Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwance kamar ko yaushe, sai dai yanzu an rigada an kashe masa t.v'n idanun sa a lumshe suke. Muryan ta da ya ji yasa ya buɗe idanun yana sauke wa a kanta, yalwataccen murmushi ya sakar mata yana mata alama da ido a kan, "tazo gare shi".

Da sauri ta iso tana me duƙa wa a gaban gadon tare da sanya hannayen ta biyu ta riƙo nashi duka, da raunanniyar fuska take kallon shi kamar wacce zata saki kuka

Sai ya janye hannun sa ɗaya ya shafa kanta still Yana murmushi yace, "Alfu mabruùkin ya Ummy, Baárakil lahu fií hayaátiki, jazaákumul lahu aksara min zaliki watamjudniy". ("ina taya ki murna Ummy, Allah yayi ma rayuwar ki albarka, Allah yasa ki fi haka ya ɗaukaka min ke".)

"Amin Abee". Tafaɗa tana me kwantar da kanta saman ƙirjin sa zuciyar ta na farin cikin addu'ar da yayi mata wanda har sai da hawaye suka watso a saman kuncin ta

Shafa kanta kawai yake yi yana murmushi ba tare da ya sake cewa komi ba. Sun ɗau lokaci a haka kafin ya kira sunan ta, "Ummy".

"Na'am Abee". Ta amsa mishi ba tare da ta ɗago ba

"Al'aán ba'ada an tahaƙƙaƙu hilmaki fiì tusbiha suhfiìyan, kana haáza hilmaki daá'iman, al'aàn ba'adi inyihaá'i baƙiìyatiz zawaáj, uriduki an tatazauji hatta yahda'a ƙalbiì fiì kulli marrati azhaba fiìhaá ilal firaásh, uriduki an tahdira khaɗììbaki watatawaƙƙafu anil tahaddas ila waálidihi". ("Yanzu burin ki ya cika kin zama Ƴar jarida, mafarkin ki kenan a koda yaushe. Yanzu saura aure ya rage zaki yi, ina son inga kin Yi aure domin zuciya ta zata fi kwanciya a duk sanda na tafi na barki, ina son ki fito da wanda zaki aura mu tsayar da magana da iyayen shi".)

Saurin ɗago da kai tayi tana kallon sa, nan da nan hawayen ta suka ci gaba da kwaranya, cikin amon muryan ta dake fita da rawa tace, "Laá Abee, la astaɗiìu an atazauja wa'azhaba wa'aƙuùla wadaá'an, laá yumkinuniìl zahaábu li'aƙuùla wadaá'an fiì haálatil mardi haázihi, laƙad saámahtu zawaáji Abee, lan atazauja hatta tatahassana". ("A'a Abee. Bazan aure in tafi in barka ba, bazan iya tafiya in barka a wannan halin na rashin lafiya ba, na yafe aure Abee, bazan yi aure ba har sai sanda ka samu lafiya".) Sai kuma ta fashe da sabon kuka tana me riƙo hannun sa sosai tace, "Abee Ummee... She's going.. and..." harshen ta kawai ke motsi ta gaza furta abin da take son furta wa saboda yanda wani abu me ƙunci ya tokare mata maƙogwaro

Shima Abee tuni ya soma zubar da hawaye, ya saka hannu ya kwantar mata da kanta a saman jikin sa yana rarrashin ta, "Aásifa". Kawai yake iya furta wa shima a laɓɓan sa zuciyar sa na masa ƙuna, shi kaɗai ya san me yake ji a wannan lokacin daure wa kawai yake yi

A haka suka kasance har barci ya ɗauki MEEMA a wurin

Numfashi yaja yana me lumshe idanuwan sa, jikin sa rawa yake masa ga azaban zafi da yake ji, gaba ɗaya yau ba ya jin daɗin jikin sa, daure wa kawai yake yi saboda yau ranan murna ce ga Ɗiyar sa, ba ya son ko kaɗan ya ya ɓata mata wannan ranan me muhimmanci.



