Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abinda kike so fa kika aikata, kuma duk rarrashi da ban bakin da nayi miki domin ki koma amma kika ƙi bin shawara ta".

"Hajiya ba haka bane wlh nayi nadama tun ba yanzu ba, abun da na aikata yana damu na a zuciya na rasa yanda zan yi in koma, ban san ya Faruk zai kalle Ni ba shiyasa na kasa koma wa, baƙin ciki na yanzu ya koma ga mahaliccin mu ban nemi afuwar sa ba Hajiya, ya zan yi da raina?". Ta ƙare maganar cikin muryan kuka

Tsam MEEMA ta tashi zata wuce ɗaki

Hakan yasa Hajiya ta dakatar da ita tana tambayar ta, "where to go?".

"There is something I have to do.". Daga haka ta wuce ba tare da ta jira cewar ta ba

"Yanzu ya ya zan yi Hajiya ɗiya ta ta dawo tana ƙauna ta? Bazan iya jure halin da take ciki ba, Ina son ganin farin ciki a fuskar ta, ina son ta ɗauke Ni a matsayin mahaifiyar ta me ƙaunar ta. Nayi kuskure sosai ban san ya zan yi in dawo da farin cikin da ta rasa ba, na san MEEMA ta kasance a cikin baƙin ciki na tsawon lokaci, nayi ƙoƙarin neman ta a waya a baya but wayoyin su duk ba sa shiga."

"To ai haƙuri zaki yi tunda ke kika jawa kanki, a sannu wata rana zata gane idan kika fahimtar da ita, Ni dai ban ce ki riƙa damun ta ba na gaya miki domin idan har ta bar gidan nan sai dai ke ma ki bi ta."

Shiru kawai Ummee tayi yayinda hawaye ke zuba a saman fuskar ta, hannu ta sanya tana share wa zuciyar ta na mata zafi da raɗaɗi

"Ki je ki karya ga Breakfast ɗin ki can a dainning Zabba'u ta shirya miki". Hajiyan tafaɗa tana kallon ta

Bata ce komi ba ta tashi ta wuce kan dainning ɗin.





                ******

       Shigan MEEMA ɗakin kwanciya tayi a saman gadon tana hawaye, danne kanta tayi a ƙasan pilow ta saki kuka me tsuma rai, ta jima tana kukan kafin ta tsagaita tana tashi zaune ta sanya hannayen ta tana share hawayen. Sai ta miƙe ta nufi jakar ta ta ciro computern ta ta soma aiki a ciki

Bata jima da fara wa ba Zabba'u ta shigo ɗakin da sallama

A ciki-ciki ta amsa mata bayan ta ɗago ta kalle ta sau ɗaya ta mayar da kanta

Cikin washe baki Zabba'u tace,
"good job. Hajiya says let me call you cooking is complete."

Gyaɗa kanta tayi ba tare da ta furta komi ba ta mayar da hankalin ta ga computern

Ita kuma Zabba'u ta fice


Kamar mintuna goma kafin ta rufe ta tashi ta fita.








*WhatsApp only*
07065334256
[10/10, 3:47 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                        💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



                 *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._


















                             *NO_20*

             Tafiyan MEEMA ya ja tashin hankali matsananciya a wajen su Uncle Ali. Musamman ma Sajjad domin hauka tuburan ya nuna musu a kan, "sai sun nemo mishi ita duk inda ta shiga." Kuka sosai yake yi duk ya hargitsa musu gida, su kansu sun kasa zama suyi tunanin mafita illa rarrashin sa da suke yi a kan, "ya kwantar da hankalin sa zasu nemo ta duk inda ta shiga."

Mutanen da suka soma taruwa sai dai suka tafi a washe garin ranan tunda an nemi Amarya an rasa. Wasu har tsegumi suke yi da dalilin tafiyan nata

Su kuma tun suna ɗaukan abin da Sajjad yake yi a matsayin na ɗan lokaci dole zai haƙura; sai kawai zazzaɓi ya kama sa, sosai yake jin jiki wanda a koda yaushe sai dai yayi ta musu sambatu, "shi fa a nemo masa Zulaiha, bazai iya rayuwa babu ita ba." Hakan yasa suka wuce da shi asibiti tunda abun nasa sai gaba yake yi.


