Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nufi kofar palon yana amsa sallamar, kallon Gwaggo mum tayi kafin tace "Da alama barkama ya san da zuwa mai gadin nan fa" murmushi gwaggo tayi tace "Ni dai ba ruwa na kun fi kusa ai" mum na kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa "Mum i need to see your previous pictures before you got married to my dad nan take face ɗin mum ta sauya, nan take taji ba daɗi taji zuciyar ta na mata ciwo Jehan ta tuna mata baya, shiru tayi bata yi magana ba.

Da sallama daddy ya dawo palon hannun sa ɗauke da carton irin na turo sako daga kasar wajen nan, a tsakiyar palon ya ajiye, da sauri Jehan ta miƙe ta kariso wajen tana faɗin "What is this daddy?" Miƙewa zaune Rimsha tayi ta zubawa daddy dara daran sleeping eyes ɗin nan nata ba tare da ta je wajen ba.

Buɗe kwalin daddy yayi ya fara fito da kayan yana faɗin "Kaya na saya muku daga Dubai" ya kai karshen maganar tare da fitowa da Jehan wasu kayan masu kyau na yan kwallo dan Jehan a koi ta da son kayan yan kwallo sosai, daddy na kokarin yin magana Jehan ta ansa kayan daga hannun sa tana dariya ta wuce ta haye sama ta nufi bedroom na su dan taje ta gwada, girgiza kai kawai daddy yayi ya ci gaba da fito da kayan, ita dai Rimsha ta zuba masa dara daran sleeping eyes nata tana kallon yadda yake fitar da kayan, ɗago kai yayi yace "My siha close your eyes, i want to surprise you" ba musu ta ta rufe idon na ta, wani leda ya ɗauko daga cikin kwalin ya nufe ta, ya zauna gefen yana faɗin "now open your eyes" da sauri ta buɗe idon nata dan ta ƙagu ta ga me daddy zai mata surprise a kai, miƙa mata ledar yayi yana kallon face nata, cikin zumuɗi ta ansa tare da buɗewa

a sukwane ta miƙe tsaye tana faɗin "What? Daddy am I dreaming or not?"

Sosai daddy ke murmushi dan bashi da wani burin da ya wuce yaga farincikin yayan sa, wan nan murmushi dake kan face ɗin Rimsha ya fi masa abubuwa kaso 80 cikin ɗari na rayuwar sa.

Fito da kayan Rimsha tayi tana ta dariya kamar bakin ta ba zai rufu ba, kyakkyawan dimple nata sai motsawa yake ga open teeth nata dake tsakanin fararen hakwaran ta kamar gonar audiga, cikin zumuɗi ta zuje zip ɗin jacket ɗin ta sanya a jikin ta tana faɗin "daddy ai na ka samu irin jacket ɗin GAR dan Allah" "Saya na yi mana, My siha daga Dubai na sai miki saboda son da kike wa guy ɗin shi ne na ga kuma yana yawan sanya irin jacket ɗin shiyasa na ɗauki hoton na tambaya wurare daban daban da kyar na samu a Dubai, na ɗau wajen 2 weeks ina neman jacket nan company company, su kan su company da suka buga jacket ɗin na tuntunɓe su ta number su na WhatsApp, amma sai suka ce min gaskiya iya shi kaɗai su kayiwa shi ya kawo sample suka masa dan haka ba zasu iya yi min ba, wan nan ma na hannun ki ba sak irin nashi bane copy ne babu irin na sa shi kaɗai suka bugawa" shiru Rimsha ta ɗan yi kafin tace "Daddy to shi ma copy ɗin yana da tsada ne? Dan naji a Tv sun ce Jacket ɗin na shi na da tsada sosai, gashi kuma yana da su kala kala, sai dai duk design ɗaya ne color ne daban daban" jinjina kai daddy yayi kafin yace "Hmmm My siha kuɗin da na sayi jacket nan ba zai faɗu ba ke dai kawai ki saka irin jacket na GAR ɗin ki ba sai kin ji kuɗin copy ɗin ba ma" juyawa tayi ta kalli mum kafin tace "Mum ya min kyau?" Mum da gwaggo har suna gaɗa baki wajen cewa "Ya miƙi kyau over Rimsha sai dai ya miki yawa sosai, Jacket ne har kasa gaskiya ki ajiye sai kin kara girma" make kafaɗa tayi tana faɗin "Ni ko yana ja a kasa ma ni sai na sa" shi dai daddy sai murmushi yake abun sa burin sa ya cika tun da Rimsha da Jehan sun yi murna, wuce wa ita ma Rimsha tayi ta nufi bedroom na su da jacket ɗin sanye a jikin ta wadda ya kai ma har idon sahu na kafar ta.

