design of fish ne san nan kuma sleeping eyes gare ta wadda idan ka ganta zakayi tunanin barci take ji amma ba barci bane gasu da girma idon kamar ball bakin ta ɗan karami launin pink lip nata na sama design of heart ne kanta ba ɗankwali curly hair ta ya nannaɗe kamar indomie ga gashin nata dark black sai kyalli yake kai kace an tsomashi cikin baby oil ne saboda curly da kyalli da yake gashin nata har gadon bayan ta duk da yana nannaɗe hakan bai hana shi kai mata tsaliyar bayan ta ba tana da dogayen gashin ido sosai kamar tasa eyelashes ga saje mai kyau dark black kwance a gefe da gefen kumatun ta tana sanye cikin wando skin tight baƙi da white T-shirt mai dauke da bajel ɗin makaranta kyakkyawan kafofin ta ba ta kalma, hannu ta na riƙe da wani katuwar teddy kamar jaririn mutun a shekaru ba zata wuce 10 years ba,
Da gudu ta sauko bene tana faɗin "Daddy kace wa Jehan ta kyaleni" tayi maganar cikin harshen shuwa arab ta kai karshen maganar tare da rungume sa, shafa curly hair ta yayi kafin yace "My Rimsha My siha where is your Abaya? Ko so kike muyi latti ne?" Girgiza masa kai tayi tana faɗin "Daddy this teddy is it not my own?" Tayi maganar sai da dimple nata irin na shi ta lotsa sosai, ta kai karshen maganar tare da ɗago masa teddy'n dake hannun ta tana nuna masa, yana kokarin yin magana Jehan ta sauko da gudu tana faɗin "I'm I playing with you? I'm I your mate?" A lokacin Jehan tana da 12 years, tana sanye cikin uniform riga me dogon hannu light blue se doguwar riga a saman ta dark blue mai hannu a kafada rigar ta tsaya a dai dai gwiwar ta se wandon uniform dark blue ƙafar ta sanye da Black socks ba takalmi a ƙafarta da gudu tayo kan daddy tana kokarin fisgo Rimsha, ihu Rimsha ta fasa tare da kanka me daddy tana faɗin "Daddy save me" fararen hannun sa yasa ya riƙo hannun Jehan yana faɗin "Haba Jehan yau fa Graduation ɗin My siha mai kuma ya haɗa ku faɗa a kan teddy kullun baku da aiki sai faɗa kan teddy ba kalan teddy da ban sawo na kawo gidan nan ba ni narasa meke damun ku" bai kai ga rufe baki ba mum ta miƙe ta amshe teddy tana faɗin "This teddy is for Rimsha whare is your own Jehan?" Turo baki Jehan tayi tana faɗin "Mum This is mine, is not for Rimsha" kallon mum daddy yayi san nan yace "bongel ɗauko min sauran kayan su yau ba ma zamu yi breakfast ba haka zamu wuce dan munyi latti, sayi breakfast ɗin a school ɗin na su ko idan mun dawo" ya kai karshen maganar tare da ruƙo hannun Rimsha ɗaya na Jehan ɗaya suka zauna saman sofa mai zaman mutun 3 yana kallon face na Rimsha, har cikin ransa yake bala'i son yaran nan nashi gashi Jehan ita ce mai kama da shi sai dai bata da dimple irin nashi ita kuma Rimsha da mum take kama sai kuma ta ɗauko dimple ɗin dad wushiryan mum, miƙewa mum tayi ta haye sama sauri sauri dan ɗauko musu sauran kayansu

Kallon daddy Rimsha tayi cikin harshen shuwa arab tace "Daddy ni zanzo first class In Sha Allah" murmushi daddy yayi ya sanya hannu yana tara mata curly hair ta da baya kitsuwa idan a ka mata kitso sai ya warware ga gashin nata da tsowo sosai a nannaɗe kamar indomie duk da naɗuwar sa kuma bai hana tsowon gashin nata bayyana ba dan a nannaɗen ma ya kai mata har tsakiyan baya "In Sha Allah my siha ke zaki zama first class" ya kai karshen maganar tare da ɗaure mata gashin nata da kyar dan sai ya kamo sai su zame shi yasa ma bata cika ɗaurewa ba dan ko ta sanya rebon fita yake shima daddy yanzu kulle mata yayi kamar igiya da gashin ya kullu, ita dai Jehan ko a jikin ta hankalin ta na kan Tv,

