Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaifin gaske wadda ke aiki da wata yar inji a jikin ta wadda akewa charji, idan aka kunna injin wannan wuka zata iya zaba ɗan adam gida biyu saboda kaifin balai da take da shi, wannan wukar Michael ya ɗauko ya nufi waje.

Kai tsaye palon kasa ya koma su daddy suna biye da shi, cikin tsawa ya kira sojojin dake musu girki, sai wani huci yake kamar ɗan zaki, cikin sauri sojojin suka fito daga cikin Kitchen ɗin, kallon sa dad yayi kafin yace "Michael what are you going to do with this AK" sunan wukar kenan AK, "that I want to cut their hand"

Tashin hankali kasa sojojin suka zube sunji Michael zai yanke musu hannu, ɗaya daga cikin su kam ma kuka ya fara yi dan yasan yaran William jacop basa maganan da ba zasu aikata ba, hakuri dad ya shiga bawa Michael yana lallaɓa sa akan ya kyale sojojin yayi hakuri ya tsaya suji dalilin da ya sa suka saka musu kifi a abinci, ina Michael yayi nisa baya jin kira ya dage sai ya yanke musu hannayen su, da sauri daddy yace da su jay su rike Michael kar su bari ya yanke wa sojojin nan hannu,

Kin rike Michael ɗin su Jay sukayi dan mugunta sai ma kara ingiza shi suke, jikokin mugaye, su Jay akoi su da mugun ta zuciyar kafurci babu ɗigon imani, shi kuwa James da ya haddasa wannan bala'i yana can suna hira da Musharraf hankali kwance sai dariya yake bai san meke fatuwa ba, sai dai shima yaki cin abinci ko da Musharraf yace yaci, sai yace a'a basa cin kifi, basu saba ba, shi a tunanin sa iya Musharraf kawai akayiwa girki da kifi.

Sojojin dake girkin kuwa sai kuka suke bayin Allah basu jiba basu gani ba za'a yanke musu hannun suna ji suna gani, ɗayan kam har da majina ya haɗe hawaye sharɓa sharɓa a fuskokin su, Tga har da cewa idan Michael ba zai yanke musu hannu ba ya bashi wukar bari shi ya yanke musu, mugun kafuri zuciya ba imani ba tawakkali, shekara wajen 8 sojojin nan suna yi musu girki ba'a taɓa samun matsala ba sai yau, yau ɗin ma matsalar daga wajen James aka samu shine bai musu bayani yadda ya kamata ba, amma su Tga sun murje ido sunce dole su yankewa sojojin nan hannun su, daga saman wajen hammatan su zasu yanke gaba ɗaya.

A ɓangaren Romeo kuwa, tsaye yake gaban mirror ɗaure da towel mai laushi fari tas a kugun sa, soft skin na sa kaɗai abun kallo ne, yaji hutu sosai yana kwance lif sai sheki yake ga tsantsi kamar fatar jariri, kasan cewar babu riga a jikin sa, hakan ya bayyanar da kakkarfar suran jikin sa, Romeo yana da tsawo sosai, dan ya fi su James tsawo dukkan su, daga shi sai James Michael ne ya ɗauko tsawon mum ɗin su ɗan dai'dai da shi, James kuma tsawon uncle Tga ya ɗauko, Romeo kuma tsawon daddyn su, har ma yafi daddyn su tsawo kaɗan, amma shima daddy ba baya ba a tsawo.

Romeo yana da buɗaɗen kirji sosai sannan gashi yana ɗaga karfe sosai wato gym kenan, hakan yasa kirjin nasa ya kara buɗe wa sosai kamar wani irin manya manyan zakunnan nan, wayan da suka riƙa, damtsen hannun sa kawai idan ka gani ya isa ya sa ka razana har kaji kamshin suma, breast nasa kuwa ba'a magana a cike suke bul bul gwanin burgewa, yana da korjinin bala'i wadda ganin sa yana cikin farinciki ma kawai yana sanya hantar manyan jaruman maza ta kaɗa, shiyasa mum nasu take cewa ganin lion yana cikin farinciki ma razana ta yake,
## Korjinin sa ya sanya idan yayiwa mutane tsawa suke iya mutuwa, gashi da bala'i farinjini kamar me, ba iya mace ka ɗai ba har maza idan suka ganshi kyasawa suke, maza ma bala'i san shi suke ina ga mata kuma ai ba'a magana, ko wani jinsi son shi suke kamar me, gashi kuma ko full face nasa basu sani ba, haka suke son shi, wasu da dama masoyan kyakkyawan kiran jikin sane, wasu kuma masoyan tarin dukiyar da Allah ya bashi, wasu masoyan matsayin sa a wajen aiki wato THE GENERAL OF THE ARMY, wasu kuma masoyan kuruciyar sa ne, da wuya a samu mai san shi dan Allah bacin iyayen sa da Triplets nasa, kullun fiskar sa a ɗaure take tamau kamar hadari bai san menene dariya ba.

