Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[08/10, 2:50 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                   💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._













             *NO_1 & 2*

             *RIYADH NORTH*
         Hannun ta riƙe da bairo tana juya wa a kan book ɗin but ta kasa rubuta komi, tunani ne sosai a ranta wanda ya hana ta saƙat, shin yaushe ne zata kasance cikin farin ciki? Har yaushe ne komi zai wuce a rayuwar ta? Komi ya koma mata kamar baya? Idan ta zauna tana irin waɗannan tunanin sai taji da ace ba'a haife ta ba...

            Faɗin da bairon nata yayi ne ya sanya ta dawo cikin hayyacin ta, idanun ta a kan bairon amma ba ta da alamun ɗauka, sai ta tsira mishi Sexy eyes ɗin ta a ɗan soconni kafin ta janye su tana jan ajiyan zuciya, lumshe idanun tayi a lokaci ɗaya tana buɗe su, ko kaɗan fuskar ta babu ɗigon fara'a wanda dama ta jima rabon da ta ganta cikin farin ciki, idan kuwa ka ga tayi murmushi sai dai tana gaban Abee ɗin ta ne, wannan kuma domin farin cikin shi take yi, ba ya ga haka babu wanda ke ganin dariyan ta bare murmushin ta a yanzu, ko yaushe a yanayi ɗaya take, walau farin ciki ko baƙin ciki, abin har ya zame mata jiki

Tashi tayi tana saka room silifers ɗin ta da ta zame su daga ƙafafun ta, sai ta taka a hankali ta nufi bakin windown ɗakin ta, hannayen ta ta sanya ta zuge cootin ɗin wanda haske ya bayyana a cikin ɗakin da ada babu, kanannaɗe hannayen ta tayi a ƙirji tana bin wajen da kallo, yayinda ta faɗa duniyar tunanin da ya zame mata jiki ko yaushe, tana tuna abubuwan dake faruwa a rayuwar ta

Daga ita sai guntun riga me ruwan Powder, dressed sleeping ne, sai gashin ta da ta ɗaure shi a ƙasan ƙeyanta ta sanya baƙin hula me kauri wanda ya fito mata da tuntun gashin nata, har kunnen ta ta rufe a cikin hulan wanda da alamu garin da akwai sanyi ne, duk da haka be sa ta sanya kayan sanyi ba, illa hulan dake kanta na sanyin, kuma ba wai don ba ta jin sanyin ba, sai dai ta saba da yanayin ne.

          Ta jima a nan a tsaye kafin ta janye idanun ta tana wuce wa cikin Toilet, wanka tayi ta fito ɗaure da Towel a jikin ta, a lokacin ne ake mata Nocking a bakin ƙofar ta

"Na'am". Tace tana me zama gaban dressing mirror

Buɗe ƙofan aka yi wata budurwa ta shigo da uniform a jikin ta, da alamun ƴar aiki ne don sai da ta duƙa ta gaishe ta kafin cikin harshen larabci tace, "ji'itu liru'uyatiki, li'annani ƙultu laki lah takruj".
( "dama na zo duba ki ne saboda naji ki shiru baki fito ba".)

Bata kalle ta ba ta bata iznin tafiya

Sai ta tashi ta fice

Ita kuma lotion ta shafa a jikin ta tare da Powder, sai ta miƙe ta nufi wardrobe ɗin ta, buɗe wa tayi ta ciro kayan da zata saka, ta shirya cikin riga da wando masu taushi brown color, sai ta ɗaura after dress baƙi sannan ta yane kanta da gyalen shi, flet shoes ta saka a ƙafafuwan ta sannan ta ɗauki handbag ɗin ta ta fito. Steps ta taka ta sauka ƙasa ta nufi ɗaya daga cikin ɗakunan

Bata kai da shiga ba wata mata ta fito tana sanye da fararen kaya, da alamu Nurse CE ita

Sai ta kalle ta tace, "Abee".

Murmushi matar tayi mata tace, "jasadahu khafifun jiddan, wal'aán huwa naà'im". ("jikin shi da sauƙi sosai, yanzu haka ya samu barci ne".)

