Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

buɗe. Binciken farko da Umar Faruk yayi a kanta wajen abokin shi wanda ya santa sosai. Shi ya tabbatar mishi da Malama ce ita sosai da kuma ƙoƙarin ta. Hakan yasa ya faɗa soyayyar ta kafin komawar shi ƙasar waje. Be yi ƙasa a gwiwa ba da taimakon abokin nashi ya bayyana mata soyayyar shi. Inda cikin ƙanƙanin lokaci suka gina soyayyar su me tsafta har zuwa sanda ya gama karatun shi ya dawo ya aure ta. A lokacin ya rasa iyayen shi domin tun yana yaro mahaifiyar shi ta rasu, shi kuma mahaifin shi ya auri Hajiya Salamatu wacce ita ce Momy, ta zo da yaran ta biyu gidan kuma tayi zama da mahaifin shi na shekara ɗaya kafin Allah ya ɗauki ranshi sakamakon ciwo da yayi. A lokacin Umar Faruk ya sake zama Maraya babu uwa babu uba bare ƴan uwa, sai Momy da ƴaƴan ta da suka nuna mishi ƙauna bisa son mallakar dukiyar shi da suke son yi, ya ɗauke su tamkar jinin shi be taɓa tunanin ba da zuciya ɗaya suke ƙaunar shi ba, be da wasu dangi da suka fi mishi su, duk abinda suke so yana musu kuma yana tsananin yiwa Momy biyayya tunda ya ɗauke ta kamar ita ta haife shi, yana ji a ranshi ya rasa uwa ce amma ita ce ta maye mishi gurbin ta. Sai dai shigowar Nusaiba cikin rayuwar shi sai ta fara fahimtar zagon ƙasar da suke yi mishi, wanda ta so ta fahimtar da shi ba ƙaunar shi ta Allah da Annabi Momy take yi ba amma ina bata ci galaba ba. Lokacin ta haifi Hafsah da shekara biyu ta samu cikin Yusra. Tun lokacin suke tagen yanda za ayi su kashe ta domin ba sa son tazo ta haihu ta sama mishi Magaji na miji, domin shi kanshi so suke yi su kawar da shi a doron duniya su mallaki komi da kuma dukiyar shi, basu ci Nasara ba sai da ta haihu a lokacin tana fama da rashin lafiya sakamakon haihuwar ya zo mata da tangarɗa, suka saka mata guba a cikin abinci ta ci ta mutu wanda ya ja cece kuce a tsakanin likitocin asibiti da ƴan sanda sakamakon a asibiti ta mutu, an gane cewa guba taci sai dai maganar be kai ga kunnen Umar Faruk ba suka san yanda suka yi suka siye ɗan sandan aka binne maganar.



        Mutuwar Nusaiba ya taɓa Umar Faruk sosai domin Allah ya ɗaura mishi ƙaunar ta a zuciya, yana matuƙar son ta kuma yana jin ta a zuciya matuƙa. Mace ce me shiga zuciya bata da hayaniya ko kaɗan, tana da kirki da halin ƙwarai wanda idan har ka zauna da ita dole ne sai ka so ta. Mutuwar ta ya taɓa shi hakan yasa har yayi jinya sabida damuwar da ya saka a zuciya, wanda yanzu ya haifar mishi da ciwon zuciya.




             Har yanzu burin su Momy su ga bayan shi amma sun kasa cin Nasara, yanzu haka suna ta shirin yanda zasu kashe shi ne ba tare da an yi zargin kisa bane domin su mallaki komi, mahaifin Umar Faruk wato Alh. Aliyu Bature ya rasu ya bar mishi ɗumbin dukiya har da gidajen mai guda uku wanda ake ji da su a nan Kaduna. Yanzu haka shi Umar Faruk ɗin ya gina babban Company na sarrafa shinkafa wanda shi ke kula da shi tare da Abdul. Sanadin shigan shi siyasa kuma mutanen mahaifin shi ne suka saka shi, tun ba ya sha'awa sai dai ya basu gudummawa domin ya san manyan mutane sosai, har dai a yanzu sun ci galaba inda kai tsaye suka nema mishi kujeran Senata kuma ga shi Allah ya ba shi.










