Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajen mum da dad na sa bai da wani ɗan uwa i think yana using eye contact ne" mum ce ta ansa zancen da cewa "Ni ma tun da jimawa nake son mata wan nan tambaya ban samu dama ba amma fa dukka idon da light blue da light ash ɗin duk suna masa kyau sosai" da sauri Rimsha tace "A'a mum light blue nan yafi masa kyau idan ya sanya ta zaki ganshi idan ya ɗago idon nasa har wani kyalli take kamar madubi, tana ɗaukan hankali idan kikaga idon nasa zaki yi tunanin light ash ne amma kuma light blue ne ni kasa ganewa ma nake har sai ya ɗaga idon nasa ko yana kallon mutun ko yana kallon wani abu a nan ne nake iya gane light blue ne amma idan kika gan shi at the first time zaki yi tunanin light ash ne" ta kai karshen maganar tare da miƙa wa ta nufi bene tana faɗin "Mum an gama shirin dan shi baya wuce 15mins yake badawa a cikin time na sa, yace kowani second a rayuwar sa tana da matukar muhimmanci" girgiza kai kawai mum tayi tana mamaki irin kaunar wan nan Christan da Rimsha keyi, mutumin da bai san hanyar Nigeria ba ma amma ita tana nan tana fama da kaunar kallon face na shi da labarai a kan sa.

💞💞💞💞💞💞💞💞

*UNITED STATES OF AMERICA*

*WASHINGTON DC*

*HARVARD UNIVERSITY*


*Allotment garden*

Babban filine mai girman plot 10 filli ne mai matikar kyau da kawatuwa, wajen cike yake da shuke shuke kanana kanana da manya manyan flowers masu bala'i kyau da ɗaukan hankali launin yellow da kore, wani wajen an yi design of heart da flowers wani wajen kuma an rubuta Harvard University, daga bakin katafaren gate ɗin shigowa an rubuta Welcome to *Allotment garden* da flowers kore da yellow an kawata wajen sosai da sosai gwanin ban sha'awa sai kamshin furanni ke tashi a wajen, gaba ɗaya garden ɗin shinfiɗe yake da wasu kanana ƙanana grass masu bala'i kyau kai kace grass carpet ne a shifiɗe a wajen ga wasu Gumaka da a ka kawata su suna zubar da ruwa, ƙatuwar Giwa a ka gina ta a tsakiyar wajen ta ɗaga hancin ta sama ruwa na zuba ta kofar hancin nata kasan ta kuma an kewaye shi kamar rujiya ruwan na taruwa a wajen daga gefen Giwa ga kuma maciji shima ya ɗaga kai yana fesa ruwa daga bakin sa, ko ta ina ka zaga a wajen fitullune masu haske gaske ke haske wajen ga wasu tamtsama tamtsaman kujeru na alfarma masu numfashi, launin Milk color cike a wajen, daga karshe karshen ginin dogayen bishiyoyi ne masu ganye ja da kuma yellow, Allotment garden ya kawatu iya kawatu wa,
duk girman wajen shiru babu mutane sai wani haɗaɗen Bature dake zaune saman sofa fari tas da shi jikin nan nasa ka rantse da Allah bai taɓa taka kasa ba saboda laushe da kyau gashi a kwance luwai luwai Kyakkyawan farin matashi ne mai jini a jika, sosai yake da hasken fata da kallo ɗaya zaka masa kasan asalin 𝑩𝒂𝒕𝒖𝒓𝒆 ne, dogone cikakken namiji, yana da faffaɗan kirji da yasa muscles ɗinsa Fito wa sosai cikin baƙar top din Salvatore ferragamo da ya Fito da kakkarfar farar surar jikinsa, kyakkyawan fuskarsa ɗauke take da dogon hancin da ya ƙara wa fuskarsa kyau, ɗan karamin bakinsa ɗauke yake da kyakkyawan laɓɓa dark purple da yayi wa karamin bakinsa kawanya , a hankali ya ɗago da dara daran eyes dinsa masu shegen kyau kamar yasa musu kwalli, kwayar idanuwansa da ta kasance light brown mai ɗaukar ido, idan kayiwa idon na shi kallo a fusge sai kaga kamar idon damisa (tiger) a hankali ya fara motsa idanuwansa dogayan eye Lashes dinsa suka kara fitowa sosai , daga saman idanunsa kuwa sosai girarsa take a cike da taso haɗewa sabida cikarta, gefe da gefen fuskar sa duk gargasar gashi ne da yasha gyara, kyakkyawar dark brown hair sa har gadon bayan sa ya kai masa sai curly gashin kan nasa keyi, zaune yake shiru fuskar nan tasa a ɗaure take tamau kamar bai san me dariya ba, daga gefen da gefen sa wasu mahaukatan karnuka ne jibga jibga guda uku masu gashi sosai a jiki, biyu daga cikin su farare ne kal ɗayan kuma ja gashin jikin su har ja yake a ƙasa saboda yawa manaya manya ne sosai karnukan sun samu kiwo nai kyau. Wan na shi ne *Michel*