Bata ce komi ba ta ɗago hannun ta tana duba wrist watch ɗin ta, sai kuma ta juya ta nufi kan dainning, zama tayi tana ajiye handbag ɗin ta saman dainning ɗin, sai ta saka hannu ta janyo Cup ta haɗa tea rabin Cup, ta soma sha a hankali duk da akwai zafi, sai dai hakan be dame ta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama tana miƙe wa tsaye

A lokacin ne Nurse ɗin nan ta fito daga kichen riƙe da faɗeɗen bowl a hannun ta

Fuska ba walwala kamar ko yaushe tace da ita, "a'atani bihi jiddan min fadlik". ("ki kula dashi Please".) Bata jira cewar ta ba ta juya tayi hanyar fita, tana fita compound ɗin gidan ta shiga motan ta ta fice. Tafiyan mintuna goma ya kaita cikin school ɗin su, kai tsaye department ɗin su ta wuce, tana yin parking ta fito ta wuce class ɗin su

A lokacin babu wasu mutane a ciki sosai, sai ta samu wuri ta zauna a gaba ta ciro wani book tana duba wa

Har Malamin ya shigo ya soma musu karatu babu wasu mutane sosai

Hankalin ta na kan malamin har ya gama ya fita

Time ɗin ne waɗanda ke gefen ta suka samu damar mata magana, Esha ce tace, "Hello, my beauty, are you already here today?" Ta ƙare maganar tana murmushi

Ɗago kai tayi ta kalle su, memakon ta bata amsar sai tace, "where is Zamiya?"

"Today she will not come". Cewar Ummu Hani

"Why? But she didn't inform me?"

Ummu Hani Said, "you know the pain she is going through, today she is suffering."

"Let's go check on her before the teacher comes in."

"Ok".

Suka tashi su ukun suka fice, kai tsaye Hostel ɗin makarantan suka wuce, room ɗin da Zamiya take suka nufa, until they were Nocking before she opened it for them

Seeing them, she jumped up and hugged them happily

Esha na dariya tace, "Oh are you okay? Let's go back".

Hararan ta Zamiya tayi tana turo baki tace, "wlh I don't feel comfortable, glad to see you".

Duk dariya suka yi ban da Meema dake bin su da kallo, duk da a ranta tana jin farin ciki, amma kuma baza ta iya nuna shi a fuska ba

"Let's come in". Tace dasu tana yin gaba

Zama suka yi a kan sofa, inda Zamiya ta dubi Meema tace, "My Beauty What about Abee's Body?"

"Alhmadulillah easily".

Ummu Hani Said, "By the way, we forgot we didn't hurt him. Please I'm sorry."

"It's alright". Cewar Meema tana duba wayan ta, sai kuma ta ɗago tana kallon Zamiya tace, "what about your body?"

"Alhmadulillah, I was relieved. I wanted to go to school but I didn't get a chance."

Esha said, "Did you hear anything. You don't care about your body, do you?"

Tana dariya Zamiya tace, "Allah has made it easy for me. Let's get ready and go together."

"You are not enough wlh, you will not follow us". Esha tace hakan tana hararan ta

Ummu Hani na dariya tace, "where is your water? It's easy for her, please let her go."

"is what I see like her body". Zamiya tafaɗa tana dariyan itama

"Get up and let's go". Cewar Meema

"No there is still time for us Meema, sorry stay please?" Tayi maganar da marairaice fuska

Kallon ta Meema tayi tace, "We're going to be late for class. It's too late for us to leave, but we'll be back soon, God willing."

"Yeah then, but what can I cook for you?"

Esha tayi tsagal tace, "How are you Can you cook for us? "No, we forgive you."

"I can wlh". Zamiya Tayi maganar cikin shagwaɓa

Dariya Ummu Hani tayi tace, "The king of racism is not in front of Ummee you are".

Cike da gajiya wa Meema dake kallon su suna dariya tace, "let's go please".

Sallama suka yi mata suka bi bayan Meema da har ta fice ma, ita kuma Zamiya ta rako su har bakin ƙofan ɗakin ta sannan ta koma

Suna fita wayan Meema ta soma ringing, ɗago wa tayi tana kallo sai taja tsaki tana sauke hannun ta ƙasa suka ci gaba da tafiya

Esha da ba ta iya shiru tace, "Is that Ishaq?"

Meema bata kalle ta ba bare ta tanka ta

Sai ita kuma ta sake cewa, "but why do you want to change him? Please don't let your worries affect your love, you are suffering a lot from it, Please do peacking you see he calls again".

"Hmm". Kawai Meema tace bata kula ta ba

Ummu Hani Said, "here he is".

Duk ɗaga kai suka yi suna kallon inda Ummu Hani take kallo

Wani kyakykyawar Balaraben saurayi ne tafe zuwa wajen su, fuskar shi ɗauke da yalwataccen murmushi ya iso wajen su

Daga Ummu Hani har Esha tsaya wa suka yi wajen sa suna amsa sallaman da yayi musu

Ita kuwa Meema har ta yi gaba zata wuce, sai Esha ta janyo ta baya tana cewa, "Please O'o Meema".