                       *****

       Ajiyan numfashi ya sauke yana miƙe wa tsaye tare da nufan drowan mirror ya buɗe, maganin shi ya ciro ya buɗe ya ɗauki wanda zai sha sannan ya wuce bakin Fridge, buɗe wa yayi ya ɗauki faro ya sha maganin dashi sannan ya wuce bakin gadon shi ya soma cire kayan jikin shi. Wanka ya shiga ya fito yana tsane jikin shi da towel bayan wanda ya ɗaura a ƙugun shi. Wayan shi da ta fara ƙara ya nufa ya ɗauka yana zama a gefen gadon, peacking yayi yana kara wa a kunne. Congratulations ɗin da ake masa yasa ya saki murmushin shi me kyau yana amsa wa cike da farin ciki. Koda ya gama amsa call ɗin sai wasu kuma suka ci gaba da kiran shi dole ya ɓata lokaci yana amsa calls kafin ya tashi ya shirya a cikin sauri, wani farin tissue ya saka wanda har farin Singlet ɗin da yayi using dashi ana gani. Kayan sun yi masa kyau sabida ƴan dai-dai ne iya jikin sa, sai ya murza hula baƙi ya nufi gaban mirror yayi amfani da turarukan shi wajen feshe ko ina na jikin sa da turare, nan da nan ɗakin ya sake tashi da ƙamshi sosai. Bayan ya gama jerin takalman sa ya nufa ya zari ɗaya wanda ya kasance baƙi ne ya zura ya ɗauki keey ɗin mota da wayan shi ya fito

Fitan shi sai ga motoci sun fara shigowa gidan. Sun yi kusan goma haka suke ta tururuwan shigowa, Mutane ne cike a cikin su suka firfito suka nufe shi ko wanne yana mishi congrats

Hannu yake basu fuskar sa a washe yana amsa musu

Abdul ne ya iso wajen yana son mishi magana

Dole ya ɗau excuse a wajen su ya matsa zuwa wurin shi

Nan Abdul ɗin ya sanar mishi, "Momy ce tace a sanar mishi akwai girkin da ta shirya musu shi da abokan shi zuwa bayan sallan isha'i."

Murmushi yayi cike da farin ciki ya gyaɗa mishi kai kana yace, "ok insha Allahu zamu yi ƙoƙarin zuwa, ka sanar mata zuwa ƙarfe goma zamu zo."

Abdul ɗin amsa mishi yayi ya juya ya tafi

   
Shi kuma ya koma cikin mutanen suka ci gaba da gaisawa. Kana kuma suka ɗunguma gaba ɗaya suka fice a motocin su, while Umar Faruk Yana a cikin nashi tare da securities ɗin shi da suka bi su a baya.
[14/10, 9:56 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*



*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._



















*NO_24*


*WASHE GARI*
"I want you to tell me about your country, because I also want to go abroad, especially to the Arabian Peninsula." Cewar Laɗifa tana murmushi

MEEMA wacce take latsa Laptop, ɗago Kai tayi ta kalle ta da murmushi a fuskar ta, a ranta Habibah kawai ta faɗo mata a rai. "Ok, I'll tell you, but not now. We have a lot of work to do now."

Ɓata fuska Laɗifa tayi tana miƙa tare da kwantar da kanta a saman kujeran da take zaune, sai kuma tace, "I'm very tired too, and I'm hungry so we should go and get something to eat."

Hannun ta MEEMA ta ɗago tana duban agogo sai ta mayar da idanuwan ta a a kanta tace, "It's 12:40 pm. Stay tuned."

"No now we're going. I'm tired of work." Ta sake faɗa tana miƙe wa. Sai ta saka hannu ta rufe Laptop ɗin gaban MEEMAN tana cewa, "Get up and let's go please. I'm very hungry."

Shigowar Idris yasa MEEMA tayi shiru bata ce komi ba

Shi kuma kallon su yayi, sai kuma ya kama haɓa yana mayar da idon sa kan Laɗifa yace, "ke kuma fa? Where are you going when you get up?"

"Wlh Brother na gaji yau yunwa nake ji kamar ban ci abinci ba."

Hararan ta yayi yace, "kin gan ki? Na kula ke acici ne wlh. Ok, let's get up and eat now."

Washe baki Laɗifa tayi tace, "yauwa ko kai fa Yayan mu."