a tare mum da gwaggo suka sauko hannun mum riƙe da Abayar Rimsha Black colour da Hijab fari da takalmin ta da Black socks ita kuma Gwaggo na shirye cikin Abaya fari tas ta yafa gyalen abayar a kan ta idon ta sanye da glass ɗan siriri mai matukar kyau da tsada, hannun ta rike da Hijab ɗin Jehan light blue Dan Karami kalar T-shirt ɗin uniform ɗin, mum ta shirya Rimsha Gwaggo ta shirya Jehan

bayan mum ta gama shirya Rimsha ne ta ɗago ta kalli daddy tace "Yanzu Barkama da gaske kake ba zan biku ba?" Dogon hancin ta yaja yana faɗin "Duk abun da zai faru a School ɗin daga farkon har karshen zaki gani ki kunna TV kuma in muka dawo nayi alkawari zan biya" hararar wasa ta masa tana musu addu'a, riƙo hannun Rimsha yayi gwaggo kuma ta rinƙo hannun Jehan suka nufi hanyar fita daga palon "eyeeee My siha yau ba zuwa da jaka kenan" mum tafaɗa tana dariya, dariya ita ma Rimsha tayi kafin tace "Mum yau hutu za'ayi ai" komawa mum tayi ta zauna saman sofa tana faɗin "Allah ya bada Sa'a kuzo min da first class" a tare gwaggo da daddy suka amsa da Amin dai dai lokacin suka fice daga palon suka nufi parking space na gidan, da gudu wani ɗan sanda ya nufo su ya buɗe wa daddy da gwaggo kofar motar daddy kirar Roll-Royce boat Tail a tare suka shiga gidan baya daddy ya ɗaura Rimsha saman cinyar sa ita ma gwaggo ta ɗaura Jehan saman cinyar ta, ɗan sandan ya shiga ya tada motar yaja suka nufi gate, tun basu kariso wajen gate ɗin ba iliya mai gadi ya wangale musu tampatsetsen gate ɗin cikin kwarewa da iya tuki ɗan sandan nan ya danna hancin motar waje suka miƙi titi,

Cikin kankanin lokaci suka isa bakin katafaren gate ɗin Great Heights Academy horn ɗaya ɗan sanda yayi mai gadin ya wangale musu gate ɗin, ɗan sandan ya kutsa motar sa cikin school ɗin.

Makarantar cike take makil da jama'a ga manya manya baki da manya manyan yan siyasa da sarakuna sunzo taya yaran su murna masu kammala primary da jss 3 da ss 3 Rimsha na cikin wayan da za su kammala primary 6 na su tana cikin wayan da suka zana common entrance while Jehan na jss 2 yanzu, sai murna Rimsha take ita ma zata shiga secondary zata kamo Jehan.

Ɗan sanda na parking a parking space na school ɗin ya fito ya buɗewa daddy da gwaggo suka fito nan take manya manyan alhazawan dake tsaye a wajen suna jiran fitowar daddy suka kariso cikin murna da fara'a suka fara bashi hannu a kan su gaisa, kasan cewar shine babban bako a wajen hakan yasa director makarantar da sauran malamai suka kariso wajen da sauri dan tarban sa, cikin girmamawa director ya miƙawa daddy hannu yana faɗin "Barka da zuwa gaskiya munji daɗi da amsa gayyatar mu da kayi muna alfahari da hakan" murmushi daddy ya saki har sai da dimple na shi ta lotsa yace "Ai dole nazo ko dan siha ta" ya kai karshen maganar tare da shafa kan Rimsha cool murmushi ta saki har sai da dimple nata ya lotsa siririn open teeth dake tsakanin fafaren hakoran ta ya bayyana hakoranta fafare tas da su kamar gonan audiga, manya manyan Alhazawan dake wajen dukkan su Rimsha ta matikar burge su sosai. Malamar su Rimsha ce ta ƙaraso ta gaida daddy cikin girmamawa ta kama hannun Rimsha tana faɗin "let's go and get ready" a hankali ta lumshe sleeping eyes nata ta sake buɗe wa kafin tace "Bye daddy see you in the Hall" ta kai ƙarshe maganar tana yi masa bye bye da hannunta shima bye bye ɗin ya mata ita dai Jehan tun saukowar su ba ta jira kowa ba ta wuce wajen friends nata,
Director ne yace "sir please let's go in"
Kallon Gwaggo daddy yayi yace "Anty A'isha muje Koh"