            Uncle Ali da Uncle Zubairu sun rasa inda za su fara zuwa su neme ta, hankalin su a matuƙar tashe yake sabida rashin amsar komi daga wurin ta, tabbas suna tunanin ta gane auren da zasu yi mata ne ta gudu, kuma ko kusa basu yi tunanin zata iya zuwa wajen Ummeen ta ba kasancewar ita Ummee ta bar su tun ba yanzu ba, ba sa tunanin cikin sauƙi zata je can. Shiyasa suka yanke shawarar zuwa Riyadh ɗin su duba ta

Umma duk ta tashi hankalin ta itama sai kuka take yi, a yanda ta ga Sajjad ya ƙi haƙura da zancen MEEMAN yasa itama take kuka da faɗin, "a nemo ta duk inda ta shiga don ɗan ta bazai mutu a kanta ba, a nemo ta a ɗaura mishi aure da ita idan har ɗan ta zai samu lafiya."

Uncle Zubairu shi ya je har Riyadh ɗin amma masu aikin gidan suka ce, "bata zo ba". Kwanan sa biyu a can yana zaman jiran ko zata zo amma babu ita babu alamar ta, dole ya dawo gida ya sanar wa da Uncle Ali. Hankalin su ya sake tashi sosai, sai dai babu yanda suka iya dole suka mayar da hankali wajen samun lafiyan Sajjad tunda har yanzu ya ƙi dangana shi a dole sai an nemo ta. Har ya samu sauƙi sun koma gida ya tayar da hankalin sa, "shi da kansa zai je neman ta a Riyadh ɗin." Ba don sun so ba suka bar sa ya soma shirye-shiryen tafiya. A ransa ya ƙudura aniyar, "muddin be ganta ba bazai dawo gidan ba, dole tare za su dawo, a ko ina take a faɗin duniyar nan sai ya nemo ta, ba shi da matar aure sama da ita, yana matuƙar ƙaunar ta bazai taɓa barin ta ba".








✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

            Zaman da MEEMA tayi a gidan ta samu kwanciyar hankali sosai, duk abin da take so Hajiya tana mata, tare suke zama suyi ta hira har da Zabba'u don yanzu ta saba da ita kasancewar ta akwai surutu da shiga abun da babu ruwan ta, yanda take shige wa MEEMAN ne dole ta saki jiki da ita, sai dai matsalan ko kaɗan ta ƙi bai wa Ummee dama wajen ganin ta wanke kanta daga laifukan da tayi mata, ko magana ba ta mata koda suna zaune wuri ɗaya, tun Ummee na damuwa sosai a yanzu har ta saba da halin MEEMAN, itama a hankali yanzu take ɗan shiga sha'anin ta duk da ba kula ta take yi ba, amma wani abun sai ta riƙa mata ko don ta faranta mata, musamman girkin da ta san tana matuƙar so irin ciman Larabawa, haka zata zaƙe tayi mata but ko kula wa ba tayi, Hajiya ke sanya ta taci wani lokacin shiyasa take ɗan ci idan ta ga dama.



           Yau ma suna zaune da Hajiyan, Zabba'u na gefe tana musu surutu Hajiya na amsa ta, ita kuma MEEMAN tana zaune tana kallon su wani lokacin idan suka sako ta a zancen su tana tsulma musu baki

Dayake Ummee na wajen aikinta bata dawo ba

Duban Zabba'u Hajiya tayi da cewa, "yauwa Zabba'u kira min drever zan aike sa, zai siyo wa MEEMA layin waya ne ta ce min  tana buƙata."

"To Hajiya bari in je." Tayi maganar tana tashi da sauri ta fita

MEEMA da ke kallon su sai tace, "grandma I also want to learn Hausa because I want to know what you are saying".

Dariya Hajiya tayi da cewa, "Are you tired of hearing us talk? Don't you understand?"

Ita kuma sai tayi murmushi tana jinjina mata kai, sai kuma ta ƙara da cewa, "yet I want to be able to."

"Ai kuwa zaki koya, da sannu ai zaki saba dama".

"You say what?"

Hajiya smiled and said, "I said you will learn slowly."

MEEMA smiled at her looking at her

"But I think your stay there makes you very anxious. what i was thinking why not get a job you going out, It will help you a lot and you will forget about any worries."

"Na'am grandma. I need a job, I want to start working." She spoke excitedly

Hajiya itama murmushi tayi da cewa, "If that makes you happy, you will be offered a job".



