Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba na son ki takura mata don Allah saboda zaki iya rusa mana shirin mu".

"Abba wai meye shirin naku?" Cewar Sajjad

"Ka bari zuwa anjima zan sanar maka, sannan zancen auren ku mun tsayar da shi nan da wata ɗaya me zuwa domin so muke yi ayi-ayi".

Umma zata yi magana ya katse ta da cewa, "Please Jamila ba na son musu kiyi abin da nace miki kawai, taso mu je ɗaki akwai maganar da zan faɗa miki". Ya ƙare maganar da tashi tsaye

Haka ta tashi itama ta bi bayan sa kamar zata fashe

Suna shige wa ɗaki Murjana ta bi Sajjad ɗin da kallo dake ta faman farin ciki sai tace, "wai Yaya don Allah me ka gani a wurin yarinyan nan da zaka aure ta? In fact ma su Abba fa so suke yi su amshi kaf dukiyar ta su kora ta ta bar gidan nan".

Fara'an fuskar sa ne ta gushe yana kallon ta yace, "whattt Are You saying? Ban fahimta ba?"

Sai a lokacin ma ta gane katoɓaran da tayi sai tayi saurin cewa, "suna so ne su amshi dukiyar ta su mallaki komi nata ya dawo hannun su shiyasa ka ga sun bar ta ta zauna, amma na san tunda ka kawo zancen auren ta sabida kai ne fa kawai zasu iya barin ta a gidan nan, kuma na san Abban zai buƙaci ka taimaka musu idan ta zama matar ka tunda ta ƙi yarda da su".

Shiru Sajjad ɗin yayi be ce komi ba illa tunani da ya faɗa, sai da Murjanan tayi masa magana kafin ya ɗago ya kalle ta yace, "to Ni ina ruwa na idan har zan aure ta? Su dukiyar ta suke so Ni kuma ita nake so, in dai zasu bar Ni in aure ta wannan me sauƙi ne ai, bari in je wurin Abban." ya tashi ya wuce ɗakin Abban da ya ga sun shiga

Itama Murjanan bin Bayan sa tayi da sauri.







      ********** *****

      MEEMA da ta shiga ɗakin; computern ta ta ɗauko dana Abee ɗin ta ta ci gaba da aiki, sai dai gaba ɗaya fuskar ta babu wani walwala aikin kawai take yi but tana tuna abubuwan da Murjana ta gama sanar mata. Tana ganin zaman ta a gidan ya kusa zuwa ƙarshe idan har zasu takura mata... Shigowar Murjana ya dawo da ita cikin hayyacin ta, da sauri ta rufe computern ganin ta a gaban ta tana kallon cikin computern

Wayance wa Murjanan tayi tana sakin guntun murmushi da cewa, "Please barrow me your phone because I don't have a card in my own, I want to make a phone call with my friend's".

Mamaki ne ya hana MEEMAN motsi illa kallon ta da take yi. Bata ce komi ba dai ta ɗauki wayan ta miƙa mata

Sai da tace, "You did not remove the code."

Sannan ne ta tuna ta cire mata ta miƙa mata

Murjana ta so ta ga yanda take cirewan ne, but yanayin yanda take sauri wajen danna code ɗin yasa bata fahimci komi ba, dole ta amshi wayan don kar ta gane wani abu, ta samu wuri a gefen gadon ta zauna sannan ta saka Numban Abba ta kira sa. Yana peaking tace dashi, "hello Murjana ce". Shiru tayi tana sauraron sa sai kuma tace, "eh na amsa wayan amma ban ga yadda ta cire ba"... "Ok to". Daga nan sai ta katse wayan ta goge Numban ta miƙa mata tana sakin guntun murmushi da cewa, "thanks".

