Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗin na su, gidan gaba ɗaya sai kara duhu yake kamar dare, ga wani iska mai karfin gaske dake tasowa daga ta saman gidan mai birkita tunanin ɗan adam.

Nan take Rimsha taji an ɗaure mata maƙogwaro da karfi kamar za'a tsinke mata shi, ta kasa magana shiru tayi tare da waro sleeping eyes nata waje, wadda yanzu suka sauya sukayi ja sosai kamar garwashin wuta, Saboda kuka da wahala ga yinwa da barci duk sun haɗe mata waje guda.

Kamar a mafarki taji an ɗaga ta sama ta rabu da kasa haka zalika ta fita daga cikin igiyar da suka ɗaure ta,
sama sosai sukayi da ita, sai da ta kusa kurewa tsayin gidan, a hankali ta kalli kasa, ba karamin tsorata tayi ba lokacin da taga babu wanda ya ɗaga ta haka nan ta tashi sama, runtse ido tayi a ranta tana ambato sunan Allah, dan afilin kam ta kasa faɗa sun shake mata maƙogwaro.

Almost 5mins tana tsaye a saman iska kafin su fara bujijjigata suna wainata kamar fanka, ga wan nan iskar guguwa mai karfi mai haɗe da yashi wato kasa sai shiga mata hanci yake dan ta runtse idon ta kam sosai, da kyar take samu tayi mumfashi nan ma sai ta buɗe bakin ta take samun damar yin numfashin

da karfi suka ja ta da tsafin su suka bugata da jikin wani bango sai da ta fasa ihu mai rikita ƙwaƙwalwa, a cikin ihun nata ne take kiran "wayyo daddy na mummy gwaggo Jehan ina kuke zan mutu kuzo ku taimake ni, wayyo na shiga uku mutuwa zanyi wayyo Jehan kizo ki taimake ni"

ba shiri ta sake fasa wani ihun sakamakon buga mata kai da sukayi da jikin wani karfe dake tsakar gidan, jijjigata da karfi suka sake yi kafin su juyo da ita kan ta na kallon kasa kafafun ta a sama, da karfi sukayo kasa da ita, kamar zasu makata da kasa, sai kuma suka da katar da ita, dark black curly hair tan nan ya curkuɗe saboda wahala yana ja a kasa, yayin da kafafun ta ke saman iska, tana lilo tsakanin kasa da sama, a nan ma kara jujjuya ta sukayi kamar fanka, sai da suka tabbatar ta jijjigu a ganin su tafita hayyacin ta sannan suka juyo da ita suka sauke ta kasa

Suna sauke ta kasa su kuma su barbushi suka dakata da ambaton sunan suwagabannin tsafin na su, suna dakatawa gidan ya washe duhun ya tafi haske ya gauraye ko ina, haka shima kuran ya ɓace ɓat kamar ba'ayi ba.

Shiru Rimsha tayi ta kasa buɗe idon ta saboda wahala,
ta kuma kasa zama waje guda sai juyawa take saboda jijjigata da sukayi suka ta juyata kamar fanka, amma dai har lokacin Allah da ikon sa bata fita hayyacin taba

su barbushi sun sha ruwan mamakin ganin bata fita hayyacin taba, basu taɓa yiwa wani ɗan adam irin abun nan da suka mata kuma a ce mutumin bai fita hayyacin sa ba sai ita sun yi mamaki sosai, sun kuma kara jin haushin ta da tsanar ta.

Ita kuwa ta kasa buɗe idon ta sai jin duniya na juya mata take, ban da sunan Allah da sunan daddy da mum ba abun da take kira a ranta.

Haka su Barbushi ba dan sun so ba suka bada umarni a kai ta next room wato Part 2, su kuma sauran yaran sanadiyyar abun da a kayiwa Rimsha yasa wasu daga cikin su suka fargaɗo wasu kuma suka dawo cikin hayyacin su,

Santilago ne yasa sauran magicians suka tsince yara masu hankali a ka haɗa su da Rimsha a ka wuce dasu wani ɗakin, su kuma sauran yaran da basu dawo hayyacin su ba, Barbushi ya yankasu, kamar yadda suka saba suka kaiwa dodannin tsafin su jinin, kai da kafa kuma a ka kaiwa dodannin su masu cin kai da kafa, su kuma suka wuce da naman dan suje suyi ferfesun su.