               Zabba'u da Ummee ne suka shigo a tare

Hajiya ta amsa musu sallaman tana kallon su

"Sannu da gida Hajiya." Inji Ummeen tana zama a kan sofa

"Yauwa an dawo?"

"Eh."

Zabba'u da itama ta zauna take faɗin, "Hajiya wai ya fita zuwa shago yanzu zai dawo, na bar wa me gadi sallahu idan ya dawo ya faɗa masa kina neman sa."

"Tom shikenan." Cewar Hajiyan kafin ta mayar da kallon ta kan Ummee dake yunƙurin tashi tace, "zauna zamu yi magana".

Koma wa tayi ta zauna tana kallon ta

"MEEMA tace tana son Fara aiki kinga ke ya kamata ki nema mata abun da ya kamata tayi".

"To Hajiya sai in nema mata a wurin aikin mu hakan zai fi mu riƙa zuwa tare." Inji Ummeen tana kallon MEEMA da murmushi

Hajiyan kallon MEEMA tayi tana sanar mata da abun da Ummee tace

Fuskar ta babu walwala ta dubi Hajiyan tace, "Laá. I do not like."

They were silent

Sai kuma Hajiyan tace, "But you said you needed it, or did you break it?"

Kafin tayi magana sai Ummee tace, "a'a Hajiya ina ga ba ta son yi a inda nake yi ne, kuma dama mass.com ta karanta Ni ce dai nake son tayi aiki a companin da nake aiki hakan zai sa ko yaushe muna tare, amma tunda ba ta so sai in Yi ma Idris magana ya samo mata a wajen aikin su na gidan t.v hakan zai fi."

Hannun MEEMAN Hajiya ta riƙe tana kallon ta tace, "well. Now you're going to get a job somewhere, did you?"

Kanta kawai ta ɗaga har yanzu kyakykyawar fuskar ta a turɓune

Ita kuma Ummee tashi tayi ta haura sama

While su kuma suka ci gaba da taɓa hira ban da MEEMA da ke latse-latse a cikin wayan ta

Nocking ɗin da aka yi ne yasa suka yi shiru suna ba da iznin shigo wa

Drever ne ya shigo da sallama a bakin sa, ya isa wajen su ya durƙusa yana cewa, "Hajiya gani an ce kina nema na".

"Eh Salihi. Layin waya zaka siyo wa Jika ta."

"To Hajiya".

"Yauwa Zabba'u ɗauko mishi 2k a ɗaki na ya je da shi."

Amsa mata tayi tana tashi ta wuce

Drever'n yace, "amma Hajiya wani iri ne zan siyo?"

Kallon MEEMA tayi da cewa, "What brand do you want with the Simcard?"

Sai a lokacin ta ɗago da idanun ta daga duba wayan da take yi, "MTN." Ta furta a taƙaice

"To kaji. Mtn take so ka siyo mata."

"To Hajiya."

Koda Zabba'u ta kawo kuɗin ta miƙa masa ya fice. Ita kuma tace, "Hajiya bari in shiga kichen in ɗaura mana abinci. Ko zaki taya Ni ne MEEMA?" Ta ƙare maganar da kallon ta tana washe baki

Jin ta kira sunan ta yasa MEEMAN ta kalle ta ba tare da ta furta komi ba

Hajiya tace, "kin yi mata Hausa taya zata san me kika faɗa mata?"

"Oh wlh manta wa nake yi Hajiya." Sai ta maimaita mata da turancin

Girgiza kanta MEEMA tayi tace, "laá I can't."

"But you should always learn that it will benefit you even at your husband's house."

Murmushi kaɗai MEEMA tayi bata ce komi ba ta mayar da hankalin ta kan wayan ta

Ita kuma Zabba'un sai da ta gama zuba surutun ta da Hajiya duk dai a kan MEEMAN kafin ta wuce kichen ɗin

Hajiya ta kaɗa kai da cewa, "Zabba'u baki da dama ke dai, a nan kika fi auki wajen surutu, ayi mutum kullum ba ya gajiya kin girma baki san kin girma ba."

Ɗago kai MEEMA tayi ta kalle ta tace, "grandma you do it for me?"

Tace, "No, I'm not doing it. I'm doing Zabba'u. She's worried about you coming. She's going to teach you how to cook."

"I can't grandma." She spoke in a calm voice

"Then if you want she can teach you, because you should learn. If you get married who will go and teach you?"

Shiru MEEMA tayi and she drops head down

"If you have time, she will teach you ok?"