Sai faman shafawa kan sa tsadaddun hair cream nasa masu bala'i kamshi da kyau da tsada yake, ga gashin nasa sai kyalli yake yana wani curly gwanin ban sha'awa

Mai kala uku ya shafa a kan nasa, duk wannan fitinannen kamshi mayu kan dake tashi daga gashin nasa hakan bai hana shi ɗaukan turaren gashin mai bala'i kamshi, ya sake fesawa curly hair na saba, dan shi ma'abocin kaunar kamshi ne sosai, kullun yana cikin zuba kamshi har kamshin turaren nasa ya kama jikin sa, ko bai sa turare ba kamshi yake zubawa, amma a haka sai ya saka.

Bayan ya gama ne ya ɗauko almakashi ya rage tsawon wannan guntun gashin gaban goshin nasa, dan yanzu gashin ya ɗan yi tsawo ya zo masa har wajen gemu shi kuma bai san haka ya fison na gaban goshin ɗan guntu zuwa kyakkyawan dogon hancin sa, shiyasa duk bayan 1 week yake rage tsawon gashin gaban goshin ya bar na bayan da yake har tsakiyar bayan sa.

Dressing room nasa ya nufa bayan ya gama shafe jikin sa da gashin kan sa da tsadaddun mayukan sa, 10mins ya ɗauka a dressing room ɗin sannan ya fito, jikin sa na sanye da pajama launin sky blue mai kyau da tsada, ya ɗaure gashin kan sa a baya, ya saki wannan ɗan guntu na gaban goshin da ya datsen ya kara rage mata tsawo yanzu, sai tashin fitinannen kamshi perfume nasa yake.

Saman katafaren lallausan gadon sa ya haye tare da jawo laptop nasa dake saman bedside drawer ya kunna wutar gaban screen ɗin tare da cire password ya shiga bincike a kan James

Kasan cewar ya saukar da idon sa kasa yana kallon screen na laptop ɗin hakan yasa idon nasa tayi kamar a rufe, zara zaran eyelashes nasa suka kara bayyana, dan shi da Michael irin eyelashes ɗin daddy gare su dogaye sosai kamar sun kara dana kanti, ga gashin geran su kiris ya rage su haɗe da juna dan cikan gashi dake wajen, sai dai duk cikan gashin gerar nasu a kwance yake lif yana ta shaƙi kamar wayan da akayiwa make up, duk cikin su lips na Romeo ne yayi red sosai kamar ya sanya jan baki, shi Micheal lips nasa dark purple ne, shi kuma James red ne irin na Romeo sai dai bai kai na Romeo yin red sosai ba.

Duk wannan badaƙala na yankewa sojoji masu yi musu girki hannaye da Michael ke shirin yi Romeo da James basu sani ba, suna nan suna aikin gaban su, Micheal na tsula tsiyar sa a palon kasa son ran sa...


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞


TRIPLET'S💞



💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)



*Gargarɗi*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_




WhatsApp me for more information 09162620621






Episode 40-41


Duk wannan badaƙala na yankewa sojoji masu yi musu girki hannaye da Michael ke shirin yi Romeo da James basu sani ba, suna nan suna aikin gaban su, Micheal na tsula tsiyar sa a palon kasa son ran sa.

Da gaske Michael ya nufe su zai yanke musu hannu, nan fa suka fasa ihu mai karfin gaske, wadda ya sanya James fitowa da gudu dan yaga meke faruwa, shi kuwa Romeo daman kome za'ayi a cikin gidan baya tankawa in dai ba yaji muryan James da Michael ko daddy a cikin hayaniyar ba baya fitowa, ba ruwan sa baya shiga harkan kowa.

