Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son magana, magana wahalan yi take masa, ga izzan bala'i idan ka masa magana sai ya dauki mintoci kafin ya amsa maka, bai son hayani, baya shiga tsabgar kowa, sannan bai yarda da kowa ba, sai Triplets na sa, da dad, su Uncle Herry, bayan su bai yarda da kowa ba, imma mace ko namiji.

Ɗaure kwalaben Michael yayi, sai famar harbin su yake da irin silent pistol gun ɗin nan, wayan nan kananan bindigun marasa karan nan.

Michael ya karan da bullet sau uku, yana kare wa yana kara wani amma ko kwalba ɗaya bai samu ya iya harba ba, saboda harbin wayan nan kwalabe ba wasa ba, sai wanda yaji training ya koshi, sai manyan jiga jigan sojoji masu saiti da kyau, Romeo na zaune yana ganin sa ta wutsiyar ido.

Wucewa James yayi har zai zauna kusa da Romeo, sai kuma ya fasa, ya nufi Michael tare da amsan gun ɗin, kwata kwata ya manta sai abun ya masa kamar wajen ta'addancin su yake, sai ta kwalaben yayi ya fara harɓi, tsabar iya saiti irin na James, kan kace me, ya fashe kwalaben nan dukkan, ba tare da yayi missing na bullet ko ɗaya ba, ba wani bullet da ya faɗi kasa ba tare da ya fasa kwalbar ba, sosai abun ya bawa Romeo mamaki, dan kuwa wanna abun da James yayi kananan sojoji basu iya yin sa, horo ne mai wahala, dan ko Tga bai jima sosai da gama iya ire-iren wayan nan horon ba, abun ya ɗan bawa Romeo mamaki, kallon tsab yayiwa James yana tunanin, a iya sanin sa dai James ko yadda ake riƙe bindiga bai iya ba, dan bai koya musu ba, gara Michael ma daman shine mai karanbanin ɗaukan kananan bindiga yace zai koyi harɓi, amma James bai taɓa ɗaukan gun ba ko da sunan wasa to tayaya ya iya harbin wayan abubuwan, kuma yayi harbin ne cike da kwarewa da kwarin gwiwa, kamar wadda ya ɗauki 10 years yana karɓan horo.

Shi kuwa Michael rungume James yayi yana turo baki a shagwaɓe yace "Why to ni na kasa harbin ko ɗaya" raba jikin su James yayi yana faɗin "Baka mai da hankali ka sanya kan ka bane amma da zaka iya ai dan ba wahala" ya kai karshen maganar tare da wucewa zai zauna kusa da Romeo, sai lokacin idon sa ya sauka kan Romeo da ya tsare sa da dara daran blue eyes nasa yana kallon su da mamaki

Nan take James ya sha jinin jikin sa, dan kuwa yasan me Romeo ke wa mamaki, kwata kwata ya macen da ina yake shiyasa ya harbe kwalaben, kuma yasan wanna horo ne mai wahala, dan sai da yayi wata biyu yana koya kafin ya iya, dan ma yana da ƙwaƙwalwa da basira shiyasa yayi saurin iyawa.

Cikin sauri ya kawar da kan sa daga kallon Romeo ya fasa zaman da zai yi ma, dan dama yazo ne ya sanar da Romeo zai je party a New York kuma ba zai dawo ba sai gobe karsu neme sa, a zahirin gaskiya kuwa Meeting na su na criminals zai je.

A nitse ya sanar da Romeo zai je party, shiru Romeo ya masa har lokacin bai ɗauke blue eyes nasa daga kan James ɗin ba, ganin haka yasa James ya sauka daga wajen ya nufi hanyar fita daga wajen yana faɗin sai ya dawo, cikin sauri Michael yace "wait for me I want to go to White House so mu fita tare kawai" shi dai Romeo ido kawai ya zuba wa James yana kokarin fahimter wani abu, tunani yake ai na James ya iya wanan harbi haka

Kasan cewar baya yi musu tambayoyi a kan abun da ya shafe su, sai yayi shiru bai tambayi James ɗin ai na ya koyi har bi ba, idan ya ga wani abun da bai masa ba a tattare dasu bincike kawai yake da kan sa gani, baya tambayar su, har suka fice daga wajen bai dai na kallon suba.

Sai bayan sun tafi da jimawa sannan ya miƙe ya bar wajen shi ma, ya koma cikin gida.