MEEMA tashi tayi itama ta bi bayan su suka fice. A motan Idris ɗin suka ƙarisa restaurant da suke shiga cin abinci. Kowa yayi odan abinda zai ci suka zauna suna ci suna hira. Ƙarfin hiran duk Idris ne yana basu labari suna dariya, kasancewar sa me son Wasa da dariya shiyasa ko baka yi ninya ba sai kayi dariya idan har yana baka labari. Da suka gama suka koma wajen aiki. Sai three O'Clock suka tashi kamar ko yaushe, Idris ya ɗauki MEEMA suka wuce gida

Suna zuwa layin gidan su suka ga motoci kusan biyar a jere, sai wasu masu baƙaƙen kaya da alamu securities ne

"It looks like something is being done here." Cewar Idris yana faka motan shi daga bakin Gate ɗin su

MEEMA bata ce komi ba illa kallon wajen da take yi, sai kuma ta juyo da kallon ta gare shi tace, "And who are these people?"

"I don't know MEEMA, but I think someone came here."

"Ok." Tace tana ɗaukar jakar ta. Sai da tayi masa godiya sannan ta buɗe motan ta fice

Shi kuma ya danna horn me gadin su ya buɗe mishi ya shige

MEEMA da ƙafa ta taka zuwa bakin Gate ɗin su ta shige ciki. Tana isa bakin ƙofan parlour zata buɗe sai Uncle Hashim ya buɗe suka fito shi da Umar Faruk. Da kallo ta bi su tana ɗan matsa wa baya

While they are also watching her

"My daughter are you back?" According to Uncle Hashim he was smiling at her

Itama murmushin tayi tana gyaɗa masa kai don she could not speak

Uncle Hashim kallon Umar Faruk wanda idanun sa ke kan MEEMA yayi yace, "this is MEEMA, the Aunty's girl."

"Really?" He asked looking at him

"Yes. She is back here to stay." Sai kuma ya kalli MEEMAN yace, "My daughter this is my friend, my best friend, his name is Umar Faruk."

MEEMA kallon shi tayi ta ɗan yi murmushi kaɗan tare da cewa, "Hello Uncle."

"How far?" Yafaɗa shima yana kallon ta

"I'm fine." Sai kuma ta kalli Uncle Hashim tace, "Uncle I'll go inside."

"Ok daughter. Let me accompany him outside."

Kanta kawai ta jinjina mishi tana wuce wa ta shige ciki

Su kuma suka taka suka nufi waje. Sai da suka fita suka tsaya a bakin Gate ɗin

Umar Faruk yace, "but I know this girl, kwanaki ta zo gida na."

"Haba dai? To wa ta sani a gidan?" Uncle Hashim yafaɗa da mamaki

"Sun zo ne ita da wata, amm.. ina ga From t.v I see they come."

"Ok I understand. Tana aiki ne a gidan t.v ai, but Dude I'm wondering if I'll give it to you? Don kallon da kake mata I think kana ciki ne." Yafaɗa yana dariya

Shi kuma murmushi yayi da cewa, "kai halin ka na nan ko? Baza ka sauya ba, dama aka ce idan ka rabu da ganin mutum kar ka tambayi idan ya canza, domin halin shi na nan."

Murmushi Uncle Hashim yayi yace, "Allah da gaske nake yi, ka san daughter na ce kuma wlh kun dace sosai. Tunda naga ka ƙi sake aure tun tafiya na ga shi har yanzu kana nan a haka, na san yanzu ai Yusra ta girma sosai tunda tana shan nono muka rabu."

"She's grown up, now she's in school too."

"Allah Sarki Yusra da Hafsah, insha Allahu I will come in and see them later, zamu gaisa da Momy ai".

"Allah ya kai mu." Sai ya ba shi hannu suka gaisa suna wuce wa wurin motan. "But will you stay here for two days?"

Uncle Hashim yace, "insha Allahu. Zan yi two weeks ni gaskiya, sai dai Jalila za su koma tunda akwai school ɗin Habeeb."

Daga nan sallama suka yi ya shiga motan da ɗaya daga cikin securities ɗin ya buɗe mishi

Har sai da motocin suka tafi kafin Uncle Hashim ya shige gida. A haraban gidan ya tsaya yana amsa call, yana nan tsaye ne ya hangi wani guy yana shigo wa ciki, ganin ya dumfaro wurin shi sai ya katse kiran yana mayar da hankalin sa a kan shi, kallon sani yake mishi sai dai be ce komi ba har ya iso wurin shi, ya ba shi hannu suka gaisa kafin ya tambaye shi, "wane yake nema?"

Murmushi Sajjad yayi yana ɗan shafa kanshi kamar yanda ya saba yace, "suna na Sajjad Aliyu, ni ɗa ne wajen Kawu Faruk surukin nan gidan."