Ganin abun dake faruwa yasa James saukowa kasa da yar gudun sa yana faɗin "Stop Michael" turo baki Michael yayi yana faɗin "Kifi fa suka saka a abinci" ɗan shafa kan sa James yayi dan yasan shi yasa su saka kifin, da murya irin na mai rarrashi yace "Sorry our heartbeat ni nace su saka kifi a abincin Musharraf, to nayi kuskure ban faɗa musu a nashi kawai zasu saka ba" miƙa wa John wukar AK Michael yayi yana faɗin "To suje su kwashe duk wani abun da ya taɓa kifin nan su zubar da shi, ko spoon karsu rage min bana so gani, kuma shima uncle ɗin naka ka faɗa masa ba'a cin kifi a gidan nan, ba dan ma ya sa hannu a takarda ba da ya bar gidan nan yanzu" ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun dad suka haura sama yana faɗin "My dad I'm so sorry kaji?" Gyaɗa masa kai daddy yayi yana shafa kan sa yana faɗin "Kun cika zuciya over kamar mum ɗin ku" ɗaure fuska Michael yayi kafin yace "Dad ka dai na maganar ta, I don't want" shiru dad yayi yana jin kaunar yaran nasa har cikin ransa

Part ɗin Michael suka shiga sai shagwaɓa da sangarta Michael ke zubawa daddy, daddy kuma yana biye masa, dan yasan ba laifin sa bane matsalar daga kwakwalwan sane, Allah sarki Michael shi bashi da zafin zuciya sosai kamar na James da oga kwata kwata wato lion, ciwon sa yasa wani lokaci idan ya binkice sai ya zama kamar mahaukaci kamar mai tsananin zuciya, amma a zahirin gaskiya duk cikin triplets Michael yafi su saukin kai, dan shi bai yi karatu ba, cikin sauki zaka masa wayo kasa shi yayi maka abu koda baya so, kuma yana da saurin yarda da magana idan aka masa, shiyasa ko yayi fushi yake saurin sauka, shi James ba saukin kai gare shi ba kawai basaja yake, shi kuma oga lion ma ai ba'a magana karshe ne shi a zafin kai da zafin zuciya.

A ɓangaren su James kuwa, umarni James ya bawa sojojin a kan su sake yin wani girkin wannan duk su kwasa su zubar da shi, sannan kamar yadda Michael yace duk wani kwanon da pots da suka san kifin nan ya taɓa to su zubar da kwanikan dukka har da tukanen, sai murna suke James ya cecesu Michael bai yanke musu hannu ba, har wani yar sakin fiska sukayi yau, sosai suka zubawa James godiya da fatan alkhari sannan suka amsa umarnin da ya basu, suka tashi suka koma bakin aikin su, dan su sake yiwa family'n daddy abinci, dan duka yaran daddy ba wanda ya iya cin abinci a waje, sai dai idan tafiya sukayi, shima tafiya idan suka san zasu fi kwana ɗaya a waje tofa ɗaukan mai aiki suke, duk wuya a gida suke cin abinci, su wasu irin mutane nen da suke da kyamar bala'i dukkan su karku cire kowa, suna da kyama sosai, ba kuma iya abinci suke kyama ba har da ɗan adam, haka suke, mu samman Romeo yafi kowa wannan ɗabiar yana da kyama over, sannan baya son wani ya raɓe sa, ammafa yana da kyauta sosai, ga sadaka duk wasu gidan marayu dake cikin birnin Washington DC kullun ranar Sunday yana kai musu ziyara na kyaututtuka masu yawan gaske, haka duk wani wajen bauta yana kai sada bai ware ko ɗaya ba, har masallaci, dan akoi wani babban masallacin ma wadda shi ya gina da kuɗin sa, haka akoi wani babban church da ya gina da kuɗin sa, time to time yana kai ziyara gidan tsofaffi da ga jiyayyu haɗe da makarantun gomnati, sannan a ɓangaren wasanni ma, irin su kwallon kafa da sauran su yana basu kyauta sosai, amma pannin wasanni yana bada kyautar ne saboda Michael, shi baya kallon kwallo da sauran su Michael ne mai kallon kwallo, to da Michael yaga Team nasu taci zai zo ya sanar da Romeo a kan ya musu kyauta, akoi islamiyoyi da dama da yake kai musu ziyara tare da kyaututtuka da dama, baya ware wani addini guda ɗaya yace ba zai musu kyautaba a'a idan ya tashi dukka addinan yake haɗawa ya basu kyauta, duk wasu manya manyan masallatai da church's dake birnin Washington DC ya sai musu manya manyan motocin na zuwa da'awa, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya ya kasan ce mai bala'i farinjini ta ko'ina, yana ɗaya daga cikin abun da ya sanya ya sawa ransa babu wani ɗan adam da zai soshi domin Allah sai dai dan kuɗin sa ko kyan sa ko mukamin sa a wajen aiki, hakan yasa ma baya yarda da kowa.