Gyaɗa kanta tayi kawai. Sai kuma ta miƙe tana kallon Hajiyan da cewa, "I'll go into the room and lie down."

Hajiya amsa mata tayi ita kuma ta wuce zuwa ɗaki.



        Tafiyan ta babu jima wa wani saurayi wanda bazai fi sa'ar MEEMAN ba ya shigo da sallama ciki

Hajiya ta amsa mishi tana masa lale da faɗin, "idon ka kenan Idrisu?"

Dariya yake yi ya ƙariso ya zauna yana cewa, "Allah ya bar mu da Hajiyar mu. Kin ci zamanin ki kina cin tamu, tsohuwa me ran ƙarfe an buga an bar ki, na same ki lafiya?."

"Ai bazan amsa ba tunda sai yanzu ka san da Ni, gaba ɗaya ka manta da Ni sai yau zan ga ƙafafuwan ka a gida na."

"Woo! Hajiya kina da ƙorafi ne na rantse da Allah, ban da abun ki duka-duka yaushe ne na ɗauke ƙafafu na a gidan nan? Kin san kuma aiki na ne ba ya bari na in shigo amma da sai kin gaji da gani na." Yafaɗa still yana dariya

Hajiya tace, "babu wani nan, da ace ban san daɗin bakin ka bane."

"Tukunna dai Hajiya inyaso daga baya sai mu ci gaba da taƙaddamar tamu, ina Aunty ita take nema na?."

"To ka ji batu ashe sai da aka neme ka ka shigo?"

Dariya yayi da cewa, "Hajiya tawa ke dai so kike yi ki laƙaba min laifi, kowa ya san ina mugun ƙaunar ki, ko su Umma sun san cewa ina na fito wurin ki ne, ina zan tafi wurin ki ne, amma kike faɗan haka; idan wani ya ji ai sai yayi mana dariya Allah kuwa."

"Ni zan fara yin dariyan kuwa. Dama ai ba yau kuka saba ba, sunan dai kuna miji da mata ne." Cewar Zabba'u da fitowar ta kenan daga kichen ta tsinkayi maganar nasa

"To kin gani ko Hajiya ta? Ai dama nace miki akwai ƴan saka eyes wlh, kin ga ɗaya ta ɓullo. Bamu san kuma nawa za su ƙaru ba a nan gaba."

Dariya suke yi su duka

While Zabba'u tana faɗin, "ai yau har gidan su Umman taku sai na je kai gulman ku."

"Kin gani ko Hajiya? To ki faɗa mata ba faɗa muka yi ba."

"Ƙyale ta Idrisu na, duk wanda yace zai gan mu a rana ai zai ruɓe ne, Ni da miji na ai ba ma ɓaci. Yanzu dai kira Zulaihan a waya tana sama ne."

Wayan sa ya ɗauka yana latsa wa yana ci gaba da bai wa Zabba'u amsa wacce ta sako shi a gaba sai ba'a take mishi. Bayan ta ɗau wayan ne ya sanar mata, "ya zo."

Ba'a jima ba kuwa sai ga ta ta sauko. Ta zauna a kan sofan tana amsa gaisuwar sa, kana ta ƙara da faɗin, "Idris aiki zaka samo wa yarinya ta MEEMA a wajen aikin ku, Ina fata za'a samu?"

"Eh Aunty za'a iya samu insha Allahu, idan ma hakan ya gagara zan yi ƙoƙari ko a ina ne in samo mata, amma Aunty Kar dai ace yarinyan ki ta Riyadh ita ce ta zo?"

"Eh ita ce." Ta ba shi amsa tana murmushi

"Wow! Gaskiya zan so in ganta, kin san na daɗe da jin labarin ta wajen Hajiya sai dai baki taɓa zuwa da ita nan ba."

"To ai yanzu sai ka gaji da ganin ta kuwa Mijin, tunda muna nan da ita ta dawo gaba ɗaya." Cewar Hajiya tana dariya

"Allah Hajiya ta?"

"Ƙwarai kuwa Mijin. Yanzun nan ma ta tashi ta shiga ɗaki."

"To in dai haka ne insha Allahu I will try my best to get her a job. But I need her documents so I can go with them."

Ummee da sauri ta kalli Zabba'u tace, "ki kira ta sai ki faɗa mata ta kawo takardun nata."

Tashi Zabba'un tayi ta wuce ɗakin MEEMA. Bata jima ba ta dawo ta sanar musu, "ga ta nan zuwa".

