Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

illa shirun da taci gaba da yi

Sai yace, "Weldon, I hope I didn't bother you calling you last night?"

Duk da ta gane shi but hakan be sa tace, "But to whom am I talking?"

Shafa kansa yayi a hankali ya furta, "Are you talking to Umar Faruk, hope now you understand Me?"

Still shiru tayi

Sai yace, "Do you still understand MEEMA?"

Jin yanda ya kira sunan ta yasa ta lumshe idanuwan ta tana zamewa a kan gadon ta kwanta, still she's silent

Hakan sai ya saka jikinsa yayi sanyi sosai, a hankali ya sake furta sunan ta

"Na'am." She answered him briefly

"I don't know why you don't want to talk to me. Does that mean you don't need me in your life? Tell me the truth."

Shiru ta sake yi tana jin zuciyar ta na bugawa sosai fiye da sanda ta gane shi ne

"I know I'm restricting you but I'm sorry please, Don't say I'm bothering you That's not my nature, but I'm in a political situation. But I have nothing to worry about, I look forward to seeing you whenever you want to let me know."

 
MEEMA rufe idanun ta kawai tayi tana sauraron muryan nashi wanda ke ratsa mata can cikin kunnuwa yana saukar mata da kasala da wani irin yanayi a jiki

"MEEMA." Ya kira sunan ta in a slowly

Buɗe ido tayi a hankali tana amsa mishi

"I restrict you with my words?"

"Laà."

Sai ya ja numfashi yace, "ok but did you allow me to call you? I don't want to restrict you because I am a person who does not want to restricted."

Shiru tayi kamar baza tayi magana ba sai tace, "Na'am."

"Ok thanks. I will let you rest until tomorrow. Sleep well, dream of me please."

Wani abu ne ta ji ya tsarga mata, tayi saurin mayar da idanun ta tana sauke numfashi

Shi kuma jin tayi shiru sai yayi mata sallama ya kashe wayan. Ajiye wa yayi yana saka hannu a fuskar sa ya shafo sajen sa yana me lumshe idanu, kyakykyawar fuskar ta kawai yake hango wa hakan yasa ya saki murmushi a hankali, sai ya gyara kwanciyar sa yana buɗe idanun sa ya kafa wa wuri ɗaya ido. Tunani yayi masa yawa dole ya miƙe zaune ya buga tagumi, sai kuma can ya koma ya kwanta yana mayar da idanun sa ya rufe still haka ya ci gaba da tunanin ta a ranshi.










                   "*****

           MEEMA kuma tunda ya kashe wayan itama ta kasa motsi, idanun ta a rufe har sai da ta ɗauki kusan mintuna ashirin a haka kafin ta tashi ta gyara kwanciyar ta sosai ta haye kan gadon, duk yanda ta so ta cire tunanin sa tayi barcin ta but ta kasa. Sai dai ɓarawo barci daga baya ya zo ya sure ta cike da mafarkin Umar Faruk.
[14/10, 10:05 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*



*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
















*NO_29*

*THE FOLLOWING DAY*
MEEMA tana tashi da safe da text ɗin Umar Faruk ta soma cin karo, haka kawai sai ta ji farin ciki ya ziyarci zuciyar ta, ta karanta text ɗin ya fi sau uku, yanda ya nuna kulawar sa a kanta da yanda ya damu da ita sosai ya saka ta farin ciki, shiyasa gaba ɗaya a lokacin ta ji ta a wani irin yanayi na nishaɗi wadda ta kasa gane meye ya saka ta wannan farin cikin sosai haka, duk da gefe ɗaya kuma tana jin wani irin faɗuwar gaba. shirin ta take yi but tunanin ta na a kanshi, har ta gama shiryawa yau ta sanja shiga, haka kawai yau take son saka kayan hausawa kasancewar tunda aka ɗinko mata bata taɓa amfani da ko ɗaya ba, atamfa ce kalan ruwan madara sai aka yi amfani da ja da baƙi wajen design ɗin flower, ɗinkin riga da skert ne da suka kama ta cif kasancewar ta me diri tubarakalla, sosai kayan suka yi mata kyau suka sake haska skin ɗin ta, ita kanta ta kasa ɗauke kai daga kallon surar jikin ta sabida yanda kayan suka yi mata kyau, sai juyi take yi a gaban mirror tana ƙara kallon kanta, murmushin kan fuskar ta ya kasa gushe wa still sai juyi take yi, sai da ta gaji don kanta kana ta ɗauki ɗankwalin da ninyan ɗaurawa, sai dai duk yanda ta so ta ɗaura ɗin ta kasa, sai cikuikuiye shi take yi tana ɗaura wa tana kwance wa but ya ƙi mata yanda take so, dole ta haƙura ta gyara gashin ta ta tufke shi a ƙeyan ta, kana ta ɗauki veil ja tayi Rolling da shi ya saukar mata a iya kafaɗa, sai tayi using da black flat shoes da saman ya kasance ja, yanda ta ga kayan sun yi mata ne yasa ta ɗauki after dress tana shirin saka wa, sai kuma tayi shiru tana ɗan tunani idanun ta a kan mirror tana kallon kanta, sai kuma ta mayar ta ajiye ba tare da ta saka ba sannan ta ɗauki Handbag ɗinta ta fice ba tare da ta shafa komi a face ɗin ta ba