Michael kuwa, suna fita kai tsaye white house ya wuce, dan yau yace bari ya kaiwa president ziyara, tun daga bakin gate bodyguard da sojojin dake tsaron white house suka fara sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba, da wata Winter Sports Hat nasa da yansa a kan sa, saboda yawan gashin kan sa, sai hat ɗin tayi masa katuwa a kai.

Kai tsaye cikin ya wuce bai bi ta kan kowa ba, da fara'a President ya tare sa, sai turɓune fuska Micheal keyi kamar wadda aka sa shi zuwa dole, shiko president sai daɗi yake ji, saboda murna ya rasa ina zai sa Michael, saboda kaunar da yakewa GAR ne ya shafi su Michael, yana son family William jacop sosai, kasan cewar kakan su Romeo jacop Roshan babban ɗan siyasa ne kafin ya mutu, shiyasa suke da damar shiga ko ina a kasar ba wata shamaki sai ma girmamawa da suke samu daga manya manyan yan siyasa masu tasowa yanzu.

Wata dankareriyar diamond watch mai bala'i kyau da tsada president ya ɗauko ya bawa Michael kyauta, first time da Michael ya cire diamond watch na su na Triplets ba barci zai yi ko wanka ba, kuma ya cire ne dan ya sanya wanda president ya bashi, saboda ya nunawa president yaji daɗi.

Sosai president yaji daɗin abun da Michael ɗin ya masa, na cire diamond watch na su na Triplets da yayi ya sanya wadda ya ba shi, sosai agogon tayiwa Michael kyau kamar dan hannun sa a kayi ta, sanya diamond watch nasu na Triplets yayi a aljihun jacket nasa ya bar na president ɗaure a hannun sa, suka ci-gaba da hira kamar wasu friend, bayan kuma president ya kusa jika da Michael, amma saboda son da yake musu, sai ya zama kaman friend nasu idan suka zo wajen sa.

Shi kuwa James kai tsaye wajen taron su ya nufa, a in da zasu gudanar da taro cikin dajin palace, a nan zasuyi taron, manya manyan criminals uban nin gidan su James sun hallara, sun zauna sai hira suke suna jiran saukowar sauran jiga jigan ogannin nasu, sai a fara taron.

Shi kuwa Romeo yana kwance saman lallausan katafaren gadon sa, yayi kwanciyar rigingine ya tasa system a gaba yana bawa yaran sa dake shirin tafiya yaki umarni, sai faman lumshe dara daran blue eyes nasa yake kamar mai jin barci, ga daddaɗar kamshin air freshener da sanyin Ac dake ta faman tashi a bedroom ɗin nasa, gaba ɗaya wutar ɗakin nasa ya kashe farin wutar ya kunna sky blue, sky blue light ɗin ba karamin karawa ɗakin nasa kyau yayi ba, abun gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali.

A ɓangaren TGA kuwa, sosai wayan nan kwari suka masa illa, dan kuwa a kan gaban sa suka matsa wanna tsiyar, wajen ya kunbura sosai yayi jawur kamar jini ne a ciki, duk jarunta irin na soja sai da TGA yayi kuka, saboda ciwo a irin wanna waje ba karamin abu bane, yana da zafi sosai over, Allah sarki bawan Allah ko wando baya iya sawa saboda azaba, ga sanyi Ac amma duk da haka sai daddy ya kunna rechargeable fan ya kawo masa sai tin gaban nasa yana shan iska saboda azaba, shi kaɗai kwarin suka yiwa irin wanna lahani mai muni sosai haka, duk wannan hali da TGA ke ciki Romeo bashi da matsani dan yana can ya nitsa cikin aikin da yake.

Mu leƙa Jehan mu dawo

💞KATSINA💞

Yau ya kama Monday, tun 8 na safe a ka shiga da mum ɗakin da za'a mata aiki, while ita kuma Jehan ta shirya tsab cikin wata dakakkiyar atamfan ta super wax mai bala'i kyau ɗinkin riga da skit, kayan sun zauna a jikin ta sosai, sunbi shape ɗin coca colan ta sun mata ɗas, kasan cewar bata son ɗankwali ma bare hijabi hakan yasa ta ɗauki ɗan karamin Malaysian hijab ɗin ta pink color tare da takalmi pink color, ta ɗauko jakar ta suwaga shi ma pink color ta fito tsakar gida, ba karya duk da cewa fake face ne a fuskarta ba ƙaramin kyau tayi ba sai kamshin sauran perfume da ya rage mata take.