            Nurse Zara ce ta shigo tace masa, "time to take his medicine". Haka ta ba shi maganin ta fice

Dayake akwai na barci sai ya samu barcin ya sure sa.



           Sanda MEEMA ta farka ana kiran magriba ne, ganin Abee na barci sai ta miƙe ta wuce ɗakin ta, sallah ta gabatar kafin tayi wanka ta shirya cikin kayan barcin ta, riga da wando masu ruwan Powder and dressed less, ta sauko ƙasa ta zauna a kan dainning, sosai take jin yunwa shiyasa taci abincin da yawa, ta miƙe ta nufi ɗakin Abee

Har a lokacin be tashi ba domin a time ɗin jikin sa ya yi zafi zau, shiyasa Nurse Zara take gasa mishi jikin a time ɗin domin ta shafa masa magani

Da kallo MEEMA take bin ta dashi tana sake tamke fuska, ko sannun da tayi mata bata amsa ba sai ta jeho mata tambayar, "He hasn't gotten up yet?"

"Yes, he don't get up".

Tsaya wa tayi kawai a wurin tana naɗe hannayen ta a ƙirji ta kafe su da idanu, bata jirga a wajen ba har sanda Nurse Zara ta gama duk abinda zata yi masa kafin ta fice, sai ta taka a hankali ta isa bakin gadon ta zauna, hannu tasa a hankali ta kamo nashi tana tamke wa a cikin nata, shiru tayi tana bin sa da kallo zuciyar ta a raunane, sai kuma ta matsa setting kanshi ta saka hannu tana shafa mishi gashin kanshi, nan taji kamar da zafi jikin sa, taɓa wuyan sa tayi taji da ɗumi sosai, lokaci ɗaya ta lumshe idanu hawaye na saukar mata a fuska, sai ta buɗe tana bin shi da kallo tana tamke bakin ta don hana bayyanuwar kukan da ya taho mata. Kanta ta ɗaura a ƙirjin sa ta ƙanƙame shi. A haka ta kwana a jikin sa ko runtsa wa bata iya yi ba

Ko sanda Nurse Zara ta dawo duba sa a cikin daren, ganin ta yasa ta koma taje tayi barcin ta tunda ta san tana tare da shi.



             Sai asuba MEEMA ta tashi ta koma ɗakin ta, lokacin barci sosai ne a idanun ta sakamakon kwana da tayi bata runtsa ba, sallah tayi ta nema wa Abee ɗin ta sauƙi a wurin Allah, kafin ta haye kan gado barci ya sure ta.



               Sai 12:30pm. Ta farka, da mafarkin mahaifin ta ta tashi shiyasa duk jikin ta ya mutu, bata iya taɓuka komi ba ta fito ta sauka ƙasa don duba lafiyan sa, tana shirin shiga Likitan sa dake zuwa duba sa ya fito daga ɗakin, hakan yasa gaban ta ya faɗi ta nufe sa da sauri kamar zata faɗa kansa idanun ta ware a kansa tace, "Doctor what's happened?".
[08/10, 2:54 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                   💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍




*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*




              *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._














                 *NO_9 & 10*

               Sai da ya gyara wa eyeglasses ɗin sa zama kafin yace, "calm down please let me explain".

"No Doctor what happened to my Dad?" She asked him again with a smirk

Numfashi ya ja kafin yace, "Your father is very sick. We have to take him to the hospital because he needs to be examined. He needs special care."

Hawaye ne kawai ke zirya a kan fuskar ta ta gaza ma magana

Hannu yasa a kafaɗan ta yace, "Calm down MEEMA insha Allahu he will get up he will be fine".

Idanun ta kawai ta lumshe still hawayen ciki na tsiyaya, sai kuma ta buɗe su tana shirin wuce sa ta shiga ɗakin

Sai ya tsayar da ita yana faɗin, "No, don't come in, let's get an ambulance now and we'll pass, Sorry ok?"