wasu matasan Turawa ne su uku suka shigo wajen suna tafiya suna kwaɓe fuska kusa da Michel suka zauna, ɗaya daga cikin su yasa hannu yana shafa gashin jikin karen dake kusa da shi,

cikin harshen turanci Michel yace "Dest me ya tsayar da ku sai yanzu kuka zo?" Guntun tsaki Dest ya ja kafin yace "Wan nan ban zan uncle da a ka kawo sabon nan ne mana wai yaji labarin mune marasa ji a School nan dan haka zai sa mana ido kullun idan yazo mana lecture bai gammu a class ba sai ya hukun tamu" dogon tsaki Michel yaja ba tare da ya sake magana ba "Michel muje mu sha giya ko? Ina jin yinwa" Cewar ɗayan dake daune ta ɗayan ɓangaren Michel ɗin, ata kai ce Michel yace "As from Today na dai na shan wine" waro ido waje Dest yayi kafin yace "Michel kana jin me kace kuma? Ka dai na shan giya?" Shiru Michel yayi bai sake magana ba, a ƙule Johnson ya buɗe baki zai fara magana kenan wani Bature ya shigo wajen jikin sa sanye da suit kallo ɗaya zaka masa kasan lecturer ne, miƙewa tsaye gaba ɗaya guys ɗin suka yi amma ban da Michel dake zaune kamar bai da mutumin a wajen ba, kasa da murya Johnson yayi dai dai sai tin kunnen Michel yace "Wan nan shine sabon teacher'n shi bai san mu ba zai iya sanar da Romeo idan muka masa taurin kai" kallon sama da katsa Michel yayiwa Johnson kafin ya mai do da kallon sa kan uncle ɗin dake tsaye yana musu kallon tuhuma kasa kasa Michel yace "Romeo baya kasar nan tun jiya" bai karisa rufe baki ba uncle ɗin ya daka musu tsawa "Kai dest dana ce kuje ku zauna kuyi karatu shi ne kuka zo kuka zauna a nan kuna shirme ko? To yau zaku yi bayani, ba kunce ku baku ji ba tun da na shigo makarantar nan ko wani malami sai yace min kar na shiga har kan ku kuna da haɗari, ku gaku tantirai to nima tsohon ɗan daba ne kafin daga baya na ajiye dabanci na rungumi bairo da takarda, ku fara frog jump daga wajen da kuke, yau sai kun kewaye min garden ɗin nan sau hamsin" ya kai karshen maganar tare da dawo da kallon sa kan Michel yace "Kai ne ogan su ko to naka hukunci daban ne kukace ku yan iskan gari ba?, ba zaku yi karatu ba sai dai ku zauna kuna jagaliyanci ku addabi masu karatu parents naku na kashe makudan dukiya a banza, to ni zan gyara muku zama" duk wan nan magana da su cikin harshen turanci suke yin sa, ganin wan nan uncle ɗin ba zai dai na wan nan surfa uwar masifa da yake bane gashi ya toshe masa kunne yana da mun sa yasa Michel ɗin ya miƙe tsaye tare da shafa kan ɗaya daga cikin jibga jibgan karnukan sa kasa kasa a sai tin kunnen karen yace cikin harshen turanci "Lucky ko ya masa hankali" ya kai karshen maganar tare da komawa ya zauna saman sofa ɗin,

dirowa kasa lucky yayi tare da girgiza jikin sa wani jibgege da shi ya ɗaga wuyan sa sama ya fara takowa a hankali hankali ya nufi uncle, baya baya uncle ya fara ja yana faɗin "Ku dakatar da karan nan" kamar jira lucky yake uncle yayi magana ya rufa masa, a guje uncle ya juya yana ihu, da ɗan ma dai dai cin gudu lucky ya bi bayan sa ta yadda ba zai kama sa ba zai kuma hawalar da shi, kwashewa da dariya su Johnson suka yi suna faɗin "New uncle ma ya shiga layi" suka kai karshe maganar tare da tafa hannu shi dai Michel yana zaune shiru,