Wani part dake cikin gidan suka wuce da su Rimsha, sai a lokacin Rimsha ta samu damar bude dara daran sleeping eyes nata sunyi ja sun kan kance saboda wahala, a hankali ta fara bin wajen da kallo, ba karamin tsorata tayi ba ganin wajen, waje ne mai cike da gumakan dodannin tsafin su, abun gwanin ban tsoro da rikitarwa,
bata kara tsinke wa ba ma sai da suka buɗe wani kofa suka jefasu suka rufesu sukayi tafiyar su, su uku ne rayar da su ka rage masu hankali sai Rimsha ta huɗu.

Wani irin ɗaki ne idan ka ganshi zakayi tunanin gidan prison ne, gefe da gefen dukka an sanya burglaries daga sama har kasa an tare wajen kamar keji, shi kuma tsakiyar an barshi kamar hanyar wucewa, gaba ɗaya wajen sai wani irin fitinanniyar wari mai tada hankalin mai shaƙa ke tashi.

Wayan nan magicians ɗin suna jefa su Rimsha ciki, wasu jibga jibgan dodanni ne suka taso ta cikin burglaries ɗin suka fara miƙo hannun su ta cikin burglaries ɗin suna son kama su Rimsha
jibga jibga ne sosai masu siffar spider (gizo gizo) sai dai girman jikin su ya kai kusan giwa, gashi ido ɗaya gare su a tsakar goshin su, gasu da bala'i muni, fuskar su kawai ya isa ya sanya mai rai suma saboda muni, hannun su da kafafun sun nan babu kyan gani ko kaɗan, bakin su kuwa kamar mutun yayi ta kwarara amai idan ya gani, haka suka bufo su Rimsha suna gurnani mai razana kwakkwal mai rai.

Gudun cetan rai su Rimsha suka fara yi a wajen gashi wajen ba wani faɗi ne gare sa ba, sai zuro hannu dodan nin nan suke suna son kama su, da gani a matsanancin yinwace dodannin suke, abin ci kawai suke buƙata

ihu sosai Rimsha take kamar makogwaron ta zai fashe, gwanin ban tausayi, duk in da ta gudu a wajen sai dodanin sun je gashi an ɗaure mata makogwaron ta bata iya kiran sunan Allah, hakan ba karamin cutar da ita yayi ba, sai ihu take tana gudu ta rasa ina zata sanya ranta, sukam sauran, yara biyu daga ciki sun sume a wajen, saura yarin ya ɗaya dake ta faman gudu tare da Rimsha, su kuwa dodannin sai musu barazana suke, dan hannun su ba zai kai su iya kama su Rimsha ɗin ba, su Rimsha ke ganin kamar dodannin zasu kama su.


*KADUNA*

Aafia

In da ta bar Aunty a nan ta fito ta same ta, kallon sama da kasa ta mata kafin ta ɗauki remote ta can za channel na Tv, shiru Aunty tayi bata yi magana ba, amma tana son kallon film ɗin da take kallo a arewa 24 sai dai ba yadda ta iya dole ta hakura ta zauna shiru ta zubawa Tv ido kawai tana kallon wakar da Aafia ta sa, ba dan taso ba.

A wannan halin Abbi ya dawo ya same su, da sauri Aafia ta miƙe ta faɗa jikin sa tana dariya, rungumeta yayi yana faɗin "My daughter ana hira da Aunty ne?" Shiri Aafia tayi masa kamar bata ji me yace ba, dai dai lokacin idon ta ya sauka a kan yarinyar dake biye da Abbi a baya, cikin sauri ta ɗago daga jikim Abbi tana faɗin "Abbi wace ce wan na kuma?" Juyowa Abbi yayi ya kalli Aunty dake zaune tana son yi masa oyoyo amma ta kasa saboda Aafia,

wucewa yayi ya zauna kusa da Aunty yana faɗin "Mai aiki na samo muku hajiya zuwaira ce ta kawo min ita, sai ku riƙe ta da amana kun dai ga yarinyace" a kule Aafia tace "Abbi to ita kuma wan nan fa me zata rinƙa yi" tayi maganar tana nuna Aunty da hannun ta, ba tare da ya kalle ta ba yace "Ke zoki zauna ina Umaisha take? Kuzo na muku wani albishir" cikin zumuɗi ta dawo kusa da shi ta zauna tana faɗin "Albishir ɗin me Abbi?" "ina Umaisha take?" Cikin sauri Aafia ta miƙe har tana haɗawa da yar gudu ta nufi bedroom nasu, Aafia na tafiya Aunty ta kira mai aikin da Abbi yazo da ita a kan tazo ta zauna, yarinya ce karama wadda ba zata wuci sa'ar Umaisha ba wato 18 years kenan, ba musu Yarinyar tazo ta zauna a kasa kusa da kafar Aunty, gaba ɗaya a tsorace yarinyar take taki sakin jikin ta da su,