Gyaɗa mata kai kawai tayi ta amshi wayan ta ajiye, sai dai ta kasa ci gaba da abun da take yi domin har yanzu mamakin ta take yi. Ganin ta ƙi tashi a wurin sai ma kwanciya da tayi shiyasa ta kashe computern tare da miƙe wa ta kai ta ajiye a cikin Trolly ɗin ta, sai ta koma can gefen gadon ta soma dealing Numban Ishaq, sai dai har yanzu ba ya shiga that's why ta mayar da akalan kiran ga Esha. Gyara zaman ta tayi jin ta ɗauka ta sauya harshe zuwa larabci suka soma waya, sun jima suna waya duk a kan Ishaq ne da yanda za'a yi Eshan ta je gidan su ta duba mata shi, sai ta samo mata Numban shi

Murjana na zaune tana jin ta sai dai ba ta fahimtan komi shiyasa ta tashi ta fice

Fitan ta yasa MEEMAN ta tsakaita wayan tare da yin ma Esha sallama sannan ta ajiye wayan. Shiru tayi tana me faɗa wa tunani, a haka har aka kira sallah ta tashi tayi ta koma ta sake kwanciya, ko fita ta ci abinci ta ƙi yi

Sai ga Murjanan ta zo kiran ta, "su ci abinci".

She looks at her in amazement, sai dai bata ce komi ba and she got up and followed her

Suna zaune duk kan su a saman dainning

Da sauri Sajjad ya tashi ya ja mata kujeran kusa da shi yana mata murmushi da cewa, "have a seat Baby".

Ko kallon sa bata yi ba ta samu wuri ta zauna

"Daughter, don't go into the room. You sit here with your siblings, stay in them and talk to them ok?" Inji Abba yana kallon ta da murmushi

Jinjina kanta tayi kawai ba tare da tace uffan ba

Sajjad da ya ɗauki Plate zai yi serving ɗin ta yace, "What will you eat if I pour it on you?"

"Nothing".

Abba said, "you mean you don't eat anything?"

"I'll have some tea."

"Tea is not food Daughter. Carry and eat ok?"

Still kanta ta jinjina masa

Sai yace, "Sajjad serve her".

"Ok Abba". Shi ya zuba mata jollof rice ɗin tare da veggies ya tura mata a gaban ta

Bata ce komi ba ta ɗauki spoon ta soma ci kaɗan-kaɗan don ko kwatan cokalin ba ta iya cuko sa

Shiru wurin ya ɗauka kowa sai cin abincin sa yake yi, while Sajjad gaba ɗaya hankalin sa na kan MEEMA, sosai yanda take cin abincin nata ya ɗauki hankalin sa har yana manta wa da shima abincin yake ci

Sai da Murjana ta bugi cokalin sa sannan ya dawo hayyacin sa, "kai yaya ka mayar da hankali a kan abincin ka ba guduwa zata yi ba kuna tare".

Hararan ta yayi yana langaɓe kai ya kalli Umma yace, "Umma ki ce mata ta fita harka ta yarinyan nan".

Taɓe baki ita kuma tayi bata ce komi ba illa abincin ta da take kaiwa baki fuska babu walwala

Murjana tace, "Yaya ya kamata ka kaimu shopping da ita hakan zai saka mu sake shiga jikin ta, ko ya Abba?"

"Yes haka ne Murjana," sai ya kalli MEEMAN yace, "Daughter, are you going shopping with your siblings and seeing the city."

MEEMA da ta ɗago kai tana kallon sa kasa cewa komi tayi. Sai da ya sake maimaita mata sannan tace, "ok". Ta mayar da hankalin ta kan abincin da take ta faman cakala. Ita ta soma tashi ta wuce ɗaki

Hakan yasa da sauri Murjana ta tashi ta bi bayan ta. Tana shiga ɗakin ta ganta a zaune sai tace, "get ready to go don't Bro Sajjad hear us silently".

Bata ce komi ba ta miƙe ta shiga Toilet ɗin, wanka tayi bayan ta fito sai Murjana ta shiga

MEEMA tayi shirin ta kamar ko yaushe yanda ta saba, bayan ta saka riga da wando sai ta ɗauki Abaya baƙa me kamar alkyabba ta sanya, ta yane kanta da farin gyale me Stones wanda ya ƙara fito da cuty face ɗin ta sosai ta ƙara yin fayau kasancewar babu abinda ta sanya, babu wani annuri a face ɗin ta haka suka fice a ɗakin ita da Murjana

Sajjad dake jiran su a Parlour tun fitowar su ya kasa ɗauke ido a kan MEEMA, gaskiya Allah yayi diri a nan wurin, yana rasa nutsuwar sa a duk sanda yayi tozali da ita ji yake yi kamar ya je ya haɗiye ta tsaban shauƙin da yake ji a kanta, har yana jin kamar bazai iya jure har nan da one month be mallake ta ba, be san ya zai yi da tarin buƙatuwar ta a zuciyar sa ba. Daƙyar ya iya control kansa suka fice a gidan bayan sun yiwa su Abba Good bye

Da suka fita MEEMA baya tayi ninyan shige wa sai Sajjad ɗin yace, "ta dawo gaba".