Shi kuwa uncle gudu yake kamar zai tashi sama yana ihu a kawo masa ɗauki amma ina duk in da yazo wucewa sai student sun tashi sun gudu dan sun san halin lucky duk wan da ya kwana ya tashi a Harvard University to yasan da zaman Lucky da Winston Copper karnukan nan bala'i ne basu da mutunci gashi sun samu horo da kyau wajen Michel, duk abun da Michel ɗin yace suyi shi suke idan yace su rikita mutun zasu bi mutun amma ba da gudu sosai yadda zasu kama mutumin ba sai su bishi da gudu kaɗan kaɗan dan su galabaitar da mutun san nan duk in da ka shiga sai sun bika ba wanda ya isa ya raba ka da su sai shi Michel ɗin da ya haɗa ka da su,

Tsabar gudun da uncle yake har sai da wandon sa ta cire ya rage daga shi sai Short sai uban zufa yake yana ihu yana neman tai mako,

a guje ya shiga Harvard Community garden wajen cike yake da student, ganin uncle da gudu yana ihu ga kuma lucky na bin sa a baya ne yasa gaba ɗaya student ɗin suka fara gudun cetan kan su suma,

uncle dai yanzu karfin sa ta fara karewa ya rage gudu daker yake nishi girgiza jiki Lucky yayi tare da yin haushi mai firgita kwakwalwa nan take uncle ya ji sabon karfi yazo masa ya kara kwasawa a guje ya nufi wajen garden ɗin yana ihu kamar mahaukaci,

a guje ya shiga wajen Harvard swimming pool dake kusa da goro place watermelon, manya manyan swimming pools ne a wajen wadda a kalla zasu kai 20 an kawata wajen sosai da sosai,

a sukwane uncle ya faɗa cikin pool ɗaya, a tunanin sa ya tsira sai nishi yake sama sama kamar zai mutu, lucky na shigowa wajen shi ma ya faɗa cikin ruwa ihu uncle ya fasa tare da fita a sukwane jikin sa duk ruwa tsantsin tiles ya kwashe shi ya faɗin ƙasa ya buga kai a tiles, rage gudu lucky yayi har sai da uncle ya miƙe ya ci gaba da gudu san nan shi ma lucky ya rufa masa baya.

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu shin ya uncle zai ƙare da *Lucky* wayyo ni *Princess Teema* Michel na sha'anin sa 🤣🤣🤣🤣🤣

💞Star Lady💞

*💞TRIPLET'💞




*💞The beginning💞*


*Episode 9*


.....Idan uncle yayi kamar zai tsaya sai Lucky ya girgiza jikin sa yayi haushi mai rikita ƙwaƙwalwa, uncle kuma da yaji haka sai yayi tsammanin lucky ya kusa kama shi ne sai ya daure ya kara karfin gudun nasa, gaba ɗaya student da ke ganin halin da uncle ke ciki sun tausaya masa ba kaɗan ba dan ya fara manya ta a kalla zai kai 45 years ba yaro bane, ga abun dariya ga kuma abun tausayi,