Babu kowa a parlour'n kasancewar safiya ne, sai Zabba'u wacce take ta ƙoƙarin shirya Breakfast a saman table. Ganin ta yasa ta washe baki tana cewa,
"wow MEEMA, you look so good, the stuff looks so good to you."

Ita kanta murmushi take zuba wa har ta iso kusa da ita tace, "thanks. Good morning."

"Hope you are feeling well?"

"Alhamdulillah." Tafaɗa tana jan ɗaya daga cikin kujerun dainning ɗin ta zauna. Sannan ta soma haɗa tea

Ita kuma Zabba'u surutu ta soma jan ta dashi a haka har ta gama shirya komi a inda ya dace. Kana ta juya ta koma kichen

While MEEMA sipping tea ɗin take yi a hankali tana ɗan lumshe idanuwan ta, tunani ne a ranta har ta gama shanye tea ɗin ta ajiye sannan ta tashi ta wuce ɗakin Hajiya

Lokacin Hajiya na zaune a saman sallaya tana ta lazimin safe

Da shigar ta ta nufi wajenta tare da kiran sunan ta

Hakan yasa Hajiyan ta sakar mata murmushi tana kallon ta har ta iso ta duƙa a gaban ta

As usuals hannun ta ta kama ta sumbata tana kallon fuskar ta cike da murmushi a face ɗin ta tace, "Grandma good morning."

Sai da ta shafa addu'ar nata kafin tace da ita, "Morning my dear. Today you have done very well, Masha Allah you look so cute."

"Thanks Grandma." Tafaɗa itama tana murmusawa

"You eat breakfast?"

"Na'am grandma. I'm go".

"Ok God help give Luck. Take care of yourself?"

Amsa mata tayi tana sake mata peak a hannun ta kana ta tashi ta fice

While Hajiya ta raka ta da kallo.

Sama ta nufa sabida su gaisa da Uncle Hashim. Kafin ta sauko ne Idris ya shigo gidan, yana zaune a Parlour suna surutu da Zabba'u ta sauko ƙasa

Shima yana ganin ta ya miƙe yana murza idanu, sai ya ɗan soma ɗaga kai Like yana leƙen bayan ta

Ita kuma tsayawa tayi tana kallon sa da mamaki, sai tace, "what you look?"

Waro ido yayi da cewa, "wai You mean like you? A mean MEEMA?"

Murmushi tayi coz ta gane tsokanar sa ne ta motsa

Itama Zabba'u da ke jin su dariya tayi tace, "Today you see her has changed a lot, she has joined us Hausa, she is very beautiful."

Tafa hannayen sa yayi yana matsowa kusa da ita, fuskar sa cike da fara'a yace, "wow my cuty friend! I never thought you were so beautiful until today, have you seen? You've done very very well, You look so cute." Ya ƙare maganar da ɗaura hannun sa a baki ya huro mata kiss 😘

Sosai take dariya a lokacin nan wanda hakan ya bai wa dimples ɗin ta damar fito wa sosai

"I've never seen you laugh beauty. Laughter is so good for you. Please do it ok?" Yafaɗa still yana kallon ta yana murmushi

Bata ce komi ba illa sake ƙawata fuskar ta da smile da tayi

Shi kuma juyawa yayi ga Zabba'u yace, "to ranki ya daɗe! Yau dai bazan ci abincin ki ba sauri muke yi, idan Hajiya ta fito kice ina gaishe ta mu mun tafi."