Tabbas sai a yanzu ya gane fuskar MEEMA yake gani a tare dashi, sai ya washe baki yace, "ah kace daga Yola kake? You Are welcome, let's go inside."

Sajjad bin Bayan shi yayi har cikin gidan

Sai dai babu kowa a Parlour, sai yace mishi, "ya zauna bari ya kira mutanen gidan." Ya wuce ciki. MEEMA ya fara kira sannan ya kira Ummee, ya shiga ɗakin Hajiya ya gunguro ta suka fito

Tunda MEEMA suka yi ido huɗu da Sajjad ai sai ta ja ta tsaya daga inda take ta kasa ƙarisowa

Shima haka yana ganin ta ya miƙe tsaya idanun sa ƙyam a kanta nan da nan farin ciki ya cika shi da ganin ta

Fitowar Uncle Hashim tare da Hajiya ya kalle ta yace, "let's go daughter." Sannan ya wuce

Ummee itama sai a lokacin ta fito suka zauna a kan sofa

"Ka zauna mana." Uncle Hashim yafaɗa yana kallon Sajjad ɗin

Babu musu ya zauna. Sai kuma ya fara gaishe da su

Ummee da ke mishi kallon sani tace, "kamar na so in Gane ka? Sajjad ko?"

Murmushi yayi yace, "Yes Ummee Ni ne."

"Ikon Allah kai ne a nan? Kai da wa kazo?" Tafaɗa da mamaki

"Ni kaɗai."

Murmushi tayi sai kuma ta kalli Hajiya tace, "Hajiya wannan ɗa ne wurin miji na, mahaifin shi Yayan Faruk ne ai."

"To Masha Allah, sannu da zuwa, ki ce ɗan uwan MEEMA ne ai, Ga kamanni wlh." Tafaɗa cike da fara'a

Uncle Hashim yace, "to ai ga daughtern can ta ƙi ƙariso wa." Sai ya ɗaga murya ya kira ta

Dole a yanzu ta iso wurin sai dai fuskar ta a ɗaure tamau tana kallon Sajjad ɗin

"Daughter do you recognize him? This is your cousin". Cewar Uncle Hashim Yana murmushi

"Na'am. I recognize him Uncle, But what did he come to do here? I don't want to see him."

Mamaki duk kan su suka yi da maganar ta

Musamman Ummee da ta san zai yi wuya MEEMA ta gane Sajjad, kasa shiru tayi tace, "How come you know him after you've never seen him?"

Cikin muryan kuka da ya ƙwace mata tace, "When I landed here country I went to their house and stayed. They wanted to marry me without my knowledge. One day before we were to get married I knew. That's why I came here. And I don't want him, I hate him so much."

"Subhanallah.. married again? Don't you know?" Hajiya tafaɗa da tsantsan mamaki

Itama Ummee kalman auren ta sake maimaita wa fuskar ta cike da damuwa

Sajjad da kanshi ke ƙasa ya kasa cewa uffan

Sai Uncle Hashim da ya tashi a zuciye yace, "kai tashi ka kama hanya ka bar mana gida, nan ba wajen zaman ka bane..."

Hajiya ce ta katse shi da cewa, "a'a Hashim ai baka san me ya kawo shi ba, kuma kana da tabbacin da laifin shi ne?"

"Da laifin shi mana Hajiya, ba shi ne wanda za'a ɗaura mishi aure da ita ba ba bare da amincewar ta ba? Don kawai zalunci, dama ai ba ƙaunar ta suke yi ba kuma mun san da haka, tabbas akwai abinda yasa suke son yi mata aure ba tare da amincewar ta ba, wato auren dole suka so suyi mata?" Yafaɗa a fusace

Da gudu MEEMAN ta isa wurin Uncle ɗin ta rungume shi tana kuka

Hakan ya ƙara hassala shi yana kallon Sajjad ɗin da cewa, "kai baka ji me nace maka bane? Ka tashi ka bamu wuri ka koma inda ka fito tunda baku da mutunci."

Cikin hawayen da suka kufce mishi Sajjad ɗin ya zube a kan gwiwowin shi yana roƙon su da Allah, "su bar shi a nan ya zauna, wlh yana tsananin ƙaunar MEEMA bazai iya rabuwa da ita ba..."

Katse shi yayi da cewa, "tashi nace, wlh ka bari na sake maka magana sai dai uwar ka ta haifi wani a gidan nan."