Kai tsaye kitchen ta nufa wajen maman Sadiq, suka gaisa sanna maman Sadiq ta mata addu'ar fatan fara aiki a Sa'a, yar murmushi tayi ta amsa da amin sanna ta fito daga kitchen ɗin da sauri saboda hayaki.

Tana fitowa sukayi karo da Sadiq yana kokarin shiga kitchen ɗin, ɗan baya kaɗan tayi tana faɗin "Good morning" zuba mata ido yayi yana kallon ta yana mai kara jin kaunar ta a ransa, tab lallai ita kuwa Jehan babu wani abu wai shi soyayya a ranta, bata san shi ba, kuma bata da wani ra'ayi a kan soyayya, ita da namiji da mace duk kallon abu guda take musu, namiji baya gaban ta, maza basu isshe ta kallo ba, kai har matan ma ita a wajen ta basu isshe ta kallo ba, bata taɓa kawo wani abu wai shi tunanin aure ma a rayuwar ta ba, a nata wautan har ta mutu dasu mum ɗin ta kawai zata yi rayuwa.

Ganin Sadiq ya zuba mata ido ne yasa ta raɓa gefen sa zata wuce, cikin sauri yace "Jehan dan Allah ki koma ki cire kayan nan ki sanya uniform da suka baki karki ja su hana ki aikin nan, kuma kinga dai akoi bashin kuɗin aikin mum a kanki ta wanna aikin ne kawai zaki iya biyan bashin da ake binku, to dan Allah karkiyi sanadin rabuwar ki da aikin nan kar kiyi wani kuskuren da zasu kore ki daga wanna aiki" ba tare da ta kalle sa ba, a takaice tace "I can't wear this uniform" girgiza kai Sadiq yayi kafin yace "Kiyi hakuri ki sanya jehan" cike da izza tace "Babu wanda ya isa ya zaɓa min abun da zan yi a rayuwa ta, ba zan sanya wani banza uniform nasu ba, ai ba sayata sukayi ba da zasu ce abun da suke so zanyi, ni Jehan babu wani da ya isa ya min iko da rayuwa ta bayan dad and mum, ko gwaggo lallaɓani take in tana son nayi abu, so kayan nan nayi niyar sawa babu kuma wadda ya isa ya sanya na canza" ta kai karshen maganar tare da sa kai ta nufi hanyar fita daga gidan.

Dawo da kallon sa Sadiq yayi kan maman sa dake tsaye a cikin kitchen ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah "Ina kwana mama?" Ya faɗa yana sunkuyar da kai, dan yaji kunya ashe mama na tsaye tana kallon sa yadda ya zubawa Jehan ido, da fara'a maman sa ta amsa masa.

Bayan sun gaisa ne ya mata sallama ya wuce yabi bayan Jehan, sai addu'a mama ke musu da fatan alkhari, yana amsawa da amin amin ya wuce.

A ɓangaren Jehan kuwa tana fitowa wajen gidan tayi karo da baban Sadiq yana shigowa, ko kallon in da yake ba tayi ba ta wuce, zata wuce shi ne yace "Sannun ki yarinya" yauwa kawai tace masa ta wuce tana ɗaure fuska kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, dan haka kawai taji ta tsani baban Sadiq ɗin nan bata son shi, kawai tana masa karane saboda Sadiq.

Jehan uwar dirama ta koyawa baban Sadiq da amarya hankali, yanzu amarya har gaishe da su Maman Sadiq take da safe, kuma yanzu sun ɗan samu zaman lafiya da fitinar amarya, ta daina takurawa kowa dake gidan, ta shiga hankalin ta da kyau saboda tsoron aljanu, wanna shine idan baka yi sharan masallaci ba kayi na kasuwa, duk iskancin ka akoi baban ka.

Jehan zata wuce ta nufi bakin hanya ne, sai taga Hanan zaune gaban murhun gawayin ta na tuyar awara ta kifa kai da gwiwa tana kuka, da kamar ba zata kula taba zata wuce dan ita ba mai shiga harkan mutane bane, idan kuma ka kuskuren shiga nata harkan sunan ka sorry, dan Jehan ba sauki.

Kasan cewar Hanan yarinya ce so silent bata da hayaniya kuma bata neman magana hakan yasa Jehan ta matso kusa da ita tare da dafa kafaɗar ta tana faɗin "Ke lafiya kike kuka haka?" Yar firgigit Hanan tayi tare da ɗago kan ta idon ta sunyi jawur kamar jini saboda kukan da tasha, "Subhanallah lafiya kikayi irin wannan kuka haka?" Cewar Jehan tayi maganar tana tsugunnawa kusa da Hanan ɗin, dai dai lokacin Sadiq ya fito.