Tana dariya tace, "kace yau abinci na ya huta da tsegumi? yau babu sharhi. To a dawo lafiya Allah ya tsare."

"Ai kar ki damu yau zan ci na rana a nan don haka ki girka da Ni, ki gode wa Allah ma yau ina sauri but anjima dai zamu haɗe ɗin." Yafaɗa yana yin gaba ya bi MEEMA wacce har ta fice ma.





✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

Gaba ɗaya yau tunda Luwaira ta tashi babu walwala a tattare da ita, idanunta duk sun kaɗa sun yi jawur sabida kukan da ta sha a daren jiya, ga rashin barci da bata samu tayi ba. Shirin ta na school tayi saboda tana son ta je ta rubuta test, ba don haka ba ba ta tunanin zata iya zuwa ko ina a halin da take jin kanta. Koda ta fita Parlour ɗakin Momy ta shiga, ta sanar mata, "zata wuce school".

Kallon ta Momy tayi tace, "ba dai kuka kika yi ba Luwaira?"

Shiru tayi tana ɗauke kanta gefe

Tsira mata idanu tayi na ɗan lokaci kafin ta kaɗa kai da cewa, "kin yi Breakfast ne da zaki tafi?"

"Ba na jin yunwa Momy." Sai ta juya ta fice bata jira cewar ta ba

Ita kuma Momy ta raka ta da kallo har ta fice. A yanda take jin baƙin ciki a zuciyar ta da zata iya cire soyayyar Umar Faruk a zuciyar ƴar ta da tuni ta cire, sosai take baƙin ciki da hakan sai dai babu yanda zata yi, tabbas koda ta saka auren su ya yiwu ba ta jin zata kasa cika burin ta a kansa, dole ne sai ta mallaki komi nashi kafin hankalin ta zai kwanta, dukiyan sa da ƙadarorin sa duk mallakin su ne, ta san ita kanta Luwaira baza ta gane abinda take guje mata ba sai nan gaba. Amma kuma yanzu ta yanke shawaran barin ta ta auri Umar Faruk domin hakan shi ne maslaha a wajen su a kan ya auro wata ya kawo ta cikin gidan nan, inyaso daga baya bayan Luwaira ta haihu da shi sai su kashe shi su mallake komi ya dawo hannun su, a lokacin kuma zata san duk hanyar da zata bi domin fahimtar da Luwaira sannan ta mantar da ita shi a gaba ɗaya rayuwar ta, a lokacin zata auri wanda ya fi shi ta sake sabuwar rayuwa, su kuma burin su ya cika. Numfashi ta ja tana yalwata fuskarta da murmushi, tabbas ta san Umar Faruk yana jin maganar ta idan har ta ba shi umarnin auren Luwaira zai amince, amma ta ina zata bi ta fahimtar da shi ba tare da ya ɗarsa wani abu a cikin zuciyar sa ba?



********

Tana fita mota ta shiga drever ya ja ta zuwa school ɗin su. Koda ta shiga aji ta tarar da Abida tana zaune, sai dai kasancewar tayi latti a lokacin Malamin su ya shigo shiyasa basu yi wani magana ba suka natsu suka mayar da hankalin su kan karatun. Bayan ya fita ne wani ya shigo daga nan ne suka sami break

Abida wacce ta lura da yanayin Luwairan ita ta soma mata magana da tambayar abinda ke damun ta ganin halin da take ciki

Sai kawai Luwaira ta fashe mata da kuka saboda tsananin ƙuncin da ke damun ta

Da sauri ita kuma ta sanya hannu ta kama ta tana faɗin, "Haba Luwaira zaki tara mana mutane ne? Me ke damun ki meye ya saka ki kuka? Please kiyi shiru haka nan ki sanar min."

Daƙyar ta iya tsakaita wa da kukan duk da bata yi shiru duka ba, daƙyar ta buɗe baki take sanar mata da zancen auren Umar Faruk, kana ta ƙara da cewa, "ban san ya zan yi ba Abida, ban san ya zan yi ba muddin ya ƙara aure, wlh ji nake yi kamar zan kashe kai na tsaban ƙunan da nake ji a raina, ina matuƙar ƙaunar sa amma be san ina yi ba, ya zan yi ne?"