Wucewa James yayi ya bar palon ya koma wajen Musharraf dan su ci-gaba da hiran su, Tga da John kwata kwata basu ji daɗi ba sun so Michael ya yankewa sojojin nan hannu da mugunta irin na zuciyar kafurci, cike da jin haushi suka wuce kowa ya koma bedroom na sa.

Misalin karfe 8 Na dare Romeo na tsaye a balcony bedroom nasa ya goya hannayen sa a saman faffaɗar kirjin sa, saboda sanyin da ake sosai yasa ya sanya puffer Jacket nasa mai ɗan girma wadda yazo masa har gwiwar sa duk tsawon nan nasa, ya sanya hulan jacket ɗin a kan sa, ga wannan kyakkyawan guntun gashin gaban goshin nasa ba karamin kyau yake karawa fuskar sa ba, sai dai fuskar kamar kullun a ɗaure take tamau kamar hadari, sai tashin fitinannen kamshi yake, yayi shiru yana tunani a kan James

Kamar a mafarki ya hango James a kasa harabar gidan, yana kokarin fita ta kofar sirrin su dake ta bayan wajen lambun daddy, zuba masa dara daran ido sa Romeo yayi yana kallon yadda yake lallaɓawa alamar mara gaskiya

Ganin zai fice ne yasa Romeo yayi sauri Juyawa ya komo cikin ɗaki, ya shige dressing room nasa yana tunanin ina James zai je a daren nan da zai fita ta kofar sirri sannan kuma ba tare da motar sa zai fita ba, satar hanya zai yi kenan ko me.

Jim kaɗan Romeo ya fito sanye da takalmi Booth baki mai shegen kyau a kafar sa, sannan ya sanya face mask a fiskar sa tare da hand gloves a hannun sa, ya sa bakin glass a idon sa, a takaice baka iya ganin komai nasa kuma ba zaka gane wanene ba, wayar sa ya ɗauka da sauri ya nufi waje dan yabi bayan James.

Yana fitowa Palon sa sukayo ya karo da Michael yana kokarin shigowa, baya kaɗan Michael yayi ya bashi hanya, da sauri Romeo ya fice ba tare da ya kallin in da Michael ɗin yake ba, bin sa da ido Michael yayi yana mamakin ina zai je yake wannan saurin.

Sai da Romeo ya kurewa ganin Michael sannan ya wuce ya karisa cikin bedroom ɗin, yana shiga ya faɗa saman lallausan katafaren bed ɗin Romeo yana wani sauke ajiyar zuciya.

A hankali ya kai hannun sa ya kwance diamond watch nasu na Triplets dake hannun sa yana kokarin ɗaurawa saman bedside drawer kwatsam idon sa ya sauka a bayan watch ɗin, ganin wajen yayi tamkar anyi ajiya a wajen.