Tsaya wa tayi tana kallon sa while tana sake haɗe kyakykyawar fuskar ta

Shi kuma murmushi yayi mata yana sake roƙon ta a kan, "She Return the front seat".

Kasancewar Murjana tuni ta shige baya shiyasa ta buɗe gidan gaba ta shiga

A haka ya ja motan suka fice a gidan

Duk inda suka bi idanun MEEMA na kai, sai kallon yanayin garin take yi duk da ba wai farin ciki take ji a zuciyar ta ba

Hakan da Sajjad ɗin ya gani ne yasa yake mata bayanin duk inda suka wuce

Sai dai bata kula sa ba har suka kai wani ƙaton shop Mall suka fito. Tana biye da su duk inda suka sanya ƙafa har suka shiga ciki. Sai dai duk yanda suka yi da ita, "ta dauki abun da take so." but ta ƙi ɗauka

Dole Sajjad da kansa ya dinga jidan mata abubuwan duk da ya ga yayi masa

Itama ta fannin Murjana duk abinda ta ɗauka tana daukar mata, domin tana ganin ta hakan ne zata sake shiga jikin ta sosai idan ta bata kayan a matsayin gift ɗin ta.



        Har suka gama suka fito suka wuce wajen shan Ice cream, nan ma MEEMA ta ƙi taɓa duk abin da suka bata, ce musu tayi, "she does not want to drink anything." Dole suka kyale ta sabida banza tayi da su daga baya

Murjana tace, "gaskiya Yaya kana da jan aiki a gaban ka wajen yarinyan nan, Allah ba na tunanin zata so ka ko kaɗan, kana gani fa abun da take yi ko magana wannan bata taɓa yin maka ba".

Sajjad da kamar zai yi kuka yace, "Murjana nima ban san meyasa take min haka ba? Kina ganin akwai makusa a jiki na da har zata ƙi so na?"

Murmushin ƙeta tayi kafin tace, "babu Yaya sai dai kawai ina tunanin har yanzu bata saba da mu bane, tabbas akwai abun da ke ranta da har ta ƙi sakin jikin ta da mu, amma ina ga duk sanda ka aure ta sai yanda ka juya ta Yaya, nayi maka alƙawari sai ka juya ta kamar waina domin sai ta koma a tafin hannun ka, kawai ka bari lokaci yayi Yaya kai da kanka zaka sauke mata duk wani abun da ke kanta".

Dariya yayi yana ɗan shafa tulin gashin kansa, sai ya kalli MEEMAN da hankalin ta ke kan waya amma tana sauraron abun da suke faɗi, sai dai kasancewar ba ta gane abun da suke cewa shiyasa bata san da ita suke yi ba. "Ƙanwata nima wannan lokacin nake jira, abu ɗaya ne yake hana Ni aikata abin da ke raina a halin yanzu a kanta, sabida kawai ina son mallakan ta that's why komi nake yi a sannu, ai kamar yau ne wata ɗayan zai cika." Sai ya ci je leɓe yana faɗin, "zata san waye Sajjad Aliyu Ahmad Riskuwa".


Dariya Murjanan ta sheƙe da shi tana ɗago Glass cup ɗin hannun ta dake cike da Ice cream ta miƙa masa suka haɗa Cup ɗin sannan suka ci gaba da sha suna ci gaba da hiran su. Daga ƙarshe gida suka wuce bayan sun gama zagaye-zagayen su.