Da sauri ya kariso wajen su yana faɗin "Lafiya Hanan me ya same ki?" Cikin kuka Hanan ta fara yi musu bayani "Wani Alhaji ne dake yawan zuwa wajen nan sayan awara, yaya Sadiq ba ka san shi ba? Wannan mai farar ƙatuwar motar nan?" Gyaɗa mata kai Sadiq yayi yana faɗin "Eh na san shi me ya faru? Wani abun ya miƙi ne?" Ci-gaba da magana tayi tana kuka "To daman yace yana sona kuma ni bana son shi, kullun idan yazo nan ba sayan awara yake ba, kune kuke ganin kamar awara yake saya, hira kawai yake zuwa sai in ya tashi tafiya ya bani kuɗi, to ni bana karɓan kuɗin sa, ce masa nake bana so, yayi ta haɗani da Allah naki karɓa dan ni tsoron masu kuɗin nan nake, watarana baba yazo wucewa sai yaga Alhajin yana bani kuɗi naki karɓa yana roƙana na karɓa, shine da baba ya ga haka sai yayi sauri yazo shi ya karɓe kuɗi daga hannun Alhajin ba tare da an bashi ba, ya fara washe baki yana zubawa Alhajin godiya, Alhajin ya fito zai masa faɗa akan me yana bani kuɗi shi kuma zai wani sanya hannu ya karɓa, sai nayi saurin cewa Alhajin baba nane, shine Alhajin ya kyale sa ya kara masa wani kuɗin ma har da wani cewa baban ki kam ai baban nane, tun daga lokacin da baba yaga motar Alhajin yazo zai zo ya zauna a zaure yana jiran Alhajin ya bani kuɗi ya tafi shi kuma yazo ya karɓe kuɗin, ni wanna dukka bashi ne damuwa ta ba, damuwata shine kullun idan Alhajin yazo sai ya rinƙa yimin maganar banza, wai in munyi aure a ranar farko zai bani ciki, idan na nuna masa bana son maganar sai yace ai yana son ya koyamin yadda akayi ne tun yanzu dan na iya kar sai munyi aure naje na kasa yi masa abun da yake so, kuma sai ya rinƙa cemin ya kamata na rinƙa binshi muna fita zuwa hotel, ko gidan sa, bashi da wata magana sai na banza, idan nace bana so sai yace zai faɗa wa babana ina zagin sa, kuma kasan halin baba tun da Alhaji na basa kuɗi duk abun da Alhajin ya faɗa masa yarda zai yi ya haukai ya zauna ya kamani ya min duka, saboda tsoron hakan yasa kawai nayi shiru ina sauraron maganganun banzan da Alhajin yake faɗamin, jiya da daddare Alhajin yazo lokacin kuna cikin ɗakin mama kuna hira, baba yasa na fito dan muyi hira da Alhajin, dana fito Alhajin yace na shiga motar sa muyi hira naki, yace dole na shiga ai shi mijina ne tun da baba ya bashi aure na, kuma idan ban shiga ba sai ya faɗawa baba, ina tsoron ya faɗa wa baba shine na shiga na zauna, haka ya rinƙa taɓa min kirjina yana wasa da su har da gaba na ya rinƙa sa hannun sa yana wasa da shi, har yanzu sai zafi suke min, da kyar ya barni na dawo cikin gida bayan ya gama wasa dani, na rasa wazan faɗa wa, tunjiya da daddare nake kuka yau da zazzaɓi na tashi, babban abun da ya sake sani kuka yanzu, shine ina fitar da wanna murhun zan fara tuya, sai ga Alhajin yazo, wai jiya yaji daɗi kuma ya kasa barci na tayar masa da hankali dan haka na shirya anjima zaizo ya ɗauke ni, muje gidan sa mu ɗan huta, ina cikin faɗa masa ba zanje ba sai ga baba yazo zai shiga gida, da yaga Alhajin shine yazo suka gaisa, nan fa Alhajin yace masa wai yace zaizo ya ɗauke ni muje shopping ya sai min kayan arziki nace bana so, shine baba ya mare ni, ya rinƙa faɗa wai dole nabi Alhajin ko kwana ma yace zamuyi ba sai maje mayi ba, bare kuma kaya kawai zai saya min mu dawo, dan munafurci irin na Alhajin nan sai bawa baba hakuri yake wai baba ya dai na yimin faɗa baya so ana yiwa matar sa haka, sanna ya ciro kuɗi dayawa ya bawa baba ya shiga Motar sa ya tafi yana faɗin karfe ɗaya na rana zaizo ya ɗauke ni, baba kuma kuɗin ne kawai damuwar sa, yana karɓan kuɗi ya wuce cikin gida yana faɗin dole ma ta bika ai shegiya mai kashin tsiya arziki na bin ta tana gudu, abun yamin ciwo shiyasa nake kuka dan nasan idan nabi Alhajin nan wlh shikenan zai rabani da mutunci na" ta kai karshen maganar tare sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Ba laifi Jehan ta fahimci abun da ta fahimta a zancen Hanan ɗin, ta gane in da zancen nata ya dosa, duk da cewa wasu abubuwan bata gane su ba, ɗago ido Jehan tayi ta kalli Sadiq.