Shi kuwa Michel yana zaune hankalin sa kwance,
kallon sa test yayi cikin muryan neman alfarma yace "Please Michel ku ɗauke ni aiki mana a gidan ku koda goge muku takalma ne idan zaku fita ina son in ganni dai na zauna a cikin gidan ku" shiru Michel ya ɗan yi kafin yace "Babu wan da ya isa ya kawo wani Mai aiki gidan mu idan ba Romeo ba shi kaɗai yake iya ɗaukan masu aikin da yake so, ko daddy bai isa yace ya ɗauko mai aiki ba kuma shi Romeo kafin ya ɗauki mai aiki yana da doka, dokar kuwa itace idan har yaga ka dace ya ɗauke ka aiki tofa zaku yi agreement da shi ne zai rubuta maka takarda kasa hannu misali idan zai ɗauke ka aiki zai faɗa maka aikin wata kaza ko Shekara kaza zaka masa idan ka amin ce to zai rubuta maka takarda kasa hannu, idan kuma kasa hannu tofa ka sani komai zai faru sai ka cika adadin shekarun da kukayi da shi ko da baban kane ya mutu a ranar sai kazo aiki baka da wani iko da kan ka sai abun da yace kayi kuma shi aikin sa bata da time ko wani lokaci yana iya saka aiki koda cikin dare ne, babu wan da ya isa ya tinkari Romeo yace ya ɗaga maka kafa, ko daddy ka sani tsoron sa yake, kuma mu ai kasani dukka gidan mu sojoji ne masu aiki har abinci sojoji su ke girkawa wan nan tsarin Romeo ne" "please Michel ka ɗan roƙe sa mana ya ɗauke ni ko da mai goge muku takalma ne" kallon sama da kasa Michel ya masa kafin yace "Ko daddy bai isa ya ce da Romeo ga abun da zai yi ba shifa abun da ya ga dama yake, kai mutun ma ya isa ya tinkare sa yace masa yayi wani abun hmmm ka tambayi Johnson ya faɗa maka, kai bama sai an faɗa maka ba ni zan baka 1 million $ idan ka iya tinkarar Romeo ka gaida shi ma kawai" ya kai karshen maganar tare da miƙa wa ya bar wajen cikin sauri dest da test da John ɗin suka rufa masa baya, da sauri karnukan sa biyu Winston da Copper suka diro kasa tare da girgiza jikin su wasu jibga jibga da su cikin takun ƙasaita suka rufa masa baya,

A ɓangaren uncle kuwa kasa cigaba da guduwa yayi ya zube kasa a dai dai Allston dake kusa da hanyar tafiya community garden, ya kasa ci gaba da numfashi, numfashi ta masa wahalar jawuwa hakan yasa numfashin sa ta ɗauke ya sume, da guduwa Lucky ya kariso kansa yana kokarin kai masa cizo a kafa Michel da ya iso wajen yanzu yace "Wait Lucky" ba musu lucky ya tsaya tare da juyawa da gudu ya koma wajen Michel ɗin shafa kan sa Michel yayi kafin ya juya ya bar wajen Lucky Winston Copper suka sufa masa baya san nan su dest suka rufawa su lucky baya,

Su Michel na tafiya sauran uncle's ɗin suka zo suka ɗauki uncle dake sume suna ta masifa "da ma ai mun faɗa maka karka shiga sabgar wayan nan kaƙi yanzu gashi kaji a jikin ka ai" haka sukayi ta surfa masifa har suka wuce da shi cikin *(HUHS) Harvard University Health Services*

Shi kuwa Michel kai tsaye ya wuce *Harvard Square Parking Garage* yaje ya shiga dankareriyar motar sa kirar *Aston Martin* a guje Winston Copper suka shiga gidan baya shi kuma Lucky ya shiga gidan gaba, Johnson ma wucewa yayi ya shiga motar sa, kuɗi Michel ya ɗebo dollars ya miƙawa su dest yana faɗin "Kai test zaka iya zuwa ka gaida Romeo ne gobe na zo maka da kuɗin ka cash 1 million dollars zan baka idan ma sun maka kaɗan zan karama" cikin sauri test yace "A'a ni nama fasa batun aikin ai" turɓune fuska Michel yayi kafin ya miƙa musu kuɗin hannun sa yana faɗin "See you next time guy's" ba musu dest da test suka ansa kuɗi, Michel ya kunna motar sa da gudun gaske ya figeta ya bar School ɗin dama shi Johnson tun isowar su parking space ɗin yaja motar sa bai tsaya wani magana ba, su ma dest da test kowa ya shiga motar sa ya wuce gida dan yau ba zama a School sun san sunyi tsiya kar aje a faɗa wa daddyn su gwara shi Machel shi da Johnson ba mai karfin gwiwar iya nufan hanyar gidan su ma bare ya kai karan su.

John wadda kuka fi sani da Johnson ɗane ga uncle ɗin su Romeo, mai suna uncle herry a gidan su Michel ɗin yake da zama da shi da ɗan uwan sa jay.