Tare Umaisha da Aafia suka sauko sai murna suke suna jin daɗi, har rige rigen zama kusa da Abbi suke, ganin haka yasa Aunty ta miƙe ta bar musu sofar ta koma mai zaman mutun 1, Abbi bai wani damu da hakan ba shi a ganin sa su Aafia yarane basu girma sosai ba shi yasa bai cika tsawatar musu a kan faɗa da suke wajen zama kusa da shi ba har su sanya Aunty ta tashi ta basu waje, Allah sarki Aunty baiwar Allah bata taɓa damuwa ba da sun fara zata basu waje ita ta koma gefe.

Cike da farinciki Abbi ya ciro takardun daga jakar sa tare da key ɗin motoncin guda uku, Aafia na kokarin ansan key ɗin ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu yana faɗin "Ki bari auntun ku ta fara ɗauka tukun nan" kallon sama da kasa Aafia tayiwa aunty tare da turo bakin nan nata kamar biro tana jin kamar taje ta tsake Aunty ta kashe ta kawai kowa ya huta, shi kuwa Abbi sai murmushi yake yana kallon Aunty bai lura da abun da Aafia ke yi ba.

Ganin Aafia ta ɓata rai ne yasa Aunty tace "A'a Abbi ka bawa Aafia ta fara ɗauka ni ku bani ko wane ma ina godiya" Aunty tayi wannan maganar ne ba dan komai ba sai dan ta samun zaman lafiya da Aafia, ko kaɗan bata son irin zaman da suke da Aafia bata jin daɗi shi yasa take kokarin duk yadda zasu yi su sami zaman lafiya, amma duk a banza saboda Aafia da zancen su Rufee take aiki ba da nata tunanin ba.

Girgiza kai Abbi yayi kafin yace "Ke nace ki fara ɗauka ai, ba kece babba ba?" Haka ba dan taso ba ta sanya hannu ta ɗauki key ɗaya, sannan Abbi ya miƙa wa Aafia, kamar ba zata ɗauka ba amma sai ta ɗauki ɗaya dan tasan halin Abbi yana da wasa da dariya amma bai son a kawo masa shirme a lamuran sa yanzu zai harzuƙa ya fara faɗa

Key na karshen ya miƙa wa Umaisha yana faɗin "Key ɗin sabbin motocin da na sai muku ne" a sukwane Aafia miƙe tana faɗin "Abbi ina motar take? Tana waje ne?" Sai murmushi yake yace "Motar na sabon gidan mu da zamu koma ga takardun gidan nan ma, shine albirushir da zan muku daman" Aafia da Umaisha har suna rige rigen rungumar Abbi dan murna da farinci, sai murmushi ita ma Aunty take bakin ta yaki rufuwa, sai godiya ga Allah take a ranta

"Ina key ɗin tsofaffin motoncin ku?" Abbi ya tambaya yana kallon su, har suna haɗa baki wajen cewa "yana bedroom" "je ku kawo min" da sauri Umaisha ta miƙe ta haye sama.

Jim kaɗan ta dawo hannun ta riƙe da keys ɗin tazo ta miƙa wa Abbi, ansa yayi ya miƙa wa aunty yana faɗin "Ki bawa yayan ki da kanin nan naki yama sunan su? To ki basu su rinƙa hawa" Aunty ta ansa tana kokarin yin magana kenan Aafia ta katse ta cikin jin haushi tace "Haba Abbi ni gaskiya a'a zan bawa Rufee nawa motar gaskiya Sai dai a bata na Umaisha" tsare ta da ido Abbi yayi kafin yace "da Auntyn ku da Rufee ɗin wace ta fi muku?" Har suna haɗe baki wajen cewa "Rufee tafi mana Abbi" tashin sense "What?" Abbi ya furta da mamaki a face nashi, kukan shagwaɓa Aafia ta sa masa tana bubbuga kafa a kasa