Fito da sauran kayan daddy yayi ya bawa gwaggo nata san nan ya bawa mum nata wadda ya kasance irin ɗaya ne dana gwaggo Dubai jallabiyas ne masu kyau da tsada, shi ma ya sai wa kan sa Dubai jallabiya na maza masu kyau da tsada, miƙewa yayi da na shi ya wuce bedroom na shi, miƙewa ita ma mum tayi tabi bayan sa, ita kuma Gwaggo ta wuce bedroom nata dan taje ta ajiye kayan.

"Washington DC*


*08:00 am*

Zaune suke gaba ɗayan su a palon kasa, Micheal, James, Jay, ko wan nen su kan shi na kan wayar sa yana latsawa yayi da shi kuma daddy yana hira da uncle Herry.

A buge John ya shigo palon kwata kwata ya manta da Romeo ya dawo, Sanye yake da Bluetooth a kunnen sa, jikin ne sa sanye da wando crazy irin na shararrun yan duniya nan, yau yayi kitso bibbiyu ta gefe da gefen kan sa, yayin da jikin sa ke sanye da t-shirt baka mai zanen horo da jan kala a gaban, hannun sa wuyar sa duk sanye suke da chain na maza masu kyau da tsada, kallo ɗaya zaka masa ka san yau a cike da iya shege yake,

taku yake ta baya baya ya shigo palon yana tafiya yana girgiza kai da jiki yana bibbiye wakar da yake ji daga ta cikin Bluetooth ɗin, kasan cewar su basa jin wakar da yake ji sai dai wanda yake bibbiyewa suke ji sai hakan ya musu ban bara koi saboda wakar yan china yake ji, shi dai Jay kallon tsantsar mahauakci ma yake masa, dan wakar da yake bi ɗin ma basu taɓa jin irin ta ba, idan yayi taku ɗaya sai ya tsaya ya tiki rawar sa iya son ransa kafin ya ci gaba da tafiya, gaba ɗayan su sun zuba musa ido suna kallon sa, ba karamin tausayi ya basu ba, dan da alama yau wine ɗin nasa tasa ya manta da Romeo ya dawo, shi ko ko ajikin sa dan daman mayen son rawa da waka ne kamar Michael Jackson, kai tsaye saman bene ya nufa ko kallon in da suke bai yi ba.

Dai dai lokacin Romeo ya fito daga part na shi jikin sa sanye da wando jeans guntu zuwa gwiwar sa sai riga fara mara nauyi mai karamar hannu, yau ma kamar kullun ya ɗaure dark black curly hair sa da ta sha gyara sosai sai kyalli da kamshi take, ya ɗaure ta a bayan sa, kaɗan ya zubo masa ta gaba goshin sa kasan cewar gashin gaban goshin nasa ya ɗan yanke ta bata kai tsawon na bayan sa ba, hakan yasa bata iya kai wa ya haɗa da ita ya ɗaure shi yasa ko ya ɗaure gashin na shin nasa wan nan na gaban goshin bata shiga ya ɗaure da ita sai ta zubo masa a kyakkyawar face na shi, hakan kuma ba karamin kyau yake kara face na shi ba, kamar kullun yau ma a koi face mask a face nashi, wan nan daddaɗar fitinanniyar kamshin perfume nashi ne ya kai wa su Michael karo a hanci hakan ya sasu ɗagowa a sukwane kuma a tare har da su daddy, dan ko ina kamshin perfume ɗin ya gauraye gaba ɗaya duk girman palon, tun ma bai shigo cikin palon ba