Bata bi ta kanshi ba ta buɗe ƙofan ta shige, wajen Abee ɗin ta da idanun sa ke rufe yana fitar da numfashi daƙyar ta nufa, Kasancewar doctor yayi masa alluran barci sabida a samu a kai shi Hospital ba tare da wani problem ba. A hankali ta zame a wajen tana riƙo hannayen sa, cikin kuka daƙyar ta kirayi sunan sa, sai dai ta kasa yin maganar dole tayi shiru tana danne bakin ta, ɗaura kanta tayi a cikin sa tana ta shashsheƙan kuka.


              A haka aka zo da ambulance aka ɗauke shi suka wuce Hospital ɗin

Gaba ɗaya MEEMA ta gaza nutsuwa sai kuka take yi, duk rarrashin da Doctorn yayi mata kafin su shiga duba Abee amma ina taƙi yin shiru, haka ma Nurse Zara tana tare da ita tana faman rarrashin ta amma ina taƙi shiru, dole ta tafi ta barta a wajen tana ta sintiri duk ta gaza zama, gaba ɗaya idanuwan ta sun yi jawur sun kumbura suntum, kallo ɗaya zaka yi mata ka gane tana a cikin tashin hankali domin hakan ya gaza ɓoyuwa a kyakkyawar fuskar ta

Daga baya ne House Girl ɗin su ta zo shi ne suka zauna tare har sanda Doctorn Abee ya fito

Da gudu ta isa wurin sa tana kuka tana tambayar shi jikin Abee ɗin

Cike da tausayin ta yace, "I'm so sorry MEEMA: Just be patient. As your father is in a difficult situation, we will have to wait and see what the situation will be like."

Jiri ne ya kusa kwasar ta sai house Girl ɗin su tayi saurin tare ta ta faɗa jikin ta, kuka sosai take yi tana son tsaya wa da ƙafafuwan ta amma ina ta gaza, dole sai da taimakon House Girl ɗin su dake riƙe da ita ta iya tsayuwa. Cikin kukan take cewa,
"Doctor help my father please, I love him I don't want to lose him, please help me don't let him go". Break the words and burst into tears

Rarrashin ta kawai yake yi yana bata baki, dole yace wa House Girl ɗin, "she holds her and passes her to his office".

Haka suka wuce can ta samu ta zauna

Nan yace mata, "Now they put oxygen on him and he is asleep, or later she will check on him. But she calms down and nothing will happen. He will be fine soon."

Har ya fice bata iya magana ba, a haka suka zauna a Office ɗin har zuwa yamma babu abinda ke tayar da su sai sallah, gaba ɗaya ita MEEMA ta gaza saka komi a cikin ta illa kai kukan ta wurin Allah da take yi, after dress ɗin ma da ta sanya a jikin ta take sallan House Girl ta koma ta ɗauko mata a gida, don daga ita sai kayan barci ta zo, kuma duk rarrashin da tayi mata taci wani abu ta ƙi magana bare ta kalle ta, duk tayi wani zuru-zuru da ita fargaba da tashin hankali yasa ta fita hayyacin ta, mahaifin ta kawai take burin ta gani yanzu.


             Sai bayan magriba ya farka likitan ya zo ya sanar mata don ta je ta duba sa

Shima Abee ɗin tunda ya farka ya nemi a kira ta

Da gudu tabi bayan Nurse Zara da tayi mata jagora zuwa ɗakin da Abee yake ciki. Tana shiga ta ƙarisa wurin sa da sauri tana me kiran sunan sa a lokaci ɗaya hawaye na kwaranya mata, Abee.." ta sake faɗi bakin ta na rawa

Idanun sa ya sauke a kanta yana mata murmushi

Hannu tasa ta riƙe nashi tana me sake kiran sunan sa da cewa, "Abee, please recover. Abee I need you in my life. I love you so much. I don't want you to leave me. Please get up."