a tare suka ranƙaya zuwa cikin katafaren hall ɗin dake cikin School ɗin a nan za'ayi taron ƴan jarida sunzo ɗaukar new gidan TV kala kala gaba ɗaya student na ciki kowa na zaune saman kujera an kawata hall ɗin sosai da kalar makarantar Dark blue da light blue an rubuta Sunan Makarantar da ballons dark blue da light blue idan nace zan tsaya zayyana muku haɗuwar da hall ɗin nan yayi to zamu kwana mu wuni bamu kammala ba kawai ku kawata shi a ran ku, hall ne mai girman gaske an cike sa da kujeru da student suka zazzauna, ta gaba kuma inda aka tanadar na ɗaliban da sukayi graduation ɗine, daga saman staircase wani ya opposite ɗin students ɗin, a ka shirya wasu haɗaɗu kujeru masu kyau sun kawatu iya kawatuwa ga wata doguwar table a gaban kujerun an jera drinks a sama da ruwan faro masu sanyi wadda daga ka gani kasan wajen baki na musamman ne daga tsakiyar kuren a kwai wata haɗaɗiyar kujera golden color an mata kwalliya sosai kamar kujerar sarauta daga gani kasan mutun na musamman a ka tana dawa,

manya manyan alhazawa da sarakuna ne zazzaune saman sauran kujerun da a ka jera layi sai wan nan ɗayan mai kama dana sarakuna shi da na kusa da shi ne babu kowa a kai, saman sa daddyn su Jehan yaje ya zauna ita kuma gwaggo ta zauna a kujerar kusa da na shi, nan take student suka miƙe suka fara kwasan gaisuwa daddy na amsa musu da fara'a a face na sa, duk school nan ba wanda bai san shi ba sai dai in new comer amma student ɗin school ɗin sun san shi dan mutun ne shi mai fara'a da kyauta gashi da son yara duk kuɗin da yake da shi, shi da kan sa yake kawo su Jehan school kuma ya dawo ya ɗauke su dan gani yake kamar idan ya bari driver ya kai su ba zai kula masa da su sosai ba, shi yasa ko abu suke so yake ɗaukan su suje shopping tare da shi komai aikin da yake zai ajiye yazo yayi attended nasu, yana bala'i kaunar su sosai,

Bayan sun gama kwasan gaisuwa ne suka koma suka zauna.
Mike director ya ɗauko ya sanya a saitin bakin sa ya fara magana cikin harshen turanci "Ina mai farincikin zuwan wan nan rana mai albarka Jehan Nawazudden Salman kizo ki buɗe mana taro da Addu'a" shiru hall ɗin yayi, gaba ɗaya manya manyan bakin da suka halakci taron sun zubawa Jehan ido wadda ta taso tana tafiya a nitse, a hankali ta tattaka saman staircase ɗin ta hauro sama taje ta tsaya kusa da director, miƙa mata mike ɗin director yayi ta ansa cikin kyakkyawa turancin ta da zazzakar voice nata mai sanyi da daɗi ta fara da yi musu sallama san nan ta fara jero addu'a "We take refuge with Allah, The Supreme and with His Noble Face, and His eternal authority from the accursed devil In the name of Allah, and prayers and peace be upon the Messenger of Allah O Allah, open the gates of Your mercy for us Amin" ta kai karshen Addu'ar tare da rufewa da Ayatul kursiyyu, sosai jama'a suka yi ta kabbara ciki hadda daddy da gwaggo sosai daddy yaji daɗi, ji yayi kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha,

bayan Jehan ta sauka ta koma mazaunin ta ne director yace a shigo da ɗaliban da sukayi graduation ɗin, a cikin layin suka shigo cikin tsarin suna sanye Cikin graduation gown kalar uniform ɗin makarantar daga bayansu kuma malaman sune kowa fuskarsa cikin annashiwa da tsantsar farin ciki, kai tsaye inda aka tanadar domin su suka karasa sannan sukayi Anthem ɗin makarantar aka basu iznin zama
Director ne fara kiran graduates ɗin ɗaya bayan ɗaya sukazo su gabatar da kan su san nan suyi jawabi tare da nuna farincikin su sai suyi karatun al Qur'ani mai girma,

ba laifi yaran sun iya kira'a daddy ya kosa a kira Rimsha ɗin sa haka ita ma gwaggo ta kosa taji karatun Rimsha, duk yarinyar da tazo a kace ta karanta Al Qur'ani mai girma bata wuce karanta sura daga nasi zuwa amma ko sabbi,