jiki na rawa Aunty tace "A'a Aafia ga key ɗin naki kiyi hakuri" kallon ta Abbi yayi kafin yace "Ita ta baki key ɗin ne?" Cike da ladabi Aunty ta girgiza kai tana faɗin "A'a kayi hakuri" kallon Aafia yayi kafin yace "Ba dai Rufee kike son bawa mota ba?" Da sauri Aafia ta gyaɗa masa kai alamar eh "Je ki bedroom na yayan ku ki ɗauki key ɗin motar sa ki bata dan shi ma ya sayi sabbi guda biyu" nan take murmushi ya kubcewa Aafia cike da murna ta miƙe ta bar palon, shima Abbi miƙewa yayi rike da takardan sabon gidan da ya sai musu da jakar sa ya wuce bedroom na shi, cike da murna Umaisha ta miƙe ita ma takoma bedroom nasu

kallon yarinyar da Abbi yazo da ita Aunty tayi kafin tace "Muje na nuna miki ɗakin ki ko?" Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tayi gaba yarinyar ta bita zuwa ɗakin masu aikin dake kusa da kitchen, nan Aunty ta kai ta san nan ta fito ta wuce bedroom nasu dan taje ta tayiwa Abbi godiya, sai murna take yayan ta da kanin ta sun samu mota.


**💞WASHINGTON DC💞**



*HARVARD UNIVERSITY🎉*


Gudu Test yake shatarawa kamar zai tashi sama a chikin katafaren fillin *Harvard football place* kallo ɗaya zaka masa ka gane gudun cetan rai yake, da wani mahaukacin gudu Michael ya biyo bayan sa, kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yana chikin matsanancin bachin rai.

Sosai Test ke gudun cetan rai, yazo dai dai tsakiyar wajen *Harvard basket ball Place* kenan Michael ya kai masa wani wawan bugu a bayan wuya wadda ya sanya shi ya faɗi kasa,
gadan gadan Michael ya nufeshi kamar wani mayinwacin zaki sai huci yake ran maza ya ɓaci, gadan gadan ya nufe sa da niyar dukan shi, wani dattijo ne ya kariso wajen da gudu ya tsugunna ya kama kafar Michael ya fara magana chikin harshen turanci "Sorry Michael, kayi hakuri ka kyalesa" babu ko tausayi Michael yasa kafa ya hambare dattijon har sai da dattijon ya faɗi kasa, a fusace rai amatukar ɓace ya nufi kan Tast gadan gadan, hannu ya dunkule zai kai wa Test naushi a fiska, wani kyakkyawan Bature matashi ya riƙe hannun nashi ta baya,

A fusache Michael ya juyo chike da ɓacin rai yace "Robertson ka sake ni" "No Michael ba zan sake kaba me yasa zaka bugeshi wai ba friend naka bane?" "Please Rob ka kyaleni na kashe wannan jakin" ya karisa maganar tare da kwachewa daga rikon da Robertson ya masa
yana kokarin kai wa Tast duka a cikin, cike da izza Rob yace "Allah Michael idan ka sake ka buge sa sai na kira Romeo yanzun nan" a sukwane Michael ya juyo, chike da ɓacin rai ya fara magana "Rob kasani awannan karon Romeo ba zai che komai ba sai dai ma ya kashe Test (Tase) da hannun sa, kasan me Test yamin ne da har yasa nace sai na illatashi!? "Aa Michael ban san me ya maka ba amma ko ma me ya maka kamata yayi ka masa afuwa tun da friend ɗin kane, tukun nan ma me ya maka?"

Shiru Michael yayi na ɗan lokachin kafin yace "dazun na sai musu kyautan mota, dan na canza musu tson da suke hawa da murna na kawo musu key ɗin shi da Dest, wai ina miƙa musu keys ɗin buɗar bakin Tese wai God bless your mum har da wani cewa Allah yasa ta dawo gare mu"

iya ɓacin rai Rob ranshi ya baci, dan bai son abun da Michael ke yi wa mahaifiyar sa ko kaɗan, duk da chewa da gaske mum nasu ta musu laifi amma bai kamata suna yin abin da suke yin nan ba, cikin sigar rarrashi yace "Michael please stop saying this i knew mum did something wrong to... Rob bai kai karshen maganar ba Michael ya daga masa tsawa yana faɗin "Rob please live this place, for now i don't want to see you" "what!? Micheal are you heard what you said ? Ni kake chewa na tafi? Good, to ba zan tafi ba Please ka kyale tese kazo muje" "Rob idan kaga ban illata Test ba yau to sai dai in nine na mutu" ya kai karshen maganar ya juya, a fusache ya rufe Test da duka, girgiza kai kawai Robertson yayi yana mamakin zuciya irin na Michael, san nan yana tausayawa su Test dake friends nashi.