Daƙyar ya iya furta, "Ummy sickness and death all belong to God, I have no power to continue living except the one God has chosen for me". Sai ya tsakaita kafin ya sake sakin murmushi zuciyar sa na ƙuna da ganin tana hawaye be da yanda zai yi ya share mata. Ya fito ta yayi alamun ta matso

Da sauri ta matso sosai tana me ɗaura kanta a jikin sa

A hankali ya soma raɗa mata magana cike da rauni wanda daƙyar yake furta kalaman

Ita kuma sai zubar da hawaye take yi har sanda ta kasa jure wa da kalaman nasa ta hau girgiza masa kai tana cewa, "laà Abee I can't.." abinda take iya furta wa kenan tana kuka sosai

Shi kuma lumshe idanun sa yayi while hawaye masu zafi suna sauko masa a kunci. Yana riƙe da hannun ta gam ya ƙi saki

Ita kuma sai kuka take faman yi

Sai da Nurse Zara ta shigo ta janye ta kafin ta samu ta fita tana me sake ɓarke wa da wani sabon kukan, a jikin ƙofan ta zame tana kuka sosai duk fuskar ta ta sharɓe da hawaye tayi jazur

Me aikin su da Nurse Zara suka kama ta suka mayar da ita Office ɗin Doctor.



              Daga ranan kullum a cikin ƙunci da kuka take kwana, a kan sallaya take wuni tana sallah da roƙon Allah ya warkar da Abee ɗin ta, ko abinci ta dena ci sai an yi da gaske, a kuma asibitin take kwana ko jirga wa ba ta yi, kuma tun daga ranan ba'a sake barin ta ta duba Abee ba sabida ganin tana ɗaga hankalin ta, ga shi ciwon nasa yanzu yayi tsanani sosai.



           Five days after his arrival, he died at the hospital. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un bazan iya misalta muku tashin hankalin da MEEMA ta shiga ba, gau ta sume bata sake sanin inda take ba har sai da aka yi kwana uku da jana'izar shi, a ranan da ta farka ƙaramin hauka tayi musu a kan, "sai sun dawo mata da mahaifin ta," duk ta fita hayyacin ta tamkar mahaukaciya, da farko sun yi tunanin ta haukace ne ashe zafin rabuwa da mahaifin ta ne ya janyo mata rasa tunanin ta gaba ɗaya, sai da aka koma ɗaura ta a kan magani don abubuwan da take yi bata da maraba da mahaukata. Da ban baki da nasiha tare da treating ɗin ta har aka samu ta soma samun sauƙi

Likitan mahaifin ta shi ya ɗau ragamar komai na jana'izar Abee har aka yi aka gama lafiya, kuma ya samu mutane ba kaɗan ba sabida babban masallaci na garin Riyadh ɗin aka kai shi aka yi masa Sallah.




               Sai da aka yi kwana bakwai da rasuwan sa kafin aka sallami MEEMA. House girl ɗin su ita ke kula da ita domin tsananin tausayi take bata, ita take ta ɗawainiya da ita a asibitin har suka koma gida, a lokacin sam baza kace MEEMA bace sabida yanda ta sake rame wa tayi fari fat tamkar mara jini a jiki. Ko magana ba ta iya yi kullum sai zubar da hawaye, ta kasa yarda cewa Mahaifin ta ya rasu ya bar ta, har ji take yi a wannan lokacin gwara mutuwar ta da rayuwar ta, ta gummaci ta bi shi a irin wannan Rayuwar, a yanzu tana buƙatar mutuwar ta fiye da rayuwa, ta rasa komi nata, bata da kowa sai ita kaɗai, taya zata iya rayuwa a haka? Komi nata na farin ciki ya wargaje ya barta. Mutuwa shi ne ya fi cancanta a gare ta.




              Amma a haka babu gajiya house Girl ɗin ta take bata kulawa. Ita take lallaɓa ta ta samu ta ci abinci, sai ta kwana ta wuni daga ruwa sai ruwa take zuba wa a bakin ta, idan kuma ta matsa mata da cin abinci har marin ta take yi ta daka mata tsawa ta kore ta, amma kuma haka anjima zata sake kawo mata, da haka har ta soma shawo kanta wani lokacin ta ɗan kalle ta taci abincin, wani lokacin kuma idan ta birkice tayi ta zagin ta tana daka mata tsawa a kan, "ta tafi ta barta ko ta kashe ta, tana damun rayuwar ta," duk waɗannan abubuwan haka house Girl ɗin take iya ƙoƙarin ta wajen jure wa.