Matso da agogon yayi sai tin fiskarsa ya zubawa agogon ido na yan mintoci kafin ya kai hannun sa ya zaro abun da idon sa ke gane masa, memory card ne guda biyu wadda James ya ajiye cikin agogon, sosai Michael ya sha ruwan mamaki tare da shiga ruɗun waye ya sa masa wannan memory's ɗin a cikin agogon sa, sai dai abun da bai sani ba wannan ɗin agogon James ne ba na shi ba

Ɗayan hannun sa ya kai ya jawo laptop ɗin Romeo dake saman bedside drawer ya kawo gaban sa, kunna wutar screen ɗin yayi tare da cire password, kasan cewar already ya san password ɗin, nan fa idon sa yayi masa arba da abun da ya kara jefa kwakwalwan sa a cikin ruɗani, da sauri ya kara waro brown eyes nasa waje dan ganin abun da yake gani gaskiya ne

tabbas idon sa gaskiya yake gane masa, kofar gidan mum ɗin sune Romeo ya sanyawa camera dan yaga masu shiga da masu fita, Michael yayi mamaki over, kenan duk wannan kiyayya da tsana da Romeo ke nunawa mahaifiyar su yana bata kulawa da kariya to yaushe ya fara yin hakan, da sauri Michael ya fara tariye camera'n baya dan yaga yaushe hakan ta fara faruwa bai sani ba, sai yaga ashe ɗazun ba jimawa aka sa camera'n bata ɗauki abubuwa da yawa ba, yasha mamaki sosai, fita wajen gaba ɗaya yayi ya ɗauko card reader a cikin bedside drawer ya sanya memory card guda ɗaya daga cikin biyun da ya fitar, ɗayan kuma ya ajiye saman laptop ɗin

Sanya card reader yayi a laptop ɗin ya fara duba memory dan yaga menene a ciki ko zai gane waye ya sa masa memory's ɗin a jikin agogon sa.

Bayanai ne na duk wani abubuwan har kallan su James, bayanai ne na daga in da suke sayo makamai har in da suke sayarwa, duk wani sheɗanci da suke yana cikin wannan memory, ga kuma hotonan manya manyan jiga jigan yan ta'addan na duniya, wasu ma ba wanda ya taɓa ganin hoton su, sai sunan su na ta'addanci kawai aka sani, sunyi kaurin suna wajen ta'addancin amma James yana da hotonan su duka, kasan cewar shi Micheal ba wani karatu ya tsaya yayi ba, sai bai gane komai da ke rubuce a wajen ba, kawai kallon rubutun yake, sai dai ya shiga folder nan ya fita ya shiga wannan amma ba wani abu da ya fahimtar, ga bayanan da gomnati da kuma Romeo suke nema ruwa a jallo Michael ya same su a ɓagas amma ba abun da ya fahimtar, kallon shirme ma yakewa bayanai dan rashin karatu, ba abun da ya iya karantawa aciki.

Da yaga sai gayyan rubutu ne a wajen sai ya cire memory card ɗin, kamar zai sanya ɗayan memory ma ya gani, sai ya fasa ya kwashe su ya mai dasu cikin watch ɗin yana faɗin "Bari lion ya dawo na bashi na tambaye shi ko dai nashi ne shiya ajiye a wajen" da wannan tunanin ya mai da laptop ɗin saman drawer ya kwata yana kallon sama, kamar mai tunani.

Abun da Michael bai sani ba shine ɗayan memory card ɗin videos ne makare a ciki na yadda suke shirya ta'addancin su har yadda James ke canza fiska ya shiga cikin yan ta'addan yayiwa kan sa video yana cikin ɗayan memory da Michael ɗin ya fasa sawa cikin laptop ɗin

A ɓangaren su Romeo kuwa, shima ta kofar sirrin yabi ba tare da ya bari wani soja ya lura da fitar sa ba, dan bai son kowa yasan meke faruwa, idan ma wani abu James ke aikatawa to bai son kowa ya sani sai shi kaɗai, dan in wani yasan James na aika ta ba dai'dai ba maganar ba zata tsaya iya nan ba shiyasa yayi fitar sirri shima ko mota bai ɗauka ba.

Sai sauri James yake Romeo na biye da shi a baya ba tare da ya sani ba, dan akoi tazara mai ɗan nisa a tsakanin su, saboda James ya riga Romeo fitowa.

Sai da James ya fita daga anguwar su gaba ɗaya sannan ya nemi motar haya ya hau, shima Romeo karo na farko daya fara hawa motar haya, kaɗan kaɗan yacewa mai motar hayan nasa ya tafi a hankali kar James ya gansu.