Gudu sosai Machel ke shararawa a kan makekiyar titin *beach drive* duk motar da tazo sai dai ta kauce ta bashi hanya ba dai shi ya kauce ba, mutane na girmama shi saboda tambarin dake gaban bambam motar sa wadda a ka rubuta *William jacop Family* saboda wan nan suna yasa suke kaucewa su bashi hanya,


*Washington DC*

Birni ne mai matukar kyau da ɗaukan hankali kuma shi ne babban birnin Usa gaba ɗaya garine na manya manyan masu kuɗi ta duniya, garine mai cike da dogayen gine gine na alfarma ga wurare daban daban na wasanni da kayatar da ɗan adam, duk ta in da ka juya irin wayen nan kyawawan jirgin kasa na masu shiga har cikin anguwa nan ne (Portland train) ma su kama da luckgerious bus, ko wani bakin titi zaka samu kyawawan kujerun zama wadda passenger zai zauna ya jira jirgin kasa ko Asalin Bus, kowani wajen da kujera yake an sanya masa runfa mai matukar kyau saboda ruwan sama kowa harkan gaban sa kawai yake ba ruwan wani da wani, *Washington DC* garin ya haɗu ta ko ina ya kayatar matuka, kawatuwar sa ba zai faɗu a baki ba,

Sosai Michael ya kunna kiɗar sa ya kure volume yana sharara gudu yana kaɗa kai su lucky na tayasa,
cikin kankanin lokaci ya iso katafaren unguwar su mai suna *lot 33*, anguwa ce ta manya manyan masu kuɗi da masu mulki ma'ana yan siyasa da sarakuna, ko ta ina a anguwar the most billion dollars gidaje ne a wajen wata gidan ma idan ka ganta kace da gold a kayi ta, anguwar tsab tsab take babu alamar datti ko kaɗan kamar mutane basa rayuwa a waje saboda hasken da tsabtar unguwar tayi, har kan titi babu alamar datti ko kaɗan duk wani lungu da sako na anguwar titi ne mai matukar kyau shifiɗe har bakin kofar gidaje, gaba ɗaya gidajen dake wajen babu hawa 2 daga uku yayi sama dogayen gini ne sosai a unguwar kai dagani ba tambaya kasan anguwar na masu shi ne.
Wata dankareriyar hanya Michel ya miƙa kai da ganin hanyar kasan ta musamman ce, kai tsaye wata aljannar duniya ya tinkara, dan wan nan gida itace aljannar duniya, tun daga nesa ya fara danna horn na motar sa,

a guje wasu jibga jibgan sojoji masu jini a jika lafiyayyu masu razana mai rai suka wangale masa tampatsetsen gate ɗin wadda da ganin gate ɗin kai kasan ba gidan wasa bane a wajen, dan haɗuwar gate ɗin gidan kawai ma abun lallo ne,

yana kari sowa wajen ya danna hancin motar sa cikin gidan ya nufi second gate sai sara masa jibga jibgan sojojin suke, in da second gate ɗin yake, kafin ka karisa wajen sai ka shiga ta wani waje kamar ɗaki wadda a ka rubuta scanning a wajen, cikin wajen yana bada wuta launin purple, wajen bai da nisa da gate 2, wajen cike yake da na'urorin da a ka haɗa su da jikin bangon wajen, san nan wajen babu kofa zaka shiga ta nan idan wajen ya gama scanning naka sai ka fita ta can haka wajen yake

ko da Michel ya isa wajen, dai dai wajen da a ka rubuta scanning place ya tsaya, yana jira, sai da na'uran dake wajen tayi scanning na motar sa tsab dan tabbatar da ba wani mugun abu a motar tasa,
bayan na'uran ta gama scanning sai da ta ɗauki 2mins san nan gate 2 yayi kara kiii kafin ya buɗe kansa da kan sa alamar motar Michel babu komai dan gate ɗin an haɗata da nauran ne idan a koi wani mugun abu a tattare da kai to gate ɗin bazata buɗe ba zatayi kara kamar jiniyar motar yan sanda su kuma jibga jibgan sojojin dake bakin gate na farko suzo su kamaka su binciki me kazo da shi yasa nauran ke kara shiyasa a gate ɗin farko a kasa sojoji na biyu kuma gate mai aiki da na'ura mai buɗe kan ta kuma ta rufe kanta.