               Da haka kwanaki suka soma shuɗewa haka ma satikai, ga shi yanzu har an yi sati Uku curr da rasuwar Abee.



                  A wannan lokacin ne Ishaq ya zo gidan yin mata ta'aziyya, domin sai a lokacin yake jin labarin kasancewar ba ya ƙasar

Sanda ya shigo gidan da House girl yaci karo, ita tayi masa jagora har cikin ɗakin MEEMA kamar yanda ya ɓukata yana son ganin ta.



              MEEMA na kwance a saman faffaɗan gadon ta while ta tusa kanta a ƙasan pilow. Daga ita sai ƙaramar vest fara da leggings da iyakan sa gwiwowin ta shima fari

Ishaq da ya ƙariso ciki a hankali ya isa bakin gadon ya samu wuri ya zauna yana ƙure ta da kallo, shiru yayi na ɗan wani lokaci sai kallon ta yake yi kafin ya sanya hannu a bayan ta yana shafa ta tare da kiran sunan ta

Jin muryan sa tamkar a mafarki ya sanya ta ciro kanta da sauri tana ware manyan idanuwan ta da suka sake girma suka yi jawur sabida kukan da take wuni yi ko da yaushe. Kallon sa kawai take yi ba tare da ta iya furta komi ba daga bakin ta

Shi kuma sai ya sakar mata murmushi tare da mamakin sauyawan ta lokaci ɗaya haka, ya san tsananin ƙaunar ta da mahaifin ta dole zata shiga wani yanayi da rashin sa, shiyasa ya ji tausayin ta ya tsarga masa zuciya a lokaci ɗaya ya lumshe idanun sa yana me sake buɗe su a kanta tare da kiran sunan ta

Shiru tayi masa sai dai ta kasa ɗauke idanun ta a kansa

Hakan yasa yaci gaba da faɗin, "MEEMA sorry with the temptations that God has bound for you, or what life is mortal everyone will leave this world, I offer you my condolences for the loss of your father, may God have mercy on him and forgive him, I left that's why I did not come early I'm sorry".

Take ta mayar da idanuwan nata ta rufe su ruf hawaye na wanke mata fuska. Sai ta sanya tafukan hannayen ta ta rufe fuskar ta tana me fashe wa da wani sabon kuka wanda dama shi take jin yi amma ya gaza fito wa, but yanzu jin ana mata ta'aziyya sai kawai zuciyar ta tayi rauni sosai wanda hakan yasa kukan nata fito wa

Ishaq hankalin sa ya tashi sosai ganin kukan da take yi sosai, da sauri ya sanya hannayen sa ya cire nata daga fuskar ta yana bata haƙuri

Ita kuma idanun ta a rufe suke ruf ta kasa buɗe wa sai kuka take yi

Duk rarrashin ta da ya so yi ya kasa, dole ya zuba mata idanu har tayi ta gaji don kanta tayi shiru ta koma shashsheƙan kuka. Sai ya saki ajiyan numfashi yana cewa, "be patient MEEMA so your destiny has come, Abee needs nothing from you but your prayers, please refrain from him and pray for him with the hope of being right with the ya Rabbi".

Sai a lokacin ta buɗe idanuwan nata tana kallon sa da jinjina masa kai tana me ƙumshe bakin ta don hana kukan nata fita

Shiru ne ya gifta na ɗan wani lokaci kafin ya kalle ta yace, "Although I know you are now in a state of ecstasy and happiness, and I know my words will upset you but I have to do it, MEEMA a second time I beg you to agree to marry me, I desperately need you in my life, I know Abee's problem is why you abandoned my love but now I'm back I need your answer, I really love you MEEMA, I can't live without you, Abee is gone and you need me in your life, you can't live alone no marriage, think about it".