Tausayin ta ne sosai ya kama Abida, tabbas so da zafi musamman idan kana yin shi a inda ba'a san ma kana yi ba, hakan ya fi komi ɗaci da tada hankali. Rarrashinta ta soma yi kafin tace, "Ni a nawa shawaran Luwaira ki fito fili ki sanar mishi kina ƙaunar shi, that is the only solution. Idan kika bar abun a ranki be san ma kina yi ba, idan da tun farko kin sanar mishi maybe da tuni be ga wancan ya ce yana so ba, kina fa da duk abinda ɗa namiji zai so ki, Ni a tsari na ba na barin abu ya cutar da Ni don haka dole ke ma ki samu hanya mafi sauƙi ki sanar mishi, sai ki ga me zai ce, idan ya amshi soyayyar ki Fine, Idan kuma be amsa ba dole mu san abin yi, ko ta wani hanya ne zamu bi domin ki samu zuciyar shi, ke ƙawata ce Luwaira zan taimaka miki a duk sanda kike neman taimako, ai yanzu kai ya waye sai mutum ya so yake barin damuwa ta karshi."

Kallon ta Luwaira tayi yayinda idanun ta suke ci gaba da zubar da hawaye tace, "Abida wlh hanya ɗaya ce na san zan samu Umar Faruk cikin sauƙi, muddin Momy ta amince da auren mu na san shima zai amince ko ba ya so na, but She is still silent and refuses to tell me anything and yesterday she told me we would talk."

"To meyasa baza ki same ta kuyi maganar ba? Inaga idan kun zauna kika sanar mata da halin da kike ciki zata fahimce ki, Ni abun yana ɗaure min kai meyasa ba ta son ki da shi ne?"

"Uhmm baza ki gane bane Abida." Sai kuma tayi shiru tana ɗaura kanta a kan deks

Itama Abidan shiru tayi tana kallon ta, sai kuma tace, "idan har baza ki iya zuwa wajen ta kuyi magana ba ni zan je, Let's go together sai in faɗa mata halin da kike ciki."

Ɗago kai Luwaira tayi ta kalle ta, ba dai tace komi ba illa ɗauke kai da tayi tana saka hannu ta soma share hawayen ta

Sai Abidan ta dafa ta tace, "don Allah ki kwantar da hankalin ki, ki bi shawara nan yau ɗin nan ba sai gobe ba ki same shi ki sanar mishi, barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa kina jina?"

"Abida faɗan ba sauƙi ne da shi ba, da ace zan iya tunkaran shi da wannan kalman ai da tuni na daɗe da furta mishi, Umar Faruk ya wuce yanda kike zato, yana da wani irin kwarjini da kamalan da bazan iya tunkaran shi da zancen nan ba, sannan a yanda ya ɗauke Ni yana matuƙar girmama Ni a matsayin ƙanwar sa hakan ke saka wa nake kasa yin komi."

"Haka nan zaki daure ƙawata". Abida tafaɗa tana sake dafa ta, "na tabbata zaki iya, idan ba haka ba wankin hula ne zai kai ki ga dare, shawaran da zan baki kina da Numban shi ki tura mishi a text message, na tabbata zai fahimce ki idan har yana ƙaunar ki, do that please."

Shiru tayi Luwairan tana kallon ta, sai kuma ta gyaɗa kanta tace, "insha Allahu I will try my best. Zan tura mishi zuwa anjima, amma kina ganin zai amince bayan ya sami wacce zai aura?"

Murmushi Abida tayi tace, "ba na tunanin zai ƙi amince wa sabida dole zai fahimci a halin da kike ciki, idan har bazai fasa wancan auren ba sai dai ya haɗa ku duka amma ba na tunanin zai ƙi amince miki, ko don halaccin da Momy tayi masa, ko domin kunyan ta bazai ƙi son ɗiyar ta ba."

Daga haka shawara Abidan ta ci gaba da bata. Har sanda lecturer ya shigo sannan suka dakata suna gyara zaman su tare da ba shi attention ɗin su.



✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

Dariya sosai Laɗifa take sha saboda yanda MEEMA ta dage wajen furta yaren Hausa, tana koya mata ne amma duk kalma ɗaya idan ta faɗa sai ta tuntsire mata da dariya har da riƙe ciki

Tun MEEMAN ba ta kula ta itama tana tayata dariyan har dai ta gaji ta koma hararan ta, ganin ta ƙi denawa sai ta ɓata fuska kamar zata yi kuka tace, "Since you're laughing at me I've stopped learning."

Cikin dariyan Laɗifa tace, "I'm so sorry my dear. Wlh dariyan ne refused to stop, but..." Sai ta kama bakin ta sabida wani sabon dariyan da ya taho mata, daƙyar ta riƙe shi tana murmusawa tace, "But I'm sorry again."

Still fuskarta a turɓune ta balla mata harara tana cewa, "I will not ask you to teach me again since you will laugh at me. I will go to Idris and he will teach me."

Laɗifa bata kai ga yin magana ba wani saurayi yayi Nocking Yana turo ƙofan. Shima ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ne

And they all followed him, watching him

He smiled and said, "Hi how far?"

Laɗifa ta amsa mishi tana cewa, "Brother Idris ya turo ka waje na? I have not finished but I will finish now."

"Eh shi ya turo Ni, amma duk da haka there are strangers who come to MEEMA." Ya ƙare maganar da kallon MEEMAN wacce ta mayar da hankalin ta kan computer tana latsawa

Hakan yasa ta ɗago kai tana kallon sa sai dai bata furta komi ba

Laɗifa tace, "And strangers? Who are they?"

"I don't know wlh, they were outside in the car, they demanded that I call MEEMA saying they would miss a message being sent."

"Ok to zata zo".

Daga haka shi kuma ya fice

Sai Laɗifan ta kalli MEEMA wacce itama ta zuba mata ido tace, "Is there anyone you expect to come to you?"

Girgiza kanta tayi sai kuma tace, "No, no one."

"Ok get up let's go check."

Tashi tayi suka fice tare. Suna fita bakin Gate ɗin suka hangi baƙar mota ƙirar jip a fake, kasancewar glasses ɗin tited ne ba a ganin kowa daga ciki. Kai tsaye wajen motan suka nufa

Sun kusa isa sai wayan Laɗifa tayi Ring, tsayawa tayi a wajen tana peaking call ɗin

Hakan ya bai wa MEEMA damar karisa wa wajen motan tana bin ta da kallo

Sai kawai aka zuge ƙofa wani mutum ya fito da sauri, kafin ƙiftawar minti ɗaya har ya tura MEEMA a cikin motan ya rufe an ja motan a tsiyace

Laɗifa wacce take waya a kan idanun ta komi ya faru, sai dai kasancewar ta shiga shock ko motsi ta kasa sai da suka tafi ne sai ta kwatsa ihu tana bin Bayan motan, tuni ta jefar da wayan hannun ta sai zuba ihu take yi, ganin sun yi mata nisa da gaske ai sai ta zube a wurin tana ɗaura hannaye a kai tana ihun kiran sunan MEEMA

Kankace kobo har tsirarun mutanen da ke wajen sun nufo inda take don a zaton su wani abun ne ya same ta, kasancewar basu san me ta biyo ba shiyasa suke tambayar ta ba'asi?


Hannu kawai take nuna wa ta inda motan ta bi bakin ta na rawa tana kiran sunan MEEMA but sai dai gaba ɗaya muryan ta ba ya fita sabida tsaban ruɗu da tashin hankali.
[14/10, 10:07 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                     💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                   *P.W.A✍️*