dukan shi yake ba ji ba gani kamar an aiko sa, ta ko ina yake sauke masa hannu a jikin,
Kamar daga sama yaji an riƙe hannun sa ta baya, a sukwane ya juyo dan ganin wanene, karaf idon sa ya sauka kan face ɗin James dake tsaye fuskar nan tashi babu alamar annuri ko kaɗan kallo ɗaya zaka masa kasan yau yana cikin ɓacin rai over.

Sakin Test Micheal yayi ya taho ya rungume James yana huci yana jin zuciyar sa na masa zafi kamar zata fashe ta fito waje, ajiyar zuciya James ya sauke kafin yasa hannu yana ɗan bubbuga bayan Michael alamar rarrashi

"What happened between you and your friend Tese" James ya tambaya yana tsare Test da ido, cike da tsoro da tashin hankali Test yace "I'm sorry Michael it was a mistake" "I did not ask you whether it's mistake or not, I say what happened" cewar James a tsorace Test yace "we warmly received a car gift early morning from him, mistakenly I say to him, God bless your mum because I'm really happy, I forgot he hate his mum"

Dawo da kallon sa James yayi kan face ɗin Michael da ya kwantar a saman kafaɗar James ɗin, sai wani huci yake yana lumshe brown eyes na shi, girgiza kai James yayi a ransa yana faɗin Michael ɗan rigima, a zahiri kuma shafa kumatun Michael ɗin yayi kasa kasa yace "It's okey, let's go home" shiru Michael ya masa kamar bai ji me yace ba, dawo da kallon sa kan Test yayi cike da bada umarni da izza yace "be careful Test, don't repeat this mistake again" cikin sauri Test yace "Okey sir thank you very much"

sake kallon Michael James yayi "Are you okey Michael? Where is Lucky and copper?" "They are at home" Michael ya bashi amsa tare da wucewa ya nufi hanyar parking space, girgiza kai James yayi kafin ya bi bayan Michael ɗin suka jera tare, suka bar su Robertson da Test tsaye a wajen, suka shiga motocin su suka nufi gida.

Lokacin da suka dawo gida babu kowa a palon kasa sai daddaɗar kamshin air freshener da sanyin Ac da ke tashi, ko ina a gyare tsab kamar sabbin abubuwa a ka zuba a wajen.

Kai tsaye saman bene suka wuce, a tare suka shige part ɗin Romeo babu ko excuse,

Suna shiga Michael ya faɗa saman katafaren bed ɗin Romeo yayin da shi kuma James ya zauna gefen gadon yana sanya hannun sa ya ɗauko wayar Romeo dake saman bedside drawer kusa da system,
Dai dai lokacin Romeo ya fito daga toilet ɗaure da towel a kugun sa, wow asalin kyansa ta sake bayyana, soft skin nan nashi a kwance luf kamar ka latsa jini ya fita, asalin surar murɗanɗan jikin sa ta bayyana, hannun nan nasa kamar zasu fashe saboda horo, kasan cewar jikin sa a koi ɗan ruwa ruwa hakan yasa kyakkyawan dark black gashin kirjin sa suka kara kwnciya luf, gashin kan sa a jiƙe alamar ya wanke, zubo masa gashin yayi har bayan sa yayin da shi kuma guntu na gaban goshin sa ya zubo masa a face na shi, sai faman tattare wa yace lallausan laɓɓan nan nasa kamar ya sanya musu lipstick ja dan sun kara ja sosai, lallausan gashin dake kwace a cinyoyin sa da hannayen sannan sun kara kwanciya sosai gwanin ban sha'awa, ya kware wajen iya lumshe ido, a yanzu ma sai fama lumshe dara daran blue eyes na san yake kamar mai jin barci, ga wasu guraye a flat tummyn sa irin na jaruman maza.