Kara zaro ido tayi tana kallon Sadiq ɗin, lokaci guda kamannin sa sun sauya, idon nan nasa sunyi jawur zuciyar sa na tafasa ji yake kamar yaje ya shaƙe baban sa ya kashe sa dan haushi, tunani yake a ransa yanzu yana cikin gidan nan jiya wani katon banza yazo yana matse masa kanwa, wani ihu yayi kamar mahaukaci cikin fushi yace "Aina Alhajin yake?" Ita ma Hanan ba karamin tsorata da ganin Sadiq a haka tayi ba, dan tasan Sadiq mutun ne mai hakuri ga murmushi ba zaka taɓa ganin fuskar sa a ɗaure ba, duk damuwa da matsalar da gidan su ke ciki, kullun cikin murmushi yake.

Murya a dashe saboda kuka da tayi Hanan tace "Nima ban san in da Alhajin yake ba" a fusace Sadiq yace "Jehan tun da kin san hanya kije wajen aikin kawai, idan kin taso ki wuce asibiti, ni zan tsaya a nan ba yace karfe ɗaya zaizo ya ɗauke taba, to zan jirashi, idan kinje hospital ki gaishe min da gwaggo da jikin mum sai da yamma zan zo in ɗauke ki mu dawo" miƙewa tsaye Jehan tayi kafin tace "Yaushe ake tashi daga restaurant ɗin?" Shiru ya ɗan yi kafin yace "Inaga ku yan safe karfe ɗaya zaku tashi, sai yan yamma su karɓe ku, amma dai in kinje ki kara tambayar Ibraheem" jinjina kai Jehan tayi kafin tace "Okey koma karfe nawa ake sallamar mu, ni dai by 1 dole zan dawo, dan inason in bawa Alhajin nan capital warning" tsabar bakin ciki da ɓaci rai sun hana Sadiq bawa Jehan amsa, dan ji yake kamar zuciyar sa zata buga saboda haushin abun da Alhajin nan yayiwa Hanan.

Komawa Jehan tayi ta tsuguna ta gogewa Hanan hawaye, tana bata hakuri tare da mata alkawarin ba zasu bar Alhajin ya ɗauke taba.

Sai da ta tabbatar Hanan tayi shiru sanna ta yiwa Sadiq sallama ta wuce bakin hanya dan tarar abun hawa ta wuce restaurant, yau asibiti ma sai ta taso daga restaurant zata biya ta can, gashi sai tunanin mum take, dan an shiga da ita ɗakin da za'a mata aiki.

💞SUPER RESTAURANT💞

Tana shigowa kai tsaye reception wajen Ibraheem ta nufa, tun daga nesa Ibraheem ɗin ya hangota, ganin bata sanya uniform nasu ba yasa ya ɗaure fuska ya ɓata rai sosai, dan yasan ogan su ba zai yarda da rashin sanya uniform ɗin ba.

Tana karisowa wajen sa tun bata yi masa magana ba yace "Ina uniform naki? Me yasa baki saka ba?" Ɗaure fuska sosai ita ma tayi kafin tace "Ai tun jiya na faɗa maka ba zan sanka uniform ɗin ba, au kai daman ka ɗauka wasa nake maka, to idan ma baka sani ba ka sani ni Jehan bana faɗan abun da nasan ba zan aikata ba, garama kasani tun yanzu idan nace ba zanyi abuba tofa da gaske nake ba zan yi shi bane" tsabar haushi Ibraheem bai san lokacin da ya ɗaga hannu kamar zai mare ta, sai kuma ya dakata yana wani huci, yariya yar karama kamar wanna ta tsaya tana faɗa masa magana, gently tace "Ya ka dakata? Ai da ka marenin ina ga zai fi" shiru Ibraheem yayi yana mai dana sanin taimaka mata da yayi.