Rimsha itace yarinya ta goma da a ka kira cikin nitsuwa ta taso tana tafiya a nitse ta hauro saman wajen ta ansa mike ɗin da zazzakar voice nata ta fara da bilmillah san nan ta karanta suratul fatiha daddy yaji ba daɗi a tunanin sa a suratul fatiha zata tsaya sai yaji ta sake wata Bismillah ta fara karanta Suratul Baƙara,
shiru hall ɗin yayi ba abun da ke tashi sai zazzakar voice ɗin Rimsha dake tashi, gaba ɗaya kowa ya nitsu tsit suna sauraron baiwar da Allah ya mata farincikin a wajen daddy da gwaggo ba'a magana,

hawaye Rimsha ta fara yi tana karatu ko da tazo In da Allah ke magana a kan itaciyar da ya hana Annabi Adam ci Annabi Adam yaci ta sanadiyar haka Allah ya fito da shi daga aljanna, sau uku tana mai mai ta ayoyin san nan ta ci gaba tana karatu tana kuka, tun muryan ta na fita sosai har ya fara sarkewa saboda kuka da take idan ta tuna girman Allah ta tuna mutuwa kwanciyar kabari gadar siraɗi hisabi sai ta kara fashe wa da kuka shi kan sa daddy sai da kwalla ta cika masa ido duk wani mai imani a wajen sai da idon sa ta kawo kwalla dan kukan da Rimsha ke yi tana rero kira'ar nan, masu saurin kuka kam ma tuni sun fara rera nasu kukan cikin harda Jehan,

da kyar Rimsha ta iya kai karshen suratul bakara tana kokarin durkushewa kasa a wajen daddy da ya kasa hakuri ya taso da sauri yazo ya rungume ta yana faɗin "It's okey my siha" cikin kuka tace "Daddy me mutun zaiyi a dunuyyar nan da ya wuce bautan Allah daddy mutuwa gaskiya ce kwanciyar kabari gaskiya ce gadar siraɗi gaskiya ce hisabi gaskiya ce haka zalika wuta da aljanna gaskiya ce daddy, duk wani rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa daddy, duk lokacin da na kalli kwayar idon ɗan Adam daddy ina kara jin tsoron Allah da ganin girman Allah a rayuwata dan idon ɗan adam ma kawai ya isa yasa bawa mai hankali ya kara jin tsoro Allah, duk lokacin da na tuna da mutuwa hisabi kwanciyar kabari gadar siraɗi wutar jahannama daddy ina shiga tashin hankali sai in ji gaba ɗaya duniya ta fitamin a rai na daddy, me ya rage bawa yake so bayan yayi bautar Allah dan ya samu ya tsira ranar gobe kiyama, daddy ban taɓa kwaciya barci na sawa rai na zan farka a duniya ba, ban taɓa lissafin me zai faru gobe na ba kullu lissafi na iya yau nake dan bana sawa rai na zan kai goben mutuwa gaskiya ce kuma tana ɗauka duk lokacin da kwanan mutun ya kare ba ruwan ta da abun da kake ko in da kake zata ɗauke kane kawai, daddy duk wani musulmi kamata yayi ya sawa ransa iya yau kaɗai garesa ba zai kai gobe ba dan ya samu damar aikata aikin Allah, daddy duk lokacin da na samu dama har tsawon kwana na ya kai nayi sallar issha, ji nake tamkar an sauke min wani katon dutse a kai na dan kullun ina cikin fargabar kada na mutu gab da wata sallar ko azahar ko la'asar kuma a ce ban samu damar yin wan nan sallar ba" ganin maganar da Rimsha take babban magana ne yasa director ya kawo mata mike ɗin sai tin bakin ta dan kowa yaji maganar nata, sosai hall ɗin gaba ɗaya suka ɗauka da kuka babban magana miƙewa manya manyan sarakuna irin su sarkin Zazzau Sarkin kano Gombe Bauci da dai sauransu suka yi, ba karamin tashin hankali magangun Rimsha ta jefasu ba yariya yar karama kamar wan nan amma tana da karfin imani har haka shi kan shi daddy yayi shocked da jin maganar Rimsha yasan dai tafi Jehan ilimin addini dan ita kullun tana tare da mum tana koya mata karatun addini

Please Login or Register in order to submit comment