Hararan ta Meema tayi bayan ta dakata daga inda take

Shi kuwa kallon ta kawai yake yi yana doka murmushi

Esha says, "we'll pass the class, when you're done find us in class".

Daga haka suka yi gaba ita da Ummu Hani

Kanta a ƙasa bata kalli inda yake ba

Hakan yasa ya ƙarisa kusa da ita ya tsaya yana faman kallon ta, sun ci mintuna biyu babu wanda ya furta komi

Sai ta ɗago kanta ta zuba masa idanun ta, ganin kallon da yake yi mata sai ta balla masa harara tana cewa, "Please I will be late for class. "

Cikin sanyin muryan sa yace, "why Beauty did you change me? Wlh I really love you! Why do you want to part with me?"

Cikin ido take kallon shi yayinda ta sake ɗaure kyakykyawar fuskar ta tamau kafin tace, "please let's stop saying that now, let's do it later".

"No, I do not agree. I cannot leave here unless you answer my questions. You know that I love you and this decision you have taken has made me very sad. How do you think I can part with you after tasting your honey love? Wlh I love you Meema, if you want I will kneel in front of you because I will apologize". Ya ƙare maganar kamar zai yi kuka

Itama fuskar ta da alamun gajiya wa in a calm voice she said, "I told you we will talk later. Please let Me go".

"Ok When?"

Dafe goshi tayi tana kallon sa tace, "Ishaq problems".

Dariya yayi yace, "on your love I am crazy".

Taɓe baki tayi kafin tace dashi, "by tomorrow insha Allah". Tana gama faɗar haka ta wuce ta bar shi nan. Kai tsaye aji ta wuce, tana zama malamin da suke dashi ya shigo class ɗin.




              Zuwa ɗaya suka sami break, sai suka wuce Hostel wajen Zamiya, a can suka yi sallah suka ci abincin da ta girka musu, sai faman hira suke yi suna dariya amma banda Meema da sai jefi-jefi take saka musu baki.

              Three O.clock suka koma class suka yi lecture ɗaya, sannan kowa ya wuce gida.

               Meema na koma wa gida tayi parcking ta fito tayi cikin gidan, gaba ɗaya a gajiye take amma hakan be sa da ta shiga ta wuce ɗakin ta ba, ɗakin Abee ta wuce ta shiga da sallama

Nurse ɗin dake kula dashi ta amsa mata sallaman tana faɗaɗa fara'an ta tare da mata maraba

Da kallo kawai ta bi su daga ita har Abee ɗin nata ta kasa amsa wa, sai dai gaba ɗaya fuskar ta ta sake haɗe wa ganin ta da poo a hannun ta, "taya ma za'a ce wata ce zata riƙa kula da mahaifin ta a irin wannan yanayin?.."

Muryan Abee ɗin ta da ya ratsa mata kunnuwa yasa ta ƙifta idanun ta da suka kawo ruwan hawaye, cike da ƙunci a zuciyar ta ta ƙarisa wajen sa

While Nurse Zara tuni ta shige Toilet don plushing kashin da yayi

A gaban gadon ta durƙusa tana kallon sa, sai ta saka hannayen ta ta kamo nashi hannun guda ɗaya, cikin rawan murya tace, "Abee.."

Murmushi ya sakar mata a hankali yace, "Ummy why are you crying?"

"Nothing Abee, I'm not crying". Ta ƙare maganar hawayen ta na silalo mata saman kunci

Girgiza mata kansa yake yi, cike da raunin murya na wanda ciwo yaci sosai yace, "Please Ummy I beg you to stop crying ok? I'm not happy to see your tears."

Tamke bakin ta tayi tana saka hannu biyu ta share hawayen tana faɗin, "ok Abee I'm stop, you see?" Sai ta ƙare maganar da sakin murmushin da ya bayyana jerin ƙananun fararen haƙoran ta, wanda har dumples ɗin ta suka samu damar fito wa

"Ok, did you go to school today?"

"Na'am Abee, I went to school, but I'm sorry I didn't come in to check on you. "

Murmushi yayi yana gyaɗa kansa yace, "don't worries, go eat and rest ok?"

Amsa mishi tayi kafin ta ɗago hannun nasa a hankali ta sumbace sa, sannan ta tashi daga durƙuson da tayi, a time ɗin ne Nurse Zara ta fito daga Toilet ɗin, kallo ɗaya Meema tayi mata ta ɗauke kai tana fice wa

Ita kuma Nurse Zara ta gyara mishi pilown da ya sauke kansa, sannan ta tambaye sa "ko da abinda yake buƙata kuma?"