               *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._



*SAKAMAKON SALLAH 1*
_Mun sani cewa a shika-shikan musulunci ɗin nan guda biyar bayan imani sai tsayar da sallah. Abdullahi Ibnu Mas'ud ya ce, "Na taɓa tambayar Manzon Allah cewa wane aiki na ɗan Adam Allah ya fi so?" Sai Annabi ya ce, "sallah". Na sake cewa, "daga ita fa?" Sai Annabi ya ce, "kyautata wa iyaye". Na sake cewa, "daga wannan fa?" Sai ya ce, "sai jihadi."_
_Manzon Allah ya taɓa ce ma Abu Zarrin, "in Mutum yayi Sallah domin neman yardar Allah, duk zunuban sa za su zube Kamar yadda ganye yake zubewa daga itace," Abin lura a nan shi ne sallah tana kawar da ƙananan zunubai. Manyan kam sai an tuba. Amma in Allah ya ga dama yana iya yafe sagiran da kaba'iran don sallar da mutum yayi. Amma kuma, ko can ba ayi ma musulmin ƙwarai kallon zai riƙa kuntuka kaba'ir, manyan laifuka. Ban da ma haka duk mai Sallah yakan yi istigfari ne, a ƙarshe ya roƙi Ubangiji ya gafarta masa zunuban sa, manya da ƙanana._
_Abu Sa'id Khudri, Allah ya yarda da shi ya ce, "ya taɓa jin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na cewa: "ko wace ɗaya daga cikin sallolin nan biyar tana kankare zunuban da suke tsakanin ta da wadda ta gabace ta." Bari mu kawo misali da wani wanda aikin sa yake sa yayi butu-butu da ƙura. Akwai ƙoramu guda biyar suna gudana tsakanin gidan sa da inda yake aikin. In ya tashi zuwa gidan yakan yi wanka a kowace ƙorama. To, haka fa sakamakon yin sallolin nan biyar yake. Ana yafe duk wasu kurakurai da zunubai da suke tsakanin salloli biyu saboda istigfari da tuba da ake a kowace sallah._
_Manzon Allah yakan riƙa kawo mana ire-iren misalan nan ne don ya nuna mana irin ƙarfin da sallah take da shi wajen kawar da zunubai. Idan mun yi watsi da jin tausayi na Ubangiji, ba za mu kuka da kowa ba sai kan mu._
_Ba shakka ɗan Adam mai yin kurakurai ne. Muna iya yin ayyuka da dama wa'danda za su saɓa ma Ubangiji, mu kuma gamu da hushin sa da horon sa. Amma kuma mu duba irin jin ƙan da Ubangijin mu yake mamaye mu da shi. Ya nuna mana yadda za mu sadu da rahmar sa da jin ƙan sa. Abin takaici ne ƙwarai a ce mun bari wannan baiwa ta wuce mu, bamu kama ta mun riƙe da hannu bibbiyu ba. Rahmar Allah kusa take ƙwarai ga mai Sallah. Sallah falala ce daga Allah ya zo, ya gusar da abin da yake damun zuciya. Haka aka san Manzon Allah da Sahabban sa suke yi._
_Ɗan Adam yana yin Sallah tun safe har ya zuwa sallar isha'i da fatar dacewa da rahmar Allah. Bayan isha'in mutane sun kasu gida uku. Akwai waɗanda suke su gare su daren hanya ce ta samun lada da tubarraki. Waɗannan su ne masu raba dare suna bautar Allah, lokacin da wasu suke ta shara Barci. Su kam lada suke samu daga Ubangijin su. To, sai kuma mutanen da suke mayar da daren wani kaya mai nauyi da masifa gare su saboda yin ka-ce-na-ce cikin miyagun ayyuka da talatainin dare. Ba abin da daren yake kawo musu sai baƙin ciki. Sai kuma kashi na uku wanda ya ƙunshi masu hayewa gado kawai bayan sun gama isha'i. Su kam ba yabo ba fallasa. Irin su sun kauce wa hadisin Manzon Allah da yake cewa, "ku dimanci yin Sallah a gidajen ku ko baiwar Allah da rahmar Allah su iso gare ku." Allah yasa mu dace duniya lahira._





















                      *NO_30*

             *IN TWO HOURS*
               Idan ka shiga gidan Hajiya tamkar an yi mutuwa saboda tsaban tashin hankalin da suke ciki. Tunda labarin ɗauke MEEMA ya iso gare su suka shiga tashin hankali, masu kuka nayi masu salati nayi, Ummee har wannan lokacin ta kasa yin shiru sai kuka take yi saboda ta fi su shiga tashin hankali gaba ɗayan su. A yanzun ma suna zaune gaba ɗaya a Parlour sun Yi cirko-cirko suna jiran dawowar Uncle Hashim Wanda ya fita tun ɗazu shi da Idris da masu

Please Login or Register in order to submit comment