Har ya dire maganar sa bata ɗago ta kalle sa ba bare ya sa ran zata amsa mishi

Sai yace, "Please I beg you MEEMA to give me another chance to enter your life, I will give you back the happiness you lost, I will be your mother and father in your life, I will take care of you accordingly, you will be happy in your life insha Allah ok?"

Shanyayyun idanuwan ta ta ɗago ta kafa masa su, sai da tayi luu da su kamar zata rufe sai kuma ta sake ware su tana kallon sa, cikin sanyin muryan ta da ya disashe daƙyar yake fita ta soma magana a hankali, "I don't need to get married now in my life Ishaq, in fact I will return to Nigeria..."

"What.. What are you saying?" Yayi maganar da sauri yana katse ta

Sai da ta sauke ajiyan zuciya kafin tace, "I said I would return to Nigeria."

"No MEEMA why would you do that to me? Please don't go and leave me, what will you do in that country after this is your country? Please stay and live happily ever after, how do you think you will go and leave Me when I need you? Or do you just not loving me MEEMA? Tell me, have you ever loved me?"

Hannu ta sanya a goshin ta tana rufe idanu, still ta ware su a kansa cikin raunin murya tace, "I love you Ishaq, I personally don't go there because I don't like the people there, but I am going to Nigeria because Abee told me to go," sai ta fashe da kuka tana ƙara faɗin, "Abee told me to go there. He told me to go back and look for my mother. I never thought Abee would remember her again because of what she had done to him. She left us for a long time. she chose her life on her own, but Abee told me to go to her, and I didn't love her and I don't want to go.."

"So why don't you stay here and get married, why?" Yayi maganar kamar zai yi kuka yana dafa mata cinyoyi

Hannun nasa tabi da kallo sai kuma ta mayar da kallon ta a kan fuskar sa tace, "Ishaq I have to go, Abee says don't stay here and go back there, if I go Ummee doesn't answer Me and ask his relatives to stay there. I have decided not to go to Ummee but to go to my father's family and stay there." Sai ta riƙo hannayen nasa tana kallon ƙwayan idanuwan sa tace, "I love you Ishaq. If you really want me, we will live together. I will be with you wherever I go. We will get married."

"How do we get married?" Yayi maganar a hankali shima ya kasa ɗauke nashi idanun a cikin nata

"Make sure we are together, going there will not separate us, if you really want me to follow ME there and marry Me".

"What are you saying?" Yayi maganar yana me zame hannayen sa a cikin nata. "Ok I know. you want me to let everyone follow you there and get married?"
   

"No, I want you to go there and ask for my marriage. I don't have anyone here. You must follow me there and ask for my marriage."

Shiru yayi yana kallon ta, sai kuma ya tashi ba tare da yace uffan ba ya fice


Da kallo ta bi sa itama ta kasa cewa komi, har ya fice tana bin ƙofan da kallo.
[08/10, 2:56 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                   💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍




*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*




              *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._













                     *NO_11*

             A ranan da Abee yayi arba'in su Ummu Hani suka zo wajen MEEMA, dayake sun zo sun mata ta'aziyya tun ranan da yayi kwana ɗaya, a lokacin tana asibiti babu lafiya shi ne suka yi ta zarya ita da Esha har sanda suka zo ta farka suka yi mata ta'aziyya, basu sake zuwa ba sai yau ɗin da Zamiya zata zo tunda ita bata samu ta zo ba sai yau tace zata zo, zata yi kwana biyu before ta koma can Indian.



              Duk da MEEMA ba ta cikin walwalan ta amma ta ji daɗin zuwan su saboda sun ɗebe mata kewa sosai

Da jirgin Zamiya ya sauka drever MEEMA ta sanya ya ɗauko ta. Koda suka haɗu sai duk suka rungume juna cike da farin cikin sake haɗuwa wuri ɗaya.


"I'm so sorry MEEMA for

Please Login or Register in order to submit comment