Girgiza mata kai kawai yayi

Sai ta juya ta ɗauko airfreshna ta fesa a ko ina sabida warin kashin da ya ɗuma ɗakin ya fice, bayan ta gama ta fice a ɗakin.






                  ******

               Da kuka Meema ta koma ɗakin ta, tana shiga ta faɗa kan gado tana ci gaba da rera kukan nata, wanda inda da sabo ya rigada ya zame mata jiki, a kullum tausayin Mahaifin nata ƙara yawa yake yi a zuciyar ta, ta kasa saba wa da wannan ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa, kullum gani take yi tamkar zai tashi ya koma kamar da, ya riƙa mata wasa kamar yanda ya saba yin mata, su riƙa cin abinci tare suna wasa da dariya tare, amma kuma ciwo ya yanke mata wannan ƙauna da jin daɗin, wanda tana ganin babu ranan da zata sake shiga cikin farin ciki idan har ba mahaifin ta bane ya warke ya koma kamar da ba, ba ta ganin akwai ranan da walwala da jin daɗin ta zai dawo

Hawayen ta ta saka hannu tana share wa yayinda wasu suke sake ɓullo mata, babu abinda ke sake bata haushi illa yanda mahaifiyar ta ta kasa kula da Abee ɗin ta, sai wata ce take iya cin kashin sa taci fitsarin sa, sannan kuma ta ƙetara muhallin da ba nata ba, a kullum sake jin tsanar mahaifiyar ta take yi, tana ganin kamar har da baƙin cikin ta Abee ɗin ta ya kasa samun lafiya, ko da be faɗa mata ba ta san yanda yake jin ƙuna da azaban tafiyan ta, ta zaɓi son duniya da son zuciya ta rabu da su, a kan abinda be taka kara ya karya ba, ita a ganin ta babu mahaifiyar da zata tafi ta bar ɗiyar ta da mijin ta a halin ƙunci da neman taimako, mahaifiyar ta ba mutum bace, kuma bata da zuciyar imani

Fashewa tayi da wani sabon kukan, cikin tsananin ƙunan zuciya tace, "I hate you so much Ummee! I hate you!! I hate youuuu". Hannu ta sa ta rufe fuskar ta, in slow voice tace, "Why Ummee? Why did you leave us?". Ta jima tana kukan wanda har kanta ya ɗau zugin zafi, sannan ta dakata tana tashi ta zame kayan ta ta shiga Toilet, wanka tayi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallan Asar bayan ta saka shimi iya gwiwa da dogon Hijab, tana idar wa ta ɗaga hannu ta soma kwararo addu'o'i tana kuka, gaba ɗaya duk wani addu'ar ta yanzu nema wa Abee ɗin ta lafiya take yi, domin shi ne farin cikin ta a yanzu, idan har babu shi haƙiƙa ba ta ba sake farin ciki a duniya.



            House girl ɗin su ne ta shigo da sallama

Hakan yasa ta dakatar da addu'ar nata tana shafa wa a fuskar ta, sannan ta sauke kumburarrun idanun ta a kan ta ba tare da tace mata komi ba illa amsa sallaman da tayi a ranta

"Sayyadaty, hunaki duyuufu fiis saàlun, jaà'uu ila Abee". ("Ma'am akwai baƙi a Parlour, sun zo wajen Abee ne".)

Jimm MEEMA tayi har a lokacin tana kallon ta, sai kuma tace, "izhab wa'as'al man hum?" ("Je ki tambaya su wane ne?")

"Ok Ma'am". Ta miƙe da nufin fice wa

Sai kuma ta dakatar da ita tana ce mata, "Ƙaàlat lahum an yaruûhaà huna". ("tace musu ga ta nan.")

Bayan ta fita sai ta tashi ta zare Hijab ɗin jikin ta, daga ita sai shimin jikin ta sannan ta zira room slippers a ƙafafuwan ta ta fice, tana sauka downstairs ta hange su su biyu a cikin parlour'n, bata gane ko su wane ne ba sai da ta iso gab da su sannan fuskokin su suka yi mata maraba, baza ta taɓa manta waɗannan mutanen ba, duk da kusan shekaru shida kenan rabon su da tako wannan ƙasan, yayyin mahaifin ta ne dake zaune a Nigeria da suka haɗa uba ɗaya, waɗanda suka watsar da su suka raba hanya da su, saboda tsantsan tsanar da suka yiwa mahaifin ta, shiyasa ma ko zuwa nan ɗin ba sa yi.