  
[10/10, 3:45 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*



*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._


















*NO_18*

Tun daga ranan MEEMA ta soma ganin canji a gidan, sosai Murjana ta shiga jikin ta duk inda ta sanya ƙafa tana biye da ita, tun ba ta sakar mata fuska har dai itama ta saki jiki da ita sosai tunda har ɗaukar ta take yi su fita wajen friends ɗin ta tare, ko kuma wajen dangin su suyi ta yawo hakan yasa MEEMAN ta sake sakin jiki da ita har suka shaƙu sosai

Gefe ɗaya kuma ana ta shirye-shiryen auren ta ita da Sajjad but babu wanda ya sanar mata sai da ana jibi biki Habiba ta dawo gidan saboda bikin, da ɗokin ta ta je wurin MEEMAN tana tsokanar ta da, "Amarya Amarya."

A nan ne abun ya bata mamaki take tambayar ta, "Who is the Bride?"

"Oh you mean you don't know who bride is? I know everything wlh, I just wish you the best of luck you are lucky you got Bro Sajjad, I congratulate you because you are compatible with each other".

MEEMA fa kanta ya ƙulle cike da rashin fahimta tace, "I do not understand you. Please explain to me?"

In Surprised Habiba said, "You mean you don't know this week you're going to get married? Are you kidding me?"

Quickly MEEMA stood up looking at Habiba but she couldn't say anything

While Habiba itama miƙe wa tsaye tayi ta kamo hannun ta ta mayar da ita tana cewa, "What's going on? What's wrong with you?"

Idanuwan ta ciko wa suka yi da hawaye still tana kallon Habiban tace, "I don't know what you mean. You said I was going to get married but who am I going to get married without my knowledge?"

"You and Sajjad, I think you are in love, and any service you see in this house is for your marriage."

"I don't know about it. I don't love Sajjad. In fact I hate him in my heart. I don't love him! How can I trust him to marry me? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ta ƙare maganar tana tashi tsaye da sauri duk ta gama rikice wa. Sai kuma ta juyo a firgice tana kallon Habiban da cewa, "I will not marry him. I hate him! I have to leave this house today. I will not stay." Ta wuce wajen kayan ta cikin ruɗe wa har hawaye sun soma zubo mata

Da sauri Habiba ta je ta riƙo ta ta dawo da ita bakin gadon suka zauna, "Calm down Zulaiha, I understand your situation but there is no way you can leave this house now, be patient please stay".

"Do you want me to marry him? Do you want me to marry someone I don't like?"

Jinjina mata kai tayi tana kallon ta and she Said, "yeah but..."

"Noo! it is not possible. I have someone I love, and Sajjad is not one of the few men I can marry. How can they marry me without my knowledge? It is not possible until I leave this house." Sai ta saki kuka tana kifa fuskar ta a tafukan hannayen ta

Sosai Habibah ta rikice ganin yanda MEEMAN ke kuka sosai. Duk rarrashin da tayi mata taƙi yin shiru. Buga ƙofan da ake yi yasa Habiban ta sake rikice wa tana kallon MEEMA a firgice tace, "Please Zulaiha be quiet, I will help you to leave this house but be quiet so no one understands".

Kallon ta MEEMAN take yi da idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur sai tsiyayar da hawaye take yi

Hannu ta saka ta share mata hawayen tana cewa, "Don't let anyone understand what's going on. Please pretend there's nothing ok?"

Gyaɗa mata kai tayi itama tana sanya hannun wajen share face ɗin nata tare da gyara wa

Ita kuma Habiba zuwa tayi ta buɗe ƙofan. Murjana ta gani a tsaye sai tayi saurin sakin murmushi da cewa, "har kin dawo?"

"Yes na dawo, wai me kuke yi ina ta buga ƙofa kun yi banza da Ni?" Tayi maganar tana ƙoƙarin shige wa

Jirga mata tayi a hanyar tana me rufo ƙofan da cewa, "babu komi muna hira ne da Zulaiha, dama yanzu nima nake son in tafi".

Murjanan da ta shiga ɗakin suna haɗa idanu da MEEMA ta nufe ta da mamaki tana cewa, "Sister, what's wrong with you? I look at you with tears in your eyes".

Shiru MEEMA tayi tana kallon ta sai kuma ta mayar da idanun ta ga Habiba, zata buɗe baki tayi magana kenan

Sai Habiban tayi saurin zama kusa da ita tana cewa, "wani abu ne ya faɗa mata a idon shiyasa kika ga sun yi ja, yanzu na gama cire mata har kuka tayi min kamar wata Baby". Ta ƙare maganar tana dariya

Itama Murjanan dariya ta saki tana cewa, "I'm sorry sister".