a sukwane su Michael suka kara nitsuwa kowa ya ajiye wayar sa dake hannun sa suka zubawa John dake rawa yana tafiya yana tinkarar Romeo dake kokarin sauko wa kasa, ganin John na zuwa a buge yasa Romeo tsayuwa ya zuba masa dara daran blue eyes na shin masu ɗaukan hankali nan yana kallon sa, duk wata halitta mai rai dake cikin palon sai da ta nitsu tsit ka ke ji ko numfashi a hankali suke fitar wa dan gudun shiga matsala, shi ko John sai kaɗan kai da hannu yake yana tafiya yana wani bouncing, ya sanya hannun sa ɗaya ya rinƙo wandon sa ta tsakiya dai dai sai tin gaban sa irin yadda gayu keyi, zuba masa ido gaba ɗaya palon suka yi yayin da shima Romeo ya zuba masa ido yana kallon gudun ruwan sa

John bai an kara ba sai ji yayi ya daki kirjin mutun sai da yayi baya yayi tangal tangal ya faɗi kasa, a sukwane ya ɗago kai cikin muryan yan maye yace "Who is this?" kara waro ido sa waje yayi yana kallon Romeo, sai dai kash saboda shaye shayen da yayi ta sa bai gane ko wanene a wajen ba hakan yasa ya ja dogon tsaki tare da banko uban ashar yana kokarin miƙewa

Raɓawa ta gefen sa Romeo yayi a nitse ya nufi hanyar fita ba tare da yace komai ba, har su James suna haɗa baki wajen cewa "Good morning Lion" jinjina musu kai yayi ba tare da yayi magana ba, ya wuce ya nufi waje

dai dai lokacin Tga ya sauko daga saman benen shima face na shi sanye da face mask san nan kayan jikin sa kusan iri ɗaya da na Romeo, dai dai tsakiyar palon ya tsaya ya kalli su daddy cikin harshen turanci yace "Good morning daddy and uncle" da murna daddy da uncle Herry suka amsa masa, san nan suma su Micheal suka gai da shi a ta kaice ya amsa musu san nan ya nufi waje yabi bayan Romeo

har ya kai bakin kofa ba tare da ya juyo ba yace "I want to see all of you know in my place, excluding uncle and dad, James come with John" ya kai karshen maganar ya fice daga palon

tun da sukaji Tga yace su sa me sa a wan nan filin, jikin su ya fara kerma dan sun san shike nan horasu zai yi, dan wan nan fili daɗi baya kai mutun sai wahala, filline gari guda da Romeo ya saya kusa da gidan su wajen yake daga gidan su ta baya a koi kofa ta wajen zaka buɗe ka shi ga wajen, Musamman Romeo ya sayi fillin yasa a ka kawata masa wajen dan ya rinƙa basu horo a wajen,

da sauri Michael, Jay, suka rufawa Tga baya, shi kuma James ya wuce yaje ya damko wuyar rigar John ya jawo sa suka nufi waje, sai zagi da sambatu John ke tayi amma James bai kula sa ba, komawa daddy da Uncle sukayi suka zauna, suna masu tausayawa John.

Filline mai girman gaske an kawata wajen, ga wasu kyawawan kujeru a saman stair an sanya kyakkyawar runfa a wajen kujerun, kamar dai wajen hutawa, an raba wajen gida biyu rabi an sanya masu tiles, rabi kuma an sanya grass carpet mai kyau, fillin bai da faɗi sosai sai tsawon bala'i.

Zaune saman sofa mai laushi ga kyau Tga ya isko Romeo zaune yana latsa wayar sa, kusa da shi Tga yaje ya zauna, cikin girmamawa yace "Good morning Lion" shiru Romeo ya ɗan yi na yan mintoci, kafin ya ɗago kan sa daga kan wayar sa, ya sanya kyakkyawan farin hannun sa gently ya zame face mask ɗin face na shi zuwa gemun sa, Subhanallah tsarki ya tabbata ga Ubangiji da yayi wan nan hallitar,

kyakkyawa ne ajin farko, yana da face mai design mai kyau, ga dogon hanci har baka mai matikar kyau, soft skin na shi ba'a magana, kwance yake luf yaji hutu, bakin sa ɗan karami mai ɗauke da lips red color kamar ya sanya lipstick ja saboda kyau, idon sa kuwa kamar ya kara musu girma ne da ya cire first mask ɗin, dan har wani kyalli suka kara yi, gashin gerar san nan kamar an zana masa Calvin san nan suna cike dan kamar zasu haɗe saboda cikan kyakkyawar dark black gashin dake wajen, gefe da gefe kumatun sa dukka kyakkyawar dark black gashi ne kwan ce a wajen sai sheƙi da kyalli yake, kyau iya kyau kamar shi yayi kan sa Masha Allah.