             Tana isowa tabi su da kallo hannayen ta a ƙugu, ko ba'a faɗa mata ba ta san ba arziƙi ya kawo su ba kamar yanda suka saba zuwa a shekarun baya, tunda su ko kaɗan basu da mutunci, shiyasa itama yanda take ji a ranta duk abinda suka zo dashi tana dai-dai dasu, zuciyar ta sosai take mata ƙunci baza ta taɓa raga musu ba idan har za su taɓa mata Abee

Wanda yake shi ne Babba ya soma magana da faɗin, "ke baki da kunya ne zaki zo ki tsaya mana akai dan uban ki?"

Sai ɗayan yace, "taya zaka tambayi kunya a nan Yaya bayan ka ga yanda tazo mana a tsatstsaye tana turo mana ƙirji? Ai daga gani ka san babu kunya domin Faruk be koya mata ba, shiyasa yaƙi yarda ya koma ƙasar sa tunda ya san abinda yake faman yi a nan. Yanzu dan ubanki ke da kika zo gaban mu kika yi ƙere-ƙere rashin kunya zaki yi mana ko me? Uban naki shi ne dai-dai damu ba ke ba".

Duk maganganun da suke faɗa ko ɗaya MEEMA bata ji su ba domin ba ta jin Hausa. kuma su ma sun san da hakan; amma dayake tsiya yaci ransu shiyasa suke ta maganar ba tare da sun tuna ba

She then said to them, "what are you saying I do not hear you".

Tsaki Yaya Ali yaja yana cewa, "matsiyaciya ubanki muka ce shegiya.." sai kuma ya juya harshe cikin turanci yace, "ina shi uban naki muka ce?"

Wani kallon banza ta watsa musu kafin tace, "He is not here, what you want?"

Salati suka saki lokaci ɗaya suna kallon ta

"Yanzu Zulaiha mu kike faɗa wa wannan maganar? Yanzu har idanun ki sun buɗe da zaki yi mana rashin kunya a matsayin mu na Yayyin ubanki? Tirƙashi.." cewar Yaya Ali cikin harshen turanci

Ita kuwa bata ma tsaya sake jin ta bakin su ba ta juya zata wuce

Sai Zubairu ya kwaɗa mata kira, "Zulaiha.. Zulaiha".

Amma ko juyo wa bata yi ba ta haye Steps da gudu tayi ɗakin ta, kan gadon ta ta haye tana ɗaukan wayan ta ta soma Game cikin sauri-sauri, sosai ranta ke a matuƙar ɓace shiyasa ta kasa controling kanta tsaban yanda ranta ke ƙuna, sai kuma ta jefar da wayan a saman gadon tana miƙe wa da sauri, fita tayi da gudu ta nufi downstairs, ganin babu su a parlour'n sai ta nufi ɗakin Mahaifin ta da sauri ta bankaɗa ƙofan da ƙarfi

Yaya Ali da Zubairu dake gaban gadon da Abee yake kwance sun tasa shi gaba suna ta tsitsiye shi da bala'i duk da kuwa sun ga mawuyacin halin da yake ciki, hakan be sa sun dakata daga amayar masa da tijaran da suka ɗibo ba, ko tausayi babu a lamarin su. Buɗe ƙofan da MEEMA tayi ne sai duk suka tsaya suna mayar da kallon su kan ƙofan, inda suka sauke idanuwan su kanta da itama take bin su da kallo idanuwan ta sun kaɗa sun yi jawur tsaban ɓacin rai.
[08/10, 2:51 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
               💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*





          *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._













                 *NO_ 3 & 4*

     Gaba ɗaya idanuwan ta sun rufe ta manta da cewa su ɗin ƴan uwan mahaifin ta ne, ta nufi ciki a zuciye tana cewa, "what are you doing here What brings you to my Abee room? Get out .. get out..."

Zubairu ne ya dage ya falla mata marin da sai da yasa ta duƙe a wajen tana tsandara ihu

Daga Nurse Zara da House girl ɗin su dake Parlour sun yi cirko-cirko sai da suka tsorata saboda ihun MEEMA da suka ji, musamman ma Nurse Zara tunda bata san su ba sai House girl ɗin ne tayi mata bayani da suka nemi shiga ɗakin Abee zata hana su, dayake ita ta san su tun shekarun baya da suke zuwa.

   

Please Login or Register in order to submit comment