MEEMAN murmushi kaɗai tayi mata ba tare da tace uffan ba don bata san me Habiban ta faɗa mata ba

"Ok yanzu ki tashi mu je Part ɗin ku akwai kayan da na kai can zamu haɗa a can, kin san su Khalid zasu zo min bikin nan, akwai tanadin da nayi musu but ba na son su Umma su gani don ba wanda zan ba shi".

Dariya Habibah tayi tace, "to mu je". Har ta tashi sai kuma ta kalli MEEMAN tace, "will you follow us?"

Murjana tayi saurin cewa, "No, leave her let's go. We'll be back soon."

Har suka fita MEEMA bata ce da su komi ba. Shiru tayi tana lumshe idanun ta tears welled up in her eyes

Habiba ce ta dawo ɗakin da sauri tana ce mata, "sorry i'll help you later, but please don't go and stay till i come back ok?"

Gyaɗa mata kai tayi tana me aza kanta saman pilow ta mayar da idanun ta ta rufe ruff

Ita kuma Habiban ta fita ta barta a ɗakin.


Zuwa magriba sai ga ta ta dawo, bata bari kowa ya ga shigowar ta ba har Murjana don a lokacin tana ɗakin Umma, ta shiga da sauri tace ma MEEMAN, "She picked up her Trolley and left". Ita ta taimaka mata da ƙaramin jakar suka fice har wajen gidan. Kasancewar an shiga sallah shiyasa babu wanda ya gansu. Rungume ta tayi tana hawaye tare da kallon ta tace, "Where are you going from now? I don't want you to go because I will miss you!"

With tears in her eyes, she said, "I miss you too! but I have no choice but to go back to Riyadh Saudi Arabia."

"No, please, I beg you not to go back and live alone like everyone else. If they refuse to hold you honestly they want to marry you. I know your mother will hold you in both hands. Please go back it will be better for you. If you live alone you will not be happy. Stay here in Nigeria or one day we will see each other please." Habiba ta ƙare maganar hawaye sosai a wannan lokacin suna fitar mata a idanu

MEEMA kasa magana tayi kasancewar itama shashsheƙan kukan da take yi ya ci ƙarfin ta. Tana shirin zame hannayen ta ba tare da tace da ita uffan ba

Sai Habiban ta sake rungume ta kafin ta sake ta tana share hawayen fuskar ta da bayan hannun ta, ta ɗaga mata hannu tana cewa, "Please stay here in Nigeria, hurry up and leave here to let Abba come out to see you". Daga haka ta juya ta shige gida da sauri

Itama MEEMAN jan Trolley ɗin ta tayi tana rataye da ƙaramin a hammatar ta taci gaba da tafiya. Har sai da ta fita titi kafin ta tsaya tana faman waige-waige. Bata sha wahala ba ta samu keke napep tace, "he peak her with hotel". Kasancewar ta ga dare yayi baza ta iya zuwa wani wuri da daren nan ba. Kai tsaye ana kaita hotel ɗin ta kama ɗaki ta shiga. Zuwa washe gari zata wuce Kaduna tuna wa da tayi akwai mahaifiyar Ummee ɗin ta da ƙanin ta, ko a wajen su zata iya zama ba sai a wajen Ummeen ta ba, duk da bata so yanke wannan shawaran ba amma tuna wasiyyar mahaifin ta da kuma maganar Habiba yasa taga ya dace ta koma wajen su, bata da kowa a can Riyadh baza ta iya rayuwa ita kaɗai ba.




Da safe bayan ta gama shirya wa ta fito ta sami me napep ya kaita tasha inda zata samu motan Kaduna. Wannan karon ma drop ta ɗauka suka wuce Kaduna, wajen goshin magriba suka isa.