Slowly ya lumshe dara daran blue eyes ɗin nasa ya sake buɗe, tare da ɗagawa Tga kai ba tare da yayi magana ba, dai dai lokacin su Michael suka shigo wajen, slowly ya dawo da kallon sa kan su, sai sambatu John ke yi kamar zararre,

A gaban su Tga James yazo ya durkusar da John, ya wuce ya zauna saman sofa, suma su Micheal wuce wa sukayi suka zauna saman sofa, John na kokarin miƙewa sai sambatu yake, slowly Romeo ya juyo da dara daran blue eyes na shi ya kalli Tga ba tare da yayi magana ba

Da sauri Tga ya miƙe ya damko wuyar John tare da ware yatsun hannun sa kamar mai zagi, ya ɗaga hannun sama da karfi ya cakawa John yatsun nasa a cikin sa kusa da cibiyar sa, nan take John ya fara kwara amai, yana tari, kara caka masa yatsun nasa Tga yayi a karo na biyu, sosai John ke tari yana sheƙa amai, ganin yana amayar da wine ɗin ne yasa Tga ya sake sa ya koma kusa da Romeo ya zauna, yana kallon John ɗin , yayin da shi kuma Romeo ya miƙe gently ya taka stair ɗin ya sauƙo kasa ya nufi wata yar siririyar hanya dake cikin fillin.

Sai da John ya amayar da gaba ɗaya wine ɗin da ya sha san nan ya kwanta a wajen na yan mintoci yana mai da numfashi, kafin ya ɗago kai yana kallon jama'ar dake wajen, while Tga ya sunkuyar da kan sa kasa yana latsa wayar Romeo da ya tashi ya bari a wajen, ihu John ya fasa lokacin da idon sa suka sauka kan Tga dan a tunanin sa Romeo ne, kasan cewar Tga ya sunkuyar da kai kasa, baka ganin kwayar idon sa

jin ihun John yasa Tga ɗago kai, yana kallon sa, miƙewa zaune John yayi ya fara kuka, dan da Tga da Romeo duk mugun tar su kusan ɗaya, dan mafiyawanci lokaci ma Tga ke hukun ta masu laifi, shi Romeo sai idan abun yayi yawa yake sa bakin sa, bai cika shiga har kan su ba, amma dai idan ka kuskura ya damke ka tofa in ba kayi Sa'a ba sai na lahira ya fika jin daɗi, haka shima James ya kware wajen iya hora mutane ya iya mugun ta kamar Tga.

Jibga jibgan Bodyguard biyu ne suka zo suka fara gyara wajen da John yayi amai, sai bayan sun gyare wajen tsab har da perfume suka sa, nan take wajen ya ɗau kamshi sosai, sai da suka gama san nan Romeo ya dawo wajen.

In da ya tashi ya koma ya zauna tare da mai da face mask na face na shi, Tga na kokarin yin magana, bodyguard huɗu suka fito da manya manyan dawaki guda uku masu lafiya da ji da karfi, sun ci sun koshi sun samu kiwo mai kyau, sai daka sukuwa suke,

daga farkon in da a ka sanya grass carpet ɗin nan bodyguard ɗin suka tsai da dawakin ba tare da sun saki linzamin su ba, kallon John Tga yayi a ta kai ce yace "Get ready" in da sabo John ya saba dan wan nan ɗaya ne daga cikin salon hukuncin Tga da Romeo, basu cika bugun mutun ba sai ta kama dole amma horo kala kala na mugunta sun iya

kallon John ɗin James yayi kafin yace "Ko dai wine ɗin bata sake ka bane? Na ga ka kasa tashi kamar ba da kai a ke magana ba, ko dai sai nazo nayi nawa ne?!!" A hankali John ya miƙe dan wine ɗin ta sake sa tsab kamar ma bai sha ba, kasa ya sauko ya tsaya wajen da a ka sanya tiles while su kuma dawakin suna ɗan gefe wajen grass carpet

counting from one to three Tga yayi, yana kai wa three bodyguard ɗin suka saki linzamin dawakin, yayin da shi kuma John ya kwasa a guje, suma dawakin sukuwa sukayi kafin su fara gudu, dam, dam, dam, kallo ɗaya zaka yiwa dawakin kasan a kan hakan a ka horasu, ka ida shi ne idan ka bari dawakin nan ɗaya ya wuce ka sai ka karɓi hukunci mai tsanani, wan nan ɗaya ne daga cikin punishment da Romeo ke musu.