       
          Ba'a jima ba MEEMA ta fito riƙe da documents ɗin a hannun ta ta taka a hankali zuwa wurin su

Hajiya na murmusa wa tace, "to ka ganta nan Idris, Jika ta kenan."

Idris da ke faman kallon MEEMAN miƙe wa tsaye yayi fuskar sa yalwace da fara'a yace, "gaskiya tana da kyau Hajiya, Allah ya baki jika kyakykyawa. Anya Hajiya ba daga can ƙasar kika sanyo ta da naki ba?" Sai kuma ya kama haɓa yana sake ƙare wa MEEMAN kallo da cewa, "Hajiya Ni fa ban yarda ba, kwata-kwata ban ga tayi kama da ke bane ai."

Dariya suke yi duk kan su sabida abin da ya faɗa

While Hajiya tace, "ai yaro duk kyawun nan da ka gani kaɗan ne da wanda nayi a zamanin da nayi ƴan matanci na, wannan ai bata kai Ni kyau ba."

"Nima haka na gani ki bar sa kawai Hajiya don ya ga kin taƙwarƙwashe ne shiyasa yake faɗan haka." Inji Zabba'u tana dariya

They all laughed. while MEEMA na tsaye tana kallon su bata ce uffan ba tunda ba jin su take yi ba

Idris yace, "ƴar uwan tawa ba ta magana ne Hajiya naga tayi shiru ko fara'a ba ta yi?"

Zabba'u tayi tsagal ɗin cewa, "ba ta jin ka ne shiyasa, baka yi mata da Yaren da zata gane bane."

"Kina nufin larabci?" Yafaɗa yana ƙwalalo ido. "To ai Ni ban iya ba."

Ummee tace, "kayi mata da turanci."

Murmushi yayi ya kalli MEEMAN da cewa, "sorry sister. My name is Idris. Our house is looking at this house, we are staying outside Hajiya, I am happy to meet you."

Guntun murmushi tayi masa da cewa, "me too."

"Ok Bring the documents." Yafaɗa yana miƙa mata hannu

Handing him the fetus without saying anything again she turned and walked away

Hajiya tace, "to sai ka ƙoƙarta Idrisu na."

"Kar ki damu Hajiya ta baki da matsala. Ni zan tafi don akwai inda Abba ya aike Ni dama. Zuwa gobe ko jibi zaku ji me ke akwai in Allah ya yarda."

Daga nan sallama suka yi ya fice ya bar su. Su kuma suka ci gaba da ɗan taɓa hira, inda Zabba'u ta wuce kichen domin ci gaba da aikin ta.


              Ba'a rufa kwana biyu ba Idris ya dawo gidan ya shaida musu, "an dace da samun aikin MEEMA".



                 Zuwa Monday suka soma fita aikin tunda a wurin aikin su ta samu, tare suke fita da Idris kasancewar sa me son Wasa da barkwanci a cikin ƙanƙanin lokaci suka soma saba wa, idan ya shirya sai ya zo gidan su tafi tare

Tunda ta fara fita aikin ta sake sakin jiki sosai, abubuwan da ta gani a wurin aikin nasu da kuma yanda ake gudanar da al'amura gunun sha'awa a wurin ta. Musamman yanda mutane suke son mu'amala da ita domin sosai tayi farin jini a wurin jama'a, kowa MEEMA kowa MEEMA sai hakan yake sanya ta farin ciki da nishaɗi, duk da ba kowa take kula wa ba iyakan gaisuwa sai kuma abun da ya kaita tunda ko yaushe suna tare da Idris, ga kuma cousin ɗin shi Laɗifa komi tare suke yi, ita take jan MEEMA a jiki tana koya mata wasu abubuwan musamman idan bata fahimta ba kasancewar yanayin mu'amalar mu ta nan bata san da su ba, ga kuma rashin iya Hausa da har yanzu ko Eh ta gaza fahimta.