Suna cikin tafiya ne wata babban mota irin mai kwantena a bayan nan, irin na ɗaukan kaya tazo a guje saura kaɗan tabi ba kan motar su Romeo, kasan cewar hanyar akoi fitullun kan hanya masu bala'i haske, sun haske ko ina hakan ya bawa Romeo damar ganin motar da kyau, kasa kasa yace da driver motar hayan ya dakatar da mota, dan bai yarda da wancan motar da ta wuce su ba dan yadda take wannan uban gudu alamar rashin gaskiya ne, gashi kuma yana son bin bayan James, amma yafi son bin wancan motar saboda yasan ko ba komai dole James zai dawo gida kuma in ya dawo dole ya faɗa masa in da yaje, ita kuma motar idan ya barta ta tafi ba lallai ya sake ganin taba, dan haka sai yace da driver motar hayan daya juya subi wancan motar.

Ba musu driver ya juya duk da bai san waye ya ɗauko a cikin taxi ɗin nasa ba, sosai wancan motar ke tsala gudu a kan hanya duk da girman ta, hakan yasa Romeo ya kara zargin motar sosai da sosai.

Dai dai wani check point na kan hanya wasu yan sanda dake tsayawa a wajen suka dakatar da motar, shima Romeo dakatar da mai taxi ɗin sa yayi ya fito yace wa mai taxi ɗin "I'm coming" ya nufi wajen motar can, dai dai lokacin driver motar ya bawa ɗan sandan cin hanci, ba tare da yan sandan sun binciki motar ba sukace motar ta wuce dan sun karɓi cin hanci.

Driver ya koma cikin motar yana kokarin tada motar Romeo bai yi wata wata ba ya fisgo driver motar yayi wurgi da shi waje, cikin sauri sauran dake cikin gaban motar suka fito, su biyu ne, da ka gansu kaga rikakkun yan daba, ga jikin sunan duk tabon shatin yan kan wuka,

Saboda jacket da ya sa ya kuma saka hular a hansa ga face mask da glass a fiskar sa gashi dare ne hakan yasa har yan sandan dake wajen basu gane shi ba.

A guje wayan nan yan daba biyun sukayi kan sa da nufin dukan sa, duk kan su duka ɗai'ɗai ya musu suka zube kasa kamar wasu kayan wanki

Abun ku da rashin gaskiya irin na duniyar yanzu, sai yan sandan dake wajen suka ciro bindigu suka saita Romeo da shi wai ya ɗaga hannu sama ko su harbesa a kan me zai daki wayan nan mutane, saboda sun basu cin hanci yasa suke wannan hargagin, hakan da yan sandan sukawa Romeo yasa ya kara zargin su ya kara sawa a ransa kenan kullun motar tana wuce suna bata hanya kenan.

Bai ɗaga hannun sa ba sai ya juyo yana kallon yan sandan, sun dage zasu harbe sa idan bai ɗaga hannu ba, a hankali ya ɗago kafar sa ya fara tinkarar su, sai kokarin harbin sa suke amma bindigar taki harbi saboda tsorata da sukayi jikin su nata kerma sun kasa danna kunamar bindigar da kyau, ɗaya daga cikin sune ya kira wayar over over akan a karo musu yan sanda ga ɗan ta'adda sun kama yana kokarin yi musu illah.

Wannan danganta Romeo da ɗan ta'adda da sukayi hakan ya ɓata masa rai a fusace ya kwace bindugun hannun su, ya musu dukan tsiya, wadda ya sasu sumewa a wajen, da farko bai yi niyar dukan su ba, a matsayin su na jami'an tsaron yaso ya sa a cire musu kakin sune ma'ana a kore su daga aiki sannan a basu hukunci dan sune ɓata garin tun da su suke karɓan cin hanci su bar masu laifi su gudu, amma danganta shi da ɗan ta'adda da sukayi yasa ransa ya ɓaci ya musu dukan kawo wuka duk ya fashe musu fuska, shi kuwa driver taxi daya kawo Romeo tuni ya juya kan motar sa ya gudu, yaga Romeo na dukan yan daban nan kar ya shafesa dan shima bai san wa ya ɗauko a taxi ɗin nasa ba, shima cewa yake ko dai ɗan ta'adda ya ɗauko ne.

Daman yan sanda uku ne a wajen lilis Romeo ya musu da duka, sannan ya ɗauki bindigar ɗaya daga cikin su yana kokarin

Please Login or Register in order to submit comment