Sosai John ke gudu kamar zai tashi sama, ga tsantsin tiles kamar zai faɗi kasa, gashi ba halin cire ta kalma, dan yana ɗan tsayawa dawakin nan dazu wuce sa, duk da yasan daman dole zasu wuce sa dan ba wanda ya taɓa cin wan nan jarabawar ta Romeo amma duk da haka zagewa suke suta sharara gudu kamar zasu tashi sama, haka suma dawakin suke sharara gudu dan sun san gasa ce, John dai yana gudu yana kuka, sai dariya Jay ke masa yana masa mugun addu'a dan daman rashin kunyar John da Michael ya ishe sa a gidan

"Where is your exam card Michael?" Cewar Tga, kallon Romeo Michael yayi kafin yace "I already discussed this issue with lion" kallon Romeo Tga yayi, yana faɗin "is that so?" Jinjina masa kai Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, yana latsar wayar sa

"Okey what about James, it's better for him to start work?"Jay ne ya ansa zancen da cewa "Gaskiya is better, dan ya kammala karatu ba shi da aiki sai zuwa clubs da partys" girgiza kai Romeo yayi gently ya miƙe ya nufi hanyar sauka daga wajen cikin nitsuwa da sexy voice na shin nan yace "I will think about it" yana kai karshen maganar ya fice daga wajen,

Romeo ko mai na shi a nitse yake yin sa, san nan komai daki daki yake bin sa ɗaya bayan ɗaya, baya son hargagi da rashin nitsuwa a lamuran sa, bai taɓa damuwa da yan uwan sa sai sun yi aiki ba, shi a ganin sa dukiyar sa ya ishe su da suji daɗin duniyar su, shi yasa yake sake musu kuɗi baya damuwa da lallai sai ya san abun da suke saboda ya yarda da su, a baya kafin yanzu baya basu kuɗi sosai lokacin da James ke School wan nan dalilin yasa James ya shiga wan nan har kan, daga baya bayan ya kammala school Romeo ya fara sake musu kuɗi over dan a cewar sa yanzu sun yi hankali, bai taɓa bibiyar su ko bincikan su dan yaga me suke ba, dan ya basu yarda 100, yana bala'i son su fiye da tunanin mai tunani, amma duk da wan nan son da yake musu baya hanawa ya basu horo idan suka masa ba dai dai ba, duk cikin yan uwan sa yafi son Michael hakan yasa ko Michael yayi laifi baya iya hukun ta shi dan yana kaunar sa over, bai taɓa hora Michael ba, idan Michael yayi laifi a gaban kowa, kowa yaga yayi laifin kuma sun san yayi laifin, sai Romeo ya fiske yace Tga ya hukun tashi ko kuma James, gaba ɗayan su daga James ɗin har Tga ɗin basa iya hukun ta Michael ɗin saboda son da suke masa, shi yasa Michael ke zuba tsiyar sa iya son ran sa, yanzu haka jiya da daddare yaje ya samu Romeo ya rinƙa zuba masa kukan shagwaɓa yana rokan sa da yayi hakuri a kan bai rubuta Exam ba amma next time yayi alƙawarin zai rubuta, sosai Romeo ya masa faɗa a kan ya tsaya yayi karatu, amma ya kasa hukun ta shi, su uncle Herry duk sun fi kaunar Michael fiye da kowa, sosai Romeo ke sakar masa kuɗi yana abun da ya ga dama, sai dai yana da kyau ta over da mutun ya roke sa zai bada, abokan sa su dest duk ya sai musu motocin hawa, a School na su kowa ya san shi da kyauta idan ka cire tsoro kazo ka tambaye sa tofa zai baka abun da ma baka taɓa zato ba, haka zalika duk kuɗin nan da Romeo ke bashi hakan bai sa ya nemi matan ban za ba, shi mace ma bata gaban sa, saboda gani yake halin su ɗaya da mum ɗin sa, a baya yana shaye shaye daga baya yazo ya dai na saboda wani friend na shi dake hana shi, kuma yana kaunar abokin nasa over, duk sati yana zuwa gidan gajiyayyu da marayu ya ta raba musu abubuwa kamar dai yadda yaga Romeo na yi, sai dai shi Romeo har da church ɗin su yake bawa taimako shi kuma Michael saboda tsanar da yayi wa Pasto church ɗin ma sai an yi da gaske yake zuwa kuma baya bawa Pasto ko biyar, idan yaje church ɗin ma baya sauraron komai da suke faɗe, saboda gani yake ba amfani, dan bai da ilimi ba karatu yayi ba shi gani yake ɓata masa lokaci kawai suke da surutun banza, kan sa emty yake duk mate na shi a School wasu sun zama lectures wasu kuma sun kama aikin yi amma shi yana nan sai jagaliyanci ya sa a gaba, wan nan dalilin ne yasa ba abun da ya sani sai kashe kuɗi da zuwa party clubs da abokan sa, hakan yasa yake kallon Pasto a matsayin mahaukaci mara aikin yi, shi kwanta kwata bai yarda da wasu addinai ba a cewar sa duk adinin nan ɓata lokaci ne.