          Musamman Ummee ta siyo mata mota sabuwa fil domin ta riƙa zirga-zirga da ita na yau da kullum zuwa wajen aiki, amma ta ƙi amsa


Hajiya da kanta ta kira ta, ta miƙa mata keey ɗin motan daƙyar ta amsa. Sai dai bata taɓa hawa ba kullum Idris take bi tunda sun zama tamkar friends ne a cikin ɗan ƙanƙanin lokacin da be gaza wata ɗaya da haɗuwar su ba. Wani lokacin ma har gidan su take shiga wajen Umman sa, kasancewar gidan akwai yara shiyasa zaman gidan yake mata daɗi, kowa so yake yi ya ja ta a jiki saboda farin jinin ta. Shiyasa a ɗan ƙanƙanin lokaci ta saki jikin ta ta soma saba wa da sabon rayuwar ta, a hankali ta soma manta duk wani rayuwar ƙunci da tayi na tsawon shekaru, duk da har yanzu ta kasa manta wa da Abee ɗin ta duk idan ta tuna sa tana zubar da hawaye sosai, sai ta riƙa jin tsanar Ummeen ta yana sake zama sabo a zuciyar ta, tana jin tamkar baza ta taɓa yafe mata ba. Ita ce silan komai.
[14/10, 9:53 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                          💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



             *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._



            *FAƊAKARWA*
'''Manzon Allah yayi mana bayani cewa, "Bambancin da yake tsakanin mumini da kafiri shi ne rashin yin Sallah." Busaida ya ruwaito wani hadisin mai kama da wannan inda ya ce, "na ji Manzon Allah yana cewa," "haƙƙin da ya bambanta mu da su shi ne salla. Duk wanda yayi watsi da ita ya zama kafiri."
      Shi kuwa Abdullahi Ibnu Umar ya ce ne wata rana Annabi yayi magana a kan Sallah yace, "Ga wanda yake tsayar da sallah, takan zame masa haske, shaida da kuma tsira a ranar lahira. Wanda ba ya tsayar da ita kuwa, gare shi babu haske, babu shaida, babu tsira, kuma a ranar lahira za a haɗa shi da Ƙaruna da Fir'auna da Ubayyu ibnu Khalaf."
       Da hadisai da ayoyin Alkur'ani duka suna nuna irin munin zunubin da yake rataya da ƙin yin salla, suna kuma nuna matsayin mai yin hakan duniya da lahira. Dokar musulunci dai tana yin gargaɗi ne ga mabiya addinin cewa su riƙe shi da gaskiya ta yin Sallah, babban jigon Islama kuma aikin addini mafi girman daraja. Ashe ba abin mamaki ne ba mu ji cewa duk wanda ya guje mata ya kafirta, ya kauce ma hanya miƙaƙƙiya. Alƙur'ani kam na kiran irin wannan mutum mai zunubi wanda aka tanadar wa wutar jahannama, mai ƙona komai, mai cinye Mutane da tsananin zafin ta. Kyakykyawan sakamako ga wanda ya bijire. Ubangiji ba ya zaluntar kowa. Allah yasa mu dace yasa mu gama da duniya lafiya.'''


















                     *NO_21*

                 Yau ma kamar kullum MEEMA tayi shirin ta kamar yanda ta saba, Abaya ta saka blue color da aka yane shi da kwalliyan Stones daga saman wuya har ƙasa, sai faffaɗan hannu me kamar alkyabba shima an sanya Stones da kuma bakin lessi, tayi Rolling da jan veil sai ta saka cover shoes Shima ja, haka zalika agogon hannun ta. Iyakan Powder da lipstick ta saka sai ta zizara kojol a idanun ta, I can't describe to you how beautiful she is, but her beauty is even more beautiful. Fita tayi Parlour inda Idris ke zaune da Hajiya suna hira yana jiran fitowar ta

"You look so cute Zulaiha." Cewar Hajiya kenan sanda ta ƙyalla ido ta ganta

Ita kuma murmushi tayi ta isa wurin ta tayi mata peak a goshi tare da faɗin, "thank you Grandma."

Idris da ya miƙe tsaye a yanzu ɗin yace, "to Hajiyata mu zamu wuce sai mun dawo."

"To Allah ya bada Sa'a Allah ya tsare." Tafaɗa tana murmushi

Daga nan sallama suka yi mata suka fice. Sanda suka isa bakin motan Idris ɗin da kanshi ya buɗe wa MEEMA ƙofa yana solute ɗin ta

Kyakkyawar murmushinta ta sakar mishi tana ƙarisawa ta shiga ciki

Ya rufe shima ya zaga ya shiga ya ja motan zuwa wajen aikin su. A cikin motan sai janta da hira yake yi duk da kasancewar ba amsa mishi take yi ba sai dai tayi masa murmushi kawai, a haka har suka kai

Please Login or Register in order to submit comment