Su Hajiya sun san halin Uncle Hashim akwai zuciya ba ya son raini, dama dalilin da yasa ya shiga aikin soja kenan domin akwai shi da zuciya sosai idan ranshi ya ɓaci. Dole Hajiya ta soma rarrashin sa da cewa, "ka ga Hashimu kayi haƙuri ya fita a hankali kar kayi masa wani abun kaji ko?"

"To Hajiya uwar me yake jira da bazai fita ba?"

Duk hayaniyar Uncle Hashim ɗin ne ya fito da su Jalila da Zabba'u suka zo suka tsaitsaya suna kallon ikon Allah

Sajjad ba don ya so ba ya tashi ya fice yana sharan hawaye

Zabba'u da ita ce bakin ta ke ƙaiƙayi take bin ba'asin me ya faru. Sai da aka sanar mata sannan hankalin ta ya kwanta. Sai kuma ta koma tana faɗan albarkacin bakin ta, sai tsiya take yi tana faɗin, "ai wannan mugunta ne ace zasu yiwa yarinya aure ba da amincewar ta ba, haka ake yi ne?"..

Shi kuwa Uncle Hashim tuni ya ja hannun MEEMA zuwa ɗakin ta, a can ya rarrashe ta domin kuka take ta yi sosai ta kasa yin shiru. Sai da ya kwantar mata da hankali kafin ya fito ya yiwa su Hajiya sallama a kan, "zai je gidan abokin shi." Ya fice

Su kuma sai mayar da zacen suke yi, daga ƙarshe kuma suka koma hira.

The following day. Lokacin Hajiya na zaune a ɗaki tana lazimi Uncle Hashim ya shigo ɗakin duk a rikice. Kallon sa tayi tana tambayar sa, "lafiya Hashimu wani abun ne ya faru?"

Sai da ya zauna a kan sofa ya gaishe ta kafin yace, "wlh Hajiya babu lafiya, ina zaune a ɗaki aka kira Ni ake sanar min Umar Faruk yayi hatsari jiya da dare."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. a garin ya ya? Da sauƙi dai ko?" Tafaɗa itama a rikice

"To Hajiya ban sani ba wlh, sai dai idan na je yanzu zan gani."

"Subhanallah.. ai ba kai kaɗai zaka je ba, mu tafi gaba ɗaya, Allah sarki jiyan nan fa ya zo gidan nan, yanzu da ace mutuwa ce sai dai mu ji an ce ya mutu, oh Allah! Allah yasa dai ba magauta bane domin dama duk wanda ya shiga siyasa ai baza a raba shi da su ba."

"Haka ne Hajiya. Nima wlh Ina tunanin haka." Yafaɗa fuskar shi duk a dame

"To ka jira Ni bari in Yi wanka. Ka turo min Zabba'u da Allah."

Yace, "to." Yana miƙe wa ya fice. Sai da ya je ya sanar wa Zabba'u wacce take kichen tana haɗa kumallo kafin ya nufi Steps zai haye

A lokacin ne MEEMA ta fito daga ɗaki a cikin shirin ta na zuwa Office. Ganin shi yasa tayi saurin ɗaga murya da cewa, "Uncle good morning."

Tsaya wa yayi ya juyo. "Ah ah my daughter. You wake up?"

"Na'am Uncle." Tafaɗa tana Isa wurin shi. Ta kama hannun shi tayi masa kiss tana kallon shi

Shi kuma ya shafa kanta yana murmushi da cewa, "Do you go to work?"

Jinjina masa kai tayi tana mayar mishi da martanin murmushin

"Ok. Let's go out together I'll drop you off at work. We're going to greet my friend who came here yesterday. It had an accident last night."

Waro ido waje tayi da cewa, "This one we greeted yesterday?"

"Yes daughter."

Fuskar tausayi tayi tace, "eyya. God forbid. He don't hurt?"

Sai da ya riƙe hannun ta da alamun rarrashi yace, "insha Allah It's easy for him, will you go and greet him?"

Gyaɗa kanta tayi don ta kasa magana, haka kawai taji gaban ta na faɗuwa while idanun ta sun cika da hawaye

Ganin yanda ta koma sai yayi murmushi yana cewa, "You Care about him?"

Still gyaɗa mishi kai tayi don ta kasa yin magana, sosai bakin ta yayi mata nauyi

"Ok let's go to my room, don't worry ok? Insha Allah he will be fine."