Ganin yayi shiru ne yasa tace "Menene aiki na? Ka faɗa min naje na fara yi dan ina son tafiya gida karfe ɗaya dai dai" zaro ido yayi yana kallon ta da mamaki, wato ita ma zata yanke wa kan ta hukunci ga lokacin da zata tafi cab lallai aiko aiki dole na koyawa yarinyar nan hankali.

A fusace ya buɗe baki zai yi magana, wayan dake gaban sa saman table ta fara kara, dogon tsaki yaja tare da sa hannu ya ɗauki wayar, irin wayar nan ne da ake ajiyewa saman table wadda costumers ke kira dan bukatar abu. Picking na call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnen sa.

Jim kaɗan ya ajiye wayar ya ɗago ya kalli Jehan yace "Kije room 22 akoi wani costumer da yake bukatar ma aikaci ɗaya" rai a ɓace tace "to me zan masa" mai da wayar yayi ya ajiye yana faɗin "Idan kinje ai koma menene zakiji" guntun tsaki taja ta wuce ta tafi ta bar Ibraheem da binta da ido yana mamaki.

Ko da taje bakin kofar Room 22 ɗin sai da taja dogon tsaki kafin tayi knocking na kofar, bugu ɗaya tayi aka buɗe kamar daman jira ake.

Wani Alhaji ne kato bakin kirin da shi gashi da katon ciki, yana sanye da gajeren wando, kaya ya miƙo mata yana faɗin "Wanki ne zaki min" zaro ido tayi ta kalle sa kafin ta kalli kayan dake hannun sa yake miko mata, singlet and boxers ne, dawo da kallon ta kan face nasa tayi a kule tace "Yanzu saboda baka da hankali nice zan wanke maka shot naka? Ko kunya baka ji ba kato da kai, hauka nake zan wanke wandon kato kamar ka, tab lalai to Jehan dai ba za tayi wanna kazantar ba sai dai wata, daman wanna aikin shine aka kawo ni nayi, to wlh ba zata saku ba, ba zan iya ba"

Tashin hankali zaro idon mutumin yayi kafin ma yayi magana, Jehan ta sa kai ta wuce ta bar wajen, da sauri mutumin ya leƙo da kan sa waje yana kallon ta, mamaki ya sa ya kasa komawa cikin ɗaki, a ransa yana faɗin "wannan yar yarinyar dai a shekaru da wuya ta wuce sha bakwai tsawo ne kawai gare ta, shine zata cemin katon banza, anya wannan a gaban iyayen ta ta taso kuwa, anya ta samu tarbiya, to wlh ba zan zauna a hotel ɗin nan ba, basu san darajar costumer ba, har ma'aikaciya tana da bakin cewa costumer ba zata yi masa abun da yake so ba, tab lalai da sake" da wannan tunani ya koma cikin ɗaki ya ɗauki waya ya sake kiran Ibraheem,

Ita kuwa Jehan kai tsaye wajan sauran ma'aikatan tan restaurant ɗin ta nufa dan ta tambaye su ko shine aikin da suka zo yi kenan wato wankin kayan costumers.

Da sallama ɗauke a bakin ta ta karisa wajen da sauran ma'aikatan ke zaune, har suna rige rigen amsa mata sallamar nata, sunga kyakyawa, dan Jehan akoi farinjini na fitar hankali, duk in da taje sai an so ta, haka itama Rimsha

Sai wani washe baki ma'aikatan suke suna ɗaga mata gaisuwa, ita kuwa kara ɗaure fuska tayi kafin tace "dan Allah zaku iya faɗa min aikin me muka zo yi a nan?" Kallon kallo suka fara yiwa junan su, lallai wato wanna ma bata san aikin da ya kawo ta nan ba tab akoi cakwakiya.

Ɗaya daga cikin sune ta miƙe ta dafa kafaɗar Jehan ta fara yi mata bayanin irin aikin da ya kawo su nan "Wanke wanke, shara, mopping, kai wa mutane abinci idan suka zo ci, sanna kaiwa yan ɓangaren hotel abinci room nasu idan suka buƙata, wasu costumers ɗin zasu buƙaci mu musu wanki su biya mu,

Please Login or Register in order to submit comment