Bari mu leƙa Nigeria mu dawo


*KADUNA*

Har bakin hanya Rufaidat ta rako Aafia sai murna take tana zuba mata godiya, ita kuma Aafia sai fatan alkhari take wa Rufaidat da fatan ta tsaya tayi karatu da kyau, dan karatu shi ne mutun, anguwar nasu shiru ba hayani sosai, shi kan shi bakin hanyar ba jama'a sosai, kafa ta ɗauke saboda ba babban hanya bane, irin kana nan titin nan ne dake ratsawa ta cikin layi

suna tsaye a bakin hanya suna jiran taxi yazo Aafia ta hau ta koma gida, wata dankareriyar mota kirar *Mercedes-Benz* tazo tayi parking a gaban su, a hankali mamallakin motar ya sauke glass ɗin motar sa, babban Alajine mai ɗan yawan shekaru, dan a kalla zai kai, 45 to 47 years, sanye yake cikin manyan kayan hausawa da hula, yayi shiga irin ta kamala da cikar bahaushe, nan take Aafia ta ɗaure fuska kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, ita kuma Rufaidat sai washe baki take an ga mai kuɗi.

"Sannun ku yan mata" Alhajin ya faɗa yana washe baki, cikin sauri Rufee tace "Yauwa Alhaji Sannun ka" ita kuwa Aafia ko kallon in da yake ba tayi ba dan a koi ta da jiji da kai over "Yan mata idan ba damuwa ku shigo na kai ku in da zaku je mana, dan baku yi kalar tsayuwa cikin ranar nan ba" yana magana yana kallon Aafia, kara washe baki Rufee tayi tace "Kawata ce kaɗai zata tafi ita zaka ragewa hanya ni kuma ga gidan mu a nan idan ka dawo" a sukwane Aafia ta juyo tana kallon Rufee da mamaki, wato ita rufe har tallan kan ta take, shi kuwa Alhaji washe baki yayi tare da shafa gemun sa yana faɗin "Daman ai kawar taki ita ta tsai dani" hannu Aafia ta miƙawa Rufee suka gaisa, san nan tace "Sai kin zo gida ko sai mun haɗu ga taxi nan zuwa na wuce"

"Wow gaskiya izzar ki ya kara burgeni ba kaɗan ba, hakan ya sa naji na kara son ki" cewar Alhaji, ita kuwa Aafia wucewa tayi abun ta, ta tari taxi ɗin da yazo ta shiga, cikin sauri Alhaji ya buɗe motar ya fito waje ya nufi wajen taxi ɗin yana faɗin "Dakata malam, haba yan mata, dan Allah ki tsaya mana, minti biyu kawai nake bukata daga gareki" a kule Aafia tace "Kai malam ko in ce baba, kai baka ji kunyar tare

Please Login or Register in order to submit comment