Hannun su a saƙale da juna suka wuce sama. Ɗakin Ummee yayi Nocking still Yana riƙe da hannun MEEMA

Tana buɗe wa suka haɗa ido da MEEMA

Ita kuma tayi saurin ɗauke kanta tana sake haɗe kyakykyawar fuskar ta

Ummee yanda ta ga MEEMAN ne yasa ta tambayi Uncle Hashim bayan ta amsa gaisuwar shi. "Me ya sami MEEMA kamar akwai wani abun da ke damun ta?"

Sai da ya ɗan kalli fuskar ta kafin yace, "eh Aunty, na sanar mata da hatsarin da Dude yayi ne shi ne duk ta shiga damuwa. Dama shi na zo faɗa miki Umar yayi hatsari jiya da dare."

"Subhanallah.. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. da sauƙi ko?"

"I don't know aunty, Amma Hajiya tace mu shirya gaba ɗaya sai mu je mu duba shi."

"Ok to bari in shirya." Tafaɗa tana koma wa cikin ɗakin

Shi kuma ya ja hannun MEEMAN suka wuce nasu ɗakin

Shigan su ɗakin Jalila ganin su tare yasa ta washe baki tace, "oh yau tare kake da daughtern taka har nan?"

Murmushi yayi yana zama a gefen Habeeb

While MEEMA na tsaye. Sai ta gaishe da Jalilan tana ɗan sakin fuskar ta

Habeeb da sauri ya taso ya rungume ta yana kiran ta da, "Aunty."

Hakan yasa ta saka hannu ta sake rungume shi tana mishi magana

While Uncle Hashim kuma yana sanar da Jalila abun da ke faruwa. Sannan ya sanar mata, "ta shirya su je duba shi".




MEEMA tana tare da su har suka shirya sannan suka sauko ƙasa. Tun suna yin Breakfast gaba ɗaya ta sauya, abincin kawai take ci hankalin ta ba ya jikin ta, haka kawai a zuciyar ta ta ƙosa ta je ta ganshi, duk ta damu fatan ta Allah yasa yana ƙoshin lafiya. Babu abinda ke mata gizau sai kyakykyawar fuskar shi, ita kanta mamakin yanda ya tsaya mata a rai take yi, amma kuma gani take yi tausayin sa ne ya shige ta kasancewar hatsari yayi, Allah-Allah take yi su tafi






Da suka tashi tafiya mota biyu suka cika suka tafi asibitin da aka ce yana can.


[14/10, 9:58 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                        💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



                 *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._



                *NASIHA*
_Duk wanda ya karya ginshiƙin addinin sa, duk wanda ya bijire wa umurnin mahaliccin sa, duk wanda ya saɓa wa koyarwar Annabin sa wanda aka aiko shi ya kasance jagora ga al'umma, duk wanda ya ji kalmomin Ubangiji da suke gaya masa me ya kamata yayi ya kuma fahimce su amma duk da haka ya dage a kan hanyar tsageranci da hamɓare su, duk wanda yake fankamar shi ya fi ƙarfin ya bauta wa Allah Ubangijin sa, to, duk wani horon da ya same shi bai yi yawa ba. In ya tsaya tsaf ya ƙi yin Sallah lalle ya fita daga daular Islama kuma ba shi da damar ya kuka da hukunci da ya dace da shi Kamar dai yadda Alƙur'ani yayi bayani. Allah yasa mu dace._

















                             *NO_25*

                A haraban Hospital ɗin suka tsayar da motocin kafin suka fito. Uncle Hashim ya fito da Hajiya ya zaunar da ita a wheelchair ɗin ta, sannan sai Zabba'u ta tura ta suka yi cikin asibitin. Tun kafin ma su tambayi ɗakin da aka kwantar da shi suka hango securities a gaban wani ɗaki. Hakan ya tabbatar wa da Uncle Hashim nan ne ɗakin da Abokin shi yake. Can ya nufa suka take mishi baya

Securities ɗin tsayar da su suka yi suna tambayar, "ina zasu je?"

Uncle Hashim ne yayi musu bayani

Kasancewar sun gane shi yasa suka bar su suka shiga

A ɗakin daga Momy sai Abdul ne zaune sun tasa Umar Faruk a gaba gunun tausayi, kai kace sun damu da shi ne a yanda suka nuna, musamman ma Momy wacce gaba ɗaya idanun ta sun jiƙe da ruwan hawaye sai kai gyalen

Please Login or Register in order to submit comment