Da gudun gaske Michel ya figi motar sa zuwa cikin gida

````Wow````

Gida ne mai girman Hectare 4 wato plot 24 kenan, gida ne gari guda, gaba ɗaya gidan har jikin bango da kasa, tiles da glass ne kai kace ginin tiles da glass ne kawai, hawa huɗu ne gidan, ginin ya tsaru iya tsaruwa ya fita iya fita ko gidan shugaban kasa albarka parking space na gidan kawai taci 3 palo san nan shi kan shi parking space ɗin a keɓe yake waje guda an sa masa katafaren gate da na'urorin da zasu wanke motar da a ka fita da ita idan an dawo, kamar ɗaki a ka gina parking space ɗin motocin ne kala kala jere a wajen,

a tsakiyar harabar gidan wani gini a kayi kamar rijiya a ka kewaye wajen san nan a kayi wanin gini a tsakiya kamar fai fai ruwa na zuba a wajen,

garden na gidan ya kai girman plot 2 cike yake da kana kanan flowers masu kamshi launin je da kore a dai dai kofar shiga garden ɗin daga ɗan gefe an rubuta *Romeo da flowers*, ga manya manyan kujeru masu numfashi na hutawa shirye a wajen, ga fitillu masu hasken gaske sun haske ko ina, gaba ɗaya garɗen ɗin kewaye yake da glass ƙasan sa kuma tiles ne wani gefen kuma grass carpet, tsayawa zayyana muku haɗuwar garden ɗin nan zai cimana lokacin sosai, wajen lambun daddy kawai yaci 2 plot, dan daddy mutun ne mai son lambu sosai, kowani ɗaki a gidan yana da balcony ta gaban sa an kawata wajen da furanni masu ɗaukan hankali, gaba ɗaya gidan kewaye yake da jibga jibgan sojojin masu jini a jika suna tsaye rike da manya manyan bindigu fuskar nan tasu kamar an aiko musu da sakon mutuwa, idan ba kana da dakakkiyar zuciya ba ka kalli face ɗin sojojin nan to zaka iya sumewa dan babu alamar annuri a face nasu ko kaɗan, kowani lungu da sako na gidan jibga jibgan sojoji ne riƙe da manya manyan bindigu kai kace wajen yaki zasu tafi, kai daganin hakan kasan ba gidan wasa kazo ba,
manya manyan swimming pools uku ne a gidan ɗaya na Romeo ne shi kaɗai ba mai zuwa wajen sai shi, biyun kuma na sauran yan gida, haɗuwar wan nan gida ba zai faɗu a baki ba dan gidan nan gari ne guda,

Kai tsaye parking space Michael ya nufa yana zuwa wajen, daga saman gate ɗin wata yar na'ura kamar yar baby ta fara karanto number motar sa daga farko har karshe san nan ta kira sunan wadda ya fita da motar, nan take gate ɗin ta buɗe kan ta, Michael ya shige, duk wani kofa na gidan sai da Romeo ya sai tata da nauran sa dan ya rinƙa samun information a kan waye ya fita waye ya shigo, ko mota zasu ɗauka sai yasan da wani mota suka fita kuma waye ya fita da motar, ko wani kofa a koi matakan tsaro a jikin ta, idan ba gate ɗin farko na shigowa gidan ba bawani waje dake da mai gadi shi ma gate ɗin farko ya bar shi ne dan criminal ya samu ya wuce gate ɗin farko ya shiga gidan, gate na biyu ya tonasa asiri, kuma ba halin guduwa sojojin dake gate na farko zasu yi ram sa shi wan nan shi ne dalilin da yasa ya bar jibga jibgan sojoji a wajen,

Michel na shigar da motar sa ya kashe ta ya fito tare da su lucky, ya danna wani waje kamar remote san nan ya fice daga wajen su lucky na biye da shi, nan take ruwa ya fara sauƙowa yana wanke masa motar tasa, a she ruwa ya danna dan ta wanke masa motar.

Yana fita ya wuce wajen ɗakin su lucky dake kusa da garɗen, ɗakin karnukan ma duniya guda ne har da katon gado a ka sanya musu kai kace ba kuɗi a ke sawa ake sayen abubuwan nan ba, yana kai su ɗakin su ya rufe su ya fito

Kai

Please Login or Register in order to submit comment