Wucewa yayi ya shiga wani wajen da aka keɓe da glass ba tare da ya lura da su Michael ba.

Good 40mins ya ɗauka a cikin wajen kafin ya fito, nan take bedroom ɗin ya gauraye da wannan fitinanniyar kamshin perfume ɗin nasa, shirye yake cikin wandon jeans baki mai bala'i kyau da tsada sai Turtle high blue daya sanya a jikin sa ya ɗaura puffer Jacket baki a sama, ya ɗaure kyakkyawar dark black curly hair sa da ya sha gyara a bayan sa, ya bar wannan guntu na gaban goshin nasa ya zubo masa a saman kyakkyawar face ɗin sa, sai kyalli gashin ke yi yasha gyara ga kamshi mai bala'i daɗi da yake zubawa, ba karamin kyau yayi ba, still wannan diamond watch ɗin nasu na manne a hannun sa, sai kyalli yake yana ɗaukan ido, yayin da wuyar sa ke sanye da gold chain necklace masu bala'i kyau da tsada, sai kyalli suke suna ɗaukan ido, hakan ba karamin kyau ta kara masa ba, kyawawan fararen kafafunsa na sanye cikin wata laullausan bedroom slippers fari tas mai bala'i kyau da laushi kamar jikin mage, sai fitinanniyar kamshin wannan perfume ɗin nasa ke tashi daga jikin sa.

Wannan fitinanniyar kamshin ita ta kai wa su James sakon Romeo ya fito, a tare su ɗago kai suka kalle sa, wucewa yayi ya zauna gefen gadon kusa da Micheal tare da jawo system na shi dake saman bedside drawer ya kunna ta
cikin sauri har suna haɗe baki wajen cewa "Good morning lion" shiru ya ɗan yi na yan mintoci, ba tare da ya kalli in da suke ba, kasa kasa da wannan sexy voice ɗin nashi mai kwantar da hankalin mai sauraro yace "How are you doing this morning?" A tare suka amsa da "we are doing well what of you" shiru ya musu ba tare da ya sake magana ba.

Matsowa kusa da shi Micheal yayi tare da kwantar da kan sa saman cinyar James cikin murya kamar mai yin shagwaɓa yace "lion please I need money I'm broke" "same here" James ya faɗa, yana matsewa Michael kumatu da hannun sa, shiru Romeo ya musu bai yi magana ba, shiru suma suka zauna basu sake magana ba sun zuba masa ido suna kallon sa.

Almost 30mins suna zaune shiru in da sabo sun saba,
gently yasa hannu ya ansa wayar sa dake hannun James tare da juyowa ya kalli Michael dake ta faman turɓune fuska irin na shagwaɓa, "i need hot coffee" ya faɗa in a cool voice, kallon time James yayi a jikin diamond watch na shi 11:00am dai dai yana kokarin niƙewa dan yaje ya kawo wa Romeo breakfast na shi, dan lokaci yin breakfast na shin tayi, bai kai ga miƙewa ba Michael ya rigasa miƙewa, da sauri ya diro daga gadon ya nufi waje

Michael na fita James ya juyo ya dubi Romeo "a nan zaka yi breakfast ne?" Gyaɗa masa kai Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, daman can shi Romeo bai cika zuwa table cin abinci ba dan time ɗin cin abincin sa daban dana kowa a gidan 11 na safe yake breakfast, yayin da su kuma su Michael suke breakfast 8, sai 4 na yamma yake cin abincin rana yayin da su kuma su Michael suke cin na su 2, da daddaren kam bashi da takamaimen time na cin abinci wani lokaci yaci da wuri wani lokaci har 2 na dare yake kaiwa wani lokaci ma baya cin abincin daren maltina kawai yake sha, bai damu da cin abinci sosai ba, musamman abinci mai nauyi bai damu sosai da ci ba da daddare.


"Bro I want go somewhere" cewar James shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba yayin da hannun sa ke kan wayar sa ga system nasa a saman lallausan cinyar sa.

A haka Michael ya dawo ya same su, hannun sa ɗauke da katuwar tray mai shake da kayan abincin su na turawa, saman Chinese carpets dake kusa da gadon ya ajiye tray ɗin sannan ya faɗa saman gado yana faɗin "I'm tired" miƙewa James yayi ya fara serving na

Please Login or Register in order to submit comment