A cikin G.R.A Ummeen ta take zaune ita da Mahaifiyar ta da ƙanin ta, shi yanzu ƙanin nata ya koma Abuja da zama da shi da Matar sa da ɗan su guda ɗaya, wajen shekaru shidda kenan da aka tura sa yaƙi ya tafi ya bar matar tasa a can Abujan kasancewar tana aiki shiyasa bata dawo nan Kaduna ba, sannan kuma ɗan su na school wannan dalilin ne ya zaunar da su can, sai dai jefi-jefi tana zuwa Kadunan ta gaishe su. Yanzu haka mahaifiyar Ummee me suna Hajiya Halima suna kiran ta da Hajiya, tana cikin halin rashin lafiya na hawan jini wanda yasa har ta rasa ƙafafuwan ta tana zaune a wheelchair ne. Mahaifin su Ummeen shi ya daɗe da rasuwa, su biyu Hajiya ta haifa daga ita sai ƙanin ta Captain Hashim. Kuma mahaifin su dai-dai gwargwado ya bar musu dukiya me ɗumbin yawa, don gidan su babban gida ne me hawa biyu. Part ɗin Hashim da matar sa daban duk a ciki idan ya zo hutu suna sauka a nan, sannan sai na Hajiya sai kuma inda Ummee ke zaune a halin yanzu, tana aiki ne a wani Company tun dawowar ta daga Riyadh.



Kwatancen da MEEMA ta yiwa Me motan be sha wahala ba wajen tambayar mutanen garin, tunda sun rigada sun shiga G.R.A ɗin, duk da MEEMA bata taɓa zuwa ba amma ta riƙe sunan gidan su Ummeen nata sosai tunda ba wani ɓoyayye bane, har Numban gidan sai da Abee ya sanar mata da zai rasu hakan yasa nan da nan suka gano gidan.


Bayan ta sauka ta sallami me motan ta ɗauki kayan ta ta taka a hankali zuwa bakin Gate ɗin. Ta jima a wurin tana ta kallon ƙofar gidan ta kasa buga wa, lokaci ɗaya idanun ta suka cika da hawaye yayinda zaciyar ta ta soma zugi tsaban ƙuncin da ya ziyarce ta a halin Yanzu ɗin. Ba komi ya haifar mata da hakan ba sai tuna wa da tayi a yau zata haɗu da mahaifiyar ta wacce ta guje su a cikin rayuwar su gaba ɗaya, kuma bata taɓa tunanin ta neme su ba har ga shi Abee ɗin ta ya bar duniya da baƙin cikin ta, ta kasa gane wani irin abu ne Abee ya aikata mata da har ta zaɓi tayi masa wannan mummunan hukuncin? Baƙin ciki da ƙuncin da take ji a wannan lokacin tamkar yanzu ne Ummeen ta tafi ta bar su, sanadin ta sun rasa farin cikin su wanda hakan yasa ta rasa mafi soyuwa a rayuwar ta wato Abee ɗin ta. Sai kawai ta fashe da kuka sosai har bata iya ganin komi tsaban yanda hawayen suke kwaranya a face ɗin ta. Hannu ta sanya ta dinga share wa yayinda wani tuƙuƙin baƙin ciki ke kai komo a maƙogwaron ta. Ta kasa ɗaga ƙafafu ta isa bakin Gate ɗin bare ta buga. Tana nan tsaye wadda ta fi mintuna talatin a wurin har an kira sallan magriba ana shirin shiga

A lokacin ne aka buɗe Gate ɗin gidan wanda me gadi ne da shi da masu hidiman gidan su biyu suka fito zasu wuce masallaci. Da kallo suka bi ta ganin ta da suka yi a wannan yanayin kuma a jikin gidan su. Sai dai babu wanda ya samu halin yin magana illa idanu da suke bin ta da shi kamar wacce basu taɓa ganin halitta makamanciyar nata ba, gaba ɗaya a cikin zuciyoyin su mamakin ganin Balarabiya a bakin ƙofar gidan suke yi. A haka har suka wuce ta suna waigen ta

While MEEMA tunda tayi musu kallo ɗaya taci gaba da share hawayen ta kafin ta ja ƙafafu a hankali ta isa ƙaramin ƙofan ta tura ta shige. Kallon gidan take faman yi tana tafiya a hankali har ta isa ƙofar da zata shiga gidan, a nan ma ta ɓata lokaci kafin ta sanya hannun ta dake faman rawa ta soma Nocking. Kasancewar a hankali take Nocking ɗin shiyasa sai da ta ɗau lokaci tana yi kafin a zo a buɗe mata

Wata mata ce me jiki don a ƙalla zata kai shekaru arba'in, wanda daga gani ƴar

Please Login or Register in order to submit comment